Showing 24001 words to 27000 words out of 188939 words
Chapter 9 - SAKAYYA Book 1 complete BY GARKUWA.txt
Khausar tayi tace.
“A'a zanci anan”.
Ta juyi ta dubi Khausar da kyau tace.
“Kizo mu tafi nace”.
Shi kuwa Lamiɗo cike da ladabi yace.
“Da kin barta munci anan ɗin babu matsala”.
Juyawa Hajja Nana tayi kafin tace.
“Toh shikenan”.
Miƙewa Khausar tayi tabi bayanta ta karɓo ƙananan akwashi aka zuba mata sannan suma suka zuba,Yanayin sanyin da ake tsugawa agarin yasa mazauna garin ke bukatar abu me ɗumi,Suna cin zabbin suna ɗaurawa da Nono me ɗumi bayan sun gama Khausar ta miƙe ta tattara akushin ta mayar.
Ganin ta mayar ne yasa Hajja Nana fitowa suka zauna.
Atake sega yara suna ta shigowa a jere a jere angama abincin rana suna kawowa duk gida Jen garin Hajja Nana tana da kwanonta acan suna kawo mata abinci domin ita bata girki abinci safe ne kawai bata Yarda akawo mata ita take dafa wanda zata ci,Duk ƙannenta taran nan sai ankawo kwanuka tara an ajiye mata ga kuma na 'ya'yansu da sukayi Aure tana da ƙore goma sha uku.
Ga yaran garin ƙanana kyawawa dasu farare soll kamar irin yaran ƙauyen larabawa.
Lamiɗo da kansa da yaga yaran na shigowa sun basa sha'awa,Ko wacce idan tashigo zata ce.
“Goggo Hajja! Goggo Hajja!! Aɗonna”.
Ƙannenta da Addah Nana suke kiranta 'Ya'yan ƙannenta kuma Goggo Goggo Hajja idan kuma jikoki zasuce mata Hajja Nana.
Duk Wacce ta kawo mata abinci zata ce nice,daga gidan Sadu,Nice daga gidan Garga,saboda yawansu kowa ke gabatar da kansa.
Duk wanda yazo ya ajiye zata ce.
“Angode masu nomawa Allah ya basu ƙarfi da lafiyar nomawa masu girkawa ma Allah yabasu ƙarfin girkawa”.
Sannan ga yanayin tsarin yaran garin babu alamar ƙazanta ajikinsu ko wanne tsaf dashi ga kuma tarbiyya duk wanda suka zo sai sun tsugunna sun gaida Lamiɗo da Momy da fulatanci kasancewar basu iya Hausa Sosai ba.
Ɗaya daga ciki data zone ta ajiye kwanon Idanunta akan Khausar tace.
“Goggo Hajja Khausar naa” .
Murmushi Hajja Nana tayi tace.
“Eh”.
Murmushi yarinyar tayi ta matso kusa da Khausar tace.
“Sunana Dija”.
Murmushi Khausar tayi tace.
“Yayi kyau Dija”.
Dija ta kuma murmushi tace.
“Kullum Goggo Hajja na bamu labarin ki rabonki da nan tun kina ƙarama yanzu ya kai shekara shidafa ake cewa”.
Kai Khausar ta jinjina da faɗin.
“Eh”.
Hannunta Dija ta riƙe tace.
“Kizo muje gidanmu ku gaisa da Mamana”.
Ta ƙare mgnar tare da jan hannu Khausar suka fice...
Kiran sallan Azahar yasa Lamiɗo ya miƙe ya tafi masallaci tare da Ƙannen Hajja Nana ita kuma Momy tayi alwala tare da gabatar da sallah bayan sun idar da Sallah Hajiya Aysha ta ɓude jakan da tazo dashi ta fito da turaman zannuwa da Sabulai ta miƙawa Hajja Nana.
Murmushi Hajja Nana tayi tace.
“Hadda ɗawainiya haka?,To angode Allah yayi albarka”.
“Ameen”, Momy ta amsa kafin tace.
“Hajja ga Khausar nan na kawo tayi hutu amma mako uku ne hutun nasu”.
Murmushi Hajja Nana tayi tace.
“Toh Nagode”.
Ita ko Momy tana gyara mayafinta tace.
“Sati uku ne hutun nasu”.
Faska Hajja Nana ta tsuke tare da cewa.
“Sai kin sake Jaddada min ne?”.
Da sauri Momy ta girgiza mata kai.
Cikin isa tace.
“Toh sai sanda naga dama zata dawo kinyi naki saura nawa”.
Ƙasa da kai Momy tayi tare da faɗin.
“Shikenan Hajja duk yanda kikace yayi mukan zamu tafi”.
Miƙewa Hajja Nana tayi tace.
“Bari akira muku Khausar kuyi sallama”.
Cike da ladabi Momy tace.
“A'a Hajja base ankira taba”.
Dan tasan muddin aka kirata sai tayi kuka kafin su rabu.
Sallama suka sake yi musu kafin suka fice suka tafi...
Acan Gembila kuwa Washe gari.
Asabar Moddibo ya shirya kamar ko yaushe cikin Jallabiya Sky blue Kansa sanye da hula da kuma hirami cikin nutsuwarsa kamar ko yaushe ya shiga cikin makarantar yana motsa laɓɓansa alamar tasbihi da hannu kawai yake amsa gaisuwar da ɗaliban haddar ke masa kai tsaye Ajin haddarsu Khausar ya nufa yayin da Aransa yayi ƙudurin sawa Malam Bello ya casa masa ita saboda gaba ta kiyaye domin ya lura ganganci da sakalci ke damunta.
Cikin rashin sa'a yana shiga ajin ya samu bata nan.
Asma'u ya kira.
Cike da ladabi ta fito tare da tsugunnawa agabansa tace.
“Gani Yah Moddibo”.
Tsayuwar sa ya gyara cikin yanayin sanyin Muryansa yace.
“Ina wannan Birin?”.
Asma'u kuwa kanta aƙasa tace.
“Nima yau da nazo ban ganta ba sai nake tambayar Amina ina take shine tace wai taje garin Kakanninta”.
Ƙwafa yayi yace.
“Shikenan yayi kyau”.
Kana ya juya ya bar waje....
Acan mota kuwa Momy ta dubi mijinta tace.
“Kayi hakuri da Hajja Nana yanayin tsufa ne”.
Murmushi yayi still Idanunsa ahanya yace.
“Ai bakomai ba gamu da Gimbiya Dadu ba ai haka take”.
Acan Rugar Jauro yaya kuwa bayan Khausar ta dawo gida ta tar da Momy ta sun tafi ta tsare Hajja Nana da ido tace.
“Meyesa ba ki kirani ba kafin su tafi?”.
Salati Hajja Nana ta sanya tace.
“Tuhuma ta kikeyi? Ko kuma me?”.
baki ta cinna sama tare da cewa.
“Ai gaskiyane abinda ya dace na faɗa”.
Salati Hajja Nana ta sanya tare da faɗin.
“Ohhh ni Shatu Allah ya nuna min 'yar Usmanu yarinya kamar ruwan aski sai rashin ta ido”.
Ta ƙare mgnar tana kallon Khausar dake tsaye fuska akumbure cikin tsawa tace.
“Bari kiji in faɗa miki ni agarin nan idan nayi magana kamar yankan wuƙa yake babu me bani Amsa ko musu ko jayayya dani!”.
Ita kuwa Khausar wani irin juya Ido sama tayi tare kana tace.
“Uhummm to gwara ma ki sani.
Idan maganarki yankan wuƙa ne to kin samu me yankan rez”......!
Littafin SAKAYYAH na kuɗine biya ki karanta 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA
By
*GARKUWAR MARUBUTA*
📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇
*SAKAYYAH*
_Page 5_
*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FREE PAGE*
*LITTAFIN SAKAYYAH NA KUDINE, 1K NE KACAL ki biya ki karanta cikin Aminci ba haƙƙin wani a kanki. 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276.*
Zare Ido Hajja Nana tayi cikin faɗa da fushi tace.
“Ke! Ke!! Ke!!!.Faɗimatu ki kiyayi kanki dani fa zan tsige Miki fuka-fukinki!”.
Ita kuwa khausar fuska ta haɗe Idanunta tsaye akan Hajja Nana tace.
“Nifa ba tsuntsuwa bace da zaki tsige min fuka-fuki, ai gaskiyane tsakani da Allah da Annabi mahaifiyata zata tafi kinsa ankawo ni aise ki kirani muyi sallama na musu Allah ya tsare”.
Ta ƙare mgnar tare da juyawa ta kalli Dija tace.
“Fisabillilhi ba haka ya kamata ba Dija?”.
Dija kuwa tuni ta sunkuyar da kanta yayin da jikinta ya shiga ɓari tsananin tsoro ya bayyana afuskarta sanin halin Hajja Nana babu wanda ya isa tana magana yana mayar mata da martani!.
Cikin rawan jiki da tsoro daya bayyana amuryanta tace.
“Khausar kidena kar ki sake bata amsa ki bata haƙuri”.
Tana ida maganar ta tsugunna gaban Hajja Nana tace.
“Goggo Hajja Waɗɗu munyal”.
Hajja Nana kuwa kwaffa tayi kana tace.
“Aaaa Dija matsa kusa da ita inzo na same ta ai ke ba ruwanki”.
Ita kuwa khausar batare da tsoro ba tace.
“Toh kizo mana kawai dan mutum ya faɗi gaskiya don dai ba'a son gaskiya da zaman lafiya ai yakata dai akirani muyi sallama da Momyna tunda dai ansa an kawoni wataƙila ma sai nayi sati biyu ko uku bangan taba aida se akirani muyi sallama ince agaida mutanen gida sannan nayi musu fatan isa gida lafiya”.
Ita kuwa Hajja Nana afusace tace.
“To idan kece zaki kaisu gida lafiya kada Allah yasa ki kaisu shegiyar yarinya mara ji Ɓee Usmanu La'ilaha illallahu ohoho gabtarel”.
Tuni Baffa Jauro da Baffa Sadu suka shigo idanun su akan yayar tasu suka ce.
“Lafiya Addah Hajja?”.
Kai ta girgiza tare da nuna Khausar dake cika tana ba tsarewa tace.
“Ɓeee Usmanu,Nikam ban taɓa ganin fitsararriyar yarinya kamar 'yar Usmanu ba”.
Itade Khausar na jingine jikin bango tana tura ƙaramin bakinta dake ƙarawa fuskarta kyau.
Kallon ta Hajja Nana tayi cikin harara tace.
“Nikam Usamanu na Kam ba haka yake ba, haka zalika Mahaifiyarki ko surukata ce bazan mata ƙazafi ba macece mao mutunci amma ke kam waya fitsare miki Ido? Kodan zama tsakiyan Mayun gidan kune yasa kika zama haka!?”.
Khausar dake jingine da bango ta ɗago kanta kana ta wara manyan Idanunta masu kyau da tsari tace.
“Nikam de kar kice min Mayya idan su Mayu ne toni ba Mayya bace idan kince ni Mayyace sede idan awajenki na gada!”.
Baffa Jauro da Baffa Sadu suka dubi juna alokaci ɗaya cikin ƙasa da murya yanda Hajja Nana ba zata jiba Baffa Jauro yace.
“Lalle akwai rigima anan? Addah Hajja ba abata amsa idan tayi magana amma ga 'yar Usmanu daga zuwa tana bata amsa gatse-gatse jika kenan mafi akasari duk zafin mutum jikoki bazasuji tsoronka sosai ba”.
Murmushi Sadu yayi yana jinjina kai.
Baffa Jauro kuwa kan Khausar ya ɗan buga yace.
“Kay Hausajo kidena mu ba'a rashin kunya agarin nan!”.
Ita kuwa khausar inda ya ɗan bugeta tasa hannu ta riƙe tana sosawa duk da cewa bawai zafi ya mata ba ta tura ƙaramin bakinta tace.
“To ai muma ba rashin kunya bane wannan kam”.
Dan ƙolo ya mata yace.
“Dije jata ku tafi”.
Kai Dije ta gyaɗa wacce se alokacin ta samu kuzarin miƙewa tace.
“Khausar kizo mu tafi“, Sannan taja hannunta suka fita.
Suna fita Khausar kuwa hannunta dake cikin na Dije ta janye tace.
“Yanzu ina zamuje?”.
Murmushi Dije ta sakar mata tace.
Rafi zamuje”.
Murmushi mai sanyi Khausar ta sakar mata wanda ke ƙarawa fuskarta kyau tace.
“Toh mu tafi”.
Dan sosai weather garin yake abin burgewa da sha'awa.
Cikin nutsuwa suka nufi Rafin suna hira.
Da sauri Dije ta riƙon hannun Khausar tare da nunawa mata gefen damansu, masu wasa da birine ke tafiya kana yaran rugagen dake gefe dasu na biye dashi, bisa alamun yanzu kuma rugarsu zasu shiga.
wani ƙaton Biri yake ta kolongoiso yara nata ja da baya.
Cike da nishaɗi Khausar tace.
“Muje muma mu gani”.
Kai Dije ta gyaɗa mata , kana suka nufi wajen me wasa da Biri suna ganin yanda Birin ke duk abinda aka sashi.
Cike da farin ciki Khausar ta kalli mai wasa da Birin tana ƙara kusawa cikin yara matan tace.
“Mai Biri yanzu duk abinda na sashi zai min?”.
Kai mai wasa da Birin ya jinjina yace.
“Idan kuma baki yarda ba ki gwada ki gani”.
Kusa da Birin Khausar ta matsa tana murmushi tace.
“Yauwa yaya salon mugun Malami yake idan zai daki ɗalibansa?”.
Da sauri ta ware idanunta ganin.
Birin ya wani ja baya tare da harɗe hannunsa aƙirji kana ya ɓata fuska tare da harɗe sawunsa sai kuma ya ɗauki wani sanda ya riƙe yana nuna Khausar da Dije.
Hannu Khausar tasa ta dafa kafaɗar Dije tare da tintsirewa da dariya mai cike da sautin shauƙi yayin da ɗaya hannun kuma ta ɗaura saman shafefen cikinta tana mai cigaba da dariyar.
Domin kuwa babu wanda ya faɗo mata arai lokacin da Birin ke gwadawa face Moddibo duk da kasancewarsa ba mutum ne mai Fara'a ba amma duk sanda zaisa a zaneta a makarantar Islamiyya seya sake tamke fuskarsa..
Dariya sosai takeyi wanda da yawa cikin yaran tayata sukeyi.
Ganin bata da niyyar daina dariyar ne yasa Dije jan hannunta cikin dariya tace.
“Khausar Mu tafi,Dariyar me kuma kike haka!?”.
Tsagaita Dariyar Khausar tayi sai kuma lokaci ɗaya jikinta yayi sanyi tuna wa da tayi Moddibo zai iya jira duk lokacin da tawo ya yanke mata hukunci ahankali tace.
“Kawai na tuna da wani Malamin mune”.
Murmushi Dije tayi tace.
“Allah sarki shike zaneki kena”.
Kai ta jujjuya tare da cewa.
“Wancan da shegen madarar ƙasaita sawa yake a zaneni dai yana nan jiki kamar auduga ai shi dukan ma aikine a wurinsa”.
Murmushi Dija tayi tare da cewa.
“Da Goggo Hajja zataji haka sai ta sa mishi al'barka”.
Baki ta tura ba tare da tace komai ba sukaci gaba da tafiya.
Suna shiga Rafin idanun Khausar ya sauƙa akan Bishiyoyin Piya, Caɓɓulle, Mangoro, Ayaba, Gwanda, Gwaba, Lemo, da sauran kayan itatuwa duk sun yiwa wajen ƙawanya.
Sake wara Ido Khausar tayi ganin bishiyoyin Inabi guda uku a jere,
Cikin farin ciki ta dubi Dije tace.
“Harda Inabi Laha'Ila Ha'illalhu Masha Allah zan kuwa ci”.
Ta ida maganar tare da nufar jikin Bishiyar zata hau.
Saurin riƙe hannunta Dije tayi tace.
“Kada ki hau Khausar Baffa Liman ya hanamu yace ba shida amfani 'ya'ya mata su riƙa hawa bishiya ba tarbiyya bace mai kyau”.
Ita kuwa khausar janye hannunta dake cikin na Dije tayi tace.
“Ke rabu dashi da ƙa'idojinsa hawa za muyi mu cire abinmu, ai kuma ba har can sama zamu hauba”.
Langwaɓar da kai Dije tayi kafin tayi magana suka hango wani farin saurayi kyakkyawa daga ɗaya gefen.
Hannu Dije ta ɗaga masa da faɗim.
“Yawwa Sadik dan Allah zoka cire mana Inabi wai zata ci”.
Ƙara sowa Sadik yayi idanunsa akan Khausar yace.
“Dije wannan yarinyar wa kika samo?”.
Murmushi Dije tayi tace.
“Yarinyar Marigayi Baffa Usmanu cefa yaron Goggo Hajja”.
Murmushin fuskarsa ya faɗaɗa yace.
“Allah sarki itace wacce take Birni ko?”.
Kai Dije ta gyaɗa tace.
“Eh itace”.
Ita dai Khausar ba tace komai ba.
Raɓar bishiyar yayi ya ciro musu Inabi kana ya koma bishiyar Ayaba shima ya ciro yasa musu aƙaramin kwandon dake hannunsa irin na saƙar kaba na gargajiya miƙawa Dije yayi.
Sai asannan Khausar tace.
“Mungode”.
Murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba,
suka fara tafiya cikin rafin akai-akai Khausar ke lumshe idanunta tana wasa da yatsun hannunta sosai weather garin ya mata daɗi.
Juyowa tayi ta kalli Dije tare da cewa.
“Garinku yayi min daɗi”.
Cikin sauri Sadik yace.
“Garinmu de kin cire kanki ne a ciki? Ko kin manta nanne tushenki kuma asalinki nanfa cibiyarki take abinne”.
Dariya tayi kafin tace.
“Hmmm Shiyasa ma naji daɗin garin inba haka bama masifar wannan tsohuwar yasa bana sha'awar zuwa garin nan”.
Zare ido Sadik yayi yace.
“Wacece masifaffiyar!?”.
Asanyaye Dije za tace.
“Wai Goggo Hajja take cewa masifaffiya”.
Sake zare ido Sadik yayi se kuma yace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”,Ya dubi Dije yace.
“Meye sunanta ma kika ce?”.
“Khausar”
Dija tace.
Ya maida kallonsa kan Khausar da hankalinta yabi shuke-shuken da kallo yace.
“Khausar kiyi Istigfari”.
Khausar kuwa kallon mamaki tayi masa kafin tace.
“Saɓon Allah nayi da zanyi Istigfari?”.
Habarsa ya riƙe still Fuskarsa ɗauke da Mamaki yace.
“Goggo Hajjan kike cewa Masifaffiya”.
Baki ta taɓe tace.
“Yo ba masifaffiyar bace daga zuwa na fa kawai takama yimin bala'i”.
Kai ya jinjina kafin yace.
“Toh kar ki sake wallahi in Goggo Hajja taji abinfa baze miki daɗi ba”.
Cikin sanyin murya Dije tace.
“Allah de ya kyauta anma wannan baƙunta ai akwai kallo aciki”.
Ba wanda ya sake magana har suka fito daga cikin Rafin.
Gani tayi Sadik ya ɗauki wani babban kwando da sunyi ta fiya kaɗan sai ratsa cikin ciyawa ya buɗe ya ɗibi ƙwan Zabbi ya saka acikin kwando.
“Me kakeyi haka?”.
Khausar ta tambayesa tana kallon wajen da ciyayi masu kyau da tsari suka lulluɓe wajen.
Murmushi yayi yace.
“Ƙwan Zabbi nake tattarawa”.
Cikin lumshe ido tace.
“Ohhhh lalle kam Masha Allah abamu naci”.
Murmushi yayi tare da faɗin.
“Toh babu damuwa”.
Haka suka riƙa tafiya suna hira jefi-jefi sun kusa fita daga cikin Rafin ne Khausar ta jiyo hayaniya na tashi kamar kasuwa anata surutu da dariya jujjuya wa tashiga yi amma bata ga inda sautin surutun ke tashi ba.Ta dubi Sadik da Dije tace.
“mene nake tajin hayaniya da surutun nan kam a cikin daji?”.
Sadik ne yace.
“Mutanen Bishiyar ƙare zancen kane”.
Da sauri ta sake duban sa tare da cewa.
“Bishiyar ƙare zancen ka?,Wai mene ma'anar Bishiyar ƙare zan cenka?”.
Dije ce tace.
“Ai mu garin nan bamu da service, Service ɗinmu waje ɗaya ne inde mutum yana so yaje yayi waya seya je ya hau bishiyar ƙare zencen ka anan ne ake samun network idan kina wajen zaki iya kira sannan za'a iya kiranki kina sauƙa daga bishiyar ko kuma kina Matsawa daga wajen bishiyar toh shikenan Service ya yanke ba zaki samu kiyi magana ba kuma shima sai in layin MTN ne ko Zain”.
Cike da Mamaki Khausar tace.
“Ikon Allah wannan wani irin ruga ne?. Dama ashe har yanzu akwai irin wuraren nan daya rage aduniya?”.
Murmushi Dije tayi tace.
“Sosai ma”.
Ahankali Khausar ta ɗaga kanta nan ta hango manyan tsaunika da bishiyoyi Kallonta ta mayar kan Dije tace.
“Haba ko wannan manyan tsaunuka da bishiyoyin ai sa tare muku service da network”.
Kai Dije ta gyaɗa tace.
“Lalle kam da alama shi ya tare”.
Ta dubi Sadik dake tsintar ƙwai tace.
“Muje inga wajen”.
Kai ya gyaɗa sannan yashiga gaba ita da Dije na biye dashi ta cikin wata siririyar hanya Sadik na cigaba da tsintar ƙwo'yin suna fita asirin hanyar Khausar ta hango wani ƙaton bishiyar ɗaurawa dake ɗauke da rassan bishiya masu taren yawa saura daga sama saura kuma sun zuba yayin da ƙasansa bishiyar duwatsu ne baƙaƙe masu sheƙi ke zube wanda suke kamar kujeru.
Juyawa tayi ta maida Idanunta kan dandazon mutanen dake wajen mafi yawa Matasane sai kuma Dattijai tana ɗaga kanta sama ta hango Baffa Jauro yana waya.
Dariya ta ƙyalƙyale dashi tace.
“Baka tsoron ka faɗo ko tsohon nan?".
Dije ce ta ɗan bigi ƙeyarta tare da yi mata hararan wasa tace.
“Baban nawa ne tsoho?”.
Murmushi Khausar tayi tace.
“Toh baya tsoro ne kiga ya hau kan bishiya ya ɗane kamar birin can”.
Tsayuwa Dije ta gyara tare da mata hararar wasa tace.
“Ai shikam dole seya zo nan yayi waya tunda shine Jauron garin nan akwai ɓuƙatar magana da Jauro da sauran Jaurorin garirruwa”.
Khausar kuwa kai ta gyaɗa tace.
“Ikon Allah lalle de kam irin wannan gari haka”.
Tayi maganar tana kallon matasan dake sanye da kayan Fulani kowa na amsa wayar, Idanunta ne suka sauƙa akan wata tsohuwa dake waya.
Ta maida kallonta kan Dije tace.
“Wannan kuma fa?”.
Dije tace.
“Tafff!, Wannan ƙawar Hajja Nana ce”.
Kallonta Khausar ta sake yi tace.
“Ƙawar Masifa de zaki ce”.
Sadik dake gyara kwandon ƙwai yace.
“Ki bari fa”.
Ta kallesa da manyan Idanunta dake lumshe tace.
“Ai da gskene Hajja Nana in ba masifa ba meta iya!?”.
Duk mutanen wajen juyawa sukayi tare da zuba mata idanu jin tana kiran Hajja Nana Masifa,Wasu daga cikin mutanen ne suka ce Dije ina kika samu wannan yarinyar.
Dije kuwa tayi murmushi tace.
“ 'Yar Baffa Usmanu ne”.
Jin Abinda Dije tace yasa sauran mutane dake saman bishiyar kashe wayansu suka sauƙo.
Wani kyakkyawan Matashi fari ne ya nufosu kallo ɗaya zaka masa kasan akwai wayewa atare dashi yace.
“Wannan itace 'yar Baffa Usmanu itace ƙanwar Nenne ko Masha Allah?”.
Kai Dije ta gyaɗa tare