Showing 21001 words to 24000 words out of 188939 words
Chapter 8 - SAKAYYA Book 1 complete BY GARKUWA.txt
niyyar mu gaida Innayi nace ki raka ni amma kada kice baza ki sake raka niba na tuba”.
Kallonta kawai Khausar tayi amma ba tace komai ba, sake langwaɓar da kai Asma'u tayi cike da tausayinta tace.
“Ki zauna awancan dakalin se inja miki ƙafar!”
Kai Khausar ta girgiza tana rintse Idanunta tace.
“Basai kin ja minba kawai sama mana adedeta mu hau”.
Kai Asma'u ta jinjina tare da riƙe hannunta suka ɗan tsaya bakin titi cikin sa'a tsayuwar su babu daɗewa suka samu adedeta hawa sukayi tare da yimasa kwatancen inda ze kaisu...
Aƙofar gida me Adedeta ya sauƙe su bayan sun isa Asma'u ce ta ciro kuɗi ta basa kana ta riƙe hannun Khausar suka nufi gate Khausar ce tasa hannu ta tura gate ɗin cikin rashin sani suka buge juna da Samira Sani wacce ke ƙoƙarin fita Amina na biye da ita.
Saurin ɗago kai Khausar tayi jin Samira Sani na cewa.
Ke 'yar uban waye da zaki haɗa kafaɗa dani shin dame kike taƙama!?”.
Kamar Khausar za tace wani abu sai kuma ta fasa taja siririn tsaki tare da jan hannu Asma'u suka bar wajen tana me cigaba da ɗingisa ƙafarta.
Ƙwafa Samira Sani tayi cikin kumfar baki tare da tsanan Khausar aranta tace da Amina.
“Wallahi na tsani wannan shegiyar yarinyar me kama da sadaka yalla Idan ban sabautata ba bazan taɓa samun nutsuwa ba!”.
Tsaki Amina taja tana kallon Samira tace.
“Allah ne kaɗai yasan irin abinda zan mata”.
Kafin su ƙarasa shiga falon Khausar ta janye hannunta dake cikin na Asma'u kana ta gyara tsayuwar tare da dai-dai ta tafiyarta tana me rintse Idanunta sam bataso Momy ta fahimci abinda ya sameta.
Asma'u kuwa kallon ta tayi cike da tausayinta amma batace komai ba Ƙofan falon suka tura
suka shiga tare da haɗa baki wajen cewa.
“Assalamu Alaikum”.
Momy dake zaune kan kujera ta ɗaura ɗaya kan ɗaya ce ta faɗaɗa Murmushin fuskarta tace.
“Wa'alaikum salam har kun dawo?”.
Zama suka yi daga gefen ƙafarta aƙasan chanis capet Asma'u tace.
“Eh Momy”.
“Masha Allah ya jikin Innayin?”.
Cewar Mommy.
Khausar na ƙoƙarin miƙewa tace.
“Da sauƙi Momy” Sannan ta nufi Bedroom ɗin ta da sauri Asma'u ta miƙe tabi bayanta.
Bakinta ɗauke da sallama tashiga ɗakin nata kana tayi saurin ɗin gisa ƙafarta se kuma ta kwanta agefen gadonta dake shimfiɗe da white bedsheet tana sakin ajiyar zuciya akai-akai alamar har yanzu akwai tsoro atare da ita.
Zama Asma'u tayi agefenta ganin yanda ƙafan Khausar ke rawa yasa tace.
“Bari na ɗebo ruwan ɗumi na matsa miki”.
Kai Khausar ta girgiza da faɗin.
“A'a ga can man zafi agaban mirrow ki ɗauka min na shafa”.
Kai Asma'u ta gyaɗa kana ta miƙe ta ɗauko man zafin ta ɓude kana ta kama ƙafar Khausar tana mulka mata.
Khausar kuwa rintse Idanunta tayi tanajin zafin man na ratsa jikinta yayin da aƙasan zuciyarta tsakanin tsoro da firgicin hukuncin da Moddibo ze ɗauka akan tane.
Asma'u kuwa hira ta riƙa yiwa Khausar na ɗebe kewa kana daga bisani ta miƙe ganin yamma tayi seda ta biya ta kichen ta sake yiwa Momy Sallama kana ta tafi.
Khausar kuwa yanayin zogin da ƙafarta da kuma hannunta ke mata yasa bayan tafiyar Asma'u ba jimawa bacci ya ɗauke ta...
Ita kuwa Momy ganin har maghariba tayi bata jiyo motsin Khausar kuma bata nemi Raudat suyi salla ba se abin ya bata mamaki bayan ta idar da Sallah ta fito daga Bedroom ɗinta Kai tsaye Bedroom ɗin Khausar ta nufa,
bakinta ɗauke da sallama ganin Khausar na bacci yasa ta ƙarasa bakin gadon tare da taɓa fuskarta da hannunta dake da damshin ruwa ruwa tana kiran sunanta da faɗin.
“Khausar! Khausar!! Khausar tashi kiyi Sallah maghariba tayi”.
Momy ke faɗa tana me sake shafa fuskarta da hannunta dake da damshin ruwa.
jin muryan Momy da kuma damshin hannunta da take shafa fuskarta yasa ta buɗe Idanunta ahankali tace.
“Na tashi Momy”.
Juyawa Momy tayi ta fita ita kuwa khausar miƙewa tayi tare da furta.
“Alhamdulillah”,Jin babu ciwo da Zugin da ƙafar ke mata se kuma hannun data ji ya sake baki ɗaya tamkar ba ajikinta yake ba.
Ta lumshe lumsassun idanunta kana ta miƙe ta nufi toilet tana me furta.
“Allahumma Inni Auzubika Minal khubsi wal khaba'is”.
Kana tashiga cikin toilet ɗin da komai ke akimtse yana fitar da wani irin ƙamshi Anutse tashiga yin alwalan har ta ida kana ta fito bayan ta furta.
“Gufra naka”.
Bayan ta gabatar da Salla tayi adduo'i ta miƙe tare da naɗe darduman se kuma ta juya ta fice tana me buɗe hannunta da rufewa koda ze dawo dai-dai...
Zaune ta samu Momy kan kujera hannunta riƙe da hisnul Muslim tana Azkharul Masa,Yayin da Raudat ke gefenta daga ƙasa tana bin bakinta zama Khausar tayi daga gefen Raudat kanta aƙasa tace.
“Momy gobe zan tafi JAURO YAYAH”.
Da mamaki Momy ta zuba mata ido jin mgnar a bakatatam cike da mmki tace.
“Zaki tafi Jauro yaya kuma Khausar?”.
Ataƙaice Khausar tace.
“Eh”.
tana mai cigaba da jan yatsun hannunta.
Momy ta sake duban ta da mamaki akaro na biyu tace.
“Anma babu yanda banyi dake ba jiya kan cewa kishirya yau kutafi tunda mutanen garinsu na zuwa sallan jumma'a sosai ku tafi tare, kika ce ba zaki tafi dasu ba kuna hadda, sannan kun kusa zuwa ƙarshen surar idan kika tafi karatun ki ze koma baya sannan na yarda na barki kan cewa se sati me zuwa yanzu kuma kice zaki tafi gobe”.
Murmushi ta ƙaƙalo tare da faɗin.
“A'a Momy babu damuwa munyi magana da Asma'u tace koda awaya zan iya ƙarawa da kaina batare da anwuce Ni ba”.
Dubanta Momy tayi tare da cewa.
“Kin tabbata Khausar har cikin ranki kikeson zuwa Jauro Yaya!?”.
Kai ta gyaɗa tace.
“Eh”.
Aranta kuwa cewa tayi ba gwara masifar wancan tsohuwar ba dan ko yaya bazan tsaya ta dake niba amma wannan mutumin ya riƙa tsareka da firgitattun idanunsa masu saka tsoro da fargaba, baya ga haka in banyi sa'a ba duka na zai sa ayi banyi masa lefi bama idan yasamu sarari sawa yake aci zalina bare kuma nayi masa laifi...
Muryan Momy dake cewa.
“Toh shikenan nima nafi so ki tafi Kinga idan hutun ku ya ƙare sannan anƙarasa muku gyaran makaranta seki dawo”.
Ya dawo da ita daga duniyar data lula.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Shikenan Momy”, Sannan ta miƙe ta shiga Bedroom ɗin ta.
Momy kuwa Hisnul Muslim ta ɗauka ta cigaba da Azkhar yayin da Raudat ta miƙe tabi bayan Khausar.
Ita kuwa khausar na shiga ɗaki ta hau kan stoll ta janyo trolley ɗin ta sannan tashiga haɗa kaya Raudat dake kallonta tace.
”Dani Zaki tafi Addah Khausi?”.
Girgiza mata kai Khausar tayi alamar a'a.
Kuka Raudat ta fashe dashi tana cewa.
“Ni zan biki”.
Zama Khausar tayi ta riƙe hannunta tare da langwaɓar da kai tace.
“Raudat garin bashi da daɗi fa, ga tsohuwar garin ta fiye masifa, kana yi mata kuskure kaɗan zata zane Mutum”.
Jin haka yasa Raudat ta girgiza kai tace.
“Nide ba zanje ba idan haka ne”.
Aɓangaren Momy kuwa bayan tashiga turakar Lamiɗo sunyi shirin kwanciya ta dubesa fuskarta ɗauke da murmushi me sanyi tace.
“Uhum wai ɗazu Khausar ke cemin idan Allah yakaimu gobe tana son zuwa Rugar Jauro Yaya”.
Zamanshi ya gyara tare da faɗaɗa Murmushin dake fuskarsa kana yace.
“Allah ya kaimu hakan nada kyau idan yaso tunda gobe weekend ne zamuje dukan mu kema sai ku gaisa tunda kinyi shekaru baki jeba”.
Kai ta jinjina kafin tace.
“Kai naji dadi Allah ya kaimu”.
Amin yace kana sukaci gaba da hirarsu.
Washe gari Ya kama asabar da wuri Khausar ta tashi ta gyara ɗakinta sannan ta nufi ɗakin Momy ta gyara kana ta share har zuwa falo da kuma duk sashen saida ta gyara ko wani lungu da saƙo.
Bayan ta gama ta dawo ta shiga kichen ta zuba musu Breakfast soyayyan cheaps da tea ita da Raudat ke ciki.
Bayan sun kammala ta miƙe tana ƙoƙarin tattare wajen Momy tashigo Idanunta akan Khausar.
fuska ta ɗan tsuke tare da faɗin.
“Maza kije yanzu Aunty Jamila tayi Miki kitso”.
Aunty Jamila matar ƙani Lamiɗo ne sannan Momy tasan inba tayiwa Khausar dagaske to baza taje ba domin bata ƙaunar kitso.
Ganin fuskar Momy babu walwala yasa Khausar gyaɗa kai tare da shiga Bedroom ta ɗauko dogon hijabinta fari Nevy blue daya sha ninkin guga ta ɗaura akan riga da wandon dake jikinta kana ta fice ta nufi gidan Aunty Jamila tana zumɓura baki da kuma kifiya da kum a hannunta.
Bakinta ɗauke da sallama tashiga gidan, Aunty Jamila dake zaune ta amsa Sallamar tana faɗaɗa fara'ar dake fuskarta tace.
“A'a Khausar kece?, sannu da zuwa”.
Sake fuska Khausar ta ɗanyi tace.
“Eh nice Aunty wai kitso nazo kiyi min zanje Jauro Yaya”.
Murmushi Aunty Jamila tayi tare da cewa
“Masha Allah kice zakije ziyara?”.
Kai Khausar ta gyaɗa tana murmushi.
Cikin sakin fuska Aunty Jamila tace.
“Allah Ya kaiku lafiya".
“Amin ya rabbil izzati”.
Cewar Khausar.
“Kinga kuwa kinyi sa'a duk na gama aiyuka na”.
Da sauri tace.
“Aunty Jamila manya fa zakiyi shida ko takwas”.
Murmushi Aunty Jamila tayi.
Kana ta miƙe ta shiga ɗaƙi tare da kwantar da yaronta kana ta fito,
Akan kujeran roba Khausar ta zauna ita kuma ta tsaya ta fara yi mata kitson suna cikin kitson ne suka jiyo Sallamar Gimbiya Dadu.
Anutse Aunty Jamila ta ɗago kanta fuskarta ɗauke da murmushi tace.
“Sannu da zuwa Mama”.
Asaman laɓɓa Gimbiya Dadu ta Amsawa Aunty Jamila baki ɗaya nutsuwarta da hankalinta suna kan Khausar.
Miƙewa Aunty Jamila tayi tashiga ɗaki dan ɗaukowa Gimbiya Dadu Darduman zama.
Ita kuwa khausar ahankali ta ɗago kanta caraf Idanunta suka sauƙa akan Gimbiya Dadu data tsareta da ido ita kuwa khausar cikin hanzari tayi ƙasa da idanunta tana mai karanto duk wata addu'ar da tazo bakinta kamar minti ɗaya Khausar ta sake ɗago kanta akaro na uku still Idanun Gimbiya Dadu na kanta.
Ita kuwa khausar kasa jurewa tayi ta tsayar da Idanunta akan Gimbiya Dadu cikin dakiya tace.
“Wai dan Allah Gimbiya Dadu Meyesa kike kallona haka?”.
Wani murmushi mai cike da ma'anoni Gimbiya Dadu tayi tare da cewa.
“Uhum yaro man kaza,
ai tunda kika bar cikin Awaki 'yan uwanki kika dawo cikin Kuraye ai dole akalleki! In kalleki in kuma”.
jin abinda Gimbiya Dadu tace yasa ta miƙe cikin rawan jiki da alamar tsoro aƙwayar Idanunta ta sanya hijabinta ta fita batare data jira Aunty Jamila ta fito ta ƙarasa yi mata kitson ba...
Sauri-sauri gudu-gudu take tafiya har ta isa bakin gate dinsu da sassarfa ta shigo coumpund ɗin su har yanzu jikinta be daina ɓari ba tana gyara zaman hijabin kanta Momy ta fito,Kallonta Momy tayi tare da cewa.
“Har angama kitson ne".
Ka ta gyaɗa mata ba tare da tace komai ba.
“Dama yanzu zan aika Haiydar ya kira ki kizo mu tafi”.
Murmushin karfin hali ts ƙirƙira kana tace.
“Eh mun gama”.
Wuce ta Momy tayi taje tashiga gaban mota Ita kuwa khausar kallon Raudat, Ramadan, da kuma Haiydar dake tsaye tayi tare da ɗaga musu hannu suma hannu suka ɗaga mata ahankali ta juya ta nufi wajen motar tana isa tasa hannu ta buɗe tashiga gidan baya Haiydar da Ramadan na cigaba da ɗaga mata hannun.
Babban gate mai gadin ya buɗe musu kana Lamiɗo ya cilla hancin motarsa.
Khausar kuwa jingina bayanta ajikin motar tayi tare da lumshe Idanunta zuciyarta na bugawa da mugun sauri abu biyu ne suka yiwa zuciyarta ƙawanya na farko hukuncin da Moddibo zai ɗauka akanta na biyu kalaman Gimbiya Dadu wanda suke ƙara tabbatar mata da zantuka dake yawo a gari cewa matar nan mayyace...
Anutse Momy ta dubi Moddibo dake sharara gudu akan Lafiyayyan titin nasu tace.
“Abban Haiydar gudun nan baiyi yawa ba”.
Kanshi ya ɗan jujjuya mata,
Ita kuwa cikin sanyi tace.
“Gsky dai ka rage gudun kamar yayi yawa”.
Juyowa yayi ya kalleta da murmushi a fuskarsa yace.
“Lokaci na tafiya kinga yanzu goma tayi gwara mu isa da wuri kada rana tayi mana mu samu mu juyo da wuri”.
Kai ta gyaɗa kafin tace.
“Amma duk da haka arage gudun".
Tattausan murmushin ya sakar mata tare da gyaɗa kai...
Sunyi tafiya mai tsawo kafin suka fara hango garin Atake suka fara tabbatar da sanyin da ake acikin Gembila wasa ne.
Domin tun kafin su shiga garin suka hango tamkar hayaƙi ke tashi saboda masifaffen sanyin da ake tsugawa acikin Jauro yaya suna shiga cikin garin suka fara ratsa bishiyoyi masu korayen ganye suna rangaji tare da fitar da sanyayyan Iska kasancewar hantsi ne duk makiyaya sun tafi se kuma,
'yan dalo da aka ɗaɗɗaure masu kyan launi ga kuma kukan tsuntsaye dana zabbi da ke tashi suna ajiye ƙwai.
Suna shiga tsakiyar Rugar Jauro,
kai tsaye ƙofar gidan dake kusa da babbar fadan Rugar suka nufa anan sukayi parking motar tare da fitowa.
Wasu dattawa dake zaune aƙofan masallacin dake kusa da babbar fadan suka taso baki ɗaya idanun su akan Khausar data fito daga mota tana gyara zaman hijabinta suna faɗin.
“Audiii Barka da zuwa kece?”.
ɗaya daga cikin dattijon ne ya taso wanda ya kasance shine Jauron garin ya riƙe hannun Khausar.
Fuskarsa ɗauke da murmushi yake faɗin.
”Addah, Addah, Addah, kizo ga Khausar”.
sauran ma bin bayansu sukayi zuwa cikin gidan suna masuyiwa Momy da Lamido Barka da zuwa.
Biyu daga cikine suka ce da Momy da kuma Lamiɗo.
“Sannunku da zuwa ya kuka tsaya ku shigo daga ciki”.
Kai Momy ta gyaɗa kana suka yi musu godiya bisa jagoranci suka nufi cikin gidan.
Jauro kuwa yana riƙe da hannun Khausar yana mata wasa da faɗin.
“Iyeee girman falo ji jiki kamar auduga,
bakisan riƙe sandar kiwo ba sannan baki san ta tsar nono ba girman burodi wayon shayi kawai”.
Ita kuwa khausar hannu ta wara da faɗin.
“Ban iya ba kam”.
Murmushi yayi kana yace.
“Zamu koya muki ai”.
maƙale kafaɗa tayi tace.
“Bana so ba kace min girman bread wayon tea ba”.
Murmushi yay i tare da cewa.
“To girman fura da nono”.
Akuma dai-dai lokacin suka shiga ɗakin tsohuwar wanda yake ginin gargajiya shatin kobo.
Suna shiga Jauro yace. “Addah ga 'yar Usman tazo”.
Ya mutse fuska Hajja Nana tayi tare da kallon Khausar tace.
“Shegiyar kaya me wuyar ɗauka se yau kika ga damar zuwa??”.
Murmushi Jauro yayi still hannunsa na cikin na Khausar yace.
“Tazo da mahaifiyarta da kuma Mahaifinta”.
Wani kallo Hajja Nana ta masa tare da cewa.
“Kai Jauro ka gyara kalamanka,
badai mahaifinta ba mahaifin riƙo dai ko? ka manta mahaifinta da kai aka binnesa shekaru goma sha biyar da suka wuce?”.
Kai ya jinjina alamar hakane amma bece komai ba ita kuwa miƙewa tayi ta ɗauko taburma ta shimfida tare da ɗauko darduman kilisa ta shimfiɗa.
A kuma lokacin Momy da Lamiɗo suka shigo cikin sakin fuska tashiga yi musu lale marhaba.
zama Momy da Lamiɗo sukayi akan shimfiɗar data musu kana ita kuma ta zauna awajen zamanta na farko yayin da duka ƙannenta maza suka zauna daga bayanta se ta zamto tamkar sarauniya acikinsu ko wannensu fuskarsa ɗauke da murmushi yake faɗin.
“Addah yau kam ga Khausar tazo”.
Haka yasa ta juyu.
Ta dubi Khausar da alamun farin cikin ganinta afuskarta saidai yanayin zafinta bazai sa ka fahimta ba.
Ta dubi Khausar da tayi kicin-kicin da fuska tace.
“Menene kike wani kumbura fuska? gwara ma ki saki ranki fa”.
Zumɓura baki Khausar tayi saidai ba tace komaiba.
Hajja Nana kuwa sake kallon Khausar tayi akaro na barkatai tace.
“Ki tashi ki kawo ma baƙi abin taɓawa”.
Lumshe idanu tayi kafin tace.
“Nice zan kawo abin taɓa wa?,Nima ai baƙuwa ce akawo mana dai”.
“Ina magana kina magana!?”.
Hajja Nana ta fadi a faɗace.
Cikin tura baki tace.
“Ai gaskiyane”.
Danƙolo Momy ta yiwa Khausar hakan yasa ta tsuke bakinta.
Ɗaya daga cikin ƙannen Hajja Nana wanda ya kasance shine ƙaramin su (Autah)ya miƙe da faɗin.
“To bari na kawo musu”.
Sannan ya shige uwar ɗakan Hajja Nana ba daɗewa ya fito hannunsa riƙe da Akwashi ya ajiye agabansu sannan ya koma ya ɗauko goran zuma kana ya koma ya sake ɗauko wani Akwashin.
Hajja Nana ta dubi Momy tare da cewa.
“Ayyah wallahi ban san da zuwanku ba”.
Kai Momy ta gyaɗa tare da cewa.
“Ai inata gwada kiran layin ki baya shiga”.
Murmushi Hajja Nana tayi kana tace.
“Kinsan Rugar tamu bamu da network se kaje bishiyar ƙare zancenka in kaje bishiyar ma seka hau sama ni kuma ban cika son zuwa ba da girmana Inje in hau bishiya na faɗo”.
Khausar kuwa taɓe baki tayi tace.
“Hmmm ba network kuma har sai anje wani bishiya?”.
Harara Hajja Nana ta watsa mata ta cigaba da cewa.
“Wallahi bansan da zuwan kuba dana shirya muku abin taɓa wa”.
Murmushi Momy tayi batace Komai ba.
Akwashin da aka shigo dashi ne Autansu Hajja Nana ta buɗe Nono ne me zafi yana tururi ga kuma goran zuma dake gefe ɗayan kuma daya buɗe ɗumamen danɗerun zabbi ne suna tururi.
Sauran mazan dake kewaye da Hajja Nana ce suka shiga Gaisawa dasu Lamiɗo.
Muskutawa Hajja Nana tayi tare da gyara zamanta ta kalli Lamiɗo dake zaune ya tanƙwashe ƙafafunsa tace.
Wa'annan daka ke kallo duka ƙannena ne mu goma ne acikin mahaifiyarmu gaba ɗayansu Mazane ni Kaɗai ce mace kuma nice 'yar Fari.
Jinjina kai Lamiɗo yayi yana sauraronta da duka nutsuwarsa duk da yasa abinda take faɗa kishin. tunda ba yaune zuwansa na firkoba.
Ita ko Hajja Nana nuna wanda ke gefenta tayi tare da cewa.
“Ga mai bina Jauro, Sannan kuma sai Sadu, Sannan se Abubakar, Sai kuma Garga, sannan sai Aliyu liman, Sannan kuma sai Dumau ,Sai Salmanu, Sannan kuma Isa sai kuma Umaru”.
Lamiɗo kuwa kallon su yake yana sake tabbatar da abinda ta faɗa saboda kamannin dake tsakanin su.
Hajja Nana tayi murmushi tace.
“Duk ƙanne nane sannan kuma duk da matansu”.
Ta nuna Jauro tace.
“Matan sa biyu,Garga ma Matansa biyu, Sannan Sadu ma matansa biyu, sai kuma Liman shima Matansa biyu”.
Ta sake nuna Jauro, Sadu, Garga, da kuma Liman tace.
Jauro da Sadu 'ya'yansu maza biyu sunyi aure kuma 'ya'yan Liman da Garga suka Aura ma'ana Auran dangi sukayi”.
Lamiɗo kuwa murmushi yayi alamar yana fahimtar abinda take faɗa masa.
Ita kuwa Hajja Nana cigaba tayi da cewa.
“Duk garinmu babu bare mu ya mune, sannan kuma babu maye mu garinmu atsarkake yake kushigo hankalin ku kwance ku fita lafiya,
Salamun Ƙaulan Min rabbil Raheem”.
Momy kuwa sunkuyar da kai ƙasa tayi Saboda tasan ana zargin Mahaifiyar Lamiɗo da Maita.
Shima Lamiɗo sun kuyar da kansa ƙasa yayi dan yasan zargin da ake yiwa Mahaifiyar sa kenan kasancewar sa mutum me haƙuri da kuma dattako saiya ɗago kansa fuskarsa ɗauke da murmushi yace.
“Masha Allah yayi kyau zuri'a tayi albarka Allah yaƙara rufa asiri”.
Murmushi Hajja Nana tayi tace.
“Ameen ya Allah”.
Domin Hajja Nana 'yar takife ce bata tsoro inma tsoron wani abu ake itace ke isar dashi.
Miƙewa Sauran sukayi suna kallon Lamiɗo suka ce bari mu barku kuci abinci sannan suka fice.
Itama Hajja Nana miƙewa tayi tace.
“Khausar zo mu shiga ciki kici naki”.
Girgizi kai