Showing 63001 words to 66000 words out of 188939 words
Chapter 22 - SAKAYYA Book 1 complete BY GARKUWA.txt
tsaye sashen Hajiya Bunayya ta nufa bakinta ɗauke da sallama tana faɗin.
“Ummah”.
Shigar ta yayi dai-dai da lokacin da Hajiya Bunayya ke riƙe da waya tana cewa.
“Kedai Hajiya Lami bari buƙata ɗaya ta biya saura ɗaya, tana can kwance a asibiti cikin ya zube yabi makwarari, saura ɗayan daman jira nake inga ya zata kaya ne ki shirya jibi zamu koma”.
Komai Hajiya Lami ta faɗa ohon musu, ita dai Hajiya Bunayya cikin jin dadi ta kece da wata mahaukaciyar dariya mai nuni da tsantsar farin ciki.
Lokaci ɗaya kuma dariyar nata ya tsaya ganin Khausar tsaye, sai kuma ta katse kiran tare da kallon Khausar.
Kafin tace wani abu Khausar tayi saurin cewa.
“Ummah ina Mommy mu?”.
Hajiya Bunayya ta wani langwaɓar da kai kana tace.
“Ayyah Khausar am Mommy ku tana asibiti bata da lafiya wallahi cikinta ya zube”.
Da sauri Khausar da kanta ke ƙasa ta ɗago ta kalli Hajiya Bunayya tana sake maimaita kalmar cikinta ya zube akasan ranta lokacin ɗaya hawaye masu zafin gaske suka cika kwarmin Idanunta.
Sai kuma tayi saurin maida hawayen ta kafin tace.
“Shikenan ɓuƙatar magauta tabiya hankali ya kwanta. Allah ya raya mata wa anda ta haifa. Ubangiji ya tsaresu daga sharrin mai sharrin”.
Ta ida maganar tana ƙoƙarin fita.
Da sauri Hajiya Bunayya tace.
“Ke Khausar zo nan Me kike nufi?”.
Anutse Khausar ta juya tare da sauƙe manyan Idanunta da suka sauya launi zuwa ja ta zubawa Hajiya Bunayya kana tace.
“A'a Ummah babu abinda nake nufi, kawai dai addu'a ce nayi”.
Cikin tsuke fuska Hajiya Bunayya ta watsa mata Harara da faɗin.
“Sannan su waye ne Magautan?”.
Ware hannu Khausar tayi tare da faɗin.
“Nikam ban sansu ba, amma dai nasan Allah Mabuwayi gagara Misali ya sansu kuma zaiyi maganin su, domin ai bahaushe yace rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya, suji tsoron ranan da Ubangiji zai musu kamun talala!”.
Cike da Mamaki Hajiya Bunayya tace.
“Wai Khausar me kike magana kamar habaici kike min ko kuma hannunka mai sanda!?.”
Ware ido Khausar tayi tace.
“Haba Ummah in Miki habaici kuma ayanda kike ƙaunar Mommyn mu kinfi ƙarfin habaici ko hannunka mai sanda kin wuce haka sai dai mgnar ce tazo kamar zaurance”.
Ɓoyeyyen Ajiyar zuciya Hajiya Bunayya ta saki domin tayi zaton yarinyar ta gano lagonta ne.
Khausar kuwa murmushi tayi tare da faɗin.
“Bari na tafi asibitin kar dare yayi”.
Da sauri Hajiya Bunayya ta gyara zamanta Idanunta akan Khausar tace.
“Toh kibari in ƙara sa abinci mana sai ki tafi dashi”.
Kai Khausar ta gyaɗa da faɗin.
“Toh amma bari na shiga gidan Aunty Ruƙayya kafin ki ƙarasa”.
Kai Hajia Bunayya ta gyaɗa tare da faɗin.
“Toh ki gaisheta”.
Kai kawai Khausar ta gyaɗa Sannan ta wuce sashen su.
Tana shiga Bedroom direct toilet ta wuce ta cire Uniform ɗin ta sannan ta watsa ruwa bayan ta fito ta dauki dogon rigar material pinch colour ta sanya, kana ta nufi kichen Agurguje ta dafawa su Haiydar jollof ɗin shin kafa da yaji bushesh-shen kifi da kayan ƙamshi nan da nan kichen ɗin ya ɗauki ƙamshi Warmers ta ɗauka ta juye sannan ta tafasa musu tea kana ta ɗura musushi, sannan ta fita falon dai-dai lokacin da Haiydar ya shigo.
Kallonsa Khausar tayi tare da kiran sunansa tace.
“Haiydar”.
Ya amsa da.
“Na'am”.
Cikin sanyi tayi ƙasa da muryanta tare da faɗin.
“Dan Allah Haiydar ka kwana anan kai da Ramadan, Raudat kuma zamu tafi da ita asibiti sai mu kwana da Mommy”.
Kai ya gyaɗa mata sai kuma yace.
“Nima ai inaso naje na dubata”.
Jinjina kai Khausar tayi tace.
“Ba damuwa kazo mutafi dukan mu amma yanzu zan fara shiga gidan Aunty Ruƙayya in sanar mata, idan yaso kai da Ramadan ku taho tare da Ummah,
In yaso sai ku dawo tare amma kubar min Raudat dan zamu kwana tare”.
“Toh shikenan Allah ya bata lafiya”.
“Ameen”,
Tace kana ta juya ta tafi har ta kusa fita ta sake juyawa ta kalli Haiydar dake tsaye Ahankali tace.
“Dan Allah Haiydar ka kula, bakomai za'a baka kaci ba, akwai abinci na dafa muku sannan duk wani abu da zaku buƙata akwai”.
Da sauri ya dafe kansa tare da faɗin.
“Ke dai jeki da rashin yardan ki kedai haka Allah ya halicce ki baki da yarda”.
Cikin sanyi ta girgiza kai kana tace.
“Shikenan ni dai ban san sai yaushe zaku yarda dani ba”.
Ta ida maganar tare da ficewa”.
Kai tsaye gidan Aunty Ruƙayya ta nufa.
Tare da Sallama tashiga Babban falon da yaji kayan alfarma kujerun set biyu aciki Black and Ash sai kuma babban tv plasma dake Manne abango daga ƙasansa kuma horm teater ne ƙasan falon kuma shimfiɗe yake da chanis capet.
Aunty Ruƙayya dake bedroom ta fito fuskarta ɗauke da murmushi tace.
“Khausar kece sannu da zuwa, shigo ciki”.
Da sauri tace.
“A'a Aunty sauri nakeyi ai”.
Cikin kulawa tace.
“Yo yasu Mommy ki?”.
Murmushi Khausar tayi tace.
“Wallahi Aunty Ruƙayya Mommy ce ke asibiti bata da lafiya, shine nace bari nazo na faɗa miki, Ni yanzu ma zan wuce ko za muje tare?”.
Cike da tausayawa Aunty Ruƙayya tace.
“Ayyah Allah ya bata lafiya zanje bari ina zuwa mu tafi tare”.
Kai Khausar ta gyaɗa da faɗin.
“Toh”.
Aunty Ruƙayya kuwa bedroom ta shiga tare kiran mijinta a waya, bayan ya bata izinine, ta ɗauko key mota da mayafinta suka fita,
suka shiga mota,
jingina kai Khausar tayi da jikin motar kalaman Hajiya Bunayya nayi mata suwwa akunne.
Juyawa Aunty Ruƙayya tayi ganin yanda Khausar ta zurfafa cikin tunani yasa tace.
“Ki riƙa yi mata addu'a”.
Kai kawai Khausar ta iya gyaɗa mata.
Cikin Mintuna kaɗan suka isa Asibitin bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga ɗakin da aka kwantar da Mommy saboda Hajiya Bunayya ta faɗa mata.
Kwance akan gado suka tarar da ita yayin da Lamiɗo ke gefenta akan kujera hannunsa riƙe da kofin tea yana miƙa mata da faɗin.
“Ki tashi kisha”.
Yana jin Sallamar Khausar ya juya yana kallonta har ta isa kusa dashi.
Cike da kulawa yace.
“Khausar har kun dawo?”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Eh Abba ya jikin Mommy!?”.
Sai da ya ɗan kalli Mommy dake jingine da pillow sai kuma ya mayar da Kallonsa kan Khausar yace.
“Da sauƙi”.
Sai asannan ya lura da Hajiya Rukayya ya ɗan yi murmushi da faɗin.
“Hajiya Ruƙayya sannu da zuwa”.
Zama tayi akujeran dake kusa da ita tana cewa.
“Yawwa ya Hajiya Aysha da jikin kuma?”.
Ɗan Murmushi yayi kana yace.
“Da sauƙi”.
Tana kallon Mommy tace.
“Ubangiji Allah ya ƙara sauki”.
Ya amsa da.
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.
Khausar kuwa bakin gadon ta ƙarasa ta riƙe hannun Mommy acikin nata.
Cikin raunin murya tare da tausayawa mahaifiyar tata tace.
“Sannu Mommy ya Jikin?”.
Lumshe idanu Mommy tayi kana ta buɗe su a hankali tace.
“Da sauƙi Khausar bana jin komai in dan ta nice ma, da su sallame ni in koma gida mu kwana tare, dan bana jin ciwon cikin yayi sauƙi babu inda yake min ciwo!”.
Ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe tare da faɗin.
“Masha Allah Mommy Allah yaƙara sauƙi Ubangiji ya ƙara tsarewa ya kare”.
A ranta kuwa cewa tace.
Ayyah da ace duk addu'o'in da takeyiwa Mommynta tun randa taci ferfesun da ace tana haɗa addu'ar da yaron cikin wata ƙil da bai zube ba.
Shafa kanta Mommy tayi cike da ƙaunar ta tace.
“Ameen Khausar ki kwantar da hankalin ki ba najin Komai”.
Ta faɗi hakan ganin yanda Khausar tayi zuru-zuru da ita.
Hajiya Ruƙayyance ta kalli Mommy kana tace.
“Hajiya Aysha ya ƙarfin jikin!?”
Murmushi Mommy tayi kana tace.
“Dasauƙi Hajiya Ruƙayya ya ‘Yar taki ya kuma rigima a makaranta!?".
Kallon Khausar Hajiya Ruƙayya tayi kana tace.
“A'a yanzu ai ta daina ta fara girma!”.
Jin haka yasa Khausar tayi murmushi.
Lamiɗo kuwa miƙewa yayi idanunsa akan Mommy yace.
“Toh shikenan bari na tafi dama ganin babu kowa ne yasa nake zaune bari na samu naje nayi wanka dan tunda muka zo ban samu na koma gida ba”.
Hajiya Ruƙayya tace.
“Ayyah ai babu komai Alhaji kaje”.
Jinjina kai Mommy tayi tace.
“Allah ya tsare”.
Ya Amsa da.
“Ameen”sannan ya juya ya fice.
Tafiyar Lamiɗo babu daɗewa Hajiya Bunayya da Hajiya Lami suka zo Raudat na riƙe da hannunta.
Suna shiga Hajiya Bunayya ta zauna daga gefen gadon tare da kallon Mommy tace.
“Sannu ƙanwata ya ƙarfin jikin?”.
Murmushi Mommy tayi kana tace.
“Ai naji sauki Yaya”.
Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi cikin yanayin tausayawa tace.
“Allah ya baki lafiya”.
Hajiya Ruƙayya kuwa kallo ɗaya tayi wa Hajiya Bunayya da Hajiya Lami taji sam basu kwanta mata arai ba musanman ma Hajiya Bunayya dake wani shish-shugewa Mommy.
Ta dai daure tace.
“Sannunku da zuwa”.
Hajiya Bunayya da Hajiya Lami suka haɗa baki wajen cewa.
“Yawwa ya mai jikin”.
Ataƙaice Hajiya Ruƙayya tace.
“Da sauƙi”.
Hajiya Lami kuwa jikin gadon ta matasa Idanunta akan Mommy tace.
“Ayyah Sannu Hajiya Aysha Ashe ga abinda ya faru kuma? Amma wannan abu yayi yawa ai gwara Alhj yayi ƙoƙari ya fitar dake waje wannan matsalar ko yaushe da ansamu ciki ya zube ai babu daɗi!”.
Kafin Mommy tayi magana Hajiya Bunayya tayi saurin cewa.
“Kede bari Hajiya Lami abin nan yana damun mu, gaba ɗaya mun kasa gane menene ainihin matsalar, amma hankalinmu na tashi kullum cikin yanayin nan, abin babu daɗi yanzu ciki takwas kenan yana zubewa abin ai babu daɗi!”.
Taɓe baki Khausar da Hajiya Rukayya sukayi alokaci ɗaya.
Ahankali Mommy ta gyara matashin data kishingiɗa akai kana tace.
“Uyummm ya za'ayi da abinda Allah ya tsara, amma ni inaga nin ba wani matsala bane, tun da gashi na haihu bayan haihuwar Haiydar ma haka nata fama da ɓare-ɓaren nan, kuma daga baya da Allah ya kawo Ramadan da Raudat an haifesu ba komai ai”.
Cike da kirsa Hajiya Bunayya tayi yaƙe kana tace.
“Hakane kam, toh Allah ya kawo masu albarka”.
Hajiya Lami kuwa harara ta gallawa Mommy tare da taɓe baki aranta tace shegiya me iyayin jaraba keda haihuwa sai dai kiga anayi.
Idanun Hajiya Ruƙayya da Khausar na kan Hajiya Lami alokacin data taɓe baki ta harari Mommy,
Juyawa Hajiya Ruƙayya tayi ta kalli Khausar tare da jinjina kai itama Khausar kai ta jinjina.
Miƙewa Hajiya Ruƙayya tayi tare da kallon Mommy tace.
“Toh Hajiya Aysha Ubangiji Allah ya ƙara sauki sannan Allah ya tsareki daga sharrin abin ƙi ni zan wuce!”.
A hankali Mommy ta ɗan yunƙura tare da lumshe Idanunta kana tace.
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum Hajiya Ruƙayya Nagode”.
Hajiya Lami da Hajiya Bunayya kuwa baki suka saki suna kallon Hajiya Ruƙayya da Mamaki aransu suka ce kaji shegiyar mata da iyayi uban wa takewa wannan addu'ar.
Miƙewa Raudat tayi tare da riƙe hannun Hajiya Ruƙayya tace.
“Aunty Ruƙayya ni zan biki gidanki, Inje in kwana dasu Salman tun da gobe babu makarata”.
Da sauri Khausar ta kalli Raudat dake riƙe da hannun Aunty Ruƙayya tace.
“Ayyah Raudat am baza mu kwana ba?”.
Girgiza kai Raudat tayi tare da langwaɓar da kai kana tace.
“ Ni dai Ina tsoro ni bazan zauna ba”.
Kai Khausar ta gyaɗa da faɗin.
“Shikenan kibi Aunty Ruƙayya”.
Murmushi Aunty Ruƙayya tayi tare da jan hannun Khausar dake cikin nata
Har sun kai ƙofa Hajiya Bunayya ta ƙirƙiri murmushi tana kallon bayan Raudat tace.
“Oohhh Raudat ba zaki bini mu tafi gida ba?”.
Kafaɗa Raudat ta maƙale tace.
“A'a ni zanbi Aunty Ruƙayya”.
Aunyty Ruƙayya kuwa jan hannun Raudat tayi suka fice batare data sake jiran jin Abinda Hajiya Bunayya zata ceba.
Bayan tafiyar Aunty Ruƙayya babu da ɗewa Hajiya Bunayya ta miƙe tare da kallon Mommy tace.
“Toh ƙanwata zamu wuce Allah yaƙara sauƙi”.
Murmushi Mommy tayi da faɗin.
“Nagode Yaya ahuta gajiya”.
Hajiya Lami tace.
“Babu Gajiya”.
Sannan suka fice Khausar kuwa jinginar da kai tayi kamar mai bacci.
Da daddare Khausar ta miƙe daga kan dogon kujeran asibitin da take kwance ta dubi Mommy da bacci ya fara fisgarta tace.
“Mommy”.
Buɗe idanu Mommy tayi tare da kallon Khausar tace.
“Na'am Khausar ya akayi?”.
Ajiyar zuciya Khausar ta saki tana wasa da yatsun hannunta tace.
“Mommy baki zargi perpesoup ɗin nan da kika ci azubewar cikin nan ba!?”.
Sosai Mommy ta tsira mata ido na second uku zuwa biyar sai kuma ta miƙe daga kwanciyar da take Atake fara'ar dake fuskanta ya gushe cikin ɗaure fuska cikin kakkausan Murya tace.
“Khausar!, Khausar!!, Khausar!!!, Ki cigaba Nagode da abinda kike min Khausar, duk irin tarbiyyan da nake baki fatali kike dashi ko, kina ɗaukar rashin yarda kina ɗaurawa mutane ki sani Manzon Allah (S.A.W) Yace.
:Azzana zambu walau kana haƙƙun”.
Khausar kuwa ƙasa da kai tayi hawaye masu zafi suka cika Idanunta shin sai yaushe mahaifiyarta zata amince da gaskiyar da take so ta sani akan Hajiya Bunayya basa ƙaunarta cutar da ita suke sonyi.
Cikin sanyi murya tare da rauni gami da ban haƙuri tace.
“Shikenan Mommy kiyi haƙuri Allah ya huci zuciyarki”.
Mommy bata tanka taba ta juya ta gyara kwanciyar, ta itama Khausar juyawa tayi ta kwanta zuciyarta babu daɗi.
Washe gari Alhamis Da safe Dr ya shiga ya basu sallama dan jikinta yayi sauƙi Sosai Lamiɗo da kansa yaje ya maido su gida.
Suna dawowa Hajiya Bunayya ta shigo hannunta riƙe da babban Warmers da tayi Perpesoup ɗin Kaji ta shigo dashi.
Zama tayi akan 2sitter tace.
“Sannu ƙanwata ya ƙarfin jikin?”.
Mommy tayi yar dariya tare da faɗin.
“Jiki yayi sauƙi Yaya sai faman hidima kike dani kamar wacce tayi haihuwar farko?”.
Dariya Hajiya Bunayya tayi da faɗin.
“Ai mai ɓari yafi son akula dashi fiye da mai haihuwa”.
Khausar dake tsaye duk takaici ya gama cikita gashi babu dama ta faɗawa mahaifiyarta gaskiya sai ta hau kanta da faɗa bayan da ta iya daga ƙarshe ma Saboda takaici kawai sai ta koma Bedroom ɗin ta ta fara karatu.
Wunin ranan haka Hajiya Bunayya ta yini tare da Mommy ta cigaba da kulawa da ita.
Washe gari juma'a dai-dai lokacin da maza suka tafi Juma'a dai-dai lokacin da kowa ya tafi Sallar juma'a Akuma lokacin ne Hajiya Bunayya da Hajiya Lami suka tafi gidan Boka Kar'uzu.
Khausar da Mommy ne zaune suna hira sosai jikin Mommy yayi ƙarfi abinka da mai juriya ga kuma kulawa da take samu.
Sallamar Aunty Ruƙayya ya katse musu hirar da suke.
Khausar ta faɗaɗa fara'ar fuskarta kana tace.
“Aunty Ruƙayya sannu da zuwa ina Affan?”.
Murmushi Aunty Ruƙayya tayi tana zama tace.
“Affan yana lafiya bacci ma yake ya mai jikin”.
Khausar tace.
“Jiki da sauƙi”.
Aunty Ruƙayya tace.
“Masha Allah Ubangiji ya ƙara sauki”.
Cikin sakin fuska Mommy ta gyara zaman hular dake kanta tace.
“Hajiya Ruƙayya sannu da zuwa ya gajiyarki?”.
“Hajiya Ruƙayya tayi murmushi da faɗin.
“Babu gajiya ya jikin naki?”.
“Jiki yayi sauƙi ya yara?”.
Alhamdulillah ta bata amsa.
Khausar kuwa miƙewa tayi cikin neman izinin tace.
“Ayyah Mommy zanje gidan su Asma'u?”.
Ido Mommy ta zuma mata, na tsawon second bakwai tana kallonta kana tace.
“Toh yayi kyau”.
Khausar kuwa juyawa tayi ta shiga Bedroom Dogon rigar dake jikinta ta cire tare da ɗaura towel tashiga toilet,
shawer ta ɓude ta sakarwa kanta ruwan ɗumi,
ta ɗauki kusan minti shabiyar kafin ta fito ɗaure da towel da tsawon sa bai wuce gwiwar taba yayin da ƙarami ke kanta tana tsane ruwan kanta.
Stool ta janyo ta zaune tare da goge ruwan jikinta ta ɗauki Vassiline lotion ta shafa kana ta ɗauki powder ta shafe sai kuma Kajol ta zizara a idanunta mascara ta ɗauka ta taje gashin Idonta da sukayi tsayi tamkar tasa Eyelashes golb mai sheƙi ta ɗauka ta shafa asaman pinch lips ɗin ta sai yayi kamar jan baki ta shafa kallon fuskarta tayi a mirrow sosai tayi kyau.
Miƙewa tayi ta nufi jikin durowar ta buɗe uban kayan dake ciki ta zubawa ido ahankali Idanunta suka sauka akan wani Less Coffee da aka masa adon cycle da rastin Milk colour ta janyo ta sanya Masha Allah Sosai ɗinkin less ɗin ya mata kyau tare da fitar da shape din jikinta skirt ɗin ya zaune ɗass ajikinta tare da fitar mata da tsarerrenn ƙugunta haka ma rigar ta zauna ɗass ajikinta ɗan kwalin ta ɗauka tayi ɗauri mai kyau sai kuma ta ɗauki glaye medium size milk color kana ta feshe jikinta da turarukanta masu daɗin ƙamshi.
Falon ta fita tun kan ta isa Aunty Ruƙayya ta ɗago kanta tare da tsira mata Idanunta jin ƙamshin daya ratsa hancinta ta saki murmushi kana tace.
“Iyeee Masha Allah Khausar irin wannan kyau sai kace preety ta ƙasar India”.
Hannu Khausar ta sanya ta rufe fuskarta tana dariya sai kuma ta buɗe tace.
“Kai Aunty Ruƙayya Ina Zan samu koda rabin kyawunta ne?”.
Ware ido Aunty Ruƙayya tayi kana tace.
“Allah kuna kama dan da zakije India ma cewa za'ayi ke ƙanwarta ce, har rawan kanki ma irin natane a Film ɗin Chori-Chori Cubke-Cubke ne”.
Mommy Kam murmushi take musu batare da tace komai ba.
Khausar kuwa Murmushin jin daɗi tayi tare da tsugunnawa ta ɗauki wayar Mommy tace.
“Mommy zan tafi da wayarki".
Kai kawai Mommy ta gyaɗa mata sannan ta ɗauƙi wayar tare da faɗin.
“Na tafi”.
ta ida maganar tana gyara zaman Handbag din Hannunta tare da ciro earpiece aciki
Suka haɗa baki wajen faɗin.
“Adawo lafiya".
Kai ta jinjina tare da ficewa,
Abokin gate ta haɗu da Haiydar riƙe da MP ɗin sa, cikin sauri tace.
“Yauwa Haiydar dan Allah aramin MP ɗinka”.
Cike da mamaki ya zuba mata ido tare da cewa.
“Yau kuma to ke kuma da ba jin kiɗa ya dameki ba, me zakiyi dashi?”.
Kai ta ɗan jinjina tare da cewa.
“Wallahi yau dai shauƙi nakeji zanje wurin Asma'u mu ɗan rausaya”.
Murmushi yayi yana mamakin wai yau Khausar ce da cewa zata sha ƙiɗa, kawai miƙa mata yayi. Tare da cewa.
“Kuma kikasa gyale ko?”.
Cikin daɗi tace.
“Ngd kai rabani kullum mutum liƙe da hijabi kamar maitakaba” na mgnar tana fita ta tari adaidaita sahu ta shiga.
Acan ɓangaren Moddibo kuwa bayan an idar da Sallah juma'a ya kalli M Jameel dake Driving yace.
“J yakamaya muje mu gaida Ummi kafin mu koma gida!”.
Kai ya Jinjina kana yace.
“Dama abinda nake son faɗa kenan ka rigani”.
Gyara zama Moddibo yayi tare da lumshe idanunsa yana sauraron ƙira'ar dake tashi amotar kana ya shafa sajensa yace.
“Muje toh”.
Kai M Jameel ya gyaɗa tare da juya akalar motar zuwa unguwar su Ummi.
Suna cikin tafiya wayar M Jameel ya hau ruri yana duba screen ɗin wayar yaga Bahrain ba suna sai Number Dariya M Jameel yayi still hankalinsa nakan Driving din yace.
“Jalaludden! Wallahi Jalaludeen!! nayi mana abinda ransa keso”.
Moddibo da Idanunsa ke lumshe yayi ɗan guntun Murmushi ba tare daya buɗe idanun ba yace.
“Toh ka ɗaga mana kar ya yanke”.
Picking M Jameel yayi tare da Sallama.
Amsawa Jalaludeen yayi da faɗin.
“Idan kun isa ku gaishe da Ummi”.
M Jameel yayi Murmushi kana yace.
“Kana biye da mu ne?”.
“A'a bana biye daku na dai rigaku zuwa na gaisheta”.
Cewar Jalaluddeen
Dariya M Jameel yayi sai kuma ya zare ido yace.
“Wallahi Jalaludeen kada ka razana mana tsohuwa!”.
Murmushi Jalaludeen yayi yace.
“A'a bazata ra zanata ba sannan ba zata tsorata ba ai mun taɓa zuwa tare daku baku dai sani bane kuma na bayyana mata ta ganni”.
“Wallahi Jalaludeen ka kiyaye mufa”.
Dariya Jalaludeen yayi kana yace.
“Tare dai mukayi sallama jumma'a a sahu daya.
Yanzu kuma Na dai hango ku ahanya zakuje yanzu ina katakon nan?”.
Da sauri M Jameel yace.
“Wani katakon?”.
Cike da