Showing 69001 words to 72000 words out of 188939 words
Chapter 24 - SAKAYYA Book 1 complete BY GARKUWA.txt
mu fara aiki shiko aikin za'ayi na tsawon watanni shida kafin ta fara nuna masa muradanta”.
Kana ya maida kallonsa ga Hajiya Lami data zabga uban tagumin tana kallon sa cikin Muryansa Mara daɗin Amo yace.
“Kema naki hakanne sai tayi wannan watannin”.
Dafe ƙirji Hajiya Lami tayi tare da zare Ido kana tace.
“Har Watanni shida shida Boka kafin wannan lokacin fa har sun kusa gama Ss 2 ma zasu tafi 3 awannan lokacin daka ɗiba mana”.
Cikin tsawa da hargagi yace.
“Dole sai anbi wannan ƙa'ida idan ba haka ba babu abinda zaku samu ya tafi dai-dai!”.
Ta gumi Hajiya Lami ta rafka kana tace.
“Shikenan Babu damuwa Indai burinmu zai cika tunda ai makarantar basu gama ba zamu bi ahankali”.
Ya yamutse fuska tare da watsa musu wani kallo da jajayen Idanunsa cikin wata murya mara daɗin Amo yace.
“Ƙa'idah ne yanzu zata je tayi ta aiki da wannan maganin na tsawon watanni ukku fuskarta zai koma dai-dai a Idanunsa sannan bayan wannan kuma tsawon watanni kar kuyi sallah daga nan kuma zan fara haɗa magani na tsawon watanni shida kafin su tun kare su daga magana”.
Murmushin Hajiya Bunayya tayi tare da gyara zamanta tana fuskantar Boka Kar'uzu da kyau tace.
“Toh shikenan ba matsala.
Amma fa ciki ya zube aiki yayi kyau!”.
Wani irin mahaukaciyar dariya mai matuƙar razanarwa Boka Kar'uzu ya saki da faɗin.
“Ai dama dole aiki zaiyi kyau idan kun bishi da ƙa'ida wannan ma ku kuka je kuka ɓatashi!”.
Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.
“Godiya muke Boka ana gaba zamu kiyaye”.
Kai ta gyaɗa kana yace.
“Toh ya batun aikin toshe mahaifar!?”.
Kai Hajiya Bunayya ta Girgiza tare da faɗin.
“Boka muga ma da batun aikin Amina tukunna, kaga ga yayar ta ma tana zaune ba tayi aure ba, sannan ga itama Aminan ta girma shiru, amma ita kace rabonta ne yayi nisa abin ya ɗaure mana kai mun rasa yanda zamuyi har wajen ƙan wata na tura ta Aƙasar Khautal ko zata samu rabonta acan amma acan ɗin ma shiru kuma kaga ta dade da gama karatu amma har yau Auren bai samu ba zamu jona mata wani makarantar ta fara zuwa jami'a kawai, tunda itama kanta Amina dan wasa da karatun take da tayi shekaru biyu da gamawa amman sai aikin maimaita aji gashi har shegiyar yarinyar nan ta kusan cimmata”.
Kai Boka Kar'uzu ya ɗago daga bugun ƙasar da yake tare da cewa.
“Babu matsala ita Aseeya rabonta yana nan tafe”.
Cike da jin daɗi Hajiya Bunayya tace.
“Godiya muke Boka Uban bokaye La'anannen Uban La'anannu Mugu Uban mugaye Hatsabibi Uban Hatsabibai!”.
Wata mahaukaciyar dariya Boka Kar'uzu ya kece dashi cikin jin daɗin kirarin da ta masa yace.
“Aikin ki zai tabbata ƙaramar la'ananniya Aljani ɗan ƙundalu mai ido Atsakiyar kai zai cika miki burinki ku fita da ƙafar hagu ta baya!”.
Miƙewa sukayi suka fice kamar yanda ya faɗa ransu fesss suna tsalle da kafar hagu kamar kutaren agwagi...
Acan ɓangaren su Ummi kuwa bayan sun isa gidan su Khausar sun gama gaisawa da Mommy da kuma Hajiya Ruƙayya da har zuwa lokacin suke tare.
Mommy tana murmushin tace.
“Ummi ya fama rigimar Khausar, ɗazun nan tace zata je ta duba ki ashe kina hanya”.
Dariya Ummi tayi tace.
“Ai lalle dai kam Hajiya Aysha babu ruwan Khausar ai”.
Murmushi Mommy tayi tace.
“Kina dai karate ta Amma Khausar ba dai rigima ba?".
Aunty Ruƙayya tayi Dariya kana tace.
“Ai Khausar bata da rigima ita dai baza'ayi gulma agaban Idanunta bane, sannan ba za'a cakake ta ta haƙura ba, kunga kuwa ai da gaskiyar ta”.
Dariya Ummi tayi tace.
“Aikam de lalle da gaskiyar ta”.
Ita kuwa Mommy Dariya tayi kana suka cigaba da hira.
Washe gari Asabar suka koma makaranta Khausar kuwa cikin tsoro da fargaban abinda Moddibo zai mata ta zuciyarta ya riƙa bugawa da ƙarfi lokacin da yashigo raba musu questions pepar tayi zaton zai mata hukunci sai taga baima kalli inda take ba.
Shikuwa Moddibo kawai ya fita sabgarta ne ganin alamar bata da cikikakkiyar nutsuwa in ya biyata zata zarar dashi.
Akwana atashi haka al'amura suka cigaba da tafiya komai yana wakana Moddibo ya kammala rubutun Kur'aninsa ya bawa M Jameel ya tafi wa da Sheykh Jabeer Habibullah Nuruddeen Joɗa na Adamawa.
Satin M Jameel biyu ya dawo tare da shedawa Moddibo ya karɓa harma ya fara dubuwa Insha Allah nan kusa zai turo masa.
Karatun su Khausar na tafiya komai na tafiya dai-dai yanda ake buƙata Anyi gasar musabaƙa jihar Taraba Makarantarsu Khausar Al'ansar Academic school_ shine yazo na farko Khausar ce tazo na ɗaya a haddar Izu arba'in yayin da Asma'u tazo na biyu Aishatu Abdullahi tazo na uku ,A haddar Izu biyar Raudat ce tazo na ɗaya kyaututtuka masu yawa suka samu kana suka dawo cike da nasarori.
Yanzu karatu na tafiya akwana atashi babu wuya wasa gaske yanzu Khausar suna Ss2
thirth term suna shirye shiryen fara Exam gashi kuma Ramadan ya kawo kai yayin da ake ta shirye shiryen shiga Ramadan tuni Gwamnatin Jaha ta rarraba malamai zuwa inda ko wanne zaiyi Tafseer kamar yanda aka saba Moddibo da M Jameel antura su Babban Masallacin juma'a dake ƙofar sarki Gembu anan zasuyi Tafseer ɗin su na Ramadan.
Lokaci natafiya karatun su Khausar na sake tafiya yanda ake buƙata tsakanin Amina da Khausar babu wani jituwa hasalima gaba ce domin har gobe M Jameel na sake nuna kulawa ta musamman akan Khausar yayinda Moddibo kuwa kwata-kwata baya lura da al'amuran Khausar hasalima idan tayi laifi zai yanke mata hukunci fiye dana kowa wannan dalili yasa basa shiri kana babu wata jituwa atsakaninsu.
Alhamdulillah ayaune Khausar suka rubuta exam na ƙarshe kuma da Geography suka rufe.
Taro Moddibo yasa aka haɗa kamar yanda aka saba a kowani ƙarshen hutu ko baki ɗaya Malaman sun haɗu awajen zamansu haka ma ɗalibai Khausar da Asma'u na zaune awaje ɗaya.
Shi kuwa Moddibo cikin nutsuwarsa da kuma kamala ya nufo wajen as usual cikin shigar sa kaman ko yaushe sanye yake cikin Jallabiya fari kansa naɗe da hirami idanunsa sanye da ɗan siririn farin glass daya ƙawata kyawun fuskarsa yalwataccen sajensa zuwa gemunsa ya kwanta luf-luf yana sheƙi.
Cikin tsantsar nutsuwa da sanin darajar kansa ya gyara zaman microphone ɗin tare da hura iska kaɗan kana yayi gyaran murya yace.
_“Bismillahir Rahmanir Rahim, Innalhamdulillah nahmaduhu wanasta'inuhu wanastaghfiru wa'nazubillahi min shururi anfusna wamin sayyi ati a'amalina, man yahdillahu fala mudillahlah waman yudlil fala hadiyala, Wa'ash hadu Allah ilahalillahu, Wa'ash hadu anna Muhammadu Abduhu wa Rasulullah (S.A.W)”._
Sai kuma ya ɗan lumshe idanunsa tare da sauƙe Ajiyar zuciya kana ya cigaba da cewa.
“Duk kan yabo da godiya su tabbata ga Allah subhanahu wata'ala mai kowa mai komai, da yakawo mu wannan lokaci da muke shirin karɓan hutu saboda gabatowan wannan wata mai falala, haƙiƙa watan Ramadan wata ne mai falala da rahma wanda duk kan musulmi yake da burin ganinsa.
Baki ɗaya wajen shiru yayi kowa ya maida nutsuwarsa zuwa garesa yayin da Samira kejin aduk lokacin data mallakesa babu macen da takaita sa'a a faɗin wannan duniya tamu ta bani adam.
Malam Arɗo kuwa Aransa yake jin Moddibo ne Garkuwa kuma ginshiƙin makarantarsa.
Moddibo kuwa cikin yanayin sanyin Muryar sa mai cike da nutsuwa ya cigaba da cewa.
“An abu Huraira ta radiyallahu anhu,
_Manƙama Ramada Imanan Wahtisaban gufra lahu mata ƙaddama min zambi muttafaƙun Alaik”_
Ma'ana ankarbo daga Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda, yana cewa Duk wanda watan Ramadana ya kama yana mai Imani da kyautatawa ana kankare masa zunubansa da suka gabata”.
Ya sauƙe sanyayyar Ajiyar zuciya mai sanyi kana ya cigaba cewa.
“Wannan kaɗai zai iya nuna maka muhimmanci da kuma darajar wannan wata hakika wannan watar ba wata bane na wasa watane daya kamata mu tsaya mu miƙa lamuranmu ga Ubangiji Mabuwayi gagara Misali, sannan mukasance masu yawan Karatun Alkur'ani, Istigfari, hailala da kuma tasbihi, ba sai na tsawaita ba ko naja duk abinda zance kun sani”.
Sai kuma ya maida kallonsa ga sauran Malaman yace.
“Koda akwai mai magana?”.
Duk suka girgiza kai alamar babu Moddibo kuwa M Jameel ya miƙawa microphone ɗin kana ya koma ya zauna shi kuwa M Jameel bayanai ya ƙara akan na Moddibo kana ya sanar dasu Bayan Sallah da sati ɗaya zasu dawo.
Yana gama Maganar ya juya tare da kallon Khausar da ita adai-dai lokacin Idanunta na kasansa cikin Sanyayyar Murya yace.
“Lelewal zoki rufe mana da addu'a!”.
Anutse Khausar ta gyaɗa kai tare da miƙewa.
Shikuwa Moddibo kallon mamaki yabin M Jameel dashi amma baice komai ba.
Amina kuwa jitayi tamkar zuciyarta zai buga saboda baƙin ciki da kishi.
Ita kuwa Khausar cike da tsoron Modibbo dake sa ta nemo nutsuwa ta amshi microphone ɗin cikin zazzaƙan Muryanta tayi addu'a kana aka tashi kowa ya watse dalibai nata murnan hutu kowa ya koma gidansu cike da farin ciki.
Da daddare Khausar na zaune akan 1sitter hannunta riƙe da wayar Mommy yayin da Mommy kekan 3sitter ta miƙe ƙafafunta Hannunta riƙe da kofin tea.
Anutse Mommy ta ɗago kanta tare da sauƙe Idanunta dake kan Khausar Wacce baki ɗaya hankalinta ke kan wayar da take dannawa ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.
“Khausar tunda an baku hutu ko dai za kije Jauro Yaya kuyi azumi tare".
Da sauri Khausar ta ajiye wayarta tare dasa hannu ta dafe ƙirjinta tace.
“Nashiga Ukuna! Dan Allah dan darajar Annabi Mommy Kar kiyi Wannan maganar, kibar tsohuwar nan tunda dai bata ne maba”.
Kai Mommy ta gyaɗa kana tace.
“Toh shikenan yanzu azumi saura sati amma nasan zaiyi wuya acikin satin nan idan bata neme kiba”.
Marerece fuska Khausar tayi kana tace.
“Allah yasa karma ta nemeni duk da garin yamin daɗi Mommy amma inaso in tayaki aiki”.
Murmushi Mommy tayi kana tace.
“Toh shikenan ba matsala hakan ma Allah ya zaɓa Mana abinda yafi zama alkhairi”.
Acan ɓangaren su Hajiya Lami kuwa zaune take afalon Hajiya Bunayya tare da Samira Sani da kuma Amina.
Kallon Hajiya Lami Hajiya Bunayya tayi kana tace.
“Yanzu dai saura mana watanni biyu mu gama cika Umarnin Boka Kar'uzu na watanni shida daya ɗiba mana kada muyi Sallah, kafin na ƙarshe da zamuyi muje mu karɓi maganin su zo suyi aiki dashi”.
Murmushi Hajiya Lami tayi tare da jinjina kai tace.
“Eh haka ne bayan Sallah da sati Uku zamu gama”.
Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.
“Gashi kuma azumi ya gabato amma acikin wannan azumin ma ace ba zamuyi sallah ba kuma watan falala da ibada!?”.
Wani kallo Hajiya Lami tayi mata kana tace.
“Idan ke zakiyi sallah ki ɓata aikin da kikayi to kinyi na wancan watannin shida da kika samo fuskar ’yar ki ya dawo dai-dai a idanunsa, sannan yanzu wata ɗaya da rabi daya rage ne zaki ɓata ba zaki iya jira ba. Agaskiya nikam zan cika ƙa'idata domin in samu cikar burin ‘yata”.
Samira kuwa zama ta gyara tana fuskantar Hajiya Bunayya da kyau tace.
“Agaskiya Ummah kar muyi wasa da wannan damar da muka samu idan yaso idan muka gama sai mu rama bashin sallah dake kan mu!”.
Ita kuwa Amina Kallon mahaifiyarta tayi tare da ƙanƙance Idanu kana tace.
“Yanzu ke Ummah wasa zakiyi da wannan damar da muka sha wahala tsawon watanni muna yi!?”.
Zare ido Hajiya Bunayya tayi tare da nuna kanta da yatsa tace.
“Ina waya faɗa miki ko an faɗa miki daɗi nake ji ga yayarki azaune gaki kuma kema azaune”.
Ta ida maganar dai-dai lokacin da Asiya ta fito daga Bedroom bayan ta gama sauraron duk abinda suke faɗa zama tayi akan 1 sitter dake fuskantar Hajiya Bunayya cikin sanyin murya tace.
“Gaskiya Ummah!, Gaskiya Ummah!! Kada neman duniya yasa mu rasa ƙiyama tare da rahamar Ubangiji, Ummah sallah da arayuwar duniya itace farkon abinda za'a bin ciki mutum dashi aranan gobe hisabi idan tayi kyau abin cika sauran abubuwa idan kuma ba tayi kyauba, baza ma aje ga sauran abubuwan ba”.
Tayi ƙasa da Idanunta ganin shegen kallonda Umman take bin ta dashi bata damu ba ta cigaba da cewa.
“Ummah aduniya Allah ya Umarceki da kiyi sallah da Azumi amma Boka La'anannen yace kada kiyi, sannan ki biye masa har ki yarda sannan ki riƙa ɗaura ‘yarki akan gurɓatacciyar hanya nikam wannan al'amari yana tayar min da hankali, wannan al'amarin sam bai yi ba yanzu dama akan wannan turban kuke tafiya?”.
Ta saki Ajiyar zuciya tare da gyara zamanta kana tana ƙoƙarin maida hawayen dake ƙoƙarin zubo mata cikin dauriya ta cigaba da cewa.
“Shiyasa tun da na dawo sati biyu banga kinyi alwala ko Sallah ba?, Ni nayi zaton ma al'ada kike yi,Itama Amina naga bata sallah dana tambayeta saita kama yimin rashin kunya”.
Amina dake jifanta da mugun hararane tayi saurin katseta tare da cewa.
“Anyi miki rashin kunyar keda ba kyabin Ƙa'ida da Umarnin Bokan baga ki har yanzu baki auru ba!sai shegen iyayi da kwainane!”.
Asiya da Idanunta suka ciko da ruwan hawaye ta kalli ƙanwar nata cike da mamaki sai kuma tayi murmushi mai ciwo tace.
“Wannan Allah ne bai nufaba, idan Allah ya saƙƙo da lokaci zanyi shi domin Aure da mutuwa lokacine”.
Atsawace Hajiya Bunayya tace.
“Rufe min baki, keda ma can ba'a haɗa shiri dake ya tafi dai-dai, dama ke da magautana kike tare kina nan kamar wancan matar ce ta haifeki”.
Asiya ta danne kukan dake neman kufce mata tace.
“Ba haka bane Ummah zanso mu gudu tare mu tsira tare ne, bazan so ganin ku cikin halaka ba Umma kuyi tunani akan wannan rayuwar da kuka jefa kanku".
Hajiya Lami kuwa cikin fushi tace.
“Wannan dai akwai gantalelliyar yarinya shegiya mai shegen mugun halin jaraba, duk yanda akayi wancan gafalalliyar kishiyar Uwar taki ta baki nononta kinsha”.
Kallonsu kawai Asiya keyi cike da mamaki.
Hajiya Bunayya kuwa Afusace tace.
“Bana son gaskiyar taki ki riƙe abarki.
ki gudu ke kaɗai mu ma mu gudu mu kaɗai kiga wanda zai riga isa tsakanin mu da ke”.
Cikin tsananin tashin hankali Asiya tace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n.
Allahumma Ajirni fi musibati wa'ahlif khairan minha”.
Ta ida addu'ar tare da miƙewa ta shiga Bedroom ɗin su akan gado ta faɗa tare da dafe kanta tace wannan wani irin Masifa ce Ummah ta jefa kanta.
Acan falo kuwa Ummah suka cigaba da tattaunawa tare da tsaida matsaya akan idan sun kammala aiki zasu biya Sallolin da ake binsu.
Washe gari.
Da hantsi misalin 12:00 Khausar na kwance A Bedroom kamar daga sama tajiyo Sallamar Hajja Nana da sauri ta miƙe tare da zama Atsakiyar gadon ta kasa kunnenta dan tabbatar wa shin ita ɗin ce ko kuwa.
Aikuwa Muryan Mommyn ta taji tana cewa.
“A'a Hajjar Allah Maraba sannu da zuwa Allah raine Jaɓɓama,Jaɓɓama Yottu,yottu”.
Ita kuwa Khausar wani irin zare ido tayi sai kuma ta miƙe da sauri ta fito abakin Bedroom din ta tsaya Idanunta akan Hajja Nana da Dije dake tsaye agefenta.
Jan zuciya Khausar tayi tare da tsaida idanunta akan Hajja Nana tace.
“Kece?”.
Harara Hajja Nana ta watsa mata da faɗin.
“Toh ki koreni wato ba kyason ganina!?”.
Tura baki Khausar tayi tace.
“A'a".
Sai kuma ta juya tare da kallon Dije dake tsaye tana kallon falon da dugu ta nufi Dije tana cewa.
“Oyoyoo Dije nayi kewarki ya gida ya Goggo Nanne?,Ya Yaya Abba?,Ina Sadik?, Yasu Baffa Jauro?, Baffa Sadu?,Baffa Liman?, Baffa Garga? Ina Bishiyar Ƙare zencen ka ina Rafi?”.
Murmushi Dije tayi kana tace.
“Duk suna lafiya kuma sunce agaisheki da kyau da kyau”.
Tayi murmushi tace.
“Allah sarki nima nayi kewarsu sosai”.
Cikin sakin fuska Mommy ta fito daga kichen hannunta riƙe da Flaks da kuma kofi biyu ajiyew tayi, kana ta koma ta ɗauko fruits duk ta ajiye agaban Hajja Nana data hakimce akan kujera sannan ta zauna still fuskarta da Murmushin daya kasa ɓoyuwa tace.
“Sannu Hajja kunsha hanya ya mutanen gida?”
Ta ida maganar tana tsiyaya mata Tea a kofi.
Amsa Hajja Nana tayi ta kai bakinta.
Mommy kuwa miƙewa tayi ta shiga kichen dan haɗa mata abinci.
Hajja Nana kuwa juyawa tayi tare da kallon Khausar dake maƙale da Dije kana tace.
“Wato ba zaki gaisheni ba, Dije ce kikayi farin cikin ganinta ni bakiyi farin ciki da ganina bako!?”.
Ya mutse fuska Khausar tayi tace.
“Tun ɗazu nake ta gaisheki kina fama da ciye-ciye baki jini ba”.
Sake baki Hajja Nana tayi tare da riƙe haɓa sai kuma tace.
“Ubanki nake baciye-ciye ba”
Hannu Khausar ta buɗe da faɗin.
“Ɗanki kika zaga dama kin barsa ya kwanta cikin kabarinsa acikin salama da yafi”.
Ta ida mgnar idonta na ciko da hawaye dan Allah ya sani bata son a zagar mata mahaifi.
Hajja Nana ta ajiye Kofin shayin dake hannunta ta nuna Khausar da hannu tace.
“Ki kiyaye nifa,Ki kiyayeni fa Khausar”.
Tura baki Khausar tayi kana tace.
“To ai gaskiya na faɗa”.
Ita kuwa Hajja Nana na ɗaukar kofin shayinta tace.
“To ya miki kyau koma mene ki ƙarata can, yanzu kishirya ki haɗa kayanki tare zamu tafi zamu je muyi azumi acan”.
Kallonta Khausar tayi kana tace.
“Mu tafi ina?”.
Hajja Nana tace.
“Eh mana Khausar mu tafi Jauro Yaya”.
Da sauri Khausar ta maida kallonta gareta kana tace.
“To ai muna zuwa hadda”.
Hajja Nana tace.
“To ai wannan ba abin damuwa bane idan muka je sai Malam Liman ya riƙa ƙara miki”.
Kai Khausar ta girgiza kana tace.
“Baza ki gane bane, inada abubuwan da zanyiwa Mamana ɗin nan da kike gani ina taya ta aiki”.
Hararanta Hajja Nana tayi da faɗin.
“Dama kece mai taya ta aikin ina masu taya ta aikin?”.
Zare ido Khausar tayi kana tace.
“Tayi cikin shege ankoreta ta koma ƙauyensu.
Mai gadin muma ana canza shi saboda shi ya mata ciki”.
Da mamaki Hajja Nana tace.
“Ash'sha Subhanallahi ashe gidan naku babu tsaro kenan, ashe ku gidan bayan maita hadda rashin tsaro a'a maza-maza shirya mu tafi”.
Dai-dai lokacin da Mommy ta fito girgiza kai tayi tace.
“Kai Khausar bakyajin magana maza ki ɗauka wa Dije abinci ku wuce ɗakin ki”.
Kai Khausar ta gyaɗa tare da wucewa kichen ta daukawa Dije abincin sannan suka wuce Bedroom ɗin.
Mommy kuwa zama tayi agefen Hajja Nana tare da ajiye mata tiren abinci cikin sanyin murya tace.
“Hajja Nana kiyi haƙuri da halin Khausar zaku tafi idan hakan kike so”.
Kai Hajja Nana ta gyaɗa kana tace.
“Toh babu damuwa amma tace min baki da lafiya da gaske ne?”.
Kai Mommy ta Jinjina kana tace.
“Eh wallahi kwanakin nan duka ban cika jin daɗi ba bansan meke damuna ba!”.
Jinjina kai Hajja Nana tayi kana tace.
“Subhanallah Allah ya sawwaƙa Allah ya yaye.
Kuma da gaske ne mai aikin ku ta haihu cikin shege?".
Dai-dai lokacin Hajiya Bunayya da Amina suka shigo falon.
Ɗaga kai Mommy tayi tare da kallon Hajiya Bunayya data zauna tace.
“Hajiya ga Kakar Khausar”.
Murmushi Hajiya Bunayya tayi Idanunta akan Khausar tace.
“Ai na ganeta Hajja Nana sannu da zuwa ina yini ya gajiya kunzo lafiya?”.
Ita kuwa Amina batare data ƙarasa shiga falon ba ta ɗaga sautin Muryanta da faɗin.
“Khausar!, Khausar!! Khausar!!!,”.
Daga ciki Khausar tace.
“Me?".
Afusace Amina tace.
“Bana son rashin kunya