Showing 105001 words to 106900 words out of 106900 words
Chapter 36 - ALJANAR RUWA CE COMPLT BY ASHA M.B .txt
ce kamar yadda kuka sani, dan aka yanzu na samar mata da makarantar medicine, insha Allahu idsn ta gama, hospital ɗin ta yana nan a hajiye, mallakin ta".
Masha Allah, gaba daya suka furta tare da fadin, gaskiya abin yayi sosai muma yanzu munada likita a gida cewar grandma.
Saida suka kara ci suka sha, sannan su Kabir suka tashi, sannan yace musu zasu tafi akwai wani guri dasasu je.
Ba yadda Ammi ta iya, aka ta rabu dasu suka tafi.
Futar su keda wuya, shima doct Habib ya fuce daga gidan.....
Tuka motar yake yi batare da jinkirtawa ba. Kallon sa Amriya tayi, sannan ta mintsini hannun sa, dan ƙaramin kara Kabir ya saki!, sannan yace, "Maman Hydar kodena da zafi fah". Ya fada tare da haɗe rai.
Taɓe baki Amriya tayi tace, ɗazu naji kace zaka yi min kishiya koh, toh yau nisa kaine. Murmushi Kabir yayi, sannan yace, "aba Aljanar ruwa ta, wasa nake fah".
Haɗe fuska Amriya tayi tace, " bana ce karka kara kirana Aljanar ruwa bah?, ta fada tare da galla masa harara.
Hydar dake kwance a cinyar ta ne ya motsa da alama ya gaji da kwanciyar. Mikar dashi Amriya tayi sannan ta fara masa wasa, yana dariya har suka isa wani makeken gida, kana gani kasan naira sunyi aiki hanan. Most especially colour da kuma design na gidan, gaba daya a tsare gidan yake gwanin ban sha'awa.
Fitowa Amriya tayi daga cikin mota hannun ta rike da Hydar tace, " nan kuma ina ne ka kawo mu?.
Murmushi Kabir ya sakar mata, daga bisani kuma ya karbi Hydar daga hannun ta yace,"mu siga ki gani mana.Ni fa tsoro nake ji cewar Amriya.
Dariya Kabir ya kwashe dashi sannan yace, "aba jaruma, sai kace bake ce wannan Aljanar ruwan ba wacce koh kaɗan batasan tsoro ba".
Ture masa keya Amriya tayi tace, "Ni nace maka banaso Koh, nace kadai na cemin Aljanar ruwa, Ni yanzu mutum ce kamar kowa ba Aljanar ruwa bah". Shi kenen toh kiyi hakuri mu shiga Koh cewsr Kabir.
Kallon sa tayi cike da jin aushi tace muje toh. Shiga ciki suka yi, masha Allah abinda baƙin Amriya ya furta kenen.
Kallon parlour tayi wanda komai golden colour ne sai milk din labulaye. Saida Kabir ya zaga da Amriya gaba daya gidan. Tukunan suka fito waje.
Kallon sa Amriya tayi cike da mamaki tace, "wannan gidan waye?, meyasa muka zo. Murmushi Kabir yayi yace wannan gidan ki ne halal malak. Ni na siya miki shi tun shekara daya daya gabata. Kuma nan zamu dawo da zama insha Allahu ".
Farin ciki ne ya lulluɓe fuskar Amriya! tace, "gaskiya nagode sosai Kalb, murmushi Kabir yayi sannan yace, " menene kuma na godiya, bayan ba'a gama bah, jan hannun ta yayi sannan ya nufi parking space da ita.
Mika mata mukullin mota yayi sannan yayi mata nuni da ɗan yardar sa. Kallon inda ya nuna tayi, taga kerarriyar mota kirar ferari.
Maida kallon ta tayi ksnsa tace, wannan fah?, Kabir ya bata amsa da faɗin, " shima kyauta ce na musanman na baki, domin idan zaki je school ki dinga tukawa, dan bayan iya karbar miki driver bah, saboda ni inada kishi, bayan juri ganin wani namijin yana tuka matata bah, kuma sannan ya dinga lalle mun ita bah".
Ba zato, yaji ta rungume shi! tare da fashe wa da kuka, rungume ta shima yayi,sannan ya fara shafa batan ta. Ɗago ta yayi yace, " menene kuma na kuka, bana ce miki banaso na kara ganin hawaye daga fuskar ki ba?".
Share hawayen ta Amriya tayi sannan tace, "ina mai godiya a gare ka Kalb, ina fatan muyi doguwar rayuwa tare.mu samu zuri'a mai albarka, yaran mu su sami ingantacciyar rayuwa, sannan na kasance da kai har nunfashi na, na karshe a duniya".
Ameen Kabir ya fada yana mai faɗin, "yanzu dai muje na koya miki mota koh, yau gaba daya Abuja zamu zagaye, sabo da yau ranar ki ne mu Queen".
Murmushi Amriya tayi sannan tace tom shikenen Kalb muje koh.
Tada motar Kabir yayi, sannan suka bar harabar gidan.
Comments & share Please
ALKALAMIN
A'ISHA M.B
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JYYV16dbYaX1dykLX7EE91
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
ALJANAR RUWA CE 🧜♀️🧜♀️🌊
(LAST PAGE)
PAGE 5️⃣9️⃣▶️6️⃣0️⃣
WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY AISHA M.B💞💞
(Zinariyar 🪙 Jajirtattu)
____________________
Aka rayuwa ta cigaba, tsakanin waďan nan ma'aurata guda biyu.
Yayin da suke farin ciki da qaunan juna. Gefe guda kuma salma ta samu karuwa na santalelen ďanta Wanda yaci suna Junaid.
Sosai akayi farin ciki da samu wannan ďan da su Salma suka yi.
Bangere guda kuma su Amriya suka koma hadadden sabon gidan su, cikin ta kuwa harda fara zuwa makaranta nursing school da Amriya ta fara yi. Sannan ta kuma haifo yarta kyakyawa son kowa kin wada ya rasa, wacce ta ci sunar mahaifyar yusuf, wato Khadeejert, amma suna kiran ta Mama.
"BAYAN SHEKARU BIYAR"
Fitowa tayi cikin labcourt ďinta, wanda yayi mata kyau sosai, bangare guda rike take da statoscope ďinta a wuya.
Da gudu wannan karamar yarinyar kyakyawa, sakk suke kama da mahaifyar ta. ta shigo cikin parlour sannan tace, "miemie kiyi sauri zamu yi late fah! ".
Murmushi Amriya tayi daga bisani tace, "Mama kenen yahya kin Hydar baiyi complain bah sai ke, keda Baban ki ban san wanda yafi wani takura bah". You mama kije Gani nan zuwa". Ta fada tana mai sanya takalmin ta, wanda yayi matukar kara mata kyau.
Mike wa tsaye tayi, sannan ta ja hannu Mama suka nufi hanyar waje, direct parking space suka nufa,
yayin da gefe guda, Kabir yake rike da yarinya wacce ba zata wuce shekara guda a duniya bah. Shima yayi kyau yayi kiba, yayi fresh.
Murmushi ya sakar mata, sannan yace matar, kinga yadda kika yi wani kib'a kuwa?, gaskiya na iya kiwo, shagwabe fuska Amriya tayi, sannan ta karbi Elharm daga hannu sa tace, " ba wani nan, Kai baka ga yadda kayi kiba bah, ai nice nafi kula da kai".
Murmushi yayi sannan ya Kalli su Hydar yace, "tsakanin ni da miemie ku wanene yafi Kula wa da wani?.
Kallon Amriya da Kabir Hydar yayi sannan yace, "my super hero Dad kaine Kafi kulada miemie ". Mama tace,
"no Miemie tafi kula da Dad". so miemie is my favorite ". Murmushi Amriya tayi tace, "yes! that's my dear ".
Kallon su Kabir su Amriya suka yi sannan suka yi musu gwalo. Hade rai Hydar yayi yana gunguni. Janyo shi Kabir yayi sannan yace, "don't mind them, karka damu ko zamu rama aii.
girgiza kai Hydar yayi sannan yace, "yes Dad, idan muka siya rufaida kada mu san musu, mu shanye koh, murmushi Kabir yayi yace, "yes son abinda zamu yi kenen, idan muka siya kada mu basu ".
Kallon juna su Mama suka yi da Amriya daga bisa ni suka kwashe da safiya!,
Kallon su Mama tayi tace, "na gani, ba bari, mun fi karfin rufaida, mu mai gaba daya zamu yi, company ta gaba daya zamu je mu dauko, saimu ga a ina zaku siyo". Ta Karashe maganar tare da ďaga wa Hydar gira ďaya.
Murmushi Amriya tayi, yayin da take Kallon ahalin ta cike da farin ciki, da qaunan juna. Hawaye taji yana kokarin zubo mata. Da sauri ta share hawaye ta sannan tace, "maza ku tawo mu tafi, kada na makara a wajan aiki".
Shiga cikin motar gaba daya suka yi, daga bisani Kabir ya tada mota sannan ya kalle su yace, " kun san menene? , Yau babu gurin aiki ba makaranta".
Kallon sa Amriya tayi tace, meyasa?, Kabir ya bata amsa da cewa, Yau zamu je yawon shaka tawa ne. Amriya tace, "Aa ni ina da abin yi a office bazan je bah ".
Please miemie ki yarda muje cewar Mama. Kawar da Kai Amriya tayi tace,
" no am going nowhere ".
Hakuri suka shiga bata gaba daya, yayin da suka cika ta da surutu.
Ganin babu sarki sai Allah yasa ta faďin, "shikenen na amin ce mu tafi".
. Yeeee! Yaran suka furta cike da farin ciki. Murmushi Kabir ya sakar mata yace, matar kinsan ina zamu je?
Girgiza masa kai Amriya tayi tace nop! ban sani bah .
Kabir ya bata amsa ta cewa swimming costume zamu je, ya fada tare da ďaga mata gira daya.
Zaro idanu Amriya tayi sannan tace, "what! no bazan je bah a dawo lafiya.
Dariya Kabir yayi yace, " koh kina tsoron zama Aljanar ruwa ne eh?. Ya fada tare da kista mata ido ďaya.
Ture masa keya tayi, sannan tace, "bana tsoro muje ďin toh".
Murmushi Kabir yayi sannan yace,"your wish is my command ". Yana kaiwa nan ya tada mota, tare da kunna musu waka suka fara rerawa daga bisani ya figi motar suka fice daga gidan. Cike da farin ciki da qauna Kabir yace princess yau dai za'a a bani abin koh, harara Amriya ta galla masa sannan tace, "bazan bayar bah ta fada yayin da take him sonsa na Kara shigar ta. Murmushi kabir yayi yace, "ai nasan mah ba zaki hanani bah, domin yaran mu uku kuma ni ina bukatar kari". Murmushi Amriya tayi tace shikenen toh.
Kara wa motar gudu Kabir yayi cike da suka cigaba da tafiya a motan......
*💞 THE END💞*
*Alhamdulilah, Alhamdulilah Alhamdulilah, ya Allah ina Godiya daka bani ikon kammala Wannan littafin cikin koshin lafiya*
*Darusan dake tattare da wannan littafin in mai amfanuwa ce ya Allah kasa ta amfane alumma muslumai gaba daya.*
*Kura-kurai dake littafin kuma ya Allah ka yafe mana Dan falalar wannan watar da muke ciki na shita shauwal.🙏🏻🙏🏻🙏🏻*
*Insha Allahu Gobe zan cigaba da rayuwa da macijiya paid 300 Complt*
*kuma sannan zan fara sakin WAYA FI CANCAN TA*
, *kamar yadda kuka sani paid book #500, masu tambaya na nawa ne toh 500 ne Complt dinsa. Dan aka idan kinyi shirin biya, ki tuntube ni*
*fan's masu labe duk ina Kallon ku, Dan aka kada kubari a Baku labari WAYA FI CANCAN TA, domin kuwa littafin zaizo muku da sabon salo na kayatarwa, ilimantar wa, wa'azantar, da kuma nishadantar wa*
*DIAMOND 💎 STAR 🌟
LADIES🧝♀️*
(*we stand together*)
My greetings to you all
*Mom muwadda*
*Elharm pinky darling*
*Meerat Umar*
*Maman ihsan* *momeeyn irfa*
*Allah ya kara shige muku gaba sarauniyar mu, muna gdy da kara karfafa mana da kuke yi, Allah ya kara hada kan zuka tanmu*.
*Toh my fan's, my regards to you all*💃💃💃
*saimun hadu daku a littafin mu na gaba*
*ALKALAMIN*✍️
*AISHA M.B*💞💞💞
(*Zinariyar 🪙Jajirtattu*)
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 08138873799
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************