Showing 42001 words to 45000 words out of 132567 words
Chapter 15 - BARRISTER IBRAHIM KHALIL Complete Document by Nafisa Isma'il Lawal.txt
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️ ~What'sapp Number 07065334256~
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 30*
Washe gari ƙarfe 07:15am. Saleema tagama shirin ta na zuwa school, tana shirin ɗaukan jakan ta taji cikin ta yasoma murɗa mata, dasauri tariƙe tana runtse idanun ta, lokacin ne Halwa tafito daga Toilet tana kallon ta, ganin tana riƙe da ciki taƙi jirgawa yasa tamatso kusa da ita cikin sanyin murya take tambayan ta "ko wani abun na damun ta?" Murmushi Saleema taƙaƙalo tare da girgiza mata kai, sai dai har alokacin tana riƙe da cikin nata ne, hannu tasanya taɗau jakan kafin takalle ta tace
"Ni natafi school sai na daw.."
Bata ƙarisa maganar ba tadurƙushe nan ƙasa tana faɗin
"Wayyo cikina wayyo Allana".
A ruɗe Halwa tabi ta ƙasan tana kiran sunan ta tare da tambayan ta abinda ke damunta, ganin tasoma kuka sosai tana sake riƙe cikin ta yasaka tamiƙe dasauri tafita, ɗakin Ummi tashiga dasauri, tana tsaye kuwa itama tagama shirin ta nazuwa Hospital kasancewar ita ɗin Nurse ce, taburmo ɗakin tana kiran sunan ta, Ummi kallon ta tayi tace
"Lafiya Halwa meke faruwa?"
Cikin rawan murya kamar zatayi kuka tace "Saleema ce babu lafiya".
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Ummi tafaɗa cikin tashin hankali kafin tanufo wajen ta tana faɗin
"Tana ina? Ina take?"
"Tana ɗaki".
Atare suka isa ɗakin lokacin gaba ɗaya Saleema tafita hayyacin ta sai kuka take yi, ga duk kan alamu tana jin jiki sosai, riƙo ta Ummi tayi tana kiran sunan ta tare da tambayan ta "Ina ke mata ciwo?" Duk hankalin Ummi atashe yake tarasa ma me zatayi
Halwa tace "Ummi ko za'a kira Abba akaita asibiti?".
Sai alokacin tunanin hakan ma yazo ma Ummi, tayi saurin cicciɓan ta Halwa tatayata suka fito da ita, suna fita waje Drever yazo da gudu yabuɗe musu mota suka saka ta, Ummi tashiga baya kusa da Saleema, ita kuma Halwa tashiga gaba tare da drever suka tafi, sai acikin motan Ummi ta'ari wayan drevern takira Abba tasanar masa.
Lokacin da suka isa asibitin tuni an amshe ta kasancewar ba yau suka saba zuwa ba, kuma dama tana da Doctorn da yake duba ta na musamman acikin asibitin, ana shiga da ita Abba shima ya'iso duk hankalin sa atashe, Halwa yanda taga su Ummi sun tashi hankalin su sosai itama sai taji duk ta damu, haka tazauna waje ɗaya tatakure tana tuna ɗan zaman da sukayi daga jiya zuwa yau, sosai tafahimci ita ɗin yarinya ce me tausayi da son mutane, sannan kuma ta fahimci akwai ƙauna sosai a tsakanin ta da iyayenta, take taji hawaye ya zubo mata tayi saurin saka hannu tana sharewa.
Koda aka fito da ita Abba ne yanufi wajen doctor, Ummi da Halwa kuma suka shiga ɗakin da aka kwantar da Saleema, tana kwance ne asaman gado, abun tausayi kamar ba itace lafiyan ta lau yanzu ba, amma Allah da ikon sa numfashi ma bata iya yi sai da taimakon Oxygen, Ummi hawaye tasoma zubarwa da ganin tilon ƴarta a irin wannan yanayin, takawa tayi taƙarisa wajen gadon, itama Halwa ahankali ta'isa jikin gadon tana ƙure Saleeman da idanu, zama Ummi tayi tariƙo hannun ta ɗaya wanda ba'a saka mata drip ba tana ƙare mata kallo, cikin zub da hawaye tace
"Allah Sarki Saleema, Allah yabaki lafiya, haƙiƙa kinga jarabawa a rayuwan ki, ko yaushe ne zakiji daɗi kamar kowa?"
Cikin tsananin tausayi da jin kalaman Ummin Halwa tazame nan gefen gadon tazauna, share hawayen ta Ummi tayi taɗago kanta tana kallon Halwa tace
"Tun tana ƙarama Allah yajarabce ta da ciwon zuciya, dashi tataso har girman ta, duk iya maganin da muka nema akan ta Allah be sa an dace ba, tasha baƙar wahala kamar bazata rayu ba, acikin shekaru biyu da suka wuce akayi mata aiki a ƙasan OXFORD, Allah yasa an dace, duk da haka muna gudun ɓacin ranta domin da zaran ranta ya ɓaci ciwon ta yana ƙoƙarin tashi ne, sai dai ba'a rufa watanni biyu ba tasoma ciwon ciki me tsanani, koda muka kaita asibiti aka gano tana ɗauke da ciwon hanta ne".
Cikin sheshsheƙan kuka Ummi taci gaba da faɗin
"Bamu san ya zamuyi ba idan muka rasa Saleema, muna tsananin ƙaunar ta Ni da mahaifin ta, kuma ita kenan gare mu ita kaɗai ce mallakin mu, amma kuma Allah ya ɗaura mata ciwon da muke ganin koda yaushe zamu iya rasa ta, a kullum burin mu shine musaka ta farin ciki, duk abinda take so shi muke yi, sai dai fargaban mu wanene zai ci gaba da kula mana da ita idan har takoma ƙarƙashin sa, wani namiji ne zai iya zama da ƴar mu yasaka ta farin ciki kamar yanda Likitoci suka sanar mana? yah Allah gamu gare ka, ya Allah kasauƙaƙa ma wannan baiwa taka, Allah yabaki lafiya Saleema".
Halwa batasan tana zirarar da hawaye ba sai da taji danshin su akan hannun ta, cikin rawan murya ta'amsa ma Ummi da "Ameen". Tana saka hannu tashare hawayen, Abba ne yashigo cikin ɗakin, dasauri Ummi tamiƙe tana kallon sa tace
"Abban Saleema me likitan yace? Da fatan babu abinda yasami ƴar mu? Ya Allah..". Sai tafashe da kuka tana saka hannu tarufe idanun ta
Ahankali yasaka hannun sa yana bubbuga kafaɗan ta, cikin ƙarfin hali yace
"Kiyi shiru don Allah, babu abinda zai sami ƴar mu insha Allahu, Doctor yace ciwon ta ne kawai yatashi but zata sami sauƙi very soon".
Ummi tace "Ina jin tsoro sosai Abban Saleema, ina jin tsoro kar mu rasa ta".
"Baza mu rasa ta ba Asma'u, ki dena faɗan haka kinji?"
Rarrashinta yayi sosai, sai da yaga tayi shiru ta kwantar da hankalin ta kafin yamayar da kan sa zuwa ga Halwa da har yanzu take zuban hawaye, gaba ɗaya ta takure waje ɗaya ta duƙar da kanta ƙasa, kiran sunan ta Abba yayi kana yace
"Kema ya dace kiga likita coz ɗazu kafin nafita Saleema tafaɗa min da zazzafan zazzaɓi kika kwana, kuma dama Yakamata aduba lafiyan ki da abinda ke cikin ki, be kamata abarki haka da ciwo ba, bari nafita nayi ma Doctor ɗin magana".
Daga haka Abba fita yayi ita kuma Ummi takoma tazauna tare da riƙo hannun Saleema tana kallon ta.
***** ****** ******
Ƙarfe 01:10pm. Brr. Khalil yagama Shirin sa, ya saka riga da wando white colour, sannan yaɗau rigan aikin sa tare da hulan yariƙo briafcase ɗin sa yafito, Direct wajen farar motan sa yanufa yabuɗe yashiga yazauna, ya kai wajen five minutes kafin yatada motan yanufi bakin Gate, hon yadanna Gate man yazo yabuɗe masa yaja motan ahankali yafice, sai da yadaidaita motan saman kwalta kafin yaɗau wayan sa yakira Sameer
"Hello Bro".
Daga can Sameer ya'amsa mishi da faɗin
"Kana gida ne ko ka tafi?"
"No gani a hanya, zan wuce gidan Mom".
"Ok shikenan, dama tambayan ka zanyi don mu mun riga mun isa". Sameer ɗin yafaɗi hakan
"Ok nima bazan daɗe ba, yanzu insha Allahu zan ƙariso".
Daga haka sallama sukayi ya'ajiye wayan, sannan yamayar da hankalin sa ga tuƙin sa, be ɗau lokaci ba ya'isa gidan su Kasancewar yau ɗin ya ɗan taka motan da gudu, yana yin parcking yafito yanufi cikin gidan, a Parlour yatarar da Mom tana zaune tana shan Fuirt, ƙarisawa yayi yazauna gefen ta yana riƙo hannunta yayi mata peck a bayan hannu kana yace
"Sannu da hutawa Mom".
Murmushi tasakar masa tace
"Yauwa My Son, har ka iso?"
Gyaɗa mata kai yayi yana ɗaukan Apple yasoma gutsira yana taunawa a hankali
"Masha Allah.. yanzu itama Nazeefan tashiga ɗaki taje shiryawa, nima wannan karon dani za'a je, bari inje in shirya".
"Yakamata kam, but ina Dad yake?"
"Oh Dad ɗin ka yafita tun safe akwai meating ɗin da yake dashi, but yace "idan sun gama da wuri zai same mu acan".
Nazeefa ce tafito cikin shirin ta na riga da wando farare, sai taɗaura Coffee ɗin Hijab, sosai tayi kyau kasancewarta fara, tana hango Khalil shima da fararen kayan sai wani irin farin ciki Yakamata, ko ba komi sun yi anko yau, kuma hakan yayi mata daɗi
"Ƙariso mana kin tsaya, me kike tunani?" Muryan Mom yadawo da ita hayyacin ta
Sai alokacin Khalil yakalli inda take tahowa, idanun sa kawai yaƙura mata har ta'iso wajen kanta a ƙasa tagaishe sa, amsa mata yayi yana tauna Apple ɗin dake bakin sa har yanzu kuma yaƙi kau da idanun nasa kanta
Mom tace "bari inje in shirya".
Tashi tayi tawuce ɗakinta, shima kuma Khalil dake kallon Nazeefa yayi mata alama da ido alaman tazauna gefen sa, babu musu tazauna cike da kunya, sauran tufan dake hannun sa yamiƙa mata, hakan yasaka taɗago kanta tana kallon sa don bata fahimci abinda yake nufi ba
"Ki ci". Yabata umarni yana kawar da kansa
Ahankali tasanya hannu ta'amsa takai bakin ta idanun ta akan sa, gutsira tayi tana lumshe idanuwanta cike da wani irin daɗi da yaziyarci zuciyarta, shi kuma hakan yabashi daman sake maida idanun sa kanta yana ƙare mata kallo, har sanda tabuɗe idanun ta tasauke acikin nasa, sai tayi saurin Sad da kai ƙasa tana murmusawa
kiran sunan ta yayi, bata amsa ba sai ɗago kai da tayi tana kallon sa
"Kina jina ina son in sanar dake, kikasance me juriya ga duk tambayoyin da za'a yi miki a Court, bana son ki nuna tsoro ko firgita a wajen, ina son ki amsa duk wasu tambayoyi da za'a miki batare da fargaba ko tsoro ba, Nazeefa kina dani a wajen don haka kiɗaura wa kanki ƙwarin gwiwa kinji?" Yayi maganar cikin tausasa murya still yana kallon ta
Gyaɗa masa kai tayi, kana tace "insha Allahu Yaya zan amsa duk wata tambaya batare da na nuna tsorona a fili ba".
Murmusawa yayi kawai yana kau da kan sa, lokacin ne kuma Mom ta'iso wajen tana cewa
"Kutashi Muje to na shirya"
Gaba ɗaya suka tashi suka fice, motan Khalil ɗin suka shiga yaja yafice a gidan.
[9/29/2020, 12:58 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 31*
Lokacin da suka isa, gaba ɗaya haraban court ɗin cike yake da mutane, Khalil ce musu yayi "su shiga ciki". Don haka suka fice suka bar sa cikin motan yaɗau wayan sa yana neman layin Brr. Tahir.
*20 minutes*
Shigowan Alƙali yasaka kowa yayi shiru, duk kan su tashi sukayi har sai da Alƙali yazauna kafin kowa ma yazauna, daga nan Maga-takarda yamiƙe yasoma bayani kamar haka:
"Ayau 26 September 2020 zamu ci gaba da gabatar da shari'ar Alhaji Mubarak Mai kuɗi da Nazeefa Shehu".
Sannan yamiƙa takardun ga Alƙali, shi kuma ya'amsa yana gyara glass ɗin sa yasoma dubawa, sannan yaɗago kansa yana cewa
"Lauyoyi zaku iya farawa".
Khalil ne yatashi yasoma gabatar da kan sa
"Ni sunana ```BARRISTER IBRAHIM KHALIL ABDURRA'UF.``` lauya me kare wacce takawo ƙara, tare dani kuma akwai abokan aikina..".
"Brr. Tahir .A. Tahir". Cewar Brr. Tahir kenan da shima yatashi yagabatar da sunan shi
"Tare dani Brr. Bilkisu Ahmad Sofana".
Zama sukayi gaba ɗayan su.
"Ni kuma ni ne Brr. Mahmud Sudais, lauya me kare wanda ake ƙara, tare dani akwai..".
"Brr. Shamsudden Munir".
Su ma zama sukayi, Alƙali duƙar da kansa yayi yaɗan yi rubutu tukun yaɗago kai yana kallon su, hakan yasaka Brr. Khalil yamiƙe yasoma magana
"Ya me girma me Shari'a, ina son agabatar min da Nazeefa Shehu don in mata tambayoyi".
"Kotu ta baka dama". Alƙali yafaɗi hakan yana aje Bairo ɗin hannun sa
Maga-takarda yamiƙe yace "idan akwai Nazeefa Shehu anan tafito".
Nazeefa da jikin ta yayi mugun sanyi, gaba ɗaya sai taji cikin ta yasoma rugugu ƙafanta kuma sai faman rawa suke yi don bata taɓa tsayawa cikin taron mutane ba, Mom dake kusa da ita tace
"Tashi kije mana, ki cire tsoro aran ki kinji".
Gyaɗa kai kawai tayi taɗago tana kallon mutane nan idanun ta yafaɗa akan na Khalil, kafe ta da idanu yayi ko ƙiftawa baya yi hakan yasaka tamiƙe tafara nufo shi, tana isowa wani ɗan sanda yace tashiga nan". Babu musu kuwa tashiga tatsaya kanta a ƙasa, takowa Khalil yayi ya'iso gaban ta
"Kotu zataso taji cikakken sunan ki".
Bata ɗago kai ba tace "sunana Nazeefa Shehu".
"To Nazeefa Shehu zan so in san menene alaƙan ki da wanda kika kawo ƙara, ina nufin Alh. Mubarak me kuɗi".
Sai alokacin taɗago kanta tana kallon Khalil, yayi mata alama da ido, hakan yasaka tamayar da idanun ta kan jama'a sai kuma tasauke kanta tasoma bayani
"Muna aiki ne a ƙarƙashin sa".
"Kenan kina nufin ke ƴar aikin gidan sa ne?"
Gyaɗa kanta tayi sai kuma tace "Eh".
"Ok zan so ki bama kotu taƙaitaccen labarin ki, da yanda har kuka zauna a gidan Alh. Mubarak".
"Ni bansan sanda muka soma aiki a gidan sa ba, sabida alokacin bani da wayau sosai, sai dai a sanda mahaifina yarasu nasan sanda muka koma gidan sa da zama".
Daga nan tasoma bada labari tiryan-tiryan abun da yafaru da ita a gidan, har sanda yaɗauke ta yakaita wani gida, zuwa taimakon da Khalil yayi mata har kawo iyanzu, tanayi tana kuka, sai da tagama bada labarin surutun mutane yasoma tashi, sai da Alƙali yabuga guduma kafin sukayi shiru
"Ya me girma me Shari'a iya tambayoyin da zan iya mata kenan" Khalil yafaɗi hakan kana yaje yazauna
Brr. Mahmoud ne yatashi
"Ya me girma me Shari'a ina so nayi ma Nazeefa Shehu tambayoyi".
"Kotu ta baka dama".
Ƙarisawa wajen ta yayi yana ƙare mata kallo, ita kam har yanzu kanta a ƙasa yake tana share hawaye, don haka batasan ma yanayi ba
"Malama Nazeefa zaki iya faɗa min iya adadin mutanen da suke aiki a ƙarƙashin Alh. Mubarak?"
Ɗago kanta tayi takalle sa sai tace "Eh zan iya, zamu kai mu Goma ne".
Jinjina kansa yayi kana yace "A sanda Alhj. Mubarak yafita cikin motan yabaki umarnin kijira sa, meyasaka kika fito?"
"Wani ne yace min in zo yana kira na".
"Kina nufin wani ne yajagoran ce ki zuwa ciki? Meysaka to kika bishi? Alamu sun nuna kenan ta yiwu wasu ne suka aikata miki hakan?"
"Ya me Shari'a Brr. Mahmoud yana ƙoƙarin canza mata tunani sannan yatilasta ta tafaɗa abinda bashi ne ba".
Alƙali yace "kagyara tambayoyinka Barrister Mahmoud".
"Ok ya Me Sharia".
Sannan yamayar da kallon sa gare ta yaci gaba
"Ina jinki, kin tabbatar kinga Alh. Mubarak a wannan gidan koda kika shiga?"
"Eh na gansa alokacin da suka shigo shi da wani mutum har sukayi min allura".
Jinjina kansa yayi kafin yajuyo yana kallon Alƙali yace
"Iya abinda zan iya tambayan ta kenan". Sannan yaje yazauna
Miƙewa Khalil yayi yace "zan so a gabatar min da Alh. Mubarak Me kuɗi don amsa tambayoyina".
"Kotu ta baka dama".
Fito da Alh. Mubarak akayi, wasu ƴan sanda suka tsaya bayan sa
"Alh. Mubarak shin kasan wancan yarinyan?".
Kallon Nazeefa yayi sannan yace "Eh na santa".
"Menene alaƙan ka da ita?".
"Babu wata alaƙa da nake da ita, illa ita ɗin ƴar aikin gidana ne".
Jinjina kan sa Khalil yayi kana yace
"To yanzu ka yarda da abinda tafaɗa ko har yanzu kana tantama?"
"Ni ban yarda da abinda tafaɗa ba, coz ni ba mutumin banza bane da har zan yi wannan mummunan harƙallan".
Murmushi Khalil yayi yace "kenan duk kanaso kace mana abinda ake zargin ka ba Gaskiya bane?"
"Eh ba Gaskiya bane, don Ni taimakon ta kawai nayi shine take so ta saka min da sharri".
"Kamar ya taimakon ta kayi?"
"Eh lokacin da naganta a hanya shine naɗauke ta nakaita gida, shikenan iya abinda yahaɗa ni da ita".
Khalil yace "a matsayin ka na babban mutum ka taho ka ganta a hanya, sannan kuma babu nisa da gidan ka da inda take, meysaka kayi sha'awan kaɗauke ta a mota ka ƙariso da ita gidan ka?"
"Kasan taimako ajinina yake don haka don na ɗauke ta na kawo ta gida wannan bazai saka a zarge Ni ba, sannan kuma ina tausayin ta ne saboda Mahaifiyar ta a gidana ta rasu".
"Ya me girma me Shari'a iya tambayoyin da zan masa kenan,, sannan zan so abani dama nasake yin ma Nazeefa tambayoyi". Khalil yafaɗa hakan sannan yakoma wajen zaman sa
Alƙali da yagama rubutu yaɗago kansa yace "ko lauyan da yake kare wanda ake zargi yana da abin cewa?"
Miƙe wa Brr. Mahmud yayi yace "A'a ya me Shari'a, sannan yakoma yazauna
"Kotu ta baka dama".
Tashi Khalil yayi ya'isa gaban Nazeefa yace "zan so ki sanar dani tun sanda kika taso da wayon ki kika ganki agidan Alh. Mubarak masu aiki nawa ne aka sanja agidan? Ko waɗanda kika sani iya su ne agidan har tafiyan ki?"
Cikin sanyin murya Nazeefa tace "gaskiya tun zuwana gidan har sanda natafi masu aikin gidan waɗanda aka sauya bazan iya ƙirgawa ba, amma suna da yawa sosai".
"Kenan kina nufin a gidan Alh. Mubarak ansha sauya masu aiki batare da wasu dalili ba?.."
Miƙe wa Brr. Mahmoud yayi yace "Of jection my Lord Brr. Ibrahim Khalil yana neman yaɗaura wacce yake karewa akan hanya".
"Kakula Brr. Ibrahim". Cewar Alƙali
"Nagode ya me Shari'a, ok ina jin ki, ko zaki faɗa min akwai wani laifi da kikasan suna yi ake sauya su?"
"A'a Ni bansani ba, haka kawai muke neman su mu rasa sai akawo sabbi".
"Ok zaki iya komawa kizauna".
Sannan yajuya ga alƙali yace "ya me Shari'a ina son nayi ma Malam Umaru tambayoyi".
"Kotu ta baka dama".
Maga-takarda yatashi yayi kiran sa sannan yafito
"Malam Umaru abaya na tambaye ka wasu tambayoyi, sannan nace idan da buƙatar nasake kiran ka zan sake".
Gyaɗa kansa Malam Umaru yayi
"Yauwa a lokacin da Nazeefa tafita gidan Alh. Mubarak a matsayin ka na me gadi kana ina?"
"Ina bakin Gate ɗin tazo tafita".
Kaɗa kansa Khalil yayi kana