Header Ads
Showing 51001 words to 54000 words out of 188939 words

Chapter 18 - SAKAYYA Book 1 complete BY GARKUWA.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

juyawa yayi tare da kallon M Jameel yace.
“J ka da keta”.
Da sauri M Jameel ya juya tare da nuna kansa da babban yatsa kana yace.
“Ni!?”.


Cike da tsuke fuska Moddibo ya gyaɗa masa kai kana yace.
“Eh ka daketa!”.
Zare Ido M Jameel yayi tare da cewa
“Meyesa?”.
A kufule Moddibo yace.
“J kadaketa nace!”.
Kallon mamaki M Jameel yake masa tare da cewa.
“Akan me zan daketa?”.
Cike da ɓacin rai Moddibo yace.
“Idan fa ka bari nace ni zan daketa zan sumar da ita fa!, zan karyata fa!!”.
Cikin tsananin fusata ya ida maganar.


Ita kuwa Khausar tuni jikinta ya hau rawa Allah ya sani bata son duka, sannan mari ɗaya daya mata ya mugun gigita mata ƙwaƙwalwa wanda har zuwa yanzu take jin raɗaɗin sa asaman fuskarta.


Fuskarsa babu walwala yace.
“Idan har nace zan daketa zan sumar da ita”.
Ita kuwa Khausar jin azaban mari ɗaya daya mata, aranta tace Ashe Allah ya rufa min asiri da yasa duk lokacin da nayiwa Moddibo laifi baya duka na yake sa Malam Adam display master ke dukana na tabbata dashi yake dukana kullum da tuni ya kasheni!.


Cikin hanzari ta juya tare da kallon M Jameel ta miƙa masa hannu Muryanta na rawa tace.
“Malam ka dakeni!”.
Girgiza kai M Jameel yayi cikin sanyin murya yace.
“Ni dai kam bazan iya ba bazan iya dukanta ba Moddibo, ka dubi fuskarta fa mari ɗaya da ka mata kalli fuskarta fa ai ya wadatar wani hukunci ya rage bayan wannan?”.
Ya kare mgnar a hankali
Moddibo kuwa cikin fushi yace.
“Kada keta in kuma baza ka daketa ba zan daketa da kaina fa”.
Cikin sauri M Jameel ya fara girgiza kai yayi cikin wata Sanyayyar murya me cike da zallar jin ƙai tare da tarin tausayi gami da rauni yace.
“La! La!! La!!! A.J bazan iya ba! Wlh Bazan iyaba ba wannan ba hurumina bane hurumin taɓa ta awajenka yake bani da karsashi ko ƙwarin gwiwar da zan iya taɓa ta!”.
Ya ida maganar cikin wani irin salo na daban, kana dai-dai lokacin Amina tazo Office ɗin domin kiran M Jameel ya shiga ajinsu wani irin sarawa kanta yayi jin yanda yake cewa bazai iya ba.
Da sauri ta dafe ƙofar office ɗin jin jiri na ɗibarta kadde ace dokon soyayyarsa za tayi abanza, kadde Khausar yake so yanda ya ƙarashe maganar na nuni tamkar itace rayuwar sa.


Da sauri Moddibo ya juya ya kalli M Jameel jin yanda yayi magana da kuma yanda ya lanƙwasa harshensa abun ya bashi mamaki.
Azuciye Moddibo yace.
“In daketa kenan?”.

Langwaɓar da kai M Jameel yayi cikin sanyin murya yace.
“Kayi haƙuri ina mai bada haƙuri amada dinta ka nemi wani punishment ɗin ka bata amadadin wannan, amma nikam bazan iya dukan taba sannan kaima banaso ka daketa!”.
Baki ɗayan su kallon Mamaki suka bi M Jameel dashi ganin yanda yake lanƙwasar da murya tare da nemawa Khausar ya fiya, ita kuwa Amina wasu hawaye ne masu zafin gaske ne na tsananin kishi da baƙin ciki, suka zubo mata saurin ta sanya hannu ta share.
Kwantar da Murya M Jameel ya kuma sakeyi ya cigaba da cewa.
“Kallifa A.J mari ɗayan nan da kamata kalli fuskarta fa ka daketa awaje mafi daraja”.


Moddibo kuwa lumshe idanunsa yayi kana ya buɗesu akan M Jameel tare da cewa.
“J kadaketa ni idan nace zan daketa bazai mata daɗi bafa”.
Sake Langwaɓar da kai M Jameel yayi kana yace.
“Kayi haƙuri Moddibo ni bazan iya dukanta ba!”.


Ita kuwa Samari Sani na tsaye agefe ta harɗe hannayenta aƙirji yayin da ta zubawa Moddibo ƙananun Idanunta ko ƙyaftawa ba tayi.
Ita kuwa Amina Idanun ta nakan M Jameel da idanunsa ke kan Khausar zuciyarta nayi mata zafi.


Khausar kuwa kallon M Jameel ta sakeyi akaro na barkatai tace.
“Malam Jameel ni dai ka dakeni”.
Kai ya girgiza mata tare da faɗin.
“Bazan iya dukan ki ba Khausar!”.


Shi kuwa Moddibo cikin tsananin ɓacin rai ya juya ya kalleta a kufule yace.
“Toh inda keta da kaina!?”.
Girgiza kai M Jameel yayi sai kuma yace.
“A'a asassauta mana dan Allah”.
Ƙwafa Moddibo yayi da faɗin.
“Shikenan kije ki kaɗe ɗan kwali sau ashirin”.


Cike da tsoro ta zaro ido domin kaɗe ɗan kwallon da yace yana nufin ta cire ɗan kwalinta tasa abokitin ruwa ta matse kana ta kaɗe har sai ya bushe,
sannan ta sake sakawa cikin ruwa ta matse kana tayi ta kadewa har sai ya bushe.
Tofa jin haka ne yasa a tsorace ta zare Ido Jin hukuncin daya yanke mata ba zata manta lokacin daya sata kaɗewa sau goma ba awannan lokacin ma saida tayi sati biyu gaɓɓanta na ciwo ko abu zata ɗauka da ƙyar take iyawa.


Cikin yanayin neman alfarma M Jameel ya sake langwaɓar da kai kana yace.
“Dan Allah ka sassauta mata karage mata”.
Jin Muryan M Jameel yasa ita ma ta kalli Moddibo cikin wata raunatacciyar murya tace.
“Dan girman Allah Malam kayi haƙuri karage min”.


Shi kuwa Moddibo wani kallo ya watsa mata cikin haɗe girar sama dana ƙasa yace.
“Kada ki sake haɗa ni da girman Allah da kinsan darajar girman Allah da zaki mutunta Malama ki,
kije kiyi shabiyar kinci darajar girman Allah.
idan kika sake cemin dan Allah in rage miki kuwa nida ke bibbiyu!”.
Gyaɗa kai tayi kana tace.
“Toh shikenan”.
Shi kuwa M Jameel kallon Moddibo yayi cikin jujjuya ido yace.
“Ina neman alfarma abarta tashiga aji tayi karatu idan antashi Break sai tayi”.


Shi kuwa Moddibo Ɓata fuska yayi yace.
“Bana son ganinta a aji Idan naganta a aji zan kakkaryata in wurgar ta window”.
Ita kuwa Samira Sani cikin lanƙawasa harshe tace.
“Malam Moddibo mu tafi”.
Sake tamke fuska yayi tare da juyawa ya watsa mata wani bayyane harara sai kuma ya nuna mata ƙofa alamar ta ɓace masa da gani.


Sum sum ta juya da sauri ta fice.
Da harara yabi bayanta Aransa yace.
Shegiyar yarinya mai kama da Mayya,
sai shegen kallon jaraba tasani gaba zakiyi dan rashin kunya.


Samira Sani kuwa tana shiga ajinsu ta lumshe Idanunta tare da kallon gefen ko wannen kujera dake ɗauke da flowes ta saki murmushi mai cike da jin daɗi,
tasan wannan aikin Moddibo ne domin kaf cikin Malaman shike son flowers.
Hajia Ruƙayya ce ta dubi Samira data shigo kana tace.
“Ni kam ya banga Khausar ta shigo ba har yanzu kuma ɗazu na hangota kafin na haura”.
Juye Ido Samira tayi tare da faɗin.
“Tana can tayiwa Moddibo rashin kunya yana cin Ubanta, shegiyar yarinya fitsararriya ‘yar marasa tarbiyya!".


Asma'u ce ta juya ta kalleta rai a haɗe tace.
“Haba Samira meyesa zaki zagi iyayenta ai bai kamata ki zagi iyayenta komai yaya iyaye nada daraja”.
Harara Samira ta wurga was Asma'u kana ta buɗe baki da niyyar magana ta fasa sakamakon shigowar Moddibo.


Ganin shigowar Moddibo yasa ta tsuke bakinta tare da neman waje ta zauna cike.
Cike da ladabi suka gaishesa cikin harshen larabci tare da faɗin.
”صبحل خير ىاعثتذ“
Ya Amsa da.
“صبحل نور كىفل قراء“.
Suka amsa da.
”الحمد الله“
Kasancewar Tafseer zasuyi dake yanzu lokacin Islamiyya ne yasa yace.
“Kuyi muraja”.
Cikin bawa ko wanne harafi hukuncinsa suka shiga karanta suratul Muhammad har zuwa karshe.
Bayan sun gama kawo haddan ya jinjina kai tare da faɗin.
“Sai gobe Insha Allah zamu fara tafsirin sa”.


Aɓangaren M Jameel kuwa tare suka jera da Amina suka nufi ajinsu yayin da azuciyar Amina yayi baƙiƙƙirin data tuna yanda M Jameel ke karyar da murya akan Khausar har suka isa ajin tunanin da take aranta kenan yanayin yanda tsarin ajinsu Khausar yake haka ko wanne aji yake cike da ƙwarewa M Jameel ya shiga yi musu ƙarin Mi'atu Hadith daga na Arba'in bayan sun karanta masa.
Ko wanne aji da Malami aciki suna darasi.


Ita kuwa Khausar ita kaɗai ce tsaye aharabar Makarantar cikin gajiyawa ta ɗaga boket ɗin ruwan ta koma rana wai ko zata samu yafi bushewa da wuri, tsoma ɗan kwalin tayi aciki kana ta matse sannan ta fara kaɗewa.
Nannauyan ajiyar zuciya ta saki tun akaɗewa na uku taji hannunta ya sage aranta tace.
“Insha Allah Ina komawa gida zan nemi ɗankwali mai shara-shara mara nauyi wanda kodan irin rana ta yau ta faru zaimin sauƙi.
Cike da gajiya ta miƙe ta riƙe ƙugunta da hannu ɗaya ta lumshe idanunta sosai ta gaji.


Shi kuwa Moddibo daga can sama acikin ajinsu Khausar yake kallonta tana kaɗe-kaɗen ganin ta tsaye ta riƙe ƙugu gaban ƙirjinta duk ya jiƙe da fuskanta, ganin ta tsayanne yasa ya buɗe glass ɗin window dake saitin ta tare da ziro hannunsa ya ƙyasta yatsunsa da ƙarfi wanda hakab yaja hankalin Khausar da saurin ta ɗaga kanta.
Ganin abinda yayi yasa da sauri ta cigaba da kaɗewa tana mai rintse Idanunta.


Har Moddibo ya gama teaching ɗinsa ya fita Khausar nakan punishment Koda ya saƙƙo ya ganta Harara ya watsa mata kana a kufule yace.
“Ba zaki shiga ajiba yau har sai kin gama abinda nasaki”.
Fuska ta Shagwaɓe tare da langwaɓar da kai tace.
“Ayyah Malam dan Allah kayafemin duk ɗan Adam ajizine!”.
Harara ya watsa mata ya wuce batare daya bata amsa ba,
bayansa tabi da kallo tana tura ƙaramin bakinta, to har wani malami ya sake shiga yayi darasi Khausar bata gama ba sai sha biyu dai-dai lokacin tashin matan Aure sannan Yara da ‘Yan mata suyi suci abinci su koma ajin boko.


Hajiya Ruƙayya ce da Aunty Khadija ne suka fito tare da ƙarasawa kusa da Khausar dai-dai lokacin da Khausar ke faɗin.
“Wayyo hannuna”.
Ta faɗa tana matsa yatsunta dake raɗaɗi.


Dafata Hajiya Ruƙayya tayi kana tace.
“Ayyah sannu Khausar kece bakyaji me kika yiwa Moddibo!?”.
Langwaɓar da kai Khausar tayi tare da marairaice murya tace.
“Allah babu abinda na masa kawai ina tahowa ne mukayi karo dashi har System ɗinsa ya faɗi kuma ma naji malam Jameel yace System ɗin beyi komai ba amma sai da ya sani wannan kaɗe-kaɗen sabida in baici zalina ba baya jin daɗi rayuwarsa ta duniya”.
Ta ida maganar da faɗin.
“Affan zo”,tare da miƙa masa hannu.
Murmushi Aunty Khadija tana mai jujjuya kai.
Ita kuwa Hajia Rukayya
Miƙa mata yaron dake ta faman ƙyalƙyala mata Dariya Aunty Ruƙayya tayi Sai kuma tayi saurin janye hannunta tana cewa.
“Wayyo Aunty Ruƙayya hannu na ya gaji yaukam bazan iya riƙe sa ba”.
Ta ƙare mgnar tana ƙara matsowa kusa da Aunty Ruƙayya kan kumatunsa ta sumbata tana faɗin.
“Affan gaye".
Shi kuwa yaron sai dariya yake ƙyalƙyala mata tare da miƙa mata hannu alamar yana so ta ɗauke sa dan sosai yaron ya saba da ita saboda Aunty Ruƙayya na zumunci da Mommy Khausar sannan Khausar na shiga lokaci zuwa lokaci.


Samira Sani da Abeeda Sule ne suka ƙaraso wajen Kallon Abeeda Sule Samira tayi da faɗin.
“Ai Moddibo shike maganin tantirai marasa mutunci ’ya'yan Fitsararru awannan makarantar yana min dai-dai!”.


Sake hannun Affan Khausar tayi ta juya ta kalli Samira da kyau tace.
“Waye ‘Yar marasa mutuncin?
Akwai ‘Yar marasa mutunci daya wucike ne ‘Yar magulmata Munafuka kawai! Inbanda munafurci da gulma da biye-biyen bokaye Me kuka iya!?”.
Afusace tace.
“Ke Khausar zanci Ubanki fa!".
Wara ido Khausar tayi kana tace.
“Ubana kuma, uhmm saide Kici naki uban domin ni kam nawa Ubana tuni Ubangiji ya daɗe da yimasa sutura sai dai kije kici naki ‘Yar matsiyata?”.
Ta ida mgnar cikin tsiwa,.


Abeeda Sule ne tace.
“Ke akwai ma ƴar matsiyata irinki, kina tsammanin bamu san cewa munsan ke Agwola bace acikin gidan sarki da kike nunawa kamar gidan ku ne?”.


Dariya Khausar tayi kana tace.
“Dan Allah rufe mana baki ‘Yar Alhaji sule baka layya kibari tukunna in Babanki ya fara layya saiki faɗa wa mutane Magana?”.


Zare ido Abeeda tayi tare da hayayya ƙowa tace.
“ ‘Yar iska ni zaki cewa Ubana baya layya”.
Taɓe baki Khausar tayi tare da faɗin.
“Ke rufe min baki ai bani na faɗa ba Inkiyarsa ce hakan, ko ba sunan sa bane? Alhaji Sule baka layya!! ko kuma ni nasa masa ko kuma dan tsoronki sai inki kiransa da sunan da aka sa mishi”.


Hajiya Ruƙayya ce tace.
“Khausar rabu dasu”.
Gyaɗa kai tayi.
Ita kuwa Samira cikin takaici tace.
“ ‘Yar banza kawai agola”.
Dariyar rainin hankalin Khausar tayi sannan tace.
“Eh koma menene inma ni Agolace inada daraja sannan ina da tushe dama ni ban ɓoyewa cewa Agola bace Ni saboda idan kinga sunan su Amina da sunana kin san ba yar gidan bane,
Ni sunana Khausar Usman Abubukar Lelewal sukuwa kinga ba haka sunan su yake ba daga nan ma mutum yasan Ni Agola ce ko dama anɓoye miki ne?”.


Hannunta Hajiya Ruƙayya taja suka bar wajen zuwa gefe tace.
“Khausar kifita har ƙansu kiyi abinda ke gabanki kinga duk yau baki samu karatu ba”.
Kai Khausar ta gyaɗa mata sannan tayi mata Sallama ta tafi.
Asma'u ce ta ƙaraso wajen Idanunta akan Samira da Abeeda dake zagin Khausar cikin yanayin sanyin muryanta tace.
“Khausar kifita sabgar wa'annan yaran dan Allah keda su ba ɗaya bane kada ki ringa biye musu muta nen da ƙwaƙwalensu basa ja, kinga fa yanzu da ya kamata suna SS 3 nefa daƙiƙancinsa kesa kullum basa gaba sunan a jaɓe har muka isosu”.
Yamutse fuska Khausar tayi kana tana matsa yatsun hannunta tace.
“Kinsan Allah Asma'u Indai basu fita sabgata ba zan basu mamaki zan nuna musu Khausar Usman Abubakar Lelewal ba kanwar lasa bace”.


Hannunta Asma'u ta riƙe tace.
“Ni dai dan Allah ki fita sangarsu ai ko kare bai haushi shi kaɗai tukunna wai me kika yiwa Moddibo ya saki Punishment?”.


Rau-rau da ido Khausar tayi sai kuma ta ya mutse fuska tare da jan tsaki kana tace.
“Mutum yana nan kamar wani sabon boss sam fuskarsa babu fara'a yana nan sai baƙin mugunta.
Kuma wallahi Wuta bal-bal ban yafe masa ba, ai bani kaɗai nayi kuskuren ba shima yayi yana tafiya kamar makaho, kuma yaseen saƙo na baki ki faɗa masa ehe”.
Ta ida mgnar cike da tsiwa da murguɗa baki
Asma'u kuwa dariyar dake cinta ta danne kana tace.
“Aikuwa gashi nan abayanki yana ma jinki ba sai na faɗa masa ba”.
Arazane Khausar ta saki ihu tare da rintse Idanunta cikin tsananin tsoro da rawan jiki ta juya tana mai faɗin.
“Dan Allah! Dan Allah!! Dan Allah!!! kayi haƙuri Allah bada kai nake ba kuskuren harshene ni da kainama nakeyi”,
Ta ida maganar tana buɗe Idanunta jin be tanka taba ga mamakinta bata gansa ba.
Kallon Asma'u tayi wacce zuwa lokacin ta saki dariyar ta tace.
“Fattanah sarkin tsiwa dama gwada ki nayi inga da gaske saƙon kika bani”.


Harara Khausar ta zabga wa Asma'u amma batace Komai ba.
Murmushi Asma'u tayi tare da jan hannunta zuwa resting chair dake cikin harabar makarantar suka zauna Asma'u ta fito da kula da ɗauke da pride rice da yaji kayan hadi da namar kaza suka ci.
Bayan sun gama cin wannan Khausar ta buɗe bata kukan.
Peper checking ne guzurin zabbin data dawo dasu.
Sunaci suna ɗan hirarsu dai har suka gama, suka mike tare da zagaya classes din makarantar suna kallon yanda aka tsara makarantar kamar ba shiba.
12:10 suka koma aji.
Bayan komawar su Malam Isa dake ɗaukar su Economist ya shiga ya koyar musu sosai Khausar da Asma'u ke fahimtar karatun 1:15 dai-dai suka fita sallah.


Bayan sun fita Al'wala sukaje wajen da aka tanada dan alwala sukayi gefen maza da ban na mata da ban Amma masallacin guda daya ne saidai anraba daga tsakiya anyi katanga mata zasu shiga ta gefen dama maza tagefen hagu.
Bayan sun idar da Sallah ƙarfe 1:30 suka koma aji wasu Malaman suka sake shiga.
Sosai Malaman suka dage wajen koyar dasu domin anƙara musu Salarie sannan ankawo sabbin Malamai hakan yasa babu period din dake wucewa ba tare da anshiga ba 5:00 dai-dai suka tashi motar su Khausar tazo ta ɗauke su.


Washe gari.
Ma haka suka gudanar da karatunsu kamar na jiya.
Acikin satin karatu suke gadan gadan babu kama ƙafar yaro saboda suna son dai-dai-ta komai na lokacin daya wuce ahutu koda wasa Khausar bata sake yin ganganci wani abu ya haɗa ta da Moddibo ba bare tayi masa laifi da zaran ya shiga ajinsu zata tattara duk kan nutsuwarta akansa tana sauraron abinda yake koyar musu kuma sosai take fahimta yayin da ita kuma Samira Sani zata tsaya aikin Kallonsa aduk sanda ya shiga musu shikuwa Moddibo duk yana lura da yanayin ko wannensu.


Yau Alhamis ya kasance babu makaranta suna hutu.
Khausar ce zaune a falon Mommy ta tana duba Mi'atu Hadith,Mommy dake Bedroom ta ƙwala mata kira Amsawa tayi tare da ajiye Hadith ta fita.
Bakinta ɗauke da Sallama tashiga Bedroom din Kallonta Mommy tayi tace.
“Khausar ɗibi wannan kayan ki kaiwa Hajiya Bunayya kala ɗaya nasiya mana”.
Kallon mamaki Khausar ta yiwa Mommy anma wannan basabon abu bane ko yaushe Mommy na zaune zuciya ɗaya da ita tana kyautata mata, amma ita Hajiya Bunayya ba da zuciya ɗaya take zaune dasu ba.
Gyaran Murya Mommy tayi tace.
“Khausar tunanin me kike?”
Murmushi Khausar tayi tare da ɗiban kayan tace.
“Toh”,Mommy sannan ta fice.


Bakinta ɗauke da Sallama ta shiga falon Hajiya Bunayya kana ta nemi waje ta zauna aɗaya daga cikin kujerun dake falon tace.
“Ummah gashi Mommy na ta siya musu iri daya”.
Washe baki Hajiya Bunayya tayi tare da kallon turamen Zannuwa da tsadaddun less ɗin tace.
“Aaaa lalle kam Khausar Nagode Allah yayiwa ƙanwata al'barka muje inyi mata godiya”.
Kai Khausar ta gyaɗa tare da miƙewa dai-dai lokacin Hajiya Lami mahaifiyar Samira Sani tayi sallama suka shigo atare.
Kallon Khausar Hajiya tayi tace.
“Khausar jeki nayi baƙi kice mata Nagode zan shigo anjima”.


Kai Khausar ta gyaɗa tare da ficewa yayin da Samira ta bita da mugun kallo.
Kallon Hajiya Lami Hajiya Bunayya tayi kana ta mika mata hannu suka tafa Dariyar ƙeta Hajiya Bunayya tayi tace.
“Kalli Sokuwarki wai kaya ta saya mana iri ɗaya”.


Dariya Hajiya Lami ta fashe dashi tare da cewa
“Aaaa Ikon Allah sokuwa ta ƙarshen zamani kuwa wato hadda siya muku anko”.
Tsaki Hajiya Bunayya tayi tace.
“Bar ‘yar banza mai kama da ‘ya‘yan mayu tazo ta liƙewa mijina”.


Hajiya Lami tace.
“Aikam wa'annan mutanen sai Allah aike kika sake kika basu dama, kika bar mijinki ya ƙara aure ni yanzu Baban Samira ya isa yace zai ƙara aure ne, sannan bayan kin bari yayi auren ma kika barta tahaifi santalelen yaro me jikin girma bayan shi hadda ‘yan biyu da kawunansu kamar ‘Ya‘yan ruwa ga shegen gashi kamar ‘ya‘yan Aljanu”.


Ƙwafa Hajiya Bunayya tayi kana tace.
“Ai wallahi nayi sake amma daga ‘yan tagwayen babu ita ba sake haihuwa ina lura da ita kwannan kamar cikine da ita to bazan bari ta haife sa ba zanje wajen boka Kar'uzu azubar dama duk cikin ta uku kafin ’yan biyu ni nake sawa azubar shegiya ai bazan barta ba kenan yanzu ma inada niyya zanje wajenki jibi muje wajen Malami”.


Gyara zama Hajiya Lami tayi tare da faɗin.
“Aini ma abinda ya kawoni kenan Hajiya Bunayya in sanar miki”.
Kallonta Hajiya Bunayya tayi tace.
“Toh Meye faru?”.
Ajiyar zuciya Hajiya Lami

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads