Header Ads
Showing 78001 words to 81000 words out of 106900 words

Chapter 27 - ALJANAR RUWA CE COMPLT BY ASHA M.B .txt

Ads the beginning of article before Image

Aisha MB   

28 May 2024

1073

Ads at the middle of Article

saimun hada su aure, domin akan takara mana zumunci


Nida Amina yar uwarta mun kasance masu kokari a class, yayin da ita bata da kokarin ko kadan, akan yasa muke yawan samu matsala da ita, take nuna k'ishin ta a bayyane, koda gasa ake ta makaranta toh nida Amina ne kawai ake kira gasa.


Amina itace hussainan ta. Amina ta kasance Mace mai hakuri da Kuma kawaici, Tana da farin jini sosai a makaranta, Duk inda Ta shiga mutane na yabon ta.
Ashe akan na bakan tawa Karima, kwatsam wata rana Aka aiko mana da sakon gayyata na makarantu wanda za'a fafata tsakanin dalibai.


Kamar yadda muka saba, a lokacin ne itama Karima tace tanason Shiga gasar da akeyi, Tana son ta nunawa duniya cewar itadin bah doluwa bace bah, abunda yar uwarta keyi zata iya yin finsa mah.


Malaman makaranta kuwa basu ja da akan bah, amma suka mata gargadin cewar indai ta bawa makaranta kunya toh za'a sallameta daga makarantar, cikin rashin tsoron abunda zaizo ya biyo baya Karima ta amince da Sharadin da malamai suka fada mata.


bayan nan, gabadaya makaranta muka hallarci wajan taron daliban da akeyi, yayin da akace Duk wacce taci za'a bata babban kyauta dakuma scholarship na makaranta.


Ni da Kuma Amina mun fafata Kuma munyi nasara, yayin da Karima kuwa ta bamu kunya a bainan jama'a, ganin hanata mata dariya yasa bakin ciki da kuncin ya dameta ta futa daga cikin hall din da gudu tana kuka.


Yayin da mu Kuma aka bamu kyautu tuka da Kuma scholarship, iya kyauta muka karba bamu karbi scholarship bah, akan bah karamin bawa mutanen wajan mamaki yayi bah, inda dalibai suke fatan su sami scholarship, amma mu mun samu munce bamua so, dalilin akan kuwa shine Karima,


Domin kada Karima taji Ba dadi akan yasa muka ki karba, bayan koma wan mu hostel, Karima ta daina mana magana, koh mun mata magana bata kula mu, saidai taita kula wasu kawayen banza marasa tarbiya, akan bah karamin damun yar uwata keyi bah,


Hana tsaka da aka, wani matashi Mai suna Habib Dan sarkin bauchi ya fada a soyayyar Amina, sosai masoyan nan suke shan soyayya, Wanda baki bazai iya masalta irin son da suke wa junan su bah,


Lokacin da muka rubuta WEAC din mu, muka futo da sakamako Mai kyau Dama mu a bangaren science muke nida Amina Ita Kuma Karima ART class, amma duda akan bata futo da sakamako Mai kyau bah.


Akan bah karamin bata ran mahaifin su yayi bah domin kuwa mahaifinsu yana da kudi, dukiya, da Kuma wadatar arziki. Amma ace yarsa bata da kokari koh kadan, cikin baccin rai kuwa, budar bakin mahaifin su keda wuya ya kirata da Mai kwakwalwar kifi, jin akan datayi yasa tun daga ranar ta dora tsanan duniya ta dora mana. Amma akan baisa ta bayyana mana bah.


Hana aka Habib yaje wajan Amina hira, daidai lokacin itama ta ganshi taji duk duniya babu Wanda takeso kamar shi,


Ni kuma a lokacin ne mahaifin ku yace yayi min miji nida Maryam, daga nan sai na dora karatu na a inda na tsaya ban musa bah Kuma na amince da maganarshi, saboda a lokaci Banida wani a raina,


Lokaci zuwa lokaci Habib ke zuwa gidansu Karima har wani sa'in yake futa damu shopping, Hana aka har labari yaje kunnen iyayen su, har sukace masa ya turo magabatan sa, jin akan bah karamin sanya shi farin ciki yayi bah,


yayin da aka ce itama Karima ta futo da miji. Jin akan da Karima tayi yasa ta bayyana wa kowa abunda ke cikin ranta, jin akan kuwa bah karamin bata ran mahaifiyar su mai suna Jamila yayi bah, da Kuma y'ay'an su Suleiman bah.


Amina tace tayi hakuri domin kuwa bazata iya sadaukar da soyayyar ta bah, ita kuwa Karima ta nuna mana cewar, komai ya wuce babu komai a zuciyar ta, ashe itadin munafuka ce.


Bayan wasu kwanaki Habib ya turo magabatan sa , yayinda aka tsaida auren Amina da Kuma Habib.


Ni kuma a lokacin an kusa bikin mu nida Maryam. A lokacin kuwa, Karima ta bijiro da kule kulen samarin, harta kawo min wani saurayi mai suna Harun, wai yana sona, ta karfi da yaji, Karima tasa na fada a soyayyar Harun,


Yayinda muke soyayya Cikeda burgewa, Harun, ya kasance masu matsakaicin karfine, amma akan bai hana ni k'in sonshi bah,


Ranar aure na kuwa, ta zuga ni wai mu gudu da Harun, ni kuwa nace mata gaskiya bazan iya butulci bah, kunyi mun abubuwa da dama, amma in rasa da abunda zan saka muku sai wannan.


Aka dai taita zuga ni, nace indai saboda soyayya zaisa na gudu toh saidai na hakura, data ga nak'i sauraron ta, ta shakamin abu a hanci na, cikin kankanin lokaci bacci yayi hawan gaba dani. Aka suka cincibe ni suka kaini daji batareda nasan inda kaina yake bah,


Bayan farfado wata, take fadamin cewar saita dau fansar abunda muka aikata mata nida Amina, lokacin ne Harun ke fadamin cewar bah sona yakeyi bah ita ta biyashi danya cimin zarafi Kuma nasa ahalin da suka yarda dani, su tsaneni, Suji kaff duniya babu ma yaudariya maciya amana sama dani,


Kuka kamm nasha shi Harna godewa Allah, Hana tsaka da aka, Harun ya bayyana mun soyayyar sa agareni, tareda cewar shin zan auresa, Babu bata lokaci na yarda muka daura aure nidashi, yayin da ya gina mana gida na masu rufin asiri,


Ashe a lokacin Karima ta dai photo na da Kuma Harun ran auren mu, ta tura muku, akan yasa kuka nuna baccin ranku akaina, rana bazata tashi ta fadi ba Tareda nayi kuka bah,


Hana aka naji labarin itama Amina an daura mata aure da Habib, murna sosai nayi shi, domin kuwa har naso zuwa inda gidan ta yake amma kuma bansan gidan ta bah. Ba yadda na iya, aka na hakura na fauwala wa Allah komai, domin shine Mai jikan bayinsa.


Babu bata lokaci, Harun ya neman mu makarantar Jami'a, na fara zuwa Harna karanci medicine, yayin da itama Amina abunda ta karanta kenen.


Hana aka mukaji labarin cewar Abba ya mutu bisa hatsarin mota daya gamu dashi, kuka mai cike da danasani nayi, saboda a ganina nice sanadiyar mutuwarsa .


Bayan lokaci ne Kuma naji labarin kayi aure ka auri Fatima. saboda kunya abunda na aikata bah Lallai ku yarda dani bah yasa nak'i zuwa auren.


Hana aka kwatsam watarana na fara amai mukaji asibity, hanan likitoci suke sanar mana da cewar ina dauke da cikin wata biyu.


Sosai mukayi murnan wannan cikin yayin da Haruna ya dora son duniya akaina har cikin yakai wata Tara.
Ganin muna rayuwa cikin farin ciki da qaunan juna, yasa Karima ta kuma dawowa cikin rayuwar mu, a wannan karan bah ita daya bane, su dayawa ne domin kuwa tayi joining yan kungiyan asiri .


Lokacin ta umarci mijina Harun da ya dunga mata aiki, shikuwa yace bazai taba aikata akan bah. Kuma yace da ita sai ya tona asirin ta a idon jama'a, ya dau Wayanshi Tareda kira police.


Karima na ganin akan ta harbe shi da buduga, ya fadi a wajan mutacce, daidai lokacin kuwa na kuda ya kamani.


Babu bata lokaci police zuka zo, suka kamata, aka kaita police station.


Ni Kuma a lokacin na Haifi dana, kuka nashashi Harna gode Allah, yayinda aka suturta harun aka kaishi gidansa na gaskiya.


Bayan shekaru biyu na gama makaranta na nayi NYSC na a garin Kano, yayinda akayi posting dina'a hospital, na Fara aiki


bayan wasu lokaci naji labarin ta futo daga cell, akan bah karamin tayar min da hankali yayi bah, domin kuwa bansani bah ko wannan futowar tata ya kasance wani gagarumar matsalan, cikin sa'a kuwa ta daina bibiyar rayuwa ta.


Hana aka na shirya Domin naje na nemi gafarar ku, zuwa na keda wuya naganta acikin gidan nan wai a matsayin matar aure, ganin aka bah karamin tayar min da hankali yayi bah, domin kuwa nasan da cewar bah alkhairy ne ya kawo ta wannan gidan bah.


Akan yasa na juya na tafi gida na cigaba da lallaba rayuwata da Kuma na dana. Ina nan duty na a hospital naji kira ya shigo bah bata lokaci, na d'aga Kiran tareda karawa a kunne na,


Muryar dana ji ne yayi matukar girgiza ni, muryar dana ji kuwa bata kowa bace illa na Amina, sosai Nayi murna Mara misaltuwa a ranar, mu ka taba hira, Kuma tace min zata dawo asibity da nake aiki.


Nadira tace kina nufin Doct Amina itace yar uwar Mom, Doct khadija ta bata amsa da fadin kwarai kuwa itace yar uwata, amma kuma har yau har gobe babu wani a tsakanin su dayasan cewa sudin yan uwa bane, domin kuwa, duk saida na bi hanyan danasan cewar Karima baza ta ga Amina bah, domin karta ganta.


Kamar yadda nake fada, bayan kwanaki aka kawo matar yahya, asibity zata haihu, yayinda iyaka Karima take na kuda, a taredai naga kun kawo su asibityn, ganin akan dana yi yasa nasa face mask ta yadda baza ku gane ni bace,


Na karbi haihuwar Fatima da Kuma na Karima, cikin rashin sa'a Kuwa, dan da Karima ya haifa ya ruga mu gidan gaskiya,


Shine sai Karima tamin barazana da d'ana, tace idan ban sauya yaron bah, na bata na Fatima saita kashe d'ana, jin akan yasa na dauki video a memory na, sannan na chanza danta da Kuma dan Fatima, yayinda ta kuma cemin, nace Fatima ta mutu, koh Kuma ta kashe dana, jin akan danayi bah karamin tsorata ni bah, amma ba yadda na iya aka na dauk'i wannan babbar kasadar, nace muku dan ku dakuma Fatima sun rasu.


A lokacin naga hankulan ku bah karamin tashi yayi bah, bayan na isa gida nai ta kuka da danasanin abunda na aikata a gareku. Tabbas ban muku adalci bah, Kuma banyi wa Fatima adalci bah, domin kuwa babu abunda Fatima tayi wa Karima amma saboda rashin imani irin na Karima ta sa na raba da da mahaifiya. Kuma har yau har gobe, ban sake hada ido da dana bah, bansani koh yana raye koh Kuma ta kashe shi bah.


Tana kaiwa nan ta fashe da wani matsanan cin kuka mai cin rai. Hada hannayen ta guri guda tayi tace, iya abunda nasani kenen dan Allah ina neman gafarku daku yafe min, dan Allah ku yafemin tabbas na aikata muku kuskure,


Jikin kowannen su ne yayi sanyi, Hawaye yafara gangaro wa a idanuwan Fatima, fatima tace ni na ruga dana yafe miki duniya da lahira.


Tashi su Nadira sukayi ,tareda rungume ta, Dad yace mun ruga damun yafe miki yanzu babu komai a zuciyoyin mu kinji kanwata.


Kuma insha Allahu Karima saita gurbi abunda ta shuka. Domin kuwa bata ci bullus bah. Amma shin meyasa take cewa mun ci mata dukiya, fansa zata dauka, doct khadija tace wannan Kuma ita zata bada amsa Domin ni kaina bansan me take nufi bah.


Dad yace toh amma shin Amina bata haihu bane har yau, Doct khadija tace ta haife danta Kuma saikuma karamar yarta amma bata kai shekara bah ta rasu.
Allah ya jikan ta, gabadaya suka amsa da Ameen.


Khalid yace yanzu ya zamuyi mu futa muje wajan Amriya Domin ta tashi Kabeer, Aunty amarya tace, inada wata hanya wanda bah kowa yasan da hanyar bah a gidan nan, domin ta hanyar nake bi nake zuwa kungiya,
Kamar hadin baki suka ce, kungiya Kuma!






????????????????


WANNAN NA KUNE FAN'S, ASHA RUWA LAFIYA.


COMMENT & SHARE PLS ?
ALKALAMIN ??
AISHA M.B
(BABY ISHA) ???










Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JYYV16dbYaX1dykLX7EE91




https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*??
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.??




ALJANAR RUWA CE ??♀???
PAGE 4??8????4??9??
WRITTEN & DIRECTED ?? BY
AISHA M.B??
(Baby isha)








--------------------------------------
Kwarai kuwa kungiya, nima ina daya daga cikin yan kungiyan asiri ,amma bah nashiga bane don cutar da al'umma, nashiga ne kawai Domin tseratar da rayukan ahalin nan, da Kuma na Kabir, so da dama tayi yinkurin kashe Kabir, amma Allah bai bata ikon yin akan bah.


Dan Allah karku yimin gurguwar fahimta, yanzu zaku iya bin nan hanyar Ba tareda kowa ya ganku bah, tashi su Khalid sukayi Tareda daukan mukullin mota,


Doct khadija tace me Kuma zakuyi da makullin mota, Khalid ya bata amsa da fadin, ai da mota zamuje, doct khadija tace toh kenen dai Baku shirya zuwa neman Amriyan bah gaskiya,


Kamar ya Khalid yafada, kamar dai yadda kaji, Baku shirya zuwa bah, ya za'a yi ace zakuje da mota, bayan kasan body guard dinnan na wakan sun zagaye gate baki daya, toh yanzu fadamin ta ina zaku futa da motan.


Sai a yanzu Khalid ya tuna da cewar tabbas akwai yan kungiyan Mom a wajan, sadiq yace toh yanzu a ina zamu je kenen?


Aunty amarya tace, abunda zakuyi shine ku tafi a napep, shine kwanciyar hankalin mu.


Tom shikenen bara mutafi, amma doct khadija zaki biyomu, koh saboda bamusan gidan bah, yes of course doct khadija ta Bashi amsa, tashi gabadayansu sukayi, inda sukayi musu fatan nasara daga bisani su ukun suka fuce daga cikin gidan.


Tafiyar su keda wuya, Mom ta banko cikin dak'in, a razane gabadayansu suka mike tareda ja da baya.


Kallon su Mom tayi tareda watsa musu banzan kallo tace, me kuke shirya wane, koh Kuma shirya yadda zaku tseratar da rayukan kune,


Nadira ta bata amsa da fadin, kwarai kuwa, idan mun tseratar da ran mu laifi ne? Koh kuwa akan ya shafe ki, buge mata baki Aunty amarya Tayi, tana mai fadin Nadira ki kiyaye ni, kada ki kuskure na karajin ki hanan,


Maida Kallon ta kan Mom aunty amarya tayi tace, kiyi hakuri Karima, kinsan har yanzu yarinta ne ke damun ta,


Murmushin mugunta Mom tayi tace, yarinta bah, toh shikenen Tunda yarinta ke damun ta, nima zan gwada salon yarintar tawa, Tana kaiwanan ta zaro wani zabgegen dorina, a hassale tayi kan Nadira da dorinan.


Su Abdul na ganin aka, suka nufi inda take tareda ririke ta, Grandma tace yauwa ku rike ta, shegiya annamimiya, munafuka, da sauri Adeef ya futa, ba'a fi mintuna bah, ya shigo da doguwar igiya.


Kwace kanta daga garesu mom ke sanyi amma ina akan ya cutura, daddaure tah sukayi, saida sukayi mata d'aurin rago, sannan suka rabuda ita. yayin da Grandma ta wafce dorinan daga hannun ta, tace


Wato ke nan uwar shedanu koh, bah uwar shedanu bah, in mah kece kakannin mayu da aljanu, wannan bai shafeni bah, munafuka mai hanci socket, bamu zaki daka bah toh ni barana nuna miki salon yadda ake jibgan karnuka da akuyoyi irin ki,


Tana kaiwanan, bata yi wata wata bah, ta fara shauda mata ajiki, ihuu Mom ta fasa, da sauri Amar ya toshe mata baki da zani, ya yinda yayi mata alama da hannunsa tayi shiru,


Tattaro karfin ta gabadaya Grandma tayi, ta fara zuba mata dorinan Ajiki bah kakkautawa, ihuu Mom keyi da iya karfin ta, yayin da takejin dorinan na Shiga har cikin kwakwal war ta da Jikin ta, cigaba da zuba mata dorinan Grandma tayi, tana mai fadin,


Bake uwar shedanu bah, toh yanzu ki ceci kanki a wajena,ai yau koh wallahi Mai cetan ki a wajena sai Allah.


Tausayin Mom ne ya Kama kowannen su na dak'in, Dad yace Mama ki rabu da ita kawai, Kibari Allah yayi ikonsa akanta,


Grandma tace, bazan barta bah, Tunda ita uwar shedanu ce, toh ta kira shedanun tah zuzo su ceceta a wajena,


Saida Grandma taga Mom ta cigata, sa'anan ta rabuda ita, tareda danna mata rankwashi akai,


gabadaya Mom ta zama abar tausayi, idanuwanta sunyi jajir kamar tsohuwar mayya. Kallon shi gabadaya tayi, yayin da take hayyana irin azabtar war da zata musu .




------------------------
Ammi bara naje nasha magani, naji kamar zazzabi nason kamani, Tom shikenen yusuf amma ka tabbatar kasha fah, Tom shikenen Ammi insha Allahu zansha. yinkurin tashi yusuf keyi amma ya kasa, inda a karshe yayi nasaran tashi,


Hatake jiri mai karfi ya dauke shi, luuu ya tafi tareda faduwa a wajan sumamme.
Innalillahi wa innahilahi rajihun! Ammi ta fada tareda nufan inda yusuf ke yashe a kasa tafara jijigashi, ganin koh motsi Bayayi, yasa ta kwalla wa baban yusuf kira,,


Cikin kankanin lokaci, baban yusuf ya bayyana a wajan, ganin yusuf a kwance bah alamun motsi a tattare dashi ga kuma Ammi Tana ta faman kuka, akan yasa yayi Saurin isa inda suke.


Amina meyafaru da yusuf? Ammi ta Bashi amsa da fadin wallahi bansani bah kawai muna Zaune yace min yanajin zazzabi, shine yace min Zaije ya shafa magani, ban hankara bah naga ya fadi, dan Allah kayi wani abun.


Jin kamar Hana kuka yasa Amriya futowa daga cikin daki, tareda nufan hanyar falo, abunda ta gani ne ya girgiza ta, da sauri ta nufi inda su Ammi suke, tana mai fadin, Ammi meyafaru? Tun daga abunda yafaru harkashe Ammi ta zayyane wa Amriya.


Kallon yusuf Amriya tayi tareda shafa kansa ta rintse idanuwan ta. Da sauri ta Bude idanuwan ta tace, yana bukatar taimakon gaggawa, ya ka mata mu kaishi asibity yanzu nan.


Mikewa Ammi tayi tareda hawa kan upstairs da sauri, ta dauko hijabin ta da kuma na Amriya. Daukan car key baban yusuf yayi, sanya hijabin Ammi tayi, sannan ta bawa Amriya itama hijabin, karba Amriya tayi tareda sanya wa ajikin ta.


Yinkurin daukan Yusuf babansa keyi amma ina akan ya cutura, wani dabara ne ya fadowa Amriya, saita hannun ta tayi daidai inda yake yashe, sannan tayi amfani da karfin ta na ALJANAR RUWA. ta Fara ju yashi,


Bah bata lokaci, yusuf yayi sama, hanyar waje Amriya tayi da gangar jikin sa, su Ammi naganin akan suka biyo bayansu,


Masu tsaron gidan na ganin aka, sukayo wajan da sauri, yayin da kowannen su ya tada mota, shigar da yusuf sukayi cikin mota, bah bata lokaci suma suka Shiga mota.


in da masu gadi suka bude musu kofar gate, daya bayan daya, motocin suka Fara futa har suka gama

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads