Header Ads
Showing 90001 words to 93000 words out of 132567 words

Chapter 31 - BARRISTER IBRAHIM KHALIL Complete Document by Nafisa Isma'il Lawal.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jul 2024

1160

Ads at the middle of Article

yanda yaƙara min muni ya mayar dani sai kace wata uwa".




Dariya suka yi gaba ɗaya kafin Halwa tafice




Ita kuma Saleema tagyara kwanciyar ta.




Tana fita tatarda Khalil ɗin zaune saman sofa yana latsa wayan sa




Ƙarisawa tayi ahankali tayi masa sallama




Hakan yasa yaɗago kai yana kallon ta at the same time yana amsa mata sallaman tare da ɗaura murmushi a fuskar sa




"Maman Husna". Yafaɗa idanun sa akan ta




Murmushi tayi tana Sad da kanta ƙasa don bata son ko kaɗan suna haɗa idanu, sai taji kamar wasu abubuwa suna fita ta cikin nasa idanun su shiga cikin nata




"Dama yaya Khalil nazo ne kayi min wannan assignment ɗin".




Gyara zaman sa yayi yana ajiye wayan yace "mu gani".




Miƙa masa tayi




Ya'amsa yana duba wa, ya ɗau tsawon mintuna biyu yana duba wa kafin yaɗago kansa yana kallon ta yace "ina Bairo ɗin?".




Miƙa masa tayi dasauri




Ya'amsa yaci gaba da dubawa kafin yasoma rubutun




Ita kuma tana tsaye tana kallon sa




"Baki gaji ba? ki zauna mana".




Tatsinkayi muryan sa yana faɗin hakan batare da ya ɗago ya kalle ta ba




Babu musu tazauna kan hannun kujeran




Tsawon mintuna goma yaɗauka yana mata kafin yagama yakalle ta yana cewa "matso in yi miki bayani yanda zaki fahimta koda nan gaba".




Hakan kuwa yayi mata daɗi don babu ita akai karatun shiyasa duk bata wani fahimta ba




Zama tayi kan kujeran sosai, shima kuma yamatso ta yanda zata iya ganin rubutun sannan yasoma mata bayani




Sosai tatsayar da hankalin ta waje ɗaya tafahimce sa duk da kuwa yanda take ji sabida kusancin su da yayi yawa




Sai da yagama sannan yaɗago kai yana kallon ta da murmushi yace "yauwa to na gama saura biya ko?"




Itama kallon sa tayi tana fid do idanu waje tace "ba kyauta kayi min ba?"




"Laa ba kyauta nayi miki ba, ki duba ai nayi ƙoƙari Yakamata ace kin biya Ni" yayi maganar yana shafa suman kanshi yana dariya ƙasa-ƙasa




"To nawa ne sai in biya ka?".




"Duk yanda kika ba da babu matsala, amma meyasaka kike son karantan Low?"




Kanta tasauke ƙasa, batasan me zata ce masa ba illa jujjuya Bairo ɗin hannun ta da take yi




"Kinyi shiru". Yace mata a hankali idanun sa ƙyam akanta




Ɗago kai tayi takalle sa, ganin sun haɗa ido tayi saurin maida kanta ƙasa tana jin gabanta na sake matsanancin bugawa




"Ina so ne kawai". Tafaɗa a matuƙar sanyin murya




Shiru yayi be yi magana ba, illa kallon ta kawai da yake yi cike da ƙauna, wannan kusancin nasu ya saka sa matuƙar nishaɗi da wani irin farin ciki ainun




Miƙe wa tayi ta ɗan saci kallon sa kafin tace "na gode yaya Khalil, Allah yasaka".




Murmusawa kaɗai yayi be ce komi ba




Har ta juya kuma sai yace "ina Saleema?"




"Bata jindaɗin jikin ta shine takwanta".




"Subhanallah.." yafaɗa yana miƙe wa




"Muje in duba ta".




Ɗakin suka nufa




Suna shiga sukai wajen gadon, zama Khalil yayi yana kallon fuskarta




Har ta samu barci, gaba ɗaya jikin ta a rufe yake ruf sai fuskarta dake waje, a yanda take fitar da numfashi da ƙarfi zaka san jikin ta be mata daɗi, gashi fuskarta ya jiƙe sharkaf da zuba, gaban goshin ta sai tsatstsafo da gumi yake yi




Hannun sa yaɗaura a saman gashinta kasancewar ɗankwalin ta ya zame, shafa gashin kawai yake yi yana kallon ta cike da tausayi




Haka zalika Halwa dake tsaye itama kallon Saleeman take yi cikin tsananin tausayin ta




Babu wanda ke magana cikin su kowa da tunanin dake ransa, tsawon wasu mintuna kafin Khalil yamiƙe yafice a ɗakin




Yana fita Halwa takoma inda yatashi tazauna, tasaka hannun ta itama kamar yanda yayi tana shafa mata gashin




Bata tashi a wajen ba sai da taji kiran sallan Asar, kafin tashiga Toilet taɗauro alwala tafito, sallah tayi tacire Hijabin tana zama kan sofa, sai tabuga tagumi kawai tana kallon Saleema, sai dai abaɗini tunani kawai take yi






Daga ƙarshe tashi tayi tafito parlour, sai tayi hanyan kichen tana tafiya a hankali, tana shiga sai tatsaya tana tunanin abinda zata yi




Ta ɗan jima a tsaye kafin ta'isa wajen kanta tasoma kiciniyar ɗaura musu girkin dare, duk da dama girkin ranan Khalil ne yayi musu Take-away, ita taje yin test a makaranta, Saleema kuma rashin jindaɗin jikin ta yasaka bata girka ba, da Khalil ɗin yadawo sai be ma tambayi ba'asi ba yakoma yasiyo musu




Motsin da taji a bayan ta ne yasaka tajuya dasauri




Khalil ne tsaye ya harɗe hannayen sa akan ƙirjin sa ya zuba mata kyawawan idanun sa masu tsananin kaifi da burge wa, fuskarsa kuma yalwace da murmushi




Duƙar da kanta tayi tana jin matsanancin kunya ya kamata kasancewar ta bata da Hijab a jikinta, duk da riga da sani ne na atamfa a jikin ta, amma kuma duk da haka cikin ta yafito sosai ga kuma ƙiba da yasaka ta tayi




"Me zaki yi?" Yatambaye ta yana kallon ta yana ji kamar yahaɗiye ta sabida tsananin ƙaunar ta da yake ji a ransa




Halwa taba shi amsa batare da ta ɗago kai ta kalle sa ba




"Dama zan yi mana girki ne".




Khalil yace "a'a ki bar shi kawai, idan na fita anjima zan siyo kar ki wahal da kanki uhmm?".




Kaɗa masa kai tayi kamar ƙadangaruwa, bata sake ɗago kai ba sai da taji tafiyar sa kafin taɗaga kanta a lokaci ɗaya kuma tana sauke ajiyan zuciya me ƙarfi har da dafe ƙirji




Bata san meyasa take zama wata daban ba a gaban sa, sai takoma kamar ba ita Halwan da tasani ba




Murmushi tayi a fili tace "wlh na sauya sosai kamar ba Ni ba".




Sai kuma tasaki dariya tana juyawa tanufi wajen Freezer bayan ta ɗau ɗanyen naman da taɗauko tamayar cikin Freezern, sai kuma tatsaya tana tunanin abinda zata girka taci, sosai take jin kwaɗayi tana son ta ɗan saka wani abun da zai mata text a baki




"Ko dai inyi ɗan wake ne?" Tafaɗa tana juya ido alamun tunani




Sai kuma tagirgiza kanta




"A'a bari in yi dai kalallaɓa, yeessss shi zan yi". Taƙarike maganar da dariyan farin ciki a fuskarta




Kasancewar suna da komi sabida haka cikin ƙanƙanin lokaci tayi tagama sannan taɗauki Plate ɗin da tazuba tanufi hanyar fita, har ta kai bakin ƙofa sai tadawo taɗau Robbern yaji tafice




A Parlour tazauna taɗaura plate ɗin saman cinyan ta, tana ci tana kallon ta cike da nishaɗi da jindaɗin kalallaɓan






Bata san sanda Khalil yazo wajen ba sai tsinkayan muryan sa tayi




"Ashe dai hanci na be jiyo min ƙarya ba".




Dasauri taɗago kanta a tsorace tana kallon sa




Hakan yasa yayi dariya yana zama yace "sorry na tsorata ki ko? Menene wannan kuma?"




Yaƙarike maganar yana kallon cikin Plate ɗin




Tana murmushi taba shi amsa da "kalallaɓa ne, bismillan mu".




Taɗago Plate ɗin tana ajiye wa a tsakiyar su




"Ai kuwa zan ci, wannan abun tun daga ɗakin karatuna na jiyo ƙamshin sa". Yayi maganar yana dariya




Sai kuma yasaka hannu yagutsira yakai bakin sa




Duk tana kallon sa tana murmusawa




Taunawa yasoma yi a hankali yana ɗan yamutsa fuska, sai kuma yasoma gyaɗa kansa yana wani lumshe idanu




"Waiii wannan abun daɗi yake dashi, me kika ce ma sunan sa?"




Dariya tayi tace "kalallaɓa".




"Uhmm kalallaɓa yayi daɗi fa, Ni ban taɓa cin abun da yakai wannan daɗi ba, so texting".




Murmushi tayi me fid da haƙora tace "ko dai santi kake yi?"




Saurin girgiza mata kai yayi yana taunan wanda yasaka a baki, a kuma time ɗin yake bata amsa da "a'a dagaske nake miki".




Halwa dariya kawai take mishi, shi kuma sai zuba santi yake yi cike da barkwanci




Be cire hannun sa ba sai da suka cinye gaba ɗaya




Halwa ƙoƙarin miƙe wa tayi zata maida Plate ɗin kichen




Yayi saurin cewa "no koma ki zauna bari in Kai".




Ya'amshi plate ɗin yakai kichen tare da wanke hannun sa yafito




"Gaskiya yayi daɗi, kinga daɗin sa ya saka na cinye miki ban rage miki ba, Allah yasa dai ya ishe ki?" Yayi maganar bayan ya dawo wajen ya zauna




Murmushi Halwa tayi tace "sai yanzu kenan zaka tuna bayan ka gama cinye min? To ya zan yi haka nan zan haƙura ai tunda ba wani".




Shafo kansa yayi yana dariya yace "sorry na manta ne wlh".




"Babu komi ai". Tafaɗa cike da nishaɗi




"Wai yaushe ne zaku soma Exams ɗin nan ne, naga time na ƙure wa?"




Halwa tace "jibi ne insha Allahu".




Zai sake magana wayan sa yasoma ƙara, ciro wa yayi cikin aljihun wandon sa yana kallon screan ɗin wayan, be ɗaga ba sai yamaida kallon sa gare ta yana faɗin




"Bari inje Tahir na jira na, idan Saleema tatashi jikin babu daɗi Please ki kira ni kinji? Bazan daɗe ba ma zan dawo".




"To sai ka dawo Allah yatsare".




"Ameen na gode". Yafaɗa alokacin da yake miƙe wa yayi hanyan fita yana ɗaura wayan a kunne sa bayan yayi peacking call ɗin




Bin bayan sa tayi da kallo har yafice






"Yana da matuƙar kirki".


Tayi maganar a fili tana murmusawa tare da kwanciya kan kujeran, lumshe idanun ta tayi cike da tsantsan farin ciki tare da tunanin Khalil ɗin




Yau dai baza ta iya hana kanta tunanin sa ba, don haka tabaje zuciyarta tana tariyo duk wani abu da yataɓa shiga tsakanin su, har da ma wanda be faru ba sai da zuciyar nata takawo mata tunanin tare da ƙawata mata abun ta yanda zai saka ta nishaɗi.






_kun san dai zuciya 🤣🤣🤣🤣__
[12/3/2020, 5:34 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️




*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_




*بسم الله الرحمن الرحيم*






*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```


*JIKAR LAWALI CE*✍️


*Wattpad: UmmuDahirah*👈




*\F.W.A📚/*


```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._


*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._




*BOOK TWO*




.


_______________________________


*CHAPTER Fourteen*


________🎓Sai da akayi kiran sallan magriba sannan tamiƙe tanufi ɗakin Saleema




Har a lokacin barci take yi bata farka ba, don haka tawuce kai tsaye cikin Toilet taɗauro alwala, hijab tasaka tayi sallah




Lokacin da tasallame Saleema tatashi




Jin motsin ta yasa Halwa juyawa tana kallon ta, sai kuma tamiƙe dasauri tanufe ta tare da faɗin




"Sannu Sister ya jikin?"




Ahankali ta'amsa mata da "alhmadulillah" tana yunƙurin tashi




Taimaka mata tayi tatashi zaune kafin tasake tambayan ta




"yanzu ina ke miki ciwo?"




Murmusawa tayi tana kallon ta tace "babu, sai dai kawai ƙarfin jiki ne bana ji".




"Sannu gashi jikin ki duk zafi". Halwa tafaɗa cike da tausayin ta bayan ta ɗaura hannun ta saman wuyan ta tana tattaɓa wa




Saleema tace "taimaka min in tashi zan yi sallah".




Taimaka mata Halwan tayi tamiƙe sannan tariƙe ta takai ta har Toilet ɗin tafito, sai da tadaidaici ta gama abinda zata yi takuma komawa tariƙo ta suka fito, akan dadduma ta'ajiye ta taɗauko mata Hijabin ta




Sai da tafara sallan kafin tazauna gefen gado tana kallon ta




A zaune tayi sallan har ta idar




A Lokacin ne Khalil yashigo ɗakin da sallama




Halwa ce ta'amsa masa yayinda Saleema tabi shi da idanu




Takowa yayi zuwa wajen Saleeman yaduƙa agaban ta yace "Ya jikin naki?"




"Da sauƙi".




Hannun sa yasaka yana taɓa jikin ta yaji zafi sosai, sai yamaida idanun sa kanta yace "but ga jikin ki da zafi anya baza muje asibiti ba?"




Duƙar da kanta kaɗai tayi batare da ta bashi amsa ba, domin ko kaɗan bata son yin magana sabida kanta sara mata yake yi




Hannun sa yamaida kan haɓan ta yaɗago kanta yana ƙura mata idanu, yayinda itama tazuba nata idanun cikin nashi tana kallon sa cike da rauni




Halwa dake zaune tana faman kallon su, sai tamiƙe dasauri tayi hanyan Toilet, sai kuma tadawo tayi wuri-wuri tarasa ina zata bi kawai sai tafice a ɗakin




Shi Khalil be ma lura da fitan ta ba illa ɗago Saleema da yayi tamiƙe tsaye, yajanyo ta jikin sa suka nufi kan gado suka zauna, hannun ta ɗaya yariƙe yana murza wa yayinda ita kuma takwantar da kanta saman kafaɗan sa ta saƙalo ɗaya hannun zuwa bayan sa tana lumshe idanun ta




Sun jima a haka babu me magana, sai kuma yasaki hannun nata yana ɗago kanta yace






"Bari in ɗauko ruwa da towel in rage miki wannan zafin jikin ko zaki ji daɗi".




Bata yi magana ba har yamiƙe yashige toilet, ita kuma sai takwanta tana sake rufe idanun ta.








Fitan Halwa ɗakin ta tashige takwanta saman gado tana tarufe idanun ta tare da sauraron bugun zuciyar ta, sai kuma tasoma juye-juye ta kasa zama waje ɗaya don dai kawai tahana kanta tunani da kuma abinda take ji cikin zuciyarta




Tsaki taja tana miƙe wa zaune, sai kuma tamiƙe tafito parlour, anan tatarda ledojin da Khalil yashigo dasu, ɗauka tayi taduba sai taga abinci ne ciki hakan yasa ta kwashe tanufi dasu kan dainning




Kichen tanufa taɗauko coolars tasake abincin, sannan tasake farfesun kayan ciki shima a cikin coolar tarufe su yanda bazai yi sanyi ba, sai da tagyara wajen tayi setting komi abinda zasu buƙata kafin takoma ɗakin ta, sallan isha'i tayi tazauna nan tana lazimi batare da ta fita ba, sai da taji motsin su a Parlour kafin tatashi tafito itama




Saleema ce kaɗai zaune, ta sauya kaya zuwa kayan barci me taushi riga da wando farare




Wajen ta tanufa tazauna tana cewa "sannu Sister ya jiki?"




Murmushi Saleema tayi tace "alhmadulillah, dama ke nake shirin kira muci abinci kuma kin ƙule ɗaki".




Dariya kaɗai Halwa tayi batace komi ba tamiƙe




Itama Saleeman miƙewa tayi suka nufi dainning, bayan sun zauna Halwa take cewa




"Ina yaya Khalil ɗin ko ya fita ne?"




"A'a yana ɗakin sa, yace be jin yunwa yana da aiki ya shiga yi".




Gyaɗa kanta tayi tana zuba musu abincin




A haka sukai ta ci suna ɗan taɓa hira har lokaci yaja suna nan zaune a wajen




Daga ƙarshe Halwa tamiƙe ta tattara kayan takai kichen tafito tana kallon Saleema da har yanzu tana nan zaune bata motsa ba




"Sister Ni zan shiga ɗaki ina son Nima in Yi bitan karatu".




Miƙe wa Saleema tayi tanufo ta tana faɗin "to muje nima in taya ki karatun".




Halwa dariya tayi tace "kai sis ke dai ki wuce wajen mijin ki kar yaji ki shiru, ko baki san dare yayi bane?"




Itama dariyan tayi tace "na fiki sani ai, Ni dai muje in tayaki bana jin barci wlh, yanzu idan naje shima ya ƙufe akan aiki sai in ta zama Ni kaɗai".




Shiga ɗakin suka yi suka zauna, Halwa ta jawo handout ɗin ta tana karatun Saleema na kwance tana jinta, kaɗan-kaɗan kuma suna taɓa hira




Sai wajen 10:00pm. Kafin Saleema tamiƙe tayi mata sallama tafice




Itama tashi tayi tarufe ƙofan sannan tasauya kayan ta zuwa na barci takwanta, bata ɗau lokaci ba barcin ya ɗauke ta tunda shine cike fal a idanun ta.










**** ***** ***** ****** *****




*WASHE GARI*


Washe gari ta kasance Sunday ranan da ake ɗaura auren Zainab




Babu laifi gidan an cika maƙil don dama suna da ƴan uwa da yawa, yayyin Zainab su uku duk ka mata ko wacce ta zo da iyalan ta, Haka zalika shima babban Yayan su dake zaune a Yola da nashi iyalan shima ya zo




Umma dai babu yanda zata yi ne amma kowa yaganta ya san akwai abinda ke damun ta, don ko gayyan mutane sai Zaituna ne ta'aika ma mutane, kuma ita taraba ma mutanen anguwa Chwingum duk dai don Umma taƙi yi.






Ƙarfe 11:30am. Aka shaida ɗaurin auren Zainab da Aliyu




A ranan kuma ƴan uwanta suka je ganin ɗakin ta suka ga abinda Yakamata su saka sannan suka wuce kasuwa, labulayen ɗaki da ƙarafen da za'a buga duk suka siyo, da sauran abubuwan buƙata, sannan suka koma gidan suka kafa




Lokacin ne kuma aka ɗauko kayan ɗakin ta da Abba yayi mata, don haka suka tsaya suka shirya mata komi inda yadace, ɗakin Amarya yafito fes gunun sha'awa




Sabon gini ne da yayyin Aliyu suka haɗa kuɗi sukai masa tunda dama yana da filin sa a cikin gidan su, daga Umman sa sai shi sai kuma autar su agidan.




Sasan sa daban akayi masa, sai da aka kewaye da gini, ɗakuna ne ciki biyu sai ƙaramin parlour a tsakiya, sannan ko wani ɗakin akwai Toilet a ciki, idan kafito a bakin ƙofan ɗakin shine kichen ɗin ta yake, har da kantan kichen sai da akayi mata inda zata riƙa ajiye-ajiye




Sai kuma babban Bayi dake sasan Umma




Komi yayi dai-dai gunun sha'awa Amarya kawai yake jira ɗakin






Da dare aka kawo ta gidan ta inda kowa yatafi yabar ta ita da Angon ta, sai muce Allah yasanya alkhairi *ZAINAB* ya nuna mana na ƴan baya lafiya.




















_sai mun zo cin dubulan da cin-cin, kar agaji damu_🤣
[12/4/2020, 5:52 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️




*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_




*بسم الله الرحمن الرحيم*






*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```


*JIKAR LAWALI CE*✍️


*Wattpad: UmmuDahirah*👈




*\F.W.A📚/*


```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._


*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._


_Wannan shafin naki ne *NANA ALIYU* ki more kiji daɗin ki ke kaɗai bance wani yataya ki ba, na gode da ƙaunar ki gare ni._






*BOOK TWO*




.


_______________________________


*CHAPTER Fifteen*


________🎓 *TWO DAYS*


Yau agajiye yadawo aiki, bayan yayi parcking motan sa yafito riƙe da briafcase ɗin sa da Suit ɗin sa da yacire, rufe motan yayi yanufi cikin gidan cikin tafiyan sa me burge wa, duk da kuwa a yanzu ɗin salon tafiyan ya sauya yana yi ne kamar me tsoron taka ƙasa, nan kuwa duk cikin gajiya ne




Tura ƙofan yayi kafin yayi sallama wanda a dai-dai laɓɓan sa yatsaya




Babu kowa cikin parlour'n don haka kai tsaye ɗakin sa yanufa, sai da ya'ajiye komi na hannun sa sannan yazauna yasoma zare Combat ɗin ƙafafun sa da Socks, bayan ya gama sai yaɓalle bottles ɗin rigan sa gaba ɗaya singlate ɗin jikin sa ya bayyana, be cire rigan ba sai yagishingiɗa akan pilow yana lumshe idanun sa




Tsawon mintuna biyar yaɗauka kafin yamiƙe yanufi parlour riƙe da wayan sa a hannu yana latsa wa




Har alokacin babu kowa a parlour'n don haka kansa tsaye yanufi kan dainning, har ya zauna kuma sai yamiƙe yanufi ɗakin Saleema




Ƙofar a buɗe

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads