Header Ads
Showing 162001 words to 165000 words out of 188939 words

Chapter 55 - SAKAYYA Book 1 complete BY GARKUWA.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

amma kuɗin hannun mu munyi munyi sun kasa kai adadin da kuke buƙata mu samu su kai adadin da kuke buƙata wannan shine matsalar mu ku temaka ku ragar mana”.
Ajiyar zuciya mutumin ya sauƙe tare da cewa.
“Wannan Moddibo ne ke magana ko?”.
Kai Moddibo ya gyaɗa kana cikin sanyin murya yace.
“Eh”
Cike da gadara Mutumin yace.
“Toh shikenan ku bada Million ɗari da hamsin”.
Cikin raunin murya Moddibo yace.
“Mungode amma dan Allah ba zaku ƙara rage mana ba?”.
Cikin wata razananniyar tsawa Mutumin yace.
“Dan ubanka dan ka samu na zabge Million hamshin.
Atake to wallahi acikin Million ɗari da hamsin Naira biyar ba zamu rage ba kuma wallahi idan ku ka yarda kuka sake yi mana batun ragi kuɗi to wallahi akan ran Jameel domin kuɗi ne dai mu ki ya rayu ko ya mutu zamu samesu”.
Cikin tsanananin tsoro da kaɗuwa Moddibo ya dafe ƙirjinsa yayin da kansa ya sara da masifan ƙarfi.
Cikin tsawa Mutumin ya cigaba da cewa.
“Yanzu Moddibo gashi kayi magana dashi na ƙarshe wanda ko bacci yake yana kiran sunan ka gashi kayi magana dashi dan wataƙil shine maganarka na ƙarshe kenan dashi matukar dai baku haɗa kuɗin nan ba ku kasake yi mana batun ragin kuɗin to kayi magana dashi na ƙarshe kenan”.
ya faɗa tare da wurgawa M Jameel wayar.


Cikin sauri M Jameel ya cafke wayar tare da maƙalawa akunnensa kana cikin raunin murya yace.
“A.J”.
Cikin sauri da zaƙuwa Moddibo yace.
“J ina kake?”.
Girgiza kai M Jameel Yayi tare da cewa.
“A.J ban san inda nake ba ina Ummina!?”.
Runtse Idanu Moddibo yayi tare da taune lips ɗinsa kana yace.
“Tana lafiya J?”.
Cikin sanyin Murya M Jameel yace.
“J ka tabbata?”.
Cikin raunatacciyar murya yace.
“Na'am”.
jin haka yasa yaci gaba da cewa.
“Kace mata kada tayi kuka tayi ta min. Addu'a A.J ina sonka Ina son Ummina Ina son Abbana Ina Son Asma'u Ina son Bashir”.
Da sauri Moddibo ya dafe ƙirjinsa dake harbawa da masifan ƙarfi cikin raunin murya M Jameel ya cigaba da cewa.
“A.J Ina son Khausar tashigo rayuwar mu”.
Cikin tsanananin rauni Moddibo yace.
“Na sani J nasan kana son mu muma muna sonka, kuma in sha Allah duk zamu kasance a tare, zata shiga rayuwarka J zan mutunta abinda kakeso J”.


Girgiza kai M Jameel Yayi still cikin raunin murya yace.
“Ngd A.J in kayi haka kayi min komai, kayiwa Ummina magana idan akwai wani abu a hannunta ta bayar ahaɗa azo a karɓeni awajen nan dan Allah katemaka min”.
Araunane Moddibo yace.
“Insha Allah J zan taimaka da duk kan iyawa ta da kuma duk kan damata J koda ace da raina ne zan fanshi ranka da rayuwarka Insha Allah zamu fito da kai”.
Jinjina kai M Jameel yayi tare da faɗin.
“Nagode Nagode A.J ina maka fatan al'khairi acikin rayuwarka ga Amanar Ummina, Asma'u, Bashir,Abba da.... ka kula dasu kafin in dawo sannan kada ka mance batun Kh”...
Fisge wayar akayi daga kunnensa tare da katsewa.


Dafe kai Moddibo yayi cikin wani irin azabebben rauni ya fashe da matsanancin kuka tare da miƙewa batare da yace komai da Abba ba ya fice yana fita ya shiga motarsa tare dayi mata key.
Kana ya ciro wayarsa tare da dearling number Ummi tana ɗagawa murya a raunace yace.
“Ummi”.
Cikin sanyin murya tace.
“Na'am”.
Cikin ƙoƙarin hana kansa kuka yace.
“Ummi munyi waya da J yanzu”.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe kana tace.
“Dagaske Babana?”.
Kai ya gyaɗa kamar tana gabansa.
Cike da tsoro Ummi tace.
“Babana to Meyesa kake kuka?”.


Fashewa yayi da kuka kana cikin sheshsheƙa yace.
“Ummi ina kukan rashin J akusa dani ne Ummi wanda suka sai motarki Alhj Abdallah kice ya tura Azo aɗauki motocina da na J duka azo asiya ahaɗa kudin duka”.
Numfashi Ummi ta fesar tare da rintse idanunta kana tace.
“Sunƙi ragewa ko?”.
Girgiza kai yayi tare da cewa.
“A'a Ummi sun rage mana Million hamsin akai yanzu ya zama Million ɗari da hamsin suke buƙata”.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da cewa.
“Toh Alhamdulillah wataƙila zamu iya cin nasara".
Cike da rauni Moddibo yace.
“Insha Allah Ummi da izinin Ubangiji”.
Ya faɗa tare da katse kiran jin wani kuka na neman kufce masa.


Kai tsaye hanyar gida ya nufa ba abinda ke yawo acikin kunnensa face sautin Muryar J ɗinsa yana isa gida yayi Parking tare da rufe musu gate.
Kai tsaye sashen Innayi ya nufa yana isa ya zauna abakin baranda tare da riƙe kansa da hannu duka biyu,
Kana ya fashe da wani irin kuka mai masifar ciwo a zuciya.
Wani irin azaban zogi yaji zuciyarsa na masa hadi da zafi da raɗaɗi yayin da wani masifaffen rauni ya lulluɓesa.
Innayi da bacci ya fara fisgarta ne, ta miƙe da sauri jin kamar sheshsheƙan Kukan Moddibo kana ta fito tare da Kallonsa yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ya ɗauki rawa cikin sanyin murya tace.
“Ya dai Moddibo lafiya kuwa mai ya faru da Jameelu?”.
Cikin matsanancin kuka yace.
“Innayi ya zamuyi taya zanyi in.
Samu in taimaki J duk kan tattalina ya ƙare babu abinda zan samu in saida cikin gaggawa.
Zan saida tsohuwar motar da kika siya min da wannan sabuwar da kuma na J duka za'a siyar sannan Innayi nasan koda an siyar dasu duka, kuɗin ba zasu ciki Million ɗari ba”.
Sai kuma ya kife kansa bisa guiwowinsa ya sake fashewa da sabon kuka kana yace.
“Innayi sunce idan muka sake neman ragi akan kuɗin kamar mun nemi akashe J ne”,.
Jingina kansa yayi jikin fillan dake gefenta tare da fashewa da matsanancin kuka hadda sheshsheƙa.


Cikin Sanyin jiki Innayi ta zauna kusa dashi batare da tace yayi shiri ko kuma ya daina kukan ba, domin ta tabbata duk abinda yasa Moddibo kuka ba ƙaramin abu bane, kana idan har bai yiwa wannan abin kuka ba to mai zai yiwa kuka arayuwarsa.
Moddibo kuwa kuka ya cigaba da yi tamkar ransa zai fita har shidewa yake.
A ƙalla ya ɗauki Mintuna masu tsawo yana kuka kafin ahankali ya ɗago kansa tare da kallon Innayi kana yace.
“Innayi”.
Cikin sanyin murya tace.
“Na'am Moddibo”.


Cikin Muryansa daya dishe da kuka yace.
“Innayi ta wace hanya ce wace damace wane daliline kike samu kike mana duk kan buƙatun rayuwarmu?
Innayi in dai har adana kuɗi kikayi in dai har basu ƙare ba Innayi ki fito mana dasu ki taimakeni aceci J dashi”.
Jinjina kai tayi kana tace.
“Moddibo gaba ɗaya tattalin da mukayi na zaman rayuwar mu awannan yanki awannan gari a wannan ƙasar anje matakin da gaba ɗaya tattalin namu yazo ƙarshe sabida lokacin komawa muhalli ya kusan cimmmana”.
Sai kuma ta kalli Moddibo da har zuwa lokacin hawaye ke bin Fuskarsa kana tace.
“Na tanadi komai ne domin sanin cewa muna da bukatar su kama daga karuntaka, ci, sha, Jinya, sutura.
Da dai sauransu to yanzu kuma lokaci ya tafi rayuwa ta juya abubuwa sun tafi baki ɗaya tattalin namu yayi ƙasa tsadan rayuwa ya cinye kaso mafi tsoka”.
Numfashi Moddibo ya fesar kana yace.
“Innayi koma wani irin tattaline shin babu ragowa ne ko kaɗan ne?”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Akwai ragowa”.
Cikin kuka yace.
“Menene amfanin ragowan duk tattalin arzikin da kike dashi matukar dai ba zai fito atemaki J ɗina da shiba Jamelunki fa ya fito daga inda yake fa”.
Ya ƙare mgnar cikin ƙunan rai, domin gani yake kamar ma duk duniya ba'a damu da J ɗinsa ba.
Ita kuwa Innayi cikin tafiya wani sashi nazarin Jinjina kai tayi tare da cewa.
“Bashi da amfani Indai bazan fito dashi ba, amma bari na fito dashi amma yanzu ka fara yin shiru tukunna kana kayi min al'ƙawarin cewa bazaka tambayeni komaiba akan duk abinda zaka gani”.
Kai ya gyaɗa mata kana yace.
“Innayi muga abinda zan fara samu awajenki tu kunna zanfi jin sanyi, ni yanzu a duniya babu tambayar da ke bakina daya wuce ina J yake , wanne hali yake ciki”.
Sai kuma ya fesar da zazzafan numfashi tare da cewa.
“Wallahi Allah ji nakeyi tamkar naje na zauna abakin masallacai inyita bara asamu ahaɗa kudi in cikata in karɓo J Innayi ya zanyi”.
Cike da rauni Innayi tace.
“Ba zakayi bara ba Moddibo Bari muga abinda Allah zai mana”.
Kai ta gyaɗa tare da jan hannunsa suka nufi bayan ɗakinta inda randunan ƙasa ke ajiye.
Kallon Moddibo da har zuwa lokacin hawaye ke zuba a idanunsa tayi kana tace ɗaga min randan nan”.
Sauri kallonta yayi kana ya Kalli randan ƙasan tare da cewa.
“In ɗaga miki randa kuma?”.
Ba tare data kallesa ba tace.
“Kada kayi min musu idan na baka Umarni kabi”.
Kai ya gyaɗa cikin sanyin yace.
“Toh”.
Tare da ɗaga randan ya matsar gefe.
Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.
“Toh ɗaga fantekar”.
Kai ya ɗaga tare da matsar da fantekar dake cike da ƙasa gefe.
Yana janye fantekar yaga ƙasan wajen alailaye.
Ahankali Innayi ta zauna agaban wajen Moddibo kuwa cikin sanyi jiki ya durƙusa agefenta.
Itako Innayi hannunta ta sanya ta fara tono ƙasan dake wajen ganin duhu agarin yasa Moddibo sanya hannunsa acikin aljihu ya ciro wayarsa tare da kunna tochligt ya haska mata inda take tonawan.
Innayi kuwa ahankali ta cigaba da tono ƙasan bayan ta gama kwashe ƙasan ya rage sauran wasu manyan duwatsu ahankali ta ciresu duka.
Cike da mmki Moddibo ya tsaida idanunsa akan fafakekken rami an lailayeshi da siminti yana rufe da murfin tukunya kamar na lamba uku, da ɗan ƙarfi ta ɗago Murfin tukunya.
Cikin sauri Moddibo yayi saurin rintse idanunsa da karfu sakamakon wani haskene mai masifar sheƙi daya ɗauke masa idanu daya kashe masa idanu,
A hankali ya kuma saƙe buɗe inadunsa, da sauri ya mitso ganin yadda cikin ramin ke sheƙi da ƙelƙeli mai ɗauke ido yake fitowa daga cikin ramin, acan ƙasan ramin kuwa cike yake da ƴan ƙananan sulallan gwala-gwalai wanda basu fiye yawa ba sosai hasken ya ɗauke masa idanu saboda hasken wayarsa daya haske cike da tsanananin mamakin ya sunkuyo tare haska cikin ramin da kyau kana ya sanya tafin hannunsa acikin ramin ya ɗebo guda huɗu tabbas sulallan Gwalne...!




Littafin SAKAYYAH na kuɗine ko kin ganshi a wani wurin na satane. Ki biya ki karanta cikin Aminci 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA.




By
*GARKUWAR MARUBUTA*
*Littafin SAKAYYAH dai na kuɗi ne ba free book bane 1k ne kacal ki biya ki karanta cikin Aminci kada ki karanta na sata na Allah ya isa. 0661110179 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276 sai in saki a Group ɗina*




Cappande. Acikin tafin hannunsa ya ɗebo sulallan Gwal ɗin da wasu yan guntu-guntun sanduna tare da birbiɗin yashin kana ya shiga jujjuyasu, ahankali ya maida kallonsa kan Innayi data gyaɗa masa kai alamar ya fito dasu hannunsa ya zura acikin tukunyar yashiga kalato salullan wanda na ainihin Gwalne aƙalla sun kai guda ashirin, karkaɗe yashin yayi tare da fitowa dasu kana ya ɗaura su akan rigarsa tare da gyara zaman sa abakin ramin ya tsura mata Ido Innayi ma ido ta zuba masa ganin yanda ya zauna yasa tashiga maida yashin ta rufe ramin kana ta sanya duwatsun ta rufe tare da tura fantekar kan ramin kallon Moddibo dake binta da kallo tayi kana tace.
“Ɗaura min randan nan akai”.
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe still Idanunsa na Kanta cikin sanyin murya yace.
“Innayi wannan kamar Gwal?”.
Kai ta gyaɗa masa kana tace.
“Eh Gwal ne”
Still ba tare daya motsa ba ya sake kallon Gwal ɗin kana yace.
“Ina kika same su Innayi?”.
Girgiza masa kai tayi kana tace.
“Wannan ba lokacin tambayar ina nasamu gwala-gwalai bane. Moddibo lokacine daya kamata ace ka lissafa su muga adadin su kana musan nawa za'a samu mu haɗa mu karɓo Jameelu yanzu tashi mubar wajen nan mushiga ɗaki kaga dare ya tsala”.


Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.
“Toh”,Kana yabi bayanta tare da tsira mata idanu cike da ɗumbin mamaki tare da tarin tuhuma ahankali ya sake kallon sulallan Gwal ɗin dake haɗe da waɗanan sanduna guntaye aciki asaman laɓɓansa yayi sallama tare da shiga ɗaki.
Wutan ɗakin Innayi ta kunna Atake haske ya zagaye ɗakin bayan Moddibo ta ratsa tare da rufe kofar ɗakin kana ta dawo kusa dashi ta tsaya tare da sanya hannunta ta tsistsince ƴan guntulayen sandar ta shiga haɗawa kasancewar akwai wajen haɗawa ajiki Moddibo kuwa Idanu ya zuba mata cike da mamaki.
tana cigaba da haɗawa ga mamakinsa sai yaga ya zama sanda irin wanda manyan Limamai ke riƙe wa suna tafiya dashi sanda ce mai masifar kyau da tsari wacce da ka gani kasan mai tsadace.


Kallonsa Innayi tayi tare da cewa.
“Wannan sanda ce samansa inda ake riƙewa ne kaɗai keda Gwal sai kuma ƙasan sa inda ake dogara wa amma wannan bazan baka shiba saboda ba zaiyi daraja sosai ba. Saboda ahaɗe yake da sanda kana sandar kuma bazan siyar ba, sulallan dai zaka haɗa ka duba sai dai sunzo mana alokacin da bashine ba saboda sulallan baki ɗaya sun ƙare”.
Ido kawai Moddibo ya zuba mata still da shock atare dashi.
Innayi ta cigaba da cewa.
“Baki ɗaya nauyin karatunka.
Cin mu, shan mu, suturar mu, tun kana ƙarami da duk wani abinda ya kama su nake ɗauka in siyarwa Alhaji Hashim mai sayan gwala-gwalai shiyasan farashin sulallan duk yanda suke zan faɗa masa adadin da suke yazo ya siya muyi lissafi muga nawa za'a samu”.
Kai Moddibo ya gyaɗa tare da cewa.
“Toh shikenan”.Yayi mgnar tare da lumshe idanunsa, baki ɗaya damuwarsa asamu kuɗin bawai tunaninsa ya tambayi ina tasamu gwala-gwalan nan ba sannan bashida kuzarin da zai iya tambayar ta, sandar na menene, kana bashi da ƙarfin zuciyar jin mai yasa baza asayar da sandar ba, ayanzu burinsa bai wuce asamu ahaɗa kuɗaɗen akarɓo J ba.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da kallon Innayi kana yace.
“Toh zan tafi dasu ɗakina”.
Kai ta gyaɗa masa kana ya miƙe ya fita yana jin confidence da farin ciki yasan Gwal nada daraja duk da cewa ƴan ƙananun sulallane amma yasan da izinin Ubangiji zasuyi daraja.


Acan gidan Abba kuwa bayan tafiyar Moddibo Hajiya Karima ta kalli Abba daya zurfafa acikin tunani kana ta ɗan ya mutse Fuska tace.
“Alhji wai yanzu baza ka sake ƙara neman ragi ba? yanzu sai ka ɗauki Million ɗari da hamsin ka basu mai kake tunanin zai faru gaba idan sunji daɗi za'a sake ɗaukan ƴaƴanka ne fa!”.
Anutse Abba ya ɗago kansa tare da kallonta kana cikin sanyin Murya yace.
“Karima to me kike tunani?”.
Ba yabo ba fallasa tace.
“Ka nemi ragi”.
furzar da iska mai zafi yayi still Idanunsa na kanta kana yace.
“Karima kamar baki ji me yace ba, cewa fa yayi muddin aka nemi ragi akan rayuwar Jameel”.


Cikin sauri tace.
“Bafa za'a kashe Jameel ba, kawai Alhj idan zaka nemi ragi ka nemi ragi, sai kace baka sha zafin neman kuɗin ba zaka ɗauka agabtale ka basu kamar ba kasan darajar suba, amma babu yanda zaka ɗauki wannan maƙudan kuɗin ka bayar akan Jameelu!”.


Cike da mamaki Abba ya kalleta kana cikin ɗaga sautin murya yace.
“Karima to idan ban bada kuɗi akan Jameelu ba akan wa kike so in bayar? Shin Karima anya Karima?”.
Wani irin kallo ta masa kana cikin sauri tace.
“Anya me?”.
Dai-dai lokacin Hajiya Turai ta shigo baki ɗaya ta hargitse babu walwala afuskarta ta kalli Hajiya Karima kana tace.
“Ai dai kam abin nata da mamaki, idan bai ɗauki kuɗi ya bayar akan Jameelu ba akan wa kike so ya bayar?”.
Sai kuma ta maida kallonta kan Abba da idanunsa ke lumshe kana tace.
“Aini Alhj naga ƙoƙarin ku ma da har kuka iya neman ragin da suka rage muku, kuma ai sunyi ƙoƙari ni dai anawa tunanin kada ku kuskura kada ku sake yin batun ragin wasu kuɗin, suje su kashe mana yaro abanza idan aka kashesa mai son sa keda asara wanda bai sonsa kuma bai damu ba”.
Ta ida maganar hawaye na ciko kwarmin Idanunta.

Hajiya Karima kuwa wani kallo ta watsa wa Hajiya Turai tare da cewa.
“To mekike nufi?”.
Taɓe baki Hajiya Turai tayi kana tace.
“To ai gaskiya ne duk mai son Jameelu ba zai so ace za'a sake neman ragi ba”.
Taɓe baki Hajiya Karima tayi tare da watsa mata kallon banza kana tace.
“Kenan kina nufin Ni bana son Jameelu?”.
Hannu Hajiya Turai ta buɗe kana tace.
“A'a wannan ke ki kafaɗa da bakin ki amma dai shawaran da kika kawo ba shawara me kyau bace”.
Hannu Abba ya ɗaga musu tare da kallon Hajiya Karima dake kumfar baki kana yace.
“Bana son hayaniya ya isheku.
Dan Allah kubarni inji da abinda ke damuna”.
Kai Hajiya Turai ta gyaɗa tare da tsuke bakinta alamun itama ba hayaniyar take soba.
Cikin sanyi ta kalli Abba tare da cewa.
“Alhj ga Million biyu a Account ɗina zan bayar ahaɗa”.
Wani shegen kallo Hajiya Karima tabi Hajiya Turai dashi kana cikin taɓe baki tace.
“Hmmm munafurci dai da neman gindin zama haddasu kaza acikin cin danƙo”.
Cikin sanyi Abba yace.
“Nagode Turai Allah ya saka da alkhairi ayanzu kyauta koda na Naira biyar aka bani ita ina buƙatar ta, xansa acikin tumunin kudin da za'a karɓo Jameel”.
Cikin sauri Hajiya Karima tace.
“Nima Allah ya bani in bayar”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Ameen”.
Juyawa tayi ta fice Hajiya Turai kuma ta zauna gefensa tana sake tausansa.


Acikin kwanaki biyu Moddibo ya saida gwala-gwalan da kuma motocinsa dana M Jameel Yayi total ɗin kuɗin sun kama Million ashirin da biyar ya turawa Abba cikin account ɗin sa Alhamdulillah yanzu akwai Million casa'in da biyar acikin account ɗin Abba Aɓangaren Abban ma yana cigaba da fafutuka ganin ya samu kuɗi.
Acikin kwanakin baki ɗaya abubuwa sun kankama baki ɗaya sun sake maida hankalinsu kan neman kuɗin suga sun samu sun haɗa yau ya kama kwanan M Jameel goma kenan awajen Kidnappers din kana yau kwana biyu rabon Abba da Moddibo suyi waya da M Jameel Misalin huɗu na yamma Moddibo ya bar gidan Abba ya nufi gidansu bayan sun sake tattauna wa.


Acan ɓangaren Boka Kar'uzu kuwa Hajiya Bunayya da Hajiya Lami ce gurfane agabansa cikin wata sandararriyar murya Boka Kar'uzu ya kece da wata mahaukaciyar dariya tare da jujjuya gashin dake wangamemen tafi hannunsa kana ya ɗago kansa tare da Kallon Hajiya Bunayya da jajayen Idanunsa da suka tara kwantsa yace.
“Kin tabbatar gashin yaron ne dai ko?”.
Cike da ƙwarin gwiwa Hajiya Bunayya ta jinjina masa kai tare da faɗin.
“Tabbas na tabbatar Boka Kar'uzu Uban bokaye La'anannen Uban La'anannu Mugu Uban mugaye tsinanne Uban tsinannun wannan gashin kan Ramadan ne domin dana shafa turare na shafa kansa bayan na fita naga gashi ya manne ahannu shine na tattare na kawo maka kamar yadda ka

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads