Header Ads
Showing 138001 words to 141000 words out of 188939 words

Chapter 47 - SAKAYYA Book 1 complete BY GARKUWA.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

yanda yake baccin cikin kwanciyar hankali tamkar yana murmushi kyawun fuskarsa ya sake nunkuwa fiye da ko yaushe.


Asma'u data fito daga kichen ta kalli Ummi kana ta saki murmushi tare da cewa.
“Kayyy Ummi irin wannan kallon sai kace kin samu TV ”.
Sai asannan Ummi ta ɗauke Idanunta daga kansa ta mayar kan Asma'u tare da yi mata daƙuwa.
Murmushi Asma'u tayi kana tace.
“Ai gaskiya ne”.
Bashir daya shigo Bedroom din yayi dariya kana yace.
“Gsky dai Ummi kwanan nan kina yawan kallon Yah Jameel ko dan yafi mu kyaune?”.
Wara ido tayi tare da sakin murmushi kana tace.
“Waya faɗa maka yafi ka kyau ai kafisa”.
Murmushi yayi kana yace.
“Ummina kin dai faɗa min inji daɗi ne kawai”.
M Jameel kuwa cikin bacci yake jiyo hiransu sama-sana ahankali ya motsa.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da kallon sa kana tace.
“Toh katashi kayi Breakfast. Idan yaso sai ka koma baccin”.
Cikin sauri ya buɗe Idanunsa tare da Kallon Ummi kana yace.
“Uhmmm Ummi sai anjima”.
Kansa ta shafa kana tace.
“A'a tashi kaci abinci, bana son bacci da yunwa Babana”.
Hannunta ya riƙe kana yace.
“Naji daɗina Ummina ta kirani da Babana Abbana ya kirani da Babana”.
Miƙewa yayi ya zauna tare da cewa.
“Ummina banyi wanka ba sannan banyi brush ba ba zan iya Breakfast ba”.
Girgiza kai Ummi tayi tare da faɗin.
“Aikam dai gashi tun ɗazu na bawa Bashir kuɗi ya sayo maka Brush kafin ka tashi ga Brush ga Maclean kayi”.
Miƙewa yayi kana ya ɗauka, toilet dake falon yashiga ya wanke bakakinsa.
Asma'u kuwa tun shigansa toilet ta Miƙe tankwaso musu kayan Breakfast ɗin yau ma kamar jiya haka atare sukayi Breakfast ɗin.
A hankali ya kai kofin tea bakinsa sai kuma yayi sauri ajiye cup din jin wayarsa ta hau ruri Asma'u dake kusa da wayar ta miƙa masa karɓa yayi tare da sakin murmushi kana yayi Picking tare da cewa.
“Assalamu Alaikum A.J”.
Daga ɗaya ɓangaren Moddibo ne yace.
“J yana jika shiru gashi Innayi ta haɗa mana Breakfast na kasa ci ni kaɗai”.
Murmushi M Jameel yayi tare da kallon Ummi, Asma'u,da Bashir kana yace.
“A.J gani tare da Ummina da Asma'u da kuma Bashir muna Breakfast tray ɗaya kamar yanda mukayi jiya, ina jin farin ciki inaji kamar wani gurbi na cike wanda ban samu damar cike saba tsawon shekaru”.
Lumshe idanu Moddibo yayi kana ya gyaɗa kansa tabbas ya fahimci farin cikin da M Jameel ke ciki ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa.
“Shikenan hakan yayi kyau bawa Ummina mu gaisa”.
Kai M Jameel ya gyaɗa tare da miƙawa Ummi wayar.
Cike da so Ummi tace.
“Babana na ƙwace maka Amini ko?”.
Murmushi Moddibo yayi wanda take iya jiyo sautin sa kana cike da ladabi yace.
“Ayyah Ummina bakomai ai kawai ina kewar sa ne Ina kwana?”.
Murmushi tayi tare da faɗin.
“Lafiya Lau ya Innayi?”.
Ahankali yace.
“Tana lafiya tace agaishe ki”.
Daga haka sukayi sallama tare da katse kiran Bayan sun kammala Breakfast ɗin Asma'u ta tattare kwanikan kare da kaiwa kichen kana ta dawo ta gyara wajen.
M Jameel kuwa jingina kansa da guiwar Ummi yayi kana suka cigaba da hira cike da tsananin ƙaunar junansu...!








*Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276*




By
*GARKUWAR MARUBUTA*


SAKAYAH


26


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇






Isrnejg. Acan ɓangaren gidan Lamiɗo kuwa Ramadan ya fito daga Bedroom da gudu kai tsaye Bedroom din Mommy ya nufa afalo suka ci karo da Hajiya Bunayya wani irin kallo tabisa dashi dai-dai lokacin da Khausar ta fito sanye cikin riga da skirt na less ɗinkin ya zauna ɗas ajikinta kana ta sanya Blue Black hijabi mai Facemaks jikinta na fitar da sanyayyan ƙamshin turaren Oud Ma'aruf fuskarta ɗauke da simple Make-up.
Cak ta tsaya tare da kallon Hajiya Bunayya data tsirawa Ramadan idanu ganin tsayuwar Khausar yasa Hajiya Bunayya sakin murmushi tare da cewa.
“Ikon Allah Ramadan ƙafa tayi sauki sosai”.
Sai kuma ta juya tana cewa.
“Ki cewa Aysha ankawo kayan tazo ta gani ta zaɓa mana”.
Girgiza kai Khausar tayi tare da kallon Ramadan dake cewa.
“Addah Khausi ƙafana tayi sauƙi”.
Murmushi tayi tare da shafa kansa kana tace.
“Alhamdulillah Ramadan amma ka daina wannan gudun har yanzu ƙafanka baiyi ƙwari ba”.
Kai ya gyaɗa mata kana yabi bayanta zuwa Bedroom ɗin Mommy bakinsu ɗauke da sallama.


Ƙara sawa Ramadan yayi tare da faɗawa jikin Mommy kana yace.
“Mommy ƙafana yayi sauƙi badan Addah Khausi tace kar inyi gudu ba da nayi kin gani”.
Murmushi Mommy tayi tare da shafa kansa kana tace.
“Masha Allah mun godewa Allah, ka riƙa bi ahankali insha Allah zaiyi sauki”.
Khausar na murmushi tace.
“Mommy zanje gidan su Asma'u”.
Kai Mommy ta gyaɗa kana tace.
“Toh Allah ya kiyaye ki gaishe su amma kada ki daɗe Allah ya tsare”.
Kai ta gyaɗa kana ta fice.


Tare da Sallama ta ɗan tura ƙofar Falon.
Tana shiga Idanunta ya sauka akan M Jameel dake zaune kan 2 sitter murmushi ta sakar masa kana tace.
“Laa Yah Jameel”.
Murmushin ya maidamata tare da faɗin.
“A'a Lelewal kece yau agidanmu?”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Eh mana Yah Jameel na kawowa Ummi ziyara ne kuma nayi kewar Asmeey”.
Wara ido yayi tare da cewa.
“Iyeee Lelewal wato wariya zaki nuna min ni bakiya kewata ba? Rabona dake tun randa kuka karkare makaranta fa”.
Rufe fuska tayi tare da cewa.
“Kai Yah Jameel nayi mana, duk makarantar ma nayi missing ɗinta da kowa nata”.
Murmushi yayi kana cikin yanayin fara'arsa yace.
“Yanzu naji bayani amman harda Modibbo kinyi kewarsa?”.
Da sauri ta tura baki tare da cewa.
“Kewar masu sona nayi banda maƙiyana”.
Dariya mai sauti yayi tare da cewa.
“Maƙiyi kuma, kai a'a kam Lelewal”.
Ita dai Khausar juyawa tayi ta kalli Ummi
kana tace.
“Ummi ina yini?”.
Cike da kulawa Ummi tace.
“Lafiya lau ya Ramadan da ƙafa?”.
Gyara zama Khausar tayi kana tace.
“Yaji sauƙi Ummi yanzu yana takawa ko ina”.
Atare suka ce Masha Allah Ubangiji Allah ya ƙara sauƙi”.
Murmushi tayi kana tace.
“Ameen”.
Kana suka ci-gaba da hira wanda duk mafi yawan hiran nasiyya M Jameel yake musu kan sukula da rayuwar duniya kana suka sance masu riƙe al'ƙawari tare da kare mutuncin su.
Ganin rana ya fara yasa Asma'u ta kalli Khausar tare da cewa.
“Khausy mushiga kichen muyi girki”.
Kai Khausar ta gyaɗa tare da miƙewa ta cire hijabinta tabi bayan Asma'u abakin ƙofar ta tsaya tare da juyawa falon kana cike da kulawa tace.
“Yah Jameel mai za'a dafa maka?”.
Murmushi yayi kana yace.
“Duk abinda kika dafa min Khausar ina so zanci”.


Jinjina kai tayi tare da sakar masa da murmushi kana tace.
“Toh shikenan Yah Jameel Insha Allah zanyi maka abinda zaka so da izinin Ubangiji”.
Khausar na shiga kichen suka fara aikin cikin nutsuwa da ƙwarewa Dambun shinkafa da yaji Vegetables suka Atake kichen ɗin ya gauraye da ƙamshi Warmers me kyau ta ɗauka ta zuba masa kana ta ɗauki Bowl ta haɗa masa Fruit Salat mai sanyi sannan ta ɗaura Ababban faranti ta fito.


Kallon M Jameel dake hira da Ummi tayi kana tace.
“Yah Jameel gashi na kawo maka”.
Wara ido yayi kana fuskarsa ɗauke da murmushi yace.
“Wai Lelewal duka Ni kaɗai?”.
Kai ta gyaɗa masa kana tace.
“Eh aina Malamina ne yanzu ma zan gasa maka nama gashin tukunya”.
Jinjina kai yayi tare da cewa.
“Lallai Khausisi naji daɗina na dafa tudu biyu ga Malami sannan kuma yaya saura cikon tudun dafawa na uku”.
Murmushi tayi tare da zama gefensa kana tace.
“in sha Allah in akwai na huɗuma duk zaka taka Yaya Jameel”.
Yana sa Fruit Salat abakinsa ya lumshe Idanunsa kana ya kalli Khausar tare da cewa.
“Uhm Yummmy na daɗe bansha Fruit salat mai daɗi irin wannan ba Lelewal da alama dai na musamman ne”.
Asma'u data fito daga kichen ta wara ido kana tace.
“Kai Yah Jameel har nawa?”.
Kai ya jinjina mata tare da sanya dariya kana yace.
“Iyee sosai ma Asmeey nifa yau komai jinsa nake na daban, girkinma tun tuni yake cika min hanci da ƙamshi”.
Kallon yanda yake dariya Khausar tayi wanda har ya bayyanar da Fararen haƙoransa kana idanunsa alumshe haskensa ya sake bayyana kana sajensa sunyi luf-luf suna sheƙi.


Ajiyar zuciya ta sauƙe still Fuskarta ɗauke da murmushi tace.
“Yah Jameel kaima yau na da banne kyawunka ya sake nunkuwa tamkar Balarabe”.
Bashir da Asma'u kuwa haɗa baki sukayi wajen cewa.
“Wallahi kuwa Muma duk akwanakin nan haka muke kallonsa”.
Wara ido yayi still Yana Shan Fruit Salat ɗin yace.
“Uhm ko dai dan na kusa Aure ne yasa kuke kallon kyawuna”.
Saurin Kallonsa Ummi tayi tare da cewa.
“Sai kace gobene auren.
Murmushi yayi tare da faɗin.
“Uyumm Ummina”.


Sai kuma ya maida Kallonsa kan Khausar tare da cewa.
“Lelewal zaman gida ya kusa ƙarewa ko?”.
Kai ta jinjina tare da cewa.
“Eh Yah Jameel Insha Allah result ɗin mu na fitowa za'a samomin Admission”.
Jinjina kai yayi tare da cewa.
“Masha Allah, haka muke fata, ku dai kiyaye ku tsare mutuncinku a duk inda kuka riski kanku”.


“Insha Allah Yah Jameel na maka alƙawari zan kasance fiye da hakan ma”.


Kallon Asma'u Ummi tayi tare da cewa.
“Kawo mana abincin muci”.
Kai Asma'u ta gyaɗa tare da miƙewa ta zuba musu ababban faranti Khausar kuwa drinks ta kwaso musu.
Kana suka zauna kallon Ummi M Jameel yayi tare da langwaɓar da kai kana yace.
“Ummi ya aka cire ni adangi gaskiya nima ajuye muci tare”.
Murmushi Khausar tayi tare da cewa.
“Toh Yah Jameel bari na zuba mana”.
Ta faɗa tare da juye nasa akan faranti kana suka zauna tare da sanya farantin Atsakiyarsu Ummi da Khausar na facin juna Asma'u da M Jameel na facing juna haka suka gama cin abincin cike da nishaɗi.


Suna gamawa ana kiran sallar Azahar M Jameel ya Miƙe tare da shiga toilet ya ɗaura alawala kana ya nufi masallaci Asma'u da Khausar kuwa wajen suka gyara tare da kwashe kwanukan suka kai kichen kana suka wuce Bedroom ɗin Asma'u suka ɗaura alwala tare da gabatar da sallah bayan sun idar suka fito zuwa falo.


Bayan an isar da salla.
M Jameel yana shigowa ya kalli Ummi dake zaune kan 2sitter kana yace.
“Toh Ummi zan tafi ina jin jikina aɗaɗɗaure tun jiya da daddare fa rabona da wanka ji nake kamar nayi wata banyi wanka ba”.
Cikin sauri Khausar ta miƙe tare da cewa.
“Yawwa Yah Jameel dan Allah ka sauƙeni agida Mommy tace kar in daɗe”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Toh Lelewal muje mana”.
Kai ta gyaɗa tare da riƙe hannun Asma'u kana suka fita.


Ummi kuwa haka nan ta tsinci kanta da ɗago kai ta zuba masa Ido batare da tace komai ba.
Ahankali ya kalli Ummi ganin shi take kallo yace.
“Ya dai Ummina?”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da girgiza masa kai kana tace.
“Bakomai ba zaka bari sai anjima ba?”
Girgiza kai yayi tare da cewa.
“Um-um Ummi ina so in tafi sauri nake”.
Cikin sanyin murya tace.
“Toh saurin me kake?”.
Langwaɓar da kai yayi kana yace.
“Toh Ummi banyi wanka bafa ba kuji na fara tsami ba?”.
Wara ido Asma'u tayi tare da sanya dariya kana tace.
“Ƙamshi dai kake Yah Jameel”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Gwara dai Inje inyi wanka”.


Dai-dai lokacin wayarsa ta hau ruri yana cirowa yaga Moddibo murmushi yayi tare da kallon Ummi kana yace.
“Kinga fa Moddibo na kira na yanzu zaice ko Breakfast baiyi ba yana jirana, haka yake dake cin abinci bai damesa ba idan bana nan sai yace yana jirana, yaita takura min da kira idan kuma ina nan yaƙi ci”.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Toh yanzu tafiya zaka yi?”.
Kai ya gyaɗa tare da faɗin.
“Eh Ummi”.
Cikin sanyin murya tace.
“Toh ka kira Baban nawa yazo nan kuci abincin”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Ummi zan tafi Insha Allah da yamma zan zo musha hiran mu”.
Sai kuma ya matsa kusa da ita tare da ranƙwafawa kanta ya kai bakinsa dai-dai kunnenta kana yace.
“Ummi sai anjima da daddare zanzo insha Allah musha hiran mu sannan in faɗa miki matar da zan Aura da kuma matar da na zaɓawa A.J na”.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Toh shikenan Babana Allah ya kai ka lafiya ya dawo min da kai lafiya Ubangiji Allah yama SAKAYYAH da mafificin Aljanna”.
Murmushi yayi tare da durƙusawa agabanta cike da jin daɗin Addu'ar ta yace.
“Ameen Ummina Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.
Ummi kuwa hannu ta sanya acikin sumar kansa tana shafawa kana tace.
“Allah ya rufa maka asiri duniya da lahira Allah yasa kagama da duniya lafiya Allah yasa Aljanna ce makomarka Allah ya tsareka da dukkan sharrin abinƙi Ubangiji ya raba ka da sharrin mai sharri”.
Tafin hannunta ya riƙe kana yace.
“Allah ya amsa addu'o'in ki Ummina, shiyasa nake da yaƙinin cewa duk abinda ya sameni, na tabbata ƙaddarar ce da Ubangiji ya rubuta minne amma addu'ar ki ba zai taɓa bari wani mummunan abu yasame niba Nagode sai dai in daga Allah ne”.
Bashir daya shigo kuwa Ido ya zuba musu yana kallon yanda Ummi ke sanya masa albarka tare da adduo'i shi kuma yana Amsawa da Ameen.
Da sauri ya isa ya durƙusa gefen yayan nashi tare da cewa.
“Ayi addu'o'in damu”.
Murmushin Ummi tayi tare da shafa kansu,l.
Asma'u da Khausar kuwa tuni suka fita suna jira ganin shiru bai fito bane yasa Khausar leƙawa Falon kana tace.
“Yah Jameel baza mutafi ba. Mommyna fa tace kada in wuce Azahar”.
Kai ya gyaɗa tare da faɗin.
“Gani nan zuwa Lelewal”.
Kai Khausar ta gyaɗa kana suka cigaba da hira da Asma'u.
M Jameel kuwa fita yayi har ya isa baranda sai kuma yayi baya tare da leƙawa falon kana yace.
“Ummi yau ba rakiya ne ko dan bamu zo da Babanki bane?”.
Ummi kuwata
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da Kallonsa kana tace.
“Na'am Jamilu”.
Langwaɓar da kai yayi kana yace.
“Ummi yau dai dan ban zo da Babanki ba ba rakiya”.
Murmushi tayi tare da faɗin.
“Toh muje in rakaka Babana”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Toh Nagode”.
Sannan suka fita afalon kai tsaye jikin motarsa ta nufa ta buɗe masa.
Murmushi yayi tare da shiga kana ya maida kallonsa kan Bashir tare da cewa.
“Bashir yau dai na ƙwace maka fadar ka”.
Murmushi Bashir yayi tare da kallon M Jameel kana yace.
“Ba komai Yah Jameel na bar maka lokacin kane ai”.


Ahankali Ummi ta tura Murfin motar tare da rufewa.
M Jameel kuwa Ido ya zubawa Ummi ta ɗan tsakanin glass din Motar batare daya jaba Itama Ummi Idanu ta zuba masa tare da juya masa hannun alamar ya dai?.
Sauƙe glass ɗin motar yayi tare da sanya babban yatsan sa acikin bakinsa yana ɗan ciza farcen a hankali.
Cikin tsare sa da ido tace.
“Ya dai?”.
Sauke glass ɗin motar yayi tare da zuba mata Ido.
Girgiza mata kai yayi still baice komai ba.
Matsawa jikin Glass din tayi kana tace.
“A'a wai meye haka?”.
Ƙasa cewa komai yayi still Idanunsa na kanta.
Sunkuyawa jikin Glass din Motar tayi kana tace.
“Ya dai?”.
Ahankali ya lumshe idanunsa tare da jan dogon numfashi kana ya fesar cikin rawan murya yace.
“Ban sani ba Ummi”.
Da mamaki tace.
“Baka sani ba kuma?”.
Kai ya gyaɗa mata still ya tsansa na bakinsa.
Cike da kulawa tace.
“Toh me kake so?”.
Juyawa yayi ya kalli faɗin ilahirin gidan nasu kana ya kalli Asma'u da Bashir sai kuma ya dawo da Kallonsa kan Ummi kana yace.
“Ummi ku nake so”.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Kai ko Jameelu ba'a rabaka da zolaya”.
Ta faɗa tare da kallonsa tsakiyar idanunsa ga mmkinta sai taga still baiyi murmushi ba kamar yanda ya saba ba.
Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.
“To ko dai ka manta wayar kane?”.
Hannu ya sanya tare da shafa aljihun gaban rigarsa still yatsansa na cikin bakinsa yana gyatsawa a hankali kana yace.
“Um-um Ummi ban manta wayata ba gashi a aljihuna”.
Cikin yanayin damuwa da jinƙai irin na mahaifa tace.
“Toh Meye ne?”.
Kanshi ya ɗaura a kan hannunta dake kan glass ɗin motar, tare da lumshe idanunsa kana ya janyo tafin hannunta ɗaya ya kife akan goshinsa tare da buɗe lumsassun idanunsa da suke sheƙi, shiru yayi kamar mai nazari.
Sai ya kuma lumshe idanu.
Khausar dake gefe tayi dariya tare da cewa.
“Kai Yah Jameel bisa dukkam alamu dai yau kam Shagwaɓa kake ji dashi?”.
Ahankali ya buɗe idanunsa dake lumshe batare daya juya ba kana cikin raunin murya yace.
“Uhm Lelewal baza ki gane ba”.
Murmushi tayi kana tace.
“Yah Jameel zan gane mana gashi yau Shagwaɓa kake yiwa Ummi”.
Ummi kuwa sun kuyowa kansa tayi sai taga ya kuma lumshe idanunsa yayi shiru Kamar mai tunani hannunta dake goshinsa ta ɗago tare da cewa.
“Menene? Shin wai meke damunka? Me kake son faɗa min mana?”.
Cikin sanyin murya yace.
“Ummi”.
Sai kuma yayi shiru.


Ahankali ya buɗe Murfin motar ya fito tare da jan hannunta suka nufi cikin falon kana ya kalli su Asma'u tare da cewa.
“Ku jirani”.
Da kallo Khausar, Asma'u da kuma Bashir suka bisu, amma babu wanda yace komai kowa da tunanin da yake Aransa.
Suna shiga falon ya zaunar da Ummi kan 1sitter kana ya durƙusa agabanta cikin raunin murya yace.
“Ummi ba abinda kikeso in miki?”.
Cikin raunin murya tace.
“Meyesa kake hakane, shin wai idan ina da ɓuƙatar abu, bani da kaina nake kiran ka in faɗa maka ba Jameelu?”.
Araunane ya kalleta tare da cewa.
“Ummi ki tuna dai! ba abinda kike so in miki kada damar ta wuceni fa Ummi? Ki tuna dai”.
Ya ƙare mgnar yana murza tafin hannunsa kan rumfa sawunta
Saurin Kallonsa tayi kana tace.
“Kamar ya damar ya wuce ka Jameelu?
Na faɗa maka bana ɓuƙatar komai”.
Cikin raunin murya yace.
“Toh bani wayar ki Ummi”.
Ahankali ta miƙa masa wayarta dake hannun kujeran karɓa yayi tare da shiga text messages ɗin ta, ya duba Alart gani yayi duka-dudu kudin dake ciki baifi dubu ɗari biyu da hamsin da biyar ba.
Kallonta yayi kana yace.
“Ummi kina da buƙatar kuɗi”.


Girgiza kai tayi tare da cewa.
“Ga kuɗi kuma mai zanyi dasu?.
Me zanyi da kuɗi komai fa kai kakeyi min Jamilu”.
Girgiza kai yayi tare da zaro wayarsa acikin al'jihunsa Atake yayi charking balance tare da cewa.
“Nima bani ba kuɗi da yawa acikin account ɗina”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.
“Ta yaya kuɗi zai zauna acikin account ɗin ka Jamilu nasan ka haka Allah yayi ka kana da yawan kyauta zaka bawa wannan ka bawa wancan”.


Girgiza kai yayi tare da cewa.
“Allah yabamu mu bayar Ummi”.
Jinjina kai tayi tare da cewa.
“Ameen”.
Atake ya Mata transfer million ɗaya zuwa account dinta.
Kana yace Ummi ga Million ɗaya na miki transfer”.


Cikin sauri ta kallesa kana tace.
“Me zanyi dasu Jameelu?”.
Hannunta ya damƙe acikin nasa kana yace.
“Ummi duk abinda kike so kiyi dashi, tunda kin ƙi ki faɗa min abinda kike buƙata ina ji kamar akwai nauyin da ban gama sauƙewa ba gani nake kamar kinada wata buƙatar”.
Ya ida maganar muryarsa na rawa sosai sai kuma ya kama gwiwoyinta da hannu kana ya kife kansa akan cinyarta.


Cikin sanyayyar murya mai cike da rauni yace.
“Ummi”.
Ummi kuwa cikin sanyin murya tace.
“Na'am”.
Still muryarsa na rawa yace.
“Idan akwai abinda na miki kiya femin”.
Cikin sauri ta

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads