Showing 6001 words to 9000 words out of 188939 words
Chapter 3 - SAKAYYA Book 1 complete BY GARKUWA.txt
bar motarsu ta shiga ne, sabida magiyar da sukayi tayi da kuma girman gidan da suka fito, da bada uzurin motar ta ɗan lalacemusu a hanyane kana da kuma ganin ma yau ba karatun za'ayi ba, hutun za'a kuma ruɓanyawa.
Suna shiga kuwa, ga mamaki su aka barsu suka shige ba hukuncin komai.
Kana ko wa ya nufi sashin da ajinsa yake.
Da sauri duk suka tsaya jin Malam Habibullah na cewa.
“Fattanah uwar yan letti yau makarar har ta 20 minute duk da yau aka dawo, duk kuyi sama ana taro a hall”.
Cikin ɗan tura baki tace.
“Toh Malam”.
Yayinda tuni su Asiya kam sun haura har sun shiga hall ɗin.
Da ɗan sassarfa ta fara take steps ɗin da zai sasanta, da hall da yake a sama ganin ita kaɗai ta rage.
Daga corridor'n steps ɗin, ta ɗan lumshe idanu ta, tare da gyara saƙala school bag ɗinta a kafaɗar dama.
Sabida ƙamshin turarensa ya shaida mata, tabbas tuni ya shiga hall ɗin.
A hankali ta sauƙe numfashin ta tare, da nemo dukkan nitsuwarta.
Lokacin da ta gama haurowa, sama, da sauri ta tsaya, jikin window dake gab da bakin ƙofar shiga, ido ta lumshe tare da buɗewa a hankali kana ta kutsa kai cikin hall din da a kalla mutane ciki sun kai ɗari da hamsin, duk da tasan bai taɓa barinta, ta shiga ajiba, muddin ya rigata shiga, to amman kullum sai ta gwada sa'anta musamman yau da yake a hall ne.
Taku ɗaya tayi ana biyu, ta tsaya, sabida, ganin ya ɗaga mata, tafin hannunsa.
Cikin yin mui-mui da bakinta tace.
“Afwan ya mu'allim sayyara...”.
Da sauri ta ɗan ja da baya ta koma jikin window ganin ya juya baya tare, da gyara ɗan masaƙalin Lapel Microphone dayake saƙale a wuyan jallabiyar jikinsa, sabida tsananin sanyin sautin muryarsa yasa dole sai dashi yake amfani a cikin class, domin ɗalibansa su samu damar jinsa sautinsa ras domin sam baya iya kware muryarsa yayi mgna da ƙarfi haka Allah ya haliccesa da nitsestsiyar sauti to bare a irin taron maƙil da hall ɗin yayi yau.
Cikin tattausar muryar sa mai cike da sanyi yace.
“Makfut?”. Cike da jin daɗin nasihar da yakeyi musu suka amsa da “Na'am”.
Kai ya jinjina tare da cewa.
“Ɗeyib!”.
Sai kuma ya ɗan juyo ya fuskancesu, hakan ya zama, ya ɗan bawa Khausar baya, tattausan sumar ƙeyansa dake kwance lib-lib ta zubawa harara.
Numfashi mai sanyi taja tare da shaƙa daddaɗan ƙamshin turarensa mai sawa ɗan adam salama.
Sai kuma tayi ƙasa da kwayar idanunta dugadigin sawunsa, ta zubawa idanu tana ganin yadda sukeyin ja in ya taka sawun, in kuma ya ɗaga sai suyi fari, baki ta ɗan tura sama ta da liƙa ƙeyarshi wani sabon hararan.
Shi kuwa Moddibo a hankali yake taku a gaban ɗaliban nasa, masu biyayya da girmamawa a garesa, cikin tattausan lafazi yace.
“Falalar zikirai da karatun Alqur'ani , nakeso son in tunasar mana, sabida kididdigar manazarta, ta nuna mana Al'ummar wannan ƙarnin sun samu naƙasun zikiri da karatun Alqur'ani mai girma, sun maida hankali akan sashin yanar Gizo-gizo fiye da yadda ya kamata, mu maida hankali kan Al'ƙurani littafin Allah da hadisan Manzon Allah, mu samman a wannan taki da muke ciki, na shuɗewar Ramadan wanda zaka samu da yawa mutane sun fuskanci aikin al'khairai da bautar ubangiji a cikin watan, da zaran watan ta gabata sai a koma gidan jiya aita sharholiyar duniya.”
Sai kuma yayi shiru, tare da fesar da numfashi a hankali, kana ya juyo a hankali yace.
“Mutane da yawa sun mance koma ince wasu basu san me Allah maɗaukakin sarki yace ba A cikin Suratul Baqara, ayata 152.
Allah maɗaukakin sarki yace.
فَاذْكُرُونِي أَذْكُرْكُمْ وَاشْكُرُوا لِي وَلَا تَكْفُرُونِ.
Ma'ana:
Ku ambaceni zan ambaceku, ku godemin kada ku butulcemin.”.
Ya ƙare mgnar da rumtse tafin hannunsa alamun ƙarfafa mgnar, wanda kuma wannan ɗabi'arsace ko ace halittar sace.
Duk mgnar da yakeyi yana kamantata ko suffantata da tafukan hannunsa like dai yadda manyan sarakuna keyin mgn turawa kuma suka cewa hakan body language, Wanda mafi akasari ɗabi'ar yan jarida ne, in suna mgn.
Shiru hall ɗin yayi alamun suna fahimta sosai.
Shi kuwa Moddibo cikin girmama zancen Allah madaukakin sarki yaci gaba da cewa.
“A dai wannan ƙarni da muke ciki da yawa, suna butulcewa faɗin Allah madaukakin sarki, daga barin ambatonsa, gaba ɗaya shagala tayiwa al'ummar mu ƙawanya, shafukan sada zumunta na yanar Gizo-gizo ya maiye gurbin da yake muhallin Qura'ani ne a wurin wasu musul manmu, sai a wuni a kwana musulmi bai ɗauki Qura'an ya karanta ya duba kyan baƙin da yake haɗawaba, amman sai ka sameshi awa 14 na awannin 24 na rana yana rungume da wayarsa, ana charting, a Facebook a koma whatsApp, daga nan a tafi Instagram, sai kuma a murgina a koma twitter sai kuma a rarrafawa zuwa wannan lalataccen kuma kazamin dandalin Tiktok, ayi ta raye-raye da waƙe-waƙe, anaiwa juna cin zarafi, wasu su koma yiwa malamai isgilanci ana yaɗa fasadi da fajirci ana meda ashariya kamar ruwan sha.”
Ya dire ayar mgnar tare da haɗe kan yatsun hannunsa gaba ɗayansu wuri ɗaya alamun ya dunƙule mgnar kenan bawai ya gamata bane zai tafi sashi mafi muhimmanci ne.
A jikin window a waje kuwa, cikin jujjuya ido Khausar ta raɓa jikin window tare da maida hankalinta baki daya cikin.
Shi kuwa Moddibo a hankali ya ɗan juyo gefen damansa, jin inda sautin surutu yake ɗan tashi kaɗan.
Ganin yana kallon sune kuwa yasa,
Samira Sani yin shiru.
Cikin nitsu ya kuma cewa.
“A wata ayar kuwa a cikin suratul Ahzab ayata 41, me Allah maɗaukakin sarki yace mana!???”.
Ya ƙare mgnar da alamun ayar tambaya, hakan na nufin su ja mishi baƙi yake so, sanin mafiya akasarinsu yan haddansa ne,
Ji kakeyi, hall din sit kowacce tayi ƙasa da kai, gudun kada ya nuna ta kaɗan daga cikinsu kuma bawai basu sani bane diricewa ne da kwarjininsa ke sasu yin ƙasa da kai.
Cikin sanyi yace.
“Na'am Samira Sani”. Da sauri tace.
“Malam ni?”. Fuskarsa ya tsuke tare da juyowa ya kalli Asma'u Ahmad dayi mata alama da hannu, tsilli-tsilli tayi da idanu.
Samira Sani kuwa ganin ya cire ido a kanta ne yasa tayi saurin buɗe Qura'an ɗin ta.
Dan dubo ayar,
sai kuma duk suka ɗago kansu suka zuwa Khausar dake jikin window idanu,
jin ta uzi shaitan tare da yin basmalla kana taja numfashinta tare da lumshe idanu murya cike da tajwed ta fara jan ayar.
Surah Al-Ahzab aya ta 41:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا اللَّهَ ذِكْرًا كَثِيرًا
Murmushin mai cike da jin dadin Asma'u Ahmad tayi tare da sauƙe numfashin, FATTANAH ta ɗauki belinsu kamar yadda aka saba, domin in dai batun jane na ƙwaƙwalwa to kwanyar Khausar ta musamman ce.
Mata da yawa kuma cikin manyan mata kallonta sukeyi cike da sha'awa da jin daɗin zazzaƙar muryarta na kuma ratsa musu kunnuwa.
Shi kuwa Moddibo ba tare da ya juyo ya kalle taba.
Ya fara kawo musu fassarar ayar.
“Allah madaukakin sarki yana cewa:
Yaku waɗanda suka yi imani, ku ambaci Allah ambato mai yawa.
Ammato kuma na haƙiƙa bawai kawai kije kiyi karatun Qura'an kara zube ko gatsa-gatsa ba, kuyi karatu kwatankwacin yadda tayi inma kunce juyawa ih zuwa irin nawa da wuya.”
Cikin sanyi Asma'u Ahmad tace.
“Malam ai karatun Khausar irin nakane, ba banbanci kawai dai, ita muryar mata kai muryar maza muna son mu koya irin ƙira'ar sosai.”
Kai ya ɗan juya ya ɗan basu baya tare cewa.
“In sha Allah zaku iya”.
Samira Sani kuwa, tattausar sajensa ta zubawa idanu cikin wani irin salo dake cikin jiki da zuciyarta.
Shi kuwa Moddibo a hankali ya kuma yin gyaran murya tare da cewa.
“A wata ayar kuwa cikin suratul A'araf aya ta 205. Allah maɗaukakin sarki na cewa...
Sai kuma yayi musu alamun suja ƙira'arar.
Cikin kauda kai Khausar ta lumshe idanu ganin wani irin masifeffen kallon daya watsa mata, wanda saida taji hantar cikinta ta kaɗa.
Cike da dagiya a fagen neman ilinta dan bata wasa kuma bata barin tsoronsa ya hanata fahimta, cikin nitsuwar da take samu in zatayi karatu tayi bismilla tare da fara jan ayar.
“Surah Al-Araf, aya ta 205:
وَاذْكُر رَّبَّكَ فِي نَفْسِكَ تَضَرُّعًا وَخِيفَةً وَدُونَ الْجَهْرِ مِنَ الْقَوْلِ بِالْغُدُوِّ وَالْآصَالِ وَلَا تَكُن مِّنَ الْغَافِلِينَ
Ta dire ayar da sauƙe nannauyan numfashi sabida tagib da taja, wanda dole ta ɗan riƙe numfashinta na kusan second 32.
Samira kuwa, wani irin malolon bakin cikine, ya tokare mata maƙoshi, sabida masifar kishi da takaicin yadda ko yaushe Khausar ke gaba dasu.
Asma'u kuwa sai murmushi takeyi,
Yayinda da yawa suke fatan Allah ya buɗa musu kwakwalensu kamar na Khausar.
Shi kuwa Moddibo a hankali ya fara fassara musu ayar.
“Abinda Allah madaukakin sarki yake cewa.
(Kuma ka ambaci Ubangijinka, a cikin zuciyarka, kana mai ƙanƙan da kai, da tsoro, ba da ɗaukaka murya a, tsaka-tsaki tsakanin asirtawa da bayyanawa da safe da kuma maraici, kuma kada ka zamo cikin falaki,.
A wata ayar kuwa, Allah madaukakin sarki na cewa.
(Da masu ambaton Allah, maza, da masu ambaton sa mata, Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma)”.
Sai ya kuma ɗan tsagaita wa tare da kallonsu yana cewa.
“Makfut?”.
“Na'am”. Suka amsa baki ɗaya,
“Ɗayyit”. Yace tare da kallon agogon hannunsa, ganin saura 9 minute lokacin da ya kamata ya sallamesu yacika ne, yasashi ci gaba da cewa
“Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace:
(Misalin wanda yake ambaton Allah da wanda baya ambaton Ubangijinsa kamar misalin rayayya ne da matacce.
A wani wurin kuma yace.
(Shin bana baku labarin mafi al'khairin ayyuka ba, kuma mafi tsarkinsu a wajen Sarkin da yake mallakarku, kuma mafi ɗaukakarsu, ga darajojinku, kuma mafi al'khairi gareku daga ciyar da zinariya da azurfa, kuma mafi al'khairi gareku daku haɗu da abokan gabanku ku riƙe dukkan wuyoyinsu kuna dukan wuyoyin suba?)
Duba Sahihul Bukhari, tare da sharhinsa Fathul Bari (11/208) Muslim ya ruwaito da lafazin:
Misalin gidan da ake ambaton Allah a cikinsa da wanda ba'a ambaton Allah a cikinsa kamar misalin rayayya ne da matacce, (1/539)
Sai Sahabbai Sukace ka bamu labari.
Sai yace musu.
(Ambaton Allah madaukaki sarki)
Kuma yace:
Allah madaukaki yana cewa:
(Ni ina tare da zaton bawana dani,
Kuma ina tare dashi idan ya ambaceni, cikin ransa, zan ambaceshi a cikin raina,
Idan kuma ya ambaceni a cikin jama'a zan ambaceshi a cikin jama'ar da ta fisu al'khairi, in ya kusanceni taƙi ɗaya, zan kusancesa kamu guda, in ya kusanceni kamu guda, zan kusancesa tsawon gaɓa guda, in yazo min yana tafiya zan zo masa ina gaggawa)”.
Sai kuma ya fesar da sassayan numfashi a hankali tare dasa tafin hannunsa ya shafa tattausan sajensa, yana mai lumshe idanunsa alamun cikekkiyar nitsuwarsa buɗe idanun yayi a hankali tare da cewa.
Tirmizi (5/459). da Ibn Majah, (2/1245). duba Sahih Ibn Majah (2/316). da kuma Sahihul Tirmizi (3/139). Bukhari (8/171). Da Muslim (4/2061) lafazin riwayar na Bukhari ne.
Cikin nitsuwa ya kuma juyowa ya fuskacesu, murya cike da kamala, da tashin lafazi yace....!
📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇
*SAKAYYAH*
Page 2
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FREE PAGE*
*LITTAFIN SAKAYYAH NA KUDINE, WANNAN FREE PAGE NE, ƳAR UWA KI BIYA KI KARANTA CIKIB AMINCI BA HAƘƘIN WANI GABA GAREKI 1k ne kacal kuɗin littafin duk da yawa shi. 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, ta nan zaku biya, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. In kuma baki da account ko matsalar Network ZAKI IYA SAYAN KATIN MTN sai ki copy number's ɗin katin ki turo min ta WHATSAPP. 09097853276. Kada ki kirani in kin san ba kayan Ɗa'a kike soba. In dai littafine kiyi min mgn a whatsapp ɗin.*
*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*
_Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun da zuƙatan mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida, kai har ma da tan kaɗen gida Shararru kuma ƙasaitattun magungunan matan dans saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata daga hannun. *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Ma'aurats ayau ma na dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki, ko ƙanwarki, ko ƴarki, ko a miniyarli, damake kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Dukansu ƙananan robobin akan dubu uku uku ne kacal Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, koriyar gumba, gumbar madara, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, dukansu a kan dubu uku uku ne ƙananan robobin, sai ta kwalli da ridi da Uku al'khairi da 3 in 1 su dubu biyar biyar ne. Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ta dawo da sabon budurci shi ƴar mitsilar robar 7k ne kana ga masin Daɗi har Maɗigan 5k ne kacal Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, 8k ne Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, su duka dubu uku uku ne, haɗin Cida kaza, kala biyu ne akwai na 18k shi yanada su tsumi da kwai da rubutu, sai kuma ɗaya haɗin shi 13k ne Ciccibi Abodi, shi 19k ne Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, duk 3k ne kana akwai maganin sanyi sadidan, wanda bani da haufi a kansu set ɗin 10k ne, rabinshi kuma 5k. Ko mai ciki zata shashi baida matsala, infection ko na cikin mahaifane yana magninsa da uzin Allah. Sai su butar sirri, audugar babbar mace, da dai sauransu...
Sai kuma fannin ƙamshi kasance da Shu'umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._ _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_
_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276. muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci idan kuna ga account no da zaku tura kuɗinku ta ciki masu son kayan Ɗa'an 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276...._
🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,
Cikin fesa sassayyan numfashi, Modibbo ya ci gaba da faɗin.
“Kuji falalar Allahu rabbil samawati garemu, ubangiji yana sonmu yana tausayin mu, yana kuma jinkanmu."
Ya dire mgnar yana ɗan sauƙe wani numfashi dan Allah ya sani ya fara jin bakinshi ya gaji da mgna. Cikin tattausan muryarsa yaci gaba da cewa.
Daga Abdullahi ibn Busr, Allah ya yarda dashi, yace:
(Ya ma'akin Allah! Shari'o'in Musulunci sunyi yawa a gareni, saboda haka ka nuna mini wani abu da zanyi riƙon da shi.
Sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa.
(Kar harshenka ya gushe yana ɗanye daga ambaton Allah.
Kuma mai tsira da amincin Allah yace:
(Wanda ya karanta harafi ɗaya daga littafin Allah yana da ladan kekkyawan aiki ɗaya, shi kuma kekkyawan aiki ɗaya yana da ladan misalin goma.
Ba ina nufin Alif lam Mim harafi bane,
A'a. Alif harafi ne, Lam harafi ne, kana shima Mim harafi ne.”.
Wani irin mayataccen kallo Samira ke bin lips ɗin Moddibo dashi, tana mai kallon dukkan yadda yake motsasu, da yadda tattausan sajensa ke zuba ƙyalli ƙawarta Ikilima Ibrahim ce ta ɗan taɓata da kafa alamun wannan wanne irin kallo ne.
Yayinda gefen damansu kuwa, wata madaidaciyar macece, Hadiza Muhammad Yahaya, wacce take cikin sabbin dalibai.
Kallon da Samira Sani keyiwa Moddibo ne ke bata mamaki.
Shi kuwa Moddibo a hankali yaci gaba da cewa.
Kuma daga Ukbatu Ibn Amir Allah ya yarda dashi yace:
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Ya fito alhalin muna cikin rumfa sai yace:
(Wannene daga cikinku zai so ya fita kullum da safe zuwa ƙoramar Buɗhan ko Aƙiƙ ya dawo da taguwa biyu masu manyan tozuna ba tare da yayi wani laifi ba ko yanke zumunta ba?
Mukace masa muna son haka.
Yace:
(Ɗayanku yaje Masallaci ya nemi sani, ko ko ya karanta ayoyi biyu daga cikin littafin Allah, mabuwayi mai ɗaukana, yafi masa taguwa uku ayoyi huɗu sun fi masa taguwa huɗu da kwatankwacin adadinsu na raƙuma.)
Kunga ashe muna ɓarar da damarmakinmu riƙe da waya ba tare da mun samu mun ribaci ilimin da iyayenmu da malanmu suka bamu ba.
Kuma mai tsira da Amincin Allah yace:
(Wanda ya zauna a wani waje, bai ambaci Allah a wajenba, wannan zai zamanto masa abin bibiya a wajen Allah, wanda ya kwanta a makwanci bai ambaci Allah a wajenba shima zai zamanto masa abin bibiya a wajen ALLAH.
Kuma mai tsira da amincin Allah yace:
(Babu wasu mutane da zasu zauna a majalisi da basu ambaci Allah a cikinsa ba, kuma basu yi salati ga annabinsu ba, face ya zamo musu abin bibiya, in Allah yaso yayi musu azaba, in yaso kuma sai ya gafarta musu.”
Jujjuya idanunsa yayi fuskarsa cike da shauƙin son Mahaikin Allah Muhammadu Rasulullah,