Showing 69001 words to 72000 words out of 132567 words
Chapter 24 - BARRISTER IBRAHIM KHALIL Complete Document by Nafisa Isma'il Lawal.txt
tunda tahaife ta ko ɗaukan ta idan ba ya zama dole bane to ko kallo bata ishe ta ba, baza ka taɓa tunanin itace uwarta ba
Basu sake magana ba har sanda suka gama cin abincin suka koma parlour, Hira suka ɓarke dashi cike da nishaɗi, sai da aka kira sallah kafin Saleema tashige ɗaki don yin Sallah, ita kuma Halwa tadasa Kallo kasancewar bata sallah
Khalil ne yaturo ƙofan da sallama a bakin sa hakan yasa Halwa ɗago idanuwan ta tasauke acikin nashi idanun wanda yayi dai-dai da yankewar gaban su a lokaci ɗaya
Kallon kallo suke ma juna cike da wani irin yanayi me wuyan fassara
Khalil sandarewa yayi a tsaye a wajen kakkaifan idanun sa akanta, ganin abun yake yi tamkar a mafarki yau yarinyan da tahana zuciyarsa sukuni tsawon lokaci itace agaban sa a kuma cikin gidan sa, kullum cikin tunanin ta a barci kuma mafarkin ta
Janye idanunta Halwa tayi daga kallon sa, ko kaɗan kuma bata gane sa ba sai dai idanun sa sun mata kama da wanda tataɓa gani
Be jirga daga wajen da yake ba illa zuba mata idanuwa kawai yayi kuma ya kasa ɗauke wa
Fitowar Saleema daga ɗakin ta tahange sa tsaye ya kafe Halwa da kanta ke ƙasa da kallo, irin kallon da yake mata shi yasaka gabanta yayanke yafaɗi, take taji wani abu ya soke ta a ƙahon zuciya da yasaka tayi saurin ɗaura hannunta a ƙirjin ta tana runtse idanu
Halwa da har yanzu take jin idanuwan sa masu tsananin kaifi suna yawo ajikin ta, dai-dai tana ɗago kanta tahangi Saleema tsaye dafe da ƙirji, dasauri tamiƙe tana faɗin "Sis lafiya kuwa?"
Buɗe idanuwan ta tayi tana kallon ta sai kuma tamaida ga Khalil da maganar Halwan shima yadawo dashi hayyacin sa, haɗa idanuwan da sukayi yasaka shi sakar mata kyakkyawar murmushin sa yana takowa cikin parlour'n
Wannan murmushin da yayi mata shi yasaka taji sanyi aranta, takalli Halwa dake nufo ta a yanzu ɗin taƙirƙiro murmushi tace
"Babu komi".
"Anya kuwa? Ko dai wani abun ke damun ki?" Halwa tasake tambayar ta cikin damuwa don bata yarda babu komi ɗin ba
Still Saleema tana murmushi tariƙo hannun Halwan suka nufi kan kujera tana faɗin
"Yaya sannu da zuwa".
Idanun sa akan su ya'amsa mata cike da kulawa
Zuciyar Halwa har alokacin bugawa yake yi kuma ta rasa dalili, har a time ɗin kuma bata iya ɗago kai ta sake kallon sa ba, zama kawai tayi tana sake mayar da idanun ta kan t.v
Cike da son kawar da abinda ke cikin zuciyarsa yayi hanyan ɗakin sa cikin takunsa me burgewa da cikan mazan taka
"Yaya baku gaisa da Maman Husna ba". Saleema tafaɗi hakan tana kallon bayan sa
Cakk yatsaya zuciyar sa na wani irin bugawa dasauri-dasauri
"Ina yini". Cewar Halwa itama da taɗago kanta tana kallon bayan nasa
Runtse idanun sa yayi da ƙarfi yana sake danne abun da yake ji, cikin wani irin murya da dole kagane akwai wata matsala ya'amsa mata da "lafiya". Sannan yawuce ciki da sassarfa
Basu kawo komi akai ba illa mayar da hankalin su ga juna da sukayi
Cikin murmushi Halwa tace "baza ki bi bayan sa bane?"
Hararan wasa Saleema tasakar mata tana murmushi da son kawar da abinda take ji cikin zuciyarta, domin kallon da Khalil yayi wa Halwa sosai yatsaya mata arai har tana son dasa zargi cikin zuciyarta, bata iya cewa komi ba sai murmushin da take faman yi
Matsowa Halwa tayi taraɗa mata magana a kunne, dariya suka fashe dashi suna tafawa.
____________________
Cike da sanyin jiki yaƙarisa kan gadon sa yazube yana ɗaura kansa akan pilow, sosai zuciyarsa yake faman bugawa kamar zai faso ƙirjin sa ba don komi ba sai maganar da Saleema tafaɗa masa Halwa itace Mamar Husna, numfashi yasoma fesarwa yana son dai-dai ta nutsuwar sa dake son gushe wa, hannun sa yaɗaura akansa yariƙe yana lumshe idanuwan sa sabida jin yana faman sara masa, baya son ko kaɗan zargin sa yazama gaskiya
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.."
Abinda yake ta faman maimaita wa kenan har yasoma jin nutsuwarsa na dawo masa tare da sassaucin bugun zuciyar sa
Dantsen hannun sa yaɗaura akan kyakykyawar face ɗin sa yayi shiru kamar ruwa ya cinye sa
Har Saleema tashigo be motsa ba
Maganar abinci tayi masa amma sai yagirgiza mata kai alaman bazai ci ba
Shiru tayi kamar zata yi masa magana sai kuma takasa tajuya tafita
Parlour takoma sukaci gaba da hiran su da Halwa, har sanda tajiyo kukan Husna dake barci a ɗakin ta, zuwa tayi taɗauko ta tadawo parlour'n tahaɗa mata abincin ta tasoma bata
Khalil har akayi sallan la'asar be tashi daga inda yake shingiɗe ba, abun duniya duk yayi masa yawa, sai daga baya daƙyar yamiƙe yasoma cire kayan jikin sa, zuwa yanzu kuma kansa sosai yake mishi ciwo kamar zai fashe
Toilet yashiga yayi wanka yaɗauro alwala yafito, jallabiya yazura yafito parlour'n fuskarsa duk babu walwala, kallo ɗaya yayi musu yaɗauke kansa saboda haɗa idanun da sukayi da Halwa
Itama dai sauke kanta ƙasa tayi tana me mamakin kanta da wannan mutumin, shiru tayi tana sauraron bugun zuciyarta wanda haɗa idanun da sukayi yahaddasa mata hakan
Miƙewa Saleeema tayi da Husna a hannun ta tace "bari inyi sallah sister".
"Ok muje nima in shirya tafiya zanyi". Halwan tafaɗa tana tashi tsaye
Hararan ta Saleema tayi tace "tun yanzu? Ai ba haka mukayi dake ba".
Dariya kawai Halwa tayi tazo tawuce ta tayi gaba
Itama tabi bayan ta tana ƙorafi
Suna shiga ɗakin Saleema tashimfiɗe Husna da takoma barcin ta, ita tasoma shiga Toilet ɗin taɗauro alwala kafin tafito Halwa tashiga
Bata jima ba tafito tazauna akan drowan Gadon taɗau wayan ta tana neman layin Drever, sai dai wayan tasa akashe ne, tsaki taja tamiƙe tanufi kan stool dake gaban mirror tazauna tasoma shafa Powder tana gyara fuskarta
Tana nan zaune har Saleema ta'idar da sallan ta tajuyo tana kallon ta tace
"Wai don Allah dagaske yanzu zaki tafi? Please ki bari sai dare mana".
Murmushi Halwa tayi tana kallonta ta cikin mirror tace "kina son gobe in ƙi zuwa miki kenan?"
Girgiza kanta Saleema tayi itama idanun ta akanta, sai kuma tace "amma dagaske zaki zo ɗin gobe?"
Cike da son riƙe dariyan ta dake son kufce wa tace "sosai ma sister gobe zan dawo shiyasa zan tafi yau da wuri".
Gyaɗa kanta tayi sannan tamiƙe tana cire Hijabin ta tace "to shikenan na yarda ki tafi amma goben ki zo da wuri".
Halwa bata iya bata amsa ba saboda dariya da yacika cikin ta sosai ƙiris yarage tasaki dariyan, ɗaga mata kai tayi tana sauke kanta ƙasa tasoma dariyan ta yanda baza ta ganta ba
Saleema kuwa kan gado tanufa batare da ta kula da ita ba, sai zayyano mata saƙon gaisuwa da zata kai ma su Ummi da Abba take yi
Ɗago da kanta Halwa tayi tajuyo gaba ɗaya tana kallon Saleema cike da murmushin da yabayyana haƙoran ta tace "amma fa na kira drever wayan sa be shiga ba kuma gashi ban fito da kuɗi ba".
Saleema tace "to nima ai bani da kuɗi gaskiya, amma bari in duba ko Yaya Barrister ya dawo sai ince yayi ma Drever magana yakai ki".
Gyaɗa kanta kawai Halwa tayi
Ita kuma tatashi tafita tashiga ɗakin Khalil
Yana tsaye ne agaban mirror ya sauya kayan jikin sa zuwa ƙananan kaya, yana fece suman sa da Cumb tashigo
Takowa tayi tazo inda yake tana kallon sa cike da ƙauna, sosai yayi mata mugun kyau har ta manta abinda yashigo da ita ta shagala wajen kallon sa
Ajiye cumb ɗin yayi yajuyo yana kallon ta, tayi saurin duƙar da kanta cike da kunyan kamata da yayi tana kallon sa
Be ce komi ba yamatsa gaban gadon sa yaɗau Wrest watch ɗin sa yana ɗaurawa a tsintsiyan hannun sa
"Uhm dama Halwa ce zata tafi gida shine nace ko zakayi ma drever magana yakai ta?". Tayi maganar a hankali tana kallon sa
Tsayar da abinda yake yi yayi yana juyowa yakalle ta, ganin sun haɗa idanu sai yagyaɗa mata kansa tare da ci gaba da ɗaure Wrest watch ɗin
Murmushi tayi tajuya zata fice, har ta kai bakin ƙofa tajiyo muryan sa
"Tafito sai in sauke ta".
Kallon sa tayi shi kuma yaɗauke kai yana takawa yanufi wajen takalman sa
Cikin sanyin murya ta'amsa mishi sannan tafice.
[11/11/2020, 7:49 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Two*
________🎓Da murmushi a face ɗin ta tashigo cikin ɗakin, tana kallon Halwa wacce itama tazuba mata nata idanun tace
"Sis ki shirya Yaya Barrister zai kai ki".
Halwa wani kallo tayi mata sai dai batace komi ba tamiƙe taɗauki Veil ɗin ta tayi Rolling ɗin sa akanta, sai taɗau HangBag ɗinta tarataya, wayan ta a hannun ta suka fito tare da Saleeman, waje suka fice a tunanin su zasu ganshi sai dai babu shi be fito ba, a compound ɗin gidan suka tsaya suna taɓa hira har sanda sassanyan turaren sa yakawo ma hancin su cafka
Saleema kallon kyakykyawar Mijin nata tayi cike da tsananin ƙaunar sa
Ita kuwa Halwa tunda tayi masa kallo ɗaya taɗauke kanta
Zuwa yayi yawuce su yanufi wajen Farar motan sa yabuɗe yashiga
Su ma takowa sukayi har wajen motan, Saleema tabuɗe mata ƙofan tashiga tarufe mata
Tana nan tsaye har suka fice a gidan kafin taja numfashi ahankali takoma cikin gidan
Shiru cikin motan babu me motsin kirki ahaka sukai ta tafiya
Halwa ma duƙar da kanta tayi ƙasa tana faman juya wayan ta
Yayinda Khalil yake tuƙi amma hankalin sa gaba ɗaya yana kanta, so yake yi yacire duk wani abu dake cikin ransa a game da ita tunda yasan ita ɗin mallakin wani ne
Tafiya suke yi sosai babu me magana cikin su
"Ina ne gidan naki?"
Tatsinkayi sassanyan muryan sa me tsananin daɗi a kunnen me sauraro, ɗago kai tayi takalle sa kamar me tunani sai kuma taɗauke kanta tana faman maimaita maganar nasa aranta har sanda tafahimta sannan tabashi amsa
"Sabon layi".
Kallon ta yayi kamar zai yi magana sai kuma yafasa, ya san cewa Sabon Layi ne gidan su Saleema, to amma taya ita zatace masa anan take? Sai kuma yayi tunanin maybe itama a anguwan take aure
Be sake magana ba har sanda yashigo cikin anguwan, yana jiran yaji ta nuna masa hanya ko wani gidan but shiru hakan yasaka yaci gaba da tafiya batare da ya sake tambayan ta ba
Sai da aka kawo dai-dai gidan su Saleema taga yana shirin wuce wa, takalle sa tace "Nan ne fa".
Tsai da motan yayi kafin yayi Rivers yakoma baya yadanna horn me gadi yaleƙo sannan yabuɗe musu, tura hancin motan yayi cikin gidan sannan yayi parcking
Tana ganin ya tsaya tabuɗe motan sannan taɗan juyo takalle sa suka haɗa idanu tayi saurin janye nata cike da tsananin faɗuwar gaba
"Na gode". Tafaɗa ahankali kafin tafice dasauri tarufe masa ƙofan tatafi
Har tashige yana kallon ta cike da mamaki aransa, yana da tarin tambayayo aran sa sai dai be san wanene zai amsa masa ba
Yasan da cewa Saleema ita kaɗai iyayen ta suka haifa bare yayi tunanin ƴar uwanta ce, sannan ma basu kama ko kaɗan, sai dai yana tunanin ko dangin ta ne
Motan sa yaja yabar gidan yanufi inda zai je.
*____________________*
Sallama tayi tashigo gidan agajiye
Umma ta'amsa mata tana kallon ta
Zuwa tayi tazauna akan tabarman da Umman take zaune
"Kin dawo?"
Gyaɗa mata kanta tayi tana me zame jakan ta kafin tace "sannu da gida Umma".
"Yauwa Zainab da alamun dai yau kinsha wahala tunda naga kina langaɓewar nan?"
Zainab tace "uhm umma ai ba'a magana, wahala kam akwai ta, ko abinci yau ban iya ci ba tun safen nan wlh lectures yayi zafi".
Sake kallon ta dakyau Umma tayi tace "sai kika zauna haka babu abinda kika ci? To ai dama Dole kisha wahala, ki tashi kije ɗakina ki ɗauko abincin ki".
Miƙewa Zainab tayi don dama sosai cikin nata yake ƙwaƙulan ta, shiga ɗakin tayi taɗauko abincin tafito tazauna inda tatashi
Tana ci suna hira kuma duk na hiran makarantan ne
"Ni wlh dama zaki haƙura da karatun nan haka nan abu yaƙi ci yaƙi cinye wa, memakon ki samu miji kiyi aure sai ƙara karatun ma kike yi shi kuma ba me ƙare wa ba".
Kumburo fuska Zainab tayi tace "Umma kema kinsan karatu nake so a yanzu, ban tashi yin aure ba shiyasa ma bana kula kowa a yanzu ɗin".
"To wa yace miki karatu na hana aure ne? Tunda gashi kin soma ai abu me sauƙi ne Mijin naki yabar ki kici gaba, shiyasa wlh nake miki sha'awar auren Nura tunda shi yayi karatun kuma bana da haufi akan zai barki kiyi karatun ki".
Tashi Zainab tayi tsam bayan da Umman nata tagama zayyano maganan, batace komi ba tashige ɗakin ta tafaɗa kan gado
Umma kuwa da tabi ta da kallo baki sake tayi ƙwafa tana faɗin "wawiya kawai wacce batasan me yake mata ciwo ba".
Lumshe idanun ta Zainab tayi wasu hawaye masu zafi suka sauko mata a kunci
Ta rasa meyasaka Umman ta take magana akan Nura, meyasa Ummanta take son auren ta da Nura, taƙi tagane cewa ita baza ta iya auren sa ba, baza ta taɓa auren saurayin da Halwa take mutuwar son sa ba koda kuwa ita tana son shi".
Hannu tasaka tana share hawayen ta tare da yin matashi da duk ka hannayen ta
Tana jin sanda Abban ta yashigo Umma take ta rattabo masa bayani, har da faɗin "wlh Malam tun wuri ayi wa tufkan hanci idan har ba so kake yi Zainab ta tsofe agida babu mashinshini ba, ga yaro son kowa ya fito yana son ta amma ita ƙiri-ƙiri ta shafe wa idanun ta toka taƙi shi akan dalilin ta na banza dana hofi, to Ni gaskiya bazan iya zuba idanu har sai sanda tagama wannan ƙaddararren makarantan ba, kawai kace ma Nura yaturo idan yaso sai taƙarisa can agidan sa yafi".
Murmushi Abba yayi yace "Jummai Ni wannan cece kucen da kike yi banga amfanin sa ba, tunda yarinyan nan ta nuna bata son yaron nan menene na son sai ta aure shi? Duk a ƴaƴana babu wacce nayi mata auren dole bare kuma kan Autana, kibari idan har sun dai-dai ta kansu falillahil hamdu amma Ni bazan mata auren dole ba".
Shiru Umma tayi tana gyaɗa kanta cike da takaici, ba wai don tarasa abun faɗa bane sai dai don haushin Abban da yake goya wa Zainab baya, idan da ya amince ita ana ta da tuni anyi an gama, in taje can sai su daidai ta.
Miƙe wa Abba yayi be sake cewa komi ba yaɗau buta yashiga bayi don taɗauro alwalan magariba da har an soma kira
Ita kuwa Zainab sanyi taji cikin ranta ko banza tasan Abba bazai bari ayi mata aure ba sai da yardan ta, kuma idan har itace zata amince da Nura kafin ayi musu aure to baza ta taɓa amincewa ba har abada..
*______________________*
Turo ƙofan tayi tashigo da sallama a bakin ta
Khalil dake zaune gefen gadon sa yana faman aiki acikin Lapton yaɗago yayi mata kallo ɗaya sannan yamayar da kansa yana amsa mata sallaman
Takowa tayi zuwa wajen gadon tashimfiɗa Husna akai sannan itama tazauna tana kallon sa
Shima alokacin yasake ɗago kansa yakalle ta sannan yamaida idanun sa kan Husna, tsawon sokonni biyar yana faman kallon ta kafin yace
"Wai ina Mahaifin yarinyan nan?". Yaƙarike maganar yana aza idanun sa kan Saleema
Shiru tayi tana sad da kanta ƙasa, ba ta jin zata iya sanar masa haƙiƙanin gaskiya kuma bata san me zata ce masa ba a yanzu
Ci gaba da danna Lapton ɗin sa yayi be sake ce mata komi ba, sai can kamar mintuna biyar yasake jeho mata tambayan
"Ina Mahaifin yarinyan nan nace?"
Yanda yayi maganar ne a kausashe yasa hantan cikin ta ya yamutse, batasan sanda bakin ta yafurta "sun rabu ba".
Cakk yatsaya da abinda yake yi yajuyo yana kallon ta
Itama ɗin shi take kallo cike da tunanin meyasaka yake son sanin Mahaifin Husnan bayan ada be taɓa tambayan ta ba?
Kau da kansa yayi yaci gaba da aikin sa
Ita kuma ajiyan zuciya tasauke sannan tagyara takwanta tana tunani aranta
"Shin meyasa nake son kawo zargi ne acikin auren mu? Meyasa zuciyata take son kawo min abinda zai hargitsa min rayuwa? Shin menene abun zargi anan?"
Kwanciyar ta tagyara tana kallon sa, ahankali kuma tafurta "Allah na tuba Allah ka cire min zargi araina".
Aikin yake yi amma maganar Saleema ke kai kawo cikin ransa, duk da yaji sanyi ta wani gefe nasa amma kuma yasan cewa mafarkin sa bazai taɓa zama gaske ba
A haƙiƙanin gaskiya zuciyar sa ta kamu da ƙaunar Halwa tun ranan farko da yaganta, amma taya zai iya mallakan ta bayan ita ɗin ƴar uwa ce ga matar sa?
Har Saleema tayi barci yana nan zaune yana latsa Lapton ɗin sa duk da kuwa tunani ne cinkushe aran sa wanda yahana sa jindaɗin aikin
Daga ƙarshe ma tashi yayi yashige toilet yaɗauro alwala, fitowa yayi yazauna a bakin gadon yana kallon Saleema dake maƙale da Husna, sosai yake mamakin yanda take ƙaunar yarinyan
Ya jima a zaune awajen yana kallon su, amma azahiri tunani ne aransa wanda har yasoma haddasa masa ciwon kai
Kwanciya yayi yaci gaba da tunanin, yafi mintuna 20 kafin yamiƙe yatashi yasoma jero nafilfilu ganin hakan shine kaɗai mafita a gare shi, domin ko kaɗan ayau ɗin baya jin barci zai iya ɗaukar sa.
.
*Plz Share and Vote*
_More Comments more typing._
[11/13/2020, 11:10 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._