Header Ads
Showing 18001 words to 21000 words out of 188939 words

Chapter 7 - SAKAYYA Book 1 complete BY GARKUWA.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

Mamy bata Matsamin irin yanda kike min gsky na gaji”.
Bai jira jin amsartaba ya wuce yashiga sashen Hajiya Bunayya,
Aseeya yayar Amina na ganinsa ta saki murmushi tace.
“Umma ga babanki yazo”.
Cikin sauri Hajiya Bunayya ta fito hannunta ɗauke da glass cup na madara tana jujjugawa fuskarta da murmushi tace.
“Gashi babana madaran shanu ne mai ɗumi”.
Amsa yayi yana murmushi saboda yanayin sanyin dake garin yace.
“Nagode Umma”.
Jujjuya Glass Cup ɗin yayi kafin ya kai bakinsa da faɗin
"Bismillahi”.


Khausar kuwa jingina bayanta da jikin bango tayi kafin ta ɗaga hannunta sama cikin raunin murya tace.
"(Ya wadud³,Ya zul'arshil makin,ya fa'alillima yurid,As'aluka bi izzatil lati la yura,wa mulki kallazi la yuda)ya Allah katsare min ɗan uwana kada Hajiya Bunayya taci galaba wajen cutar dashi”.
Kafin ta shafa ta kwanta lamo agado....


A can side din kuma cikin mugun sauri Hajiya Bunayya ta riƙe hannunsa domin bokan daya basu maganin ya tabbatar musu da zaran anyi Bismillah laƙanin maganin ya karye,ta anshi Glass Cup ɗin da faɗin.
“Bari mugani kode da zafi ne kada ka ƙone bakinka”.
Kai ya girgizi tare da faɗin.
“Ba zafi Umma”.
miƙa masa ta sake yi amsa yayi ya sake kaiwa bakinsa da faɗin.
“Bismillah”, saurin karɓa ta kuma yi tare da cewa.
“Mugani kode sugar bai jibane”.
Kai ya girgizi yace.
“Kin san ba damu da zaƙiba Umma”.
yaƙe tayi da faɗin.
“bari dai na ƙaro maka sugar”.
Ta faɗa tare da shigewa Bedroom duk aƙoƙarinta na ganin ta mantar dashi Bismillah ba jimawa ta fito ta sake miƙa masa tana jujjuyawa aranta tana addu'ar Allah yasa ya manta da Bismillah. Aseeya kuwa ikon Allah kawai take gani wajen mahaifiyarta ita kuwa Amina tasan komai domin ita ta karɓo maganin wurin boka Karƙuzu.
Karɓan Glass Cup ɗin yayi yakai bakinsa kana yayi Bismillah yasha kallon Ramadan yayi yace.
“Zaka sha?”.
Kai Ramadan ya girgiza alamar a'a...
Hajiya Bunayya kam ji tayi kamar ta haɗiye zuciya ta mutu ganin maganin data kashe maƙudan kuɗi wajen amsarsu aranta tace.
“Shegen yaro mai ta ammalli da addu'a duk uwarsu ta koya musu yin addu'a akan ko wani irin abu afili kuwa murmushi tayi tace.
“Babana sugan yayi?”.
Kai ya gyaɗa mata sannan ya shanye bayan sun sake taɓa hirane ya mata seda safe ya fice...


Washe gari da safe Ummi ta nufi gidansu Moddibo domin duba jikin Innayi bakinta ɗauke da sallama tashiga cikin gidan atsakar gida taci karo da Innayi dake faman gasa nama irin wanda ake yiwa masu jegon.
Cikin sakin fuska Innayi ta mata sannu da zuwa, Murmushi Ummi tayi tare da zama ta gaisheta cike da ladabi tare da tambayarta ya jiki kana ta kama mata aikin suka gama.
Bayan sun gama ne Moddibo da M Jameel suka dawo zama sukayi tare da gaisawa Ashagwaɓe M Jameel ya dubi Ummi yace.
“Ummi bacci nakeji”.
bai jira cewarta ba ya zame ya kwanta tare da ɗaura akansa a cinyarta
Moddibo kuwa Hararansa yayi yace.
“Kaidai ba zaka taɓa girma”.
Tura baki M Jameel yayi amma baice komaiba saboda baccin dake cinsa kwanciyarsa ba jimawa bacci ya ɗaukesa ganin lokaci na tafiya yasa Ummi tace. “Moddibo bani filo ka gani”.
miƙewa yayi ba daɗewa ya fito hannunsa riƙe da pillow Ummi ta karɓa ta ɗaura kan M Jameel akai sannan ta yiwa innayi Sallama.
Moddibo ya tafi mai data bayan sun hau kwalta Moddibo ya dubi Ummi cikin sanyin murya yace.
"Dan Allah Ummi ki riƙa yiwa Asma'u faɗa ta daina ƙawance da wannan yarinyar sam bata da nutsuwa zata ɓata Asma'u da halayyarta na rashin nutsuwa yarinya nada naci in ba da gaske mukayi ba bazamu ci nasara ba da na lura ta shiga ranta koda na yiwa Asma'u magana kan tarabu da ita.
Kuma naga kamar ba zata yiba anma idan ya zamana mu biyune muke mata faɗa zata ɗauka”.
Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
“Insha Allahu zan riƙa yi mata”.
Ahaka suka isa gida ya ajiyeta sannan ya koma...




Washe gari. Ya kama Juma'a misalin ƙarfe uku Khausar na zune kan 2sitter Raudat na gefenta tana yanke mata ƙumba yayin da Mamy ke riƙe da hisnul Muslim tana Azkhar Asma'u tashigo bakinta ɗauke da sallama miƙewa Khausar tayi tare da rungumeta tace.
"Oyoyo Ƙawar arziƙi”, Murmushi Asma'u tayi cikin sigar zolaya tace.
“Fattanah kina son karya ni ko?”.
Saketa Khausar tayi tare da tura ƙaramin bakinta tace.
“Kina so mu ɓata ko?”, Murmushi Asma'u tayi tare da tsugunnawa har ƙasa ta gaisheda Momy cikin sakin fuska Momy ta amsa tana tambayarta Umminta ta bata amsa da.
“Tana lafiya, Momy tace ma in gaidaki”.
Cikin sakin fuska Momy tace.
“Ina amsawa”.
Ita kuwa Asma'u cikin girmamawa tace.
“Ayyah Momy in ba abinda Khausar zatayi miki ta rakani mana Ummi ta aikeni kuma banason zuwa ni kaɗai”.
Sanin Asma'u yarinya ce me tarbiya da nutsuwa uwa uba kamun kai yasa Momy amincewa.
Kai ta gyada mata tare da cewa.
“Toh kada dai ku daɗe ku kuma kula da kanku banda kula maza”.
Cikin jin dadi Asma'u tace.
“In sha Allah kuwa Momy”.
Ita kuwa Khausar murmushi tayi tare da cewa.
“To ni baki nemi izinina ba”.
Ta ƙare mgnar tana
Shiga Bedroom ɗin ta, murmushin Asma'u tayi tare da bin bayanta kana ta langwaɓar da kai tace.
“Ayimin afuwa ƙawar arziƙi”.
Hira suka ɗan fara taɓa sannan Asma'u ke sanarwa mata zata raka unguwar Teku ta kai saƙo Ummi ta aiko cikin zumuɗi da son fita ta miƙe tare da ɗaukan dogon hijab maroon colour tasa akan riga da wondon dake jikinta ba tare data tambayi inda zata jeba tace su tafi dan kawai tana masifar son unguwar Teku...


Aɓangaren Moddibo kuwa bayan ya dawo daga sallar la''asar,
Side ɗinsa ya wuce,
Ruwa ya watsa tare da sauya kayan jikinsa, wani tattausan riga da wondo nevy blue mai taushi ya zira, tare da fesa turarensa oud jannah mai masifar ƙamshi,
System ɗinsa da wayarsa ya ɗauka kana ya fito, a hankali ya lumshe idanunsa jin yadda sassanyar iskar ke ratsa cikin tattausan sumar kansa da yana iya kwana biyu bai cire hulaba.
A hankali yake taka steps din yana sauƙowa ƙasa wani irin masifeffen kyau yayi collor kayan jikinsa yayi matuƙar amsarsa farar fatarsa ta ƙara bayyana, yayinda tattausan sajensa yayi lib-lib gwanin burgewa jajayen lips ɗinsa dake cikin zagayen sajensa da kota million ɗinsa sai sheƙi sukeyi, a hankali yake taka tattausan silifas dake sawunsa.
ya nufi can gefen yamma inda wasu kyawawan bukoki na zamani da yake wajen hutuwansa,
Wurine mai kyau da ban sha'awa a hankali ya zauna bisa ɗaya daga kujerin dake cikin bukkar da tafi sauran ƙawayuwa da flawers.
A hankali yake motsa lips ɗinsa alamun yana tasbihi yalwataccen sumar kansa kamar na larabawa na sheƙi da ɗaukar ido idanunsa na lumshe yana motsa bakinsa a hankali.




Cikin nutsuwa Asma'u da Khausar suka fito duk da rawan kai irin na Khausar komai nata anitse takeyi cikin nutsuwa suke tafiya yayinda hijabansu yarufe har takalmansu adedeta suka tara tare da sanar dasu inda ze kaisu.
Tafiyar Mintuna ashirin da biyar sukayi suka isa aƙofar gidan.
A gaban gate ɗin adedeta ya ajiyesu.


Asma'u ce agaba tasa hannunta da babu komai ta tura ƙofan gate ɗin yayin da ɗaya hannu ke riƙe da Kula wanda Ummi ta yiwa Innayi dambun naman kaza.
Cikin wani irin shauƙi Khausar ke bin ilahirin gidan da kallo ganin yanda flowes da shuke shuken kayan marmari suka zagaye gidan tamkar garden,
Da sauri ta juyo da kallonta kan Asma'u tare da cewa.
“Wooow masha Allah.
Kai Asma'u wannan gidan waye haka? gaskiya yayi kyau sosai”.
ta ƙare mgnar tana lumshe idanunta tare da shaƙar sassayan iskar dake haɗe da ƙamshi flawers da kuma turare jikin Moddibo.
Kana ta riƙa bin fulawowin tana shafa duk wanda hannunta ya sauƙa akai saita tsinke takai hancinta kana taja dogon numfashi tare da lumshe ido.


Shi kuwa Moddibo tun ƙarar buɗe gate ɗin da yayi ya ɗago kansa yana kallon wajen.
Cikin mamaki yace
“Khausar Usman Lelelwal a gidan nan”.
Hannunsa yasa ya tallabe habarsa tare tsuke fuskarsa.
Ita kuwa Khausar cike da shauki ta buɗe hannunta tare da jujjuyawa har hijabinta na buɗuwa cikin ɗan ɗaga sauti tace.


“Agaski Asma'u gidan nan ya min komai na ciki sun burgeni gawani irin ƙamshi da suke, ji yanda ilahirin gidan ke fitar da wani ni'imantaccen ƙamshi.
Gaskiya gidan nan shine aljannar duniya da alamu kuma mutanen ciki maƙurane wajen tsabta ina son komai na gidan nan”.
Asma'u Kam dariyar dake cinta take ƙunshewa ta tabbata da Khausar tasan cewa gidansu Moddibo ne babu dalilin dazai kawota sannan ta tabbata yau juma'a ya irin wannan lokacin Moddibo na gida babu inda zeje.


Ita kuwa Khausar juyi ta cigaba da yi tare da sauri ta nufi side din Moddibo steps din ta fara tattaunawa tana shafa furannin dake jere a kan.
Saida ta hau har tsakiyar barandar kana ta juyo ta fuskanci yama.
“Wooww Masha Allah Asma'u zo ki hau ki gani wlh ina hango bakin Teku kinga yadda ruwa da tsuntsaye keyi!".


Ita dai Asma'u hannunta tasa ta rufe bakinta tana murmushi.
Yayinda tun shigowarsu Moddibo ya zuba musu idanu saidai sam su basu lura dashi ba,da gudu Khausar ta juya ta fara taka steps din tana sauƙa ta nufi sashen da Moddibo ke zaune tana faɗin.
“Wowww gaskiya wannan gidan yayi mugun yimin kyau da ace zan rayu a ciki da wanda raina zaiso zan meda mishi gidan tamkar dausayin farin cikin duniya”.
Cikin danne dariya Asmau tace.
“Khausar zomu tafi mana”.
kai Khausar ta girgiza tace.
“A'a ki tafi ni wlh saina cire inabin can da Appel kije kawai”.
Ahankali Asma'u tace.
“Kizo muje mugaida Innayi sai mu gaya mata kafin ki cire”.
dan tasan a irin wannan lokacin tabbas Moddibo na nan shiyasa take mgn a hankali wai dan kar ya jisu.
Kai Asma'u ta dafe tare da cewa.
“Idan masu gidan kuma suka zo suka sameki fa?”.
Taɓe baki Khausar tayi tace.
“Gida kamar wannan masushi bazasuyi rowa ba, kuma ai nan kamar babu kowa babu wanda zaizo”.
ta faɗa tana komawa inda inabi yake tasa hannu ta fara tsinka tana tsalle jin hijabinta zai takurata ne yasa ta zare hijabin tare da ajiyeshi kan kujerar dake ƙasan bishiyar.
Middibo kuwa dafe kunci yayi yana ganin ikon Allah Aransa yace.
“Yarinya kamar ba mace ba dubi yanda take tsalle kamar biri wannan ba budurciba abinda yafi budurcima zata watsar domin yasan illar hawa bishiya yakan buɗa mace duk da cewa ita ba hawan tayi ba.
Tunaninsa ne yakatse asanda ta nufi bishiyar Appel tsalle tayi da niyyar tsinkowa dan bishiyar Appel irin yan masaƙaitan nanne,
tsalle ta kuma yi amman ta kasa ga dai hannunta na taɓawa sede baza ta iya tsinka ba.
tattare gashinta tayi tare da dan mai dashi bayan wuyanta kana ta nannaɗe ƙafar wandonta,
tsalle tayi tare da kamo rashen da yafi kusa,
sai kuma ta hango wasu a can sama haka yasa ta fara taka jikin bishiyar har ta hau bisa rashen duk da ba wani tsowone da shiba,
Cal sai gata akan bishiyar.


Cikin tsananin takaici da sassarfa ya mike tare da nufar wajen, yasan koda yace zeyi mata tsawa muryarsa baze fita ba saboda bashida da amo mai karfi sannan yasan dai baya cikin tarbiyya mai.kyau ƴa mace tai ta hawe-haween bishi yana isa bakin bishiyar ya tsaya tare da harɗe hannayensa aƙirji kafin yayi magana ta juyo da niyyar kai hannu zata tsinki appel sukayi ido huɗu dashi ido cikin ido sukayi kamar yadda damisa kan iya tsare kenwa da ido haka yayi mata.


Cikin tsananin firgici da tsoro da kaduwa tace.
“Hasbunallahu wani'imal wakin,
Aizubillahi Minal shaiɗanirrajim, innahu min sulaimanu wa innahu Bismillahir rahmanir rahim”.
Cikin tsananin tsoro take jera addu'o'in domin gani take shin fatalwane ko kuma aljan yazo mata asuffarsa cikin kiɗima da firgici ta rikito tayi ƙasa ta faɗo gababsa yayin da hannayenta suka sauƙa akan.....!




*SAKAYYAH*
_Page 4_


*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*Free page*


*KADA DAI KU MANTA WANNAN FREE PAGE NE, KI KI BIYA KI KARANTA CIKIB AMINCI BA HAƘƘIN WANI GABA GAREKI SAKAYYAH 1k ne kacal ƴar uwa. 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA. Sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276*




*Al'bishirunku Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA*






Tana dirowa hannunta dake dungule da Appel suka sauƙa kan ƙafarsa.
Yayinda yatsun hannunta dake ɗauke da zoban azurfa na kusa da da ƙaramin yatsa da kuma ƙaramin suka sauƙa akan faratun yatsun sa,
atake yatsun hannunta suka bada sautin ƙash! yayin da shi ma Moddibo yatsun ƙafansa suka bada sautin ƙas-ƙas!, Idanshi ya rumtse da sauri, sabida wani irin masifaffen zogi da yaji ya ratsa sa cikin sauri ya tsugunna da niyyan matsasu tuni ɗanƙwalin ta ya zame yalwataccen sumar kanta baƙi daya sauƙa zuwa kafarɗarta ya zubo yana fitar da wani sihirtaccen ƙamshi...


Khausar kuwa jin zafin daya ratsa ƙafarta data malkoɗe ne yasa ta furta.
“Wayyyo Allah ƙafata!”. ta faɗa da ƙarfi tare da ɗago kanta yayin da yalwataccen sumar kanta ya rufe mata fuska da sauri tasa hannu ta janye ta ɗago kanta.
Idanunta ne suka sauƙa akan Moddibo dake durƙushe, cikin ruɗewa da tsanananin tsoronsa ta ɗauki ɗan kwalinta kana ta miƙe da gudu tana cewa.


“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n dan Allah kayi haƙuri wallahi Allah bansani ba”.
Ta faɗa tana ƙoƙarin fita daga gate ɗin.


Asma'u kuwa fitowarta daga gate ɗin da zai sadaka da cikin farfajiyar Innayi kenan ta hango Khausar na shirin fita babu ɗan kwali akanta.
Cikin Sassarfa tabi bayanta tana faɗin.
“Khausar! Khausar!! Khausar!!!”.
ta kira sunanta har sau uku Kafin ta sake cewa.
“Dan Allah kada ki fita ahaka Khausar ki tsaya”.


Moddibo kuwa cikin yanayin nutsuwarsa da kuma sanyinsa ya kira sunanta da faɗin.
“Asma'u”.
Saidai akwai alamun ɓacin rai acikin sautin Muryansa.


Atsorace Asma'u ta juya Idanunta cike da tsoro tace.
“Na'am Yah Moddibo”.
Tsayuwarsa ya gyara tare da lumshe idanunsa masu ƙwarjini da haiba kana ya buɗe su ya dubi Asma'u da har yanzu take tsaye da tsoro a idanunta yace.
“Meyesa zaki ɗauko Biri ki kawo mana gida!?”.
Ya ƙare mgnar da bin Khausar da ido wacce tuni ta kai bakin gate.


Asma'u kuwa saurin ɗagowa tayi ta dubesa jin ya kira Khausar da Biri saidai bata yarda sun haɗa ido ba.
Shi kuwa cike da takaici
ya cigaba da cewa.
“Koda wasa kada ki sake zuwa da wannan yarinyar gidan nan, tunda ita bata da hankali da kuma nutsuwa da kamun kai”.
Ya ƙarashe mgnar yana mai lumshe idanunsa dake cike da ƙwarjini har zuwa sannan yatsun ƙafar na masa rawa tamkar alokacin ta buga masa yatsunsa.


Ajiyar zuciya Asma'u ta sauƙe ganin tuni Khausar ta fice kanta a ƙasa tace.
“Dan Allah kayi haƙuri Insha Allah hakan bazai sake faruwa ba”.
Moddibo kuwa baice da ita Komai ba saima lumshe idanunsa da yayi yana motsa laɓɓansa alamar tasbihi yaci gaba da yi.


Ita kuwa Asma'u jin baice komai ba yasa ta juya cikin sassarfa ta nufi gate dan bin bayan Khausar...


M Jameel dake zaune cikin falon Moddibo kuwa wanda ya tsirawa window idanu yana ganin duk abinda ya faru ya saki lallausan murmushi tare da miƙewa yana gyara zaman Farin t-shirt da blue jeans dake jikinsa kana ya sanya hannu ya buɗe ƙofan falon ya fito fuskarsa ɗauke da ƙayataccen murmushi cikin yanayin sa na ƙaunar Amininsa yace.
“Ba sa ido ba?,ka fita sabgar yarinya ka ƙi yanzu inba sa'a ba kasa taji ciwo dan naga lokacin da take gudu tana ɗin gishi”.
Moddibo kuwa buɗe idanunsa dake lumshe yayi tare da zab gawa M Jameel Harara cikin yanayin nutsuwarsa daya zame masa jiki yace.
“Dama karyewa tayi da shi yafi yarinya bataji bata da hankali ko kaɗan”.


Da gudu Asma'u ke bin Khausar tana cewa.
“Khausar ki jira ni mana”.
Ƙin tanka mata Khausar tayi tana cigaba da sassarfa yayin da ko wani gaɓa na jikinta ke rawa kana tana cigaba da ɗaure gashinta daya baje kasancewar unguwa ce da babu hayaniyar mutane yayin da take yarfe hannunta dake masifar zugi kana tana me ɗingisa ƙafarta.
Ganin da gaske Khausar ba zata tsaya ba yasa Asma'u ta ƙara gudunta har ta isa inda take tana sauƙe numfashi saboda gudun da tayi tace.
“Ayyah Khausar ki tsaya mana ga hijabinki saka”.
Hannunta tasa ta amshi hijabin nata tare da zirashi a jikinta kana taci gaba da tafi.
“Ayyah Khausar ki tsaya mana”.
Asma'u ta kuma faɗa tare da shan gabanta,
a raunane tace.


“Bazan tsaya ba Asma'u meyesa zaki min haka Asma'u? banyi tsammanin zaki yimin haka ba gidansu Moddibo kika kawoni mutumin da kin san baya ko son ganina.
Gashi yanzu kinsa na buga masa yatsuna masu zobe aƙafa naji masa ciwo,yanzu bansan wani irin hukunci zai ɗauka akaina ba”.


Tsoron Khausar ɗaya kada Moddibo yace zai zaneta duk irin rashin ji da ƙiriniyarta tana matuƙar tsoron bulala kana tasan duk hukuncin da Moddibo zai ɗauka bazai wuce yasa Malam Bello ya zaneta idan taje Hadda.


Cikin sanyin murya Asma'u tace.
“Ayyah Khausar kiyi haƙuri, amman kuma ai da kinji mgnata da haka bai faruba. kece bakya ji sannan ba kyaso ataɓa lafiyar jikinki”.
Kallonta Khausar tayi da Idanunta dake cike da tsoro da kuma fargaba tace.
“Meyesa zaki ce haka Asma'u kawai naga Appel da inabin ne ya ban sha'awa shiyasa na cira”.


Kai Asma'u ta girgiza tace.
“Inabi Khausar? na tabbata duk wannan abubuwan da kika gani akwai su a gidanku ku fiye ma da hakan”.


Sake Marerece fuska Khausar tayi tace.
“Na ganine ya bani sha'awa laifi ne dan na cire!?”.
Murmushi Asma'u tayi ganin har zuwa lokacin Atsorace Khausar take sai kuma tace.
“Kema dai baki jira kanki ba daga zuwa gidan mutane sai ki fara cire musu abu batare da neman izini ba”.


Ita kuwa khausar jin abinda Asma'u tace yasa ta watsa mata Harara cike da tsiwa tace
“Tun da kinsan gidan masu baƙin hali zaki je Meyesa zaki ɗaukeni ki kaini?, Kisa aranki daga yau babu inda zan sake rakaki tunda haka kikayi min”.


Wara ido Asma'u tayi sai kuma ta langwaɓar da kai tace.
“Kiyi haƙuri Khausar bansan haka zai faru ba ni kawai da

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads