Showing 141001 words to 144000 words out of 188939 words
Chapter 48 - SAKAYYA Book 1 complete BY GARKUWA.txt
kallesa kana tace.
“Wai Jameelu Meyesa kake yin haka ne?.
Wai meyesa?”.
Girgiza kai yayi tare da faɗin.
“Ai ɗa baya rasa laifin da yake yiwa Mahaifiyar sa, ko babu abinda na miki a yanzu, ai kin ɗauki nauyin cikina tsawon wata tara da kwanaki tara, kin sha wahalar naƙuda kafin ki haifeni, kinsha jidalin rainona, nayi miki kashi nayi miki fitsari na miki tumɓuɗi da amai, na hanaki bacci a lokacin da kowa ke bacci
Ummi kiya femin domin wannan ma shine babban abin neman yafiya ga iyaye, idan kuna akwai abinda na miki yayin kuruciya da girma da kuma yayin rarrafe wata ƙil har cizonki nayi yayin shayarwa dan Allah da Manzonsa duk ki yafe min, kiyi min aikin gafara”.
Ya ƙare mgnar cikin wani irin raunataccen muryar mai rawa.
Kai ta girgiza kana cikin raunin murya tace.
“Ba kayi min komai ba kuma na yafe maka duniya da lahira na yafe maka komai na raunin cewa ko da haihu da rainonka bayan haihuwa, duk na yafe maka shi tun kafin yau”.
Wasu irin tagwayen numfarfashi masu nauyi ya rinƙa sauƙe tare da cewa.
“Alhmadulillah Ummina ngd matuƙa.”
Ita kuwa Ummu cikin sarƙewan murya taci ga da cewa..
“Meyesa kake min irin wa'annan abubuwan bana sofa”.
Dariya yayi kana yace.
“Toh Ummi dan ɗa yanemi yafiyar Uwarsa sai yazama laifi?”.
Girgiza kai tayi tare da Kallonsa kana tace.
“Toh ni babu abinda ka min ka tashi mu tafi Allah yayi ma sakayya da mafifiyaciyar Al'jannah mai cike da ƙololuwa ni'ima tashi muje in rakaka”.
Ta faɗa tare da miƙewa kana ta riƙe hannunsa kamar yaro haka suka fito kana ta buɗe masa murfin motar tace.
“Toh kashiga Allah yayi maka al'barka”.
Kai ya gyaɗa tare da shiga.
Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.
“Toh kaje Ubangiji Allah ya maka albarka Allah ya tsareka Allah ya rufa maka asiri Ubangiji ya maka sakayya da mafi kyawun abin sakamako Allah yatsare min kai Allah Ubangiji ya Albarkanci rayuwar ka Allah ya azurtaka da arziki mai albarka da yara na gari”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum Ummina”.
Ya ida maganar tare da zuba mata Ido.
Asma'u kuwa ita ma shiru tayi tare da zuba masa Idanu tana kallon yanda yake kallon Ummi.
Khausar kuwa Kallonsa tayi kana tace.
“Yah Jameel gaskiya zan tafi idan kai ba zaka tafi ba”.
Kallonta yayi kana yace.
“Toh mutafi Lelewal baki sani bane duk saurin da kikeyi nafi ki sauri fa bakisan inda zanje bane fa shiyasa”.
Tura baki tayi kana tace.
“Yah Jameel Ina zaka je”.
Murmushi yayi tare da kallon Asma'u da Bashir kana yace.
“Ku kula da kanku sannan ku riƙe kada ku manta da alƙawarin da kuka min ga amanar Ummi na kafin na dawo”.
Murmushi sukayi tare da gyaɗa masa kai kana suka ce.
“Insha Allah Yah Jameel Allah yatsare sai kadawo.
Murmushi kawai yayi tare da jan motar suka fita saida Ummi taga motar ya ɓacewa kallonta kafin ta sauƙe ajiyar zuciya ta koma cikin gida Asma'u da Bashir na biye da ita.
Acan mota kuwa Anutse M Jameel ke Driving kana ahankali ya juya ya kalli Khausar data tsirawa tiri idanu kana ya sauƙe numfashi daga zuciyarsa ya fara tunanin Maganar da zai mats kana cikin sanyin murya yace.
“Lelewal”.
Juyawa tayi ta kallesa tare da cewa.
“Na'am Yah Jameel”.
A hankali ya furzar da iska kana a hankali cikin tattausan lafazin yace.
“Inne mi alfarma awajen ki mana?”.
Anutse ta kallesa kana tace.
“Toh Malam Jameel Allah yabani ikon yin duk al'farman daka ke so awajena”.
Cikin jin daɗi ya buɗe idanunsa dake lumshe ya kalleta kana yace.
“Kinyi alƙawarin duk abinda nake nemi al'farmar zaki yimin?”.
Kai ta gyaɗa masa kana tana wasa da yatsun hannunta tace.
“Na sani malam Jameel baza ka sani yin haramtaccen abu ba sannan baza ka sani yin abinda yafi ƙarfi naba kuma kafi ƙarfin neman alfarma ko wani abu awajena ina hana ka saidai ka bani Umarni Yah Jameel faɗa min me kake so inyi maka? Kai tsaye bani umarnin kawai ni kuwa in cika maka umarninka da sauri”.
Jinjina kansa yayi still Yana driving Cike da nutsuwa kana yace.
“Alhamdulillah naji daɗin Lelewal Thanks".
sai kuma yayi gyaran murya tare da juyowa ya kalleta, itama shi take kallo ganin yadda fuskarsa ta koma alamun daga can cikin ƙahon zuciyarsa abinda zai faɗa ɗin zai fito cikin yanayin neman al'farma cikin iyawa da ƙwarewa ya juya harshe zuwa sahihin Larabci mai cike da Kekkyawan lugga ya fara mgn da larabci yayinda itama Khausar ta juya harshen zuwa larabcin.
Aƙalla sunyi magana daya ɗauki tsawon minti goma sha biyar, kafin suka koma magana da yaren Hausa Inda M Jameel ya ƙare maganar da cewa.
“Nagode Khausar Nagode Nagode Lelewal Ubangiji Allah ya miki albarka”.
Khausar kuwa cikin wata raunan'niyar murya tayi ƙasa da kanta yayin da ruwan hawaye suka cika kwarmin Idanunta kana tace.
“Ameen”.
Ahankali M Jameel ya cigaba da Driving kana Yana cigaba da yi mata nasiyya akan rayuwa.
Ahankali Khausar da Idanunta ke kan madubin side ɗin da take ta juya tare da kallon M Jameel kana tace.
“Yah Jameel kamar wannan motar binmu fa take”.
Kai ya gyaɗa mata kana cikin sanyin murya yace.
“Eh nima na lura da haka Khausar tun ɗazu ma”.
Jinjina kai tayi tare da cewa.
“Toh Yah Jameel ka rage gudu mugani mana muga kodai mudin suke bi”.
Kai ya gyaɗa tare da rage gudun still sai motar dake bayansu itama ta rage gudun.
Ahankali M Jameel ya cigaba da Driving yayin da still motar ke bin bayansu.
Suna isa wani babban super market M Jameel ya kalli Khausar da hankalinta ke kan motar kana yace.
“Bari mushiga cikin Super Market ɗin nan mugani idan ma mu suke bi ai zasu tsaya”.
Suna Parking suka fita tare da shiga cikin Super Market din M Jameel ya ɗiba mata turaruka tare da Choculate da sweet da kuma Biscuits yana tsinta yana faɗa mata wasu kalamai da larabci, duk da dai ba ji nake amman yadda fuskarta ke nuna kalaman masu nauyi ne yake sanarmata.
Kana kamar kimanin minti talatin da shigarsu suka fito ga mamakinsu sai suka ga wannan motar ta faka agefen nasu kai tsaye suka shiga motar M Jameel ya mata key ita ma wannan motar sai akamata key aka tayar sunbi ta bayan motar idanun Khausar ya sauƙa akan Motar tana kallon fuskar mutanen ciki, duk da nesa ne ta gane cewa mutanen ne da ta gani Arugar Jauro Yaya sannan itace abakin makarantar su kana taga still Motar ta cigaba da binsu.
Lokaci ɗaya tsoro da damuwa ya shigeta cikin yanayin tsoro ta kalli M Jameel tare da cewa.
“Yah Jameel Motar nan mu take bi”.
Jinjina kai yayi tare da faɗin.
“Nima naga alama amma watakila arashi ake samu sunyi”.
Kai ta gyaɗa still zuciyarta na cigaba da bugawa da masifar ƙarfi suna cikin tafiya motar ta ɓacewa kallon su.
Anutse M Jameel ya Kalli Khausar kana yace.
“Kin gani kawai arashi ake samu may be suma zasu shiga Super Market ne sannan hanyar mu ɗaya shiyasa haka”.
Murmushin yaƙe Khausar tayi kana tace.
“Haka ne kam”.
Aranta kuwa cewa tayi to kodai mutanen sun gane ta ganeta ne shiyasa suke bibiyar rayuwarta wata ƙil ita suke son su kasheta kana ta raya dole idan ta koma dole ta faɗawa Mommy.
Anutse M Jameel ya juya tare da kallon Khausar data zurfafa cikin tunani kana yace.
“Lelewal muje mu gidan su Moddibo ki gaishe da Kakarmu”.
Da sauri ta dafe ƙirjinta tare da cewa.
“Gidansu Moddibo kuma?”.
Murmushi M Jameel yayi kana yace.
“Babu abinda zai miki Khausar”.
Girgiza kai tayi tare da cewa.
“Nikam ina tsoro Yah Jameel. Abu kaɗan ya fara masifa ko agidan mu ma faɗa yake min bare kuma naje gidansu”.
Cikin sanyin murya M Jameel yace.
“Nayi miki alƙawari ko hararanki ba zai yiba, Insha Allah bare kuma ya miki faɗa zai miki maraba, ki yarda dani”.
Kai ta gyaɗa kana cikin sanyin murya tace.
“Toh shikenan”.
Suna isa gidan yayi Parking a coumpund din farkon kana ya fita cike da nutsuwa yake tafiya tana biye dashi a baya, a kuma dai-dai lokacin da Moddibo ke kokarin fitowa daga falonsa, cikin sassarfa ya nufeshi.
Shi kuwa Modibbo wani irin sassayan numfashi ya fesar tare da tsaida idanunsa kan J ɗinsa.
Shi kuwa M Jameel murmushi mai cike da farin ciki yayi tare ƙara sawa wurin Modibbo rungume shi yayi da ƙarfi.
Wanda haka yasa shima Modibbo yayi masa wani irin amintaccen
runguma mai cike da son juna a tare suka sauƙe ajiyan zuciya cikin sanyin sauti Modibbo yace.
“J nayi fushi da kai”.
Cikin sanyin Muryan M Jameel yace.
“Kada kayi fushi dani A.J idan kayi fushi da J ɗin ka dawa zaka sulhunta”.
Cikin sanyin Murya Moddibo yace.
“J ka tafi gidan Ummi ka barmu mu kadai agidan, sam gidan nan ba daɗi idan baka nan shiru baki ɗaya gidan bai mana daɗi ba”.
Murmushi M Jameel yayi kana a hankali yace.
“A.J Rungumeka da nayi alfarma nake nema awajenka.
Saboda muyi maganar sirri akwai baƙuwar da nazo da ita dan Allah dan darajar Annabi A.J ko hararanta kada kayi”.
Sai kuma ya sauƙe numfashi tare da cewa.
“Ayyah A.J ka tayani cika al'ƙawarin dana ɗauka dan Allah kada ka tozar tamu ka tuna ba haushe yace baƙonka Annabin ka sannan Annabi Muhammad (S.A.W) yace duk wanda yayi imani da Allah da rana ta ƙarshe to ya girmama baƙon”.
Kai Moddibo ya jinjina kana yace.
“Toh J naji dama ya za'ayi na tozarta matar da J na zai aura har abada bazanyi hakaba?”.
Hararansa M Jameel yayi tare da faɗin.
“Kai dai kayi min al'ƙawari koma wacece ai zaka ganta”.
Kai kawai Moddibo ya gyaɗa.
Tare da cewa.
“Nayi al'ƙawari”.
Ahankali M Jameel ya sakeshi tare da matsawa.
Da sauri Moddibo ya ɗan yi gefe da kansa lokacin da idanunsa suka sauka akan Khausar da Idanunta ke ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.
Khausar kuwa cikin wata Sanyayyar murya mai cike da rauni ta kawar da kanta gefe tare da cewa.
“Ina yini”.
Kamar yanda ta kawar da kai gefe haka shima ya kawar tare da faɗin.
“Lafiya”.
Daga nan ya juya yayi gaba.
Khausar da M Jameel suka jera atare zuwa sashen Innayi bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga.
M Jameel kuwa cikin yanayin sa yace.
“Innayi ga baƙuwa na kawo miki ku gaisa”.
Daga cikin Innayi tayi murmushi tare da cewa.
“Sannun ku da zuwa ko dai matar ce ka kawo Min?”.
Murmushi mai sauti yayi kana yace.
“Ehahea lallai Innayi kenan ke dai ga tanan ku gaisa dama zan wuce da ita gida ne.
Kuma A.J nata kirana shiyasa nace bari na fara zuwa nasan idan bai ganni ba wataƙil hankalin sa bazai kwanta ba”.
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauke kana yace.
“Hmmm Yayi maka kyau da kazo a gaggauce ai da sai ka ajiyeta kafin kazo”.
Murmushi M Jameel yayi tare da cewa.
“Ai kawota nayi ta gaida Innayi kuma bamu gama tattaunawa da itaba”.
Taɓe baki Moddibo yayi ba tare da yace komai ba.
Khausar kuwa ahankali ta tsugunna tare da Gaishe da Innayi.
Kallonta Innayi tayi kana tace.
“A'a wannan ai kamar na ganeki kamar ƙawar Asma'u ko?”.
Kai Khausar ta gyaɗa tare da sakin murmushi kana tace.
“Eh nice Innayi”.
Jinjina kai Innayi tayi tare da cewa.
“Yasu mamanki?”.
Cike da nutsuwa Khausar tace.
“Duk suna lafiya”.
Ƙoƙarin miƙewa Innayi tayi kana tace.
“Bari akawo miki abin taɓawa”.
Cikin sauri Khausar ta girgiza kai tare da cewa.
“Nagode Innayi yanzu daga gidan Ummi nake ta cika min cika na da abinci”.
Saurin kallonta Moddibo yayi jin yanda take magana Anutse kamar ba ita ba baki ya taɓe tare da mgnar zuci.
“Ganta kamar gaske haka take da nitsuwa”.
M Jameel kuwa kallon Innayi yayi kana ya juyi ya kalli Khausar yace.
“Mu tafi ko”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh”.
kana tayi gaba M Jameel da Moddibo suka fito atare a hankali suke tafiya, a hankali lips ɗin M Jameel na motsawa alamun mgn yakeyiwa Modibbo, shi kuwa Modibbo kai kawai yake jinjina mishi tare da tsaresa da ido, a haka har suka isa bakin motar Moddibo da kanshi ya buɗe masa gaban motar ya shiga kana yace.
“Dan Allah kazo kada ka barni. Ni kaɗai sam bana jin daɗin gidan”.
Murmushi M Jameel yayi tare da yiwa motar key kana yace.
“A.J ka jika randa akace babu nifa?”.
Cikin sauri Moddibo ya rumtse idanunsa da karfi, sai kuma ya buɗe su da sauri ya kallesa tare da cewa.
“Jhhhh”.
Ya ja sunan a cikin maƙoshinsa.
Murmushi M Jameel yayi tare da jan motar,
Shi kuwa Modibbo hannunsa ya harɗe a ƙirji yana kallonsa har suka tafi.
Kai tsaye unguwar su Khausar suka nufa suna tafe yana tsokanarta, a haka har suka isa yana isa yayi Parking ta fita tare da yi masa godiya kana tayi cikin gida.
M Jameel kuwa Anutse ya juya akalar motarsa kai tsaye gidansu ya nufa yana isa yayi Parking tare da fita kai tsaye sashen Abban sa ya nufa yan shiga sukayi ta hira har La'asar tayi, atare suka je masallaci suka gabatar da sallah kana bayan su. Idar ya fito ya nufi Sashen sa yashiga bai sake fita ba sai da akayi Maghariba kana ya nufi masallaci bai fito ba sai da aka Idar da Isha'i sannan yana dawowa ya nufi sashen Abbansa lokacin shima Abbah bai dade da dawowa daga masallaci ba.
Cikin lumshe ido yace.
“Abba zanje wajen Moddibo za muyi magana”.
Jinjina kai Abba yayi tare da cewa.
“Allah ya tsare amma idan dare yayi ka kwana a can bana son tafiyar daren nan, kasan duniyar nan babu gaskiya”.
Kai M Jameel ya gyaɗa kana ya fice yana murmushi.
Motarsa ya shiga da addu'a kana yayi Hong mai gadi ya buɗe masa ya hau kan titi yana maiyin murmushin, wayarsa ya zaro, whatsApp ya shiga kan number'n Moddibon ya kusa kai.
Cikin sakin murmushin yayi mishi voice ɗin 1 mitune And 33 second
Ba zato ba tsammani yaji an sako hannu daga bayansa an ɗaura masa bindiga akai kana cikin wata magautacciyar murya akace kana juyawa zan fasa maka ƙwaƙwalwar kai da sauri ya saki wayar tasa ta faɗa kan cinyarsa garin ta sule ɗin ne kuma yatsarsa ma nuniya tayi sending din voise ɗin nasa da sauri ya ƙara taka motar jin mutumin ya ɗana kunaman bindigar yana cewa.
“Maza mu tafi kada kayi min gardama dan ko motsi kayi zan fasa kanka...!
Dan-dan yanzufa aka fara labarin ku biyuni, da kekkyawar yaƙini da ƙarfin zuciya.
*By*
*GARKUWAN MARUBUTA*
*A
Isrehjɗɗ. Acan Falon Moddibo kuwa zaune yake akan 2sitter hannunsa riƙe da Kofin Tea yana sha time to time zai ɗaga kansa tare da kallon agogon dake manne abango ahankali ya gyara zamansa tare da kurɓan tea dake tiriri ya lumshe idanunsa tare da buɗe su akan agogon cinyarsa ya matse da ƙarfi har saida yaji jikinsa na rawa, ƙara matse jikinsa yayi sabida yadda yake jin M ɗinsa na miƙewa yana harbawa cike da zalama, ɗan gajeren tsakiya yaja, cikin sanyin murya a fili yace.
“J har yanzu baka dawo ba”.
Yayi mgnar kamar Jameel ɗin na gabansa.
Sai kuma ahankali yasa hannunsa tare da laluɓar wayarsa a aljihun sa na hagu da dama jin babu yasa yaja siririn tsaki tare da miƙewa cikin wani irin masifeffen kasala da sanyin jiki mai kashe ilahirin gaɓɓai ya nufi bedroom ɗinsa a kuma lokaci ɗaya zuciyarsa ta buga tare da tsinkewa da masifaffen ƙarfi, da ƙyar ya iya ɗaga ƙafarsa na dama kana ya taka ya shiga Bedroom tare da furta.
“Hasbunallahu wani'imal wakin”.
Jin yanda zuciyarsa ke cigaba da bugawa cikin yanayin tsinkewar zuciya da sanyin jiki ya ɗauki ƙaramar wayar tasa, kana ya dawo falon ya zauna tare da shiga Call log zai kira M Jameel sai kuma kiran Malam Arɗo yashigo wayar sa.
Zubawa screen ɗin wayar ido yayi tare da jan siririn tsaki kamar ba zai ɗaga ba sai wata zuciyar tace ka ɗaga mana kasan menene Uzirinsa ajiyar zuciya ya sauƙe tare da picking.
Acan ɓangaren Ummi kuwa zaune take a falonta kan kujera 3sitter tayi ta tagumi da duka hannunta biyu, kana ta tsirawa waje ɗaya Idanu yayin da ƙirjinta ke bugawa da masifar ƙarfi zuciyarta na tsinkewa yana bada sautin dif-dif-dif lokaci ɗaya taji wata muguwar kasala na rufe mata jiki haka nan take jin zuciyarta na tsinkewa.
Jiki a mace Asma'u ta fito daga kichen hannunta riƙe da Plate ƙara sawa falon tayi Idanunta akan Ummi data zabga tagumi ta zauna akan 1sitter tare da cewa.
“Ummi har yanzu baki kwanta ba?”.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da fesar da numfashi kana ta gyaɗa mata kai tare da cewa.
“Eh Asma'u ban kwanta ba”.
Cike da kulawa Asma'u ta ɗaga kanta tare da kalli agogo, tare da cewa.
“Ummi kalli fa har sha ɗaya ta wuce me kikeyi afalo ke kaɗai shiru ga Abban mu yashiga tun ɗazu”.
Lumshe Idanu Ummi tayi still zuciyarta na tsinkewa kana tace.
“Babu”.
Numfashi Asma'u ta fesar tare da ajiye cokalin dake hannunta tace.
“Toh Ummi ko dai baki da lafiya ne?”.
Kallonta Ummi tayi tare da girgiza kai.
“Lafiyata ƙalau Asma'u”.
“Ayyah Ummi am to mai yasa baki kwanta ba kin zauna shiru ke kaɗai dubi yanda kika yi tagumi da hannu duka bibbiyu”.
Cewar Asma'u.
“Ban sani ba Asma'u ba wai bani da lafiya ba amma ina jin jikina wani iri bai min daɗi ba ina jin zuciyata na tsinkewa sannan ga wata kasala data rufe ni”.
Ido Asma'u ta zuba mata kamar mai son gane wani abu sai kuma tace.
“Toh Ummi ki riƙa maimaita Hasbunallahu wani'imal wakin mana kuma may be rashin bacci ne kinga jiya kwana mukayi muna hira ba kisamu kinyi wadataccen bacci ba, sannan yau da safe ma baki samu kinyi wani ishesshen bacci ba”.
Gyara riƙon da taiwa plate ɗin tayi kana taci gaba da cewa.
“Har yanzu ma baki samu kinyi Ummi, kiyi ƙoƙari kije ki kwanta Insha Allah zakiji dama dama”.
Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
“Toh ki maida Plate ɗin kichen idan kin gama sannan ki rufe ƙofar kichen ɗin kana kizo ki rufe mana ƙofan falon”.
Kai Asma'u ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh”.
Ta mike tare da ajiye Plate din ta kife Sauran abincin sannan ta rufe ƙofar tare da murza mukulli ta dawo.
Still zaune ta samu Ummi tayi tagumi.
Cike da kulawa tace.
“Ummi kije ki kwanta dan Allah kiyi baccin”.
Ahankali Ummi ta ɗago ta kalleta tare da sauƙe ajiyar zuciya kana tace.
“Toh kije Insha Allah yanzu zan kwanta”.
Kai Asma'u ta gyaɗa kana ta wuce Bedroom ɗin ta Ummi kuwa kasa tashi tayi ahankali ta lumshe Idanunta tare da komawa ta kwanta akan kujeran still zuciyarta