Header Ads
Showing 69001 words to 72000 words out of 155363 words

Chapter 24 - SARAUNIYAR KYAU_Takun Farko _cmplt. By The Nainarh Kd -2-1.txt

Ads the beginning of article before Image

Nanah Kd   

14 Jun 2024

1028

Ads at the middle of Article

fararen haƙoranta...
Idan akace kyau a farko, tofah ana zuwa kan Afeefah Ɗiyar Mister Mai Kyau, an rufe ƙofa ita ɗin kyakyawa ce na first class, a ko'ina ta gama haɗuwa ni dai (Ɗiyar Mutanen Kd💃) nayi shiru a gefe ina zare ido da kallon zallar kyau.


Wani ƙayataccen abu tayi wanda ya daɗa burge mutane, hannu tasa a cikin ƴar ƙaramar tsadaddiyar jakar dake a hannunta ta ciro tsaleliyar wayarta wacca akalla ba'a kasara ba zatakai Ten million's naira a kuɗin Nigeria, camera ta shiga ta juya ta ɗauka selfie tare da mutanen da suke akan kujeru sannan ta kumayiwa kanta ita kaɗai sai da takai tsawo mintuna biyar ɗinta dai dai, sannan ta juya zata koma aikuwa nan gurin yayi tsit kamar mutuwa ta gifta da alama mutane basu so ta koma a yanzu ba, sai da takai dai dai wajen da zata koma ciki sannan ta juyo ta kuma watso musu sumba sannan ta shige ciki, cike da farin ciki bayan wasu sakanni sai ga wata ma ta fito.


Haka aka din gi yi idan wannan ta zo taci mintuna biyar ɗinta sai ta koma wata ma tazo taci mintuna biyar ɗinta a haka har mutane goma sukayi dama kuma su goma ne chas chass Ƴan Tawagar Gasar na Abuja.








Sai da cikon ta gomar ta koma sannan, Sandra ta dawo ta tsaya a tsakiyar floor ɗin, yanzu ma cikin harshen turanci ta fara magana kamar hakan👇


"Hi Hello Welcome Namaste (Da ya ke ita ɗin haifaffiyar Indiyace shiyasa yaren ta na TELUGU ya zauna a bakinta).. Barkanku dai masu kallo muna fatan wannan gasar na 𝔖𝔞𝔯𝔞𝔲𝔫𝔦𝔶𝔞𝔯 𝔎𝔶𝔞𝔲 𝑚𝑎𝑡𝑎𝑘𝑖𝑛 𝐽𝑎ℎ𝑎, tana burgeku da nishaɗantar da ku yadda ya kamata?."


Mutane gaba ɗaya aka amsa, sannan ta ci gaba da cewa "a halin yanzu duka ƴan matan gasa zasu fiffito a tare, ko waccensu ta tsaya a tsakiyar floor kamar yadda aka saba duk shekara, daganan kuma alƙalan gasa su fidda gwana zaqwaqwura ma'ana dai wacca ta sama nasarar (win) lashe wannan gasar na bana wato SARAUNIYAR KYAU💅





Ihu game da sowa na murnar maganarta mutane suka kuma saki maza da mata abin sai wanda ya gani.
Bayan wani lokaci gurin ya kuma yin tsit kamar ba wata hallita mai motsi a gurin, Sandra ta fara da ''one, two, three.!!"


Kafin ta rufe baki saiga ƴan matan su goma rhass sun fito a tare sun tsai tsaya a tsakiyar filin gasar.

Nan fa guri ya kuma tsit mutane ana jira aji hukuncin alƙalan ƙasa.





Akalla an kwashe sama da mintuna goma a haka sannan wata Kyakyawar Baturiya daga cikin alƙalan gasan ta miƙe tsaye cikin shigarta na tsadaddun suit na mata kuma na alƙalan fashion show, da alama ita ce chairlady, sannan ne kuma ɗayar baƙar fatar dake a kusada ita, ita ma ta miƙe tsaye ɗaukar abin magana (Micro Tone) baƙar fatar tayi sannan ta fara magana cikin harshen hausa, yawancin maganar nata akan dai gasan ne sai kuma ɗan flirting (Barkwanci) da take sakawa a zancen nata, daga ƙarshe dai ta rufe da faɗin.




"yanzu dai, bari na barku haka na koma mazaunina domin na bawa. Ƴar uwa Mrs William damar bayyana mana wacece zaqwaqwurar da tayi nasara a gasar SARAUNIYAR KYAU na bana😍




Dariya akayi sannan ta koma ta zauna..
Nan wannan Baturiyar ta ɗauki abin maganar sannan ta fara da nuna murnar ta akan gasar da dai sauran su, sannan ɗaura da faɗin.


"dai dai wannan lokacin zamu bayyana muku zaqwaqwurar wacca taci wannan gasar na SARAUNIYAR KYAU matakin jaha. Wannan Shahararriyar zaqwaqwurar dai ita ce! ita ce!! ita ce...!!"

Shiru tayi tana kallon mutane fuskar ta cike da murmushi kamar yadda zuciyoyin ƴan matan gasa take bugu da ƙarfi, haka ma zuciyoyin ƴan kallo maza da mata har dama ƙananan yara, zuciyoyin suke bugun wuce ƙima, hatta sauran mutane na duniya daga kan masu kallo a t.v show, da masu wayoyin hannu da dai sauransu, gaba ɗaya jira ake aji ko wacece tayi nasara ta zamo zaqwaqwurar shekara, {☆ nima dai ƚԋҽ Nαιɳαɾԋ ƙԃ da nake gefe nayi tsuru tsuru zuciyata bugu take na wuce ƙima saboda tsoro💔®}





Murmushi Mrs William tayi ta kuma kallon doguwar paper ɗin dake a hannunta, sannan ta ɗago kanta, ta kuma kallon duka kyawawan ƴan matan gasa waɗanda duka suma idanunsu yake akanta, amma banda Afeefah da tayi kamar batasan a halin da ake ciki ba, saima magana ta ido da takeyi ita da Zaynerb sai faman murmushi suke sakarwa juna.





Gyaran murya Mrs William tayi sannan ta kuma gyara zaman medical glass ɗin dake a fuskarta, sannan ta ce.
"ba kowa bace wacca taji gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha ma'ana tazo ta ɗaya kuma zaqwaqwurarmu fa ce 'MISS F££FAH MAI KYAU..." [dayake shine real name na ta a gasar😘].



Wani irin ihun murna gaba ɗaya mutanen gurin suka saka hadda masu fito (whistle) da masu rawa (dance) Deejarh saman kujerar da take kai ta hau tana faɗin.

"Kai yasin sai Balarabiyar India, Huh Huh ta zama SARAUNIYAR KYAU ta jaha Allah ya kaimu na ƙasa ma, yaƙini nake dashi akan cewa ita ce zata cinye huh hu oh sai Balarabiyar India😛."

Haka kawai Deejarh take faɗa cike da farin ciki, wayyo masu karatu kuzo kuga murna a wajen su Auntie Nainarh, Auntie Nailah, Haleesat, Zaynerb, Lailah abin ba'a iya cewa komai Mrs Mai Kyau kuwa komai faƙonka baka isa kace ga abin da ke a zuciyarta ba, ta dage tana taya murna😆








💋SARAUNIYA F££FA MAI KYAU💋


Kuwa wani irin rumshe idanunta tayi da ƙarfi, tana sauke ajiyar zuciya sam ko'a a tunani batayi tunanin zataci wannan gasar ba, tun daga lokacin da ta ɗaura idonta akan kyawawan ƴan matan gasan, a gaskiya wannan ranar ta zama ranar tunawa a rayuwar ta, ba za ta taɓa manta wannan ranar mai cike da tahiri a gurin ta ba, har abada. Habba ai abin akwai farin ciki kalan wanda alƙalami bazai iya rubutawa ba SARAUNIYAR KYAU fa ta jaha aiko anan kasuwa ta tashi ɗan koli yaci riba ba kaɗan ba. [sai dai mu zamu so kasuwa ta cigaba da ci domin sanin mai zai faru gaba, anan dai ga Afeefah taci gasan to ita Jieddarh fa😃]…





A hankali ta buɗe kyawawan idanunta waɗanda suka kawo ruwa saboda tsananin farin ciki, jin da tayi ana nemanta domin a bata kyauta, "au dama hadda wata kyauta ne, da za'a bada?." Ta tambaya kanta, sai kuma taba kanta amsa da "gashi kuma ana kirana nazo karɓa😇."



Sannu a hankali take taku yayinda zata ƙarisa gurin Sandra wajen karɓar kyauta, cikin takun jan aji da nutsuwa irinnata ta ƙarisa gurin sai da suka gaisa da Sandra, sannan Sandra ta ɗauko wani secret box wanda aka nannaɗeshi da wasu kyawawan igiyoyi na flowers ta miƙa ma ta, sannan kuma ta miƙa mata wani haɗaɗɗen fure mai fidda sassanyan ƙamshi na musamman. Afeefah harta juya zata tafi, Sandra ta ce

"bakiji ba."

Juyowa tayi tana kallonta fuskar ta cike da fara'a ta ce "ina jinki." Sandra ta ce "am very so sorry amma please zamu iya hoto a tare?."
Tayi maganar tana marairaicewa duk a tunanin ta Afeefah ba za ta yadda ba, sai kuma ta bata mamaki da cewa "ba damuwa zamu iya."

Murmushi Sandra tayi sannan ta ciro tsadaddiyar wayar ta a aljihun dogon crazy jeans ɗin dake a jikinta suka kafta selfie kala biyar da Afeefah sannan ta juya tana nunawa mutane kyautar da ta samu sannan ta koma gurin ta cike da farin ciki, sai dai wani ɓangare na zuciyarta bugu yake na rashin dalili, tun lokacin da magana ta haɗa ta da Sandra.





Mrs william tayi gyaran murya sai da ta jira mutane aka nutsu kowa ya koma ya zauna a mazaunin shi, sannan ta ce "malama Feefah Mai Kyau, gaba ɗayan mu alƙalan gasan muna tayaki murnar cin gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha, muna fatan zamu haɗu a gasar SARAUNIYAR KYAU matakin ƙasa nan da one month ko?."

Ƙayataccen murmushi Afeefah tayi daga gurin da take tsaye ta ɗaga kanta alamar 'E,👏💪💃







Mrs william tayi murmushi sannan ta ce "haka nakeson ji." sannan ta kuma nutsuwa ta ce "yanzu kuma zamu ji wacca tazo ta biyu."
Ƙara kallon doguwar paper ɗin dake a hannunta ta kumayi sannan tayi murmushi tana mai cewa.

"ba kowa ce wacca taci gasar SARAUNIYAR KYAU na jaha tazo ta biyu ma'ana dai zaqwaqwurar mu ta biya fa ce 'SAMEEHAH SALIS MAI NAIRA'...


Ihun murna masoyan Sameeha suka saka suna tayata murna, a hankali kyakyawar matashiyar budurwar da ba za ta wuce shekaru ashirin da haihuwa ba, take taku cike da farin ciki ta ƙarisa wajen Sandra suka gaisa, sannan ita ma aka bata kyautar secret box wanda aka rufeshi da igiyoyi, amma bai kai girman na Afeefah ba, sannan sukayi pictures kala biyar ita da Sandra kana ta juya tana nunawa mutane cike da farin ciki, sannan ta koma matsayarta ta tsaya kusada Afeefah murmushi Afeefah tayi ta ce cikin ƙasa da murya.

"Hi ina tayaki murna sosai, sannan naji daɗin haɗuwa dake highly."

Murmushi ita ma Sameeha tayi sannan ta ce "me too dear Feefah Mai Kyau." Dariya sukayi a tare.


Bayan gurin yayi tsit Mrs William ta kumayin gyaran murya sannan ta ce "malama Sameeha Salis Mai Naira, muna tayaki murnar zuwa ta biyu a gasar SARAUNIYAR KYAU na jaha."

"I really Appreciate highly Madam William." cewar Sameeha cike da farin ciki.💞


*💋💋𝑆𝐴𝑅𝐴𝑈𝑁𝐼𝑌𝐴𝑅 𝐾𝑌𝐴𝑈💋💋*


*👑𝑇ℎ𝑒 𝐺𝑙𝑎𝑚 𝑄𝑢𝑒𝑒𝑛👑*



*𝑊𝑟𝑖𝑡𝑖𝑛𝑔 & 𝑆𝑡𝑜𝑟𝑦 𝐵𝑦*

*𝐾ℎ𝑎𝑑𝑒𝑒𝑗𝑎𝑟𝑡ℎ 𝑆𝑎𝑏𝑖`𝑢 𝑌𝑎ℎ𝑦𝑎ℎ*



{♥︎𝑇ℎ𝑒 𝑁𝑎𝑖𝑛𝑎𝑟ℎ 𝑘𝑑♥︎}





💘*𝘓𝘈𝘍𝘈𝘡𝘐 𝘞𝘙𝘐𝘛𝘛𝘌𝘙𝘚 𝘈𝘚𝘚𝘖𝘊𝘐𝘈𝘛𝘐𝘖𝘕*💘🤙

<><><><><><><><><><><><><><<><><><><><><><>><><><><><><><

/𝐓𝐡𝐢𝐬 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝐈𝐬 𝐃𝐞𝐝𝐢𝐜𝐚𝐭𝐞𝐝 𝐓𝐨 𝐙𝐢𝐞𝐞𝐲 𝐌𝐮𝐜𝐡 𝐋𝐨𝐯𝐞🥰/


💄The Fashion Show💄




*Page 39&40*






"Zaqwaqwurar mu ta uku, kuma ta ƙarshe a wannan gasar na SARAUNIYAR KYAU matakin Jaha, ba kowa bace fa ce ABHI GAIL ELIAS, so that, muna gayyatar miss Abhi Gail, izuwa saman floor, domin ta karɓa gift nata na mussaman kuwa."



Da takun ƙasaita take tafiyar kyakyawar budurwa har ƙarisa gurin Sandra, sannan ta tsaya fuskar ta cike da annuri.
Haɗaɗɗen Diamond ring da chain ɗin shi suna shaining da ƙalli, Sandra ta miƙa ma ta tana mai tayata murna, cike da murna Abhi Gail ta karɓa gift ɗin sannan sukayi pictures kala biyu da Sandra kana ta koma ta tsaya kusada su Afeefah da Sameeha. (💋ZAQWAQWURAN MU💋)





Mrs William ta ci gaba da faɗin "munataya ku murna sosai kyawawan ƴan matan da suka sama nasara a wannan gasar, hakama sauran da basu sama nasara ba, muna tayasu jaje, sannan ku sakama ranku shekara mai zagayo daku za'yi."


Nan ta ɗan basu baki da tausasan kalamai. Dan kuwa babu daɗi mutum ya shiga gasa ko waca kala ce, ace bayyi nasara ba.

Tana kammalawa ta koma ta zauna, sannan ɗayar Baturiyar ita ma ta miƙe tayi taƙaitattun maganganu.


Sannan ita ma baƙar fatar cikon ta huɗun su, ta miƙe ta ɗanyi ƙarin bayani daga ƙarshe ta rufe da faɗin "muna yiwa kowa da kowa duka waɗanda suka halarci wannan special gasar muna godiya sannan kuma muna fatan kowa zai koma gidajensu lafiya kamar yadda kukazo lafiya."


Tana gama faɗin haka ta koma ta zauna daga haka taron gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha ta shekarar yazo ƙarshe, daganan mutane suka fara tashi ana watse wa, daga ɓangaren ƴan matan gasa kuwa, suma komawa sukayi ta gurin da suka shigo sannan jajayen labulayen gurin suka koma da kansu su haɗe.






💗Ahalin Mai Kyau💗





Tsaye suke gaba ɗaya a gurin da sukayi parking tsadaddun motocin su, daga harabar Hall ɗin na taron, suna jiran ƙarisowar Daddyn da kuma Sarauniyar wato Afeefah 😍



Lailah ta ce "a gaskiya wannan gasar ta ƙayatar dani sosai, da ace ina da account na Tik Tok ko kuma Facebook da Instragram dana ɗaura ɗaukar, saboda abin ya tafi yadda nakeso, especially ma da Afeefah tayi NASARA a gasar ga Kalar dressing ɗin da tayi ya tafi da mutane highly."


Zaynerb ta amshe da cewa "aha ƴar uwa, ai Lailah ina faɗamiki abin yayi yadda ya kamata Allah ya kaimu Gasar na matakin ƙasa, akwai ɗaukar SHOW kuwa, huh wayaga Afeefah Mai Kyau As Sarauniyar Kyau ta ƙasa huh The Glam Queen."

"Ina da tambaya, wai shin a'ina ne, za'ayi na ƙasa ɗinne, naji wannan Baturiyar ta ce 'nanda one month' amma bata faɗa ko'a ina za'ayi ba."




Deejarh tana dariya tayi musu tambayar, Lailah ta bata amsa da, "inaga a Lagos za'ayi, nanda wata ɗayar kamar yadda kikaji ta faɗa, muna fatan shima na matakin ƙasa ɗin ƴar uwanmu Afeefan mu ta lashe gasa."



Wani ihun murna Zaynerb ta saki da ƙarfi, a lokacin da ta duba wayarta taga abin da ke faruwa ciki faɗa take "muje zuwa Guys, aha ai yanzu aka fara gasar akwai na matakin Ƙasa yana nan tafe, ku saka ranku a inuwa." Ta ƙarishe faɗar hakan tana tsalle abin ta Like a Little Kid.😎









Har rige rigen ƙarisawa gurin ta sukeyi domin ganin abin da ke cikin wayar nata da ya sakata ihun murna a cikin mutane haka.

Tsakanin Haleesat, Lailah Deejarh.
Haleesat ce ta rigasu ƙarisawa don haka, wani cafka takaima wayar dake a hannun Zaynerb ɗin, saiga wayar a hannunta da sauri tayi unlocked na wayar tana dubawa, lokacin Lailah da Deejarh suma sun ƙariso gurin Lailah cikin haki abin ka da ba'a saba ba 😅



Cikin Tik Tok Account na Zaynerb ɗin, ta tsinci wayar, da sauri ta shiga duba videos na Show ɗin da Zaynerb ta ɗaura a Tik Tok Account ɗin nata, videos ne kala kala kusan kala goma. Na farko daga ciki ta shiga ta fara dubawa, cikin ƴan mintunan da Zaynerb ta saka Videos ɗin, har ta sama Likers kusan mutune fiye da dubu ɗari, ga ruwan Comments kala kala kusan na mutane dubu goma, Kai bama iyaka ƴan Najeriya ba kowa yaba wannan gasar SARAUNIYAR KYAU na garin Abuja yake kowa da abin da yake faɗa akai.💃💃







Kakkaurar ajiyar zuciya Haleesat ta sauke ta ce "A gaskiya wannan Fashion Show, Championship ya karɓu a gurin mutane sosai, duba fa, ki kalla yadda mutane maza da mata suke zuba ruwan like da comments kala kala a wannan videon."
Tayi maganar tana ƙarisawa gurin Momy Rafi'at ta miƙa ma ta wayar Zaynerb ɗin.
Da sauri Momyn ta karɓa wayar kamar mai jira ai nan take tahau washe baki tana yabawa.

Ita dai Zaynerb tana daga gefe tana kallon ikon Allah sannan kuma idan angama a bata wayarta.😂


"Kema Auntie Haleesat ina ce kin saka a Instagram Account ɗin ki ko?, ki duba mana domin muga halin da ake ciki."


Lailah ce tayi maganar cike da zaƙuwa game da farin ciki. Da sauri Haleesat ta saka hannunta a cikin handbag ɗinta ta ciro wayarta da ya ke babu Password kai tsaye Instagram ɗin ta ta shiga bayanta kunna Data.



Zaro ido tayi waje ganin uban likes da comments da take samu suna shigowa babu qaqqautawa. Dalilin ganin yadda Haleesat ta kasa magana ne gaba ɗaya, yasa Lailah ta karɓa wayar tana dubawa. Murmushi tayi ganin ashe anan Instagram manyan qwarin suke likes ne da comments kawai ake zubowa ta wayar Haleesat kamar kamar me.
Shiga tayi cikin wani Video akalla likes ɗin da Video ɗin ya samu sunkai one million a iya tunanin ta fa.😎




Ɗagowa tayi cike da farin ciki zatayi magana ta hango Afeefah da Daddyn suna tahowa Afeefah sanye cikin kayan Gasar amma yanzu ta saka mayafi fari tayi rolling kanta dashi sai dai ta cire Fancy Glass ɗin fuskar ta.


Da sauri Lailah ta ƙarisa suka rumgumo juna da Afeefah cike da farin ciki, bayan sun gama Deejarh da ta ƙariso ita ma tayi hug ɗin Afeefah tana faɗin "Balarabiyar Indiata ina ta ya ki murna sosai sosai, sannan ina cikin farin ciki mara adadi fa"

Murmushi Afeefah tayi sannan ta ce "Ina godiya sosai nima Deejarh tawa Allah ya bar ƙauna mara adadi tsakanin mu."

Mister Mai Kyau ya ce cike da zolaya "Yanzu dai a barmin Shalele taje ta shiga mota driver yaja mu tafi gida, sannan ayi taya murnar a gida can ina ga zaifi. Dariya sukayi sannan babu musu suka ɗun guma cikin motocin su cike da farin ciki sai gida.









KANO





HUMAIRA



Humaira zaune suke a ƙaton wajen gunadanar da gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jahar Kano, wanda ya sama hallatar manyan mutane maza da mata da ƙananan yara hadda ma Larabawa da Turawa da kowa da mutane, gurin ya haɗu sosai sosai. Especially ma saman floor ɗin gaba ɗaya launin komai na gurin sky blue and White color ne, jama'a ƴan kallo gaba ɗaya an nutsu ana jira a fara gunadar da Gasa. Daga gefe gasu Photographers nan birjik, ga ƴan gidan T.V nan, ƴan jarida ne da sauransu ana sai ta camerori ana jira lokaci ya cika da.


Daga ɗayan gefan kuwa Alƙalan Gasar ne kamar yadda aka saba mutane huɗu Baƙaƙen fata biyu, sai Baturiya ɗaya sai kuma wata Kyakyawar Balarabiya suna zaune saman wasu haɗaɗɗun kujeru irinna zaman manyan mata masu jida kansu, ga wasu uban littafai da papers a gaban kowannensu, mutane an cika gurin ba masa tsinke gurin yayi tsit ana jira lokaci ya cika a fara kafta Gasa.






MISALIN ƘARF£ GOMA SHA ƊAYA DAI DAI...






Humaira suna zaune a first chairs na gurin ita da Ni'ima dake a gefanta na hagu sai kuma Auntie Mrs Komai Naka, daga gefan dama, sai su Auntie Nafeesa da su Na'ima.

Gaba ɗayansu sun bada hankulansu suna jira suga kyakyawar da zata fara fitowa. ah domin kuwa taron na kyawawa ne.



TOHM


Ta wani dogon korido wata haɗaɗɗiya kuma kyakyawar budurwa ta fito tana takun gayu, tana sanye cikin shigarta na Gasar tayi kyau harta gaji da yin kyau ɗin, duk taku ɗaya da zatayi sai ta tsaya masu ɗaukar hoto sunyi ma ta sannan...



Da sauri Humaira ta ciro tsadaddiyar wayarta a jakarta, ta fara ɗaukar Video ana gudanar da Gasar, ita kuma tana ɗaukar duk wacca tazo sai ta ma ta Video idan ta koma kafin wata tazo sai tayi saving ɗin Videon a wayarta, idan wata ta fito ita ma ta ma ta nata ɗaukar daban.




TOFAH


Gasa ta fara ɗaukar ɗumi fa, a domin kuwa ƴan matan Gasar biyar har sun fito saura biyar kenan.

Gaba ɗaya gurin ya kuma yin shiru ana jira budurwa ta shida ta fito. domin ganin nata salon kyawun😘




WOW


Daga ganin irin shigar Princely Dresses ɗin da take ciki sai ka rantse ƴar sarkin ETHIOPIA ce, saboda tsananin kyau irin kyawun da tayi.
Tayi irin kyan nan na bugawa a kowani irin takarda da kuma bayyanawa game da nunawa a

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads