Showing 39001 words to 42000 words out of 132567 words
Chapter 14 - BARRISTER IBRAHIM KHALIL Complete Document by Nafisa Isma'il Lawal.txt
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 28*
Ringing tune ɗin wayan sa ne yadawo dashi cikin nutsuwar sa, ahankali yasaka hannun sa yaɗau wayan yana duba wanda ke kiran sa, sai kuma yayi peacking call ɗin yana karawa a kunne, shiru yayi don haka Brr. Tahir yace
"Ya man meke faruwa ne wai? Nafita nazo na tarar da missed calls ɗin ka, I'm so surprised da naga kiran ka har 5missed call, ina fata lafiya dai?"
Numfashi Khalil yasauke a hankali kana yace
"Brr. Tahir yau fa daƙyar nasha hannun wasu mutane".
"Subhanallah.. wasu mutane kenan? Me kayi musu?" Brr. Tahir ɗin yafaɗa cike da firgici
"Hmm wasu mutane kasani in banda mutanen da muke Shari'a dasu, kasan da cewa kwanaki nafaɗa maka suna bibiyana but duk da haka ban yi tunanin abun ya kai hakan ba, nafita zuwa wajen Mr. Abdullah, lokacin nafito daga gidan sa sai natsaya nan Resturent inci abinci, bayan nafito nagan su sun biyo ni, wlh naji tsoro sosai coz suna ɗauke da bindiga, daƙyar nasha ina faɗa maka, ƙarshe dai can nabaro motan sai dai na'aika drever yaɗauko min".
Brr. Tahir yace "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Ib ina tsoron fa mutanen nan su cutar da kai, why not mu sanar da Police👮? sannan yakamata kabar gidan nan zuwa lokacin da za'a gama, hankalina be kwanta ba maybe su biyo ka har gida".
Shiru Khalil yayi naɗan wasu sakonni kafin yace
"Nima hakan ne araina, but nariga da nayi ma DPO magana, yace "zai turo yaran sa suyi gadina".
Ajiyan zuciya me ƙarfi Brr. Tahir yasauke kana yace
"But duk da haka dai hankalina be kwanta ba wlh".
Murmushi Khalil yayi yace "babu abinda zai faru sai alkhairi, insha Allahu gobe komi zai wuce".
"Hakane.. Allah yakaimu to".
"Ameen" Khalil ya'amsa masa
Daga nan sai da suka daɗe suna tattaunawa akan aikin nasu kafin suyi sallama, ya'ajiye wayan yana sakin ajiyan zuciya, kana yaɗan kwantar da kan sa saman pilow yana rufe idanun sa, fuskar ta ne yabayyana acikin ƙwayan idanun nasa, dasauri yabuɗe yana jin zuciyar sa na bugawa
"Meyasaka yarinyan taƙi ɓace masa?" Yatambayi kan sa yana dafe kan sa dake sara masa a hankali
Tun da yadawo gida yake tunanin ta, da zaran yarufe idanun sa kuma fuskar ta yake hangowa, kuma sosai yake ganin tsananin damuwa a fuskar nata, afili yafurta
"Wacece ita? Meyasaka tataimake ni? Meke damun ta?"
Sai yatallabo kumatun sa yana tsira wa waje ɗaya ido, ya jima ahaka yana tunanin da besan na menene ba kafin yamiƙe yashige toilet, alwala yayi yafito yashinfiɗa sallaya yagabatar da sallan magriba, yau be jin zai iya zuwa ko ina, don haka tun da yashigo ma yasanar da ma'aikatan sa kar wanda yafita, sannan yabada umarnin a kulle masa gida, yana nan zaune har aka kira isha'i yagabatar sannan yamiƙe yafita, kichen yawuce yahaɗa Coffee yazauna nan yashanye kana yakoma ɗaki, wanka yasoma yi yasauya kaya izuwa na barci, yakashe wuta yahaye gado, addu'a yayi yashafa tare da rufe idanun sa, ya jima kafin barci yaɗauke sa
Can cikin dare yatashi afirgice yana salati, gaba ɗaya yahaɗa gumi sakamakon mafarkin da yayi da ita, runtse idanun sa yayi yana tuna kukan da take masa cikin mafarkin kuma tana neman taimako a wajen sa, shiru yayi yana sauraron bugun zuciyar sa, sai yadafe kan sa da duk ka hannayen sa yana sake runtse idanun, ya jima ahaka kafin ahankali yazuro ƙafafun sa ƙasa yasauka saman gadon, sai da yayi kusan mintuna biyar a tsaye yana tunani kafin yataka yashige toilet, alwala yaɗauro yafito yasauya kayan sa zuwa jallabiya yasoma gabatar da nafila.
_*****_
Alhaji Mubarak mai Kuɗi wani babban attajiri ne da yayi ƙaurin suna a faɗin garin Katsina da kewaye, matar sa ɗaya da ƴaƴan sa biyu, Hassana ita ce Babba tana aure a ƙasan England, sai A'isha da take zaune a wajen ta tana karatun ta acan ɗin.
Mutum ne shi me taimako wajen mutanen gari, kuma kowa ya shaida hakan domin sosai ake girmama sa sabida ana ganin sa me ƙaunar talakawa, sai dai abinda basu sani ba na daga halin sa, shi mutum ne da ko kaɗan baya da imani baya da tausayi abaɗini, sana'ar sa shine kasuwan ci, sai dai babu wanda yasan da cewa yana safaran ƴan mata zuwa wani ƙasa, sannan yana harƙallan sai da Coken, yana kuma gudanar da sana'ar tasa ne batare da kowa ya sani ba.
Dr. Sabit shine wanda yake taimaka masa, kuma tare suke harƙallan tasu, babban Likita ne shi da yayi fice sosai kuma wanda ake ji dashi cikin garin Katsina, Shine Doctorn da yake ma duk wasu yara da suka samu operation yazuba musu Coken ɗin sabida afita dashi waje batare da an gano su ba.
Akwai wani Doctor Salis abokin aikin Doctor Sabit ne, shi yafara gano abinda suke aikatawa, har yayi yunƙurin kai su ƙara don yatona musu asiri, but daga ƙarshe sai dai aka nemi Doctor Salis aka rasa ya ɓace ɓat, kuma ba'a san me yafaru dashi ba.
Alhaji Mubarak ba iya mutanen gari kaɗai yake ma kirki ba, har ta da ƴan aikin gidan sa, don haka sosai suka saki jiki agidan, sai dai abinda basu sani ba yana amfani da hakan ne don cin ma burin sa, coz sau da dama yawancin masu aikin suna da yara, sannan kuma akwai ƴan mata acikin su, babu wanda yasan meyasaka masu aikin gidan sa mata basu daɗewa, sai dai lokaci kaɗan za'a neme su a rasa.
Hajjo tana ɗaya daga cikin masu aikin gidan, kuma tana ɗaya daga cikin waɗanda suka daɗe sosai suna aiki a gidan, asalin ta bafulatana ce mazauna ƙauye, sun zo tare da mijinta da yarinyan su ɗaya Nazeefa cikin birni, wata mata ce tayi ma Hajjo hanya har tasami aiki agidan, sosai take jin daɗin aiki a gidan Alhj. Mubarak me kuɗi kuma suna samun duk abinda suke so
Bayan wasu shekaru ne mijinta yarasu don haka taɗauki Nazeefa suka taho gidan Alhj. M. Me kuɗi don tanemi alfarma wajen sa don yaba su waje agidan nasa su zauna tunda ya saba yin haka, lokacin da tagabatar masa da alfarman ta gare sa babu musu ya amince, Hajjo tayi murna sosai sai dai batasan cewa Alhj. M. Me kuɗi ya amince ne don ganin Nazeefa da yayi, yasan da cewa idan suka zauna agidan sa hakan zai basa daman cikan burin sa akan ita Nazeefan.
Rayuwa taci gaba da gudana, lokaci ɗaya Allah yajarabbi Hajjo da ciwo, ashe ciwon ajali ne, don batayi sati ɗaya ba tarasu, Nazeefa tayi kuka sosai sabida tasan bata da wasu ƴan uwa kuma da suka rage mata, sannan batasan ma ina ne ƙauyen su ba bare takoma, ana haka Alhj. Mubarak yakira ta har parlourn sa bayan yayi mata ta'aziya yace
"Nazeefa sunan ki ko?"
Kanta a ƙasa ta'amsa mishi
"Ok zakici gaba da zama anan idan kinaso, sai ki maye gurbin Mahaifiyarki, sannan duk abinda kike nema ki sanar dani ko ki sanar da Hajiya, daga yau karki ɗauki kan ki marainiya tunda har kina damu".
Sosai Nazeefa tayi murna da jin maganar sa, don haka tayi masa godiya tafice, shi kuwa murmushi yayi yaɗau Jaridan sa yasoma karantawa, yasan da cewa nan da ɗan lokaci kaɗan zai cika burin sa akanta
Ana nan wata rana Hajiya ta aiki Nazeefa gidan ƙawar ta ta'amaso mata saƙo, kasancewar babu nisa da gidan su a ƙasa tatafi, bayan taje ta dawo ne a hanyan ta na dawowa gida sai ga Motan Alhj. Mubarak ya tsaya tare da zuge glass ɗin motan yana kallon ta da murmushi a face ɗin sa, ita kuwa tayi mamaki sosai ganin sa shi kaɗai babu drever, umarni yabata tashigo motan babu musu kuwa tashiga, don shi mutum ne me tsananin kwarjini da babu yanda za'ayi kayi masa musu a matsayin sa na babba, lokacin da suka iso gidan sai taga sun wuce but bata iya ce mishi komi ba, sai dai sosai tayi mamaki kuma tana son tatambaye shi sai dai babu dama, har suka isa wani babban gida yace da ita tajira sa bari yazo, fita yayi yashiga gidan, ita kuma gaban ta sai faɗuwa yake yi, tasan da cewa shi ɗin mutum ne me sauƙin kai, amma babu abinda yahaɗa ta dashi a matsayin ta na ƴar aikin gidan sa bare yaɗauko ta cikin motan sa, that's why gaba ɗaya hankalinta yaƙi kwanciya, duk tsoro ya cika ta, tana nan zaune wani mutum yazo yace mata tashigo inji shi, babu musu tafito tabiyo bayan mutumin suka shiga gidan, lokacin da suka shiga babu kowa, a lokacin ne taji kamar ana buga mata guduma a ƙirjinta, tsinkayan muryan mutumin tayi yana faɗin "tabiyo shi" wani ƙofa taga yabuɗe yashiga sai tabi bayan sa, suna shiga tatsaya tana kallon tsarin ɗakin da babu komi sai gado da sif taji ƙaran rufe ƙofa, kallon ƙofar tayi sannan kuma tawur-wurga ido cikin ɗakin taga babu mutumin da suke tare, a sukwane tanufi ƙofan da yake a kulle tasoma taɓawa tana son buɗewa, sai dai da alamun an rufeta ta baya ne, wani irin bugawa zuciyarta tayi batasan sanda tasoma jijjiga ƙofan ba tana ɓarkewa da kuka, cikin kukan take faɗin
"Don Allah kabuɗe, ina ne nan ina kakawo Ni? Na shiga uku Ni Nazeefa, wayyo Allana Wayyo Mamana".
Kuka take yi sosai tana jijjiga ƙofan da ko motsi baya yi, daga ƙarshe zubewa nan ƙasa tayi tasoma rusa kuka tana shushshura ƙafafu, ta jima ahaka tana kukan wanda har muryan ta yadena fita sai hawaye dake ta zirara.
[9/25/2020, 11:26 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 29*
Wasa wasa sai da Nazeefa tayi kwanaki bakwai a wannan gidan batare da tasan takamaiman inda take ba, tayi kukan duniya tayi ihun duniya babu wanda yazo wajen ta, sai dai da zaran tayi barci ta farka zata tashi taga an ajiye mata abinci, tun bata taɓawa da taga alamun kanta take cuta sai tasoma ci, sau da dama tayi yunƙurin kwana ido biyu don tasami nasaran guduwa idan akazo kawo mata abinci, but bata taba samun sa'a ba, abinda bata sani ba akwai Camera cikin ɗakin, idan har sukaga batayi barci ba to bazasu kawo mata abinci ba, haka zata ƙariki zamanta babu su babu alamun su, daga ƙarshe har tacire rai da samun daman fita, jira kawai take yi ranan da zasu kawo ƙarshen rayuwanta, domin a tunanin ta gidan cin kai take.
Wata rana tana zaune taga wannan mutumin da yashigo da ita yabuɗe ƙofan yashigo, zabura tayi tayi kansa da gudu tana ƙoƙarin guduwa yayi saurin cafko ta da hannu ɗaya, abinku da wacce bata da ƙarfi ko na sisin kwabo nan tadawo baya tafaɗa jikin sa, kuka tafashe dashi tana faɗin
"Don girman Allah kataimake ni kabar ni in tafi, wayyo Allana me kuke so dani ne..?"
Bata rufe baki ba Doctor Sabit da Alhj. Mubarak suka shigo, duk kan su face ɗin su a ɗaure ne babu alaman wasa, doctor Sabit ne yanufo ta riƙe da wani allura a hannun sa, ita bata kula da alluran ba sai kallon Alhj. Mubarak take yi tana kuka don takasa magana, so take yi taroƙe shi yafitar da ita amma ina, kafin ma tagama tunanin zucin ta har taji an sanƙama mata allura, batasan sanda takurma ihu ba tana riƙe hannun doctor ɗin, kallon shi take yi idanun ta cike da hawaye tana motsa baki, sai kuma tatafi luuuuuu tafaɗi nan ƙasa.
Alokacin da tafarka alluran be gama sakin jikin ta ba, ga wani zafi da yaziyarci ƙwaƙwalwanta, nan take taɗaura hannun ta saman maranta tana sakin kuka mara sauti, tayi tsawon mintuna 5 ahaka kafin tayi yunƙurin miƙewa, daƙyar talallaɓa tatashi zaune tana jin kanta na sara mata, ga wani irin jiri dake ɗiban ta tana ganin abubuwa bibbiyu, ɗakin take bi da kallo sai dai ba wanda aka ajiye ta bane, wannan cike yake da mata Sa'annin ta da waɗanda suka girme ta, su ma da alamun dai abinda akayi mata shi akayi musu, sai dai su basu farka ba saɓanin ita, Allura ne da akayi musu na tsawon awanni but abun mamaki ita be yi tasiri ajikin ta ba, mintuna 20 kenan da yin mata sannan tafarka, kuma anyi musu ne har sai an fita dasu zuwa ƙasashen da za'a kai su sannan su farka
Miƙewa tayi cikin yanayin rashin hankali tasoma tafiya aduƙe tana tangal-tangal kamar wacce zata kife ƙasa, tariƙe cikin ta dake mata bala'in zafi, ƙofa tabuɗe tafice sai gata cikin parlour, babu kowa ciki suna can suna shirin yanda zasu fitar da ƴan matan bayan sun dawo cikin hankalin su na mintuna ƙalilan, domin alokacin da suke zuwa Airport dasu a farke suke kai su har sanda zasu shiga jirgi, sai dai hankalin su da tunanin su sun riga sun gushe, duk yanda akayi dasu haka zasuyi
Direct wani ƙofa tanufa tabuɗe tafice, Allah yabata Sa'a ashe waje ne, haka tafita gidan batare da taga kowa ba, tafiya take tayi batasan inda take saka ƙafarta ba, tayi tafiyan da ita kanta batasan awanni nawa yaɗauke ta ba, sai faɗi tayi ƙasa a sume batare da tasan inda kanta yake ba.
Lokacin da tafarka garin yayi duhu sosai kuma babu wanda yaganta, kasancewar anguwan na masu kuɗi ne zai yi wuya kaga mutum a waje, zuwa lokacin tsananin azaba take ji a cikin ta, a lokacin kuma ta dawo hayyacin ta gaba ɗaya, sai tariƙe cikin ta tana ta kuka tana burgima awajen, tsawon lokaci kafin tayunƙura daƙyar tamiƙe taci gaba da tafiya tana kuka, a wannan lokacin ne Brr. Ibrahim Khalil yazo wucewa yabige ta batare da yasani ba, yana fitowa yaganta yashe a ƙasa da alamun ta sume ne, ɗaukan ta yayi yasaka ta a mota yanufi da ita asibiti, lokacin Dr. Sameer be riga ya tafi ba, shi ya'amshe ta yakira abokin sa Dr. Hashim, babu jimawa kuwa yazo yasoma dubata, duk Brr. Khalil yadamu yakasa zama waje ɗaya sai zagaye yake yi, sai da Dr. Sameer yabashi ƙwarin gwiwa tukun hankalin sa yakwanta
Sai da akayi 2 hours ana duba ta kafin Likitocin dake kan ta su fito, Dr. Hashim ne yayi musu bayanin da yaɗaga musu hankali, sosai suka shiga damuwa jin cewa Coken ne acikin ta, kuma ya kai tsawon lokacin da Yakamata acire mata but ba'a cire ba, don haka har yasoma narkewa yataɓa mata hanji dole sai anyi mata aiki an cire, sannan kuma sai anyi mata dashen hanji, Khalil ne yasaka hannu aka shiga da ita Theater, tsawon awa biyu kafin aka fito da ita, sai alokacin suka tafi gida bayan da suka tabbatar komi normal.
Watan ta biyu kafin tafarfaɗo, kuma duk alokacin tana ƙarƙashin kulawan Khalil ne tare da Doctor Hashim da Doc. Sameer, sosai take jin jiki duk da an samu nasaran aikin, ko magana bata iyayi bare tashi, komi sai dai ayi mata
Khalil sosai yadamu da halin da take ciki haka kawai yake jinta tamkar ƙanwar sa, kuma yayi imani cewa yarinyan zaluntar ta akayi, don haka alokacin ne yasoma bincike akan ta, kuma ya yi ƙudirin sai ya ƙwato mata haƙƙinta, tsawon wata yana bincike sannan yagano inda take zaune, wato gidan Alh. Mubarak, a ranan da yashirya yaje yayi hira da me gadi har yagano labarin ta a wajen sa, bayan ya dawo ne a ranan wasu suka zo kashe ta cikin asibitin, abinda be sani ba Khalil yana tafiya me gadin yasanar da Alh. Mubarak, tunda dama neman ta ake yi ana tunanin ɓata tayi, Dr. Sameer ne yashigo cikin ɗakin lokacin da mutumin da zai kashe ta yaso kashetan, shine yagudu batare da yayi abinda yazo yi ba, wannan dalilin ne yasaka suka yanke shawaran afitar da ita daga asibitin, don sun gano kasheta ake da ninyan yi, Shine Khalil yakaita gidan Baaba Talatu, anan akaci gaba da kula da ita sannan shi kuma yaci gaba da bincike kan lamarin, har sanda yagano komi akan Alhj. Mubarak tare da Doc. Sabit, babu ɓata lokaci yashigar dasu ƙara zuwa kotu
A lokacin hankalin su Ahj. Mubarak be wani tashi ba, domin acewar su babu yanda za'a yi akama su da laifi, sannan kuma su ɗin masu hannu da shuni ne waɗanda sukayi fice kuma kowa yasan halin su, babu yanda za'a yi yayi nasara, but zaman farko a kotu sai ido yaraina fata, yanda Brr. Khalil yayi takawo shaidu hakan ba ƙaramin ɗaga musu hankali yayi ba, anan Alƙali yabada hutun wata ɗaya da sati biyu bayan da kowa yagama kawo shedun sa, kuma ya bada umarnin ranan da za'a dawo yakasance Nazeefa ta hallara, sakamakon hujjojin da Brr. Khalil yaba da ne aka tsare Ahj. Mubarak tunda an gano yana da laifi
Wannan shari'ar ya ja cece kuce sosai a wajen jama'a, sosai mutane suka ƙosa suga ranan da za'a dawo don yanke hukuncin, kuma duk alokacin mutane basu yarda cewa Alh. Mubarak yana da laifi ba, sai dai mujira ranan dawowan kamar yanda yakasance gobe da ƙarfe 02:00pm.
_Hmmm masu karatu ku ma sai kushirya don jin Me zai wakana a Court._ 😅
_ina gayyatar Masoya Brr. Ibrahim Khalil da Nazeefa, kuzo kugani da idanun ku._💃💃💃💃
[9/29/2020, 12:44 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*