Header Ads
Showing 99001 words to 102000 words out of 106900 words

Chapter 34 - ALJANAR RUWA CE COMPLT BY ASHA M.B .txt

Ads the beginning of article before Image

Aisha MB   

28 May 2024

1075

Ads at the middle of Article

maka duniya da lahira, ina matukar sonka Kabir, bazan iya rayuwa ba babu kai.


Ina zuwa yanzu zan yi maka magani, Tana kaiwa nan ta mike tsaye, sannan ta shiga cikin bishiyoyin dajin ta fara tsinko ganyayyaki, sannan ta komai gare su, murza ganyayyaki 'n tayi sannan ta hade su guri guda, sannan ta dora a wajan ciwon, cije leɓen sa yayi, yayin da yake jin wani zugi da raɗaɗin a ciwon.


Dora leɓen ta Amriya tayi kan nasa, sannan ta fara zuba masa dafi,a hankali Kabir yake jin zugin da raɗaɗin na raguwa.
Saida Amriya tatabbatar ciwon yadai na mai zafi sannan ta cire leɓen ta daga nasa.


Yayin da ta fara jin jiri na diban ta, dishi-dishi ta fara gani, Babu shiri ta fadi a wajan wajan, yayin da numfashin ta fara sama-sama.


Hankalin gaba dayan su ba Karamin tashi yayi bah, ganin Amriya cikin mummunan yana yi. Da sauri Kabir ya nufi Inda Amriya take, ganin idanuwan ta sun komai jajir, yayin da bakin ta ya fara kakkarwa.


Kallon su Aunty Amarya tayi tace, " Kabir ya kama ta mu nemo zoben nan, lokaci yana dada kurewa, share hawayen sa Kabir yayi, sannan ya girgiza kai yace shikenen, zan shiga cikin wannan ruwan sannan na dauko zoben.


"Aa Kabir wannan tekun yana da matukar hatsari sosai, zaka iya illata, kuma sannan kai baka iya ruwa bah, zaka iya samun matsala, cewar Ammi".


Kabir yace," ban da mu ba, Koda zan rasa raina, mundin indai zan samu zoben nan toh komai ya wadatar". Aunty Amarya tace, inda wani hajiyayyen ƙwai, Wanda malan Haruna ya taba bani idan ina son kowane Karfi koh wani abu ya lalace,


indai na fasa shi a gefen Wanda nake son ceta, toh zai lalace, kuma ina tunanin idan na fasa shi Amriya zata koma asalin mutum yadda take tun farko.
Amma sai sai idan an kawo wannan zoben tukun an sanya mata.


Babu shiri zuka ga Kabir yayi tsalle ya fada a ruwan. Hade hannayen su suka yi, inda suka soma yi masa adua, saida aka dau kusan thirty minutes fito bah, ganin aka yasa gaban kowanen su faduwa, inda Momsy ta zauna ta fara kuka tana mai fadin, "shikenen yanzu na rasa dana, na shiga uku ni Fatima, yanzu kenen Hydar ya zama maraya kenen".


Ba zato suka ga gangan jikin sa yayo sama, ganin aka, yasa suka nufi inda yake da sauri, sannan su khalid suka fito dashi daga cikin ruwan.


Gaban su ne ya fadi!, ganin ko motsi ba yayi, sannnan kuma gefen guda ya dun ƙule hannun shi, bude hannun Sadiq yayi, sannan taga zoben Amriya.


Da sauri Sadiq ya dauki zoben sannan ya mikawa Aunty Amarya, karba Aunty Amarya tayi sannan ta nufi inda Amriya take,


Danna masa ciki suka shiga yi, amma koh alamun motsi baiyi bah, ganin aka yasa hankalin su ya kara tashi.




Saka wa Amriya zoben Aunty Amarya tayi, sannan ta dauko ƙwan wanda yake fari sall, sa'annan ta samu daidai kan Amriya ta fasa shi, tare da shafa mata shi duk jikin ta.


Ganin bata motsa bah, yasa gaban Ammi ta fadi!, sannan tace kardai ƴata ta mutu!?,
Aa insha Allahu babu abinda zai faru, ki kwantar da hankalin ki, cewar Aunty Amarya.


Motsi suka ji daga cikin ruwa, waigawa suka yi, hatake idanuwan su ya sauka akan Mom, yayin da suka ga, an kwaƙule mata idanuwa sannan an cire mata kunne da hanci, gaba daya gawar ya zama abin tsoro, ihuu!, Zainab ta saka yayin da take kokarin guduwa, ta suɓule ta fada cikin ruwan, yayin da Aljanun ruwan suka janye ta ciki.


Rintse idanuwan su gaba daya suka yi, yayin da gawar Mom ya zama abin tsoro, share hawayen ta, Ammi tayi tace,"yanzu duk izza da mugancin da kike takama dashi yana ina?, kalli yadda gawar ki ta zama wulakantanciya, yanzu gashi nan, kin mutu a wulakance, kin mutu ba tareda kin tuba bah, kin mutu ba tare da kin gyara kura kuran ki ba. Yanzu aga wanda ya kashe da wanda aka kashe, aga wa yake da riba ran gobe ƙiyama, tabbas Wanɗa da kika kashe, suke da riba. Dama ance karshen azzalumai bata yin kyau, indai mutum ya dade yana aikata zunubi bai nemi tuba ga Allah bah, toh irin abunda ke faruwa dasu kenen, mutuwa suke a wulakan ce.


Ni na yafe miki duniya da lahira, saidai kije ki fuskan ci saka makon abunda kika aikata".


Nufan inda gawar Doct Khadija yake, suka yi , tareda cinciɓar gawar suka saka s bayan Mota,


Sannan suka cinciɓi Amriya da kuma Kabir suka suka su a mota. Tada mota suka yi, yayin da suka bar harabar dajin baki daya.


Direct Asibity suka nufi dasu, yayin da aka shiga bawa su biyun taimakon gaggawa.


Gefe guda kuma, suka koma gida, yayin da aka suturta doct Khadija, aka kaita gidan ta na gaskiya, sosai kowa yayi kuka game da mutuwar ta, su Mami da kuma doct Habeeb ma, mutuwar ta bah karamin girgiza su yayi bah, babu abinda kake ji sai koke- koke, saida sukayi mai isarsu, sannan aka dora da karatun Alqur'ani mai girma, aka shiga yi mata adu'oi.


Koma wa Hospital din suka yi, yayin da Doct Habib ya zama shine special Doct wanda aka ware zai kula da Kabir da kuma Amriya.


Saida likito ci suka dau kusan 3hours basu dawo da numfashin Kabir bah, amma an samu na Amriya ya dawo.


Fitowa doct Habib yayi, yana sharfe zufa, ganin sa yasa gaba dayan su suka nufi inda yake, sannan suka ce ya jikin nasu?, Doct Habib ya basu amsa da cewa, "mun daiyi nasaran dawo da numfashin Amriya, amma. For Kabir, am sorry to say, ya fada doguwar suma, kuma a kalla zai kai kusan watanni koh shekara kafun ya far fado".


What!, gaba daya suka fada. Baki na rawa Momsy tace kana nufin ɗana ya fada doguwar suma, girgiza mata kai Doct Habib yayi alamin eh.


Innnalilahi wa inna hilaihi rajihun, la ila a ila anta suba'a naka inni kuntun mina zalumin.
Abinda kowanen su ke nana tawa kenen.


Hakuri doct Habib ya shiga basu, sannan yace "zaki iya zuwa ku duba lafiyan Amriya". Shi kenen Ammi ta fada, daga bisani suka shiga cikin ɗakin da Amriya ke ciki.


Shiga ciki suka yi, suka tarar ta far fado, abunda ya fara fitowa daga bakin ta shine, ina Kabir?, Kwantar mata da hankali Ammi tayi, sannan tace, "Kabir dinki yana cikin koshin lafiya kinji, yanzu ba lokacin magana bane, ki kwantar ki huta kinji".


Aa ni bazan kwantar da hankali na ba, ba tare da na ga Kabir bah, yana ina?, ku kaini inda yake dan Allah.


Shikenen Amriya taso mu kaiki, mike wa tayi, hatake jiri ya dibe ta, saurin riƙe ta Aunty Amarya tayi, sannan tace,"kiyi a hankali zaki iya faduwa.


Riƙe ta Aunty Amarya tayi sannan ta kaita dakin da Kabir yake.


a daddafe Amriya ta karasa inda yake, sannan ta shafa fuskan shi tace, "gani nan na dawo gare ka, babu abinda ya same ni, kuma kaiwa ina fatan Babu abinda ya same ka".


Dafa ta Ammi tayi tace, "kiyi hakuri Amriya, bazai iya magana bah, saboda ya fada a doguwar suma, taso mu tafi kada mu ta kura masa, hawaye ne ya fara bin kan kuncin Amriya tace, " kina nufin Mijina ya fada doguwar suma, me yasa bani ce na fada bah shi ya fada. Kiyi hakuri Amriya, ki taso mu futa.


Cikin sheshekar kuka Amriya tace, " babu inda zani, zan zauna hanan har lokacin far fado warsa yayi.


Da ƙyar suka samu suka shawo kan Amriya ta bisu suka fuce daga ɗakin, koma wa ɗakin da take tayi, sannan Ammi ɗauƙi Hydar ta bawa Amriya tace, "Amriya ɗan ki yana bukatar ki, ki bashi abinci.


Karɓar sa Amriya tayi, sannan ta fara shayar dashi.




BAYAN SHEKARA
DAYA(1)






COMMENTS & SHARE PLS 🙏🙏
ALKALAMIN ✍️
(Zinariyar 🪙 Jajirtattu)




https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*??
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.??








-----------------------------------------
Likitoci ne gaba daya suka fara kai kawo a Cikin Asibity. Yayin da suka fara shiga cikin emergency room, ririke shi gaba daya suka yi, yayin da yake shure _shure, sannan yake ƙoƙarin wafce kansa daga gare su, yayin da yake ta daman kiran sunan Amriya.


Ɗaukar waya doct Habib yayi, sannan ya yi dialing number Dad, ringing biyu Dad ya dauka, tare da karawa a kunne shi yace, "hello Habib lafiya naga kiran ka?, doct Habib ya bashi amsa da fadin "Yahya Kabir ya farfaɗo daga doguwar suma".


Zumbur Dad ya mike tsaye, sannan yace "kana nufin my son is back to life, ya farfaɗo, gani nan zuwa right away, kada ku bari yaje koh ina".


Shikenen toh saika zo, yana kaiwa nan ya kashe wayan. Dad na kashe wayan ya nufi parlour da sauri, yayin da ya tarar da su Khalid da Grandma zazzau ne. Sannan yace musu, i have a good news for you guy's, Sadiq yace wow Dad menene?, Dad yace Kabir ya farfaɗo.


Mike wa gaba daya suka yi cike da farin cikin jin maganar Dad,Grandma tace gaskiya nayi farin cikin jin wannan maganar, ban taba kawo wa cewa wataran Kabir zai farfaɗo ba, tabbas yau za'a ayi gagarumar shagali wanda ba'a taba yin kamar sa bah. Maza ku taso mu tafi. Ɗaukar waya Dad yayi sannan ya sanar da Mami da kuma Ammi halin da ake ciki...




Koma wa ciki Doct Habib yayi, sannan ya kalli Kabir yace, "ka nutsu Kabir, Amriya tana nan lafiya babu abinda ya same ta".


Kallon sa kabir yayi yace," tana ina?, ina bukatar ganin ta, bazan yarda da maganar ka ba har sai na ganta da idanuwa na". Please Amriya kawai nake bukata, ita nake son gani.


Dafa Kabir doct Habib yayi yace, "Kabir baka dade da farfaɗo wa bah, kama ta ai ace yanzu ka kwanta ka samu natsuwa".


Kabir yace, "tayaya zan samu natsuwa batare da naga Amriya bah, bazan taba samun nutsuwa bah indai har ba ganin ta nayi bah".


Doct Habib yace, "okay it's fine, amma yanzu bazai yi ka ganta bah, saboda yau ne ranar auren ta da Yusuf, kuma kaga yanzu ba taka nace dan aka ka cire rai akan samun Amriya.


Zumbur Kabir ya mike, tare da fizge drip din aka saka mai, sannan ya ɗago da idanuwan sa wanda suka ciko da hawaye yace," bazai taba yiwuwa ba, Amriya ni kadai take so, nine mijin ta ba wani bah, dan aka babu wanda ya isa ya kwace min ita".


Kayi hakuri Kabir, an ruga da an ɗaura auren ta dashi. Domin kuwa yanzu sati ɗaya kenen da auren su.


Zama Kabir yayi a gefen gado, yayin da hawaye suka fara saukowa kan fuskar sa, sannan yace,"why?, meyasa zaki aura mata wani ba niba, wallahi idan ban samu Amriya bah, na tabbata inda aure har abada, domin kuwa ita ce kawai mace guda daya tilo a raina.


Kallon Doct Habib yayi yace," kwanaki nawa nayi a wannan hospital din?. Doct Habib ya bashi amsa da fadin shekara daya kenen kana nan wajan.


What! Kabir ya fada, kana nufin tsawon shekara daya kenen ina kwance a wannan gadon asibitin?, doct Habib ya bashi amsa da cewa,"kwarai kuwa Kabir shekara daya kenen, babu ranar da zata tashi ta faɗi, Amriya bata zo wannan Asibity bah".


Komai ita ke maka shi, kama daga sutura, wanka, shafa mai dadai sauran su, duk ita ke maka su.


Kallon doct Habib Kabir yayi yace,"ka bani car key dinka". No Kabir ba zai yu na baka bah, su Dad na hanyar zuwa, kuma kaga ba'a ayi bellin dinka bah, so you have to be patient please.


Bazan iya hakuri bah Uncle, kawai ka bani car key na tafi gida, kallon Kabir doct Habib yayi yace,"to bazan ba ya ba.


Mike wa Kabir yayi yace,"shikenen tunda ba zaka bani ba, zan tafi da kafa, dadin ta ma na Allah basua kare wa, zan samu wanda zai rage min hanya. Yana kaiwa nan ya nufi hanyar waje.


Dakatar da shi doct Habib yayi da fadin,"tsaya! tsaya wa Kabir yayi, yana jiran mai zai kuma fito daga bakin kawun nasa. Mika masa car key din yayi yace," gahzinan ka au mota na, ba shiri Kabir ya karbi makullin motan, yayi wa kawun nasa godiya daga bisani ya fuce daga room din.


Direct parking space ya nufa, sannan ya launi motar doct Habib, hango motar yayi daga chan nesa, da sauri ya nufi inda motar yake, sannan ya shiga ciki , tare da tada motar ya bar harabar wajan.


Fucewar Kabir keda wuya, Doct Habib ya kira Dad sannan ya sanar musu da cewa, bazai sun zo bah ga Kabir nan zuwa gidan.yana gama wayan shima ya futa, ya tari ɗan sawu, sannan ya hau ya bi bayan Kabir.


Saida Kabir yayi tafiya mai nisa sannan ya isa gidan, horn yayi , yayin da yaga securities suka fara bude kofa, mamaki ne karara ya bayyana a fuskar sa , ganin sababbin securities.


Ɗaya daga cikin securities dinne yace," Sir how may I help you?, who are you looking for?,


Bin shi Kabir yayi da kallon baka da hankali. Sannan yace, raina wa kanka hankali bani ba, kamar ya Meya kawo ni, nida gidan mu kake tambaya ta meya kawoni.


A fusa ce!, security din yace, "kaga malam maza futa daga gidan nan koh nayi maka duka tsiya".


Kallon kansa Kabir yayi yace, like seriously ni yau security yake fadawa magana son ransa, gaskiya nee dama ka samu. Toh bara kaji, nine Kabir kuma first born din gidan nan, kuma nine mai Company fishes production.


Security din yace," toh waya damu da sanin koh kai waye, waya damu da sanin sunan ka, maza zo ka fuce.


Daga kan upstairs Grandma ta hango keyar Kabir, ihuuu!, ta saka, oyoyo jikana ya dawo, kallon upstairs din Kabir yayi ya hango Grandma.


Fufu towa gaba daya suka yi, yayin da matan kowannen su hannun su rike da yaro. su Khalid ne suka nufi inda yake tare da rungume sa, shima Kabir rungume su yayi cike da kewa, da qaunan juna.
Farin ciki ne gaba ɗaya ya lullube fuskokin su, karasawa inda yake su Nadira da Grandma suka yi, inda suka je cikin farin su Nadira suka tarbe shi.


Kalle_kalle ya shiga yi ganin bai hango Amriya bah, sannan kuma ya hango su Mansy da Zuby , mamaki Kabir yayi ganin meya kawo waɗanan karuwan gidan su.


Maida kallon sa Kabir yayi kan security ɗin wanda yayi zuru_zuru da idanuwa, sannan yace, wannan security din ku sallame shi daga yau karya kara zuwa gidan nan.


Murmushi Khalid yayi, sa'annan yace, har yanzu dai baka bar wannan halin naka bah. Kabir yace ni ba surutu nace kayi bah, kawai do as I said. Shi kenen mai gida za'a yi yadda ka fada cewar Khalid.


Shiga ciki suka yi yayin da suka fara hirar yaushe rabo. Kallon shi Momsy tayi tace, a gaskiya Kabir nayi munyi kewar ka sosai, da bakanan gaba daya gidan ya zama a takure babu dadi kwata _kwata, gaskiya nayi farin ciki da dawowar ka..


Ina Amriya?, maganar da suka ji ya fito daga bakin sa kenen. Kallon sa suka yi sannan suka ce, Amriya na nan kalau.


Kabir yace tana ina, ance min tayi aure, meyasa za kuyi mata aure, bayan kunsan nine mijin ta,


Cikin rashin fahimtar maganar sa gaba-daya suka kalli juna. sannan Aunty Amarya tace," waye ya fada maka akan?. Kabeer ya bata amsa da cewa Uncle Habib ne.


Doct Habib dake bayan Kabir ya Kista musu ido ɗaya, ganin aka yasa su fahimtar abin da yake nufi.


Gyaran murya Dad yayi yace,"Yes of course, anyi musu aure, kuma yanzu suna rayuwar su cikin farin ciki da qaunan juna. Kana so a tabbatar maka da akan ne.


Kwalla wa Amriya da Yusuf kira Dad yayi. Babu bata lokaci su biyun suka fara ta kowa daga kan upstairs din, yayin da Yusuf ke rike da Hydar a hannun sa, gefe days kuma Amriya ce, taci less wanda yaci design ajiki, gaba daya tayi wani ƙiba tayi fresh.


Wani mugun kishi ne ya turnuke Kabir, cikin bacci rai ya nufi inda Yusuf yake, tare da karbar Hydar a hannun sa sannan yace," waya baka izinin taba yaro na, kada ka kara dora wannan karamin hannun naka akan ɗana.


Mai da kallon sa yayi kan Amriya yace," Amriya da gaske ne kinyi wani Auren. Cikin radhin fshimta ta kalli su Dad, girgiza mata kai suka yi data ce eh.


Murmushi Amriya tayi tace kwarai kuma, baka ga alama ba. Aure muka yi, tunda yanzu ka dawo saika saka mana albarka.


Dad yace toh yanzu dai kaji, Amriya yanzu bah mallakin ka bace. Dan aka ka cire rai akan ta, Grandma tace yauwa kawa ta lubabatu tanada wata yarinya Saratu a kauye, naga zaku dace sosai, kuma gata bazawara, kaga dama ance zaurawa sunfi iya kula da miji, koh ya ka gani?.


Bazai yuba, Wallahi bazan yarda bah, saikun kaini wajan limamin da ya daura auren nan, wallahi wannan bah adalci bane.
Indai har da gaske anyi auren nan, toh wallahi saidai na dauwama a gauro, dan babu abinda zanyi da yar ƙauye kazamai.


Kallon Amriya yayi yace, "Amriya dan Allah kiji tausayi na, ki fada min gaskiya".
Kallon_kallo suka shiga yi a tsakanin su, hatare suka kwashe da dariya, sannan suka hada baki wajan fadin April fool.


Kallon su Kabir yayi ya girgiza kai, sannan yace dama wasa kuke da hankali na koh.
Janyo Salma Yusuf yayi yace,"toh nidai kaga matata uwar dakina, yanzu aka ma juna biyu gare ta. Hatake kunya ta kama Kabir, yaji kamar ya nutse kasa saboda kunya.


Murmushi Amriya tayi, sannan ta nufi inda yake tare da rungume shi hawaye ya fara bin kan kunci ta. ganin aka yasa su Dad dasu Grandma suka bar musu parlour, yayin da shima Doct Habib yayi tafiyar sa...


da sauri Kabir ya share mata hawayen ta sannan yace, "kuull kar na sake ganin kin zubda hawaye kinji. Girgiza masa kai Amriya tayi tace, nayi matukar kewar ka sosai Kabir, jin sunan nasa yayi wani iri a bakin ta, kallon ta yayi yace, menene wani Kabir, kice min Kalb kamar yadda kika saba a da.


Murmushi gaba daya suka yi, kallon su Adeef Kabir

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads