Showing 102001 words to 105000 words out of 132567 words
Chapter 35 - BARRISTER IBRAHIM KHALIL Complete Document by Nafisa Isma'il Lawal.txt
butulu ce, ta ɗau alwashi da dama aranta wanda babu wanda yasan hakan sai ita kanta.
Fannin su Mom sun haɗo akwati guda biyar maƙare da kaya, komi sai son barka, duk da a ƙurarren lokaci aka yi komi amma kasancewar da kuɗi komi ya tafi yanda suke so.
Ranan Friday Dad da kansa yakai ma Khalil kayan da zai saka, sun matsa sai da aka sallame shi a ranan saboda jikin da sauƙi sosai domin har riga yake iya saka wa
Khalil yayi mamaki sosai yanda aka bashi sabbin kaya yasaka, sannan kuma har yau yana fargaban Dad da be mishi maganar jaririn sa ba kamar yadda Sameer yafaɗa masa zasu haɗu ne, saka kayan yayi su Sameer ɗin sai tsokanar sa suke yi
Su ma a lokacin suna cikin ɗakin sun sha sabbin kaya iri ɗaya har Dad, sai dai shi nashi har da malin-malin, abun ya ɗaure ma Khalil kai amma be yi magana ba bare yatambaye su
Haka suka fito suka kwashe komi nasu suka hau mota sukai gida
A ƙofar gidan mutane ne sosai ƴan ɗaurin aure duk da ba wani gayya sukai ba, su ma su Dad basu shiga ciki ba sai suka fito suka nufi masallacin ƙofar gidan
Khalil na biye dasu yana ta mamaki, musamman da yaga wasu daga cikin abokan aikin sa, sai kuma yanda ake bashi hannu ana gaisawa dashi suna kiran sa Ango, sai abun yasake ɗaure masa kai, kallon Brr. Tahir dake kusa dashi yayi yace
"Wai meke faruwa ne?"
Dariya Brr. Tahir yayi yace "su Daddy aure zasu yi maka shine abinda ke faruwa".
"Auree". Khalil yafaɗa da tsananin mamaki wanda lokaci ɗaya gaban sa yay mugun faɗuwa
Aure kuma? Shi ɗin ne za'a yi ma aure? Mamaki al'ajabi da suka cika sa shine yakasa sake yin magana bare kuma yasake tambayan wani abun
Suna shiga Masallaci bayan sun zazzauna yana ji yana gani aka ɗaura masa aure tunda abun yafi ƙarfin tunanin sa, har fa alokacin mamaki yake yi wanda ya kasa yarda cewa maganar Brr. Tahir gaskiya ne
Amma jin sunan wacce tazame masa mata a yau ɗin sai lokaci ɗaya yayarda da cewa tabbas shine akayi ma aure, shirun da Dad yayi masa yana nufin zai aura masa Halwa ne
Baza ka taɓa sanin wani hali Khalil yashiga ba domin gaba ɗaya jin sa da ganin sa tare da tunanin sa sun tsaya cakk, be san ya aka ƙare a wajen ba, shi dai yasan Brr. Tahir ya riƙo sa sun fito taron jama'a sannan sun shiga cikin gida, ɗakin su dake gidan a nan yanufa dashi, tunda ya'ajiye sa saman gado yazame yakwanta yarufe idanun sa be sake motsawa ba
Shi kansa Brr. Tahir ya shiga damuwa ganin yanda Khalil ɗin yakoma, gashi mutane suna ta shigowa suna masa magana amma tamkar gunki haka yakoma musu, baya magana baya kuma jin su.
*****
Fannin Amarya ma hakan take, baza ka taɓa gane wani irin hali take ciki ba, ko kaɗan bata murna da wannan ranan, ita dai kawai tana yin duk abinda aka saka ta ne, har dare ba ta iya cewa uffan sai dai tabi mutane da idanu
Kuma duk a yau ɗin ne akayi sunan jaririn da yaci suna Ahmad, zai ci gaba da zama wajen Ummi ne har sanda Saleema zata samu lafiya.
Brr. Tahir ne aka wakilta wanda zai ɗauko Halwa yakai ta gida ita kaɗai, don haka lokacin da yazo har an saka ta sake yin wanka ta shirya cikin Swiss less milk colour, duk da kasancewar ta baƙa kayan yayi mata kyau sosai, bare kuma yanzu da tasake haske sosai skin ɗin ta yasake fresh
Ummi ita da kanta taraka ta har mota tabuɗe mata tashiga
Halwa bata yi kuka ba iyakan dai tunda taɓoye kanta a gyalen ta bata sake motsa wa ba
Brr. Tahir yana ta tsokanar ta yana jan ta da hira amma shiru tayi masa tana sauraron sa, har sanda suka kai yaraka ta har ciki sannan yanuna mata ɗakin Khalil a matsayin nan ne ɗakin ta, shiga tayi shi kuma yafice a gidan gaba ɗaya
Ɗakin tabuɗe tashiga a hankali, daddaɗan ƙamshin turaren sa ne yay mata maraba cikin hanci, sai taja gauran numfashi tana sake buɗe ƙofofin hancin nata don sake shaƙa, sosai take jindaɗin ƙamshin shiyasa koda yaushe burin ta kawai tashaƙa a hanicin ta, sauke gyalen daga kanta tayi tana ƙare ma ɗakin kallo, bata taɓa shigowa ba sai a yau ɗin
Sai da tadaɗe a tsaye anan tana kallon ɗakin kafin tataka tanufi gaban gadon tahaye takwanta
Allah babu yanda baya tsara lamarin sa, Wai yau ita ce aka kawo gidan nan a matsayin matar gidan, tabbas yau tana cikin wani yanayin da babu me gane wa sai ita kaɗai
*****
Khalil kuwa yana can gida su Dad sun saka sa gaba suna mishi nasiha, duk da basu san menene a ransa ba amma sun gane baya cikin nutsuwan sa ko kaɗan, sosai yake tattare da damuwa, kuma sun san cewa dole ne zai shiga wani yanayi tunda tamkar auren dole sukai mishi a ganin su
Bayan sun gama mishi nasiha yafito Drever yatuƙo sa zuwa gida batare da yayi tunanin wai yasiyo abubuwan da ake tarban Amarya ba.
Halwa na kwance taji ƙarar buɗe gate da rufe wa, bayan wajen minti 5 kuma taji an buɗo ƙofan ɗakin an shigo, a yanzu tarigada ta ƙudundune kanta cikin gyalen sai dai tana kallon inuwar sa har sanda yasoma takowa yanufo wajen gadon
Tun sanda yashigo idanun sa suka faɗa kanta, don haka yanufi wajen gadon yatsaya ƙerere yana faman kallon ta, ya saka hannun sa ɗaya cikin aljihun wandon sa
Gaban Halwa sosai yake faɗuwa jin sa a bakin gadon, rufe idanuwan ta ruf tayi tana sauraron bugun zuciyar ta da kuma abinda zai biyo baya
Leɓen bakin sa na ƙasa yacije da ƙarfi yana sakin huci, sai yajuya yanufi Toilet, wanka yayi yafito har lokacin Halwa bata motsa ba duk da kuwa tasan baya wajen
Wajen Sip yanufa yabuɗe, yamutsa fuskar sa yayi ganin babu komi a wajen, sai yanzu ma yasake ƙare ma ɗakin kallo yatabbatar an sauya masa kayan ɗaki
Be ce komi ba yasake buɗe ɗaya side ɗin anan ne yaga kayan nasa, jallabiya yazaƙulo tare da gajeren wando yakoma cikin Toilet yasaka, sai da yagama yafito yanufi ƙofa yafice, ɗakin Saleema yashiga yakwanta saman gadon ta
Rufe idanuwan sa yayi yana sauraron bugun zuciyar sa, bazai ce baya farin ciki ba a yau, sai dai abinda yasani a game da ita shine ya jagula masa duk wani buri na ransa, taya zai iya zama da mazinaciya a matsayin matar sa? Har yau yana matuƙar ƙaunar ta aransa domin kuwa ji yake yi tamkar ana ƙara masa wutan ƙaunar ta, sai dai duk sanda yatuna Halwa tayi rayuwan ƙasƙanci har da rabon ɗiya hakan na mugun ɓata masa rai, kuma ba komi yajanyo hakan ba sai tsananin kishin ta da yake yi, duk sanda yaganta sai zuciyar sa tariƙa raya masa rayuwan da tayi da ƙattin banza, shi a ganin sa tunda har ta iya haifar yarinya tabbas ita ɗin ba ƙaramar tantiriyar karuwa bace, maybe yanzu ta tuba ne shine tadawo gidan su Saleema tazauna
Baya jin zai iya rayuwan aure da ita, sai dai tayi ta zama ahaka har sanda zai huce watarana ƙila yaɗauke ta a matsayin matar sa, wannan shine shawaran da yayanke a ransa, a cewar sa yana da mata ita kaɗai ta ishe sa
Numfashi yaja yaci gaba da tunanin sa zuciyar sa duk babu daɗi sabida yanda tunani masu yawa suka zo sukai mishi rututu.
Itama Halwa tunda yafita tasaki numfashi tana fito da kanta cikin gyalen, daman tasan hakan zai iya faruwa, ita kanta tariga ta sanya ma ranta zaman gidan kawai zata yi ba a matsayin matar sa ba, baza ta taɓa amince wa da auren nan ba sai idan Saleema ta yarda zata iya zama da ita a matsayin kishiyar ta, idan har bata amince ba ba za ta taɓa zama ba dole ne tabar gidan, wannan alƙawari ta ɗaukar wa kanta duk ranan da Saleema tanuna rashin jindaɗin ta to tabbas zata bar rayuwan su gaba ɗaya.
.
_to fa masu sauraro kuna jin yanda Khalil da Halwa suka sha alwashin zaman nasu yanda zasu aiwatar dashi._
_me zai faru?_ 🤔
[12/16/2020, 10:36 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Twenty One*
________🎓Washe gari babu wanda yatashi da wuri duk kan su, barci suka sha sosai har wajen ƙarfe 11:30am. Sannan ne Khalil yasoma tashi, wanka yashiga yayi a Toilet ɗin Saleema, sai da yafito yatuna kayan sa na ɗakin sa, dayike be taɓa kwana anan ɗin ba don haka babu kayan sa ko ɗaya a ciki, jallabiyan jikin sa yamayar yanufi ɗakin sa
Yana tura ƙofan yashiga yahange ta kwance saman gado sai sharan barci take yi, wajen gadon yaƙarisa yana kafe ta da idanuwan sa
Tana kwance ta ɗaura kanta saman pilow tare da matse shi sosai a tsakankanin hannayen ta, gyalen da ɗankwalin ta gaba ɗaya sun yi hanyan su, sai ta nannaɗe ƙafafuwan ta waje ɗaya tacure kamar wata me jin sanyi
Idanu kawai yazuba ma face ɗin ta yana kallon yanda tabuɗe baki tana sharan barci, be san sanda yasaki murmushi yana jin tsananin son ta a ransa
Ya ɓata lokaci sosai yana ƙare mata kallo ko ta ina, sai da yagaji don kansa kafin yanufi sip ɗin sa yazaro ƙananan kaya yasaka, sannan yanufi gaban mirror yayi shafe-shafen sa tare da gyara yalwataccen gashin kansa yafeshe jikin sa da turaren sa masu shegen ƙamshi sannan yafice.
Ƙamshin turaren sa shine yatashe ta, lokaci ɗaya tabuɗe idanunta batare da ta motsa ba, sai da tadaɗe ahaka tana ta shaƙar daddaɗan ƙamshin sa kafin tamiƙe zaune, ɗankwalin ta taɗauka taɗaura tasauka tanufi Toilet, bata fito ba sai da tayi wanka kafin tariƙo kayan ta a hannu tana ɗaure da towel tafito, ajiye kayan tayi tanufi gaban mirror tashafa Lotions sannan tanufi wajen Trolly ɗinta tazaɓo kayan da zata saka
Doguwar riga ne na atamfa iya ƙasan gwiwan ta, sai skert pencil me tsagi ta baya, kayan sun yi mata kyau da tasaka kasancewar atamfan ja ce da ratsin blue, ɗan kwalin kawai taɗaura tafito sabida yanda take jin yunwa sosai a cikin ta
Babu kowa parlour'n sai tanufi kichen kanta tsaye, dashi tasoma cin karo yana zaune a bakin ƙofa saman kujera, hannun sa riƙe da tea Cup yana latsa wayan sa
Shigowan ta yasa yaɗago kai yana kallon ta, wanda idanuwan su suka haɗe cikin na juna, sai tayi saurin cire nata idanun tana gaishe sa
"Ina kwana?"
Be ɗauke kansa akan ta ba sabida tayi masa kyau sosai duk da kuwa babu kwalliya a fuskar ta, kuma kasancewar tana jego sai skin ɗin ta yaƙara fresh duk da kuwa ta rame a fuska, amsa mata yayi a taƙaice
Sai taƙara ce masa "Ya jiki?"
Wannan karon sai da yaja lokaci kafin ya'amsa mata wanda har ita tayi tunanin ba zai amsa ɗin ba, kuma tana tsaye a wajen taƙi jirga wa, ji kawai tayi gaba ɗaya kamar an zare mata kuzarin ta sabida yanda take jin idanuwan sa akanta, wanda ta tabbatar kallon ta yake yi shiyasa takasa gaba takasa baya
Miƙe wa yayi yanufi cikin kichen ɗin ya'ajiye Cup ɗin hannun sa sannan yafice
Fitan sa yayi daidai da sauke numfashin da tayi, dafe ƙirjin ta tayi tana jin yanda yake luguden bugawa, ta jima a tsaye bata san me zata yi ba kafin kuma taja ƙafafun ta taƙarisa ciki cike da rashin jindaɗin yanda Khalil yasauya mata tun kafin haihuwar ta, ta rasa mene tayi masa yasauya lokaci ɗaya, ada abun baya damun ta amma a yanzu sosai take jin haushi da rashin yin mata magana da baya yi
Tura baki gaba tayi tasoma neman abinda zata yi breakfast, ruwan tea ta dafa sannan tasake a Cup ɗin da yasha, sai tasoya ƙwai guda uku, sai da tagama tahaɗa Tea ɗin sannan tazauna a inda yatashi tasoma karya wa, ba ta son tafita Parlour ta tarar dashi don haka tayi zaman ta nan
Sai da tagama sannan tafito, babu shi cikin parlour'n sai tanufi ɗakin sa wanda yazama nata a yanzu, tana tura ƙofan tahange sa bakin gado, dasauri tajuya takoma parlour tazauna
Kallo takunna tayi zaman ta anan tana ta saƙe-saƙe a ranta.
Khalil be fito ba sai da yaji kiran sallan azahar, da keey ɗin mota a hannun sa yafice agidan.
Itama tashi tayi tashiga ɗaki tagyara kwanciyar ta takwanta saman gado bayan ta ɗau wayan ta da tabari akan drower, kasancewar tana jego hakan yasa bata da tsarki, wayan ta tay ta dannawa har zuwa wani lokaci, gaba ɗaya ta gaji da zaman ta haka nan har Ummi ta kira sun yi waya, daga ƙarshe sai tajawo jakan makarantan ta tasoma duba handout ɗin ta, a ranta tana tunanin dole ne gobe takoma school tunda baza tay ta zama haka nan ba koda yaushe bata da abokin hira
Da wannan shawaran tatashi tasoma gyara gidan, duk da kuwa ko ina fesfes yake jin sa, amma haka tagyara ko ina tasaka turaren ƙamshi gidan yabaɗe da ƙamshi sosai, ganin Khalil be dawo gidan ba sai tasake sakin jikin ta tana ta harkokin gaban ta, a Parlour tabaje tana ta kallo gefe ɗaya kuma ga handouts ɗin ta ta baje su tayi karatun har ta gaji
Sai da yamma tayi sosai sannan tatashi tashiga kichen tagirka musu shinkafa da miyan jajjage sannan tayi musu zoɓo tahaɗa salat, takai dainning duk ta jera tanufi ɗaki tasake yin wanka tasauya kaya.
Sai dare Khalil yadawo, lokacin tana Parlour zaune yashigo, sannu da zuwa tayi mishi ya'amsa yawuce ɗakin ta, wanka yayi yasauya kayan sa yafito Parlour
Kasancewar da yunwa yadawo yana fito wa yakalli dainning, nan yaga coololi an jera su don haka can yanufa yazauna yazuba abincin yaci
Halwa tun fitowar sa tashige ɗaki, dama zaman jiran sa take yi taga dawowar sa sabida zuciyarta haka kawai tamatsa mata da rashin jindaɗin dawowar nasa, sauya kayan ta tayi zuwa na barci riga da wando sannan tahaye gado takwanta, babu jima wa barci yay gaba da ita
Khalil be dawo ɗakin ba sai da yagama kallon sa sannan yashigo yaɗau kayan barcin sa yasaka yafice yakoma ɗakin Saleema.
Washe gari da safe Halwa tana tashi tagyara gidan tayi musu breakfast sannan taci nata takoma ɗaki tashiga wanka, tana fito wa tashirya cikin riga da skert na atamfa ruwan madara sai ratsin brown da baƙi, ɗinkin yayi mata kyau sosai ya sake haska ta matuƙa, Hijab tasaka brown Colour wanda yatsaya mata dai-dai gwiwar ta, sai taɗau HangBag ɗin ta tafito
Lokacin Khalil ya fito daga ɗaki yana shirin shiga nata don saka kaya suka ci karo
Dasauri tamatsa masa tare da gaishe sa
Kallo yabi ta dashi kafin ya'amsa mata batare da ya tashi a hanyan da yatsare mata ba, mamaki yake yi ganin ta da shiri "to ina zata je?" Yatambayi kansa gaban sa na faɗuwa jin wani sashi na zuciyar sa ta kawo masa tunanin ƙila gida zata koma
Halwa kamar tasan me yake tunani tace "Uhmm dama zan je school ne".
Be ce komi ba yamatsa mata tawuce shi kuma yashige ciki
Tana fita tahaɗu da drever, tayi masa maganar makaranta zai kai ta
zuwa yayi yaɗauko motan tahau suka fice cikin gidan.
Khalil dake tsaye bakin window yana kallon su, sai da suka fice sannan yasauke ajiyan zuciya yaƙarisa yasaka kayan sa yafito Parlour yay zaman sa, dayike ba wai ya gama samun sauƙi bane shiyasa bazai iya koma wa bakin aiki ba, har yanzu ciwon na damun sa don baya iya yin tuƙi, jiya da yafita har ya shiga mota ya zauna ya kunna yana shirin tuƙa wa yaga bazai iya ba, shine yakira drever suka fita tare.
*****
Drever na sauke Halwa tanufi department ɗin su, yau bata saka Niƙap ba don bata da sha'awar saka wa kamar ko yaushe
A hanyan ta taci karo da wata Course mate ɗin ta Nafeesa, suna mutunci sosai da ita don haka tayi saurin kiran ta
Hakan yasa Nafeesa tajuyo don taga me kiran nata, ganin Halwa sai tafaɗaɗa fara'an ta tace
"A'a yau Halwa ce a school ɗin?".
Murmusawa Halwa tayi lokacin ta ƙariso wajen ta sai taba ta hannu sukai musabaha sannan tace
"Wlh kam ya kike?"
"Lafiya lau ya gida kwana da yawa?" Nafeesa ta faɗa tana murmushin itama
"Alhmadulillah".
Nafeesa tace "to masha Allahu mu ƙarisa mana yanzu zamu yi Lecture".
Halwa bata ce komi ba har suka ƙarisa class ɗin da zasu yi Lecture ɗin
Sai da suka zauna Nafeesa tace "ya ban ga Babyn namu ba? Tunda abun ma babu gayyata ba'a ɗauke mu a bakin komi ba shiyasa zumuncin ma ba'a son yi damu".
Halwa kallon ta tayi sai dai ta kasa cewa komi, bata yi tunanin zuwan da take yi ada zasu fahimci tana da ciki ba, sabida tun lokacin da yasoma girma take zumbula Hijab har ƙasa sannan kuma tana kaffa-kaffa dashi don kar agane, kuma tana saka niƙap a fuskar ta bare su ce zasu fahimta
Abunda bata sani ba da yawa waɗanda take gaisa wa dasu sun san tana da ciki, har gulman ta suke yi ashe tana da aure ne bata faɗa musu ba, daga ƙarshe ma sai suka dena ganin ta gaba ɗaya duk da kuwa suna tunanin cewa ƙila saboda cikin ne tadena zuwa
Murmushi Nafeesa tayi tace "wai kina tunanin bamu sani ba ko? Ai kallon ki kawai muke yi tunda kin ƙi faɗa mana, kinga da mun zo suna ai".
Itama Halwan murmushin taƙaƙalo tace "eyya kiyi haƙuri Nafeesa".
"Babu komi ai". Nafeesa tafaɗa