Showing 135001 words to 138000 words out of 188939 words
Chapter 46 - SAKAYYA Book 1 complete BY GARKUWA.txt
in zuba mana”.
Murmushi Asma'u tayi tare da faɗin.
“Yah Jameel da kan ka kabari zan zuba mana”,
Girgiza kai yayi kana yace.
“A'a Asma'u kawo in zuba mana bana so ki wahalar da kanki”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Laaa Yah Jameel ka jika Allah zanyi mana”.
Lumshe Idanunsa yayi tare da saurin dafe ƙirjinsa kana ya buɗe Idanunsa tare da Kallonsu ɗaya bayan ɗaya tare da cewa.
“No Asmeey ki bari in zuba mana kaɗai”.
Saurin Kallonsa tayi tare da miƙa masa Plate ɗin.
Murmushi yayi tare ɗaukar Plate ɗin tuwon ya zuba musu akan babban farantin kana ya ɗauka ya ajiye musu Atsakiyar su tare da kallon Bashir yace.
“Ɗauko Mana drinks”.
Kai Bashir ya gyaɗa tare da cewa.
“Toh”,Kana ya miƙe ya ɗauki Plate ya ɗebo drinks da swan water ya ajiye musu.
Ya zauna sai ya zamana M Jameel da Ummi na facing juna Asma'u da Bashir ma na facing juna sai ya zama sunyi Cycle plate din na tsakiyar su.
Ummi kuwa shiru tayi tare da zubawa M Jameel Ido Batare da tace komai ba kana tana jin wani irin yanayi mara misaltuwa azuciyarta wanda takasa sanin na menene hakanan ta tsinci kanta da Kallonsa acikin kwanakin nan.
Ahankali M Jameel ya janyo kular miyar tare da ƙara musu namar da bandan kifi kana fuskarsa ɗauke da murmushi yace.
“Hayya kuci yau zakuci miyar da baku taɓa ciba irinta ba dan ni nayita ko Ummi?”.
Ya faɗa tare da ɗago kai sai yaga baki ɗaya Idanun Ummi na kansa faɗaɗa Murmushin fuskarsa yayi tare da cewa.
“Kai Ummina ya dai?,Ai gaskiya na faɗa”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.
“A gaskiya ka faɗa kam”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Toh Ummi kici mana”.
Dariya Ummi tayi tare da girgiza kai kana tace.
“A'a kai da kayi dai ka fara ci muga result ɗin da fuskarka zai bayar kafin mufara ci”.
Wara ido yayi tare da kallon Asma'u da Bashir da suma Kallonsa suke,
“Toh ɗan Auta fara ɗana mana muji”.
Kai Bashir ya gyaɗa kana ya gutsiri loma ɗaya yakai bakin sa lumshe ido yayi tare da haɗa yatsunsa hannu biyu alamar jinjina kana yace.
“Kai amma miyar tayi daɗi gaskiya Yah Jameel na baka Award”.
Murmushi Ummi tayi tare da kallon M Jameel da Yayi wani irin kyau na ban mamaki tamkar wanda aka sanya shi a inji aka sake ƙenƙesashi ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.
“Uyummm toni nayi bashi ba”.
Dariya M Jameel Yayi wanda ya bayyanar da Fararen haƙoransa kana yace.
“Toh na yarda Ummi mu duka biyu mukayi”.
Murmushi Asma'u tayi tare da kallon M Jameel kana tace.
“Aikuwa Yaya Kayi ƙoƙari sosai amma muci kada yayi sanyi”.
Kai suka gyaɗa atare kana lokaci ɗaya suka sanya hannunsu akan tuwon tare da kai tuwon bakinsu lokaci ɗaya suka kalli juna tare da sakin murmushi.
M Jameel kuwa murmushi ya saki tare da lumshe Idanunsa kana yace.
“Ina ma ace zamu kasance ahaka ko yaushe mu riƙa zama tare nuna cin abinci atare da nafi kowa farin ciki”.
Asma'u da takai nama bakinta ta kallesa kana tace.
“Yah Jameel zamu kasance atare mana Insha Allah”.
Kai ya Girgiza tare da cewa.
“Dole wataran fa zan barku sai dai ku zauna ku uku kuci abinci ba tare dani ba”.
Cikin sauri suka kallesa Bashir yace.
“A'a Yaya Jameel mai yasa zakace haka insha Allah zamu kasance atare”.
Ummi kuwa Kallonsa kawai take.
Murmushi M Jameel Yayi tare da kurɓan drinks kana yace.
”Dole wataran zan barku zanyi tafiya gari mai nisa wanda zan kasance Ni kaɗai acan batare da kuba nasan zanyi kewar ku kamar yanda zakuyi nawa tunda Abba ya dage dole zan koma Marrocco”.
Kai suka gyaɗa tare da sauƙe ajiyar zuciya kana suka ci gaba da cin abinci batare da wanin su ya sake magana ba sai dai lokaci zuwa lokaci yakan kallesu tare da sakin murmushi.
Wayar M Jameel ne ya karaɗe wajen da ruri ahankali ya ɗauka tare da sakin murmushi kana yayi Picking tare da Sallama.
Daga ɗaya ɓangaren kuwa cikin sanyin murya Moddibo yace.
“J ina ka tsaya na jika shiru ko abinci banci ba, sannan kasan bani da lafiya ko dai har yanzu kana gidan Ummi ne?”.
Murmushi M Jameel Yayi tare da gyara zaman wayar akunnensa kana yace.
“Ayyah sannu A.J Please kaci abinci sannan ka sake shan maganin dana haɗa maka Insha Allah ina hanya”.
Lumshe idanu Moddibo yayi tare da sakin ajiyar zuciya kana.
“Toh shikenan sai kazo kace ina Gaishe da Ummina”.
Murmushi M Jameel Yayi tare da kallon Ummi dake sauraron duk abinda suke faɗa kana yace.
“Zata ji”,daga haka ya katse kiran.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Ohh ina ga dai wannan ko kunyi Aure gida ɗaya zaku zauna bakwa iya minti talatin batare da kunga juna ba ko kuma kunji muryan juna”.
Murmushi M Jameel Yayi kana yace.
“Ai dai kam dole watarana arabu”.
Jinjina kai Ummi tayi,tana murmushi kana suka cigaba da cin abincin.
Bayan sun cinye tuwon farantin M Jameel ya Kalli Ummi tare da cewa.
“Ummi aƙara mana yau ina jin daɗin abinci ina so inci³ incika cikina dan ban sani ba sai kuma yaushe zan sake ci”.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“A'a to ai ko yaushe ma kakeso ai zaka zo kaci”.
Lumshe Idanunsa yayi tare da buɗe su akan Ummi kana yace.
“Toh Ummi kwanan nan zamu fara batun aikin nan kinga in dan na tafi Marocco ai bazan dinga samun ciba”.
Kai ta jinjina tare da faɗin.
“Ai in dai nan da ne ba nisa bane dashi idan ya kama sai inmaka miya da komai duk zan aika maka dasu idan yaso saika na sawa a fridge”.
Murmushi Yayi tare da cewa.
“Hmmyyym Ummina Allah ya ƙara miki nisan kwana mai amfani Allah ya barmu tare”.
Jingjna kai tayi tare da faɗin.
“Ameen Babana Allah ya ƙara maka nisan kwana inga har jikokin ka”.
Murmushi yayi tare da kallonta kana yace.
“Hmmm Ummina kenan.
Kin ko san in sha Allah ƴata ta farko sunanki zan samata,
Na kuwa tabbatar zata ga soyayya ko ƙuda bazan bari ya taɓa ta ba”.
Kallonsa Ummi tayi tare da cewa.
“Jamiluuu na”.
taja sunan tana murmushi haka nan take jin daɗin kiran sunan sa.
Bayan sun kammala cin abincin Asma'u ta miƙe tare da tattare Plate ta Kai kichen M Jameel kuwa da kansa ya mike ya ɗauki kular abincin ya kai kichen Ummi kuwa Kallonsa ta riƙa yi cike da so.
Bayan ya ajiye ya fito, woje ya nufa yana cewa
“Bari in ɗauko abu a mota".
Toh Ummi tace kana ta meda hankali kan tv.
Jim kaɗan da fitar da ya shigo riƙe da kwalayen waya masu kyau.
Ƙirar Samson, kana ya dawo ya zauna gefen Ummi Asma'u da Bashir suka zauna daga gefensa gyaran murya yayi tare da fuskantar Asma'u kana yace.
“Ga woyoyinku nan Asma'u yau dai na cika alƙawarin ko”.
Cikin tsananin jin dadi Bashir ya ruggumshi, yayinda Asma'u kuwa Ummu ta ruggume.
Cikin son juna suka rinƙayi mishi godiya tare da fatan al'khairi.
Murmushin jin dadi yayi tare da shafa kan Bashir kana yace.
“Asma'u yanzu ke wani irin makaranta kike so?”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Yah Jameel duk makarantar da ka zaɓa min ina sonta ina farin ciki da ita”.
Jinjina kai yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya kana yace.
“Zan kuwa zaɓa miki wanda ya dace dake Insha Allah naga keda ƙawarki kusan ra'ayin ku ɗaya ko yaushe amman wannan karon an samu akasi ita Jenouelist take fata naga ke kuma likitanci kike son karanta”.
Kallon Bashir yayi tare da cewa.
“Kai kuma wani irin Makaranta kake so?”.
Murmushi Bashir yayi kana yace.
“Duk wanda ka zaɓa min Yaya”.
Lumshe idanu M Jameel Yayi tare da cewa.
“Insha Allah kuwa zan zaɓa maka ina ganin Law zaka karanta zaifi dacewa da kai”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da fesar da numfashi kana ya tsira musu ido tare da cewa.
“Asma'u”.
Kanta ta ɗago tare da cewa.
“Na'am Yaya”.
Anutse ya kalleta cikin yanayin nutsuwarsa da alamun rashin wasa yace.
“Kinga ke ƴa macece ita rayuwar duniyar nan duk i da ƴa mace ta tsinci kanta ta tsare mutuncinta da darajar ta shine abu mafi daraja ki kiyaye tarbiyyar da muka sha wahalar baki nida Ummi kada ki kunya tamu kada kisa ta baƙin ciki”.
A hankali ya sauƙe numfashi tare da gyara zamansa kana yace.
“Saboda ke ƴa macece ke mukafi taraddadi akan ki kinga yanzu ga Bashir amma bana ta raddadi akansa kamar ke mace”.
Asma'u kuwa ƙasa ta sakeyi da kanta batare da tace komai ba sai wasa da yatsun hannunta da take yi.
lumshe idanunsa yayi kana yace.
“Burina da fatana inga mun kasance gida ɗaya muhalli ɗaya wallahi akanki da Bashir da kuma Ummin mu yasa nake so inyi Aure inga muna tare”.
Sai kuma ya kalli Bashir da shima yayi ƙasa da kansa kana yace.
“Ina so inga lokacin tafiyarku makarantar kana inga lokacin dawowan ku a idona sannan insan kalar mutanen da kuke mu'amala dasu".
Sai kuma ya juyo ya kalli Asma'u cikin yaƙini yace.
“Na yarda da ƙawancen ku da Khausar saboda tana da tarbiyya duk da kuwa tana da rawan kai”.
Numfasa yayi tare da kallon ta kana cikin raunin murya yace.
“Asma'u ki kula da rayuwarki sannan kisan irin mutanen da zaki dinga alaƙa dasu idan kuma har Aure kike so Asma'u ki faɗa min idan yaso idan kikayi aure sai ki cigaba da karatun ki agidan mijinki kada ki ɓoye min ki faɗa min komai ki ɗaukeni tamkar ƴar Uwarki mace”.
Cike da kunya Asma'u tayi ƙasa da kanta tare da girgiza kanta kana tace.
“A'a Yah Jameel nikam karatu zanyi”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Kin tabbatar ba Aure kike so ba sannan babu wanda kike so?”.
Cike da kunya ta girgiza masa kai tare da faɗin.
“Yaya Jameel Ni kuma wazan so kuma babu wanda ke zuwa gurina”.
Dariya M Jameel Yayi tare da kallonta kana yace.
“Mun shiga uku Ummi kadde ƙanwar tawa baƙin jini take dashi?”.
Murmushi Ummi dake aikin Kallonsu tayi tare da faɗin.
“Ba wani baƙin jini kawai dai dake tana kiyaye kanta ne babu wanda ke kawo mata wargi”.
Jinjina kai yayi tare da dai-dai-ta nutsuwarsa kana yace.
“Toh shikenan Asma'u tun da dai kin bani tabbacin karatu kike so daga nan harki kai digir-gire ki gama har ki taka duk kan matakin da kike so nayi al'ƙawarin zan taimaka miki da duk kan ƙarfina da kuɗina muddin ina numfashi zan tsaya miki”.
Kallon Bashir yayi tare da cewa.
“Sannan kai kuma Bashir zaka karanci fannin Law tunda kana da ilimin addini ina da yaƙinin zaka tsaya akan gaskiya duk runtsi duk wuya kada Kabi bayan ƙarya ka kasance mai al'ƙawarin da rikon amana aduk inda ka tsinci kan ka”.
Jinjina kai Bashir yayi kana yace.
“Yah Jameel Insha Allah Nayi alƙawari zan kasance ayanda kake fata”.
Hira suka cigaba dayi sosai irin wanda suka ɗauki tsawon lokaci basuyi irin saba wanda har dare yaraba basu lura ba.
Ahankali Ummi dake murmushi ta daga kanta Idanunta suka sauka akan agogon dake manne abango wanda ke nuni da ƙarfe sha biyu da minti goma,Cikin sauri ta kalli M Jameel tare da cewa.
“Jamilu”.
Anutse ya ɗago ya kalleta tare da cewa.
“Na'am Ummina”.
Ta sauƙe ajiyar zuciya tare da Kallonsa kana ta sake kallon agogon zuciyarta na bugawa tayi saurin dafe ƙirjinta kana tace.
“Ka kalli time fa”.
Cikin sauri M Jameel ya juya Kalli agogo tare da kallon Ummi kana...!
Cikin sakin fuska yace.
“Ummi yau anan zan kwana”.
Cike da mamaki Ummi ta juya ta kallesa, domin tunda Allah yasa tayi aure agidan mahaifin Asma'u bai taɓa kwana ba, sai dai yakan zo aduk sanda yaga dama, a hankali ta sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.
“Anan zaka kwana?”.
Kai ya jinjina tare da faɗin.
“Eh zan kwana Ummina”.
Kallon Ummi Bashir yayi cike da farin ciki ya langwaɓar da kai kana yace.
“Ayyah Ummi ki barshi kinga yanzu ma dare yayi ki gani fa sha biyu hadda kwata dare fa ya riga da yayi nisa”.
Cikin sanyin murya me ɗauke da farin ciki Asma'u tace.
“Gaskiya dai kam mu kwana kawai Yah Jameel, yau nayi matuƙar farin ciki zamu kwana agida ɗaya Allah ya nuna mana ranan Aurenka mu kasance atare na har abadan”.
Murmushi M Jameel yayi tare da shafa sajensa kana ya tsira musu ido tare da lumshe idanunsa, a hankali ya sauƙe ajiyar zuciya kana yace.
“Asmeey zamu kasance atare in sha Allah zanyi Aure kana zaku kasance gida me kyau da na al'farma da kwanciyar hankali, ni kaina bansan kamannin gidan ba amma na sani gida ne mai masifar kyau da ɗaukar hankali zan riska in sha Allah”,
Sai kuma ya sauƙe numfashi tare da lumshe idanunsa kana yaci gaba da cewa.
“Wanda kowa ke burin samu, in Sha Allah zan sameshi, domin inaji ajikina na kusa isa wannan gidan kafin ku iso zan kasance cikin farin ciki amma idan ina tare daku zanfi farin ciki na zai fi nin kuwa”.
Cikin yanayin sanyin jiki ya tsira musu ido su duka ukun.
Ummi kuwa idanu ta zuba masa ko ƙyaftawa ba tayi wani irin yanayi takeji azuciyarta, wanda takasa tantance na menene.
Asma'u kuwa murmushi tayi tare da Kallonsa kana tace.
“Yaya Jameel Allah ya baka mace ta gari wacce zata kula da Ummin mu tamkar yanda kake kulawa da ita sannan ta ƙaunace mu tamkar yanda kake ƙaunar mu”.
Murmushi yayi kana ya lumshe idanunsa tare da cewa.
“Insha Allah Asmeey matar da zan Aura, macece wacce ta fito daga babban gidane masu tarbiyya da kamala, wacce zata riƙe Ummina daku tamkar Iyayen ta da kuma ƙannenta”.
Sai kuma ya numfasa tare da tsira mata ido.
Kai Asma'u ta gyaɗa murya cike da jin daɗi tace.
“Ni kuwa Yah Jameel Nayi maka al'ƙawarin zan kasance mata tamkar yar uwa Aminiya yadda kake fata har ma fiye da haka”.
Sassayan numfashi ya fesar kana yace.
“Alhamdulillah Asmeey idan kika min haka ko a ina na kasance zanyi al'fari dake sannan zanyi farin ciki”.
Sai kuma ya maida kallonsa kan Bashir tare da cewa.
“Yauwa kai kuma Bashir”.
Anutse ya ɗago kansa tare da faɗin.
“Na'am Yah Jameel”.
cikin sanyin murya yace.
“Bashir ka maida hankalin ka akan karatun ka, kada ka biyewa aboka nan banza kasan dawaye ya dace kayi abota kada ka biyewa matan banza da abokan baza kada kasa Ummi tayi Allah wadai da halayyar ka”.
Ƙasa da kai Bashir yayi yayin da Ummi kuma shiru tai tana mai jin daɗin Nasiyyar da yake wa ƙannensa.
A hankali ya numfasa kana yaci gaba cewa.
“Bashir aikin Law aikine mai matuƙar daraja da muhimmanci sai dai wasu sun ɓata aikin da cin hanci da rashawa da tauye haƙƙin masu gaskiya, da tozartasu, ina so kamin alƙawari kai zaka kasance mutum mai adalci da karamci akan aikinsa wanda duniya za tayi al'fahari da kai sannan Ummina tayi farin ciki da rayuwarka”.
Sai kuma ya ɗanyi shiru yana kallon yadda Bashir ke gyaɗa masa kai alamar nasihar na ratsashi, cikin yanayin lallashi da jan hankali yaci gaba.
“Dan Allah Bashir kada ka bari adalilinka Al'umma su la'anci Ummina suyi Allah wadai da haihuwarka da tayi”.
Cikin rawan murya Bashir yace.
“In sha Allah zan zama yanda kake da buri har ma fiye da haka Yah Jameel”.
Lumshe Idanu M Jameel Yayi tare da shafa sajensa kana cikin sanyin murya yace.
“Nagode Bashir tabbas ko bayan ba nan Idan ka kasance mutumin kirki zanyi farin ciki, sannan ka kula min da Ummina da Asma'u kada ka bari hawayen baƙin ciki ya zubo daga idanunsu ni dai burina kayi min wannan al'ƙawarin”.
Jinjina kai Bashir yayi tare da cewa.
“Nayi maka alƙawari Yah Jameel Ummi da Asma'u baza su taɓa baƙin ciki dani ba, kullum zan saka su farin ciki sannan zan kasance mai riƙon alƙawari aduk inda na tsinci kaina”.
Murmushi M Jameel Yayi Idanunsa alumshe yace.
“Alhamdulillah³ Allah na gode maka”.
Anutse ya juya ya kalli Ummi data tsira musu Ido kana cikin sanyin murya yace.
“Yauwa Ummina faɗamin me kike buƙata ko kuma kike so arayuwar ki nayi miki?”.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe kana tayi murmushi tare da cewa.
“Toh ni kuma meya rage arayuwa wanda baka yimin ba Jamilu?
Ai ni kam kayi min komai sai dai Ubangiji Allah ya maka albarka Allah yabaka ƴaƴan da zasu yi maka biyayya”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Ameen Ummina amma yanzu baki da wata damuwa ko buƙata?”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Bani da wani damuwa ko buƙata aduniya Jamilu, domin kafin na buƙaci komai ma kiyi min”.
Hannunsa biyu ya ɗaga sama tare da faɗin.
“Alhamdulillah Allah Nagode maka ya Ubangijin Allah ka bani damar da duk ɓuƙatar da mahaifiyata take dashi kafin ma ta buƙata nayi mata shi”.
Murmushi tayi kana tace.
“Ameen Ubangiji Allah ya maka albarka Allah ya rufa maka asiri duniya da lahira Allah yasa ƴaƴan ka su ramamaka abinda kayi mana”.
Still Fuskarsa ɗauke da murmushi yace.
“Ameen ya Allah”.
Ummi kuwa ahankali ta daga kanta gani tayi har ƙarfe uku kallonta ta mayar kansu kana tace.
“Yanzu yaranan baza ku tashi kuje ku kwanta ba ku dubi time fa”.
Atare Asma'u da Bashir suka ce.
“Toh Ummi am gaba ɗaya yau bama jin baccin ma”.
Murmushi M Jameel Yayi kana yace.
“Ai dai kam”,
Ummi kuwa murmushi tayi kana suka cigaba da hira.
Jin ankira Sallar ƙarfe huɗu yasa Ummi kallon su tare da faɗin.
“Toh yanzu kam mutashi muyi alwala muyi nafillah mu rufe wannan daren da roƙon Ubangiji”.
Bayan duk sunyi Al'wala ne suka dawo falo duk suka shimfida Sallaya sukayi nafila raka'a huɗu-hudu.
M Jameel kuwa acikin sujjadar ta ƙarshene yace.
“Ya Allah katsare min Mahaifiyata da ƙannena Ubangiji ka zama gatansu anan duniya da lahira ya Allah ka tsaresu daga sharrin abin ƙi Ubangiji ka inganta rayuwar Asma'u da Bashir ya Allah ka tabbatarwa da A.J na al'khairi a cikin samun mace tagari wacce zata kula da ɗawainiyarsa ya Allah kabiyawa duk musulmi ɓuƙatar su na Alkhairi”.
Ko wannensu haka ya dinga addu'a saida aka kira Assalatu kafin suka miƙe Shida Bashir suka tafi masallaci Asma'u da Ummi kuwa anan suka Idar da Sallah.
Bayan sun dawa daga masallaci M Jameel ya kwanta akan 3sitter Ummi Atake Bacci mai daɗi ya ɗaukesa.
Ummi da Asma'u kuwa kichen suka shiga tare da soya musu soyayyen dankali da ƙwai kana suka tafasa ruwan tea da yaji citta da kanumfari sai kuma tayi musu ɗumamen tuwon jiya, ganin yadda yaketa zuba tururine yasa Asma'u tas hannun da nufin buɗe murfin tukunya, zafin da taji ya ratsa ƴan yatsunta ne yasa ta saki karfin ya faɗi ƙasa tare da bada ƙara.
Cikin sauri Ummi ta kalleta kana cikin ƙasa da murya tace.
“Kai Asma'u kiyi a hankali mana kada ki tashi yayan ku, bakiga jiya bai samu bacci ba”.
Murmushi Asma'u tare da gyaɗa mata kai kana tace.
“Toh Ummi”.
Har misalin ƙarfe tara M Jameel bai far kaba Ummi kuwa toilet tashiga tayi wanka bayan ta shirya ta fito falon har zuwa lokacin M Jameel na bacci ahankali ta zauna agefensa tare da tsira masa idanu tana kallon