Showing 27001 words to 30000 words out of 188939 words
Chapter 10 - SAKAYYA Book 1 complete BY GARKUWA.txt
da nunawa Khausar matashin tace.
“Kinga wannan?”.
Kai Khausar ta gyaɗa.
Dije tace.
“Yaron Baffa Liman ne acikin Birni yake karatun sa”.
Murmushi Khausar tayi tace.
“Ayyah Allah Sarki yayi kyau".
Ya dubi Khausar da murmushi afuskarsa yace.
“Hi Sister how are you?”.
Ta mayar masa da martanin Murmushin tace.
“Am fine how's everyone?”.
“Fine Long time?".
“Thank God”.
Dije ta wani ɓata fuska Idanunta akan Khausar tace.
“Kuyi magana da yaren da zanji”.
Murmushi Khausar tayi tace.
“Ba wani magana muka yiba kawai gaisawa ne fa”.
“Toh”.
Dije tace sai kuma ta maida kallonta kan Matashin saurayin tace.
“Ayyah Yaya Abba nima ka koya min turancin”.
Murmushi yayi yace.
“Ba matsala zan koya miki Kinga ga wata ma zata koya miki”.
Hira suka cigaba dayi yayin da Sadik ya cigaba da tsintar ƙwoyaye wasu ma da yawa nata tsintar ƙwoyin ko wannensu da alama akwai inda ƙwan Zabbinsa ke tsayawa akwai waya da ake sakawa atsakanin waje-jen...
Baffa Jauro daya gama waya ya sauƙo tare da zuwa inda Khausar take ya riƙe hannunta suka fara tafiya sai kuma ya fara matsa hannun, Janye hannun tayi tace.
“Wallahi tsohon nan ka iya mugunta inka riƙe hannun mutum kaita matsewa da faratu ni banaso”.
Murmushi Baffa Jauro yayi tare da sake matse hannun!.
Ashagwaɓe tace.
“Wayyo na tuba ka sake”.
Sake mata hannun yayi yana dariya yace.
“Ohhh in dai baki daina yiwa Adda Nana rashin jiba, toh fa hakan zanyi ta matse mata ke, ga jiki ba ƙwari ba'ason wahala”.
Sai kuma ya juya ya dubi Dije yace.
“Dije”.
“Na'am Baba”.
Yace.
“Kishirya Gobe idan Allah ya kaimu da sassafe zaki ɗauke ta kuje kuyi tsar Nono tare”.
Kai Dije ta gyaɗa kana tace.
“Insha Allah zan ɗauke ta muje tare”.
Kallonsa Khausar tayi still hannunta na cikin nasa tace.
“Nide inda wuya bazan yiba”.
Dije tace.
“Ba wuya ai zamu baki man shanu ki shafawa yatsunki yanda zai yi santsi.
Kai ta gyaɗa tace.
“Toh shikenan ba damuwa zanje”.
Kallon Dije Sadik yayi tare da bata kwandon Ƙwan Zabbin yace.
“Ki tafi dashi".
Sannan ya juya ya cigaba da tafiya.
“Khausar kuwa murya ta ɗan ɗaga tace.
“Kaifa baza ka bimu bane”.
Girgiza Kai yayi yace.
“A'a ban ƙarasa ɗiba ba”.
Kai ta gyaɗa tace.
“Toh inde kazo ka kawo min nawa”.
“Toh”,Yace sannan suka juya suka tafi.
Suna shiga rugar suka nufi hanyar gidan Hajja Nana kasancewar duk gidan da zaka je seka wuce ta ƙofanta,sannan duk lokacin da taji motsi seta tambaya waye.
Sallama Dija tayi cikin ladani kana suka shiga, Hajja Nana dake cikin uwar ɗaka tace.
“Waye”.
Cike da ladabi Dije tace.
“Dije ce".
Haɓa Khausar ta riƙe tare da cewa.
“Ikon Allah duk mai wucewa saita tambayesa waye sai kace wata Traffick light?”.
Ƙasa da murya Dije tayi tace.
“Aaa ki bari Khausar kiyi ahankali kar taji”.
Khausar kuwa baki ta taɓe tace.
“Ai wannan abu yayi yawa wannan mulkin mallaka haka ake yi muku agarin nan”.
Daga ciki Hajja Nana tace.
“Dije keda waye naji kamar ana magana ƙasa-ƙasa?”.
Dije tace.
“Nida Khausar ce zamuje gida kai saƙo ne ƙwoyi muka kawo”.
Ita kuwa Hajja Nana cewa tayi.
“Toh shikenan”.
Ajiyar zuciya Dije ta sauƙe sannan suka fice.
Lokacin da suka fita makiyaya sun fara dawowa daga kiwo sannan sanyin magriba na sake sauƙa sanyin ya fara yawa ahaka suka isa gidansu Dije Khausar sai lumahe ido take.
Suna isa suka ajiye Ƙwoyin.
Dije na ƙoƙarin shiga ɗaki Khausar da Idanunta suka sake lumshewa tace.
“Dije muje ki rakani ɗaukan Sweater na sanyi nake ji sosai”.
Kai Dije ta gyaɗa sannan suka fice kallon garin Khausar tayi ko ina baƙi ba alamar hasken wutar lantarki ta dubi Khausar tace.
“Wai kam garin nan baku da wuta ne?,tun da nazo banga ƙyallin wuta ko sau ɗaya ba?”.
Kai Khausar ta gyaɗa tace.
“Eh babu amma ana tada Generator”.
Khausar kuwa hankalin tane ya tashi jin babu wuta garin!.
Ganin yanda tayi yasa Dije sakin murmushi tace.
“Kada ki damu kinga Yaya Abba shike tada Generator sannan yake sa kawa mutane Caji kuma aƙofar gidan Hajja Generator yake akwai ɗan haske kaɗan koda ba farin wata, bare kuma in akwai farin wata rana zakiga garin”.
Sai asannan Khausar ta ɗan saki ajiyar zuciya dan Allah ya sani tana tsoron duhu.
Bakinsu ɗauke da sallama suka shiga gidan shigarsu yayi dai-dai da kiran Sallar Magriba da akayi.
A tsakar gida suka samu Hajja Nana na alwala, kallonsu tayi tace.
“Kuzo kuyi alwala kuyi Sallah”.
Kallon ta Khausar tayi tace.
“Ni gaskiya sanyi nake ji yanzu ma rigar sanyi na nazo ɗauko kuma asamar min ruwan zafi dashi zanyi alwala”.
Harara Hajja Nana ta watsa mata kafin tace.
“Wa zai samar miki ruwan zafi?,Kina yarinya ƙarama yau har wani sanyi kirki akeyi! da har zaki nemi ruwan zafi”.
Bakinta ta tura amma ba tace komaiba.
Dije ce tace.
“Muje gidanmu akwai ruwan zafi sai kiyi acan”.
Kai Khausar ta gyaɗa da faɗin.
“Toh shikenan”
Sannan tashiga ɗakin Hajja Nana kasancewar akwai hasken lanta da aka kunna inda trolley ta yake ta nufa ta buɗe tare da ɗaukar Sweater ta sannan ta rufe trolley juyawar da za tayi Idanunta suka sauƙa akan kuliya (Mage) dake kwance akan ɗaya daga cikin gadon Hajja Nana kasancewar gado biyu ne aɗakin sai kuma ɗan shirge-shigen ta na Tsoffin ruga.
Cikin matsananci tashin hankali da ruɗu mara misaltuwa daya bayyana afuskarta take faɗin.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n!!,Hasbunallahu!!!, wani'imal wakin Astagfirullah wa'atubu ilaik!!!”.
Aruɗe Dije ta shiga ɗakin tana cewa.
“Lafiya Khausar meye faru?”.
Aruɗe Khausar ke yarfe hannunta takamar wacce ta ƙone duk jikinta na rawa takasa furta komai numfashinta na wani irin fusga na tsananin tsoro da tashin hankali, da ƙyar ta iya furta.
“Kuliya”.
Sai asannan Dije ta lura da kuliyar da har zuwa lokacin ke kwance akan gadon Hajja Nana.
Ita kuwa Hajja Nana wani dogon numfashi taja.
Dan da kusan mutuwar zaune tayi dan jin irin karajin da Khausar ɗin tayi.
Ita kuwa Dija hannu tasa tashiga koran kuliyar.
Daga can waje Hajja Nana ke cewa.
“Kuliyar take wa wannan Ihun? zata kasheni tun kwanana bai ƙareba”.
Ina ita kam Khausar bata san sunayi ba, har zuwa yanzu tsalle takeyi a tsakiyar ɗakin tana yarfa hannunta tare da furta duk addu'ar da tazo bakin, istagfari takeyi ba ƙaƙƙautawa.
A gigice Dije ta fitar da kuliyar tana mai cewa.
“Khausar ki nitsu ya fita, na koreshi, kuliyar Goggo Hajja cefa.
Cikin tsananin tsoro da rawar jiki cike da gigita,
Ta fito cikin ɗakin Hajja Nana ta nufi gidan Baffa Jauro tana cigaba da faɗin.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n
Ya Allah na tuba ka yafe min”.
Yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ke rawa na tsananin tsoratan da tayi.
Jin shiganta Aruɗe yasa Goggo Nanne fitowa daga ɗaki wato Mahaifiyar Dije.
Matsawa kusa da Khausar tayi ta riƙe Hannunta tace.
“Lafiya”.
Asanyaye Dije tace.
“Kuliya take tsoro taga kuliyar Goggo
Hajjs ce take haka”.
Cike da tausayinta Goggo Nanne tace.
“Ayyah Subhanallah ki kwantar da hankalinki nan babu kuliya kar ki damu Khausar ki kwantar da hankalinki ki nutsu kinji?”.
Kasa furta komai Khausar tayi sai Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n da take yi aƙasan ranta.
Addu'a Goggo Nanne tashiga tofa mata kafin ta samu hankalinta ya dawo jikinta.
Jauro daya fito daga banɗaki yana alwala yace.
“Yau kuliya ce haka kamar wanda taga kura haka?”.
Ya faɗa yana kallon yanda tsananin razana ya bayyana afuskarta.
Juyawa yayi yana kallon Goggo Nanne yace.
“Lalle wannan baƙunta akwai saɓani a cikinsa. Ita Addah Hajja ba zata iya rayuwa babu kuliya ba ita kuma wannan ga tsoron kuliya”.
Tana sakin ajiyar zuciya tace.
“Nide bazan sake shiga ɗakinta ba shegen ɗaki ga tarukuce ga duhu sannan ga kuliya wannan ɗakin har macizai za asamu acikinsa bazan sake shiga ɗakinta ba”.
Murmushi Goggo Nanne tayi tace.
“Ki kwantar da hankalinki kada ki damu tashi kiyi alwala ga ruwan zafi abuta”.
Batace komai ba ta miƙe ta ɗauki butar ta zaga bayi sannan ta fito tayi alwala ɗakin Goggo Nanne suka shiga da Dije cikin ɗakin duhu.
Araunane Khausar tace.
“Daƙin duhu ni gani nake ma ko ina akwai kuliya”.
Dafa kafaɗar ta Dije tayi tace.
“ki kwantar da hankalinki nan babu kuliya”.
Ta ƙare mgnar tana kunna lantansu mai ɗan karen haske,
Kai kawai ta jinjina tare da sauƙe ajiyar zuciya ganin hasken, sannan ta tada sallah suka idar da Sallah maghariba Khausar kuwa jingina bayanta da jikin bango tayi ta fara addu'a.
Dije kuwa miƙewa tayi zata fita, Kallon ta Khausar tayi tace.
“Ina kuma zaki je?”.
Juyawa Dije tayi ta fuskance ta tace.
“Zanje in dafa mana ƙwoyin da kika ce kina so ne”.
“A'a kibari ba da fawa zamuyi ba soyawa zamuyi ina akwai attaruhu da albasa da kuma maggi?”.
Kai Dije ta gyaɗa tace.
“Eh akwai”.
“Ok to kibari sai munyi Azkhar”.
“Toh”,Dije tace.Sannan ta dawo ta zauna suka cigaba da yin Azkhar ɗin Khausar nayi da ƙarfi Dije na binta wani ta iya wani kuma bata iya ba sai Khausar ta tsaya ta gyara mata suna zaune har akira Isha'i suka Idar...
GEMBILA
Anutse Momy ta gama shirin baccinta bayan tayi addu'a sai kuma ta lumshe Idanunta ahankali ta sake buɗesu ta juya kwanciyar ta daga hagu zuwa dama sai kuma ta tashi ta zauna baki ɗaya kewan Khausar ɗin ta ke damunta acikin yini ɗaya da bata kusa da ita se taji kamar wata tayi ba tare da ita ba gashi basu da network bare ta kira taji muryanta.
Jin ƙaran Knowking ɗin ƙofa yasa Momy gyara zamanta kana ta bada izinin shiga,Anutse Haiydar ya shigo bakinsa ɗauke da Sallama kana ya zauna kusa da Momy.
Murmushi Mommy tayi tace.
“Haiydar lafiya ko kana bukatar wani abu?”.
Kai ya girgiza yace.
“Momy wallahi yau gidan nan ba daɗi da Addah Khausi bata nan”.
Murmushi Momy tayi cike da ƙaunar 'ya'yan nata da kuma yanda suke nunawa juna kulawa tace.
“Yau kuma?,Ko da yake dama haka kuke bakwa shiri sannan bakwa san rabuwa da juna”.
Fuska ya Marerece kafin yace.
“Allah yau gidan babu daɗi yau tunda gari Ya waye babu wanda yace min Haiydar kar kayi kaza, Haiydar zo in aikeka, Haiydar bakaji, Haiydar karenani, Haiydar kada fa kaci komai wurinsu Umma, Haiydar ban girme ka bane kam wai da in na saka abu bazakayi ba, Yau duk babu wanda ya faɗa min haka nayi missing ɗinta! Sosai wlh Momy Ina son Adda Khausi”.
Murmushi mai cike da shauƙi Momy tayi tare da zuba musu ido.
Raudat da shigowarta kenan ta Shagwaɓe fuska tace.
“Wallahi nima nayi kewarta Mommy yaukam tare zamu kwana ko?”.
Janyo hannunta Momy tayi tace.
“Autanah ba dole ba yau In kwana dake tunda Addah Khausar bata nan”.
Haiydar ne ya sake kallon Momy cikin yanayin kewar 'yar uwarsa yace.
“Momy dan Allah ki kira kice ta dawo munyi missing ɗin ta”.
Ramadan da Raudat suma sukayi saurin cewa.
“Please Momy ki kira”.
Kai Momy ta girgiza tace.
“Basu da network sai dai idan sunje wajen bishiyar ƙare magarka sun kira”.
Ramadan yace.
“Toh yanzu Mommy Gobe wa zai Miki shara?,da wanke-wanke da kuma gyaran falo?”.
Murmushi Momy tayi tana shafa kansa tace.
“Zanyi ƙoƙari nayi da kaina”.
Zare Ido Ramadan yayi yace.
“To wallahi Momy aɗauko Miki Addah Khausi yafi Miki gidan babu daɗi idan bata nan”.
Murmushi tayi tace.
“Toh”,Da haka hiran yazo ƙarshe Haiydar ya miƙe kana ya ɗauki Ramadan suka tafi ɗakinsu wanda zai ka fita falon Momy ƙofar nasu na jere da ƙofar falonta,
ita kuma Raudat gadon ta hau ta kwanta gefen Momyn.
Acan ɓangaren su Moddibo kuwa.
Zaune yake Atsarerren falonsa da yagaji da tsaruwa kana yana fitar da sihirtaccen ƙamshi mai masifar daɗin shaƙa.
Yayin da M Jameel ke kwance akan 3sitter da waya maƙale akunnensa, Anutse Moddibo ya juya ya zuba masa Idanunsa tare tsarasa da su, still wayan yake Amsawa ɗauke kansa yayi ya cigaba da operating system ɗin sa kana ahankali ya sake maida Kallonsa kan M Jameel still wayar ne maƙale akunnensa.
Cikin ga jiyawa da wayar da yake yi Moddibo ya zuba masa idanunsa tare da motsa laɓɓansa da suka sake yin pinch kana suka tattare saboda tsananin sanyi da akeyi yace.
“Wai kai da wa kake yin wayar?”.
Gyaɗa masa kai M Jameel yayi tare da juya hannunsa alamar ya kusa gamawa.
Ganin haka yasa Moddibo maida hankalinsa kan system ɗin sa yana cigaba da duba muhimman saƙonnin da suke shigo masa.
Wayarsa dake gefen Centre table ne yayi ƙara hannu yasa ya ɗaga nan yaga sunan Abba na yawo a screen ɗin wato Abban M Jameel.
Cikin han zari yayi picking call ɗin kana yace.
“Assalamu alaikum Abba Barka da dare”.
Daga ɓangaren Abba yace.
“Barka dai Moddibo ya gida ya kuma ɗalibai?”.
“Lafiya lau Alhamdulillah Abba”.
“Masha Allah kana tare da Hassan ɗinna ka ne?”.
Murmushi Moddibo yayi wanda ke sake fitar da ainihin kyawun fuskarsa yace.
“Eh Abba muna tare waya yake tun ɗazu nayi zaton ma da kai yake yin wayar”.
Abba yace.
“Aina kira wayarsa naji Line busy shiyasa nace bari na kira ka naga dare yayi bai dawo ba za'a rufe ƙofar gida”.
Murmushi Moddibo yayi yace.
“Ayyah Abba yau kam abarshi mu kwana tare gashi naga alamun Agajiye yake bacci ma yake ji”.
Kai Abba ya gyaɗa yace.
“Toh shikenan Moddibo ayi bacci lafiya Allah ya tashe mu lafiya amma gobe da safe kuzo ina son ganin ku”.
Kai Moddibo ya gyaɗa cike da mutuntaka yace.
“Toh insha Allah Abbah”.
Kana ya katse kiran.
kallon M Jameel yayi sai kuma ya ajiye System dake kan ƙafarsa ya miƙe ya isa inda M Jameel yake yasa hannu ya cire wayar daga kunnensa ya duba screen ɗin sai yaga number ba suna saidai aƙasan Number ansa Bahrain wato ƙasan Bahrain.
Kallon M Jameel yayi yace.
“Ooo kaida Jalaludeen ne dama?”.
Kai M Jameel ya gyaɗa yace.
“Eh shi ya hana ince da kai dashi nake waya”.
Murmushi M Jameel yayi yace.
“Yayi kyau”.
Jalaludeen abokinsa ne tare sukayi karatu a Jami'atul Madina asalin Balarabe Bahrain ne...
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe yace.
“Abba ya kira yace baka koma ba har dare yayi sai nace zamu kwana tare yace gobe yana son ganinmu”.
Kai M Jameel ya gyaɗa da faɗin.
“Allah ya kaimu”.
“Ameen”.
Moddibo ya amsa tare da kallon M Jameel yace.
Bacci na keji zanje nayi wanka”.
Zare Ido M Jameel yayi yana kallon Moddibo yace.
“Wallahi inba cikin kashi na faɗa yanzu ba ba zanyi wanka ba yanda ake tsuga wannan sanyi agarin nan.
Kai Moddibo ya girgiza ba tare da yace komai ba ya wuce Bedroom.
wanka yayi da ruwa mai ɗumi, kana yayi shirin bacci.
Washe gari, da safe bayan sun dawo daga masallaci sashen Innayi suka nufa lokacin da suka shiga tana zaune kan darduma tana lazimi M Jameel ya zauna kusa da ita tare da riƙo tafin hannunta yace.
“Barka da safiya tsohuwa mai ran ƙarfe!”.
Murmushin fuskarta ta faɗaɗa tare da damƙe hannunsa dake cikin nata tace.
“Jameel Ubangiji Allah ya Albarkanci rayuwarku”.
Ya amsa da.
”Ameen Innayi”.
Shi kuwa Moddibo kusa da ita ya matsa ya ɗaura kansa akafaɗarta yana mai lumshe idanunsa ahankali yace.
“Barka da safiya Innayi”.
Hannunta tasa ta shafa fuskarsa tare da cewa.
“Fatan ka tashi lafiya ya ƙoƙari?”.
Ya amsa da. “Alhamdulillah” sai kuma ya miƙe tare da kallon M Jameel da still hannunsa ke cikin na Innayi yace.
“Mu je ko”.
Bai jira cewarsa ba ya fice daga sashen nata kana ya nufi nasa yana shiga kai tsaye Bedroom ya wuce ya cire naɗin Hiramin dake wuyan sa da kuma jallabiyar.
Kai ya shiga bathroom Masha Allah Komai na cikin toilet wanka ya fesa kana ya fito bakinsa ɗauke da addu'a
“Gufra naka”.Alokacin daya ziro ƙafarsa ta dama zuwa cikin Bedroom ɗin ya fito M Jameel kuwa jin ƙamshin sabulun wankan da kuma tularensa yasa ya ɗago kai sai kuma ya miƙe ya shiga toilet ɗin.
Shi kuwa Moddibo zama yayi agaban dressing mirrow ya shafa mayukan sa tare da taje yalwataccen sumarsa kana ya miƙe ya buɗe durowarsa
Masha Allah kayane aciki masu uban yawa fannin jallabiya da ban fannin yaduka da ban haka zalika fannin ƙananun kaya daban duk da cewa bai fiye amfani dasu ba yana tsaye awajen har M Jameel ya fito daga wanka bai ɗauki komai ba.
Murmushi m Jameel yayi tare da nufar jikin durowar yana cewa.
“Nasan koda zaka kwana nan ba zaka taɓa cire kayan da zamu sanya ba kai de inba jallabiya ba baka ganewa ko wani irin kaya”.
Moddibo kuwa murmushi yayi Aransa yana jinjinawa M Jameel yanda yake iya fahimtar komai nasa koda kuwa ƙwaƙa-ƙwaran motsi yayi yasan me yake nufi...
M Jameel kuwa Wani boyel Sky blue mai gidan dara-dara ya ciro musu tare da boxer da kuma singlet Fari ƙal.
Kallon Moddibo yayi tare da miƙa masa.
Murmushi Moddibo yayi tare da karɓa yana kallon kayan amma bai ce komai ba sai ya juya ya kimtsa.
Masha Allah wani irin kyau na musamman Moddibo yayi acikin kayan kalar shigar sai ta kasance tamkar kalar sararin samaniya ƙirjinsa na ƙiran jarumtaka ya bayyana acikin rigar kana yalwataccen sumar kansa ya kwanta luf yana sheƙi,Anutse ya juya wajen M Jameel dake miƙo masa takalmi da hula kalar sky blue Masha Allah m Jameel ma sosai Yayi kyau acikin kayan sai suka kasance tamkar tagwaye masu tsananin ƙaunar junansu.
Atare suka fice sashen Innayi suka nufa tun daga farfajiyar tsakar gidan Moddibo ya lumshe idanunsa yana jinjinawa tsaftar Kakar tasa har sanda suka isa ƙofanta inda sanyayyan ƙamshi turaren wuta ke tashi.
Ganinsu atare yasa ta sakar musu da murmushi atare suka shiga ɗakin suka zauna.
Ta dubesu cikin ƙaunarsu tace.
“Ubangiji Allah ya Albarkanci rayuwar ku Allah yasanya farin ciki acikin rayuwarku Ubangiji ya tsareku da dukkan sharrin mai sharri”.
Cikin jin daɗin addu'ar da take musu ako yaushe suka amsa da.
“Ameen Innayi”.
Innayi kuwa miƙewa tayi ta haɗo musu tea mai zafin gaske saboda sanyin da akeyi sosai amsa sukayi.
A hankali Modibbo ya ɗan zuƙan tea ɗin ahankali har ya Ida shanyewa zuwa lokacin tuni M Jameel ya shanye nasa.
Yana ƙoƙarin ajiye Mug ɗin yaga M Jameel ya tsaresa da ido Harara Moddibo ya watsa masa shikuma saiya sakar masa da murmushi.
Kallon Innayi Moddibo yayi yace.
“Zamu je gaida Abba”.
Jinjina kai Innayi tayi tace.
“Idan kunje ku gaishe min dashi”.
Moddibo na miƙewa yace.
“Zaiji insha Allah”.
Sannan suka fice.
Suna fita suka nufi inda mota ke ajiye M Jameel ne ya buɗe gefen Driver ya shiga yayin da Moddibo ya shiga mazaunin mai zaman banza ahankali M Jameel yayiwa motar key suna isa gate ɗin Moddibo ya fita ya buɗe musu gate sannan M Jameel ya cinna hancin motar yafita saida Moddibo ya sake rufe gate ɗin kafin ya koma cikin motar M Jameel ya tayar suka bar unguwar.
Anutse M Jameel ya dubi Moddibo da idanunsa ke lumshe yace.
“Anma aikin makarantar nan zai yi kyau domin masu aikin sun san makamar aikinsu”.
Shi kuwa Moddibo kai ya gyaɗa da faɗin.
“Sosai Insha Allah”.
Tafiyar Mintuna Kaɗan sukayi suka isa gidansu M Jameel Hon yayi mai gadin ya taho da sauri ya buɗe musu tamfatsetsen gate din.
Wow Masha Allah babban gida ne wanda yake ɗauke da Sashe huɗu sai kuma BQ da kuma wajen ajiye motoci kamar takwas zuwa goma sai ɗakin mai gadi cikin gidan akwai shuke-shuke saida