Showing 81001 words to 84000 words out of 106900 words
Chapter 28 - ALJANAR RUWA CE COMPLT BY ASHA M.B .txt
futa baki daya.
motocin gidan ne suka jeru akan titin, ganin goslow yayi yawa, babu hanyar da zasu bi, gashi bangare guda Kuma trailers sun tare hanya, yasa Ammi dora hannu a Kai tace shikenen zan rasa dana kamar yadda na rasa y'ata,
Amriya tace insha Allahu babu abunda zai faru dashi, da yardar ubangiji babu abunda zai same shi.
Kallon motocin da suka tare hanyoyin Amriya tayi, ta rintse idanuwan ta ,tareda saita hannunta daidai wajan motocin, tafara yin wasu abubuwa da hannayen ta, Hatake motocin suka Fara rarrabuwa, ya yinda trailers din suka samu hanyar wucewa,
Sosai mutanen wajan suka Shiga yin mamaki, daya daga cikin masu tuka trailers din yace, taya akan ta faru motoci su raba kansu, kuma ta bada hanya ba tareda wani ya tu kasu bah, tabbas abun al'ajabi baya karewa.
Barin wajan su Ammi sukayi, direct general hospital suka nufa, inda nurses suka futo tareda bawa yusuf gado suka Shiga dashi cikin emergency room, bah bata lokaci suka Shiga bashi taimakon gaggawa.
Zama Ammi tayi ta kafa tagumi, zuwa Amirya tayi inda Ammi ke Zaune tareda rungume ta tace, Ammi Dan Allah kada ki sa kanki cikin damuwa. Aduar ki kawai yake bukata.
Kallon Amriya Ammi tayi tace, wallahi Amriya tsoron abunda yafaru baya nakeyi, banason tarihi yakara maimaita kansa, kanwarsa cutar Asma ne ya kashe ta,
Yanzu shima gashi yana cuta, ina tsoron kada shima ya tafi ya barni kamar yadda itama ta tafi ta barni. Amriya tace ki kwantar da hankalin ki, Kisa a ranki cewar danki yasa mu lafiya.
Daya daga cikin nurses din ce ta futo, Ammi na ganin aka tayi Saurin mikewa, tareda nufan inda nurse din ke tsaye, shima abban Yusuf ya nufi wajan.
Amriya tace ya jikin Mara lafiyan, Nurse din ya basu amsa da cewar da sauk'i, amma danku yana bukatar jini sosai saboda jinin shi yayi kasa, kuma akan kan iya sa wani Bangare na jikin shi yasamu matsala.
Dole dai hana bukatar blood group wato (Onegetive) in bah aka bah, am sorry to say, zamu iya rasa shi.
Rass gaban Ammi ya buga, yayin da Abban yusuf yace nurse dole ne sai irin jinin sa za'a bashi? Nurse ta bashi amsa da cewar yes of course and we need the blood urgently, Tana kaiwa nan, ta shige ciki.
Dafa kanta Ammi tayi, yayin da takejin kanta na mugun saramata , Abba yace toh mu bashi mana jinin koh,
Kallon Abban yusuf Ammi tayi tace, ka manta mu bah O negative bane, ka manta bazamu iya bashi jini bah, Abban yusuf yace but why?, Ammi ta bashi amsa da cewar wato har ka manta yusuf Adopted child ne, ka manta da cewar yusuf bah dan mu bane,
Sai a yanzu Abban yusuf ya tuna da cewar tabbas yusuf bah dansu bane adopted child ne.
Kallon su Amriya tayi cikin rashin fahimtar maganganun su tace, Tunda yana bukatar jini ku bashi mana koh Kuma ni na bashi nawa.
Kallon ta Ammi tayi tace, ke Amriya kina dauke da ciki bazai yu ki bashi jini bah, muma Kuma bazai yu mu bashi jinin mu bah, amma saboda me? Amriya ta tambayi Ammi,
Ammi ta bawa Amriya amsa da cewar, saboda yusuf bah dan mu bane bah.
Zaro ido Amriya tayi tace mee, kina nufin yusuf bah danku bane, toh wacece mahaifiyar sa? Ammi tace wallahi muma bamu sani bah, a bakin hanya muka tsince shi lokacin baya cikin hayyacin shi, baisan ciwon kansa bah, a lokacin muna fama da rashin haihuwa, sai Kuma Allah ya bayyana mana yusuf a matsayin da a garemu.
Kuma a halin yanzu dole Mahaifyar sace kawai zata iya bashi jini.
----------------------
Kwan -Kwan -Kwan, su Khalid suka Shiga Kwankwasa kofan gidan, daya daga cikin masu tsaron gidan ne ya Mike tareda nufan hanyar gate din ya bude musu gidan.
Kallon su Mai gadin yayi, ganin doct khadija ce yasa yayi Saurin wangale gate din, tareda gaisar da ita, amsawa Doct khadija tayi tace, shin mutanen gidan suna nan kuwa?
Mai gadi ya bata amsa da fadin, wallahi gabadayan su, Sun futa, dansu ne bah lafiya, yanzu mah suna Chan babban asibity,
Innalillahi wa innahilahi rajihun! Doct khadija tafada, babu dai abunda ya same shi koh, Mai gadi yace babu abunda yafaru, amma yana ga kamar hankalin ki ya tashi, cewar Mai gadi.
Doct khadija tace babu komai shikenen, Kallon su Khalid tayi tace, ku tawo mu wuce asibity suna Chan,
Tarar napep sukayi, yayin da suka Mai kwatan cen asibityn, direct Asibityn Mai napep ya nufa dasu, ba'a fi mintuna ashirin bah suka isa wajan. Futowa sukayi daga cikin napep din, yayin sadiq ya biyashi kudin sa.
Shiga ciki sukayi, inda suka tarar da su Ammi a zazzaune, Amriya na ganin zu Khalid tayi saurin kauda Kanta gefe. Da sauri Doct khadija ta nufi inda Ammi ke Zaune.
Ganin Doct khadija, yasa Ammi yinkurin mikewa, zaunar da ita Doct khadija tayi tace Aa kawata basai kin tashi bah, ya jikin nasa yanzu, Ammi tace da sauki, amma nurse tace dole yana bukatar karin jini Kuma Onegetive, in bah aka bah zai iya rasa rayuwar sa .
Doct khadija tace jini na Onegetive ne, muje zan bada nawa jinin, Aa khadija you don't need to stress yourself, Doct khadija tace no Amina what are we friends for, na taimake ki, kema ki taimaka min, yusuf shima a matsayin dana yake , kinga bazan ga yana cikin magagin mutuwa Kuma naki taimakon sa.
Tashi Doct khadija tayi tareda Shiga cikin room din, tareda Sanar da nurse din cewar zata bada jinin ta,
Kwantar da ita akayi sannan aka zuki jinin ta, yayin da nurse din ta bawa Doct khadija Apple ta ci. Saida aka ibi wajan leda guda na jinin Doct khadija, sannan aka sanya wa Yusuf.
Yin kurin tashi Doct khadija keyi, Nurse din ta dakatar da ita da fadin, Aa bai kama ta ki tashi bah yanzu, kina bukatar ki kwanta, ku huta, Doct khadija tace na ruga dana kwanta babu damuwa inason zanyi wani abu mai mahimman ci ne, Tana kaiwa nan ta fuce daga dakin.
Su Amirya na gani ta suka isa Inda take, Ammi tace har kin bada jinin, Doct khadija ta bata amsa da cewar Eh na bada, godiya sosai Ammi tayi mata, yayinda Doct khadija tace babu godiya a tsakanin mu.
Kallon Amriya Doct khadija tayi tace, Amriya muna bukatar taimakon ki, Kabeer yana cikin halin tsaka mai wuya, kuma da taimakon ki da taimakon Allah, zaki iya fidda shi daga wannan halin da ya shiga, Dan Allah Amriya kada kice baza ki je bah.
Kallon ta Amriya tayi tace, bazan taba zuwa wannan gidan bah, na ruga na yi alkawarin bazan Kara sanya kafana a gida nan bah, kuma dalilin Kalb, bazai sa na karya alkawari na bah,
Khalid yace, Amriya Dan Allah badan Halinsa bah ki taimaka mana, cikin fusata Amriya bazan jee bah, bana sonsa, bana kaunar ganin sa, kuma bazan taba taimaka masa bah, tun wuri kune mi inda dare yayi muku.
Idan mah kuna tunani zanje gidan nan wai da sunan taimako, toh ku maida ita tatsuniya, domin kuwa bazan je bah. Sadiq yace amma fah Amriya, kabir zai iya rasa rayuwar da, idan baki taimaka masa bah.
Amriya tace toh ni mene nawa, ai nauyi bah akaina yake bah, Allah ne sai bayarwa Kuma shine Mai karbe abarsa, Dan aka idan lokacin sa yayi Kaga saidai muce Allah ya jikan sa.
-----------------------------------------
COMMENT & SHARE PLS ???
ALKALAMIN ??
AISHA MUHAMMAD BASHIR ???
(BABY ISHA)
?BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM ?
ALJANAR RUWA CE ??♀???
PAGE 4??9????5??0??
WRITTEN & DIRECTED?? BY AISHA M.B??
-----------------------------------
Dan jimm Ammi tayi, tace Maganar ki hakane Amriya, amma da mutane zasu bi ta halin koh in kulan da ake nuna musu, koh irin rashin mutum cin da akayi musu, da babu Wanda zai Kara taimako a duniya, Dan aka baza kiyi wannan taimakon danshi bah, amma kisa a ranki cewar zaki taimake shine Dan Allah.
Amriya tace hakane amma kuma na ruga danayi alkawari, kuma banason na kasance mai karya alkawari, domin kuwa karya alkawari ba abu bane mai kyau.
Akane Amriya, amma Domin cetan Dan uwa, mu kan iya sadaukar da komai na mu, harda alkawarin mu domin cetan rayuwar sa daga cikin hatsari, nasan da cewar kin tsani kabeer, amma danne zuciyar ki zakiyi, kije ki cece shi, ke kanki zaki yi farin cikin cewar kema kin ceci rai daga mutuwa,
kuma zakiyi tsanan da kike zai tafi, kije Insha Allah komai zaiyi sau?i. Amriya tace naji shikenen zanje, amma har abada tsanan da zai cigaba da kasance wa acikin zuciyata, domin kuwa Shida kansa ya dasa min tsanar sa a zuciya tah. Ku taso mutafi cewar Amriya.
Murna sosai su Khalid sukayi ganin ta amince zata bisu.
Mikewa Amriya tayi , tareda fucewa daga cikin reception din, su Doct khadija na ganin aka ,suka bi bayan ta da sauri, tarar musu napep sadiq yayi, tareda yiwa mai napep din ?watan cen gidan. Hawa napep din sukayi, basu suka isa gida bah, sai wajan la'asar.
Futowa sukayi saga cikin napep din, yayin da sadiq ya biya mai napep din hakkin sa. ?arewa gidan kallo Amriya tayi, Tana mai fadin, ban taba jin koda sau ?aya nayi kewar gidan nan bah, Wanda nasan nayi kewar su a gidan nan sune, Aunty amarya, Dad, da Kuma Grandma.
Doct khadija tace, Allah sarki Amriya suma yan gidan abunda yasa kika ga sun miki aka, saboda idanunwan su ya rufe ne basusan gaskiya bah, amma kinga yanzu, sun fahimce ki, kuma sun gane gaskiyar lamari ,
Sadiq yace kwarai kuwa, a lokacin bamusan menene gaskiya bah, amma yanzu mun gane gaskiya Kuma insha Allah zamu kiyaye gaba, Dan Allah ki tawo mu Shiga please,
Ku shiga ciki zan biyo ku daga baya cewar Amriya, Khalid yace, kin tabbata zaki biyo mu, Amriya ta Bashi amsa da fadin kwarai kuwa zan biyo ku,
Suna jin akan yasa kowannen su Shiga ciki, yayinda suka bar Amriya a wajan.
Share hawayen dake shirin zubo mata tayi, Tana mai fadin, ban yi niyan zuwa gidan nan bah, amma zuciya ta baza ta iya juran ganin sa acikin wannan yanayin bah, dole ne na ceci rayuwar sa badan halin sa bah.
Bangaren su Doct khadija kuwa, suna Shiga ciki suka tarar dasu, Grandma a zazzaune kowa na tofa albarkacin bakin sa akan Mom,
Mamaki ne ya kamasu, ganin Mom a daddaure jikin gado, ga idanuwan ta sun kada, sunyi jajir saboda duka, cikin kidima Doct khadija tace waye yayi mata wannan dukan?
Grandma ta bata amsa da fadin, i tasidi madam, kwarai nice nan, koda magana,
Doct khadija tace babu komai, amma kuma yadda kika yi mata dukan nan, zuciyarta Kara hassala zaiyi, kuma zaku kara tunzura tane.
Grandma tace, bah tunzura bah koma sauya kammani zatayi ta koma shedaniya, bai damen bah, Tunda nidai na daki na jaki a jikin ta, an wuce wajan,
Wallahi akan mah kadan ta gani, shegiya dangin gajeru kawai.
A hassale Mom tace wallahi halima zaki gane kuren ki,
Grandma tace, kutusin karan chan, bala'i, yau akwai gagarumar fad'a a gidan nan, ni kika kira da suna na, koh sanda Maman ki saratu take yawo akan keke, koh nono bata Fara bah, bata isa ta kirani da sunana bah,
toh ki sani, wallahi yau saina ci ubanda yayi tattalin goron auren bikin gyatumar ki.
Tana kaiwa nan ta dauki dorinan ta nufi kan Mom, daga hannun ta tayi sama da zimmar sha?awa Mom bulala, ba zato, bah tsanmani taji an rike mata hannu.
Da sauri ta juya DAN ganin wanda ya dakatar da ita, hatake ta hada ido da Amriya, da sauri ta saki bulalan, tana mai fadin, Allah sarki y'ata Amriya kin dawo kenen, yau ke nake son kiyi wa wannan balamar dukan ja da baki.
Karbar dorinan Amriya tayi daga hannun Grandma, tare da, jefar dashi gefe tace, duk Bakua bukatar wadanan abubuwan, ka mata ai ku barta domin kuwa yadda kike zagin ta, kina rage mata zunubi ne.
Koh Baku yi mata Komai bah, watarana zata gurbi abunda ta shuka. Dad yace kwarai kuwa y'ata, maganar ki gaskiya yace, zamu rabu da ita, amma dan Allah kizo ki duba mijin ki haryanzu bai farfado bah,
Shidin bah mijina bane, ku bazai taba kasancewa mijina bah cewar Amriya.
Tom shikenen Amriya Amma Dan Allah ki taimaki rayuwar shi, cewar Mahaifyar kabeer.
Da sauri Amriya ta juya kamar ta taba jin wannan muryar, juya warta keda wuya suka hada ido da Fatima wato Mahaifiyar Kabeer, da sauri Amriya ta nufi inda take tareda rungume ta tace.
Dama kin futo, yanzu sungane kece asalin mahaifiyar Kabir koh, gaskiya nayi murnan ganin ki, Murmushi Maman kabeer tayi tace kuma ina farin cikin sake ganin ki, yanzu bah wannan bah, ki taimaki rayuwar dana, badan halin sa bah, for my sake kinji.
Girgiza kai Amriya tayi cikin garin ciki tace, ai kodan ke mah, dole na Samar masa da lafiya karki damu Insha Allah zai samu sauk'i.
Tashi tayi tareda nufan inda Kabir ke kwance, kare masa kallo tayi, tana karajin wani sabo tsanan da acikin zuciyar ta.
Daukan hannun sa wanda zoben ta ke sanye a jiki tayi, tareda rike zoben tsamm , yayin da ta rintse idanuwan ta.
Jikin shi ne yafara motsawa kadan kadan, yayin da zuciyar ta ke Duka da sauri sauri, amma duk da akan bata sake shi, saida takai kusan minty ashirin amma bai farfado bah.
Ganin aka yasa ta ta Fara hawaye Hatake hawayen ta ya disa akan zoben, cikin kankanin lokaci zoben yayi aske wanda ya gauraye gabadaya dak'in.
Jikin kabeer ne ya fara karkarwa, ganin akan yasa Amriya rungume shi a jikin ta,
A hankali yafara bude idanuwan sa, inda daga karshe, yayi nasaran bude su baki daya. Sakin shi Amriya tayi tareda kwantar dashi ta mike da niyar tafiya, bah zato taji ya damke hannun ta, yayin da hawaye ke bin gefen fuskan sa.
Hatake taji wani irin kasala Tareda jin tausayin shi ya Kama ta, wafce hannun ta tayi daga nasa, da sauri su Dad suka nufi inda yake a kwance, daga shi Dad yayi tareda rungume sa yace, kana lafiya dai koh Kabir,
Nufan hanyar waje Amriya tayi ba tareda ta Bari kowa ya ganta bah, Kallon su tayi gabadaya, tareda sakin murmushi daga bisani ta fuce daga gidan .
Doct khadija ce tace, Kabir Kaga asalin mahaifiyar ka nan, itace Maman ka, itace ta kawo ka wannan duniyar,
Kallon mahaifyar sa, Kabir yayi hawaye na bin kan kuncin shi yace "Mama", jin akan yasa Fatima fashe wa da kuka, rungume Kabir tayi tana mai fadin, ka yafe min dana, laifina ne, ban taba bayyana a gareka na nuna maka cewar ni mahaifiyar kace, ka gafarce ni.
Kabir yace babu abunda kika min Umma, nine ya ka mata na nemi yafiyar ki, dan Allah ki yafe min, Fatima tace na yafe maka duniya da lahira Kabir, Allah yayi wa rayuwar ka albarka.
Bangaren Mom kuwa ganin kowa hankalin shi nakan Kabir yasa ta Fara yunkurin kunce kanta, inda a karshe tayi nasaran kunce zaren da suka daure ta dashi.
Mikewa tayi da sauri, ta Kare musu kallo, sannan ta fasa wani mahaukacin dariya.
A firgice gabadayan su suka waigo, tareda kura mata ido, Mom tace wato ni zaku daure koh, you saina kashe ku baki daya,
Tashi Kabir yayi cikin kasala yace, menene muka aikata miki Mom meyasa kike haddaban rayuwar mu, indai saboda kudi ne koh dukiya, gasunan duk ki dibi na iba ki bar na bari, amma meyasa kike fadin Lallai sai kin kashe mu, ki barmu da bakin ciki da kuncin da kika sanya mu mana, iya akan bai wadace ki bane,
Mom ta bashi amsa da fadin kwarai kuwa akan bai ishe ni bah, Nadira tace Mom meyasa kike aka, ga y'ay'an kinan suma kin hada dasu, duk mene aka, menene silan aka, Grandma tace kwarai kuwa, ki fada mana wane abu aka yi miki da kike son daukar fansa?
Mom tace Yunusa yusuf wato mijin ki, shine silan komai da ke faruwa daku,
Grandma tace yanzu mijin nawa mah saboda Allah da annabi baza a bar ruhin sa yasamu salama bah, sai anyi masa sharri,
Tabbas nasan karya kike bawani mijina da ya miki wani abu. Dakatar da Grandma Kabir yayi da fadin ki bari muji menene yafaru, maida Kallon ta kan Mom yayi, yana mai fadin, ki fada mana abunda ya faru.
Dad yace dakata tukunan, dole Sai Maryam da Habib suna nan domin banason ayi komai a bayan idonsu, yanzu ku kiramin Habib da Kuma Maryam yanzu, suzo, daukan wayar sa, Sadiq yayi tareda Kiran Abban sa wato Habib, sannan shima Khalid ya dau waya Tareda kira Mahaifyar su Mami.
Bayan wasu hawanni kowannen su ya hallara .
Dad yace toh Alhmadulillah kowa yana nan, yanzu zaki iya magana
Kallon su Mom tayi tace.
SHEKARU BAYA DA SUKA GABA TAH.
Mahaifina da Kuma mahafin ku, wajen bussiness dinsu daya, Kuma sudin sun kasance babban abokai nee. Komai tare suke yi, amma mahaifin ku yafi mahaifina kudi nesa bah kusa bah, duda aka kakan ku bai taba nuna wai shidin wani ne.
Hana aka sai suka samu sab'ani Shida babana, akan wani maganar kudin da suka samu wajan Millions of Naira, sai mahaifin ku ya yanke cewar za'a kai gidan marayu, Wanda babana tsam bai amince da akan bah domin shi a ganin shi da akai kudin gidan marayu gwanda su Kara wa kansu jari, shikuwa kakan ku yace, indai rabuwa ce saidai su rabu amma bazai taba bin maganar sa bah.
Aka kuwa akayi yayinda kowannen su yayi hanyar sa, babu wanda yakara kula wani acikin ku.
Hana aka karayar arziki ta samu babana, yayinda muka talauce, koh gishiri Bamua samu mu siya saboda tsanannin talauci, a lokacin mahaifina ya yanke cewar zai Shiga qungiyar asiri domin yayi kudi ya zama sananne wanda babu kamar sa.
A lokacin yaje yayi joining qungiyan asiri, amma a lokacin aka gargadi mahaifina da cewa
kada ta kuskure ya fadawa