Showing 72001 words to 75000 words out of 188939 words
Chapter 25 - SAKAYYA Book 1 complete BY GARKUWA.txt
ni zaki yiwa rashin kunya? ina kiranki kina jina ba zaki fito ba aikin san dai tunda na kira ki ina da ɓuƙatar ki!”.
Jin surutan da take yasa Khausar ta fito tare da tsayawa daga bakin ƙofa ta riƙe ƙugunta kana tace.
“To ai tunda ke kike da ɓuƙatata kinsan inda dakina yake sai ki shiga ki sameni”.
Cike da kirsa Hajiya Bunayya tayi dariya tana kallon Khausar tace.
“Kudai in Kun hadu bakwa rabuwa da faɗa kamar wasu ƙananun yara Allah dai ya kawo muku sauƙi kuna na kamar wuta da Auduga”.
Juyawa Hajja Nana tayi ta kalli Khausar da Amina kana ta taɓe baki tare da cewa.
“To ai kinsan haka al'amarin yake, mu zuriyarmu bama gani mu ƙyale sannan bama ji muyi shiru, sannan su kuma mayu haka suke basason mai baki shiyasa baza'ayi shiri ba”.
Hajiya Bunayya tayi saurin cewa.
“Hmmm Hajiya ai tsatsonne na mayu su basu tsotsaba dan mu atsarkake muke”.
Kallon mamaki Mommy tayi mata kana tace.
“Hajiya har ke kin yarda da kalmar kenan?”.
Hajiya Bunayya ta taɓe baki kana tace.
“Ha'a abinda ake faɗa musu acikin gari mun isa mu hana ne?”.
Atake fara'ar dake fuskar Mommy ya gushe cikin rashin jin daɗin abinda Hajiya Bunayya ta faɗa tace.
“Wallahi sukam ba Mayu bane har dake ki yarda kefa komin yaya, ita Uwa ce agareki kuma kakar ’ya'yanki kuma Inde har za'ace suna ciki to mijinki ma yana ciki”.
Hajiya Bunayya kuwa cikin sauri tace.
“A'a mijina atsarkake yake.
Uwarsa kuwa ba zan musan ta mata ba yawwa a duniya idan kaji an cewa mutum maye ba zaka musanta masa ba kawai dai abinda na sani mijina ba yayi nima banayi kuma 'ya'yana na basayi.
Hajja Nana gaskiya kika faɗa taje can ta ƙarata da baƙin halinta inma tanayi can mata inma ba tayi can mata amma abinda gari dai ake faɗa tana yi, kuma mutum bashida hujjar da zaiyi musu akan hakan, gwara ma hujjar da mutum zai ɗabbaga tunda ga alamu ke yanzu ko cikin ki dake yawa zubewa bakya ta Allah ƙashi da ita!?”.
Cikin sauri tare da ɗaure fuska Mommy tace.
“A'a nikam Allah ne ya ƙaddara min zubewar ciki babu wani wanda ya zubar min da ciki”.
Murmushi Hajiya Bunayya tayi aƙasan ranta tace can miki ƙidahuma.
Khausar kuwa kallon mamaki tabi Hajiya Bunayya dashi kana aƙasan ranta tace lalle Hausawa sunyi gaskiya da suka ce iya ruwa fidda kai”.
Amina dake tsaye ta watsa Khausar Harara kana tace.
“Abbah ke kiranki kizo kakar taki tazo da wasu maza suna waje sai kije ku gaisa”.
Ta ida maganar tare da juyawa ta fice.
Ita kuwa khausar cike da farin ciki ta juya ta fice ta nufi coumpund kasa ɓoye fara'ar fuskarta tayi ganin Yaya Aliyu tsaye yaron Baffanta na Adamawa tare da Yaya Abba cikin jin dadi ta ware manyan Idanunta cike da farin ciki tace.
“Yaya Aliyu sannu da zuwa ku ƙara so”.
Ta faɗa tana yin gaba zuwa Falon Lamiɗo dake saukan baki.
Bayan sun shiga falon sun zauna ta dubi Aliyu still Fuskarta da murmushi tace.
“Yaya Aliyu yaushe kazo?".
Gyara zamansa yayi yana fuskantar ta kana fuskarsa ɗauke da murmushi yace.
“Baffanki ne ya tasoni wai sai na kawowa tsohuwar sa kayan azumi shine kuma yanzu Hajja Nana tace sai munzo”.
Khausar kuwa murmushi tayi kana tace.
“Hajja Nana rigima"
Sai kuma ta maida kallonta kan Yaya Abba dake latsa waya tace.
“Yaya Abba ya karatu?”.
Ahankali ya ɗago kansa da murmushi afuskarsa yace.
“Karatu ya ƙare yanzu wannan karon tare zamu tafi da Aliyu can Adamawa idan Allah ya nufa idan munje zan samu aiki Insha Allah tunda kinga Baffan Jimeta yana da hanya da manyan mutane Insha Allah za'a samu”.
aSaki murmushi tayi kana tace.
“Masha Allah abu yayi kyau”.
Lamiɗo ya shigo suka gaisa bayan sun gama gaisawa ya fita, Khausar kuwa Anutse ta miƙe tace.
“Ina zuwa”.
sannan ta fice.
Kai tsaye kichen ɗin su ta nufa ta ɗauko Babban Warmers da faranti ta fita.
Hajja Nana ta bita da kallo baki sake ganin Uban kula me kyau da tsari da tafita dashi.
Ba daɗewa Khausar ta dawo ta sake ɗaukan Flaks da kofuna.
Har takai ƙofa Hajja Nana data kasa haƙuri tace.
“Kede akwai Jaira mara kirki tunda nazo kike wani shan ƙamshi kamar baki so zuwa na ba, ko arzikin gaisuwa ban samu ba bare insa rai da ruwan sha, amma wa'annan saboda 'yan uwanki ne jiki na rawa kin wani kinkimi Uban kula kin fita yanzu kin dawo kin ɗauki Flaks”.
Kallonta Khausar tayi tare da taɓe baki tace.
“Kinga sai anjima Ni sauri nake”.
Tana gama fadar haka ta fice bakinta ɗauke da Sallama tashiga falon.
Amsawa sukayi tare da kallonta.
Zama tayi tare da buɗe Warmers din ta ɗauki babban Plate ta zuba musu shin kafa da miyar da yaji naman kaza sai kuma haɗin coslow kana ta zuba musu shayi dake tururi.
Yaya Abba yayi Murmushi yace.
“Da'alama wannan girkin kine saboda wannan ƙamshi”.
Murmushi tayi amma batace Komai ba.
Acan ɗaki kuwa bayan ankira sallan Azahar Mommy takai Hajja Nana har toilet ɗin ta tayi alwala kana ta fito ta gabatar da Sallah bayan ta idar tayi adduo'i.
Ta juya ta kalli Mommy dake riƙe da carbi ahannunta tace.
“Aisha”.
Cike da girmamawa Mommy tayi ƙasa da kanta kana tace.
“Na'am”
Hajja Nana kuwa gyara zamanta tayi tare da tattara duk kan nutsuwarta zuwa kan Mommy tare da cewa.
“Magana ce mai muhimmanci ta kawoni”.
Cikin girmamawa Mommy da kanta ke ƙasa tace.
“Toh ina sauraronki Hajja Nana”.
Hajja Nana kuwa Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.
“Magana ce akan Khausar da kuma ɗan Baffanta wato Aliyu”.
Jinjina kai Mommy tayi cike da ladabi tace.
“Toh Hajja Nana ina jinki”.
Hajja Nana ta gyara zamanta tare da cewa.
“Toh zuwa yanzu dai inaga Khausar ta girma, sannan inaga ta gama karatun ta yanzu idan ma bata gama ba to ta kusa”.
Jinjina kai Mommy tayi kana tace.
“Eh ta kusa Insha Allah yanzu kam Shekara ɗaya yarage bayan sallah Insha Allah zata tafi ajin ƙarshe na gama makarantar gaba da primary”.
Cikin jinjina kai Hajja Nana tace.
“Masha Allah Ubangiji ya taimaka”.
Mommy ta amsa da.
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.
Hajja Nana kuwa duk kan nutsuwarta ta tattara tare da cewa.
“To ai yanzu dai ta samu ta kori jahilci ta yaƙesa, yanzu batun aurenta za'ayi.
Ga kuma Yayanta kuma ɗan Uwanta za'a aura Matashi magana ya ƙare sannan kuma idan karatun take so ta cigaba idan sunyi aure zata yi acan jahar Adamawa tunda suna da makarantu manya-manya acan dan haka yanzu batun aure ne ya kawo mu nazo dashi za'a haɗa bayan sallah in Allah ya yarda”.
Akuma dai-dai lokacin Khausar ta shigo ɗakin, cike ka ɗuwa Idanunta na kan Hajja Nana cikin sauri tace.
“Wai me naji kina cewa?”.
Cikin isa, gadara, Hajja Nana ta wurga mata Harara kana tace.
“Batun Aurenki nakeyi”.
Arazane Khausar ta zare ido kana tace.
“Wa.....!
📝✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇
*SAKAYYAH*
_Page 13_
_NA_
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci da salama, ba haƙƙin kowa akanki. Littafin 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Sai in saki a Group ɗin littafin inda zan rinƙa posting.
Khausar kuwa cikin tsare Hajja Nana da ido ta riƙe ƙugu tare da cewa.
“Gaskiya nikam bana son irin wannan mulkin mallakar naki”.
Da sauri Mommy ta ɗaga mata hannu fuskarta babu walwala ta kalli Khausar kana tace.
“Kifita, daga nan Khausar!”.
Lokaci daya fara'ar data shigo da shi ya gushe ɓacin rai ya mamaye mata zuciya juyawa tayi ta fice daga Bedroom ɗin Mommy ta nufi nata tana shiga Bedroom ɗin ta jiyo Muryan Asma'u afalo.
Kai tsaye Bedroom ɗin Khausar Asma'u ta shiga tare da cewa.
“Assalamu Alaikum”.
Atare Dije da Khausar suka amsa da.
“Wa'alaikum Salam”.
Asma'u naganin fuskar Khausar ta ware Ido kana tace.
“Ya dai mutuniyar naga fuskarki haka?”.
Wani abu mai masifar ɗaci Khausar ta haɗiye Idanunta akan Asma'u dake tsaye ta gyara zamanta tare da faɗin.
“Babu komai ƙara so ki zauna”.
Zama Asma'u tayi tare da tsare Khausar da ido ganin yanayin damuwa atare da ita.
Kallon Dije Khausar tayi sai kuma ta juya ta kalli Asma'u tare da faɗin.
“Wannan Itace Dije”.
Murmushi Asma'u tayi Idanunta akan Dije ta ajiye Handbag din dake hannunta kana tace.
“Sannunki”.
Murmushi Dije tayi tare da faɗin.
“Yawwa”.
Juyawa Asma'u tayi tare da kallon Khausar kana tace.
“Khausar wacece ban ganeta ba”.
Muskutawa Khausar tayi tare da gyara zamanta kana tace.
“Dije ce wacce nake baki labarin ta a Jauro Yaya”.
Jinjina kai Asma'u tayi tare da faɗin.
“Ohh Ayyah na tuna ta itace tazo ita da Hajja Nana suka zone?”.
Khausar kuwa kai ta gyaɗa mata kana tace.
“Eh"
Murmushi tayi tare da faɗin.
“Ai lallai dai kam kice muna da manyan baƙi Dije amma zamu daɗe ko?”.
Kai ta girgiza tare da yin murmushi kana tace.
“A'a yau zamu koma ”.
Ware ido Asma'u tayi tare da faɗin.
“A'a yau zaku koma kuma?”.
Sai kuma Asma'u ta juya ta kalli Dije kana tace.
“Shaf-shaf haka?”.
Ita dai Khausar na gefe ta jingina bayanta da jikin gado Idanunta alumshe tana tunanin maganar Hajja Nana.
Kai Dije ta gyaɗa tare da faɗin.
“Eh ai da Yaya Aliyu muka zo”.
Murmushi Asma'u tayi kana tace.
“Ayyah ai kam munji daɗin ganinki”.
Asma'u kuwa juyawa tayi tare da kallon Khausar wacce ta tsirawa waje ɗaya Idanu cike da kulawa Asma'u ta dafa kafaɗar ta kana tace.
“Wai Meye ne kike ta haɗa rai!?”.
Iska mai zafi ta furzar tare da kallon Asma'u fuskarta babu walwala ta saki Ajiyar zuciya kana tace.
“Kina ji wata magana da wannan tsohuwar tazo dashi wai batun Aurena!kuji min tsohuwar nan da wani iyayi ta bari Iyayena suyi magana akai na mana ita kuma kaka wake maganarta!?”.
Asma'u kuwa Dariya mai sauti tayi tare da cewa.
“Iyeeee kice zamu sha bidiri!”.
Dije tayi murmushi kana tace.
“Barta dai kuma ma kinga mijin data samun ne kyakkyawa fa?”.
Baki Khausar ta kuma taɓewa tare da wurga musu Harara kana tace.
“Toni ina ruwana dashi?,
Ni bana so kada ma ayimin wannan maganar tsakani da Allah shi yafara Auren yayata fa Asma'u”.
Da sauri Asma'u ta ɗago kanta tare da cewa.
“Addarki kuma?, Dama ba kece ƴar farin Mommy ba?”.
Jinjina mata kai Dije tayi tare da cewa.
“Eh ba ita bace ƴar fari Akwai Addarta Nenne Amma ta rasu kuma itama Yayanta Aliyu aka aura mata sunyi aure da shekara biyu ta samu ciki tazo wajen haihuwa ta rasu!”.
Asma'u ta jinjina kai tare da cewa.
“Allah sarki Allah ya gafarta mata,.
Ohh Ashe shiyasa Mommy bata kunyar kiran sunanki nida duk atunanina kece ƴar fari har nace Mommy ƴar zamani ce bata ɓoye sunan ki”.
Kai Khausar ta girgiza kana tace.
“A'a ba nice ƴar fari ba ni ta biyu ce”.
Murmushi Asma'u tayi tare da faɗin.
“Ohhh lalle kam kice zamu sha biki”.
Khausar kuwa fuska ta tsuke kana tace.
“Zaku sha bikin waye?”.
Dariya Asma'u tayi tare da cewa.
“Bikin ki mana”.
Cikin haɗe rai Khausar kai ta girgiza tare da faɗin.
“Asma'u kiyi min fatan alkhairi mana, kina jin tsohuwar nan da shiririta da shirme wai ko bayan sallah za ayi ko menene oho?”.
Dije kam kai ta girgiza tare da cewa.
“Bafa cewa tayi bayan sallah ba ita dai alissafinta ki gama karatunki sai anyi idan yaso in kinaso kici gaba da karatunki sai Yaya Ali ya saki ki cigaba dayi a Adamawa bayan sallan baɗi take nufi”.
Fuska Khausar ta ya mutse kana tace.
“Aima Allah ya kiyaye abar mutum yayi karatunsa mai zurfi mana sannan ai mutum nada tsarin rayuwarsu da kuma yanda yake so ya kasance haka kawai sai atakura min”.
Dariya Asma'u tayi tare da cewa.
“Mu dai kar ki mana baƙin ciki ki hana mu shan biki”.
Harara Khausar ta maka mata kana tace.
“Ai sai kuyi shagalin ku kuka ɗai”.
Dije na dariya ta dubi Khausar kana tace.
“Yo ina zamuyi shagali ba Amarya ai dan ke za'ayi”.
Baki Khausar ta taɓe kana tace.
“Ai lalle dai kam”.
Mommy ce tashiga ɗakin bakinta ɗauke da sallama kallon Asma'u tayi kana tace.
“A'a Asma'u kece yaushe kika zo”.
Asma'u kuwa zamewa tayi daga kan gadon tare da cewa.
“Ban daɗe da zuwa ba Mommy Ina yini?”.
Mommy ta amsa da.
“Lafiya lau alhamdulillah yasu Umminki?”.
Miƙewa Asma'u tayi tare da zama agefen gadon kana tace.
“Tace agaisheki”.
Masha Allah Mommy ta faɗa tare da maida kallonta kan Dije kana tace.
“Dije kizo Hajja Nana na kiranki wai zaki rakata gidan Aminiyarta”.
Ta ida maganar tare da juyawa ta fice.
Miƙewa Dije tayi tare da kallon Khausar kana tace.
“Khausar mu tafi mana”.
Fuska Khausar taya mutse kana tace.
“A'a kuje kawai Allah ya kiyaye hanya ni bazan jeba, muyita faɗa da ita a gidan mutane muna raba hali agidan mutane duk inda mukaje sai ansan mu”.
Murmushi Dije tayi tare da faɗin.
“Toh shikenan mun tafi”.
Sannan ta fice kai tsaye ɗakin Mommy ta wuce sannan ta samu Hajja Nana atsaye.
Hajja Nana na kallonta tace.
“Wuce ki kira su Aliyu mu tafi”.
Kai Dije ta gyaɗa sannan ta fice.
Mommy kuwa Jakar data haɗa wa Hajja Nana tsaraba ta ɗauka sannan ta fice.
A coumpund ɗin ta samu Yaya Aliyu da Yaya Abba tsaye jikin mota cike da girmamawa da kuma ladabi Ya Aliyu ya kalli Mommy tare da cewa.
“Toh Mommy mun gode Allah ya saka da alkhairi Allah yabar zumunci”.
Murmushi Mommy tayi tare da cewa.
“Amin, Allah ya tsare muku hanya”.
Hajja Nana ta amsa da.
“Ameen”.
Tare da buɗe bayan motar tashiga Dije ta zauna agefenta Yaya Aliyu na gefen mai zaman banza Yah Abba kuwa shike Driving suka fice daga gidan.
Sai da Mommy taga fitar su sannan ta koma cikin gida.
Yaya Abba kuwa kai tsaye gidan su Moddibo ya nufa.
Hajja Nana nayi masa kwatance har suka isa gida suna shiga gidan.
Cikin sauri Yaya Ali ya lumshe Idanunsa kana yace.
“Masha Allah wlh Ina son garin Gembulan nan saboda yana da kyawun tsari dan yafi Adamawa kyawun tsari da komai akwai yanayin sanyi da daɗi”.
Jinjina kai Yaya Abba yayi yace.
“Aikam sosai ma”.
Yaya Ali ya juya tare da kallon Hajja Nana kana yace.
“Hajja Nana wannan kuma gidan wacece ɗinkin ne?”.
Murmushi Hajja Nana tayi alokacin da take sauƙa amotar ta kalli Ali kana tace.
“Ƙawata ce tare mukaje da ita aikin hajji na farko na biyu ma tare muka je sannan ko daga baya muna yawan zuwa Umarah tare da ita”.
Murmushi Yaya Ali yayi tare da cewa.
“Ai dai lalle kam kice gidan Aminiyar kice?”.
Dariya Hajja Nana tayi tare da cewa.
“A'a sosai ma kam”.
Dai-dai lokacin da suka isa ƙaramin gate ɗin da zai sadaka da farfajiyar tsakar gidan Innayi.
Innayi dake zaune ta hango Hajja Nana da baƙi abayanta,
Cike da fara'a ta miƙe da sauri fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi mai cike da jin daɗi ta matso kusa da Hajja Nana kana tace.
“Aaaa Lalle marhaba Hajjaju Makkatun Masha Allah Hajiya Nana mutanen Makka lale marhaba ku iso”.
Ta faɗa tare da juyawa ta shiga ɗaki tare da ɗaukan lallausan Chanis capet ta shimfiɗa musu.
Sai kuma ta fito cike da farin cikin daya kasa ɓoyuwa afuskarta kallon Yaya Ali tayi tare da cewa.
“Wannan shine Mijin namu na Adamawa da kike bamu labarin?”.
Kai Hajja Nana ta gyaɗa tana murmushi kana tace.
“Eh”.
Innayi ta juya ta kalli Hajja Nana kana tace.
“Ku shiga”.
Sannan ta kalli Yaya Abba da Yaya Ali kana tace.
“Ku ƙara so”.
Ta faɗa tare da ficewa Innayi ta nufi sashen Moddibo tare da cewa.
“Moddibo, Moddibo ga baƙi munyi”
Shi kuwa Moddibo atare suka miƙe da M Jameel suka fito.
Ɗan sake fuska Moddibo yayi kana yace.
“Sannunku da zuwa ku iso”.
ya faɗa tare da matsa musu.
M Jameel na ganin Yaya Abba ya miƙa masa hannu fuskarsa ɗauke da murmushi kana yace.
“Ha'a Abba kaine?”.
Murmushi Yaya Abba yayi kana yace.
“Ni ne dai”.
M Jameel yayi dariya kana yace.
“Sannu ku da zuwa”.
Yaya Abba na bin bayansu yace.
“Laaa Jameel nan gidan kune?”.
M Jameel yayi Murmushi tare da shafa sajensa ya kalli Yaya Abba tare da faɗin.
“Eh gidan mune!”
Murmushi Yaya Abba yayi da faɗin.
“Masha Allah”.
sannan suka shiga falon din wanda tuni Ya Ali da Moddibo suka shiga.
Innayi dake tsaye ta juya tare da cewa.
“Moddibo zoka kawo musu abin taɓa wa”.
Daga ciki Moddibo ya miƙe kana yace.
“Toh Innayi”.
Sannan ya fice tare da bin bayanta.
Juyawa Innayi tayi tare da kallon Moddibo dake biye da ita kana tace.
“Kashiga daga ciki ka gaida ƙawata Hajja Nana dana ke ce maka munje aikin Hajji na farko dana biyu kuma yawanci Umarah ma tare muke zuwa ɗakin mu ɗaya tun da take zuwa gidan nan bata taɓa samunkaba,
Kai ya gyaɗa da faɗin.
“Na'am”.Ya ida maganar tare da shiga ɗakin bakinsa ɗauke da sallama Idanunsa ya sauƙa akan tsohuwar da yaje ya yamata ta'aziyya a Jauro Yaya.
Cike da nutsuwa da kuma ladabi ya zauna daga gefenta kana yasa hannu ya shafa sajensa cikin yanayin rashin walwalarsa yayi ƙasa da kansa tare da cewa.
“Sannun da zuwa”,Ya gaisheta batare daya nuna ya ganeta ba.
Hajja Nana kuwa Kallonsa tayi kana tace.
“A'a kamar nasan wannan fuskarta fa, kwanaki kamar kunje da wani abokin Malam Liman mai suna Malam Arɗo ko?”.
Kai Moddibo ya jinjina still Kansa a ƙasa kana yace.
“Eh”.
Murmushi Hajja Nana tayi kana tace.
“Ayyah sannun ka ashe dai Jikana ne Allah yayiwa rayuwarka albarka Allah yabaka zuri'a ɗayyiban”.
Still Kansa A ƙasa ya shafa kwantaccen sumar kansa mai sheƙi da yalƙi kana yace.
“Ameen Ngd”.
Ya ida maganar a taƙaice tare da miƙewa ya fice.
Tiren da Innayi ta haɗa Gasassun Zabbi da M jameel yasa ta gasa musu, shinkafa da miyar dage-dage da yaji naman kaza sai Akwashi dake ɗauke da ƴaƴan itatuwa ta miƙawa Moddibo amsa yayi kana ya nufi sashen sa dashi.
Bakinsa ɗauke da Sallama yashiga tare da ajiye Tiren akan center table dake tsakiyar falon kana ya maida kallonsa kan M Jameel dake ta hiran Yaushe gamo da Yaya Abba kai ya girgiza tare da cewa.
“J miƙo musu ruwa acikin fridge ka barsu haka gashi har na dawo baka kawo musu komai ba”.
Murmushi M Jameel yayi kana yace.
“Wallahi muna ta hiran yaushe gamo da Abba nasan sa mun taɓa haɗuwa dashi a Adamawa”.
Jinjina kai Moddibo yayi tare da jingina bayansa da jikin kushin kana ya lumshe idanunsa tare da cewa.
“Ayyah ashe kunsan juna”.
Kai Yaya Abba ya gyaɗa alamar Eh.
Ya Ali kuwa hankalin sa ya mayar kan wayarsa yana latsawa.
Acan ɗakin Innayi kuwa zama Innayi tayu tare da kallon Hajja Nana kana tace.
“Yanzu ma kinzo wajen jikar tamu ce?”.
Kai Hajja