Showing 93001 words to 96000 words out of 106900 words
Chapter 32 - ALJANAR RUWA CE COMPLT BY ASHA M.B .txt
jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🌹BISSMILLAH RAHMANI RAHIM🌹
ALJANAR RUWA CE 🧜♀️🌊🌊 PAGE 5️⃣3️⃣▶️5️⃣4️⃣
WRITTEN & DIRECTED✍️ A'ISHA M.B 💞💞
(Zinariyar 🪙 Jajirtattu)
-----------------------------------------
Farin ciki ne ya bai baye fuskokin aljanun ruwan, hajiye jaririn suka yi kusa da Amriya, sannan suka yi tafiyar su.
Maida kallon ta Amriya tayi kan jaririn, abunda ta gani ne yayi matukar bata mamaki, ganin yaron tayi kafan mutane ne ajikin sa bana Aljanun ruwa bah.
Shafa kafar tayi, wanda suke farare gwanin ban sha'awa, share hawaye ta tayi, sannan ta mike, ta nufi bakin Kogi domin ta kimtsa jikin ta da kuma na yaron,
Saka yaron tayi cikin ruwa, amma ga mamakin ta, taga bai sauya daga jinsi mutane bah, Kallon shi tayi tace me akan yake nufi?, meyasa bai koma aljanin ruwa bah?, tunda ni ALJANAR RUWA CE, kama ta ai ace danda zan haifa ya zama irina, amma meyasa kaikuma baka zamo kamar ni bah.
Wani tunani ne ya fado mata akai, kenan akan yana nufin jinsin mahaifin sa yayo kenen, toh tayaya akan zata kasance,. Murmushi wanda yafi kuka ciwo tayi, sannan tace, kada ka damu Allah shine abin dogaro.
Tana kaiwa nan, tayi masa wanka, sannan itama ta gyara jikin ta wanda ya baci da jini,
Tana gama wa, ta mike sannan ta hajiye yaron, ta fara tsinto kara tana hadawa guri guda,
Sai data gama har hada karan, sannan ta hura masa wuta da bakin ta, babu bata lokaci ta fara gasa wa yaron cibiyar sa, kukan yaron ne gaba daya ya karade dajin, daukan placenta tayi wato mahaifa, sannan ta tona rami ta bunne shi.
Bayan ta gama bunnen placenta, ta dauki jaririn, sannan ta nufi wajan bishiya ta tsinki ganye, ta saka shi acikin ganyen.
Ƙare mai kallo tayi taga sakk kamar mahafin sa, kamar harta baci, shafa sajen yaron tayi wanda suka kwanta suka yi luff, tace kyakkyawan yaro na, ni na kusan tafiya na barka, zanyi kewar ka soaai dana, ina fatan koda kaji labari na a wajan mahaifin ka, kada ka taba manta wa dani kaji.
Kallon sama tayi taga rana ta fadi, hawaye taji na shirin zubo mata, da sauri ta share hawayen ta, sannan tace, ranar da na dade ina jira yau gashi tazo, yau zan tafi na barku baki daya, zan kaika wajan Ammi, uwa ta gari, na tabbatar kulawar da zan iya baka, shi itama zata baka, zaka samu farin ciki da kulawa mara misaltuwa.
Mike wa tayi, yayin da yaron keta faman kuka, rarrashin shi ta fara yi, daga bisani sannan ta fara tafiya.......
Saida tayi tafiya mai nisa sosai, sannan ta isa gidan Ammi, karewa gidan kallo tayi, race ga sabon duniyar ka nan, wannan gidan aciki zaka cigaba da rayuwa idan na tafi, rufe idanuwan ta tayi, hatake kamar walkiya ta bace batt..
Ba ta tsinci kanta a ko ina bah, sai Cikin gidan Ammi, parlour ta shiga batare da ta bari kowa ya ganta bah, hajiye yaron tayi, hawaye nabin kan kuncin ta.
Sannan ta nufi kan drower, ta samu biro da kuma paper, tayi rubutu aciki sannan ta nan nada takardar, ta saka shi a jikin yaron,
Kallon sa tayi yayin da kuka yaci karfin ta, sosai take kuka mai ratsa zuciya, saida tayi mai isar ta sannan, tace yau ganina dakai na ƙarshe kenen, ina fatan ka samu ingantacciyar rayuwa, ina fatan kayi tsawon rai a rayuwar ka.
Tana kaiwa nan ta fuce daga gidan.
Ficewar Amriya keda wuya, Ammi tajiyo kukan jariri a parlour, da sauri ta nufi hanyar parlour domin ganin wanene,
Tsayawa tayi chakk, ganin jariri akan kujera ga takarda a gefen sa, kwallah wa abba kira tayi, sannan ta kwalla kiran doct Khadija, da kuma Yusuf, babu bata lokaci gaba daya suka hallara a parlour.
Yusuf yace Ammi meya faru mukaji kin kwallah mana kira?, jiki a muce Ammi ta nuna jaririn da ɗan yatsarta, bin yatsar ta suka yi da kallo.
Da mamakin su, suka ga jariri kwance akan kujera, sai faman kuka yake, gaban kowannen su ne ya fadi, yayin da kowa ya rasa ta cewa.
Doct Khadija ce tayi karfin halin fadin, Wannan jaririn kuma daga ina?, tayaya ya shigo gidan nan?, kuma meyasa aka kawo shi nan gidan?, tambaya data shiga yi kenan.
A tsora ce Ammi ta kara sa inda jaririn yake, tare da kurawa jaririn kallo, hatake gaban ta ya fadi!, jikin ta ya fara bari, baki na rawa tace, kuzo ku ganshi,
Karasa wa su Doct Khadija sukayi wajan, yayin da gaba daya suka dora idanuwan su akan jaririn, gaban su ne ya bada wani sauti, yayinda zuciyoyin su ya fara duka uku -uku.
Baki na rawa Yusuf yace, wannan yaron baku ga yana mugun kama da Kabir bah,
Doct Khadija tace, kamar mah harta ɓaci, Ammi tace idan hakane kenan wannan dan yata Amriya ne, kenen akan yana nufin tazo gidan nan, share hawayen ta tayi, sannan ta dauki jaririn tace, such a cute and handsome baby, tabbas kayo kyan mahafiyar ka, domin kuwa kyakyawa irin tace zata iya haifo kyakyawa yaro kamar kai, because itadin makura ce a kyau.
Yanzu kaidin jikana na ne, nima an kusa fara ki rana da Grandma, tsuch a wonderful and great day, how I wish you were here amriya, da farin ciki na bazai misaltu bah.
Daukar paper dake kan kujera Yusuf yayi, sannan a hankali ya fara bude takardar, daga karshe yayi nasaran bude shi baki daya, kurawa takardar ido yayi sannan ya fara karan tawa kamar aka.
"Assalamu alaikum wa rahmatullahi ta'ala wa barakatu", ni'imar Allah, gafarar Allah, tausayi da kuma imani su kara tabbata a gare ku da Kuma ni baki daya. Ammi ina fatan kuna cikin koshin lafiya kamar yadda nake, wannan yaron da kuke gani, tabbas shidin ɗana ne, kuma Kalb ne mahaifin sa, ina fatan zaku kulamin dashi, ta yadda bazai san cewa ya rasa mahafiiya a rayuwar sa bah, Ammi inason ki zaba masa suna wanda ya dace dashi, domin kuwa ni bazan samu damar yin akan bah, saboda yaune rana ta, ta karshe a duniya, zan bar duniya kamar yadda na fada muku tun farko, ina fatan zaku gafarce ni kura kuran da nayi wanda na Sani da wanda bansani bah ina fatan kuya femun, kuma ina fatan suma su ahalin kalb su gafar tamin, sannan inason bayan mutuwa ta ku nemi gawa ta, sannan ku suturtani ku kaini gida na na gaskiya, naso ace naga asalin mahaifiya ta da kuma mahaifina koda so daya ne kafun na mutu, domin kuwa saina fi samun salama, amma akan bai yu bah, na roke ku, idan kuka ga asalin iyaye na, kuce yarsu ta bar musu wasiha cewa, meyasa suka rabu dani?, meyasa mahaifya ta, ta tafi ta barni, ba tare da ta waigo taji ya nake bah, ya nake ci nake sha bah. koda so daya bata taba nema na bah, amma ni koda yaushe cikin tsimayi zuwan ta nake, kuce musu ni banji haushin su bah samm, ko kadan banga laifin su bah, saboda bansan dalilin su na rabuwa dani bah, amma dan Allah kuce wa Iyaye na, tunda basu taba jin ya bugun zuciya ta ke tafiya bah, basu taba jin koda murya na bah, basu taba ganina bah, kuce su taimaka su zo jana'iza ta, domin bazan cigaba da kasan cewa a raye bah, zan mutu ba tareda nayi ban kwana da kowa bah, aka tawa kaddarar tazo, aka zan amashe ta, dan Adam baya taba guje wa kaddarar sa koh yayane, duda nima bah mutun bace, amma nima ina da tawa kaddarar. hakika ahalin Kalb da kuma Ammi mutane ne na gari da kuma amana, samun irin ku a wannan duniya da wuya, bansan da wace kalma zanyi amfani wajan gode muku bah, domin kuwa kunyi min abubuwa mara misaltuwa, na hajiye dana, kuma ina fatan zai samu kulawa da tarbiya kamar yadda uwa ta gari take bawa ɗan ta koh ƴar ta, Zanyi kewar ku baki daya, Ammi zanyi kewar murmushin ki, gaba daya zan yi kewar ku, ina fatan zaku ga wannan sakon, inaso wannan sakon ya isa ga ahalin su Kalb, ina fatan gaba daya kuyi tsawon rai, zanyi kewar ahalin Kalb, Allah sarki, yanzu aka zuciya ta zafi take min, na nemi kuka na rasa, zuciya ta tana yimin radadi sosai, yadda nake rubuta wannan sakon, gabadaya kaina da jikina suna min ciwo sosai , ina jin radadi da kuna sosai, yanzu aka saura sa'o'i biyar kafun na mutu, zan mutu ba tareda na kawar da faruwar akan bah, hmmm duniya rumfar kara, wanda ya bita a sannu zai dace, ni na tafi, zanje na tsimayi jiran mutuwa ta, domin babu wanda zai dakatar da faruwar akan, ina son kusan cewa ina sonku sosai, da ace mutane suna mutuwa su kuma dawowa rayuwa, da zanso ace na dawo a matsayin mutun, kuma na kara haduwa daku a Karo na biyu. Nasan da cewa mutuwa ta zata girgiza ku sosai, za kuji zafin mutuwa ta, amma kuma karku damu zafin na zuwa wasu lokaci kalilan ne, nan da wasu kwanaki zaku manta da komai, dama kowa mamaci ne, koda yau ban mutu bah, toh watarana yana nan dazan mutu, babu wanda zai zo duniya ba tare da ya koma ga mahaliccin sa bah, dan aka kada kusa kanku a damuwa, zama daku yasa na gane banbamcin soyayya da kuma kiyayya, yasa na gane banbamcin rikon amana da kuma cin amana, na koyi abubuwa da dama masu kyau a wajan ku, cikin ta harda sallah da kuka sa na fara yi, yanzu ina alfahari kasance wa ta musulma, mai rikon addini da kuma ibada, bansani bah ko ku, kun karu dani, amma tabbas ni na karu daku da abubuwa da dama mara misaltuwa, ya Allah mai yafiya mai jinkan bayin sa, ina fatan ka dalmiyar da dauwamammiyar farin ciki a wajan wannan ahali biyu, ka basu hadin kai a tsakanin zuka tansu, kada ka hane su da komai, kamar yadda nima basu haneni da komai bah, ya Allah ka kara musu hadin kai da qaunan juna.
Ina fatan rayuwar ku ta zama ingantacciya, Allah yasa rabuwar ku dani, itace alhkairy.
NA TAFI, FATAN KUYI DOGUWAR RAYUWA. "BSALAM"...........
Zama Ammi tayi, yayin da kuka yaci karfin ta, ta fashe da kuka, gaba dayan su, hawaye suke yi, yayin da suke jin tausayin Ammi da kuma Amriya na shigar su.
Cikin sheshekar kuka Ammi tace, ki gafar cemu yata, ba laifin mu bane, ba muda niyar rabuwa dake, rabo ya rantse cewa ba damu zaki karashe rayuwar ki bah, danasan da cewa kina raye, da tuntuni na bayyana kaina a gare ki. Tana kaiwa nan ta kuma fashe wa da wani matsanancin kukan.
Doct Khadija ce ta dafa ta, sannan ta ce, Amina yanzu bah kuka ne ya kama ki yi bah, kama ta ai ace muje mu fara neman zoben nan, sa'annan mu ceto Amriya daga shiga hallaka, in bah aka bah komai zai iya faruwa.
Share hawayen ta Ammi tayi sannan tace, hakane, maganar ki gaskiya ce, ya kama ta muje gidan su Kabir yanzu nan, if not am going to loose my only one and beloved daughter.
Mike wa tsaye tayi, tare da ɗaukar makullin mota, ta nufi hanyar waje da jaririn.
Ganin aka da su Yusuf suka yi yasa su saurin bin bayan Ammi, Ammi na isar baƙin mota, ta bude kofar motan sannan ta hajiye jaririn, daga bisani ta nufi driver seat, ganin aka yasa Yusuf sauri. Karasa wa wajan yace,
Ana Ammi, ya zaki tuka mota da kanki bayan kina da ni, Please ki koma back seat Ni zan tuka motan, jin aka yasa Ammi futowa daga cikin ta nufi back seat ta zauna.
Shiga ciki baki ɗayan su suka yi, yayin da Yusuf ya tada motan, sannan masu gadi suka wa gale musu gate, suka bar harabar gidan.
------------------------------
Kwance yake akan kafadar ta, yayin da gefe guda tana shafa masa sumar kansa. Ɗaga kansa yayi ya kalle ta, sannan yace,Momsy bansan meyasa bah tun sanda kika dawo cikin rayuwa ta nake jin kaina so special, i really love you my momsy, murmushi tayi sannan tace, Kabir kenen, duk soyayyar da k min ba zata taba kaiwa nawa bah.
tsawon shekaru kenen nake buri da fatan ganin ka, yanzu kuma ta dalilin Amriya, Allah ya dawo min dakai gareni, tabbas Amriya yarinya ce ta kwarai wacce koh wace mahafiya zata yi fatan samu irin ta.
Duda cewar bah mutum bace, amma dabi'un ta, komai nata na mutane take yi, gaskiya Kabir kayi dacen mata.
Hawaye Kabir yaji yana shirin zubo masa, da sauri ya share hawayen sa, sannan yace, hakane "momsy, tabbas nayi dace mata, amma a rashin sani da kuma rashin tausayi irin nawa, na kore ta, na yarda ni mugu ne, koda yaushe burina shine naga na kuntata mata, saboda tsananin tsana da tsangwama da nake mata.
Da'ace yau tana a gaba na, toh da babu abunda zai hanani durkusa na bata hakuri, sannan na bayyana mata irin tsananin sonda nake mata.
Kwan kwan kwan, suka ji hana bubuga kofa, tashi Kabir yayi ya nufi kofar parlour, tareda fadin waye?, bude kofan yayi, da wani irin sauri yaja da baya, ganin Mom da kuma yan qungiyar ta, sai kuma Zainab wacce tayi zuru_zuru kamar mayya.
Ganin Mom ce da yan qungiyar ta, yasa Momsy kwalla wa Dad da kuma sauran yan gidan kira.
Fitowa gaba dayan su suka yi, da mamakin su suka ga Mom da yan qungiyan ta. Alama Mom tayi wa yan qungiyar nata da fadin ku kama su, sannan duk ku daure su.
Mom na idda magana, suka shiga yin abunda ta saka su, saida suka daure gaba dayan su, sannan suka rabu dasu,
Kallon Mom Dad yayi yace, Karima me ya dawo dake kuma?, mene ne kike so?, koh har yanzu baki gama daukar fansar taki bah.
Dariya Mom ta kwashe dashi, sannan tace, kwarai kuwa, da'a tunanin ku wannan tafiyar da nayi na tafi kenen bazan dawo bah, toh wannan tafiyar da nayi badan kowa nayi shi bah saidan ku, inaso naga na kashe gaba daya wannan ahalin sannan hankali na zai kwanta. Kuma a yau bah gobe bah, zan hallaka kowa na wannsn family, duk abinda nasan ya rabe ku, yaci sannan yasha daku, toh shima saiya bakun ci lahira.
A fusace Grandma tace, toh me kike jira, ki aiwatar da abinda kika zo aiwatar wa mana, Ki kashe mu, idan kuwa baki kashe mu ba, ni da kaina zan shekeki, sannan na bawa karnuka gawar ki su cinye.
A fusace Mom ta nufi inda Grandma take tare da shake mata wuya, kuka su nadira suka saka, suna ihuun taimako!,
Kumin shiru, ta daka musu tsawa!, sannan tace, duk wata shegiyar data karamin kuka hanan, saina sadaukar da jinin ta wa qungiya, idan kuma kuna ganin karya nake, dan hallak ka fasa.
Tana kaiwa nan ta maida Kallon ta kan Grandma, tareda fadin, ke dama wannan tsohuwar ke yaka mata na fara kashe wa, domin kin tsule min ido, wane irin kisa kike so na miki, shin na harbe ki da bindiga har lahira, ko kuwa na chaka miki wuka, koh na rataye ki, ko kuma na shake miki wuya har lahira.
Grandma ta bata amsa da cewa, duk wanda kika zaba matsiyaciya, dama irin ku talauci ne ke janyo wa kuke shigs cikin qungiyan asiri, sannan ku dunga cin kuɗin haram, kudin da bata hanyar halal aka same ta bah.
Nuna Mom Grandma tayi tace, ke Karima karki dauka zaki iya tsora tani da wannan bindigar wasar da kika rike a hannu, wallahi banki na kunce kaina nayi miki tsinaniyar duka bah, ko mene zaki fada baki isa kin tsora tani bah, saidai mah ni na tsorata ki.
Dariya Mom ta kwashe dashi, ji kake, hahahahaha. Saida tayi mai isar ta, sannan tace, "nidin wai, tsoro, na rasa tsoron wa zanji saina tsohuwa, toh bara kiji har yanzu ba'a haifo wacce ta isa ta sakani na tsorata bah.
Kallon ta Nadira tayi tace, karya kike, tabbas an haifo wacce ta isa sakaki tsoro harda firgici, domin kuwa Amriya daya ce tamkar dubu, kuma ita din ce zata kawo ƙarshen zalin cin ki, dama duk inda aka samu mugu, wanda yake takama da tsantsan zalunci, toh tabbas mai maganin shi yana bayyana.
Kamar dai yadda itama Amriya itace zata yi maganin ki, domin kuwa babu inda zalinci yake dorewa, Amriya itace ajalin ki.
Kamar hadin baki gaba dayan su suka ce, "kwarai kuwa, Amriya itace zata yi ajalin ki.
COMMENT & SHARE plxx🙏🙏🙏
ALKALAMIN✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar 🪙 Jajirtattu)
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JYYV16dbYaX1dykLX7EE91
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🌹BISSMILLAHI RAHMANI RAHIM🌹
ALJANAR RUWA CE
🧜♀️🌊🌊
PAGE 5️⃣4️⃣▶️5️⃣5️⃣
WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY AISH'A M.B💞
(Zinariyar 🪙 Jajirtattu)
54 TO 55
,___________________________________
Idan ran Mom ya kai dubu, toh ya ɓaci?, cikin baccin rai tace, naga alamin kuna da mai tsaya muku Koh?, domin banga alamin tsoro a tattare daku bah, kuma ni akan bai min dadi bah, dole ne na dawo da wannan tsoron cikin zuka tanku.
"Khalid yace, sai dai mu, mu dasa miki tsoro, amma ke dai baki kai bah, domin kuwa kunkuru ba zai ce zaiyi gasar gudu da barewa bah. Dan aka ki koma inda kika fito, domin kuwa bamua da bukatar ku.
Gyaran murya "Zainab tayi tace, like seriously!, oh wait a minutes, kuna tunanin da mun zone domin muyi sulhu, that's impossible, idan kuna ma tunanin akan toh ku maida ta tatsuniya, domin kuwa bala'i, ne ya kawo mu, kuma kowa saiya ɗaɗana kuɗar sa.
Maida Kallon ta kan yan qungiyan tayi tace, maza _maza, ku daddaure su yanzu nan, babu bata lokaci suka nufi kansu Kabir da zimmar daure su,
A hassale gaba dayan su Grandma, suka dunkule hannu sannan suka kai musu naushi, ganin akan yasa gaba-dayan su yan qungiyan asirin suka yi kansu, kokawa gaba daya suka shiga yi, babu abinda kake ji a gidan sai karan naushi.
Yayin da gefe guda Grandma ta daura ɗan kwalin ta ƙugu, sannan ta kama kan daya daga cikin yan qungiyan, sannan ta gantsara masa cizo a kai, ihuu ya saka,