Header Ads
Showing 78001 words to 81000 words out of 132567 words

Chapter 27 - BARRISTER IBRAHIM KHALIL Complete Document by Nafisa Isma'il Lawal.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jul 2024

1273

Ads at the middle of Article

fito lectures




Tafiya suke yi suna hira ɗaya daga cikin su tana basu labarin gwaraman da akayi a anguwan su, sai dariya suke yi sabida yanda me basu labarin ta dage tana nuna yanda matar take ɗaukan mijin ta tana tiƙa sa da ƙasa






Daga bayan su can ɗan nesa kaɗan Halwa ce ke tafiya tana latsa wayan ta, tun daga inda take tana jiyo dariyan su sai dai hankalin ta baya kansu sai faman neman layin Drever take yi




Yau yayi late be zo ya ɗauke ta ba shiyasa take sake kiran sa taji inda yake, yana ɗagawa yace mata "gashi nan yanzu zai shigo school ɗin"




Tsayawa tayi a wajen har sanda tahango shi ya shigo cikin makarantan, sai tanufi wajen shi tana ɗaga masa hannu, shima ɗin ya ganta don haka yatsaya tahau yaja yayi reverse suka nufi bakin Gate




Lokacin su Zainab har sun kusa fita motan tazo tawuce su, har alokacin sai faman dariya suke yi, ahaka suka fita cikin school ɗin cike da nishaɗi




Suna fita sauran friends ɗin ta duk suka dare biyu daga ciki sukai musu sallama suka ci gaba da tafiya sabida babu nisa da gidajen su, ɗaya ce tahau keke napep tatafi aka bar Zainab ita kaɗai tunda ba hanya ɗaya zasu bi ba




Tana nan tsaye wajen sai ga wata dalleliyan mota ta faka a gaban ta, tunda takalli motan sau ɗaya takau da kanta tana kicin-kicin da fuska




Fitowa yayi daga cikin motan yana kallon fuskarta, ɗan taku uku yayi ya'iso gaban ta, murmushi yasaki yace




"Plz Zainab don Allah kihau in Kai ki gida, yau rana ɗaya dai kiyi min wannan alfarman".




Tsaki Zainab taja batare da ta kalle sa ba, ji take yi idan har tatanka masa zuciyarta zata iya bugawa sabida tsaban jin haushin sa, don haka batace komi ba tajuya taci gaba da tafiyan ta




Nura kallon ta kawai yake yi har sanda taɗan yi nisa sannan yanufi motan sa yashiga yabi bayan ta




Kullum ranan duniya sai yazo domin ta amma bata taɓa masa kallon arziƙi ba, kuma shi be taɓa gajiya ba sabida yanda yake jin ta cikin ransa, duk wulaƙancin da zata yi mishi zai iya jurewa idan har zai same ta, yana matuƙar ƙaunar ta fiye da tunanin mutum




Yana biye da ita abaya har sukai nisa, gashi ta kasa samun keke napep duk rana sai faman gasa ta yake yi




Shi kuwa gab da ita yazo suka jera yana mata magiya ta cikin motan amma firr Zainab taƙi kallon sa bare tatanka masa




Gajiya tayi kawai tasamu acaɓa tahaye tunda babu napep ɗin




Nura yana kallon ta har tahau suka tafi yabi bayan su, duk inda me machine ɗin yabi nan shima yake bi har suka kawo ƙofar gidan su Zainab ɗin tasauka tamiƙa ma me machine ɗin kuɗin sa tajuya tashige gida batare da ta amshi canjin ta ba, don baƙin cikin ganin Nura ƙofar gidan su ya hana ta ma tsayawa




Ajiyan zuciya Nura yasauke yana bin ƙofar gidan da kallo, ya jima acikin motan.. shi be tafi ba shi kuma be fito ba, sai da yashafe mintuna 20 zaune anan kafin yafito yana rufe motan




Kalle-kalle yai tayi sai daga baya yahangi yaro yakira sa yace masa yashiga ciki yakira masa Zainab




Da gudu yaron yashige gidan








...... ....... ....... .....
Zainab tun shigan ta da tayi sallama taji babu umma sai tashiga ɗaki kawai ta'ajiye jakar ta tare da gyalen ta tafito tashiga kichen taɗauko abincin ta




Zama tayi anan farandan ɗakin su taci abincin tagama, miƙe wa tayi takai coolarn wajen wanke-wanke taɗibi ruwa a buta tashiga Toilet.




Tana cikin Toilet ɗin tajiyo sallaman yaro, bata amsa ba har sanda tafito tabi yaron da kallo, bata raba ɗayan biyu Nura ne ya'aiko shi




Ai kuwa bata gama tunanin zucin ta ba yaron yace




"Wai ana kiran Zainab a waje".




Ajiye Butan hannun ta tayi tazauna kan dutse a bakin Toilet ɗin, sannan takalli yaron tace




"Je kace masa baza ta zo ba".




Babu musu kuwa yaron yajuya yatafi don isar da saƙon ta






Sosai baƙin ciki ke ɗawainiya da Zainab, ta rasa wani irin maye ne wannan mutumin, ko kaɗan ita bata ƙaunar sa a ranta bata jin kuma zata iya son sa ko anan gaba, sa'ar ta ɗaya Umma bata nan amma da dole sai ta saka ta fita




Shiyasa take roƙon Allah aranta Allah yasa yatafi kafin Umma tadawo




Ta soma alwala kenan yaron yasake dawowa yace




"Wai yace don Allah tazo zai bata saƙo ne".




"Dan ubanka wuce anan gidan". Zainab tafaɗa cikin tsawa tana zazzare ma yaron idanu




Da gudu kuwa yasheƙa yafice har da waigen ta






Baƙin ciki da ƙunci ne suka taru mata iya wuya, ta rasa me za tayi ma Nura don huce takaici




Ƙyalla idon ta tayi tahangi taɓarya, dasauri tatashi tanufi wajen taɓaryan taɗauka tayi hanyan fita a fusace




Yau dole ne sai ta kawo ƙarshen zuwa wajen ta da yake yi.














.










_hahaha Fans kar ku damu ba daku zata rotsa ma kai ba, Nura kawai tanufa banda ku._








_Kuyi haƙuri da wannan babu yawa, aiyuka sun yi min yawa shiyasa nayi muku ɗan kaɗan._






_kar ku manta da Comments ɗin ku shi ke ƙara min ƙwarin gwiwa._






_Ina jiran Comments ɗin ku shin ayi maganin Nura ko ya? Nasan da yawa haushin sa kuke ji bayan kuma be muku komi ba bawan Allah._😅
[11/24/2020, 2:50 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️




*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_




*بسم الله الرحمن الرحيم*






*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```


*JIKAR LAWALI CE*✍️


*Wattpad: UmmuDahirah*👈




*\F.W.A📚/*


```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._


*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._




*BOOK TWO*




.


_______________________________


*CHAPTER Seven*


________🎓Tana shiga zaure sukaci karo da Umma dole taja tatsaya tana ƙifƙifta ido




Umma da tafiddo ido waje tana kallon Zainab ɗin da taɓaryan dake hannun ta tace "na shiga uku ni Jummai me zan gani haka Zainab? Ashe dama baki da mutunci dan ubanki? Yanzu abun naki har ya kai kifita da taɓarya kije wajen Nura? To me kike shirin aikatawa kenan?"




Turo baki Zainab tayi tana sosa kai, sai kuma tajuya dasauri tayi ciki tana jefar da taɓaryan




"To dan ƙwal uwar ki zo ki wuce kije wajen shi". Cewar Umma tana bin bayan ta itama tashiga cikin gidan




"Wlh Umma babu inda zani, nifa nace miki bana ƙaunar sa bana son sa bana son sa, Ni bazan iya son sa ba wlh".




Umma kama haɓa tayi tana kallon Zainab ɗin dake masifa kamar batasan da wa take yi ba




"Zainab Ni Sa'an wasan ki ne ina faɗa kina faɗa? Wlh sai kin fita ko in saɓa miki kamanni, shashashan yarinya mara hankali.."




Kuka Zainab tafashe dashi




Sai umma kawai takama haɓa tana kallon ta




Cikin kukan take cewa "wlh Umma bana ƙaunar sa, koda kuwa be so Halwa ba Ni bana son sa, har cikin raina nake faɗa miki bazan iya auren sa ba wlh".




Sai taja majina tanufi wajen butan ta tazuƙuna tasoma alwala




"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un yanzu Zainab har kin isa in saka ki abu kice baza kiyi ba? Baza ki tashi ki wuce ba yana jiran ki?"




Cikin tsananin ɓacin rai Zainab tace "Umma zan yi sallah ne lokaci na ƙurewa, kuma kinsan illan rashin yin sallan Asar da wuri, yana ɗaya daga cikin sallolin da ake so mutum yakula..."




"Dalla rufe min baki, kiyi sauri ki idar kizo ki wuce".




Zainab bata sake cewa komi ba taci gaba da alwalan ta, sosai take mamakin Mahaifiyar ta akan yanda tasauya lokaci ɗaya akan Nura, duk da tasan Nura yana banka mata kuɗi da kaya amma kuma bata taɓa tunanin zata sauya har haka ba




Tana idar wa tashiga ɗaki tasaka Hijab tasoma sallah, ta ɗau lokaci tana yin Sallah taƙi tasallame sai da Umma tazo tasake mata magana sai faman masifa take mata




Dole Zainab ba don taso ba tamiƙe tafito tafice




Tana fita kuwa taganshi tsaye gaban motar sa, ta rasa wani irin mayen mutum ne wannan




Nura tunda tafito kallon ta kawai yake yi yana murmushi, ko kaɗan be ji haushin daɗewan da yayi a wajen ba tunda Umma tace mishi yajira zata fito, kuma yasan dole zata fito ɗin




Wani mugun kallo Zainab tabuga masa tana jan tsaki taɗau hanya taci gaba da tafiyan ta batare da taƙarisa inda yake ba




Yana kallon ta har taƙule ma ganin shi




Ita kuwa tana shan kwana tasheƙa aguje bata tsaya ko ina ba sai gidan Yayarta Zaituna




Suna zaune ita da kishiyarta suna ƙullin Gishiri sai ganin ta sukayi ta faɗo gidan




"Subhanallah..lafiya Zainab?" Atare suka tambaye ta yayinda Zaituna taƙara da faɗin




"Wa yabiyo ki ne kika shigo haka kamar an jeho ki?"




Zainab da tariƙe gwiwowin ta tayi ruku'u tana numfarfashi ta ma kasa magana




Kishiyar me suna Murjana tace "ikon Allah wai lafiya ko dai gudun fanfalaƙi kika yi ne?"




Bata ce komi ba tanufi wajen randan ruwan su tana sake jan numfashi, ɗiban ruwan tayi tasha kafin tadawo taja kujera ɗan tsuƙuno tazauna agaban su, duk sun tsare ta da idanu suna ganin ikon Allah kuma suna jiran suji abinda yakoro ta gidan da gudu




Sai da taƙara gyara zaman ta tana kallon su tace "wlh daga gida nake.."




Tsaki Zaituna taja tana hararan ta tace "amma kinji kunya wlh, ƙatuwa dake shine kika sheƙo hanya da gudu ga mutane ko kunya ko?"




"To Aunty ki tsaya mana kiji me yakoro Ni, wlh Umma ce tatakura min akan maganar Nuran nan shiyasa na'ari na kare nayo nan".




Dariya Murjana tayi tace "kai wlh Zainab baki da dama, to Ni wai meye laifin Nuran nan kullum kina wahalar dashi? Magana dai taƙi ci taƙi cinye wa".




Taɓe baki Zaituna tayi tace "kema dai kya faɗa, bata da hankali Zainab ko kaɗan, wai inace duk kina wannan abun ne don Halwa?"




"Aunty baza ki gane ba wlh, nifa gaba ɗaya tun sanda yasoma nema na natsane shi, wlh koda ba batun Halwa aciki Ni bazan iya auren sa ba, kullum idan yazo min da nacin nan nasa kullum sake jin tsanar sa nake yi araina". Zainab tayi maganar cike da baƙin ciki




"Aiki ya ganki". Zaituna tafaɗa tana ci gaba da ƙullin ta




Murjana tace "kiyi ma kanki faɗa don Allah, ko wace mace tana burin tasamu masoyi me ƙaunarta amma ke kin samu kina wasa da damar ki, wlh Nura yana son ki tunda kikaga yana jure wulaƙancin nan naki, Zainab babu batun yaudara anan ki karɓe shi hannu bibbiyu tun kafin lokaci yaƙure miki, dama ce tazo miki har gida, idan kuma kikace zaki tsaya tunanin wata to zaki rasa wannan damar taki, ki duba magana ta".




Numfashi Zainab taja, baza su taɓa gane abinda take nufi ba, ita tayi alƙawarin wlh sai dai gawan ta za'a kai gidan Nura amma baza ta taɓa auren sa ba, koda kuwa Halwa ce tazo da kanta tace ta'aure shi, amma a yanzu tarigada ta ƙudurta ma kanta dole ne tasamu saurayi tayi aure ko Allah zai sa yabarta, ada dai bata da burin aure yanzu amma tunda taga abun yazo da haka tasan komi zai iya faruwa




Yanzu ma baza ta koma gidan ba sai dare, sai dai idan ta koma Umma tahaɗiye ta




Hannu tasaka tasoma tayasu ƙulla gishirin batare da tasake cewa komi ba




Su kuma tuni sun sauya zancen ma sun ci gaba da hiran su da suke yi.










.


*__________________________*


*BAYAN WASU WATANNI*


A halin yanzu Saleema tasake samun ciki a karo na biyu, kamar dai wancan haka tasha baƙar wahala watan shi ɗaya yafice bayan da tazubar da jini sosai kamar baza ta rayu ba




A wannan lokacin ne kuma tasan matsalan ta, tayi kuka kamar baza ta dena ba, har sai da iyayen nata sukai dana sanin faɗa mata sabida gudun tashin ciwon zuciyarta




Ita kanta Halwa ta taya ta kukan kuma ta tausaya mata sosai




Sai da tayi jinya na tsawon sati biyu a asibiti kafin a sallame ta






Tun daga ranan kuma Khalil yasoma bata maganin hana ɗaukan ciki batare da sanin ta ba, ita a ganin ta duk cikin drugs ɗin da aka bata ne a asibiti tunda wani lokacin shi ke bata magungunan, kuma bata taɓa saka wa aranta zai iya cutar da ita ba bare tayi tunanin wani abu, sosai yake matuƙar tausaya mata baya son tasake shan wahala kamar yanda tasha a baya, duk da yana son yara amma hakan shine mafitan da zai iya taimaka mata idan har yana tausayin ta




A sannu a sannu rayuwa taci gaba da tafiya, tun Saleema na damuwa da matsalan da take fama dashi tunda itama tana ƙaunar yara har dai tacire komi a ran ta, ta buƙaci a dawo mata da Husna taci gaba da riƙe ta amma firr Ummi taƙi tunda har yanzu jiya iyau take, yau lafiya gobe ciwo, kuma Ummi tayi tayi takawo mata ƴar aiki but Saleema ta baɗe ma idanun ta toka akan baza'a kawo mata ƴar aiki ba, ita ta saka a ranta duk ƴar aiki tana ƙwace Mijin matar gida ne, shiyasa take jin tsoron a kawo mata ƴar aiki watarana taƙwace mata miji, anan Ummi tace "to tunda baza ta yarda akawo mata me taimaka mata ba dole tahaƙura da rainon Husna har sai taji sauƙi", ba da son ranta ba haka tahaƙura




Khalil na iya ƙoƙarin sa wajen ganin ya taimaka mata ainun, a haka zaman su yaci gaba har zuwa wani lokaci, kuma har a lokacin soyayyar Halwa na nan cikin zuciyar sa sai dai ya binne abun aransa tunda babu yanda zai yi




Ita kanta Halwan abun da take ji akan sa ne har yanzu takasa sakin jiki dashi bare su saba, ko magana zata iya ƙirga iya adadin da yataɓa shiga tsakanin su, sau tari idan tayi tunanin komawa gidan Saleema don ta tayata zama sai ta fasa, bata son ko kaɗan abinda zai sa su haɗa hanya, duk da har yanzu batasan menene musabbabin abinda yasa take jin haka daga gare shi ba, amma ita a ganin ta nesa dashi shine kwanciyar hankalin ta




Har yanzu kuma bata taɓa tunanin yin saurayi ba duk da kuwa ansha biyo ta, amma a ranan farko take taka ma mutum burki




Ummi kanta sai da tazaunar da ita akan tadena koran samari auren nata shine abunda yadace da ita, amma ita Halwa abinda take hangowa tabon da ɗa namiji yayi mata a rayuwa, ta tabbata ko wanene zai so ta idan har yasan da Husna wacce tahaife ta bata hanyar aure ba to zai tafi yabarta, bata son taba ma namiji yardan ta a karo na biyu, tunda wanda yafi kowa sanin ta a duniya kuma yafi kowa sanin me zata iya aikata wa ya juya mata baya akan hakan, tayi imani ko waye ma hakan zai mata, shiyasa maganin kar ayi kar a fara, ta yarda zata ci gaba da rayuwan ta ahaka har ƙarshen numfashin ta, idan har ba Nura bane yadawo gare ta to bata jin zata iya auruwa




A yanzu haka ta shiga aji na biyu, babu abinda tasaka a gaba sai karatu, ko ƙawaye taƙi yarda tayi har yanzu, sai dai mutunci kawai da take yi da wasu daga cikin ƴan ajin su




Har yanzu har gobe tana tunawa da ƙawarta Zainab, sau tari tana tunanin zuwa koda gidan su ne, amma kuma hakan na nufin kamar ta tona ma kanta asiri ne duk ranan da takoma wajen waɗanda suka santa, kuma hakan na nufin zubar da mutuncin su Baba kamar yanda suka guda tun farko, wannan dalilin yake saka wa tafasa zuwa.






.




*____________________________*


Baku tambaye Ni labarin Haris ba?




Tunda baku tambaya ba nima bari in ƙyale KU, byeeee👋👋👋 sai ajiman ku ko in CE sai gobe.😅🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️
















_kar ku manta don Allah 🙏🏼ku danna Vote sannan kuyi comments don jin ra'ayoyin ku, na gode._
[11/24/2020, 3:14 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️




*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_




*بسم الله الرحمن الرحيم*






*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```


*JIKAR LAWALI CE*✍️


*Wattpad: UmmuDahirah*👈




*\F.W.A📚/*


```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._


*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._




*BOOK TWO*




.


_______________________________


*CHAPTER Eight*


________🎓Haris ɗan wani babban attajiri ne ɗan siyasa, yanzu haka yana riƙe da kujeran Minister, shi ɗaya ne ɗa wajen iyayen sa duk da iyayen Familyn su ɗaya ne kuma babban Family ne dasu




Ya taso cikin gata sosai, babu abinda yarasa a rayuwan sa, wannan dalilin ne yasa yake taka duk wanda yaso yakuma hukunta duk wanda yake ƙi, sabida yana da ɗaurin gindin mahaifin sa don ko kaɗan baya ganin laifin sa




Haris yana da son mata da yawa sannan kuma yana da farin jinin ƴan matan, su da kansu ƴan matan suke kawo kansu wajen sa don yayi amfani dasu yabiya su kuɗi, duk da sau da dama suna kawo kukan su akan ya taimaka ya aure su amma shi a ganin sa babu macen da ta'isa yaso ta, shi dai kawai ya san mata a wajen sa su biya masa buƙata ne yajefar dasu don basu da wani Amfani




Ana cikin haka kwatsam yazo giftawa ta hanyar makarantar su Halwa yakusa bige ta, tun a lokacin da yaganta yakamu da tsananin kaunar ta har yana jin koda zai yi aure to babu shakka ita zai aura, duk da alokacin mafi rinjaye na zuciyarsa sha'awar ta ce, amma kuma ita kaɗai ce yake iya mata kallon wacce zata iya kasancewa matar sa anan gaba




Sai dai abinda be sani ba Halwa ta mutu a ƙaunar Nura a lokacin, duk da alokacin yaso yanuna mata kuɗi da gadara, amma da yaga yarinyan tana da taurin kai babu yanda zai yi yasame ta sai yakoma yana bin ta talalama




Sai kuma tsautsayi yagifta a ranan da Halwa tamare shi, wannan dalilin ne yaɗau

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads