Showing 117001 words to 120000 words out of 188939 words
Chapter 40 - SAKAYYA Book 1 complete BY GARKUWA.txt
dogon numfashi kana tace.
“Khausar da kece zaki ɓace fa. Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n”.
Khausar kuwa da jikinta yake rawan jitayi Idanunta sun ciko da hawaye cike da alhini tace.
“Asma'u mun shiga uku”.
Cike da rawan jiki suka ƙarasa gida kai tsaye ɗakin Khausar suka nufa tare da zama a ƙasa Capet ɗin duk sunyi zuru-zuru dasu kallo ɗaya zaka musu kasan cewa suna cikin ɗimuwa da tashin hankali mara misaltuwa.
Cikin rawan murya Khausar ta kalli Asma'u tare da cewa.
“To yanzu kam Uncle Naseer me yake nufi dani? Dama tsafi zaiyi dani, kenan Uncle Naseer ma tsafi ne Asma'u? ba kingani ba dama ni sam ban yarda da shiba, tsoronsu nake dama Gimbiya Dadu ya take bare kuma ƙanwarta mun shiga uku dama tsafi zaiyi dani Asma'u shikenan da kashe ni suke sonyi?”.
Cikin raunin murya Asma'u tace.
“Khausar wannan abin ya gigita ni na rasa ta yanda zan fassara shi”.
Ta gumi sukayi yayin da zuciyarsu ta cigaba da bugawa tsoro da tashin hankali ya bayyana atare dasu lokacin ɗaya zazzaɓi ya fara dirarwa Khsusar.
Ba jimawa Mommy ta dawo kai tsaye ɗakin Khausar ta shiga tana cewa.
“Ohhh Allah mai iko an duba fa ƙasa da sama babu ragon nan babu dalilinsa an duba ko ina babu shi ya ɓace!”.
Murya na rawa Asma'u tace.
“Mommy muma fa mun gansu”.
Mommy kuwa ahankali ta maida kallonta kan Khausar da jikinta ke rawa duk ta ruɗe cike da kulawa tace.
“Khausar ya dai?”.
Kuka Khausar ta fashe dashi tare da yarfe hannu kana tace.
“Mommy zan faɗa miki Mommy zan faɗi gaskiya”.
Kallon Mamaki Mommy tayi mata kana tace.
“Meya faru Khausar?”.
Cikin kuka sosai Khausar tace.
“Allah Mommy Zan faɗi”.
Zama Mommy tayi gefensu kana tace.
“Wai meke faruwa ne Asma'u”.
Cikin ƙoƙarin tsaida hawayen Khausar ta riƙe hannun Mommy acikin nata, kana ta zayyane mata duk yanda sukayi da Naseer da kuma shawarar da Asma'u ta bata sannan ta ɗaura da cewa.
“Mommy kuma nice ɗazun na dandala ƙyallen akan wuyan ragon, har muka ji tsoro kar Baba mai gadi ya ganmu kuma Allah wanda na shafawa ƙyellen ne ya ɓace”.
Aruɗe Mommy ta saki salati tare da sanar da ubangiji.
_“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n. Hasbunallahu wani'imal wakil. La'ilah ha Illah anta subhanaka Inni kuntu Minal Zhalimin. Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan minha_. Ohh Khausar am nashiga uku wannan rayuwa har ina Khausar kin tabbatar?”.
Kai ta gyaɗa tare da faɗin.
“Wallahi tallahi Mommy da gaske ne”.
Ta faɗa tare da cusa hannunta ƙarƙashin gado ta ciro mata ƙyallen data ajiye da niyyar idan Naseer yazo zata bashi”.
Cikin raunin murya tace.
“Mommy kingani Mommy kin gani ko wallahi shine ƙyallen”.
Jinjina kai Mommy tayi tare da kallon ƙyallen da ƙamshinsa ke bugun kanta kana tace.
“Nashiga Uku ni Aysha wannan masifa har ina?”.
Asma'u kuwa ta gumi tayi ganin abin take tamkar almara.
Khausar na share hawaye tace.
“Mommy ina dai yanzu kin gani kinga zahiri Mommy inaga yanzu kam zaki iya yarda su Mayu neko?”.
Girgiza kai Mommy tayi cike da jimami da kuma al'ajabi ta kalli Khausar tare da cewa.
“Toh su sukayi ko shi Allah am nashiga uku ba'a shaidar halin ɗan mutum”.
Girgiza kai Asma'u tayi kana tace.
“Nikam wallahi Uncle Naseer ya bani Mamaki duk da rawan kansa ban taɓa zaton zai aikata irin wannan abin ba”.
Ta gumi Khausar tayi duk abin duniya ya isheta Hausawa sunyi gaskiya da suka ce Mutum mugun Icce.
Ganin yanda suka ruɗe da al'amari yasa Mommy dai-dai ta nutsuwarta tare da cewa.
“Kar ku damu ku cigaba da addu'a domin addu'a takobin mumunice, sannan kada ku faɗa wa kowa wannan maganar ya zama sirri atsakanin mu”.
Sai kuma ta maida kallonta kan Asma'u kana tace.
“Asma'u Allah ya miki al'barka, kin cika ƙawar kirki duk inda ake neman ƙawar arziki kin kai.
Allah Ubangiji ya Al'barkanci rayuwar ku ya kuma kare ku aduk inda kuke”.
Haɗa baki sukayi wajen faɗin.
“Ameen”.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe kana tace.
“Wannan magana ya zama sirri atsakanin mu, kada ku fadawa kowa daga. Ni sai ku sai kuma Ubangijin daya halluccemu shi kuma Naseer zamu ga manufarsa.
Za muga iya gudun ruwansa sannan daga yau Khausar koda ya kira ki baza ki sake zuwa inda yake ba ko dai kina son shi!?”.
Zaro ido Khausar tayi cikin sauri ta shiga yarfe hannun tare da Girgiza kai kana tace.
“Allah Mommy bana sonshi, na tsane shi bani bashi har abada, me zanyi da matsafi ni dai bana sonshi Wallahi bana sonshi”.
Kai Mommy ta gyaɗa tare da kallon su kana tace.
“Toh shikenan ki kwantar da hankalin Allah ya tsare ku ya muku zaɓi da maza na gari, wannan ma ai addu'a ce tasa asirinsa ya tonu Allah ya ƙara tsaremu baki ɗaya ku kara riƙo da addu'a in sha Allah duk sharrin mai sherri sai dai yaga gadon bayanmu”.
Atare suka amsa da.
“Ameen”.
Haka dai akayi suna aka watse kowa na al'ajabi da ta'ajjadin ɓacewar ragon suna.
Acan gidansu Moddibo kuwa M Jameel zaune tare da Innayi Moddibo kuwa na tare da Malam Arɗo bai dawo ba.
Anutse M Jameel ya ɗago kansa tare da kallon Innayi dake zaune ta tanƙwashe ƙafafunta cikin sanyin murya yace.
“Innayi”.
Ahankali ta ɗago kanta tare da cewa.
“Na'am”.
Ajiyar zuciya M Jameel ya sauƙe kana yace.
“Innayi ni ko badan kar kice ina bincikar ki da tuhumar kiba.
Da zance da Allah Innayi ina ne asalin ƙasar ku tunda nan dai garin naji labarin zuwa kuka yi dan Allah Innayi ki faɗa min inane asalin garinku sannan, wai kwata-kwata mahaifin A.J bashi da dangi ne? Sannan Ina dangin Mahaifiyarsa”.
Ido Innayi ta tsira masa tana jin bugun zuciyarta na ƙawura.
M Jameel kuwa cigaba yayi da cewa.
“Sannan dan Allah kiyi haƙuri kada ranki ya ɓaci shin ke kakarsa ta wajen auwace ko kuma kakar sa ta wajen Uba ne?”.
Kallonsa kawai Innayi keyi tana jijjiga ƙafarta.
Ajiyar zuciya M Jameel ya saki kana yace.
“Dan Allah Innayi ki faɗa min ina son insan wannan abin kada ki ƙi faɗa min ke ta wani gefe ne kika kasance.
Kaka agaresa sannan kuma akwai abubuwa da dama da suke ɗaure min kai ina so insan su Innayi, idan har baki faɗa min suba Wallahi zan rayu da ƙumfa dan Allah ki faɗa min kada in mutu baki faɗa min ba”.
Sanyayyar Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da kallon M Jameel kana tace.
“Aaa to mutuwan nan Kam Jamilu am ai tana kan kowa, sannan ni tsohuwa ma ban ce kar in mutu ban faɗa muku ba, sai kaine zaka ce kar ka mutu ban faɗa maka ba!”.
Langwaɓar da kai yayi tare da karyar da murya cikin son karya logonta da batun zai mutu dan yasan bata son jin hakan yace.
“Ni dai ki faɗa min”.
Girgiza kai tayi tare da cewa.
“Jamilu bana son tone-tone ne Jamilu abar kaza cikin gashinta fa yafi, sannan kuma babu amfanin tone-tone da faɗe-faɗe!”.
Zamansa ya gyara tare da cewa.
“Innayi Ni dai inaso shi tone-tonen nan da faɗe-faɗen nan ina so afada min waye ne A.J Ina son insan Abu akan Abokina kuma Aminina ina so insan komai akanshi”.
Sauƙe numfashi tayi tare da kallon M Jameel kana tace.
“Toh nayi maka al'ƙawari ni kuwa zan sanar maka da komai in. Allah ya yarda zan faɗa maka abinda ya sawwaka duk da cewa bakomai zan faɗa maka ba”.
Jinjina kai yayi kana yace.
“Toh Innayi nagode amma ranan yaushe zaki faɗa min”.
Shiru tayi alamar tunani sai kuma tace.
“Duk ranan dana shirya zan faɗa maka sai kazo kai kaɗai”.
Jinjina kai yayi tare da cewa.
“Toh shikenan Innayi Nagode sosai”.
Bayan sun sake taɓa hira ne ya mata Sallama ya tafi.
Da daddare Misalin ƙarfe takwas Naseer ya shiga gidansu bayan yaje ya gama sharholiyarsa kai tsaye falon mahaifiyarsa ya nufa zaune ya samu Mahaifiyarsa da Yayunsa mata guda biyu dawowarsu daga gidan sunan kenan basu daɗe ba.
Zama yayi tare da gaishesu suka amsa cikin sakin fuska.
Aunty Hindu ce ta kallesa tare da cewa.
“A'a yau fa mun ga abin al'ajabi agidan Yaya Musa kawai ragon suna ya ɓace bat.
Ni dai gaskiya ban yarda da mai gadin nan ba da ƙyar idan bashine ya sace ragon ba yazo yana ihu da kururuwa wai rago ya ɓace rago zai ɓace shi tsuntsune ko abin tsafi ne?”.
Dariya Naseer yayi tare da kallon Addar tasa kana yace.
“Atoh ku dai bin ciki mai gadin nan rago zai ɓace haka nan ba dalili ne”.
Aunty Larai tace.
“Atoh abin dai akwai abin dubawa”.
Miƙewa Naseer yayi tare da miƙa yace.
“Bari na shiga ciki na watsa ruwa”.
Kallonsa Aunty Hindu tayi kana tace.
“Bari muje ka bani tsaraba ta da yake baka da kirki tunda kazo ba kaje gida na ba Naseer”.
Zaro ido yayi kana yace.
“Wallahi ranan naje Aunty Hindu akace min wai kinje kitso yara basu faɗa miki ba?”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Ai kuwa sun faɗa min ba shakka na tuna toh muje ka ban tsara bata”.
Ta faɗa tare da miƙewa gaba yayi tabi bayansa har suka shiga tsarerren falon nasa da komai na ciki ash colour da baƙi ne Bedroom ya wuce Aunty Hindu kuma ta zauna aɗaya daga kujerun cikin falon tana jiransa.
Naseer kuwa yana Shiga Idanunsa suka sauƙa akan yankekken rago Atsakiyar gadonsa Atsorace yaja baya cikin kiɗima da ruɗewa ya dafe kansa tare da furta.
_“Innalillahi Wa'inna Ilahi rajiu'n”_
Aunty Hindu kuwa jin Muryar sa Aƙiɗime yasa ta miƙe da sauri ta isa Bedroom ɗin Idanunta bai sauƙa ko ina ba sai kan ragon.
Dafe ƙirjinta tayi tare da cewa.
“Innalillahi ragon anan kuma?”.
Cikin sauri Naseer ya sanya hannunsa tare da rufe mata baki kana yace.
“Na roƙe ki Aunty Hindu Dan Allah ki rufa min asiri kada ki faɗa kada kiyi maganar”.
Cike da mamaki da kuma tsoro tace.
“Toh kenan Naseer kaine ka saci ragon?”.
Kallonta yayi tare da cewa.
“Kamarya in saci rago kamar wani almajiri. nima ganin sa kawai nayi akan gadona kamar yanda kika gansa”.
Harara ta watsa masa tare da kallon ragon dake kan gadon kana ta kallesa tare da cewa.
“Kai ka sace mana in ba Haka ba Naseer menene?”.
Wani shegen kallo ya watsa mata da alamun ɓacin rai atare dashi yace.
“Ba sacewa nayi ba idan ma satar zanyi ba zan saci mai raiba!? Ko ni matsiyacine da bazan iya saya ba, ko mun rasa wadatane a gidan”.
Sai kuma ya saki Ajiyar zuciya tare da dai-dai ta Muryar sa yace.
“Kawai dai akasi aka samu?”.
Cikin rashin fahimta tace.
“Kamar ya akasi aka samu?”.
Ƙugunsa ya riƙe da hannunsa biyu tare da furzar da Iska mai zafi daga bakinsa kana yace.
“Kawai an ɓata min aikina ne?”.
Cikin rashin fahimta tace.
“Aiki kamar ya?”.
Dafe kansa yayi alamun gajiya kana yace.
“Na haɗa ki da Allah da darajar Manzonsa, ni kar kiyi min tonon silili da tereren ban kaɗa dan Allah ki haɗiye wannan maganar ƴar uwa ki rufa min asiri wannan magana tsakanin mu ne kawai kin gansa magana ya ƙare”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da faɗin.
“Toh ka faɗa min menene sirrin?”.
Girgiza kai yayi tare da cewa.
“Ba zaki iya ɗauka ba”.
Kallonsa tayi kana tace.
“Ka faɗa min menene bazan iya ɗaukar ba?Abinda nasani Naseer idan ma maita ce duk mun tsotsa fa!”.
Sake ɗaure fuska yayi kana yace.
“Maita ku kuka tsotsa ni dai bana maita amma ina abin da yafi maita!”.
Zaro Ido tayi tare da cewa.
“Menene?”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe kana ya sake kallon ragon lumshe idanunsa yayi tare da cewa.
“Bokana ne ya bani laƙani idan nayi aiki da al'adan mace zanyi kuɗi zanyi arziƙi mai tarin yawa da yake ba kisan kai bane shiyasa na bayar”.
Cije labɓansa na ƙasa yayi kana yace.
“Sannan kuma duk yarinyar data saka min jininta zan zo in same ta akan gado na”.
Furzar da iska mai zafi yayi daga bakinsa kana yace.
“Aunty Hindu ina fama da matsala tun da nadawo ƙasar nan ban samu nayi Sex ba. Ina dame ina cikin tsananin buƙatar Mace, toh kinga Khausar kuma ina sonta sannan nasan cewa nizan aureta shiyasa na bata mahaɗin maganin da aka bani ƙyallen akan ta samin jininta kinga da ita zanzo in samu akan gado madadin ragon nan".
A hankali ya numfashi kana ya cigaba da cewa.
“Kinga zanyi Sex ɗina da ita baza ta hanani ba kana nasan.
Ni zan aureta shiyasa ban damu ba jini kuma ba wani abu zai mata ba kawai dai in Anyi amfani da jinin zanyi arziƙi ne, zan shiga cikin manyan Yara na wannan ƙasar sai dai kiji ƙanin ki ya zama yaro da kuɗi abokin manya, kije Makka kije Madina inkai ki Dubai in kaiki India kije duk ƙasar da kike so afaɗin duniya”.
Cike da takaici Aunty Hindu tayi Ƙwaffa tare da cewa.
“Shegiyar yarinya ta ɓata mana aiki, ai wannan yarinyar da kake gani dama ba a abin arziƙi da ita, kai dai ka dage kana sonta ne amma da wata yarinya ka samu wawuya sai ta saka maka amma wannan da shegen wayo kamar dila, kaga duk yanda akayi jinin ragon ta saka ajiki tunda dai kaga rago ne yazo maka kan gado”.
Jinjina kai yayi tare da cewa.
“Wallahi kuwa”.
Dafa kafaɗar sa tayi tare da cewa.
“Kada ka damu zan nema maka yanda zakayi kayi aikin nan”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Toh shikenan Aunty Hindu.
Amma fa muyi taka tsantsan tunda mukayi na farkon nan ya wargaje ina tsoro ko kuma kawai ma zanje in samu Bokan nawa ya canza min sabon salon aiki”.
Kallon sa tayi tare da cewa.
“Amma kana ganin hakan zai yi?”.
Kai ya jinjina mata kana yace.
“Sosai ma dama ya bani zabi biyu ne akwai wanda za'ayi amfani da jini, sannan idan inaso akwai wanda za'ayi amfani da Sparm ɗina amma matsalar nan duk yaran garin basu waye bane dake ba wani babban gari bane ba zaiyi kaje ka hakewa yarinya ba kuma ma anfiso na matata toh akwai kuma na maciji sai dai shi sai Bayan anyi aure ne, kuma yafi muni shiyasa bana sonshi amman gsky zaifi bada manyan kuɗaɗe”.
Cije lips ɗinsa yayu tare da cewa.
“Da zan samu nayi Sex ai zan iya saka Sparm ɗina ayi aiki da shi dan boka yace anfi son sama amma nace ayimin dana Period ɗin saboda zanci riba bibbiyu kinga zan samu in kashe ƙishin dake damuna, zan samu inyi da Khausar tunda Ni zan aureta, sannan kuma mahaɗin arziƙi na zaiyi”.
Ajiyar zuciya Hindu ta sauƙe kana tace.
“Shikenan kaci gaba da gwadata idan ta yarda da lallami in kukayi sex din ai shikenan”.
Jinjina kai yayi tare da cewa.
“Toh zan gwada hakan”.
Atake awajen ya ɗauki ragon yakai kichen sannan ya daddatsa yasa abako kana ya miƙawa Aunty
Hindu ya ce.
“Ki tafi dashi”.
Dariya tayi tare da cewa.
“Wato dai munci banza”.
Murmushi yayi kana yace.
“Eh sosai ma munci banza, to mun isa mu fita da ragon munce mun sameshi adakina ne, aikinga asirinmu zai tonu".
Jinjina kai Hindu tayi kana tace.
“Hakane”.
Kai tsaye gidanta ta nufa da ragon zata gyara musu kamar yanda yace.
Wayewar garin Laraba baki ɗaya Jama'ar
Garin Gembu sun tashi da lumshi tun ranan da akayi ruwa tamkar da bakin ƙwarya da kuma rugugi ba asake yin ruwa ba kusan Makonni biyu kenan garin ya zamana har sun fara ɓuƙatar ruwa duk da irin sanyin da ake musu amma garin ya fara ɗumi ga hadari daya haɗu baƙi asama sai dai babu ruwa sai Sanyayyar Iska mai sanyi da ratsa jiki da ake surarawa.
Acan ɓangaren Khausar kuwa cikin shiri ta fito daga Bedroom ɗin ta cikin riga da wando na Pakistan daga saman rigar atsuke take yayin da daga ƙasanta kuwa abuɗe take wando kuwa Pencil ne sosai kayan suka amsheta sai ya fito tamkar Kajol yayin data ɗaura Maroon ɗin hijab har ƙasa jikinta na fitar Sanyayyar ƙamsin turaren Oud Ma'arup bakinta ɗauke da Sallama tashiga Bedroom ɗin Mommy.
Anutse Mommy ta ajiye Carbin dake hannunta kana tace.
“Har kin shirya?”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh Mommy”.
Ajiye Carbin Mommy tayi tare da kallonta kana tace.
“Khausar ki kula koda Ummin Asma'u bana so ku faɗa wa abinda ya faru”.
Kai Khausar ta gyaɗa kana tace.
“Toh Mommy ni dai nasan da ƙyar idan Asma'u ta faɗa wa Ummin ta amma idan ma ta faɗa mata shikenan dan nasan Ummi koda ta faɗa mata babu matsala”.
Jinjina kai Mommy tayi tare da ciro 1k A pose ɗin ta tace.
“Ga Kudin transport”.
Amsa Khausar tayi tare da faɗin.
“Nagode”.
Kana ta fice.
Tana fita ta tari A dai-dai-ta Sahu ta shiga tafiyar minti ashirin da biyar ne ya kaisu gidansu Asma'u.
Anutse ta sauƙa tare da bashi kudin kana ta tura ƙaramin gate ɗin gidan tashiga tare da nufar falon bakinta ɗauke da sallama tashiga Ummi dake zaune a falo ta faɗaɗa Murmushin fuskarta tare da cewa.
“Khausar sannu da zuwa”.
Cike da ladabi Khausar ta tsugunna tare da cewa.
“Ina Yini Ummi?”.
Murmushi Ummi tayi tare da faɗin.
“Lafiya lau Khausar yasu Hajiya Aysha dasu Haiydar?”.
Khausar ta amsa da.
“Lafiya ƙalau suna gaisheki”.
Jin muryan Khausar yasa Asma'u dake Bedroom din Ummi tana gyara fitowa da murmushi afuskarta tace.
“Fattanah”.
Miƙewa Khausar tayi tare da wurga mata Harara kana tace.
“Ai wannan sunan na barwa wanda ya liƙa min shi amakaranta sai dai kuma ya sawa wata amma ba dai niba abi wani sarkin”.
Dariya Asma'u tayi kana tace.
“Ai Suna linzami tunda wasu ma idan za'a kwana ana ce musu Khausar basu sani ba sai ance Fattanah kinga, kuwa Yaya Moddibo ya sanya miki suna ya biki ko ba ragon suna”.
Taɓe baki Khausar tayi kana suka shiga ɗakin Ummi atare suka gyara ko ina tare da jona bona suka sa turare.
Bayan sun gama gyara ko ina suka koma ɗakin Asma'u.
Ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe cikin ƙasa da murya tace.
“Asmau'u kin faɗa wa Ummi Maganar?”.
Girgiza kai Asma'u tayi tare da cewa.
“Wallahi ban faɗa mata ba Khausar ai Mommy ta gargaɗe mu”.
Jinjina kai Khausar tayi tare da kallon Asma'u kana tace.
“Asmeey kin kuwa san har yau Naseer bai sake zuwa wajena ba sannan bai sake yi min magana ba.
Kuma wayar daya bani akwai sim card da komai da komai amma har yanzu bai sake kira na ba”.
Girgiza kai Asma'u tayi tare da faɗin.
“In dai bai miki maganar ba kada kiyi masa. waya kuma kima ajiyeta kawai dan kuɗin san nan bama asan na menene ba, kana bamusan me yake nufi dake ba”.
Tagumi Khausar tayi har yanzu abin na mugun bata mamaki koda wasa bata taɓa tsammanin Naseer zai mata haka ba.
Asma'uce ta riƙe Hannunta kana tace.
“Waya sani ma ko Lalata yayi niyyar yi dake yanda ragon nan ya ɓace wataƙil ke ki ɓace tema ma aɗakinsa za'a sameki yayi rapping ɗinki”.
Lumshe idanu Khausar tayi kana ta buɗe su akan Asma'u tare da sauƙe Ajiyar zuciya kana tace.
“Haka ma Mommy na tace kuma kinga ta karɓe wayar ma sannan