Header Ads
Showing 84001 words to 87000 words out of 106900 words

Chapter 29 - ALJANAR RUWA CE COMPLT BY ASHA M.B .txt

Ads the beginning of article before Image

Aisha MB   

28 May 2024

1076

Ads at the middle of Article

kowa, Kuma dole ya kawo babban abokin sa wanda yake matukar kauna, sannan yayi sadaukar wa da jinin sa.


Mahaifina baiyi jayayya da akan bah, ya yarda da umarnin da aka bashi. Bayan wasu kwanaki. Mahaifina yayi kudi, dukiya suka habbaka, yazama sananne wanda babu kamarshi, haryazo yafi mahafinku kudi.


Hana aka, babana ya nemi suyi sulhu da mahaifin ku, shikuwa mahaifin ku, ya hakura suka koma normal yadda suke a da.


Sosai suka kara kaunatar junan su, inda mahaifina ya yanke cewar zai fada wa mahafin ku komai da komai, abunda yasa arzikin shi yayi yawa...


Hana tsaka da aka, baba na, ya nemi su fita da Mahafin ku, babu jayayya Mahaifin ku ya amince da akan, inda baba na ya kaishi Chan cikin jeji, sannan ya Kalli abokin nasa ya ceda shi,


Tabbas Kai abokine na kwarai, Amman inason na fada maka wani sirri na, Kuma Dan Allah inason ka adanamin, karka Bari duniya ta sani, mahafinku ya ceda baba na,


Menene sirrin? Meyasa ka kawo ni daji? Me kake shirin aikata wa?


Hatake baba na ya kira sauran yan qungiyan, lokacin da mahafin ku ya gansu, yayi matukar tsorata sosai,


A lokacin babana ya sanar dashi komai da komai, inda mahaifin ku yak'i amince a sadaukar da jinin sa inda a karshe yace saiya tona masa asiri, duniya tasan cewar shidin maciyi amana ne,




Shi Kuma a lokacin mahaifina ya Shiga bashi hakuri, Kuma yayi masa alkawarin cewar zai bashi kudade Duk abunda ya keso, amma Dan Allah kada ya tona asirin shi a idanun duniya, Hatake mahaifin ku ya kira police officers, suka zo suka tafi da baba na,


Shi Kuma mahaifin ku ya kwashi kudaden baba na, ya kaiwa su police, inda police din suka raba kudin a tsanin su.


Yayin da Baba na ya tafi magarkama na wajan shekaru goma, bayan ya futo, yaga komai nasa ya yi kasa, kudaden da ya Tara da duniyan da yake dasu duk babu, akan ya sashi cikin damuwa har yasamu ciwon zuciya,


yana cikin kakarin mutuwa ya kirani, ya sanar dani duk abunda ya faru, hawaye ne suka Fara bin kan kuncin Mom, sannan ta cigaba da fadin,


Baba na yace na daukan masa alkawarin cewar zan daukar masa fansa, bazan taba rabuwa da ku bah, ni kuwa na daukan masa alkawarin cewar saina ga bayan ku baki daya, bazan bar koda kud'a wanda nasan ya futo daga gidan nan bah, saina raba ku da farin ciki, saina sanya ku cikin kunci da bakin ciki,


Ina kaiwanan, Baba na ya tashi da zummar yaje zai kaini na Shiga qungiyar asiri, rike hannu na yayi yayin da muka futa wajen layin,


Ban hankara bah, naji han fara je fawa baba na Duwatsuna, da Kuma rodi, kuka a lokacin nai tayi, yayin da na dunga rokan su, subar min mahaifina, sannan ta Kalli Amina da Kuma mahaifiya ta, wacce ke a tsaye basu tanka wa mutanen bah,


A lokacin raina yayi matukar baci, ganin mahaifiya ta da yar uwata, basu tanka wa mutanen bah, a lokacin naji tsanan kowannen su a raina,


Aka suka cigaba da jifan Baba na har saida numfashi ya futa daga jikin shi, sannan suka barshi a wajan, sukayi tafiyar su.


Babu wanda ya taimaka min, ni da kaina na dauki gawar mahaifina sannan ta kaishi makabartar yayin da yan qungiyan asiri suka taimaka min, muka bunne sa,


Tunda ga lokacin na Shiga cikin yan qungiyan asiri, yayin da jini na ke tafarfasa, fansa kawai take son dauka, hana aka na Fara bibiyar mahafin ku, ban daina bibiyar sa bah, har saida naga na kawar da rayuwar sa, bayan nan kuma, naje gidan mu sannan na lashe mahaifya ta,


Itama Amina zan kashe ta, amma abunda yasa ban kashe ta bah tana gidan mijin ta a lokacin, yasa na barta da ranta amma duda akan bai hanani bibiyar rayuwar ta bah.


daga nan kuma na shigo cikin ahalin nan a matsayin mata, na saka Y'aya na Suleiman ya bani kai a matsayin mata, Kuma na shigo gidan nan domin daukar fansa .


Kuma bazan dakata bah, har sai na cikawa mahaifina burin shi na karshe kafun na sarara Wannan shine .


Ajiyan zuciya gabadayan su sukayi, inda Mami ta fara magana kamar aka, toh mahaifin ki ya mutu, amma ai bah mahafin mu ne ya kashe shi bah,


Kwarai kuwa mahafin ku ne ya kashe baba na, da mahafin ku bai fada wa duniya wanene baba na bah, da haryanzu nasan yana raye, Kuma na ruga dana daukan wa Baba na alkawarin cewar, Har jikokin Yunusa yusuf, bazan bari bah, Domin har su zan hada na kashe. Kuma shine zai sa a kara mun matsayi acikin kungiya.


Doct khadija tace, amma meyasa ni kika kashe min dana, Kuma kika kashe yarinyar Amina. Kuma kinsan da cewar Amina batasan cewar ke yar uwarta bane Domin rabonda ku hadu yakai,


kusan shekaru talatin da yan Kai, amma ke kingane ita din yar uwarki ce, yayinda ita bata sani bah,


Mom ta bawa Doct khadija amsa da fadin, ni ban kashe danki bah domin kuwa danki yana raye bai mutu bah, zaro ido Doct khadija yayin da jikin ta yafara karkarwa tace yana ina Dan Allah ki kiramun dana, inason na ganshi.


Mom tace zan fada miki Amman kafun nan, ki kiramun yar uwata Amina da Kuma danta da mijin ta yanzun nan,


Cikin rawar jiki, Doct khadija ta dauki wayar ta, Tareda dialling number Ammi wato Amina, ringing biyu Ammi ta dauka Tareda karawa a kunnen ta tace, hello Salamu alaiki, Amsa sallamar Doct khadija tayi tace,


Yar uwa, Dan Allah keda mijin ki da Kuma danki Duk kuzo yanzun nan, Ammi tace, amma dai lafiya koh, Doct khadija tace lafiya ce ta kawo akan karki damu babu komai kuzo kawai,


Tom shikenen gamu nan zuwa gidan su Kabir din, katse wayan Ammi tayi, yayin da ta Sanar da Abban yusuf komai da komai, sannan ta samu yusuf wanda yasamu sauk'in jikin shi sosai, tace masa ya shirya zasu je gidan su Kabir, bah jayayya, yusuf yace Tom shikenen,


Cikin kankanin lokaci suka isa gidan su Kabir, yayin da Amar ya kaisu dak'in da gabadayansu suke, Shiga ciki sukayi sallama rike a bakin su.


Amsawa su Grandma sukayi, guri su Ammi suka samu sannan suka zauna, Abban yusuf yace lafiya dai koh naga kowa ya taru hanan, Aunty amarya tace lafiya lau wallahi, Dama wani Dan karamin issue ne ake tattauna wa akai.


Kallon Ammi Aunty Amarya tayi tace shin Maman Yusuf kinsan wannan matar ta fada Tareda nuna Mom, Kallon Mom Ammi tayi tace, Aa ban Santa bah, amma nasan cewar itace Maman Kabir, Kuma tana min Kama da yar uwata hassana.


Doct khadija tace idan na fada miki wani abu zaki yarda?, Ammi tace me zai Hana, zan yarda mana,


Doct khadija tace, toh dai wannan da kike gani itadin yar uwarki ce wato hassanan ki, wacce kanku ya rabu akan Abban yusuf,


Da sauri Ammi ta Mike, Tareda Kallon Mom tace, da gaske kece hassana ta? Mom ta bata amsa da fadin kwarai kuwa nice nan, nina hanaki sukuni a gidan auren ki, na saka kika rasa yarki wacce kike mugun qauna wato Sabreena,


Kallon ta Ammi tayi a hassale tace, dama kece, ina kika kaimin y'ata, bayan kinsan cewar ita kadai na haifa, wato dana kaita asibity lokacin da Asman ta ya tashi ke kika kashe ta koh, Meyasa zaki aikata min aka bayan kisan ita kadai gareni.


da kallon mamaki Yusuf ya Kalli Ammi, sannan yace, Ammi ni din fah, ni bah danki bane.


Kallon shi Ammi tayi tace kwarai kuwa kai bah dana bane, Kai adopted child ne, zama Ammi tayi hawaye na bin kan kuncin ta, tace kayi hakuri nayi boye maka gaskiya na tsawon shekaru, tabbas Kai bah dan mu bane, sabreen itace kadai yar dana haifa.


Hatake kan Yusuf yayi mugun saramai, dafa kanshi yayi, yafara karanta adu'oin rage radadi, dago kai yayi sannan ya tambayi Ammi yace, toh Wacece mahafiya ta,


Kafun Ammi tayi Magana, Mom tace khadija itace mahaifiyar ka, zaro ido gabadayansu sukayi, cikeda mamakin kalaman Mom, Ammi ta kalle ta tace, khadija Kuma! taya kika san khadija ce mamar sa,


Mom tace saboda ni da kaina na dauki Yusuf sannan na hajiye shi a kofan gidan ku, a lokacin Kuma na buya, bayan kun dawo daga asibityn da kuka je akan rashin haihuwa da kike, kuka ganshi sannan kika yanke cewar ku dauke shi.


Kallon Doct khadija Yusuf yayi yace, kenen Doct khadija itace mahaifiya ta, akan bazai taba yuhuwa bah, da sauri doct khadija ta Mike, sannan ta isa inda yusuf ke tsaye, ta Kalli bayan wuyan sa ta tabo dake wuyan sakk irin na wancan,


Sannan tace, tabbas kaine dana, kaine dana, Dama, zan sake Ada ido dakai a duniya, rungume ta yusuf yayi, yace kiyi hakuri umma tun kwanakin nan bansan cewar ke din mahaifya ta bace, sai yau, na miki alkawarin zan rike ki hannu bibbiyu, bazan taba rabuwa dake bah.


Sosai Ammi tayi murnan ganin asalin mahaifiyar Yusuf, Abba wato mijin Ammi ne ya katse su da fadin, toh ita y'ata Sabreen Tana ina? Ina kika kaita,


Dariya Mom ta kwashe dashi Tareda fadin kuna Tareda yarku, amma Baku san itace yarku bah, Dad yace bah abunda aka tambaye ki kenen bah, tambaya itace, ina yarsu take Kuma wacece yar su ,


Mom tace bah kowa bace yar su, illa "Amriya, tabbas Amriya itace yar ki.


????????
COMMENT & SHARE
PLS ???




ALKALAMIN ??
AISHA M.B (Baby isha )
???








Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JYYV16dbYaX1dykLX7EE91






?BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM ?
ALJANAR RUWA CE ??♀???♀?? PAGE 5??0????5??1??
WRITTEN & DIRECTED ?? BY AISHA M.B??
-----------------------------------------
Zaro idanuwa gabadyansu sukayi, suka hada baki wajan fadin What!, jiri ne ya fara daukan Ammi, da sauri tayi saurin dafe kanta, Tana mai fadin Amriya, itace sabreen dita, kenen itace y'ata, why? Meyasa tsawon wannan lokacin ban gano cewar ke y'ata bace, ta karashe maganar tareda fashe wa da kuka .


Mamaki ne ya Kama kowannen su na dak'in, Nadira ce tayi karfin halin fadin, idan Amriya yarki ce, that means itadin mutum ce, toh tayaya ta zama ALJANAR RUWA How?


Dariya Mom ta kwashe dashi, tareda fadin nice nan, na maida ta ALJANAR RUWA, Kuma ni kadai ce nasan a inda zata samu maganin waraka ta, ta koma asalin mutum,


Amma bazan fada bah domin nice nan zan ga bayan tah.


A fusace Ammi ta Mike tareda nufan inda Mom take tareda shake ta tace, kin rabani da y'ata na tsawon shekaru, akan bai ishe ki bah, meyasa kike son daukar rayuwar ta?


Kin ruga kin maida ta ALJANAR RUWA, akan bai wada ce ki bah, menene ta tare miki da kike son ganin bayan tah.


A fusa ce, Mom ta Kalli Ammi tace, tambaya ta kike me ta taremun, toh bude kunnuwan ki kiji, yarinyar ki ta tare min abubuwa da dama, idan bakusani bah toh yau kusani,


Ita ta hanani kashe ku tun wuri, ita take Kare Kabir a koda yaushe, lokacin birthday Nadira, ni na saka wa kabir guba, sannan ita Kuma Amriya ta dauka tasha, akan ya bata min rai sosai, banso akan bah, naso ace Kabir ne yasha sannan ya mutu,


Amma ganin akan danayi yasa na kira police domin su dora masa laifi akansa, amma still yet saida ta cece shi a wajan Police, ta hana aka ki tafiya dashi.


Babu abunda banyi bah, dan ganin na kawar da Kabir d'aga doron duniya, Amma wannan yarinyar Amriya ta Hana ni, ita take dakatar dani, nayi yinkurin kashe ku amma a koda yaushe ta kasance tana taimaka muku,


kowane shiri na toh saita san yadda tayi ta wargaza min plan's dina, now tell me, bata tare mun abubuwa bah?.


Hawaye ne ya fara bin kuncin kowannen su na dak'in, Mami ce tayi karfin halin fadin, Allah sarki Amriya, yau gashi dai gaskiya tayi halin ta, hakika kedin mace ce ta gari, duk Wanda yayi nasaran samu Mace irin ki toh hakika wannan mutum, zai kasance a koda yaushe Mai sa'a.


dafa kanshi Kabir yayi, yayin da yake jin zuciyar shi na masa zafi da kuna, tareda fadin, ki gafarce ni Amiriya, tabbas nayi dana sani, a koda yaushe kina yawan fadamin cewar, watarana saina yi dana sani, kuma saina san mahimman cin kasantuwar ki a rayuwa ta.


Tabbas maganar ki ya zama gaskiya, dan Allah ki taimaka ki yafe min yana kaiwa nan, ya mike tsaye, tareda fuskan tarsu yace, zanje na nemo matata, zan nemi gafarar ta, Kuma sannan na nemi ta dawo cikin rayuwa ta bah, domin kuwa in har Amriya bata kasance a rayuwa ta bah, toh zama na a duniyar nan ya Kare.


Tashi Ammi tayi tace, kwata kuwa Kabir nasan bazata wuce gida na bah, amma bazan bar gidan nan bah, har sai Karima ta fadamin tayaya ta maida y'ata ALJANAR RUWA, Kuma menene dalilin ta na yin akan.




Wannan shine sila, Mom ta fada tana mai nuna abban yusuf, Kallon ta Abban yusuf yayi mamaki bayyane a fuskan shi yace ni Kuma! , ta yaya nazama nine sila?


Mom tace kwarai kuwa kaine sila, Amina baki taba fada masa irin tsakanin sonda nake mishi bah, sai a lokacin Ammi ta tuna da irin tsakanin sonda Karima ta nuna wa habib shekarun baya da suka wuce,


Kallon ta Ammi tayi tace, Amma ke baki ji kunya bah, mijin yar uwarki kike so, duk mazan duniyar nan baki gansu bah, sai mijin yar uwar ki, Anya ke jini na ce kuwa, hanya tare aka haife mu, ki rasa da abunda zaki sakamin sai da wannan abun.


Toh fada mana tayaya kika mayar da Amriya ALJANAR RUWA?......


shekaru baya da suka gaba ta.
ganin auren ki da Habib, akan yasa ni cikin bakin ciki, ya sanya ni kunci wanda akan ya kusan sanadiyar rasa rayuwa ta,


Ganin bazan iya jure ganin ki, kina farin ciki, ni kuma, ina bakin ciki, akan yasa na na dau alwashin cewa saina ga bayan ki, a lokacin na tafi wajan shugaba mu na Qungiyar devilish. nace dashi inason na kawar dake daga duniya,


Inason ya zamto cewar ni kadai ce zan kasan ce a rayuwar Habib, Kuma nace da shugaban mu, banason ki haihu a gidan auren ki, inason ki kasance a koda yaushe kina kunci.


Shugaba yace min, wannan abu mai sauk'i ne, amma kada nayi gaggawa, na bari lokaci zaizo da zanyi akan, yanzu koh yayi bazai shafe ki bah, domin kuwa a koda yaushe Amina tana yawaita adua tsari daga mutum koh aljan, bazai yu na kusan shi inda take da mugun nufi baht, bazamu iya tura mata aljanu bah domin kuwa akwai kariya a jikin tah.


Amma zamu iya Hana ta haihuwa, saina ce mashi shikenen, mu Hana ta haihuwa, aka kuwa akayi, Amina bata taba batan wata, bare Asa ran tana da ciki bah.


Lokacin ne Kuma na dauke dan khadija, sannan na ajiye shi a gaban gidan su, saboda kada su je suce a musu Adu'oin samun haihuwa,


A gaban idona a lokacin naga kun dauke shi, sannan kuka dunga rainan shi kamar danda kuka haifa.


Bayan wasu shekaru kawai naji labarin cewar kina dauke da juna biyu, hankali na bah karamin tashi yayi bah, babu bata lokaci na wuce cikin qungiya, sannan na sanar da shugaban mu halin da ake ciki.


Shi kuwa ya tabbatar min da cewa, baza ki taba haifo wannan yarinya ta cikin ki bah, yana kaiwa nan ya dauki madubin tsari, da muke amfani dashi wajan kashe mutane da mukeson kashe wa,


A lokacin madubin tsafin, ya hasko Amina a ciki tana kwance akan bed, shugaba na ganin akan ya nemi da daya daga cikin yan qungiyan ya kashe yarinyar dake cikin Amina,


Aka kuwa akayi, daya daga cikin mutanen ya dauki sanda na tsafi, sannan ya saita daidai cikin Amina, ya fara magganganu, cikeda mamakin mu kuwa, muka ga ya kwalla uban ihuu, yayin da ancin shi da bakin shi ya fara zubda jini, sannan ya fadi a kasa yafara shure shure, yana kakarin mutuwa, daga bisani Kuma ya mutu a wajan.


Hankalin kowa na kungiya bah karamin tashi yayi bah, Hatake shugaban mu, ya Kalli cikin dake jikin Amina, sannan ya ce dani, tabbas kawar da wannan cikin na jikin ta abune Mai wahala, indai har munason mu kasance a raye toh tabbas sai mun bar cikin nan,


dole mu barta ta haifo yarinya, domin kuwa alamu ya nuna cewar yarinyar yar baiwa ce. Kuma jinin yarinyar nan zaisa karfin mu, da ikon mu ya karu, ya ninka na da, sai yace dani mu hakura ta haifo yarinyar.


Jin akan yasa raina yakai kololuwar bacci, sannan nace Allah ya kawo ta duniya, in har da raina toh bazan taba barin yarinyar nan bah.




Bayan wasu watanni, Allah ya sauk'i Amina, ta haifo santaleliyar yarta kyakyawa, son kowa, kin wanda ya rasa. A lokacin danaji labarin ta haifi yarinyar, yasa na fara shirye shiryen Yanda zan dauke yarinyar daga gare ta,


Aka kuwa akayi, domin kuwa na hallaci Sunan Amriya, yayinda naga duk fuskokin ku lullube yake da farin ciki da annashuwa.


Akan bah Karamin Kara tunzura ni yayi
bah, a lokacin nayi kokarin dauke Amriya, amma Allah zai nufa bah, akan yasa naji bah dadi, amma ta bangare guda naji dadi, saboda nayi nasaran bata wani kwayoyin cuta tasha,


Bayan watanni, kuwa ta Fara cuta, Tana rashin lafiya wanda ya tsanan ta, har kuka kaita asibity, ni kuma naje asibityn, sannan na dauke yarinyar, na mu sanya Amriya da wata yarinyar, na sanya mata kamanni Amriya sakk, sannan nayi fuce wa ta daga asibityn.


Bayan fuce wa ta, nurses suka gano cewar yarinyar da na musanya ta mutu, sannan suka zo suka fada muku cewar yarku ta mutu, hankalin ku bah karamin tashi yayi bah, yayin da aka Baku gawar ta, kuka suturta ta, sannan kuka kaita gidan ta na gaskiya.


Ban nufi koh ina da Sabreen wato Amriya
Bah, sai

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads