Header Ads
Showing 102001 words to 105000 words out of 106900 words

Chapter 35 - ALJANAR RUWA CE COMPLT BY ASHA M.B .txt

Ads the beginning of article before Image

Aisha MB   

28 May 2024

1069

Ads at the middle of Article

yayi yace, me kuma kuke yi a gida?, baku koma makaranta bah?,


Dariya Adeef da Ammar suka yi sannan suka ce, tsohon zance kenan, tun yaushe muka gama har mun samu ma aiki.


What!, kuna nufin kun gama makaranta?, da yardar Ubangiji ma kuwa cewar Abdul.


Gaskiya nee, toh su waɗanan fah, Kabir ya fada yana kallon su Mansy, oh wai su maryam kake nufi, ai matayen mu kenen.


What!, wait a minute, kuna nufin ku ukun nan aure kukayi kuma a cikin shekara daya,
Sosa keya Abdul yayi tace kwarai kuwa Aure muka yi, muma yanzu mun shiga saga ciki, sai ma kaga ranar auren mu, shagali iya shagali, anyi rawa na futa fitina, saima kaga photunan da mu kayi na buga wa a jarida. gaskiya babban Yahya kayi missing abubuwa da dama wallahi.


Kabir yace toh taya kuka hadu dasu, Maryam din, danni dai nasan yan duniya ne, ana yahya ya kake cewa mata yanmu yan duniya , mun hadu dasu ne fah a nan Nigeria, kuma gashi sun chanza halayen su , sun koma ga Allah, dan Allah adens tono abinda ya ruga ya wuce.


Shikenen Kabir ya fada, Adeef yace nidai Maryam itace matata, Ammar yace ni kuma zulaihat ce matata, Abdul ya janyo Kalisat yace toh Ni ma ga my wife nan. Murmushi Kabir yayi yace,"masha Allah, Allah ya kara hada kan zukatan mu, gaba-daya suka amsa da Ameen.


Nadira ce tace Yahya kaga ƴarmu, karbar yarinyar Kabir yayi yace, "Masha Allah, ya sunan ta? , Nadira ta bashi Amsa da fadin sunan ta Safiya, wow nice name, gashi kuwa tayi kama da ke sosai har dogon bakin Baban ta. Turo baki Sadiq yayi yace,"kaji dashi".


Miko Ɗan ta ita ma Fatima tayi tace,"ga shima ɗan gogon namu, ta fada tana kallon Khalid, harara Khalid ya galla mata, sannan yace zaki yi bayani ne idan muka shiga ɗaki.


Dariya Kabir yayi tare da karbar yaron, sannan ya kalli Khalid yace, toh meza kayi wa kanwar yawa idan kunne ɗakin, kardai kana dukan mun kanwa.


Khalid yace, " ita tasan abinda nake nufi". Maida kallon sa Kabir yayi yace, ta shi ma mene ne sunan sa?, Fatima ta bashi amsa da cewa sunan sa Zubairu amma hana ce masa Zubair.


dariya Kabir kwashe da shi. tare da fadin wanene ya saka masa wannan sunan dan Allah, Fatima tace ba shine bah, nace a saka masa Abdullahi, sai yace min wai tun kafun yayi aure yace indai dansa na fari namiji ne wai Zubairu zai saka masa.


Khalid yace,"toh nayi laifi ne, sunan kaka na wato mahaifin Baba na, shiyasa nace duk ɗanda na haifa indai na miji ne, saina saka masa zubairu.


Gaskiya ne,gashi kuwa kuna kama harda katon kai naka. Khalid yace oho dai duk katon kaina bankai ka ba, naga ma kafi ni.


Mika wa Fatima Zubair Kabir yayi, sannan ya mike tsaye yace, Ni zan je na dawo, inaso naje baki ɗimin mahafiyata.
A'a ka bari mu fara cin abinci tukun nan saika je cewar Nadira, aka kuwa aka yi saida suka ci abinci, sannan suka yi sallah tare da yiwa Allah godiya daya kara nuna musu rana mai cike da farin ciki .


Bayan sun idar, Kabir ya nufi part din Momsy shiga ɗakin Momsy yayi, ya tarar da ita akan kujera a zaune, zama kusa da ita yayi, tare da dora kansa akan kafadar ta yace," Momsy na, nayi kewar ki sosai, hade rai Momsy tayi tace, "ni banga alama bah","yanzu Amriya ta dawo gare ka ka manta dani koh, ta fada tana murmushi",


Murmushi Kabir yayi yace,"kunsan menene Momsy, a duk sanda na ganki bana jin cewa ina tuna wa da ita, amma idan na ganta ke ce ke fadowa a raina".


Murmushi Momsy tayi, tare da shafa kansa tace,"Allah yayi wa rayuwar ka Albarka ɗana. Maza kaje yanzu matar ka na bukatar ka, tsawon shekara daya leɓen, baka tare da ita, yanzu ya kamata ka fara nuna mata soyayya, kaji koh.


Insha Allahu Momsy zan je, amma kuma kibari na zauna, sabo da kema nayi kewar ki sosai, hira sosai suka sha, abun gwanin burge wa, yayin da suna yi suna dariya.


Ganin garin ya fara duhu yasa Kabir faɗin bara naje, nasan Hydar na chan domin kuwa shima yayi missing daddy sa. Mike wa yayi sannan yayi wa Momsy saida safe, daga bisani ya fuce daga ɗakin,


zuwa yayi ya tarar gaba daya kowa ya koma part dinsa.Murmushi ya saki, daga bisani ya shiga cikin dakin su.


Tarar da Amriya yayi da kan standing mirror a zaune, ta saka kayan barci, yayin da ta daure gashin ta wanda ya' yalalo ga tsantsi ga laushi.


Zuwa yayi kusa da ita, sannan ya rungume ta, ta baya, tare da karbar Ribon din hannun ta sannan ya daure mata gashin ta dashi.


Ɗaukar ta yayi chakk, sannan ya dire ta akan gado. Kallon sa Amriya tayi tace,"kyakyawan Mijina ya dawo gareni .
Murmushi Kabir yayi yace,"my beloved wife Sabeen kenen.


Ya mutse fuska Amriya tayi tace,menene Sabeen, ka kira ni Amriya ba Sabeen bah, ni banaso. toh shikenen gimbiya duk yadda kika ce aka za'a yi. Yanzu dai na dawo, ɗaga mata gira ɗaya yayi yace," yau dai za'a bani hakki na koh?.


Shiiii, tayi mai alama da hannun ta da yayi shiru. Kallon sa tayi tace,"aba Kalb, kana gani fa Hydar baiyi bacci bah kuma nasan yaji abinda kace".


Dariya Kabir yayi yace," my wife kenen, toh shi din babba ne da za'a ce ya fahimci abinda nace, shagwabe fuska Amriya tayi tace," Toh nidai nace A'a koh".


Kallon ta Kabir yayi, yaga ta masa kyau sosai, janyo ta jikin sa yayi ta fada kan cinyar sa, yayin da kamshin turaren ta ya bugi hancin sa, lumshe idanuwa yayi, yayin da yake ji kamar kada ya sake ta.


Kallon ta yayi yace," wai me su Ammi ke baki ne aka naga kinyi wani kiɓa kinyi kyau, ga wani fari da fresh da kika kara?,
Murmushi Amriya tayi sannan ta kawar da kanta gefe tace," sirri ne".


Murmushi yayi shikenen tunda ba zaki fada min bah, amma kinsan mene ne?, shafa sumar kansa Amriya tayi tace A'a saika fada, Kabir yace wallahi ina matukar sonki sosai, i want to stay with you for the rest of my life.


Murmushi Amriya tayi tace," nima ina sonka sosai, ta fada tare da rungume shi.
Rungume ta shima yayi, sannan ya sumbaci goshin ta.


Ɗago kai Amriya tayi tace,"kasan me na tuna, A'a Kabir ya fada.
Amriya tace," na tuna lokacin da kake yawan musguna mun, kana ce min mai sufar Aljanu.


Ka tuna idan ka shigo ɗaki idan ina ciki sai kace, ke maza zoki futa dan bazan iya hada gado dake bah.
Dariya Kabir yayi, sannan yace," Lokacin yarinta ke damuna, ban san gaskiya bane ai, a lokacin rayuwa nake cikin duhu.


Yauwa na tambaye ki mana?, Shin har yanzu ke Aljanar ruwa ce, koh kuwa kin zama mutun kamar kowa.


@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@
COMMENTS & SHARE PLS
ALKALAMIN
A'ISHA M.B
(Zinariyar Jajirtattu)




https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*??
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.??


BISSMILLAHI RAHMAN I RAHIM
ALJANAR RUWA CE
PAGE 57 TO 58
WRITTEN & DIRECTED BY
A'ISHA M.B
(Zinariyar Jajirtattu)
--------------------------------------.
Kallon shi Amriya tayi tace, "eh mana ni yanzu mutum ce kamar kowa, dan aka kar ka sake cikin Aljanar ruwa".


Murmushi Kabir yayi sannan yace," tayaya zan yarda da akan eh". Ya fada tare da ɗaga mata hira ɗaya.


Pillow dake kusa da ita Amriya ta dauka, tare da nufan sa dashi, ganin akan yasa Kabir saurin mike wa tareda ficewa daga ɗakin.


Bin bayan sa Amriya tayi, yayin da suka fara zagaye palour, daga karshe tayi nasaran jefa masa pillow din a gadon bayan sa.


Faɗuwa Kabir yayi kan three seater dake parlour ɗin, yayin da Amriya ta hau kansa, tare da ɗaukar pillow ta fara buga masa tana dariya.


Waiyyoo baya na princess kiyi hakuri mana, zaki ɓallamin gadon baya, nayi alkawari bazan sake bah


Dariya Amriya ta kwashe dashi!, tana mai faɗin," zaka kuma kirana Aljanar ruwa eh?, nace zaka kuma kirana Aljanar ruwa".


Amsa Kabir ya bata da faɗin, "wane ni da zan kara kiran ki da Aljanar ruwa, da gaske nake ba zan kuma bah.


Tashi Amriya tayi daga kan sa, yayin da ta mike tsaye ta saki murmushi. Tashi shima Kabir yayi zaune, sannan yabi Amriya da kallo ya dafa gadon bayan sa yace,"washh! baya na, gashinan zaki ɓallani tun ba'a kai koh ina bah, idan kika ɓallani yanzu taya zamu kara samun wani ɗan".


Taɓe fuska Amriya tayi cikin zolaya tace," kai yanzu sai kace bah namiji bah". Murmushi Kabir yayi, sannan yasa hannu ya chafko ta, ba shiri ta fada jikin sa, yayin da numfashin kowanne su yana gogan na juna, kallon_kallo suka shiga yi a tsakanin su, murmushi Kabir yayi, sannan ya hura mata iskar bakin shi a fuskar ta.


Lumshe idanuwan ta Amriya tayi, yayin da ta fara shiga wani irin yanayi na daban. Ba zato taji leben sa akan nata, sannan ya fara tsotsar leɓen ta cikin wani salo na daban.


Da sauri Amriya ta cire bakin ta daga nasa, ganin yana shirin fita gayyaci sh, sannan ta mike tsaye take ƙoƙarin barin parlour, ganin akan da Kabir yayi, yasa shi janyo ta jikin sa. Ƙoƙarin kwace kanta take yi, amma ina akan ya cutura, ganin ya rungume ta kamm a jikin sa yayin da yake ta shakar kamshin turaren dake tashi a jikin ta, yasa ta faɗin," ka sake ni Kalb, karka maid ni ciki man".


Ɗago ta yayi daga jikin sa, tare da zuba mata idanuwan sa masu ɗaukar hankali, yace ,"Amriya kunsan wani abu?, girgiza masa kai Amriya tayi tace,"Aa.


Kabir yace, "wallahi ina matukar kaunar ki sosai, kiyi min alkawari ba zaki taba, tafiya ki barni ba, murmushi Amriya tayi, sannan ta shafa sajen kansa wanda suka kwanta suka yi luff tace," nayi maka alkawari bazan taba rabuwa dakai bah har sai numfashi na, na karshe a duniya.


Murmushin jin dadi Kabir yayi! yace," Ni kuma insha Allahu zan yi ƙoƙarin wajan ganin cewa na baki hakkin ki a matsayin ki na matata uwar ƴaƴana, zan tarairaya ki tamkar kwai, zan kula da dake tamkar zinariya, zan tsaya tsayin daka domin ganin na kare ki kuma na biya miki bukatunki. Zan nuna miki soyayya tsantsa kawai batare da kiyayya bah. Na miki alkawari bazan kara bari wannan fuskar taki ta kara zubar da hawaye bah.


Indai ina raye babu wani bakin ciki dazan bari ya kusanci inda kike, saidai idan bana wannan duniyar kaɗai wani abu zai same ki, amma indai ina nan toh fuskar ki bazata taba gushewa da murmushi da farin ciki bah.


Murmushin farin ciki Amriya tayi, yayin da take jin kanta tamkar sarauniya, ringume shi tayi sannan tace," nima ina matuƙar son ka sosai Kalb, insha Allahu zanyi ƙoƙarin wajan ganin ban tauye maka hakkin ka bah na matsayin ka miji kuma uban ƴaƴa na".


Alhamdulillah Kabir ya furta, sannan yace, yanzu muje kuyi sallah, sannan muyi wa Allah godiya koh. Girgiza masa kai Amriya tayi tace tom, tashi Kabir yayi sannan ya mika mata bayan sa yace, "maza hau na goya ki".


Dariya Amriya tayi tace, " kana nufin goya ni zaka yi, aba dai sai kace wata yarinya". Kabir yace, " toh nidai a wajena ke komai ce dan aka maza hau mu tafi ɗakin .
Murmushi Amriya tayi tace, "kamar bakai ne wannan Kabir ɗin ba mai shegen zafin rai da kuma zuciya".


shagwabe fuska Kabir yayi yace, "nace miki kidai na tuna min abinda ya faru baya koh". Shi kenen kalb na daina cewar Amriya". Kabir yace, " yauwa koke fah, yanzu maza ki hau yau zamu yi abun.


Kunya ce ta kama Amriya, daga bisani kuma ta ɗane bayan sa. Ɗaukar ta yayi a bayan sa sannan ya nufi ɗaki da ita....


Washe gari da sassafe, Amriya ta shiga kitchen domin samar musu da abin karyawa, ganin aka yasa Kabir hana ta, sannan yace shi zaiyi musu abincin Breakfast.


Babu abinda Amriya bata ce mai bah, dan ya bar ta tayi Breakfast, amma ina bai yarda bah, ganin babu sarki sai Allah, yass Amriya ta ja gefe ta zauna tana kallon shi.


dora musu Breakfast kabir yayi, bread & egg, sai kuma ya haɗa musu coslow daban tare da shayi mai kauri. Bayan ya gama haɗa Breakfast ɗin, sannan ya nufi dining da abincin, tare da serving ɗin su.


Ganin plate na mutun ɗaya ne akan dining, yasa Amriya faɗin, " ina nawa? , Kabir ya bata amsa da faɗin, "gashi nan zamu ci tare".


Girgiza kai Amriya tayi tace, " nidai A'a nawa nake so daban, murmushi Kabir yayi yace," toh zaki karba". tashi Amriya tayi daga kan kujerar da take kai, ta nufi gurin Kabir.


Riƙe ta Kabir yayi sannan ya zaunar da ita akan ciyar sa tace, " ni zan baki a baki, kema kuma ki bani a baki okay .


Murmushi Amriya ta saki sannan tace, " shikenen tom, ɗaukar chokali Kabir yayi da folk sannan ya chaki Bread din ya fara bata a baƙi, aka suka cigaba da ciyar da kansu har suka koshi.


Bayan sun gama Amriya ta koma ɗaki sannan, ta bawa Hydar cerelak, bayan ta gama bashi abinci, sannan ta kaishi toilet sannan Kabir ya fara masa wanka, shikuws Hydar babu abin da yake yi sai wasa, farga lullube a fuskar sa.


Bayan sun gama wanka, Amriya ta shafa masa mai tare da saka masa kaya, ta lallaba shi yayi barci.


Kallon Amriya Kabir yayi yace, "kyakkyawar matata, yanzu saura mu ko, muje muyi wanka". Amriya tace, " toh kaje ka fara yin wankar mana".


A'a bazan je ba, ki tawo mu tafi tare muyi wanka, rufe fuskar ta Amriya tayi cike da jin kunya tace, "ni bazan iya bah, kawai kaje kayi naka, nima sai nayi nawa" .


Ba zato yaji ya ɗauke ta chakk, sannan ya nufi toilet da ita, shure _shure ta fara yi da kafar ta amma ina ta kasa ceton kanta.


Saka ta yayi cikin baff na wankan sannan shima daga bisani ya fada ciki.


Ni ko nace su madam Amriya saikun futo....


Fitowa suka yi cikin shigar su ta alfarma, sanye Amriya take da atamfa milk colour yaji stones da design, kayan ba karamin karbar ta yayi bah. Hannun ta kuma Hydar ne wanda yaji ke sanye da jeans da t-shirt,wanda suka masa kyau sosai.


Kallon su Kabir yayi, wow my beautiful family, kinyi kyau sosai fah, kunsha kamshi.
Murmushi Amriya tayi, sannan ta bude gaban mota ta shiga tace dashi, " ka shigo Mu tafi, nasan Ammi tana chan tana ta jiran mu".


Shiga ciki Kabir yayi, sannan ya tada mota, suka bar harabar gidan, tun da suka fara tafiya babu abinda Kabir keyi sai satar kallon Amriya ganin tayi masa kyau sosai bah kaɗan ba. Aka ya ci gaba da satar kallon su babu kakkautawa.


Ba zato suka haɗa ido da Amriya ta cikin madubi, ɗaga masa gira ɗaya Amriya tayi, tace Kalb yadai naga kana ta kallo na, hajiyan zuciya! Kabir yayi, sannan yace, "wai me yasa aka yi ki da kyau a kane, gaskiya ke makura ce a kyau, babu abin da kika rasa, gashi kin haifo min ɗa kyakyawa irin mu, gaskiya ni ɗan sa'a ne,
Samun mace kamar ki yana da wuya".


Murmushi Amriya tayi yayin da farin ciki ya lullube fuskar ta tace, "ina mai godiya a gare ka Kalb, kuma ina fatan mu dauwama a tare na ar abada".


Riƙe hannun ta yayi gamm, tare da rungume shi a jikin sa har suka isa gidan Ammi.


Isowar su gidan Ammi keda wuya, suka tarar da babu kowa a gidan, shiga ciki suka yi sallama rike a baki su, ganin ba'a amsa bah, yasa Kabir faɗin", kidai basua nan ne, toh amma ai sun san cewa zamu zo , bai kama ta ace zamu zo kuma mu tarar basua nan".


Kallon koh ina na parlour Amriya tayi, sannan tace," ni kamar ina ɗan jin motsi kaɗan_kaɗan".


Kabir yace,"kinga mudai na batawa kanmu lokaci, ki tawo mu tafi, tun da Ammi bata damu da ganin ɗanta bah, tsawon shekara guda kenen rabon da na haɗa idanuwa da ita, amma ba'a ba'a yi farin ciki da farfaɗo wa ta ba".


Aba kalb!, ya zaka ce ba'a damu da kai ba, bayan kasan yadda Ammi take sonka fiye da nima da nake yarta, kuma.....


Bata kaiga karasa wa ba, taga an haska parlourn da design da haske mai ɗaukar ido da hankali.
Daga bayan su suka ji an ce, surprise!, welcome back son.


Juya wa Kabir yayi, hatake ya haɗa ido dasu Ammi dasu Mami, sai kuma su Grandma dasu Doct habib gaba-daya kowannen su fuskokin su lullube yake da farin ciki da annashuwa.


Murmushi Kabir yayi sannan yace,"wow! duk wannan bazatar sabo da nine akayi?, Ammi ta bashi amsa da cewa,"kwarai kuwa duk saboda kaine".


Zuwa Kabir yayi inda Ammi take, sannan ya tsuguna tare da gaida ta, Albarka Ammi ta shiga sama sa. Daga bisani kuma, aka yanka cake wanda yake wajan tensteps.


Sosai aka yi shagali, aka sha firar yaushe rabo, bayan kowa yaci yasha, Ammi ta kalli Amriya tace,"daughter kina lafiya dai koh?, fatan dai kina kula wa da mijin ki da kyau".


Murmushi Amriya tayi tace," kwarai kuwa Ammi, baki ga daga jiya zuwa yau ba har yayi kiɓa, yayi fresh, sai kamshi yake buga wa, yau breakfast ma shi yayi mana".


Taɓe fuska Kabir yayi sannan yace, " Ni banso sharri fah, Ni zan dora mace girki lallai, da saidai na karo mata kishiya".

Dariya gaba daya suka kwashe dashi! gwanin burge wa, yayin da Nadira tace. Yahya a dai faɗi gaskiya fah, koda yake a bar kaza cikin gashin ta kada a fige ".


Kabir yace toh a fige mana, ita kanta tasan bazan mata girki bah. Kallon sa Khalid yayi yace,"dade a dane da kake asalin Kabir dinka shine zamu yarda, amma yanzu koh me zaka ce ba zamu yarda bah.


Sadiq yace, "Amriya ko dai kin bashi magani ne naga ya luma a kogin soyayyar ƙi". Kabir ya bashi amsa da faɗin, "A'a ka manta bita zai_zai ta bani na sha ".


Ganin abin nasu ba zai kare ba yasa Ammi tace, "yanzu dai ba wannan bah, ina da good news da nake so na sanar muku, Amriya dai ƴata

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads