Header Ads
Showing 87001 words to 90000 words out of 132567 words

Chapter 30 - BARRISTER IBRAHIM KHALIL Complete Document by Nafisa Isma'il Lawal.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jul 2024

1150

Ads at the middle of Article

farar shadda ɗinkin jamfa wanda yayi matuƙar masa kyau sosai, hulan ƙube yasaka wanda aka saƙa shi da farin zare sai aka sirka da blue colour, don haka yasaka cover shoes ɗin sa da Wrest watch ɗin dake ɗaure a tsintsiyan hannun sa kalan blue ɗin




Fitowar Saleema cikin ɗaki yasaka sa ɗaga kai yana kallon ta, ƙare mata kallo kawai yake yi yana taunan abincin dake bakin sa




Itama tana sanye da baƙin Material ne da ratsin fari, ɗinkin riga da skert ne wanda yazauna mata daidai, sai tayi ɗaurin ture kaga tsiya, sannan tayafa farin gyale har zuwa kanta wanda yarufe mata tulin gashin ta da yafito ta ƙasan ɗan kwalin, takalmin ƙafan ta Black Colour me ɗan tudu sannan sai jakan ta shima baƙi me matuƙar kyau da tsada, kallo ɗaya idan kayi mata zaka hango tsantsan raman da yake a fuskarta wanda yasa fuskarta yayi fayau sai dogon hancin ta da yaƙara fitowa sosai




Har taƙariso wajen yana bin ta da kallo, sai da tazauna sannan yace mata "kin yi kyau Matata".




Murmusawa tayi tana kallon sa itama, don ba ƙaramin tafiya da imanin ta yayi ba




"Kayi kyau kaima".




Murmushi kawai yayi yana ci gaba da cin abincin sa




Itama kuma wayan ta taɗauka tana ƙoƙarin sake kiran Halwa sai ga kiran ta ya shigo, peacking tayi tana karawa a kunne cikin fara'a tace "My dear Ina kika shiga na kira baki ɗauka ba?"




Daga can Halwa tayi magana cikin sanyin muryanta da koda yaushe a haka yake tace "wlh Sister muna lecture ne sai yanzu nafito afwan".




"Babu komi ai, dama Yayana ne yace in faɗa miki zamu biyo mu ɗauke ki idan mun dawo gaishe da Aamir".




Halwa tace "be da lafiya ne?"




"Eh yana fama da zazzaɓi".




"Eyya Allah Sarki Allah yaba sa lafiya".




"Amin". Saleema ta'amsa mata




Ɗan guntun dariya Halwa tayi tace "Sister kar ki manta fa ki riƙa yin practical kinsan yanzu kina da shigan ciki fa".




Saleema kallon Khalil tayi




Shima ɗin idanun sa na kanta tun sanda tasoma wayan, sai dai baya jin abinda Halwan ke ce wa




Kau da kanta tayi tana murmushi tace "sis ai na gane, nariga na ɗau komi tun sanda kike da cikin Husna, so abu me sauƙi ne a wajena nima in yi na masu cikin".




Sai kuma tasaki dariya tana faɗin "ok sai munzo ɗin ki kula min da Baby".




Ciro wayan tayi a kunnen ta tana sakawa cikin jaka




Shi dai Khalil kallon ta kawai yake yi batare da yace uffan ba, sai kuma ya ajiye spoon ɗin hannun sa yana miƙe wa yace




"Tashi muje".




Miƙe wa tayi tabi bayan sa suka fita, sai da yarufe ƙofan kafin suka nufi wajen motan yabuɗe mata gaban tashiga, sannan shima yazagaya yashiga yaja yanufi Gate yana horn




Me gadi na buɗe masa yacilla motan waje






Ko acikin motan hira suke ɗan taɓa wa, Saleema sai tambayan sa abubuwa take yi idan tagani ahanya, shi kuma yana bata amsa




Suna isa yayi horn a bakin Gate ɗin, sai da me gadi yaleƙo yaduba wanene sannan yakoma yabuɗe masa, shigar da motan yayi yay parcking kafin suka fito, atare suka jera har cikin gidan




Wannan zuwan shine zuwan Saleema na uku kenan




Suna shiga da sallama Hakima dake zaune Aamir na kan cinyan ta ta'amsa musu, sai kuma tafaɗaɗa fara'an ta tana faɗin




"Iyeee maraba da manyan baƙi, sannun ku da zuwa".




Saleema zama tayi kan kujera tana murmushi




Khalil kuma sai yanufi Hakiman yasaka hannu ya'amshi Aamir yana faɗin "a'a my Daddy Kai da zan zo in ganka akan gado ya naganka anan?"




Yaron na washe haƙora cike da murna cikin tsamin maganar sa yace "Ankul ai na waice".




"Haba dai?".




Sai yagyaɗa masa kai yana tsalle a jikin sa kafin yace "wayyayi".




Dariya gaba ɗayan su suka yi




Zama Khalil yayi yaɗaura sa a jikin sa




A lokacin ne Saleema suka gaisa da Hakima tana tambayan ta jikin Aamir ɗin




"Ai gashi nan yaji sauƙi sai rigima".




Khalil yace "wai haka Daddy kana rigima?"




Cinno baki yayi gaba yana maƙe kafaɗa yace "kayya ne Ankul".




Yanzu kam dariya sosai yaba su, har Khalil sai da yadara duk da be cika son yin dariya ba




Hakima tace "iyeee Ni nake maka kayyan?"




Sai yawaigo yana kallon ta yana ƙyafta idanu, kafin kuma yagirgiza mata kai alamun "a'a".




Murmushi Saleema tayi tace "My son Ni baka ganni bane?"




Sai yamayar da idanun sa kan ta, dasauri kuma yazamo a jikin Khalil ɗin yanufo gaban ta yana faɗin "Auncy.."




"Na'am ɗan Aunty". Tafaɗa tana ɗaukan sa cike da fara'a




Hakima miƙe wa tayi tana cewa "kunga na barku haka ban kawo muku komi ba kuma".




Khalil yace "ina Bro ne ban ji motsin sa ba?"




"Wlh ya koma Hospital yana da Patient". Hakima taba sa amsa tana ciro drinks cikin Fridge




Sai kuma tajuya tana nufan wani ɗan ƙaramin table da aka jera plates da Spoons tare da Cups akai anyi danki dashi




"Caa nake kunyi waya ai?" Tatambaye sa tana zaro plate ɗaya




"No ban Kira sa ba".




Zubo drinks ɗin tayi saman plate ɗin takawo musu, sannan takoma tazauna




"Saleema tace "Aunty Ina Abida yau ban ji ta ba?"




"Ai kam tana school bata dawo ba".




"My Daddy zo muje mu yawata". Khalil yafaɗa yana miƙe wa tsaye




Hakima kallon sa tayi tace "ya haka kuma zaka tafi baka ci komi ba?"




Ɗaukan Aamir yayi yana bata amsa da "A ƙoshe nake ai, bari mu fita waje".








Tunda yafice kuma sai sukai ta hira da Saleema.




*****


Lokacin da suka dawo tare da Sameer suka shigo gidan




Khalil nan yace "Saleema tatashi su tafi".




Hakima sai tsiya take mishi wai yanzu suka zo har zasu tafi baza su kai musu dare ba




Shi kuwa be ce komi ba




Saleeman ce take ta dariya tana faɗin "zasu biya ɗauko Halwa ne".




Sannan ne fa Hakima tayi shiru da bakin ta




Har waje suka rako su suka hau mota suka bar gidan




A lokacin ne Khalil yaƙyalla idanu yaga saƙon da Mom tabashi yaba Saleeman, shaf ya manta shiyasa yabar shi cikin motan, don haka ya ɗauka yamiƙa mata yana faɗin




"Gashi in ji Mom ɗazu na manta ban Baki ba".




Amsa tayi tana kallon ledan, sai kuma tabuɗe jaka tasaka tana cewa




"Allah Sarki Mom ɗina, Allah yasaka da alheri, zan kira ta in mata godiya".




Shi dai be ce komi ba illa murza sitiyarin da yake yi, ahaka har suka shiga cikin makarantan




Saleema takira ta awaya tasanar da ita inda sukai parcking motan




Don haka babu ɓata lokaci Halwa tafito cikin holl ɗin da suka gama karatu ta tunkari inda zata same su, tana sanye da niƙab da tasaka yanzu da zata fito har ta'isa wajen motan tayi Nocking




Da farko da suka kalle ta basu gane ta ba, sai kuma Saleema tasaka dariya tana zuge glass ɗin tace




"Kaii sis Wai dama kina saka niƙab ne idan zaki zo?"




Murmushi Halwa tayi wanda basu san ma tana yi ba, idanun ta tasauke akan Khalil da shima yazuba mata nashi, tayi saurin lumshe wa tana buɗe su sannan tabuɗe bayan tashiga tana faɗin




"Saboda ƴan saka idanu ne shiyasa nake saka wa, sannu Yaya".




Taƙarishe maganar tana rufo ƙofan




Jan motan yayi yana amsa mata da "yauwa, ya makarantan?"




"Alhmadulillah". Tace ataƙaice




Saleema tace "gaskiya ne Sister kuma yayi miki kyau fa wlh".




Cire niƙab ɗin Halwa tayi tana saka wa ajaka tace "ko Ƴar uwa?"




"Eh mana ki tambayi Yaya Khalil".




Kallon gefen sa Halwa tayi sai suka haɗa idanu ta mirror, tayi saurin ɗauke kanta batare da tace uffan ba




Shi kam be ɗauke idanun sa akan ta ba, kallon fuskarta kawai yake yi, a ransa kuma sosai yaji daɗin ganin ta da niƙab ɗin




Saleema ce kaɗai take ta faman surutun ta Halwa na bata amsa a taƙaice




Har yanzu bata iya sakin jiki a gaban sa, sabida yanda take ji a game dashi duk da kuwa sun ɗan saba ba kamar da ba.
[12/2/2020, 3:13 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️




*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_




*بسم الله الرحمن الرحيم*






*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```


*JIKAR LAWALI CE*✍️


*Wattpad: UmmuDahirah*👈




*\F.W.A📚/*


```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._


*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._




*BOOK TWO*




.


_______________________________


*CHAPTER Twelve*


________🎓 Koda suka isa gida Halwa wanka tasoma yi tasauya kaya zuwa riga da skert na kanti me ruwan bula, sannan tafito tasami Saleema a kichen tana ɗaura musu abincin dare




Fita tayi tanufi kan dainning taɗibo abinci tasake dawowa cikin kichen ɗin tazauna akan Kujeran Robber dake ajiye gaban Freezer, Saleema na girki tana taya ta hira.




Khalil kuwa ɗakin sa yawuce kai tsaye, cire kayan jikin sa yayi yasauya da farar jallabiya da gajeren wando sannan yafito parlour, Kallo yakunna yaɗau Remote yana sauya Channels, ya saka wannan yasaka wancan har sanda Halwa tagama cin abincin tafito don taƙara wani




Tana fitowa suka haɗa ido dashi, ɗauke kai tayi tanufi kan dainning, tana cikin zuba abincin tatsinkayi muryan sa yana cewa




"Maman Husna kawo min ruwa".




Lumshe idanun ta tayi tana sauraron bugun zuciyarta dake fita dasauri-sauri, ware idanun tayi kansa wanda shima yazuba mata nashi idanun, dasauri taɗauke kanta tana nufan Fridge tabuɗe taciro masa sannan tahaɗo da cup tanufo sa, akan Centre table ta'ajiye masa tajuya da ninyan tafiya, batayi aune ba sabida yanda duk natsuwar ta yabar jikin ta sai ji tayi tay karo da Centre table ɗin ta tafi yarab ta faɗa kansa, sai gata ɗare-ɗare a jikin sa




Kunya tsoro duk su suka taru mata lokaci ɗaya wanda hakan yasaka takasa tashi bare taɗago kai takalle sa, in banda gudun da zuciyarta ya ƙara kamar yafaso ƙirjin ta




Shi kuwa abin ma dariya yaba sa, haka kawai yatsinci kansa cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa, sai kawai yazuba mata idanu yana murmushi me sauti




Lokacin ne kuma tasamu ƙwarin jikin da har ta'iya yunƙurin tashi, har a time ɗin bata iya kallon sa ba illa miƙe wa da tayi tana shirin barin wajen




"Maman Husna halan baki gani ne kike son ki karya Ni?" Yafaɗa still yana murmushi




Ɗago kai tayi takalle shi, sai kuma taɗauke kai tana murmushi bata iya cewa komi ba tanufi hanyan kichen dasauri




Tana shiga Saleema ta ɗan kallo ta kafin tamaida kanta taci gaba da aikin ta




Zama Halwa tayi tana sauke ajiyan zuciya har da dafe ƙirjin ta tare da lumshe idanu




"Me yafaru ne Sister wannan murmushi haka?" Tatsinkayi muryan Saleema tana faɗin hakan




Dasauri tabuɗe idanun ta suka haɗa ido da Saleema wacce tajuyo gaba ɗaya a yanzu tana kallon ta




"Babu komi". Halwa taba ta amsa cike da sanyin muryan ta




Sai kuma tamiƙe tana nufo ta




"Da me zan taya ki?"




Saleema tace "ai na gama, sai dai ki kwashe min zuwa dainning".




"Ok".






Tare suka fito kichen ɗin har a lokacin kuma Khalil na zaune a Parlour yana kallon sa




Kallo ɗaya Halwa tayi masa taɗauke kai ganin sun haɗa idanu




Kan dainning ɗin suka kai suka jera, sannan Saleema tanufi parlour'n tazauna gefen sa




Halwa kuma sai tayi ɗakin ta dasauri




"Sis Ina Zaki kuma?".




Halwa da har ta buɗe ƙofan zata shiga tatsinkayi muryan Saleeman, sai tajuyo tana kallon ta tace "kawai zan ɗan kwanta ne kafin a kira sallah".




"Kwanciya kuma yanzu? Ki dawo ki zauna anan zuwa anjima kya shiga ki kwanta".




Gaba ɗaya kallon sa suka yi wanda kamar ba shine yayi maganan ba, don hankalin sa na kan t.v yana sake sauya Channel




Takowa tayi tadawo tazauna can gefen su




Su biyu kaɗai suke hiran su yayinda Halwa tamaida hankalin ta kan t.v amma tana sauraron su, idan Saleema tasako ta kuma tana bata amsa, har sanda aka kira sallah Khalil yatashi yashige ɗakin sa




Su ma tashin suka yi don gabatar da farali.










****** ******** *******


Tunda Zainab tayanke shawaran fid da miji ko ta samu sauƙin nacin Nura hakan kuwa tayi, akwai wani saurayi Aliyu da suke makaranta tare, anguwan su ɗaya dashi sai dai ba layin su ɗaya ba, to shi yana degree ɗin sa ne a school ɗin, suna yawan haɗuwa a makarantan shiyasaka suke ɗan gaisawa har idan Zainab tana da assignment ko wani abinda bata gane ba kai tsaye wajen sa take zuwa, tunda dama sun san juna sosai a anguwan su magana ce kaɗai be haɗa su




Wannan dalilin ne yasaka shaƙuwa yasoma shiga tsakanin su, har dai Aliyu yazurma son ta lokaci ɗaya, ahankali-ahankali dai bayan shaƙuwar su ta sake nisa sai yasanar mata da sirrin zuciyar sa




Zainab bata wani ja aji ba ta amince don dama itama tana son sa aranta, komi nasa yayi mata, bare kuma dama neman saurayi take yi tayi aure ta huta.




Aliyu na zuwa wajen ta, a school kuma koda yaushe suna tare hakan yaƙara ƙarfafa soyayyar su da shaƙuwar su, kuma a gidan su babu wanda be san Aliyu ba




Umma ko kaɗan hakan be mata daɗi ba tunda Aliyu ko ƙwaƙƙwaran sana'a bashi dashi, iyakan dai karatun sa yasaka agaba sai kuma ɗan jiran shago da yake yi, sosai ran Umma yasake ɓaci musamman da tasan ko shi wanene don haka tasoma rura ma Zainab wuta dole tarabu dashi takoma ma Nura tunda shi yana da sana'ar sa




Zainab ita kuma ta nuna mata sam ita Aliyu take ƙauna, hakan yajawo har sai da Umma tayi mata tsinannen duka




Ba ƙaramin ɓaci ran Abba yayi ba, a ranan shima sai da yayi kamar zai duke Umma akan abinda tayi, wannan dalilin ne yasaka yanemi Aliyu yabashi damar yaturo idan har zai iya auren Zainab




Duk da Aliyu be da wani abun yi sosai wanda ke kawo masa kuɗi, sai dai yana da ƴan uwa waɗanda ciki ɗaya suka fito su ne kuma suke taimaka masa a fannin karatun sa sabida suna da hali sosai, jiran shagon da yake yi yana yi ne kawai don rage zaman banza




Koda Abba yayi masa zancen yaturo hakan ya faranta masa, kai tsaye sai yanufi gidan Babban Yayan su yasanar masa, dayike su ma suna son yayi aure sai Yayan nasa yace "yatafi zai neme sa idan suka yi shawara da Umman su".




A cikin sati ɗaya har an nema wa Aliyu auren Zainab kuma Abba ya basu ita, sai aka saka ranan nan da wata uku bayan ta gama final exams ɗin ta da sati biyu, dama ƴan uwan sa zasu yi masa komi na bikin don haka basu wani damu ba koda aka saka ranan babu yawa.






Fannin Nura kuwa yayi baƙin cikin hakan sosai, ya tabbata ya rasa Zainab bazai taɓa samun ta ba tunda yasan bata son sa, amma kuma har yanzu yaƙi ba ma zuciyar sa haƙuri be dena zuwa wajen ta ba. Sai mu ce Allah yakyauta maka.












.








_kuyi haƙuri da wannan babu yawa._




_sai kun ji Ni a next page._






_kar ku manta plz Vote and share 🙏_
[12/2/2020, 3:31 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️




*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_




*بسم الله الرحمن الرحيم*






*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```


*JIKAR LAWALI CE*✍️


*Wattpad: UmmuDahirah*👈




*\F.W.A📚/*


```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._


*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._




*BOOK TWO*




.


_______________________________


*CHAPTER Thirteen*


________🎓 *AFTER THREE MONTHS*


"Wai jikin ne Sister?" Halwa tafaɗa lokacin da take zama gefen gadon




Numfashi Saleema taja tana sake jan bargon da tarufe jikin ta dashi a lokaci ɗaya tana bata amsa




"Wlh kuwa sis, gaba ɗaya bana jin daɗi yau, dama tunda naga a kwana biyun nan jikina ya soma kumbura na san akwai matsala".




Cike da tausayin ta Halwa tace "eyya ko dai in Kira Ya Khalil mu je asibiti, don bana son wlh ciwon ki yatashi da tsananin nan".




Ɗan guntun murmushi Saleema tasaki tana kallon ta cike da nuna jarumta tace "kar ki damu babu abinda zai faru, bari dai insha magani na sai in kwanta in ɗan samu barci insha Allahu zan ji daɗi domin barcin nake buƙata a yanzu".




"Tom bari in ɗauko miki Maganin".




Dasauri tamiƙe tazagaya side ɗin gadon tabuɗe drower taɗauko mata, tanufi Fridge tahaɗo mata da ruwa sannan tadawo tazauna




"Tashi kisha". Tayi maganar tana ajiye goran ruwan da maganin ajikin ta




Sai da tataimaka mata tatashi zaune kafin tabuɗe mata maganin taba ta tasha ta'ajiye ruwan a ƙasa




"Ki ɗan tsaya yanarke tukun sai ki kwanta".




Murmushi Saleema tayi tace "to Nagode sis, Ina jin daɗin kula dani da kike yi Allah yabiya ki da mafifin cin alkhairin sa.."




"Ya isa don Allah duk abinda zan miki be kai kwatankwacin taimakon da kikai min ba, kar ki damu sister insha Allahu Allah zai yaye miki duk wani damuwar ki, Allah maji roƙon bawan sa ne kuma yana jin mu".




Cikin jindaɗin maganar ta Saleema tace "Sister to ki je ki ƙarisa assignment ɗin naki mana ko kin gama ne?"




Gajeren tsaki Halwa taja tana shafa gefen fuskarta tace "wlh na kasa ƴar uwa, duk wani searching da zan yi ban samu abinda nake so ba, na dai ƙoƙarta nayi biyu a cikin biyar ɗin, kuma gashi Lecturer ɗin nan yace mana shine Test ɗin mu na rasa ya zan yi".




Saleema tace "to ki kai ma Yaya Barrister mana zai taimaka miki, tun farko ma na manta wlh da shi kika kai ma wa".




Halwa dai batace komi ba illa jinjina zancen da take yi aranta, ba wai kai mishin bane bata so kusancin su ne ko kaɗan bata so..




"Kin yi shiru Sister?" Saleema takatse mata tunanin ta




"To". Kaɗai ta'amsa mata dashi kafin tamiƙe tanufi kan kujera taɗau Hijabin ta tana ƙoƙarin saka wa




"Wlh Sister ban taɓa ganin wanda ciki yake masa kyau ba kamar ke, Ni har na fi ganin kyan wannan cikin akan wancan, kinga yanda kika yi kuwa?" Cewar Saleema tana dariya ahankali




Itama Halwan dariyan tayi tana ƙarisa saka Hijabin sannan taɗau Peppers ɗin ta tana kallon Saleeman




"Ke dai Sister kin fiye saka idanu, ina wani kyau anan kina ganin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads