Header Ads
Showing 87001 words to 90000 words out of 106900 words

Chapter 30 - ALJANAR RUWA CE COMPLT BY ASHA M.B .txt

Ads the beginning of article before Image

Aisha MB   

28 May 2024

1065

Ads at the middle of Article

fadar mu na cultism. Bayan na kaita, na hajiye ta agaban gunkiyar mu, a lokacin shugaba ya dauki takobi, sannan ya nufi Amiriya da zummar kashe ta, lokaci daya muka ga ya kurma ihuu, sai ji mukayi ya naku da kasa,.


Cikin fargaba da tsoro na mikar dashi, sannan nace masa, yanzu me zamu yi mu kawar da yarinyar, a lokacin yake Sanar dani cewar, me kashe yarinyar nan saiya shirya, babu wani mutum koh aljan, da ya isa nufan inda take da zimmar cutar wa, in kuma mutum yayi kokarin yin akan toh shi zai bar duniya bah ita bah.


Jin akan danayi yasa gaba na ya fadi, sa'anan nace dashi babu wata hanyar da zamu bi mu nesan ta yarinyar da mahaifiyar tah, shugaba yace mun akwai hanya guda daya, saidai idan sauya mata halitta zamu yi mu turata Chan cikin wasu jinsi daban, sannan shine burin na zai cika.


A lokacin nace ayi duk abunda ya kama ta, indai har zata Nisan ci inda Amina take babu damuwa, a lokacin Shugaba na, yafara wasu tsafa ce tsafa ce, inda a karshe yayi nasaran maida ta ALJANAR RUWA.


Cikin tsoro da fargaba na kalli Amriya sannan nace yanzu ya zamu yi da yarinyar, shugaba ya bani amsa da cewar, na dauki yarinyar na kaita nesa Chan katuwar teku inda nasan bazasu Kara haduwa da mamar taba, aka kuwa akayi, na dauki Sabreen na kaita tekun garin Lagos sannan na jefa tah aciki.


A lokacin nake ta murna cewar burina ya kusan cika, bayan komawa na cikin kungiya, na tarar shugaba ya ruga daya mutu, dalilin yinkurin kashe Sabreen da yayi.


Ganin akan yasa, nasa aka kwashi gawar sa aka yi sadaukar wa dashi, sannan aka nada ni a matsayin shugaba na kungiya.


Bayan wasu lokacin, na dunga mafarkai munana, wanda ake son daukan raina acikin mafarkin, ganin akan yasa nayi hanzarin nufa kungiya, Sannan nasamu mahaifa na mace, naci daga nan ban kar mafarkai bah. Kuma na bar farautar rayuwar Amina, nayi concentrating akan yadda zan ga bayan wannan ahalin.


Hankali na, bai tashi bah, sai lokacin da naga Sabreen ido da ido a wajan kungiya, ta saka mayafi ta rufe fuskan ta sannan tayi mana gargadin cewa kada mukara bibiyar rayuwar Kabeer, hankali na bah karamin tashi yayi bah, ganin cewar tabbas ta dawo duniyar tah, Kuma nasan da cewar itace,


A lokacin na Kuma tada makaman yak'i na, dole na kashe mutanen gidan nan, domin na cimma burina da Kuma na mahaifina. Kuma maganin dawo da ita asalin Mutum ni kadai ce nasan shi.


Wannan shine.


Innalillahi wa innahilahi rajihun! Innalillahi wa innahilahi rajihun, la'ila a'illa anta subha'anaka inninkun tun minan zalumin, Allahumma ajirni fi musibati.


Abunda kowannen su ke maimai tawa kenen. Hawaye mai zafi ne ya farabin kuncin Ammi, Kallon Mom tayi cikeda takaici da bakin ciki tace, naji kunyar kiran ki yar uwata, yanzu ke kin rabani da farin ciki na, kina walwalar ki, bakya jin cewa fah akwai hakkin wasu akan ki.


Wannan wace iriyar bushashiyar zuciya ce, toh ni yanzu bah wannan bah ki fadamin inda zansamu magani y'ata ta warke please na roke ki,


Kwashe wa Mom tayi da dariya tace, bansani bah, bani ya Kama ta ku tsaga ku kalla bah, yanzu Kuje ku nemi inda Sabreena yarki take tukunan,


Da sauri gabadayansu suka mike, yayin da su khalid suka samu suka daddaure Mom. Daga bisani suka fuce daga dak'in.


Daukar Motoci sukayi, yayin da sukayi bribing din body guards din da su barsu su futa, ganin kudade yasa, yan kungiyan asirin bude musu kofa suka fuce daga gidan,


Bayan fucewar su, Mom ta kunce kanta, sannan ta Kalli zoben Amriya da tayi nasaran zare shi daga hannun Kabir ta saki murmushi, daukar wayar ta tayi, ta kira Zainab, cikin kankanin lokaci zainab ta Iso gidan, yayin da Mom tayi mata rada a kunne, ni koh nace idan tayi tsami aji, daga bisani naga ta tattara gabadaya yan kungiyan, suka fuce daga gidan.


Direct gidan Ammi suka nufa baki daya, yayin da masu gadi suka bude musu kofa, suka Shiga ciki,


Futowa gabadaya sukayi daga cikin motocin, suka nufi cikin gidan.


Shiga parlour sukayi, cikin rashin sa'a kuwa su kaga Amriya bata gidan, ta karda Salma ta gani akan table, dauka tayi Tareda mikawa Mami, karba Mami tayi sannan ta Fara karanta wa kamar aka.






Assalamu alaiki Ammi, na rubuta wannan Sakon ne badan komai bah, saidan na gode miki akan abubuwa na alhery da kika aikata min, hakika kedin uwa ce ta gari, bansan da wane kalma zanyi amfani wajan gode miki bah, naso ace na sami irin ki amatsayin mahafiya, amma abunda Allah ya kaddara, babu wani Dan Adam da ya isa ya chanza shi, Dan aka ina godiya a gareku baki daya, ni zan tafi, zanje na cigaba da lallaba rayuwa ta, zanje na hafi danda ke cikina, a wani gurin daban, idan kuma lokacin mutuwa na yayi na mutu domin kuwa ina da tabbacin cewa tunda babu wannan zoben mutuwa zanyi, zanyi kewar ku baki daya, Dan Allah ki fadawa ahalin su Mom cewa ina matukar sonsu sosai, bazan taba mantawa da hallaci da kulawa da suka nuna min bah, ni na tafi kenen, bazaku Kara ganina bah ar abada, na koma duniya ta, duda sanin cewa ni ALJANAR RUWA CE, akan baisa kun gujeni bah, tabbas ku mutanen kirki ne, Kuma kiyi wa diyar ki Adua na sauka lafiya. nazo duniyar ku, na dandani dadin ta da Kuma rashin dadin ta, nasan yadda kuke mu'amala da mutane dakuma dabbobi, tabbas zanyi kewar ku sosai da Kuma duniyar ku, ina son ki Mika gaisuwa ta ga ahalin kalb, kice ina matukar sonsu, ban taba jin koda sau daya soyayya su ta zama kiyayya a zuciya ta bah. Ina fatan zaki karanta wannan sakon.
Na barku lafiya.




Zama gabadyaansu sukayi, yayin da gabadaya suka nemi kuka suka rasa. Rike kanshi Kabir yayi, yana ji kamar ya mari kanshi. Kallon Ammi yayi yace, kenen dama, Amriya tana da cikin dana bansani bah.


Share hawayenta Ammi tayi tace, kwarai kuwa Tana da juna biyu, Kuma danka ne.




??♀???♀???♀???♀???♀???♀???♀???♀???♀???♀???♀???♀???♀???♀???♀?






Comment & share
pls???
ALKALAMIN ??
AISHA M.B ???
(Baby isha)


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JYYV16dbYaX1dykLX7EE91


?BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM?
ALJANAR RUWA CE ??♀???
PAGE 5??1????5??2??
WRITTEN & DIRECTED ?? BY A'ISHA M.B??





-----------------------------------------
Amma wai shin meyasa baka son Amriya?, shin bata kai a sota bane?, meyasa a Koda yau she kana cikin kuntata mata,


Kabir ya bata amsa da fadin, Ammi bawai sonta ne bana yi bah, kawai dan inada wata a raina ne shiyasa, Nadirah tace Amma yahya ita ce dai wacce kake so, wacce ta cece ka acikin teku, tabbas itace,


Kuma wannan zoben na tane, bana kowa bah, so da dama tayi ?o?arin sanar dakai amma tsam baka fahimta, kuma yanzu saura wasu watanni ka?an kafin ta mutu,indai har bata samu wannan zoben bah, toh tabbas mutuwa zata yi.


Zama kabir yayi, yana jin zuciyar sa na masa kuna da radadi, dafa zuciyar shi yayi,yana mai fadin, ba zata mutu ts barni bah, insha Allahu babu abunda zai faru da ita, na aikata kuskure, tabbas na aikata babban kuskure, dole na nemo tah, domin ce to rayuwar ?i, nima na yarda dana bada rayuwa ta,indai zan ceci taki rayuwar.


Yana kaiwa nan ya fice daga parlour, su Sadiq na ganin akan,yasa suka bi bayan sa da sauri, shiga mota sukayi gaba-daya, yayin da "Kabeer ya tada mota, suka fice daga gidan.


Saida su Kabeer, suka kewaye garin Abuja ba?i daya, amma basu ga Amriya bah.


Kallon Kabir Sadiq yayi, yana mai fadin, Kabeer me zai hana muje gidan radio mu sanar da batan tah, Khalid ya ce, kwarai kuwa Kabir, maganar Sadiq gaskiya ce, ya kama ta muje gidan radio ka sanar da batar ta, tunda dai itadin matar kace.


Shikenen Kabeer ya fada, tare da fadin muje gidan radion, bah bata lokaci suka nufi hanyar gidan radio.


Cikin kankanin lokaci suka isa wajan, fitowa suka yi baki ?aya yayin da suka shiga wajan


Gaisawa da mutane wajan suka yi, inda Kabir ke sanar musu cewa, wani muhimmin abune ya kawo su, Kuma suna bu?atar su sanar da mutane.


Tashi ?an jaridan yayi, tare da bawa Kabir kujera ya zauna, zama Kabir ya yi, tare da ri?e speaker ya fara magana kamar aka.




Assalamu alaikum jama'a wannan garin, barkan ku da wannan lokacin, fatan kowa na cikin koshin lafiya, sunana Kabir Muhammad yunusa, kamar yadda mutane suka sani, nine mai Company fishes production na Abuja, nazo wannan gidan radio ne badan komai bah,sai ?an na sanar da wata muhimmiyar magana, hana cigiyar wata budurwa wacce a kalla zata kai shekaru ashirin da haihuwa, kuma duk wanda yayi ?o?arin gano inda take yana da kyautar million ?aya, za'a buga hotunan ta yanzu kuma inason a ya?a, zan hajiye number na, duk wanda ya ganta sai ya kirani, 07045421451, wannan shine number na.
Ina fatan za'a ganta.


Kabeer na hajiye speaker,wata kira ta shigo wayar sa, cikin rawar jiki Kabir ya yi saurin ?aukan wayar, ?aga wa yayi, tare da fadin Hello!, daga ?ayan ?angare naji ance, shin ina magana da Kabir",


Kabir ya bashi amsa da cewar, eh nine, waye akan layi? daga ?ayan ?angare akace sunana Sani, tambaya ce a ba?i na akan yasa na kira ka, bawai naga budurwar bah.


Kabir yace, ina jin ka fada min, Sani yace, shin budurwar da kake nema itadin wacece a wajan kah?, mene ne ha?in ka da ita?,


Murmushi Kabir yayi, yace zan fa?a muku wacece ita, kashe wayan yayi, ya saita ba?in sa dai-dai wajan speaker yace, itadin matata ce kuma kan wata, Kuma tabbas itadin rayuwa tace, idan har bangan ta bah, bana tunanin zan iya cigaba da kasan cewa a raye.


Share hawaye da ke ?o?arin zubo masa yayi, yace tabbas nasan da cewa kina jina, na ro?eki, ki dawo rayuwa ta, ba zan taba iya rayuwa in babu ke.


Kin yi min komai a rayuwa, inason nima na saka miki da abinda kika aikata a gareni, Amriya ki sani cewa ba iya sonki ka?ai nake bah, zan iya bada rayuwa ta, saboda ke da kuma ?ana na cikin ki, mahaifyar ki tana bukatar ki a kusa da ita, ki taimaka ki dawo, zamu nuna miki kulawa wacce ba?i ta?a tsammani bah. Ina fatan zaki dawo gare mu.. Yana kaiwa nan, ya kashe speaker, sannan ya fuce daga wajan da sauri, tareda nufan cikin mota,


Kuka ne yaci karfin sa, saida yayi mai isarsa,ganin su Khalid suna nufo inda yake,yasa yayi saurin share hawayen sa, tareda goge fuskan shi da handkerchief.


Shi ga cikin motan suka yi, suka tarar da Kabeer yayi jugum, hajiyan zuciya suka yi, Sadiq yayi karfin halin fa?in, Kabir why are thinking?, kwanakin baya idan ba zaka manta bah,me muka ce maka?


Lokacin da kake wulakanta ta, kayi mata duk abunda ranka yaso, duka, zagi, cin mutun cin, babu Wanda baka yiwa Amriya bah, so now tell me are you not regretting of all what you did to that innocent girl, who's suffering now between you and Amriya?.


Tagumi Kabir yayi, yayin da ya nemi kuka ya rasa, cikin kasala ya motsa leben sa, tareda fadin, lokacin rashin sani ne, tabbas dana san cewa, Amriya ita ce ta ceci rayuwa ta a teku daban aikata mata akan bah,duk abunda kuka ga nayi,duk acikin rashin sani ne, kuma ina fatan ta yafe mun kura kurai na.


Khalid yace yanzu solution muke nema,bah labari muka ce ka fada mana bah, mu tada mota muje a buga photon ta cikin jarida a ya?a, saboda a ganta, if not, am sorry to say, Ba zamu ganta bah,


Kabeer yace, na ruga dana aikata akan tuntuni, an ruga da an ya?a photon ta,kuma nayi al?awarin cewa,duk wanda yayi nasaran ganin ta, yana da kyautar million ?aya.


Khalid ya ce, Kabir bani motan na tuka,saboda yadda nake ganin ka ?in nan, bah lallai ka iya yin driving bah. Okay Kabir ya fa?a, tare da bawa Khalid driver sit ya zauna. Tada motan Khalid yayi suka bar harabar wajan.


Babu abinda kake ji a gari, sai maganar batar Amriya, gaba-daya garin Photon Amriya ne kawai ke yawo, inda gaba-daya maganar batar ta kawai ake yi a gari,yayin da mutane na ?aukan Photon a waya suna ya ?awa a kasassen sada zumunta, irinsu facebook, twitter, Instagram dadai sauran su............


Kwance take a gefen bishiya, tayi ta gumi, yayin da gaba daya fuskan ta, ya Ku kumbura, idanuwan ta, sunyi jajir, hawaye ta, ta share da bayan hannun ta, sannan tace,


Makaryaci, mugu, azzalumi, wato ni zaka nuna a idanuwan duniya ksce kana so, saboda na koma, ka cigaba da galla zamin azaba kamar yadda ka saba.


Na tsane ka Kabir,bana qaunar ganin ka, bana fatan na sake hada idanuwa dakai har tsawon numfashi na, na karshe.


Shafa cikin ta Amriya tayi, tana mai fa?in, kada ka damu ?ana, zan Kula dakai Kamar yadda kowacce mahaifiya zata kula da ?an cikin ta, bazan ta?a barin wani abu na cutar wa ya same ka bah, mundin ina raye, babu wanda ya isa ya taba ka.
Tana kaiwa nan ta mi?e tsaye, ta cigaba da tafiya.


Bayan isarsu Kabir gidan Ammi, suka tarar da kowa na parlour yayi ta gumi,
Kallon su, Sadiq yayi yace, me yasa Kuma naga kowanne ku acikin damuwa, bai kamata ace mun zauna aka bah, mafita ya kama ta , ace mun nema, ba wai kowa ya zauna yayi tagumi bah, indai akan batar Amriya ne, insha Allahu zamu ganta.


Yanzu ku taso mu koma gida kunji, insha Allahu, Allah zai bayyana mana ita. ?an jimmm Aunty amarya tayi, tareda kallo su Ammar tace, triplets Inason gobe goben nan, ki harhada kayayyakin ku, ku koma kasar Turkish.


Abdul yace, Amma umma tayaya zamu tafi bayan ba'a ga Amriya bah, damuwar ku shine damuwar mu, tayaya zamu iyayin abunda ya kaimu, bayan bamu ganku cikin walwala bah kafin mu tafi, gaskiya babu inda zamu je, in mah mutuwar ce , mu mutu tare , amma babu inda zamu je.


Daka mai tsawa Kabeer yayi! yace, Abdul Hope you are not out of your senses, Hana nuna muku hanyar daya dace, kuna yi wa mutane iska ci, toh Wallahi ksda kabari na saku a jeri mutanen da nake taming,


Maza ku tashi mu koma gida, tashi ba?i ?aya su, suka yi tare da ficewa daga parlour,suka nufi inda mototcin su ke a fake, suka shiga, yayin da su Aunty amarya,da maman Kabir suka yi sallama da juna, daga bi sani suka fice daga gidan.




Haahaha! Mom da Zainab suka kwashe da dariya, Zainab tace, ai ki min daidai karima, gwanda da kika azabtar dasu, hmmm wannan mah kadan su kaga gani.


Mom tace ke dai bari, Zainab ai ina fada maki, ina kashe su baki daya zamu kwashe dukiyar, sannan mu more duniyar mu da tsinke.


Zainab tace wallahi kamm, amma Karima, shin harda Kabir zaki kashe?,
Mom ta bata amsa da fa?in eh mana hai shi zan fara kashe wa.


Mike wa Zainab tayi tsaye tace, ba zai yiyu ba, ba zaki kashe Kabir bah, kinsan da cewa ina matukar sonsa shine zaki ce wai shi zaki fara kashe, toh gaskiya bazan yarda bah.


Mom ji tayi kamar ta kurms ihuu saboda takaici, murmushi mugun ta tayi, sannan tayi ?asa da murya tace, ana dai Zainab, ke dadi na dake bakya kwashe wa, ai bah kashe kabir zanyi bah, ina nufin shi zamu fara kwamushe wa, na saka shi ya aure ki,koh yana so koh baya so.


Murmushi Zainab tayi sa'annan tace, yanzu naji magana, amma dazu da kika ce shi za'a fara kashe wa, hankali na bah karamin tashi yayi bah.


Mom tace shikenen dai,nidai na samu matsuguni, daga yau a gidan nan zan dunga zama, har zuwa wasu kwanaki, dariya Zainab ta kwashe dashi!, sannan tace, kada ki samu damuwa shugaba, ki dauka cewa nan gidan ki ne, kiyi duk abunda ranki yake so.


Tashi Mom tayi tare da shigewa cikin ?aki,
Zainab na ganin aka ta bi bayan ta da sauri.


Zuwan su Kabir gida keda wuya, suka tarar Mom da sauran yan qungiyan ta basua nan.


Cikin gidan suka shiga, yayin da Kabir ya tura keyan su triplets gaba, yasa suka fara har hada kayayyakin su.


A ranar babu wanda yayi bacci kirki a cikin su, washe gari da sassafe, su triplets suka wuce ?asar Turkish, yayin da su kabir suka kuma koma wa gidan radio domin jin shin wani ya gano masani inda Amriya take, amma cikin rashin sa'a kuwa su kaje ba'a ji wani labari akan Amriya bah.


Aka su Kabir suka dunga zaryar zuwa gidan radio harna tsawon wata guda, saboda yadda suke zuwa akai akai, yasa mutanen wajan suka gane su.....................




Tafiya ta ke yi batare da tasan inda take nufa bah, gaba-daya ta rame tayi ba?i, fatar ta ya fara komawa ruwan tarwa?a. Yayin da gefe guda kuma cikin jikin ta ya soma girma. Wani karamin matsuguni ta samu acikin wannan jejin ta zauna, tare da share hawaye dake zubo mata.


Kallon yadda farin wata ya haska dajin tayi, ta saki dan ?aramin murmushi, tare da shafa cikin ta tace, wai yaushe zaka iso duniya domin ganin yadda take da matukar kyau, gwanin ban sha'awa.




Zan so ace a gaban idona zaka girma, amma akan bazai yihu ba, Saboda ni mutuwa zanyi na barka, amma ?ana zan roke wa wata alfarma ,


Indan Allah yayi kazo duniya da rai da lafiya, kuma ka girma, dan Allah kada kayo halin mahaifin ka, kaji koh, tsam banason ka dauko halin baban ka. Tana kaiwa nan ta jingina ajikin bishiyar tare da lumshe idonta...........




Shin kai yanzu misali idan ka samu million ?aya, me zaka yi dashi?, dariya na kusa da shi yayi, sannan yace, kaii abubuwa da dama, farko zanje ne na biya kudin makarantun yaran na , sannan na siyi kayan abinci na gida , sauran kudaden da suka yi ragowa kuma, na dora wa kaina jari.


Saurin dafa shi abokin nasa yayi yace, sani kaga mai na gani kuwa?, Sani ya bashi amsa da cewa, ni banga komai bah, menene ya

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads