Header Ads
Showing 75001 words to 78000 words out of 106900 words

Chapter 26 - ALJANAR RUWA CE COMPLT BY ASHA M.B .txt

Ads the beginning of article before Image

Aisha MB   

28 May 2024

1068

Ads at the middle of Article

tashi ya karayi bah, fashewa da dariya Mom tayi, tace ina farin cikin ganin wannan ahalin cikin kunci da damuwa, kamar yadda kuka sakani kunci, nima saina ga bayan ku,


Cincibar Dad da Kuma Kabir sukayi, suka nufi hanyar waje dashi, cikin mota suka nufa da su, Khalid ya tada motan, sannan yayi wa su body guard magana dasu bude kofan.


Ganin koh yunkurin bude kofan basuyi ba, yasa ran Sadiq baci, futowa Sadiq yayi daga cikin motan, yace bakuda hankali ne, Baku ga rayukansu na cikin had'ari bane, maza ku bude kofan kafun, ranku ya baci.


Daya daga cikin body guard din yace, ba'a bamu umarnin mu bude muku kofa ba. Aka zalika, wannan gidan mallakin uwar shedanu ne, babu wani ma'aluki da ya isa yayi kokarin futa daga gidan nan, domin wannan gidan makabartar ku ce.


Mutuwar tsaye Sadiq da Khalid sukayi! Ya rasa abun cewa, jiyayi gabadaya duniyar ta isheshi.


Dariya gabadayansu suka kwashe dashi, daya daga cikin su yace kuna mamaki ne, toh mudin bah body guard dinku bane, kamar yadda kuka tsammani, mudin yan qungiyan asiri ne, uwar shedanu kawai muke wa aiki, Baku bah, mun zo gidan nan ne badan komai bah, sai don mu taimaka mata, ta cika burinta, akan ku.


Hada hannayen sa, Sadiq yayi waje guda, yace, Dan Allah badan mu bah, ku taimaka, ku barmu, mu futa, kuna dai ganin rayukansu yana cikin hatsari, kubari mu kaisu, asibity, Dan Allah, ya karashe maganar hawaye na shirin zubo masa.


Dariya suka kuma kwashe dashi a karo na biyu, suka hada baki wajan fadin, kuda futa, saidai gawar ku, baku bah, ran Sadiq da Khalid ne ya baci, lokaci daya, sukayi kan body guard din, domin, su koya musu hankali. Kokawa suka farayi da juna.


Cikin rashin sa'a kuwa ,yan qungiyar asirin suka hadu, suka dunga dukan su Khalid, babu gaggauta wa.


Gasu Dad da kabir rai a hannun Allah, saida suka farfasa wa su Khalid jiki, sa'anan suka wurgar dasu. Basu jisu a ko ina bah, sai jikin bishiyar gidan, yayinda kan sadiq ya fashe, yafara jini, shi Kuma Khalid ya suma.


Cikin tsanani da ciwo, Sadiq yayi yinkurin mikewa, amma akan ya cutura, Hatake jiri suka dibe shi, ya fadi sumamme.




Wallahi Baku ga komai bah, saina azabtar daku, irin azabar da ko da sunan ku baza ku iya tunawa bah.


Fatima dake d'ad'aure, tace Karima, ki dakata aka, kin ruga da kin azabtar da ahalin nan, ya isa aka, Dan Allah, kiyi hakuri, ki yafe Duk abunda akayi miki, koh Allah munayi masa laifi yana yafe mane, bare Kuma mutum Dan Adam.


Mom tace, ni kuma Banida zuciyar yafiya, bana yafe Duk abunda mutum yayi mun, kamar yadda na fada tun farko, dole saina kawo karshen wannan ahalin tukunan zan samu sukuni.


Doct khadija tace, Karima why, shekaru kenen kina gallaza wa wannan ahalin Ba tareda kowa yasani bah, aka kika rabani da ahalina kikamin sharri akan abunda ban aikata bah kika ce nayi, mene kuma ya rage, muguntar ta isa aka, kodan kinga baki samu wacce zata taka miki Burki bah,


Toh ni inada wacce zata taka miki Burki, wallahi, saikin gana wa aya zakinta.


Mom tace toh shikenen, inajiran Duk wacce zaki kirawo, ina jira,


Da sauri su, Aunty amarya da doct khadija, suka nufi hanyar waje. Tarar da su Sadiq sukayi a yashe cikin jini. Sosai su ke kuka, sun rasa yadda zasu sa rayuwarsu.


Cinci barsu sukayi suka nufi part din Su nadira dasu, inda kowacce ta Fara kula da mijin ta. Kwantar da su Dad akayi, yayin da Aunty amarya ta Bawa Dad magani, yasha,


bayan hour 3, jikin kowannen su ya lafa, yayinda su sadiq sun farka, kuma doct khadija tayi musu treatment, kowa aikinsu ya tashi, amma banda Kabir da haryanzu baiko Motsa bah.


Hankalin su Khalid ne ya kara tashi, Dad yace Meyasa Haryanzu Kabir bai tashi bah, Dan Allah ku ceci rayuwansa, banason wani abu yasami d'ana, doct khadija tace, nayi iya bakin kokarina wajan ganin ya farka, amma babu alamun zai farka, ina tunanin fa ya fada a doguwar suma.


Gaban kowannen su ne ya tashi, grandma tace khadija doguwar suma fah kika ce, yanzu menene mafuta.


Dafe kanta Aunty amarya tayi, tana mai nazarin mafuta a garesu. Da sauri Aunty amarya da Dag'o, sa'anan tace, akwai mafuta, juyowa gabadayansu sukayi, suka hada baki wajan fadin, menene mafuta?


Aunty amarya ta basu amsa da fadin, "Amriya", kwarai kuwa Amriya itace mafuta, zata iya, da taimakon ta, da taimakon Allah, zata iya cetan shi.


Doct khadija tace da kyar Amriya ta yarda, tazo, saboda ta fadamin cewar bazata kara tako kafarta cikin wannan gidan bah, kuma yanzu bah karamin tsana tayi wa Kabir bah, da kyar mu iya shawo kanta tayi. Tazo, Khalid yace insha Allah zamu yi iya bakin kokarin mu, wajan ganin ta zo. balla kofa sukaji anyi.




""""""""""""''''''''''''''''''''''""""""""""""""""""
Rasss gaban Amriya ya fadi ! , zuciyar ta, yafara Dukan uku uku, dafa ta doct Amina tayi tace, y'ata Amriya meyafaru?


Amriya tace, Ammi", jikina yana bani cewar, ahalin dana baro suna cikin halin tsaka mai wuya, tundazu gabana yake ta faduwa, yusuf yace toh kije ki gani mana, ko kuma muje,


Sai a lokacin Amriya ta tuna da irin cin mutuncin da suka mata. Amsa ta bawa yusuf da fadin, bazanje bah, na fasa, na ruga dana daukar wa kaina alkawarin bazan sake sanya kafafuwa na a wannan ahalin bah, dan aka, su nemar wa kansu mafuta, batareda taimakona bah.








COMMENT & SHARE PLS.
ALKALAMIN
AISHA M.B












Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JYYV16dbYaX1dykLX7EE91




https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*??
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.??


ALJANAR RUWA CE ??♀??
PAGE 4??7????4??8??
WRITTEN & DIRECTED??
BY AISHA M.B (BABY ISHA) ???


----------------------------------------


cikin rashin fahimtar maganar Amriya Doct Amina tace, taimako Kuma! Wane taimako kike musu? Ganin aka yasa Amriya Saurin chanza magana da fadin, Aa Ammi kawai dai nafada ne cewar bazan Kara taimakon su bah, amma wasa nake babu wani abu.


Rike hannunwan ta Ammi tayi tace Amriya kenen, yanzu kenen baki yarda dani bah, kinai tsoro ne? na ruga dana fada miki cewa ki dauke mu tamkar ahalin ki, ki daukeni tamkar mahaifiyar ki, ki fadamin gaskiya,


Dan jimmm Amriya tayi, sa'anan tace ina tsoron bayyana muku wacece ni ne saboda, dalilin akan ne yasa wancan ahalin suka koreni, Kuma ina tsoron kada kuskure daya faru ya Kara maimai ta kansa.


Kallon ta bban yusuf yayi, yana mai fadin, Aa y'ata babu abunda zai faru, ki shafa wa zuciyar ki ruwan sanyi, bazamu taba butul talki bah kinji,


Gyaran murya Amriya tayi sa'anan tace, a gaskiya nidin bah mutum bace kamar yadda kukayi tsanmmani, nidin ALJANAR RUWA CE, Amma Dan Allah kuyi hakuri ban fada muku asalin wacece ni bah kafun na Fara zama daku a matsayin bakuwa, ni yanzu mah zan tafi,


Kallon Ammi Amriya tayi tace, gaskiya Duk wacce ta sameki a matsayin uwa, toh tabbas bah karamar yar sa'a bace, rayuwata bah karamin kyau zaiyi bah,
Ni yanzu zan tashi na tafi zanje na cigaba da lallaba rayuwata.


Jin kalaman ta, yasa Jikin kowanne sune yayi sanyi, shafar fuskar ta Ammi tayi tace, Aa Amriya kada kidamu muna tare dake Duk rintsi Duk wuya, baza mu taba rabuwa dake bah, Sanin cewar ke bah mutum bace akan bazai sanya mu gujeki bah, koh kadan baki yi kalan wa enda suke cutarwa bah, Kuma nidin zan kulada ke tamkar yadda mahaifiya zata kuka da yarta .


Ki sani mu dake gabadaya ahalin ne yanzu, kada ki kara bambamta kanki damu kinji, nima na rasa y'ata mafi soyuwa a gareni kamar dai yadda kema kika rasa mahaifiyar ki, dan aka yanzu kinzama y'ata


tabbas kedin yar sa'a ce, na tabbata da mahaifiyar ki tana nan zata yi farin cikin ganin wannan d'iya tata wacce take tattare da sa'a da Kuma alkhairy, na tabbata a koda yaushe zata kasance tana Alfa'ari dake.


Murmushi Amriya tayi sa'anan tace nagode sosai Ammi, hakika kedin mahaifiya ce ta kwarai, bazan taba mantawa da irin alkhairy da kika aikata a gareni bah, rungume ta Ammi tayi Tana Mai fadin Allah yayi miki albarka y'ata.


Tura baki gaba Yusuf yayi Tareda cewar, wato yanzu Ammi kinsamu Auta, ni kuma za'a manta dani koh, murmushi Ammi tayi tace Yusuf kenen sarkin k'ishi toh kaima tawo na sama albarka,


Tashi yayi ya nufi inda su Amriya ke Zaune, yana isa ya zauna a kusada Ammi yace, toh nima asaka min albarka,


Tom shikenen yusuf Allah yayi maka albarka, Allah ya baka Mace ta gari wacce zata haifa min jikoki,


Yusuf yace, Aba Ammi jikoki kuma tun yanzu, Abba yace, toh yusuf idan bakayi aure ka haifan mana jikoki bah, me kake so kayi, wai yaushe zaka futo da mata nee,


Yusuf yace kada kadamu Abba nan bada dadewa bah insha Allah, Amriya tace Kardai ka dauko mana mumuna irin wannan budurwar taka dana gani.


Kallon sa sukayi baki daya, Ammi tace Dama kanada wacce kakeso baka taba Sanar mana bah, Sosa k'eya yusuf yayi Tareda fadin, Hmmm Ammi fah karya Amirya takeyi, babu wata budurwar danake da.


Amriya tace Bawani karyar da nayi, ai ranar nan na ganta, yusuf yace a ina kika ganta din? a awajan nan.. ganin Amriya na shirin tona masa asiri yasa yayi Saurin daukan pillow zai buge ta dashi,


Amriya na ganin aka tayi Saurin mikewa tareda nufa hanyar daki da gudu, Ammi tace Kardai ka cutar min da d'iya, dan bazan kyale ka bah, Yusuf yace Kinaji fah Ammi wlh karya take min


Abba yace mum yarda karya take amma kada ka Bari wannan watan ya Kare baka kawo mana suruka bah kaji na fada maka,


Yusuf yace aba Abba wata daya fah, ina laifin shekara, yanzu ni ina zanje na samo budurwa na nawa maka cikin wata nan,


Abba yace Oho duk inda Kaga yayi maka ka samo , mudai burin mu ka kawo ta mugan ta, inba aka bah da kaina zan aurar dakai.


Shagwaba fuska yusuf yayi, yana mai fadin Ammi kinajin mijinki koh wai ni zai aurar, kenen auran dole za'a min. Ammi tace kwarai kuwa auren dole za muyi maka, danna ga idan bah auren dolen muka makaba, toh bazaka futo mana da suruka bah.


Yusuf yace Tom shikenen zan futo da mata, amma gaskiya sai an karamin lokaci, danni bah yaro bane bah, Ammi tace kaji dashi dai,




-----------------------------
Cikin tsorata gabadaya suka juya don ganin wanene, juyawar su keda wuya suka ga Mom a tsaye ta dora wuka akan wuyan Fatima wato matar Dad,


dayan hannunta kuma rike take da files, Gyaran murya tayi sa'anan tace kuna ji kuna gani zan kashe ta a gaban ku batareda kun ceci rayuwarta bah,


Dafe zuciyarshi Dad yayi wanda yakeji tamkar zata fashe sabida kunci da takaici,


Cillawa Dad document din hannunta mom tayi, tana mai fadin wannan itace kadarorin ka gabadaya, ka saka hannu, kasaka cewar wannan kadarar Ba taka bace ta Karima ce, in Kuma bah aka bah, kana gani zan kashe ta har lahira.


Kallon Fatima Dad yayi wacce ta rintse idanuwan ta hawaye na zubowa kan kuncin ta, sannan yace dama Fatima kina a raye ban Sani bah, meyasa baki fadamin cewar kina raye bah Tsawon wadanan shekarun, kinsan wane Hali na Shiga tsawon wadanan shekarun da bakya tareda dani.


Kallon shi Fatima tayi tace, Bah lafi na bane, danasan aka zata kasance daban saka rayuwar ku da d'ana a cikin hatsari bah.


Aunty amarya tace bake kika saka rayuwar mu a hatsari bah, wannan shedaniyar matar ce,


Cikeda baccin rai Mom tace kwarai kuwa, nice nan, Wato har kun manta abunda kuka aikata mu shekarun baya da suka gabata kenen, kun manta yadda kuka Shiga tsakanina da yar uwata kuka saka mu cikin kunci da bakin ciki,


Dad yace wai waye yasa kaki kunci,shin nasan ki ne a da? Fadamana me muka aikata miki,


Mom tace bani zaka tambaya bah mahaifin kah dake Kabari zaka tambaya, danshi yasan komai da komai da yafaru, abunda ya aikata shi yake shafar y'ay'an sa kuma gashi harda jikokin da yatara,
Wato kun taru kuna cin Dukiya kuma kudin haram, kun taru kuna siyan tufafi abinci, yin abunda kuka gadama da kudin da ba naku bah ,


Kuma a akan kuke tunanin zan barku ku sha, akan bazata faruba, maza maza kasa hannu akan takardan nan in bah aka bah na yanka wuyan ta yanzu nan.


Cikin fusata Dad yace bazan saka bah, Kuma baki isa kiji mata koda kwarzane ne,


Murmushi mom tayi ta cilla mahaifiyar kabir gun Dad, babu bata lokaci Dad yayi Saurin riketa,


Mom ta kallesu tace, na baka nan da 24hours, da zaka sa hannu akan files dinnan, in bah aka ba, toh na rantse da ubangijin da nake bautawa, gabadaya saina kona ku da ranku, karasa maganar ta keda wuya ta fuce daga cikin dak'in.


Rungume Mahaifyar Kabir Dad yayi, yana mai fadin, ki gafarce ni Fatima, kiyi min aikin gafara, danasan kina raye kuma kina cikin gidanan, dana saka police sun kama Karima. Kiyi hakuri,


murmushi Mahaifyar Kabir tayi tace, babu abunda ka aikata min, yanzu burina shine na sanya d'ana a cikin idona, ina d'ana yake,


Nuna mata inda Kabeer ke kwance Dad yayi, Kallon wajan tayi, yayin da ta sauke idanuwanta akan kabeer, Wanda ke kwance har yanzu ba ya motsi.


Tashi tayi da sauri tareda nufan inda yake, kuramasa idanu tayi hawaye na sauka kan kuncin ta, tace Allah sarki d'ana, wancan azzalumar matar ta rabani dakai, bata Bari naji dimin ka bah, ta dauke min Kai, yanzu bah lallai ka soni kamar yadda ka sota a baya bah.


Tabbas yanada wuya ka iya yarda cewar ni asalin mahaifiyar ka ce, domin kuwa zaka kuma dauka ko wani raina mah hankali za'a kuma yi, tunda na haifo ka wannan duniyar baka taba ganina bah, bare ka kirani mama, ka taimaka ka kirani mahaifiyar ka koda sau daya ne kafun numfashi na na karshe, tana kaiwa nan ta fashe da kuka mai ratsa zuciya,


Jikin gabadayan su ne yayi sanyi, yayin da su kaji tausayin ta ya matukar kamasu. Hawayen dake shirin zubowa Dad yayi Saurin sharewa, tareda fadin, kada kidamu Fatima" yanzu ai kin dawo rayuwar shi, tabbas nasan bazai guje ki bah, Kuma na tabbata zai rike ki hannu bibbiyu,


Fatima tace da wuya ya yarda ni Mahaifyar sace, kasan yadda zuciya ta ke kuna da radadi, kasan yadda naji yayin da ina ji, ina gani, aka raba ni da dana daya tilo, shin meyasa bata dau raina bah ta barni a raye tana gallaza mun azaba, babu irin azabtarwar da bata yi min bah, tabbas laifi na ne, dana dora mata yarda ta, daban dora mata yarda ta ba, da bata aikata akan agareni bah.


Cikin rashin fahimta Dad yace, kamar ya? Shin dama kin San tane tuntuni? Shiru Fatima tayi ba tareda ta bawa Dad amsa bah.


Daga sama sukaji Doct khadija tace, Kuyi hakuri, ku gafarta min, duk abunda ke faruwa da ahalin nan gabadaya laifi na ne,
Tabbas a yau zan bayyana muku gabadaya abunda ya faru, da har kukaji nice da laifi,
Dakatar da ita Dad yayi da fadin, Bamua son jin komai daga gareki, kawai kiyi shiru khadija, hawayen ta Doct khadija ta share, tareda fadin Yahya a matsayina na kanwar ka, ka taimaka kabani Dama daya kacal, zan bayyana Duk kulla kullan da Karima ta aikata. Kaima kasan bazan taba maka karya bah.


Ka yarda dani, Dad yace khadija a matsayin ki na kanwata ai bai kamata ki aikata aka a garemu bah, meyasa kika ci amanan wannan ahalin, meyasa kikayi mana karya, ga mama nan kema kinsan yadda mama take matukar kaunan ki duda cewar bah ita ta haife ki bah, amma tafi rubuta ki akan mu.


Lokacin da Abban mu ya kawo ki gidan mu a matsayin marainiya, aka muka dauke ki tamkar yar ahalin mu har kika girma, soyayya, kulawa, da qauna, babu wanda bamu nuna miki bah, bamu taba bamban ta kan mu da ke bah, amma akan bai hanaki guduwa da wani namijin a wajan bikin ku wanda za'a muku keda Maryam bah, sannan kika je kika aure shi. kinsan halin da muka Shiga da muka ji labarin kin gudu da wani saurayin,


Kinsan kunya da bakin cikin abunda kika aikata ya sanya mahaifin mu har silan akan yasa ya rasa rayuwar shi, meyasa tun farko baki fada mana ga wanda kike so bah, ai dashi zamu baki, basai kin kunyata mu a idanuwan jama'a. Amma bakomai komai yayi farko zaiyi karshe.


Hawaye ne yafara gangaro wa daga idanuwan Doct khadija, cikin sheshekar kuka tace Dan Allah kubani dama daya zan fada muku duk abunda ya faru , tabbas kun yimin gurguwar fahimta ne, ku tsaga ku saurare ni.


Grandma tace toh shikenen y'ata munajin ki, Muhammad Kabari ta fada mana abunda ya faru,


Dad yace Tom shikenen muna jin ki, Kallon su Khalid da su nadira Dad yayi yace, ku bamu waje zamuyi magana.


Dakatar da Dad doct khadija tayi da fadin Aa zuyi zaman su, suma aiba yara bane, ka barsu Suji abunda ya faru.
Amma dan Allah kafun na fara inaso kowa ya bada hankalin shi wajena.


Zama sukayi baki daya, yayin da kowa ya nutsu, tattaro nutsuwan ta Doct khadija tayi,
ta fara magana kamar aka.


Asali nida Karima babban kawaye ne tun muna bording school, zaro ido gabayansu sukayi, what! Dad yafada.


Kwarai kuwa nida Karima babban kawaye ne, Kuma itadin sunan ta hassana ne, sudin yan biyu ne, but not identical twins, abunda yasa bakusan Karima bah shine bata taba yarda tazo gidan mu bah, saidai Ni dakuma Amina, koda tazo bata taba yarda ta shigo bah.


sunan yar uwarta Amina , mun taso Cikeda kaunan junan mu, ko ina tare muke zuwa gidane kawai ke rabani dasu, saboda qaunan junan da mukeyi har alkawari muka daukan wa junan mu cewar Duk y'ay'an da muka Haifa

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads