Showing 66001 words to 69000 words out of 106900 words
Chapter 23 - ALJANAR RUWA CE COMPLT BY ASHA M.B .txt
kifuta daga gidanan, Kokuma nasa a kulle min kee a magarkama.
Hada hannuwanta waje guda, Amriya tayi tace, "Naji basai ka yarda dani bah, amma Dan Allah ku yarda da maganata, da macuciya kuke rayuwa, wannan matar muguwa Ce, ita takashe Ummi, Dan Allah ku yarda dani. Gaskiya nake fada muku, ku taimaka ku ceci baiwar Allah dake dakin ......" Bata karasaba, taji Khalid yana Fadin tunda yace "kije, kitafi mana."
Mom dake bayansu tasaki murmushin mugunta, Tareda daukan ruwan dake cikin Glass Cup na kan dining table, ta watsa ma Amriya Ajiki.
Gurnani Amriya tafarayi, inda fatarta yafara sabulewa, faduwa kasa tayi, tana birgima, sosai tsoro da fargaba yakama ko wannensu,
A hankali, sufarta yafara chanzawa, har sufarta na ALJANAR RUWA ya bayyana.
Zaro ido gabadayansu, sukayi, kara su Khalid suka saki, inda gradma tafadi a wajan sumammiya.
Dafe kansa Kabir yayi wanda yakeji kamar, Hana buga masa guduma. Sadiq da Khalid da sauran yan dakin suka jaa da baya, banda Kabir dayayi zololo, yana Kallon tah.
Juyo da jelanta, na Aljanar ruwa tayi tace, "kwarai nidin ALJANAR RUWA CE, nafada maku cewar, nidin ALJANAR RUWA CE, amma kuka karyatani, toh yau na bayyana kaina"
Dama nace Duk ranar da akasan ni ALJANAR RUWA CE, toh zamana a gidan nan yakare. "A yaud'inan zan koma duniyata, banki bah kona mutu konayi rai."
Zan tafi, bazan sake dawowa bah, Hawaye ne, yafara bin kuncinta, share hawayenta tayi, da bayan hannunta, tacigaba da fadin, kiyafemin, Nayi muku karyar cewar, na manta abunda yafaru, kudin mutanen kwarai nee kun zauna dani,
batareda kunsan asalin Wacece ni bah, Kuma yau zaku rabudani, Dan kunsan asalin Wacece nii, ina godiya da irin kulawa da soyayya da kuka nuna min,
Allah yasaka muku da mafifi cin alkhairy.
Ni zantafi, zan koma inda nafuto, amma Kuma taya akan zata yiwu kenen batareda zobena bah, saidai na zauna, a duniyar ku, har sai sanda aka gindaya min cewar zan mutu, idan ban koma duniyata bah.
Kallon kabir tayi tace, nagode da irin wannan sakayyar. Kuma zaka dawo neman gafarata a gareka. Tana kaiwanan, halittar ta yadawo na mutane. Tashi tayi tanufi hanyar waje.
Dakata, taji Kabir yafada, juyowa tayi tace, meyafaru, Kabir yace kin manta baki karbi takardar sakin ki bah, kije na sakeki, saki daya.
Murmushi wanda yafi kuka ciwo Amriya tayi, tace, nagode sosai. Tana kaiwanan ta fuce daga gidan.
Sosai tausayin Amriya yakama su Aunty Amarya.
Direct wajan gradma da mom suka nufa Tareda .watsawa gradma RUWA, Hatake gradma ta farfado daga suman datayi, ririke kabir Tayi tace waiyyo, ku taimakeni, kabir yace aita ruga data yi tafiyarta,
Rike mom DAD yayi yanufi dakin shi da itah, domin yayi mata maganin ciwon dake kanta.
Tafiya Amriya keyi tana kuka, batareda tasan ko ina bah na layin,
Wani bishiya ta hango, akan yasa ta nufi inda bishiyar take tareda, zama a karkashin bishiyar,
Zama tayi, ta chunkushe waje guda, tana kuka, sheshekar kukan tane ya tashi wata mahaukaciya, dake kwance a wajan,
Tashi mahaukaciyar nan tayi, tanufi inda take,
Mahaukaciyar ta ce, "Kai wanene wannan, me yasa kike kuka."
Tausayin Amriya ne yakama wannan, mahaukaciyar, daga Amriya mahaukaciyar tayi, hada ido sukayi da mahaukaciyar, da sauri mahaukaciyar taja da baya. Tana fadin kece, kece,
"Tabbas kece, Kallonta Amriya tayi, tabbas ta gane wannan matar, itace na jiya wanda ta gani a asibity."
Cikeda tausayawa, Amriya tace,
"Kedin Wacece, waye ya mayarda ke aka, menene kika aikata, ke dama asali mahaukaciya ce?"
Tsugunawa mahaukaciyar tayi, tareda fashewa da kuka, tace,
"Dama ni mahaukaciya ce, bansaniba, Dama hauka nakeyi, shikenen Ashe Dama ni mahaukaciya ce, Dama Banida lafiya."
Rike hannunwanta, Amriya tayi tace, ki nutsu, kada kidamu zaki, zaki samu lafiya da yardar Allah.
"Zan warkar dake, zaki daina hauka, Kuma Duk wanda, tayi miki aka saita dandani kudarta."
Rike hannun matan Amirya tayi gamm, Tare da rintse idanuwanta, Hatake aka Fara wani iska, Tareda guguwa, wanda ya gauraye gabadaya ilahirin, wajan.
.
MANAGE PAGE PLS 馃檹馃檹
COMMENT & SHARE 馃檹
ALKALAMIN 馃枈锔忦煐婏笍馃枈锔?
AISHA M.B (Baby isha)
2/28/24, 22:12 - AISHA M.B (Baby isha): https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
JAJIRTATTAU WRITER'S ASSOCIATION 馃枈锔?
(J.A.W)
Rubutu baiwa ce daga Allah,jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan kasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauk'i鉁忥笍
ALJANAR RUWA CE 馃鈥嶁檧锔忦煂婐煂? PAGE 4锔忊儯3锔忊儯鈻讹笍4锔忊儯4锔忊儯.
WRITTEN & DIRECTED 馃枈锔? BY BABY ISHA馃挒馃挒 (AISHA M.B)
-----------------------
Jikin mahaukaciyar ne ya fara karkar wa, ta fara shure shure da kafafunta, lokaci daya matar ta kwallah kara wanda ya gauraye dajin.
Daga bisani Kuma tayi Tsit alamun ta tsuma. Kallon ta Amriya tayi, cike da tausaya wa, tace insha Allah zaki samu lafiya, babu wanda zai Kara Kiran ki mahaukaciya,
Tana gama fadin aka ta Mike tsaye Tareda jin ginar da matar a jikin bishiya, daga bisani Kuma tayi tafiyar ta.
Saida dare yayi sosai
matar ta farka daga baccin da takeyi, Kallon Jikinta tayi, taga gany'an yak'i da datti a jikin tah.
Salati tasa ka tana mai fadin, meya ke faruwa dani, menene wannan Kuma? Taya akayi nazo wajan nan. Tambayar data Shiga yi wa kanta kenen. Rike kanta tayi domin ta tuna sanadi yar tah fada wa cikin wannan yana yin, amma akan ya cutura. Ba yadda ta iya, aka tafara ciccire dattin dake jikin ta.
Kallon ko ina na jejin tayi, tace yanzu ta ina ne zan gane hanyar gida, haske ta hango daga Chan nesa, akan yasa ta karasa wajan domin ta nemi taimako".
Zuwan ta keda wuya" ta tarar da Amriya a Zaune a wajan tayi tagumi. Kallon ta matar tayi cikin far gaba da tsoro tace! Sannu baiwar Allah.
Dagowa Amriya tayi ta dora idanuwan ta akan matan. Ganin aka yasa Amriya Mike wa, tace laa kinsamu lafiya, yanzu zaki iya fada min wanda yayi miki wannan aika- aikan
Cikin rashin fahimta doct khadija tace! Kamar ya kenen, Dama kin San ni ne,
Amriya tace, Eh nice na warkar dake daga ciwon hauka da kike, inaso ki fada min Wanda yayi miki aka.
Dafe kanta doct khadija tayi, sai a lokacin ta fara, tuna abunda ya wakana a baya. Kallon Amriya tayi tace,
Wata azzaluma,Mara imani, wacce babu tsoron Allah koh ka d'an a zuciyar tah,Dan zuciyar tah a bushe take. Koh d'igon imani batadashi
Kallon ta Amriya tayi tace, koma Wacece wan nan baza ta taba kai mom rashin imani bah.
Doct khadija tace,wacece ke, meya kawo ki cikin jejin nan tsakar daren nan ,
Amriya tace wacce tayi sanadi yar ki fada wa wannan halin da kike ciki, toh nima itace ta kawo ni jejin nan, tayi amfani da makircin ta wajan kora ta daga gidan. Na tabbata matar nan saita gasa musu haya a hannu,saboda bana nan, Kuma tasa ka sun koreni, Tana nuna musu soyayya a fili, ba tareda sun San cewar azzaluma ce bah.
Doct khadija tace kina nufin Karima devilish mother, Amriya ta bata amsa da fadin kwarai kwarai ita,
Doct khadija tace kenen ke wace a wajan su. Kallon doct khadija Amriya tayi tace, nidin matar wanda take karyar cewar danta ne,
Doct khadija tace kenen kema kin san bah ita ta Haifi Kabir bah? Amriya ta bata amsa da cewar kwarai na sani.
Share hawayen da ke kokarin zubawa Amriya tayi, sannan tace kuma na daukar wa kaina alkawari cewa nida Kara dora kafana a wannan gidan har abada. Koda kuwa akan zaiyi silan ruguje war rayuwa ta, Dama lokaci kalilan ne ya rage mun a raye, kasan cewa ta Kuma ALJANAR RUWA, akan bazai sa na kara taimakon wannan ahalin bah.
Ajiyan zuciya doct khadija tayi tace, tabbas Dan Adam butulu ne, amma kada dalilin aka yasa ki k'i karasa ladar ki na taimakon wannan ahalin, da nice na samu damar da kika samu a wan nan gidan toh da tunan na tona asirin Karima, na bayyana gaskiyar da ke boye wajan shekara da shekaru. Amma ina akan bazai yuhu bah saboda, taruga ta hura musu wutan tsana ta a zuciyoyin su.
Dan Allah inaso ki koma gidan, ki karasa aikin ki, ke kika dace ace kin kammala wannan aikin bah wani bah, saboda kema ta sha feki.
Kwance yake akan makeken gadon sa, yana juyi.gabadaya ya kasa samun nutsuwan sa, tashi yayi, yafara Kai kawo a cikin dakin.
Zama yayi sannan ya dafa kansa yace, menene yake faruwa da ni ne, Meyasa na kasa samun nutsuwa tunda na Kori yarinyar nan. Kardai ta yimin asiri, back to sender, yafada yana shafa kansa.
Daukan wayar sa yayi, ya fara Kallon videos na shiek tijjani, aka ya ci gaba da kalla har aka zo kan wani video.
Playing yayi, yafara kalla, su Ummi ne da nadira wajan upstairs, suna cewa nadira taje, zata yi nasara, shikuma a lokacin sadiq ya kunno kai, Tana shirin fada wa kan kabir, tafada jikin Sadiq.
Dariya yasaki, yana mai fadin wai Dama aka nadira ta ke sona ban sani bah, Gashi Allah yaba ta, mafi alkhairy agare ta.
Next video ya kunna Tareda Kara volume, Amriya ce Zaune tana kuka inda su nadira sai rarrashin ta suke,
Amriya tace Dan Allah inason zanje na basa hakuri, kalisat tace ke haka zalunta Kuma kece da Bada hakuri,
Amriya tace kawai inason zan Bashi hakuri, dalili na mom ta wanka masa mari, da wane ido kike so ya kalle ni, wlh bana son naga abunda zai bata masa rai. Ta karasa maganar Tareda fashe wa da kuka.
Sosai yaji tausayin ta ya kama sa, shafa fuskan ta yayi,ta wayan yace, Allah sarki tabbas na sani cewa koda yaushe cikin kun Tata miki nake,
Baki taba roka ta wata alfarma na cika miki bah, tabbas nidin mugu ne Kuma mara imani, tabbas Nayi dana sani, kiyi hakuri ki yafe min.
Murmushi Aunty Amarya ta saki, babu Kalman da take furta wa sai Alhmadulillah, Alhmadulillah, abunda take ta Nana tawa kenen.
Share hawayenta Aunty Amarya tayi, san nan ta fara Kwan kwasa kofan dakin.
Saurin hajiye wajan yayi, yace, yes who's that at this late time. Aunty Amarya tace nice Kabir,
Kabir yace come in, Shiga ciki Aunty Amarya tayi, tare da samun guri, a gefen gado ta zauna.
Cikin rashin fahimta Amriya tace taya ta shafe ni, menene hadi na dasu, nima zobe na ne ya kai ni gidan, amma da babu abunda zaisa na futo duniyar mutane .asali mah ni na tsani Bil Adama saboda ya wanci su, basuda imani.
Dan aka babu abunda zai kara hada ni da wannan gidan, tunda na barta toh na barta kenen. Zobe na Kuma sai dai na mutu, amma nida gidan nan Ar abada.
Doct khadija tace, kada ki ce aka Amriya na sanki fiye da tunanin ki, a tunanin ki yau na fara Ganin ki, Aa na sanki shekara da shekaru.
Dan aka dole ki koma cikin wannan ahalin, saboda a nan zaki San asalin Wacece ke, menene sanadin fada warki wannan halin, taya ya kika zama wata jinsi da ban bana mutane bah, toh Duka tambayar ki, amsar ta itace wannan ahalin, sune zazu baki amsar tambayo yin ki.
Mikewa Amriya tayi a fusace tace, ni na ce inason Sanin wani abu game da rayuwa ta ne, bana bukata, domin ko na sani koh ban sani bah, lokaci kalilan ne ya rage min a duniya.
Kuma nidin ALJANAR RUWA CE, bah mutum bah, wato so kike na koma wannan ahalin da suka watsa min kasa a ido, akan baza ta taba faruwa bah, Dan aka idan zaki yi wani zance kiyi amma banda, koma wa tah cikin wannan ahalin.
Dan jimmm doct khadija tayi tace, nima a lokacin da, babu abunda ban fada bah, nace bazan kara koma wa wannan ahalin bah, amma nice yanzu nake rabar su, domin na ceto rayu kansu dake cikin hatsari.
Amirya tace wannan Kuma su ta shafa bani bah, tsakanin su ne wannan, su suka San laifin da suka yi har wannan matar take neman rayu kansu ruwa a jallo.
Doct khadija tace, ni kuma idan kika min wannan al farman, kika koma gidan, toh na miki alkawarin cewar,
Zan nuna miki mahaifiyar ki, juyowa Amriya tayi da sauri, tace kin San mahaifiya ta ne, nifa mahaiya ta! ta mutu, Kuma ita din ALJANAR RUWA CE bah BIL adama bah,
Murmushi doct khadija tayi tace, kwata kwata, mahaifiyar ki bata mutu bah, Kuma ita din bah ALJANAR RUWA bace, mutun ce kamar kowa.
Amriya tace kenen mahaiya ta, bah ALJANAR RUWA na ce, BIL adama ce, Kuma tana raye .
Toh Meyasa zata tafi ta barni wajan shekara da shekaru. Meyasa ta wulakan tar dani, bata ko ne mana, akan yana nufin kenen bata damu dani bah? Kokuwa akan yana nufin bata sona.
Doct khadija tace kada kiyi wa mahaifiyar ki gurguwar fahimta, asalima ita bata San kina raye bah, Kuma babu ranar da zata tashi ta fadi bata yi kuka akan ki bah.
Dan aka idan kika cika min alkawari wajan tona asirin Karima, toh tabbas zan kaiki wajan tah.
Share hawayen ta Amriya tayi tace, shikenen zan tafi, zan koma gidan badan komai bah Dan na cika miki muradin ki, amma daba Dan aka bah, da bazan Kara zuwa gidan bah.
Yauwa doct khadija tace, sa'anan ta ce shikenen yata Allah yadawo dake lafiya,
Mi kewa Amriya tayi, lokaci daya jiri ya di beta , da sauri doct khadija ta rike ta, Tareda zaunar da ita tace, meya faru,
Amriya tace wallahi ban sani bah ,tun dazu nake jin zuciya ta na tashi.
Kallon idanuwan Amriya doct khadija tayi tareda Kallon tafun hannunta, tace shin kin keda mijin ki, kun taba yin mu amala ta aure.
Cikin jin kunya, Amriya ta rufe fuskan ta da tafi hannun ta, tace, Eh sau daya ne.
Doct khadija tace kina cikin kunci, ga abun farin ciki ya riske ki, toh na taya ki murna kinada juna biyu,
Zaro ido Amriya tayi gaban ta yayi mummunan faduwa, tace juna biyu fa kika ce, nidin Kuma,
Kallon ta doct khadija tayi tace, me ya faru, kamata ai ace kina farin ciki, da irin wannan abun.
Amriya tace, bawai bana farin ciki bah, tunanina daya ne shine nasan Kalb bazai taba son Dan da zai futo daga kar kashi na bah.
Saboda nidin ALJANAR RUWA CE, Kuma babu abunda yafi tsana a duniyar nan sama Da jinsi na wato na Aljanar ruwa. Kuma ni ina matukar sonsa.
Yanzu Gashi lokaci da ya rage min a duniya kalilan ne. Doct khadija tace kada Ki taba sare wa akan abunda kike so ,dole da jajurce warki da Kuma adua, shine zaisa ki cimma burin ki wanda yake kyakyawa.
Bai ka mata ace ki shiga gidan cikin bakin ciki bah, ka mata ai ace kishiga cikin farin ciki da annashuwa,
Yanzu ki kwantar da hankalin ki, kije gidan cikin karfin gwiwa, Kuma ki fada masa cewar ki nada juna biyu,
Nasan tabbas bazai k'i ki bah. Maza ki tafi, ki Kara karfafa wa kanki gwiwa kada ki saduda tun,kije ki fuskan ce shi, nasan tabbas zai fahimta.
Godiya amriya tayi wa doct khadija, cikin farin ciki ta bar wajan. Tareda nufa hanyar gidan su Kabir.
Aunty amarya lafiya na ganki acikin wannan lokacin, murmushi Aunty Amarya tayi tace, kwarai kuwa lafiya,
Shawara nazo na baka, badan ko bana sonka bah, sai don soyayya da nake maka da Kuma, yan gidan nan.
Okay Tom ina jinki Aunty. Aunty Amarya tace , Kabir inason ka saura reni da kyau, inason fada maka abu dake cin rai na na wajan shekara da shekaru,
Kabir! Dago wa yayi ya kalle ta sannan yace na'am aunty, Aunty Amarya tace, ina son na fada maka cewar, Duk abunda Amriya ta fada dazu babu karya acikin ta, tabbas abunda ta fada gaskiya ne. Mom itace ta kashe Ummi Kuma.... Bata karasa bah taji yace,
Aba Aunty, aba Aunty, koda kowa zai biyi bayan aci dun duniyar mom ai bazaki ciba .
Na tabbatar miki da cewar karya Amriya tayi wa mom, so take ta hada mu nida mom dina, Kuma bata San Allah yafi karfin tah bah.
Murmushi Aunty Amarya tayi, sannan tace, Allah sarki Amriya baiwar Allah, kina taimako, kina sa rayuwar ki a hatsari amma basu San kina yi bah,
Kace ka tabbatar cewa karya Amriya take koh! Kabir yace yes of course, am 100% sure that, karya take yiwa mom.
Aunty Amarya tace tunda ka tabbatar, toh menene hujjar kah.
Kabir yace ni Banida hujja amma nasan mom can never do such thing, idan mah tayi ribar mee zata ci, Amriya kawai yar leken asiri ce, maybe wani ne ya turo ta gidan nan.
Wai kai Kabir Meyasa baza ka yi nadamar abunda kakeyi bah?
Saboda mahaifiya ta, ta tsaya min, Kuma Duk mahaifiyar da ta iya tsaya wa domin Kare rayuwan danta, babu wata ma'alukiya da zata iya cin galaba akan tah.
Kenen kana nufin Amriya bah mutuniyar kirki bace,
Dai dai lokacinda Amriya ta karaso cikin gidan. Jin muryar Kabir tayi, taji yace kwarai kuwa, Amriya bah mutuniyar kirki bace,
Chakk Amriya ta tsaya, Tareda jigina ajikin kofan Tana jin abunda yake fadin.
Kabir yace tunda yarinyar nan ta dora kafa fuwanta a gidan nan, toh tun lokacin masifa da baka'i suke ta faruwa, tabbas yarinyar nan bah mutuniyar arziki bace.
Da nafara dana sani abunda na aikata mata, amma shigowar ki yanzu, yasa na tuna da cewar tabbas mashekiya ce , muguwa Kuma, Mara imani. Baby macen da nafi tsana a duniyar nan sama Da itah. Na tsane ta, na tsane ta, tsana mafi muni, kinga Kare war Ta mah, bana son na kara hada ido hudu da ita, banason na Kara Ganin ta har abadan abada.
Hawaye ne suka Fara gangaro wa daga idanuwan Amriya, hannunta ne suka Fara Kar kar wa, kuka ne ke shirin subuce mata Saurin rufe bakin ta tayi, Tareda rintse idanuwanta jin zuciyar take kamar zata futo..
Tashi tayi daga jikin dakin, inda kuka ya ci karfinta.
Juyawa gabadayan su sukayi, inda Kabir yace waye a nan.
Saurin rufe bakin ta tayi, Tareda Saurin barin gidan.
bude kofan Kabir