Header Ads
Showing 90001 words to 93000 words out of 106900 words

Chapter 31 - ALJANAR RUWA CE COMPLT BY ASHA M.B .txt

Ads the beginning of article before Image

Aisha MB   

28 May 2024

1071

Ads at the middle of Article

faru?


Nuna yatsan shi abokin nasa yayi, yayin da Sani yabi ?an yatsan nasa da ido, abunda ya gani ne yayi matu?ar bashi mamaki, dafa abokin sa Sani yayi yace, Wannan bah ita akace hana nema bah, wata ?aya daya wuce, tabbas babu makawa itace,


Yanzu zan kira Sir Kabir na sanar masa,kaga mu kuma sai a bamu kyautar million ?aya. ?aukan wayar wacce take keypad yayi, tare da dialling number Kabir.


Kabir dake kwance kan gado gaba-daya yayi wani iri, yayi sanyi bah kamar daba, ganin hana kira shi, yasa ya bi wayar da kallo, ganin sunan Sani ne bayyane akan screen din wayar sa, akai yasa shi jan tsaki, sannan ya koma ya kwanta...


Wai me yasa mutumin nan baya ?aga wa ne , koh baya kusa da wayar tasa ne. Abokin nasa yace masa, ka kara kiran sa, wallahi million ?aya bah wasa bane.


Cigaba da dialling number Kabir Sani yayi, yayin da Kabir koh takan wayar baibi bah,
Inda a karshe ya kashe wayar gaba daya ...


Kashhh!, wannan mutumin ya kashe wayar, kuma gata a gaban mu,kenen munaji, Muna gani, zamu tafi mubar ta,


Sani yace, inada wata shawara, muje mu gwada jarrabawa koh Allah zai sa a dace.
Nufan inda Amriya ke kwance suka yi, sallama rike a bakin su.


Zumbur Amriya ta mi?e, cikin fargaba da tsoro!, kallon su tayi cikin tsorata tace, su waye ku?, me kuke nema?, shin akwai wani abu na kune a wajan nan?,


Kallon ta Sani yayi yace, sannun ?i baiwar Allah, bamu zonan da nufin cutar dake bah, mun zone, domin jin matsalolin ki,menene sanadin da yasa kika kasance acikin wannan dajin?, me yasa ba zaki koma ga yan uwanki bah,


Dan jimm Amriya tayi, sa'annan tace, babu komai, labari ne mai dogon zango, kudai kada kudamu dani, babu abunda zai same ni, kawai kuje kawai, a aka kaddara ta ta zomin, kuma a akan zan amshe ta.


Sosai tausayi Amriya ya kama sani,da Kuma abokin sa Dini. Kallon ta sani yayi, tare da kallon kayan jikin ta, yaga duk sun yi kura sun yi datti sosai, ga ciki ta a gaba, wanda bazai wuce watanni bah.


Cike da tausaya wa sani yace, Allah sarki baiwar Allah menene sunan ki?, kallon sa Amriya tayi, sannan tace sunana "AMRIYA".


Toh Amili na, me zai hana kizo ki dunga zama a gida na, har zuwa sanda Allah zai sauke ki lafiya, sabo da naga alamun kina bukatar kulawa sosai, bai ka mata ki zauna hanan ba, kunji ke mace ce, ka mata ai ace ki kasance a inda yake da tsaro, domin ganin kyakkyawa irin ki, kan iyasa shedan ya rujayi zuciyar wani, sannan yazo gare ki da zimmar cutarwa.


Haka ne, na gode sosai, bana bukata, banason ace na wahalar daku wajan daukan nauyi na, ku barni hanan kawai, inason ya kasance ni kadai ce, banason na kara shiga cikin jinsin bil adama.


????????????????




COMMENTS & SHARE
PLS ??
ALKALAMIN ??
A'ISHA M.B ??
(baby Isha)






Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JYYV16dbYaX1dykLX7EE91


?BISSMILLAHI RAHMANI RAHIM?
ALJANAR RUWA CE ??♀???♀??
PAGE 5??2????5??3??


WRITTEN & DIRECTED ?? BY A'ISHA M.B?? (baby Isha)






-----------------------------------------
Kamar ya kenen? Jinsin bil adama kuma! Sani ya fada, tareda fadin gaskiya baiwar Allah maganar ki akwai alamar tambaya aciki.


Murmushi Amriya tayi, tana mai fadin, shikenen nagode, zaku iya tafiya.
Mutafi ina kenen? Mufa babu inda zamuje idan baki biyomu bah, cewar Dini.


Ran Amriya ne ya soma baci, ganin babu alamun zazu tafi su barta a wajan, danne fushin ta tayi, sannan tace, kada kudamu dani, ni nasan yadda zan kulada kaina, basai na bukaci taimakon kowa bah, kawai kuje, ni nasan yadda zanji da al'amurana.


mudai mince miki babu inda zamu, kafarki kafar mu. Cikin baccin rai Amriya ta daka musu tsawa!, wanda ya sanya jikin kowannen su ya fara bari, ?ura mata ido suka yi, yayin da suka ga kwayar idanuwanta na sauya launi .


Ja da baya suka fara yi, inda Amriya ta maida kallon ta kansu tace, ba so kuke ku tunzurani bah, ku tawo toh, banzaye marasa tunani, wallahi idan kuka yi wasa saina kashe ku hatake a wajanan.


Ha?a hannayen sa guri guda Sani yayi, sannan yace, dan Allah kiyi hakuri, bamuzo wajan ki da niyar cutar dake bah, ki taimaka ki rabu damu, na miki alkawarin koh keyar mu bazaki kara ganin bah, kinji dan Allah ki taimaka.


Tausayin sune ya kama ta, binsu tayi da kallo, sa'annan tace, shikenen ku tafi, na rabu da ku, amma kada ku kuskure Ku fada wa kowa cewa kun ganni, idan kuka kuskure ku ka fada wa koda Kabir ne, toh nan gaba ku za'a aska a jarida cewa kun zama shekakku.


Cike da tashin hankali Dini yace, na rantse da gyatuma ta laure, bazamu fa dawa kowa bah.


Toh maza maza yanzu ku bace min daga gani. Amriya na kaiwa nan, su Sani sa R, wato suka saka gudu. Amriya na ganin sun tafi yasa ta bar wajan, inda ta cigaba da tafiya.


Su Sani basu tsaya bah, saida suka ga sun shiga cikin mutane, ha?i kowanensu ya dinga yi, tare da saukar da hajiyan zuciya.


Wayan Sani yaji tana ruri, ?aukan wayar yayi yaga sunan Sir Kabir rubuce akai. bai bari wayar ta katse bah yayi saurin ?aga wa, magana Kabir ke shirin yi, Sani ya riga shi da fadin, sir Kabir ina ka hajiye wayar ka, inata kiran ka.


Daga dayan bangare Kabir yace, eh bana kusa da wayar ne, mene ne ya faru? naji kamar kana ta ha?i, badai abunda ya faru koh?,


Sani ya bashi amsa da cewa, ai sir Kabir komai ya faru, yanzun nan, naga wannan budurwa da kake cigiya wajan wata ?aya daya wuce.


Zumbur Kabir ya mi?e daga kan gado, tare da daukan car key , yanufi hanyar parlour da sauri, ganin Kabir cikin tashin hankali!, yasa su Aunty amarya dasu Grandma suka nufi inda yake.


Kabir yace sani fada min inda kake yanzu zanzo, dan Allah kada ka bari ta kufce muku, ina zuwa yanzu, katuramin da address din wajan right away. Fada masa address dinda suke Sani yayi,


Kabir yace gani nan zuwa yanzu nan, yana kawai nan ya katse wayar. Da sauri ya fara tafiya, koh kallo gaban sa bayayi saboda kidimewa da yi.


Saurin shan gaban sa Sadiq yayi, tare da fadin, ina za kaje aka?, naga kamar hankalin ka a tashe, fada mana mene ne ya faru?, dafa kansa Kabir yayi, yana ms fadin, Sadiq dan Allah ka hajiye wadan nan tambayoyin a gefe, zanje wani guri ne, and is very urgent so please allow me to go.


Kallon sa Sadiq yayi, sannan yace, wani wajan bashi da sunane, ka fada mana Kabir, meyasa kake kokarin boye abubuwa wanda ya shafi rayuwar ka,


Takaici ne ya ishi Kabir, ganin Sadiq bai gifta daga inda yake bah, yasa shi fadin,


Kirana Sani yayi, sannan yake sanar min cewa yaga Amriya, what! Gaba daya suka fada, yayin da Kowa ya mike,


Doct Khadija tace, kana nufin anga Amriya, a ina aka ganta?, ya kama ta kuyi sauri kuje ku nemo ta, inbah aka bah, toh ina mai tabbatar muku da cewa, tana gano cewa mun san inda take toh na tabbata saita bar wajan.


Yanzu bakuda ishashen lokaci, Kabir kuje, sannan ka dawo da matar ka cikin rayuwar ka.


Kabir bai jira Doct Khadija ta inda magana da ya fuce da sauri, ganin akan yasa su Khalid da kuma Yusuf bin bayan sa.


Mota gaba-daya suka shiga, yayin da Sadiq ya tada Mota, suka fuce daga gidan.


Location din wajan suka fara bi, bai dauke su Lokaci bah suka samo address din wajan.


Fitowa Kabir yayi daga mota ya hangi Sani a tsaye sai sharfe zufa yake. Da sauri ya isah wajan su Sani, Sani da gaba-daya hankali shi baya tattare dashi, ya hangi Kabir yana nufo inda suke.


Ganin Kabir yasa shi saurin nufa wajan su, kallon sa Kabir yayi, sannan yace dashi tana ina?, ka kaini wajan ta, ina bukatar ganin ta, yanzu ka kaini wajan ta Please, ya karashe maganar hawaye na sauka kan kuncin sa.


Tausayi Kabir ne ya kama kowannen su, kallon Kabir Sani yayi cikin tausaya, yace, ka kwantar da hankalin ka Sir Kabir, ina mai tabbatar maka da cewa babu inda taje, a wajan muka barota, dan aka, kasha fawa zuciyar ka ruwan sanyi.


Yusuf ne ya kalli Sani sannan yace masa, toh me zai hana ka kaimu, kaga bamu da isashen lokaci.


Kallon su Sani yayi yace, eh mana mezai hana na kaiku, amma mu fara maganar kudin da kuka ce za'a bawa duk wanda ya ganta, dole mu fara maganar kudin tukun nan, dago rinannun idanuwan sa wanda suka kada sukayi jajir, cikin muryar sa wanda ya ruga ya dashe saboda kuka yace,


Ban taba rokan wani alfarma bah, amma yau zan roke ka, na roke ka Sani ka taimaka ka kaimu inda take, indai maganar ku?in ce ba kada matsala, zan ninka maka akan wannan million ?ayan, amma first thing shine ka fara kaimu inda take Please and please.


Kin Kabir yace zai ninka ku?in akan nada yasa sani, fadin Tom shikenen tunda kace aka, ku biyoni, yana kaiwa nan ya fara tafiya. Kabir dasu Khalid naganin aka suka bi bayan sa,


Duk inda Sani da abokin sa Dini suka yi nan suma su Kabir ke yi, saida suka yi tafiya mai nisa sosai, sannan Sani ya dakata. Kallon bishiyar da Amriya ke zaune dazu yayi yaga wayam bata nan.


Hankalin Sani ne ya tashi ganin ba Amriya a wajan, zagaye bishiyar ya fara yi koh zai yi nasaran ganin Amriya, amma ina koh gizon tah bai ganin bah,


Cike da takaici Sadiq yace, ka kaimu inda take mana, kazo nan sai faman zagaye bishiya kake, dafa Sadiq Kabir yayi, sannan yace Aa Sadiq kayi hakuri, kayi masa magana a hankali,


Kallon mamaki Sadiq yabi kabor dashi, wai yau Kabir ke cewa ayi wa wani magana a hankali, tabbas ya yarda soyayya tana iya chanza mutum.


Kallon su Sani yayi yace, kuyi hakuri ta ruga ta bar wajan, da hanan take amma yanzu bata nan, munyi rashin nasara.


Dafa kansa Kabir yayi, yayin da yake ji jiri na diban sa, zama yayi a bakin bishiyar, tareda cewa why Amriya?, Why?, wannan azabtar War da kika min ya isa aka, dan Allah ki taimaka ki dawo gareni, bazan iya rayuwa bah babu ke, nayi dana sanin abubuwan dana dunga aikata miki a baya, nasan nayi kuskure, amma meyasa ba zaki bani last chance bah, me yasa zaki tafi ki barni cikin wannan halin, ya karashe maganar hawaye sabon kuncin sa.


Tausayi sa ne ya kama su baki daya, tabbas babu abinda so ba zai iya yi bah, dafa shi Khalid yayi yace kayi hakuri Kabir ka taso mu tafi, ta riga data bar wajan nan, kaji ka taso mu tafi, in Allah ya yarda wata rana zata dawo gare ka.


Girgiza kai Kabir yayi, yana mai fadin, ni babu inda zanje kawai ku tafi, ni bazan bar nan wajan ba, bah tareda naga Amriya da idanuwa na bah, kuma sannan ta furta cewa ta yafe mun bah, kuje kawai ni zan zauna a nan wajan, ya fa?a hawaye na sauka kan fuskar sa,


Kallon sa Sadiq yayi yace, Aba Kabir, ba zai yu mu tafi mubar ka hanan wajan kai kadai bah, na fada maka cewa Allah zai bayyana tah, bansan cewa mace zata iya chanza ka bah kabir, ka kwantar da hankalin ka, koh so kake wani abu ya faru dakai, kana tunanin idan wani abu ya same ka zamu kasance a raye ne, Please kada ka kashe kanka da tunanin, ga hawaye mah kullum yanzu yazamar maka ruwan dare,
Dan aka mun fauwalah wa Allah komai kaji,


Murmushi wanda yafi kuka ciwo kabir yayi, sannan yace, duk abinda ya faru laifi na ne, da tun farko na aminta da Amriya mun zauna lafiya da ba'a kai ga taki haushi ba, har tazo kuma ta tsaneni.


Kawai ku tafi, ku barni a nan, Inason na kasance hanan har sai lokacin da naji cewa ta dawo gareni, bazan bar wajan nan bah har sai lokacin da bayyanar ta zai zo.


Kuje kawai, kubar ni hanan, nasan yadda zan lallaba na rayu a wajan nan.


Cike da tausaya wa Yusuf yace, Allah sarki Kabir kayi hakuri ka tashi mu tafi, Allah ya ruga daya rubuta cewa abunda zai faru kenen, ka daina ganin laifin kanka, babu wanda yazo duniyar nan sannan yace bai taba laifi bah, so kaga Amriya zata dube ka da idon rahama kuma sannan ta yafe maka, kaji.


Maza taso mu tafi, mikar da Kabir Yusuf yayi, inda Kabir ya soma tafiya, amma cikin rashin sa'a jiri ya dibe shi ya fadi a wajan sumamme.


Hankalin su Sadiq ne ya tashi! ganin Kabir cikin mawuyacin halin, jijjigashi suka soma yi amma koh gizau baiyi ba, su Sani na ganin aka suka salallaba sannan suka harce.


Cikin tashin hankali! suka Cincibi Kabir, sannan suka fara tafiya, saida suka kai bakin titin, sannan suka nufi wajan motar su, yayin da gefe guda idanuwan jama'a akansu,


Dire Kabir suka yi acikin mota, sannan Sadiq ya tada mota suka bar wajan, basu nufi koh ina bah sai hospital. Direct reception suka shiga dashi, inda nurses suka bawa kabir gado, aka shigs emergency room dashi.


Daukar wayar sa Khalid yayi, ya sanar da su Dad da kuma su Aunty amarya halin da ake ciki.


Cikin kankanin lokaci, gabsdyaa family suka bayyana a wajan, fuskar Mommy mahaifyar Kabir ne yayi shabe shabe da hawaye, sannan tace, shidai dana tun da yazo duniya cikin fuskan tar kalubale yake, Allah ka kawo masa agaji, kwantar mata da hankali Dad ya shiga yi, .


Kallon su Khalid Doct Khadija tayi,sannan tace mene ne ya faru a inda kuka je?,
Tun daga abunda ya faru har karshe Khalid ya zayyane musu.


Jinjina kai kawai Doct Khadija tayi, sannan tace shikenen abunda nake gudu shi yake shirin faruwa, Kallon ta Aunty amarya tayi tace, menene yake shirin faruwa Khadija?,


Kafin Doct Khadija ta bawa Aunty amarya amsa, wata nurse ta futo daga daga room din,


Ganin nurse din yasa dukkan su mikewa, sannan suka ce ya jikin nasa?,


Nurse ta basu amsa da cewa alhamdulilah mun samu ya farfado, amma munji yana kiran sunan wata wai Amriya, da alamun itadin wata ce a rayuwar sa.


kuma bincike ya nuna cewa yana saka tunani a ranshi sosai, kuma yana yawan shiga damuwa akan wani abu, a gaskiya kuma ya kamata ace idan kuna da abun kuyi gaggawar bashi, in bah aka bah, wannan abun zai iya affecting kwakwal war sa.


Gaban kowannen sune ya fadi, yayin da kowa ya rasa ta cewa, Yusuf ne yayi karfin halin fadin shikenen insha Allah zamu bashi duk abinda yake bukata, shin yanzu zamu iya shiga mugan sa?.


Yes of course Why not, zaku iya shiga, amma dan Allah banda haya niya, domin mara lafiya yana bukatar hutu, zaku iya shiga, yanzu zanje pharmacy ne domin siyo maganin da doctor yayi prescribing za'a bashi, tana kaiwa nan ta fuce daga wajan.


Cikin room din suka shiga, inda suka tarar da kabir sai zubda hawaye yake, gefe guda kuma sunan Amriya kawai yake kira.


Tausayi sane yaka masu, tabbas so yayi wa Kabir mugun kamu.


Kallon sa suka yi, yayin da suka ji yana fadin. Ki dawo rayuwa ta, zan baki kulawar da baki taba tsammani bah, kada ki gujeni, domin idan kika barni zan shiga wani hali, sonki a raina ya riga daya zama dashashe, wanda babu wanda ya isa ya iya cire sonki a raina, Please Amriya, i need you, i want you to stay with me for the rest of my life, dan Allah ki bani last chance,


Ya karashe maganar hawaye nabin gefen fuskan shi.


Zuwa Mommy tayi daff dashi sannan ta rungume sa, tare da fashe wa da kuka, kuka sauran yan dakin suka fashe dashi, yayin da aka rasa mai rarrashin wani.


Jin koke-koke, yayi yawa a dakin yasa su doctor's saurin nufa dakin, tarar dasu suka yi kowannen su na kuka.


Gyaran murya daya daga cikin doctor's din yayi yace, aba dan Allah, wannan mara lafiya fah muna tunanin zaku tafi dashi gida,saboda jikin shi yayi kwari sosai, amma dubi yadda kuka sashi a gaba, yana kuka kuma nayi , an rasa mai rarrashin wani acikin ku, Please ku futo.


Futa gaba daya suka yi daga cikin dakin, bayan hours aka sallame su daga asibityn, bayan sati daya, jikin Kabir yayi sauki sosai,kamar bashi bah, Amma har yanzu bai daina tunanin Amriya bah.


Inda gefe guda kuma aka saka auren Khadija kanwar sadiq da kuma A'isha, sosai aka sha shagalin aure, akayi buki na buga wa a jarida, babu wanda bai halarci bikin bah, amma duda akan babu walwala a fuskokin su,


Bayan nan aka kaisu gidan mazajen su, inda Doct Khadija, da kuma Mommy sukayi musu nasiha mai ratsa zuciya.


,tsaknin amare da mahaifyar amare wato hajara, suka dunga kukan rabuwa, da kyar aka kwace hajara daga hannun su, sannan suka bar gidan su amare, kowa ya koma gidajen sa.......




.BAYAN WATANNI BIYAR.
nakuda take ba gaggau tawa, yayin da take jin marar ta nayi mata radadi da ciwo, rintse idanuwan ta tayi, hawaye na bin kan kuncin ta. Ba zato taji marar ta ya rike, ihuu! ta fasa wanda ya gauraye gaba daya ilahirin dajin. hatake kowane halitta na ruwa ya fara fito wa, suna nufan inda take,


yayin da aljanun ruwa da kuma yan ruwa suka fara zagaye ta, suna shafar cikin ta, wani karan! ta kuma fasawa,


Gaba daya ta jigata, yayin da numfashi ta ya fara sarke wa, huxu ta fara yi, inda gumi ya fara keto mata,


Shafa kan Amriya daya daga cikin aljanun ruwa tayi, sannan ta fara hura mata iska ajiki, yayin Da gefe guda wata Aljanar ruwaye ta fara tura cikin dan tayi nasaran haifi ?an cikin nata.


Danna Cikin Aljanar ruwar tayi, hatake Amriya ta fasa wani irin razanannen kara, wanda yasa aka soma iska mai mugun karfi,


Numfashin tane ya fara kasa, inda daga karshe tayi nasaran numfashi wanda yasa santalele jariri fadowa.


Hatake kukan jaririn ya gauraye dajin, kwanciyar Amriya tayi tana saukar da hajiyan zuciya.




??♀???♀???♀???♀???♀???♀???♀???♀?????????????????






COMMENT & SHARE PLS???
ALKALAMIN??????
A'ISHA M.B???
(Baby Isha)


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JYYV16dbYaX1dykLX7EE91


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah,

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads