Showing 21001 words to 24000 words out of 106900 words
Chapter 8 - ALJANAR RUWA CE COMPLT BY ASHA M.B .txt
kamar haka saike.
tunda nake mom dina bata taba zagina bah bare duka. Amma yau sabida ke mom dina tadaga hannu ta mareni.
Meyakamata nayi kenen, tashi yayi yafara kaikawo yace fadamin meyakamata nayi miki. Wane hukunci yakamata nayanke miki.
Cikin sheshekar kuka Amriya tace. Ka.. Mai.. Da.. Ni.. Gida.. Nayi.. Alka.. Wa.. Rin.. Zan.. Tafi...
Cikin zafin rai yazare ballet dinshi baiyi wata wata bah. Yafara zuba mata. Tun Amriya na iya ihuu har muryanta ya dashee.
Saida yayi Mai isarsa. Yasamu kafarsa yayi ball. Da ita.
Dafe cikinta Amriya tayi. Wanda yake mata mugun ciwo.
Dago kanta tayi tadora hakansa cikin zuciyanta kuwa tace. Ni, wanda naceta, wanda na taimaki rayuwansa yake duka, nayi danasani tabbas na aikata babban kuskure a rayuwata. Dana yi niyan kasheka yanzunan zan iyayi amma bazan yibah.
Maida kallonta kansa takumayi tace. Kaji... Tso..ron . Allah Kalb.
What mee waye Kalb. Ni. Are you mad. Daga ta yayi daga kasanda take yakalleta. Wani Marin yakara sharara mata.
Hadeda wurgarda ita kasa.
Numfashi Amriya tafarayi sama sama. Jini na Bin kanta da bakinta
Ni zaki fadawa adini. Inbanji tsoron Allah bah tsoronki zanji.
Ahalin yanzu numfashin amriya baya futowa sosai. Dan da kyar takejan numfashi.
Wannan kadan kika gani Wlh saina sa duniyanan ta gagareki, saina sa kinyi danasani sanina dakikayi a rayuwarki.
Yana gama fadin haka ya aura sama.
Jan jikinta Amriya tafarayi. Jini nata zuba takanta. Dafa kujera tayi zata tashi. Wani mugun jiri ne ya dibebata faduwa tayi awajan sumammiya.
Futowa Kabir yayi. Cikin kananan kaya. Ganinta yayi a kasa ba Alaman numfashi a tattareda ita.
Tsaki yaja yanufi fridge yadauko bottle water mai sanyi.
baiyi wata wata bah ya kwarara mata ajinkinta.
A matukar razane ta farfado. dagudu taban gajeshi tafara tafiya jikinta yana salubewa.
Dasauri tashige daki dabatasan ko na wayebah. Tareda rufe dakin. Hatake bindinta nakifi yabaiyana. Jan bindin tashigayi. Tashige toilet. Tashige cikin batting baff.. Hadeda Jan numfashi.
Cikin zafi rai kabir ya nufi dakin da yaga Amriya tashiga. Bubuga dakin yashiga yi. Saiyaga dakin a kulle.
dakarfi yasa kafanshi yafara buga kofan.
Faduwa gaban Amriya yayi. Saurin futowa tayi cikin ruwan. Tafara goge jikinta Amma saita kasa zama mutum.
Hawaye ne yafarabin fuskanta. Meyasa kuma nakasa zama mutum. Meyake faruwa danine. Bayanda amriya batayibah amma takasa zama mutum.
da mugun karfi kabir ya balla Koran.
Rasss gaban Amriya yabada. Nashiga uku shikenan tawa ta Kare.
shiga dakin kabir yayi. Yaga bata cikin dakin. Direct toilet yanufah.
Yace budemin kofan kafun ranki ya bacci. Amriya inbanda hawaye ba abunda takeyi. Gashi takasa zama mutum tarasa yanda zatayi rintse idonta tayi.
Bugu daya kabir yayi kofar ta balle. Zaro idoo kabir yayi, hatake gaban shi yafadi!.
*************************
MANAGE PAGE 馃憦馃徏馃憦馃徏FAN'S
MU HADU NEXT PAGE 馃尮馃尮
COMENT & SHARE PLEASE.......
ALKALAMIN 馃枈锔忦煐婏笍
BABY ISHA 馃尮馃尮馃尮
2/28/24, 22:05 - AISHA M.B (Baby isha): 馃尮BISSMILLAHI RAHAMI RAHIM 馃尮
ALJANAR RUWA CE 馃鈥嶁檧锔忦煂婐煂?
PAGE 1锔忊儯2锔忊儯
WRITTEN & DIRECTED BY BABY ISHA.
--------------------------
Gabanshi ne yafadi ganin Amriya tana numfashi sama sama Tsaki kabir yaja. Aikin banza kawai daukanta yayi chakk. Bai zarce ko ina da ita bah saikan gado. Kwantarda ita yayi dagana yayi fucewarsa.
Nannauyan Ajiyan zuciya Amriya tasauke tareda fadin Allah nagode mah. Dabakasa yaganin amatsayi Aljanar ruwa bah. Daya ganin na tabbata ta watakare.
Wai meyasa bana iya rama abunda yayimin, meyasa nake rabidashi bayan ba'a min na kyale. Damm gabanta yafadi. Tabbas sabida zobena dayake a hannunsa shiyasa nakasa aikata komai. Yazanyi kenen gash ina bukatar nashiga ruwa babba yanda zansamu saukin jikina.
Rintse ido tayi sbd yanda kanta kemata zugi da radadi. Tace tabbas Kalb Kai mugune. Saida zuciyata tacemin kada na taimake kah sanda kake kakarin mutuwa.
Amma haka Narcissus maka naceceka. Amma yau ni Dana ceceka din kake wahalar. Ba laifinka bane. Yanzu yazanyi nakarbi wannan zoben nakoma duniyata.
Nama fasa taimakonka awajan uwar shedanu zanyi tafiyata ne kawai idan nakarbi zoben .
Haka Amriya tacigaba da magana ita kadai. Bude kafar Kabir yayi. Hannu shi rikee da first Aid Box.
Ajewa yayi hakan table. Kallonta yayi hadeda ya mutse fuska cikin zuciyanshi yace kyakyawa amma ni baki munbah. daukoh wool da hydrogen yafara goge mata jinin dake zuba
Saida yagoge jinin tass sannan yakuma daukoh Wani wool din ya dangwala spirit Mai yawa yafara dandana mata fishiness da karfi.
Wani Azabeben kara Amriya tasaki. Buge bakin Kabir yayi. Yayi mata Alaman tayi shiru. Rufe bakinta Amriya tayi hawaye nabin fuskanta.
Bangaren su mom kam bakaramin tashi Hankalinsu yayi bah bakamar Khaleed dayake jin in wani habu yasami Amriya zai iya mutuwa.
Aunty Amarya mah hankalinta yayi matukar tashi. Ringing wayanta taji yanayi dauka tayi takara a kunnenta. Daga dayan bangaren taji ance. Maza ki hallara a fada yanzu.
Hana gama fadin haka haka kashe wayan. Maida kallonta tayi kan su nadirah wanda kanaganinsu kasan basua cikin yanayi Mai dadi.
Gyaran murya Aunty Amarya tayi tace kubani guri zan huta. Simi simi suka tashi tareda nufah part dinsu.
Aunty Amarya naganin sun futa tayi maza ta kulle kofan tareda shigewa daki tadauko bakaken kayanta da mask tasaka. Tafuce tatami boyeyen anya bama bakowane mutum ne agidan yasanda Hanyar bah.
Aunty Amarya bata zarce ko inabah sai fadan Lord lady. Durkushewa Aunty Amarya tayi tafara gaisheta kamar haka barkanki ranki shi dade. Uwar shedanu, da mayu. The lord of the whole universe, praise and worship most be given to you only.
Ya isahh Lord lady tafada a tsawace. Tashi aunty Amarya tayi ta tsaya a inda tasaba tsayuwa.
Magana uwar shedanu tafara kamar haka. Nashiga rudu, nashiga tunani cewar ya hakayi plan dinmu yake wargatsewa lokaci daya.
Tabbas akwai Yar leken asiri acikin wannan qungiyar. Tabbas akwai wacce take cin Amanar qungiyar uwar Shedanu
Demon lady. ,rasss gaban Aunty Amarya yafadi. Aunty Amarya ta asma da Na'am .
Inason kigano min wanda yake cin amanar wannan qungiyar.
Angama rankishi dade.
uwar shedanu tacigaba da fadin. Duk ranar da na gano da gsk wata ko wani na cin Amanar wannan qungiya. Na rantse da qungiyar devilish jininsa ne zai zamo sadaukarwa ga ruwan sha nah.
Monster. Yes lord lady. Inason ka sa yaranka suyimin kidnapping kabir gobe. Katambaye iyayenshi kadarorinsa na gidan marayu daya bude. Inkuma sukaki ka arbeshi har lahirah. Angama ranki shidade
Gaban Aunty Amarya ne yafadi jin za'ayi kiddnapp din kabir.
Alhj usnam yace. Ranki shi dade. Karkice na bujire magananki. Mai zai hana kawai idan. Sunki. A kyaleshi. Nikuma inada yarinya ZAINAB. Innace mata tadauki aiki a company sa tazama hannun damansa.baza ta bujire bah tunda nasan ta Dade Tana sonsa. Kinga abun zaizo mana da sauki. Yanda zata dunga kawomin bayanai hakan kudadensa da kadarorinsa.
Kinga daganan saimu kwashe komai.
Wannan shawarar nakawo amma inkinga baiyibah toh za'a iya kasheshin.
Shikenen na yarda da maganarkah. Amma zan tunatarda Kai kada tamana shirme. Inba haka bah. Zan hallakata.
Da yardan Allah komai zai tafi daidai.
Alhj usman yakara fadin Uwar shedanu gsk inajin tsoro hakan wannan budurwan datazo jiya tace zata hallaka mu.
Inbamuyi wasa bah kada Aje da gsk take zata hallaka mu idan bamu daina bibiyan rayuwan kabir bah.
A hassale uwar shedanu tatashi. Sauran yan qungiya naganin hakan suka durkushe taresa yimata sujjada. Suna bata hakuri.
Karya take, bata isah hallakani bah. Tabbas ba mutum bace . Dole saina gano a ina take. Kuma yanzu wasan yafara.
wannan shine. tanagama fadin haka tayi tafiyarta. suma sauran yan qungiyan suka watse.
Bangaren kabir kam. Saida yamata staff ya gyara mata fuska Dan kar aga shatin Mari a fuskanta. Tashi mutafi gida cewar kabir.
Kisameni a waje Dan bazan jira kibah.
Yana kaiwa nan yayi fucewarsa.
tabe baki Amriya tayi tareda fadin kaika sani mugu kawai. da A lokacinda zobena yana tareda nine dabaka Isah katabamin koda yatsata bah.
Tashi tayi. Wani mugun ciwon Mara taji yazomata. A daddafe tafara tafiya hannunta rikee da maranta Wanda yakemata mugun ciwo .
Saida taje daff dashi. Kawai tatafi luuuuu zata fadi. Saurin riketa kabir yayi yana Jan tsaki.
hadida zaunan da ita a gaban mota. whattt yafada. ganin yanda jikin shi yayi tsenin a jini. what's this rubbish. oh my god. Cikeda bakin ciki da takaici yace
keee bakida hankaline zaki batani da jini. kekinsan kina period bazaki iya killace kanki bah. this is embarrassing Wlh.
Cikeda rashin fahinta Amriya tace. Ni... Ban... Gane... Me.. Me.. Ka.. Ke.. Nu.. Fi.. Bah.
gigiza kanshi Kabir yayi yace wato raina min hankali zakiyi koh.
tsaki yaja yashige ciki. gidan. Yana shiga yanufi toilet. Saida ya yi wanka yakai so goma. Shinshina kanshi yayi yaji haryanzu yana karnin jini. . Saida ya hada sabulai. Wajan biyar. Sannan yacigaba da durza jikinsa kamar fatansa zata bare.
Yanagama wah. Yanufi wardrobe yasaka kananun kaya. Tareda gyara suman kanshi. Yasaka oiling lotion Mai kyau da kamshi.
Wajan turarema saida ya fesa wajan kala biyar. Sannan yafuto yanufi parkin space. Kallonta yayi jiyake kamar wani yana kara huramai wata wutan tsanar Amriya .
dauke kansa yayi daga kallonta. Tada motan yayi suka fuce daga gidan direct hospital yanufa.
parking yayi. yafuto daga cikin motan. ZAINAB dake tareda friends dinta zunzo wucewa ta hangoshi. Jikinta karkarwa tace kunga Sir kabir dream guy dina. Dole mah naje nayimai tayi soyayyata kafun lokaci yakure.
Daya daga cikin friends dinta tace amma bakya ganin Hf akan bai dace bah. Kinsan tsaff ,zai iya duzgaki agaban mutane.
murumushi zainab tayi tace ni yar Alhj usman za'a duzga. God for bid kudai kuzubah ido kugani.
gyara zaman mayafinta tayi Wanda Dashi gwara babu Dan komai najikinta anagani.
Tafara tafiya Tana lankwasa. Hartaje gabanshi. Excuse me handsome. Dago kanshi kabir yayi ya zubamata. Kallon sama dakasa yayi mata.tsaki yaja yace daman haryanzu hana samun lower class ladies bansani bah.
Magananshi bakaramin batawa zainab rai yayibah. Basarwa tayi tace. Sir kabir. Nice Yar gidan Alhj usman.
and so nace saime inke Yar gidansa ce hajiyeni yayi. Dazaki ce ke yargidan Alhj usman.
Am sorry for my words Sir amma wacece wannan. Kallon Amriya yayi. Yakuma maida kallonsa kanta yace me kika gani.
Zainab tace naga kuna tarene kamar ma'aurata. Is she your wife.
Exactly yesss she iss. And how is that your problem .
Wani kishi ne ya mamaye zuciyan zainab tace. Sorry butt.
Eh you banason nakarajin wannan banzan murya naki. Karki tunzurani aikata abunda raina baiso bah. Dan haka leave before i count three.
sir please kasaurareni dama daya kacal. Sir. kallonta yayi yace amma fah kinyi mugun raina min hankali. nayi miki kama da mazan da zan tsaya da ballagaza irinki ina mgn dasu.
Sir but you kn...... Batakarasa bah taji saukan Mari.
Amriya kam inbanda kallo ba abunda takeyi. Ita batasu takebah ta ciwo da radadin da maranta yake mata take.
how dare you am talking you are talking. did i resemble your mate.
dafe kuncinta zainab tayi zuciyanta namata kuna. Wani irin tsanan Amriya ya baibaye zuciyanta. Cikin ranta tace dukk sbd kee ya mareni na rantse hakanki zan fanshe marina.
Barnan yafada a tsawace. Saurin barin wajan zainab tayi. Tanufi inda kawayenta ke tsatsaye sai kwasan dariya suke.
maida kallonsa yayi kam Amriya yace kekuma tashi mushiga ciki. ba.. zan... iya... bah..
Cikeda baccin rai kabir yace baza ki iya bah toh sokike na goyaki kenan tsswm yaja tsaki. Dallah malama tashi duk kinbatamin seat da jini.
Tashi tayi suka nufi cikin hospital din.
wata nurse yasamu yayi mata bayani komai. rikee Amriya nurse dintayi tace kaje kawai zan kulada ita abunda hake bukata yanzu kaje pharmacy kasiyo pad dazatayi anfani.
What you mean mee. Naje nadiyo pad a big person like me. Impossible.
mikawa nurse kudi yayi wajan five thousand yace kekije kisiyo mata. Saurin karba nurse dintayi hannunta na karkarwa . Tace ok Sir. Fucewa yayi daga wajan. Yakai motan wajan wanke mota. Dan bazai iya cigaba da ganin wannan kazantan bah
shigar da Amriya nurse din tayi cikin room 2. Tace barana kiramiki doctor Amina saita dubaki. Daganan kidan gyara jikin ki kafun tazo. Toh Amriya tace. Futa nurse din tayi. Toilet Amriya tashiga tafara gyara jikinta. Saida tadau fifteen minutes kafun tadawo mutum daga Aljanar ruwa datake.
Doctor Amina ce tashigo hannunta rikee da kaya. Futowa Amriya tayi. Sharaff sukayi ido hudu da doctor Amina. Wani mugun faduwa gabane ya ziryarcesu gabadaya.
Amriya tace cikin ranta. Wannan bawanan matar bace da na buge bansanibah awajan kitso.
Tattaro nutsuwanta dct Amina tayi tace sannu yata yajikin Naki.
Da... Sau.. Ki.. Yauwa Ganshi inji mijin ki yace nabaki kisaka wannan kayan.. Amriya tace ba.. Mi.. Jina.. Bane.. kaninane... zaro ido Dct Amina tayi tace kani kuma ba yaya bah.
Amriya tace... bai.. Kai.. nakira.. shi... yaya.. bane.. shi.. yasa... nace kanina... murmushi dct Amina tayi. lck daya taji Amriya tashiga ranta sosai.
dct Amina tace inyaciki fah.. Tabe baki Amriya tayi tace.. Yaji... Din.. Mai... Zai... Iyayi.. Min.. Wanan.. Mug.... Batakarasa bah idanuwata suka sauka hakan na kabir Wanda ya tsaya fuska a murtuke hannusa rungume a kirjinsa.
Kurrrr kara cikinta yashigayi. Hannu na karkarwa ta karbi rigan hannu dct Amina tashige toilet.
murmushi Dct Amina tayi tace da Alama kanacin zalin wannan sister taka. Kalifah tana ganinkah ta rude.
Zama yayi kusada itah yace kyaleta dct zamu gamuda itane.
Ringing wayanta yafarayi dayawa tayi tareda yin sallama. Tace yusuf kafiye takura Wlh nacema idan ina duty kadaina kirana koh ban fadama bah.
Bangaren yusuf kam ya shagwabe fuska yace aba ammi kinsan bazan iyayin 1 hour banji muryanki bah.
Toh saikayi nika rabudani Wlh shiyasa mah nakeson babanka ya aurarda Kai kowa ya huta.
Hau ammi korata kikeyi kenan. Ba dolebah duk kabi ka addabi mutane kodan kasan kai kadai mukeda shiyasa kakeson samun hawan jini koh.
Noo ammi magana bazata kaimu har haka shikenan zandaina kiranki idan kina duty byeee adawo lfy.
Katse wayan tayi tareda fadin this boy bayaji Wlh .
Futowa amriya tayi cikin abaya pink wanda yayi matukar yimata kyau.
Yamushe fuska yayi tareda fadin inkingama kisameni awaje.
Yana kaiwanan yayi fucewarsa.
yauwa yata kinsa pad din. ehh... nasa... yauwa.. toh ka wannan diklophenic din kishashi da safe dakuma dare.
Godiya Amriya tayi mata daganan tafuce daga dakin.
Murmushi dct Amina tayi tace gsk she is beautiful.
Amriya na futa tanufi hanyar Motan tareda bude murfin no motan baya tashiga. Wani kallon bakida hankali yazuba mata yace. Wato ka drivern ki koh. Dallah futo kikoma gaba kafun nabata miki rai. Futowa Amriya tayi tashiga Hanan motan. Fucewa sukayi daga harabar hospital din suka nufi hanyar gida.
horn yayi hatake body guard sukashiga bude kofa. . su mom najin karan mota sukayo hanyar waje.
Parking yayi. Yafuto daga cikin motan futowa itama Amriya tayi. Su nadirah. Naganinta sukatafi da gudu suka rungumeta.
Kusada grandma zaibi yawuce tace zonan Mai kan giginya wato Kai harnakai intsaya agabanka kaki gaisheni toh fadamun ina kakai mun yar jikata.
Wajan su mom Amriya tanufah tareda gaishesu. Mom tace lfy mushiga ciki koh. Shiga ciki gabadayansu sukayi shiko gogon naku inbanda hura hanci ba abunda yakeyi...
Mom tace fadamin yata Mai kabir yayi miki dakuka futa dazu.
dago kanta Amriya tayi tadora hakan kabir harara ya watsa mata sauri dauke idonta tayi daga gareshi tace bako....mai. mun fu..tane yawo. shi...ne yake fada...min Abunda yayi...min ba...dai...dai ba..ne ku..ma inya...femai. shi...ne nace....mai naya...femai. Ya....kaini gu...rin siya...yya yasi...yamin wanan ka...yan.
Zaro ido gabadaya su Kalisat sukayi. Dan tabbas sunsa gabadaya abunda tafada karyane.
Grandma tace karyane Wlh wannan botoramin ne zai baki a hakuri AI Wlh koda AL qur'ani zaki daukoh ki min ratsuwa dashi bazan yardabah.
wannan yaron da bakin zuciyansa gareshi zai baki akuri karewanta man harda siyan kaya.
Su khaleed mah sunyi mamaki wai kabir yabawa mace hakuri
shima kabir yayi mamaki yanda ta rufamai asiri.
Murmushi Amriya tayi tace ku.. Yar.. Da.. Dani... Da.. Gsk.. Nake.
mom tace shikenan wuce daki. daddy su sadiq mah yayi fucewarsa daga gidan . Dad yace kowa zai iya tafiya.
su nadirah kam Bin Amriya sukayi hardakin Aunty Amarya. Kallonsu nadirah Aunty Amarya tayi tace kudan bamu guri zamuyi magana. Tashi gabadaya sukayi suka fuce daga dakin.
Amriya meyasa kikayi karya. Fashewa Amriya tayi da matsanancin kuka tace bazan iya fadabah Aunty Wlh bansan meyasa bah zuciyata bata iya laminta Inga hanayiwa Kalb fada. Shiyasa.
OK shikenen na fahimta ki kwatarda hankalinki.
amriya Akwai fah gagaruman Matsala . Share hawayenta Amriya tayi tace wane matsala. Uwar shedanu zata sa yaranta su sace kabir gobe .
Amriya tace Toni ina ruwana sukasheshi mah bazan kara taimakonsa bah Wlh.
Kitaimaka Amriya kekadai zaki iya dakatardasu daga Darian hakan. Amriya tace taya, taya zan iya dakatarda su. Zan yiwa mom dinshi dabara sainace mata banyarda da maganan kibah nacewa hakuri yabaki daya futardake.
Sainace mata tasa gobe kutafi wajan company sa tare yanda zamu tabbatar da cewa yabaki hakuri. Daganan kuma nasan dole yayarda kar hagane ba hakuri yabaki bah.
Ni bazanje bah. Su kasheshi din sukawo min zobena natafi duniyata.
Meee wanee zobee Aunty Amarya ta tambaya cikeda rashin fahimta Damm gaban Amriya yafadi .
*************************
MUJEDAI ZUWA FAN'S DOMIN JIN YANDA ZATA KAYA 馃尯馃尯馃尯
DA ALJANAR RUWA CE 馃鈥嶁檧锔忦煂婐煂?
COMENT & SHARE PLEASE 馃憦馃徏馃憦馃徏
DAGA ALKALAMIN 馃枈锔忦煐婏笍
BABY ISHA 馃尮馃尮馃尮
2/28/24, 22:05 - AISHA M.B (Baby isha): 馃尮BISSMILAHI RAHANI RAHIM 馃尮
ALJANAR RUWA CE 馃鈥嶁檧锔忦煂婐煂?
PAGE 1锔忊儯3锔忊儯.
WRITTEN & DIRECTED馃枈锔忦煐婏笍 BY BABY ISHA 鉁ㄢ湪
-------------------------------------------
Tashi Aunty Amarya tayi taje kusada Amriya Wanda tayi zuru zuru tana Kallonta.
Aunty Amarya tace wane duniya amriya zaki koma,