Header Ads
Showing 120001 words to 123000 words out of 188939 words

Chapter 41 - SAKAYYA Book 1 complete BY GARKUWA.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

ta tura asiya min waya acikin Taraba wayar da yafi wacce ya kawo min ma za'a siya Min”.


Muskutawa Asma'u tayi kana tace.
“Yama fi miki nima Ya Jameel yace zai siya min waya”.
Wara Ido Khausar tayi cike da farin ciki tace.
“Kice mun kusa muyi waya mu daina Aron na su Ummi”.
Jinjina kai Asma'u tayi kana tace.
“Ai dai Lallai kam munji daɗin mu”.


Acan ɓangaren Moddibo kuwa a hankali ya fito da motarsa daga gidan Malam Arɗo ya dai-dai-ta hanci motarsa akan titi cikin nutsuwa yake driven yayin da ƙira'ar ke tashi acikin suratul Muminin cikin, Sanyayyar sautin muryarsa yake bin ƙira'ar dai-dai ƙofar gidan su M Jameel yayi parking tare da ciro wayarsa yayi dearling number M Jameel Amma har ya katse ba ayi Picking ba sake kira yayi still ba amsa ajiye wayar yayi tare da buɗe Murfin motar kana ya fita mai gadi naganin sa yayi saurin miƙewa hannu Moddibo ya bashi suka gaisa ahankali Moddibo yace.
“J yana ciki ne”.
Cike da girmamawa mai gadin ya girgiza kai tare da cewa.
“A'a” godiya Moddibo ya masa kana ya shiga motarsa kai tsaye gidan Ummi ya nufa da tunanin ƙila Jameel na can bayan yayi Parking ya fito Anutse ya shiga Falon bakinsa ɗauke da Sallama.
“Ummi dake zaune tana Azkharul masa ta ɗago kai tare da faɗada fara'ar dake fuskarta kana tace.
“Babana sannu da zuwa”.
Cikin yanayin nutsuwarsa da kuma sanyinsa yace.
“Ummi ina yini”.
Ta amsa da.
Lafiya tare da tambayar Innayi
Kansa a ƙasa yace.
“Duk suna lafiya Ummi J fa?”.


Zama Ummi ta gyara tare da cewa.
“Tun shekaran jiya da kuka zo ai be sake zuwa ba amman dai nasan in sha Allah yau zaizo”.
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauke kana yace.
“Ayyah ni kuma tun safe da muka rabu bamu haɗu bane shiyasa nazo nan, naje can gidan Abba ma baya nan nayi tsammanin ma yazo nan wataƙil ko suna tare da Innayi”.
Shiru Ummi tayi alamar tunani kana tace.
“Eh to wataƙil ma yana can”.
Jingina kai Moddibo yayi kana yace.
“Ni na kira ma baya ɗagawa”.
Hannu Ummi ta miƙa tare da ɗaukar wayarta kana tace.
“Bari na gwada”.
ta faɗa tare da dearling.
Cikin sa'a yana shiga M Jameel Yayi picking tare da Sallama.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe kana tace.
“Ina kake ne?”.
Anutse M Jameel yace.
“Ummi ina wajen Innayi ce muna hira”.
Kallon Moddibo tayi tare da faɗin.
“Aikuwa ga Moddibo yazo neman ka”.
Dariya M Jameel Yayi kana yace.
“Rabu dashi Ummi be nemeni agida ba ya tafi maƙota yana nema na”.


Kallon Moddibo dake sakin ajiyar zuciya Ummi tayi kana tayi murmushi tare da cewa.
“Ai dai kam”.
Moddibo kuwa kallon Ummi yayi bayan ta katse wayar yace.
“Toh Ummi bari na tafi tun da yana gida kam”.
Jinjina kai Ummi tayi kana tace.
“Toh ba matsala Moddibo Nagode bari na kawo maka abin taɓawa”,
Ta faɗa tare da miƙewa kichen tashiga tare da ɗauko masa Alkaki da dambun naman kaza ta ajiye masa acikin wasu roba masu kyau.
Amsa yayi da faɗin.
“Nagode Ummi”.
Sannan ya juya har ya isa ƙofan Falon Ummi tayi saurin cewa.
“Yawwa Babana tsaya dan Allah ka ajiye min yarinyar nan agida”.
Ta faɗa tare da juyawa ta nufi ɗakin Asma'u tare da cewa.
“Khausar ina yanzu zaki tafi ga Maghariba ta kawo kai?”
Daga ciki Khausar ta ɗan daga sautin muryanta tare da cewa.
“Eh Ummi yanzu zan tafi”.
Kai Ummi ta gyaɗa tare da juyawa kana tace.
“Toh ki fito Yayanki ya sauƙe ki tunda dai dole sai yabi ta titin unguwar ku”.
Murmushi Khausar tayi tana ƙoƙarin sanya hijabinta tace.
“Yaya Jameel ko?”.
Cikin sauri ta fito falon Cak ta tsaya ganin Moddibo nanda nan ta nemi fara'ar dake fuskanta ta ta rasa.


Hannunta Ummi ta riƙe kana tace.
“Yawwa Babana ka sauƙe min ita agida kasan ƴaƴa mata bama so suna kaiwa dare awaje”.
Shiru Moddibo yayi tun lokacin da Ummi ta ambaci sunan Khausar ya nemi nutsuwarsa ya rasa sam baya.
Son wata alaƙar da zai haɗa sa da yarinya.
Jin yayi shiru Ummi ta kallesa tare da cewa.
“Ya dai Babana ko dai da matsala ne?”.
Girgiza kai yayi kana cikin sanyin murya yace.
“A'a”.
Still tana riƙe da hannun Khausar tace.
“Toh dan Allah kayi haƙuri ka sauƙeta aƙofar gidansu Lamiɗo”.
Jinjina kai yayi tare da faɗin.
“Toh shikenan Ummi”.
Sannan ya fice.
Har jikin mota Ummi da Asma'u daketa murmushin mugunta suka raka Khausar.
Anutse Moddibo ya buɗe mazaunin Driver ya shiga Khausar kuwa cikin tsinkewar zuciya ta buɗe gaban motar ƙiran Rang Rover tashiga cikin sauri ta lumshe Idanunta jin wani ƙamshi mai daɗi daya ratsa hancinta ne yasata lumshe ido, ahankali ta tukure jikinta waje ɗaya.
Moddibo kuwa motar yaja.
Hannu Ummi ta ɗaga musu tare da cewa.
“Toh Allah ya kare Babana Nagode Allah Yamaka albarka”.
Asma'u kuwa murmushi kawai ta saki ganin yanda Khausar tayi tsuru-tsuru tamkar za'ace ƙyat ta arta da gudu.


Tunda suka shiga motar babu wanda yace da ɗan Uwansa komai kowa da irin tunanin da yake Aransa kana ga abin hawa da suke giftawa da ɗan gudu kasancewar maghariba ta gabato Ahankali Khausar ta juya tare da satan kallon sa gudun kada tayi laifi awajen sa yace bata gaishesa ba yasa cikin sanyin murya tace.
“Malam ina yini”.
Banza yayi da ita kamar bai jiba.
Cikin sanyin Murya ta sake cewa.
“Malam ina yini”.
Still banza ya mata.
Lumshe Idanunta tayi akaro na uku kana tace.
“Malam ina yini”.
Still ƙin tanka ta yayi ya cigaba da Driving ɗinsa.
Ƙawar da kai gefe Khausar tayi tare da watsa masa Harara kana ta murguɗa baki asaman laɓɓanta tace.
“Ai dai nafita hakki ko awajen Allah”.
Shi kuwa Moddibo tunda wannan abin yafaru atsakaninsu yasa yake jin haushin Yarinyar gani yake tamkar idan suka haɗu zata rainasa kana yana ganin yanayin da suka kasance Amafarki kamar ta sani.
Cikin dakekkiyar murya yace.
“Idan kika sake tura min bakin nan, zan tsike lips ɗin in watsawa karnuka”.
Tsit tayi kamar bata cikin motar, mamaki kawai takeyi ya akayi yasan ta murguɗa mishi baki, domin ko ta inda take bai kallaba.
A haka dai sukaci gaba da tafiya.
Suna cikin tafiya wata Trailer tazo ta hannun damar su yayin da wata ƙaramar mota ke gefen hagunsu daga gabansu kuwa mai Napep ne duk ajere suke tafiya Trailer dake gefen damar su ya yanko ta gefensu tamkar zai hau kansu cikin sauri Moddibo ya karkatar da kan motar zuwa hagunsa cikin rashin sani ya gogawa motar dake hagunsa cikin sauri ya juya akalar motar zuwa gaba nan ma ya bugi mai Napep dake gabansu gaba ɗaya abun ya faru a lokaci ɗaya kamar ƙibtawar ido.


Cikin tsananin tsoro da kiɗimar ganin accident na Shirin faruwa yasa Khausar ƙwalla ƙara tare dasa hannunta kan hannun Moddibon ta damƙe fam tare da faɗin.
“Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n, Ɗiyyyyttt-ɗiyyyytttt”,Tayi ƙaran tare da hayewa jikin Moddibo ya zama na duka rabin jikinta na kansa kana ta ƙanƙame hannunsa tare da manna kanta adamten sa na dama. Har lau kuma Ɗiyyyt-Ɗiyyyyyyt take cewa kamar itace motar.


*Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci ba haƙin na kanki, 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276 sai in saki a Group na inda nake posting littafin. In dai baki biya sis kada ki karanta min littafina, kuma in kin gashi a wasu wuraren ma na satane, na Allah ya isa.*


Cikin sauri mai Napep ɗin ya ƙara gudu wancan motar tabi bayansa,Cikin ikon Allah ya zamana babu wanda yaji ciwo Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe yana sakin numfashi baki ɗaya ya gama Imagine zai haw kan mai Napep ɗin nan, baki ɗaya zuciyarsa ta tsinke.
Khausar kuwa numfashi ta shiga saukewa akai-akai tare da sake manna kanta ajikin damtsen hannunsa.
Ahankali ya juya ya kalli yanda rabin jikinta ke kansa cikin wata Sanyayyar murya mai cike da wani irin yanayin salo yace.
“Sake ni”.
Wannan shine karo na biyu arayuwarsa da yaji yayi amfani da irin wannan murya wanda shi kansa bai san daga inda ya samo shi ba.


Ita kuwa cikin sauran tsoron tayi lamo a jikinsa.
Buɗe idanunsa yayi da kyar murya a harɗe yace.
“Zaki kasheni fa”.
Haka nan taji raunin muryar da yayi mgn da ita har tsakiyar kanta.
Cike da tsoro da kuma sanyin jiki ta janye jikinta daga garesa kana ta sauƙe ajiyar zuciya cikin rawan murya tace.
“Ni dai ka sauƙe ni anan zan shiga Napep”.
Harara ya watsa mata kana ya cigaba da Driving ɗin sa batare daya tanka taba yana isa ƙofar gidansu yayi Parking cikin sauri ta buɗe Murfin motar ta fita Shikuwa kai tsaye gida ya nufa, zuwa lokacin har anfara kiran sallar maghariba yana Parking ya fito cikin nutsuwa ya nufi sashen sa tare da wucewa yashiga toilet kana ya ɗaura alwala ya fito dai-dai lokacin da M Jameel ma ya fito daga ɗaya ɗakin da alamun shima alwala yayi.
M Jameel na Kallonsa ya zuba masa ido yana murmushi kana yace.
“No wonder A.J Ashe ƙwarjininka ba halitta kaɗai bace gadone jinine mai ƙarfi ke yawo a jikinka”.
Anutse Moddibo ya juya tare da kallon M Jameel daya tsaresa da Ido kana yace.
“Meye kake kallona haka?”.
Murmushi M Jameel Yayi kana yace.
“Ina kallon kane tamkar...!




Idrneɗɗ. Cikin sauri Moddibo ya katsesa tare da cewa.
“Kana kallona kamar me?”.
Murmushi M Jameel yayi tare da shafa sajensa kana yace.
“Ina kallon ka kamar Ayu uban Jarababbun duniya”.
Harara Moddibo ya watsa masa tare da cewa.
“Mtssss kai dai baka da aikin yi”.
Ya ƙare mgnar tare da yin ƙasa da kansa yana kallon yanda Jallabiyar, lumshe Idanunsa yayi lokaci ɗaya tsikar jikinsa ya tashi cije labɓansa na ƙasa yayi kana yaja siririn tsaki tare da komawa Bedroom ɗin sa buɗe durowarsa yayi tare da ɗaukar boxes ya sanya kana yaƙara dogon wando sannan ya fito still. Yana jin tudun A ɗin sa M Jameel na ganin fitowarsa ya juya suka fice kai tsaye Masjid suka nufa tare da gabatar da Sallar Maghariba basu fita ba sai da suka idar da Sallar Isha'i sannan suka fito.


Bayan sun isa bakin gate M Jameel ya nufi jikin motarsa dake fake Kallonsa Moddibo yayi kana yace.
“A'a Baza mushiga muci abinci ba?”.
Cike da kulawa M Jameel yayi murmushi tare da cewa.
“Aini naci tunda zafinsa, kasan tun yaushe muke tare da Innayi kuwa? tun bayan sallar la'asar muna tare fa sai da aka kira maghariba nashigo nan nayi alwala”.
Wara Ido Moddibo yayi kana yace.
“Iyee gulmar me kuka yi?”.
Murmushi M Jameel yayi tare da faɗin.
“Ta faɗa min komai ta faɗa min duk kan abinda baka sani ba”.
Gyara tsayuwa Moddibo yayi tare da harɗe hannunsa aƙirji kana ya juya ya kallesa tare da cewa.
“Kamarya abinda ban sani ba?”.
M Jameel kuwa murmushi yayi tare da cewa.
“Zuwa yanzu nafi ka sanin kan ka ma nafi ka sanin wanene kai duk yanda kasan kan ka to yanzu na fika sanin kan ka”.
Lumshe idanu Moddibo yayi tare da shafa sashensa kana ya buɗe idanun nasan tare da kallon M Jameel yace.
“Iyeeeeh toh zo ka fesa min mana tunda angumtsa maka na hannun damana”.
Tsayuwa M Jameel ya gyara tare da cewa.
“Sirrine sai da nayi al'ƙawari bazan fesa maka ba kafin ake fesa min”.
Moddibo kuwa murmushi yayi tare da shafa sajensa kana yace.
“Toh yanda kayi lallaɓa nima zanje inyi lallaɓan afaɗa min”.
Cikin dariya M Jameel yace.
“Toh kaje ka gwada sa'arka, amma yanzu kam kasani bana cikin duhu”.
Taɓe baki Moddibo yayi kana yace.
“Iyyeeee wato gulmana nema kuka tayi”.
Agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa ya kalla ganin da ɗan sauran lokacin salla ne ya juyo ya kalli Moddibo tare da faɗin.
“Ba wani gulmarka da muka tayi na dai faɗa mata cewa kana ɓuƙatar aure yanzu”.
Cikin sauri Moddibo ya juya tare da watsa masa Harara Dariya M Jameel yayi tare da buɗe motarsa yashiga mazaunin Driver key yayi wa motar tare da saita hancin motar ya fara tafiya.
Shi kuwa Modibbo da ƙafa ya nufi masallacin.
A hanya ya tsaya yayi salla kana ya ƙarasa cikin gidan.


Parking aharabar gidan cike da nutsuwa ya fito tare da nufar falon bakinsa ɗauke da sallama ya shiga.
Ahankali yake bin cikin falon da kallo batare daya shiga ba cikin hasken fari gloves ɗin da suka haska falon kana da murmushi afuskarsa yace.
“Ina Umminaaaa?”.
Ummi dake zaune kan 3sitter idanu ta zuba masa batare da tace komai ba.
Malam Ahmad dake zaune kan 1sitter ya kalli M Jameel dake tsaye ƙofar falon tare da cewa.
“Ƙara so mana Jamilu”.
Juyawa yayi ya kalli Ummi kana yace.
“Kin tsaresa da ido kuma baki ce masa ya shigo ba”.
Murmushi M Jameel yayi tare da cewa.
“Ummi nayi kyau ko?”.
Jinjina kai Ummi tayi still Idanunta na kansa tace.
“Sosai ma Babana”.
Murmushi yayi tare da Wara ido kana yace.
“Iyyeee naji daɗina yau kuma nine Babanki ko da yake Baban miji ai baba ne?”.
Kai Malam Ahmad ya gyaɗa kana yace.
“Sosai ma”.
Ummi kuwa still Idanunta na kanshi.
Bashir daya fito daga Bedroom ne ya kalli Ummi kana ya kalli M Jameel data tsirawa Idanu matsawa kusa da Ummin yayi tare da cewa.
“Yaya Jameel wallahi Ummi na sonka kamar me”.
Sai asannan Ummi ta ɗauke Idanunta daga kan M Jameel ta mayar kan Bashir tare da yi masa daƙuwa kana tace.
“Haka naka Bashiru”.
Asma'u data fitowarta kenan daga Bedroom tayi murmushi tare da zama gefen M Jameel.
Miƙewa Malam Ahmad yayi tare da nufar ɗakinsa bayan sun gaisa da M Jameel.


Kallon Asma'u M Jameel Yayi tare da cewa.
“Asmeey”.
Cike da ladabi ta ɗago kanta kana tace.
“Na'am Yaya”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa.
“Zuwa yanzu kaso 85% cikin 100% na nauyin ku dake araina nake tunawa 85% sun sauƙa min saura shabiyar nake tunawa 15% ɗin nan kuma sune manya masu wuya”.
Ajiyar zuciya yauƙe tare da cewa.
“Ina so inga kinyi karatu kin gama, sannan na miki zaɓi da miji na gari Mumini, Salihi, Mai tsoron Allah, na Aura masa ke, sannan na danƙa masa Amanar ki.
Hakazalika Ina so inga Bashir ya gama karatunsa ya fara aiki ta yanda ko bana kusa zai kula da Ummin mu ba zata nemi komai ta rasaba”.
Cikin yanayin damuwa Asma'u tayi ƙasa da kanta lokaci ɗaya Idanunta suka ciko da hawaye yayin da taji zuciyarta yana masifar bugawa da ƙarfi Allah ya sani in ta tuna zatayi aure ta rabu da Unminta tanajin ba daɗi.
Cikin raunin murya tace.
“Bare ma Yah Jameel kai zaka yiwa Ummi komai kafin mu”.
M Jameel kuwa murmushi yayi tare da kallon Asma'u kana ya cije labɓansa na ƙasa tare da lumshe idanunsa yana sauraron bugun zuciyarsa ajiyar zuciya ya sauƙe tare da buɗe idanunsa akan Asma'u kana yace.
“To ai ita rayuwar dama ta gaji haka watarana ayi farin ciki watarana ayi baƙin ciki!”.
Girgiza Kai Bashir yayi tare da kallon M Jameel cikin yanayin tsinkewar zuciya ya gyara zamansa tare da cewa.
“Yah Jameel Meyesa kake karyar mana da zuciya ne!?”.
Girgiza kai M Jameel Yayi tare da kallonsu wani irin tausayinsu da kuma ƙaunarsu na ratsa dukkan zuciyarsa, bashi da wani ƙunci a rayuwarsa fiye da yadda ya kasance baya tare da Umminsa da ƙannensa a inuwa ɗaya, ciwon sakin mace ba iya kanta kawai yake tsayuwa ba, har kan ƴaƴan data haifa yake shafa.
Iska mai zafi ya fesar daga bakinsa kana yace.
“Ba karya zuciya bane Bashir burina ne, akan ku inaji kuma har yanzu akwai kason da ban idaba,
sabida ban zaɓawa Asma'u mijin aure a shine babban abinda yafi damuna sannan kai kuma kagama makarantar ƙuruciya ce sai jami'a gidan kazo nazo”.
Numfashi yaja tare da fesarwa Idanunsa nakan Bashir yace.
“Acan ne ake samun tarbiyya daban-daban da halayyar al'ummar matasa kashi-kashi ina tunanin kada ginin da mukayi nida Ummi wani yaje yayi yaɓe akai ya lalata kyakkyawan gini da kyakkyawan tubalin da mukayi maka”.
Da sauri Bashir ya jujjuya kai tare da cewa.
“In sha Allah haka bazai faruba”.
Cikin jin sanyi yace.
“Bashir kayi min al'ƙawarin zaka kasance nagari, kayi min alƙawarin zaka kasancewa Ummi farin cikinta”.
Lokaci ɗaya hawaye suka cika idanun Bashir cike da tsoron kalaman Yayan nasa.
Cikin wata razananniyar murya ya kalli M Jameel da Idanunsa ke lumshe kana yace.
“Nayi maka al'ƙawari Yah Jameel Nayi alƙawari zan kasancewa Ummi ɗa nagari zan kasance me share mata hawaye, zan kasance mai sata farin ciki idan Allah yayi duniya dan Manzo (S.A.W) ”.
A hankali ya ɗaga idanunsa tare da kallon Ummi da ta tsirawa M Jameel idanu cikin wani irin yanayi ko ƙyaftawa bata yi ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Zan kasance mai sata farin ciki, nayi alƙawari Ummi ba zata taɓa shiga ƙunci ko damuwa ba in dai a kai nane in sha Allah”.
Ahankali M Jameel ya maida kansa jikin kushin ɗin ya jingina kana ya miƙe ƙafafunsa tare da riƙe hannun Bashir aciki nasa kana ya cije lips ɗin sa.
Ummi kuwa wani irin sanyi jikinta da zuciyarta keyi cikin wani irin yanayi ta zubawa M Jameel Idanu.
Anutse M Jameel ya buɗe Idanunsa dake lumshe ya sauƙe akan Ummi Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da furzar da iska daga bakinsa kana yace.
“Ummi ya dai kike kallona haka kamar na ƙarshe!?”.
Cikin saurin Ummi ta dafe ƙirjinta daya buga da ƙarfin gaske cikin raunin murya irin na wanda ke gab da zub da hawaye ta kallesa karo na farko arayuwarta data fara kiran sunan sa tace.
“Haba haba Jamilu”.
Cike da mamaki ya ɗago idanunsa da suka sauya launi ya kalleta, Asma'u ma da sauri ta kalli Ummi haka ma Bashir karo na farko kenan arayuwar su da suka ji Ummi ta kira M Jameel da sunan sa.


Ummi kuwa lokaci ɗaya wasu hawaye masu masifar zafi suka fara bin kuncinta Shar-shar.
Cikin yanayin tashin hankali M Jameel ya sauƙa tare da ƙara sawa gabanta ya durƙusa tare da riƙe hannun ta cikin sanyin murya yace.
“Ummi kiya femin Ummina kiya femin kada ki zubar da hawayenki akaina Ummi me nayi miki!”.
Damƙe hannunsa Ummi tayi cikin raunin murya da alamun tashin hankali tace.
“Meyesa kake zuwa kake karya mana zuciya nida ƙannenka, kasani ayanzu kaine Inuwata kaine mafakar da muke samu nida ƙannen ka muke fakewa. Meyesa wasu lokutan idan kazo kake min wasu maganganu masu wuyar fahimta”.
Ta ida maganar hawaye nabin kuncinta.


Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da yin murmushi yayin da Idanunsa ke sheƙi kana yace.
“Toh Ummi inada ikon canza ƙaddarata ce? Idan son samu ne Ummi zan kasance me Kula dake har iya ƙarshen numfashi na, kuma zan kasance me saki acikin farin ciki da walwala har numfashina na ƙarshe”.
Girgiza kai Ummi tayi still Hawaye nabin fuskarta tace.
“Ko yanzu ka sanya ni farin ciki duk kan wani farin ciki da jin daɗi ka bani shi Jamilu”.
M Jameel kuwa cike da mamaki ya ɗago Idanunsa dake jiƙe da ruwan hawaye yace.
“Ummi me kika ce?”.
Cikin Muryan kuka tace.
“Jamilu nace”.
Kallonta yayi cikin rawan murya

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads