Showing 93001 words to 96000 words out of 132567 words
Chapter 32 - BARRISTER IBRAHIM KHALIL Complete Document by Nafisa Isma'il Lawal.txt
yake ba'a rufe duka ba, har ya saka hannu zai sake tura wa yashige sai yaji maganar Halwa wanda yasaka dole ya ɗan dakata yana sauraron su
"Ki dena ma maganar Haris a yanzu, yanzu na rigada na cire wannan burin a raina, Ni ce Mahaifiyar Husna kuma na baki ita har abada wlh, kin san kuma be da iko da ita tunda dai ba aure aka ɗaura mana dashi ba, musulunci ya yarda idan an haifi yarinya ba da aure ba uwa ke da alhakin riƙe ta".
Rungume ta Saleema tayi cike da farin ciki tace "gaskiya na gode ƴar uwata, kin bar burin ki akaina duk sabida ki faranta min bansan da me zan saka miki ba, Allah yabiya ki.."
Katse ta Halwa tayi da faɗin "Ni fa nace miki bana son godiya, idan na baki Husna ba ke ne zaki gode min ba, Ni ce zan gode miki, don haka ki dena min godiya don Allah".
Sakin ta Saleema tayi tana murmushi tace "ai bazan dena miki godiya ba wlh, kin bani Husna sannan kina shirin haifa min wani ɗan, idan ban miki godiya ba me zan miki?"
Halwa tashi tsaye tayi tana yamutsa fuskarta tace "kinga Ni bani da lokacin wannan yanzu, bari inje inyi wanka in shirya in tai school, tunda yau Pepper ɗaya zan yi insha Allahu zan biya gida nagaishe da Ummi".
Zaro ido Saleema tayi tace "me zaki je yi bayan kin san tace kar ki so ma ki je? Babu ruwana wlh".
Dariya Halwa tayi tace "to na fasa".
"Da dai yafi miki, banda ma kinibibi muna haɗuwa fa a Hospital salon dai ki ja mana tonon silili".
Ƙofa Halwa tanufa tana ci gaba da dariyan ta
"Dama tonon ki nake yi in ji me Zaki CE".
Ahankali yaɗaga ƙafafun sa da sukai mishi nauyi yamatsa bakin ƙofan sa yabuɗe yashige
Dai-dai da Halwa ta fito taji ƙarar rufe ƙofan nasa, kallon ƙofan tayi na ɗan seconni kafin taɗauke kan ta tana jan numfashi tare da shaƙan daddaɗan turaren sa da ya mamaye ilahirin wajen
Ɗakin ta tanufa tabuɗe tashige, tana shiga wanka tafaɗa.
***
A hankali ya ƙarisa gaban gadon sa jiki a matuƙar sanyaye, zama yayi yana dafe kansa dake barazanar tarwatse wa sakamakon abinda yaji, be ma san a wani yanayi zai fassara kalaman ta ba
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." yafaɗa a wani rikitaccen murya da dole kasan cewa yana cikin wani yanayi
A duk abinda yafahimta tana nufin kenan ita ɗin karuwa ce, ta haifi Husna ba ta hanyar aure ba, "Why zuciyar sa zatay masa irin wannan gangancin? Meyasaka zata so wacce bata kama ce sa?"
Hannu yaɗaura setting zuciyar sa yana ji tamkar yaƙwaƙulo zuciyar yawanke yagoge duk wani son ta da yataɓa wanzuwa a cikin ta
Sake runtse idanun sa yayi sai ga wasu siraran hawaye sun soma fitowa suna sauka kan dandamalin kumatun sa, wani irin ƙunci me haɗe da raɗaɗi ne yatsaya masa iya maƙogwaron sa, wanda ji yake yi tamkar yahaɗiye zuciya ya mutu sabida tsaban baƙin kishi da yake ji
Tsakiyar gadon yafaɗa yana ɗaura duk ka hannayen sa saman fuskar sa batare da ya buɗe idanun sa ba, shiru kawai yayi yana sauraron bugun zuciyar sa dake fita a wani irin yanayi me haɗe da firgitar wa ga duk wanda yasaurara
Tsawon lokaci yana a wannan yanayin mara daɗi wanda har sai da hawayen fuskar sa suka bushe batare da ya sake ƙwaƙƙwaran motsi ba
Saleema ce taturo ƙofan tashigo kasancewar Halwa da zata fita taje ta sanar mata Khalil ɗin ya dawo, hakan yasa tafito daga ɗaki tazo gare sa
Har taƙariso bakin gadon be motsa ba be kuma buɗe idanun sa ba, yana nan ayanda yake tamkar be san da wanzuwar ta ba, gadon itama tahau tana ɗaura rabin jikin ta kan nashi tace
"Mijina don Allah kayi haƙuri ashe ka dawo bansani ba, na Barka kai kaɗai".
Idanuwan sa yabuɗe waɗanda suka sauya kala ainun, yazuba mata su batare da yace komi ba, kuma babu ko alamun walwala a face ɗin sa
Kallon sa itama take yi cike da tsoro don bata taɓa ganin sa a haka ba, cikin rawan baki tasoma jero masa tambayan "Lafiya me yafaru da kai? Meke damun ka?"
Rufe idanun sa yayi yana haɗiye abinda yatsaya masa a maƙoshi tun ɗazu, daƙyar yaɗaga hannun sa ɗaya yajanye ta a jikin sa yamiƙe da hanzari yana shige wa cikin Toilet
Sai kawai tasaki baki tana bin sa da kallo cike da wani irin baƙon yanayi, tunda take ko kaɗan bata taɓa ganin fushin Khalil ba, ko kaɗan baya da saurin fushi, babu abinda zaka taɓa gani a tare dashi da zaka san ransa a ɓace yake, amma yau kallo ɗaya idan kayi masa zaka san tabbas yana cikin wani hali me wuyan fassara
Tana nan zaune duk ranta a jagule, ƙiris take jira tasaka kuka, gaba ɗaya hankalin ta yayi mugun tashi fiye da tunanin me karatu, gaban ta sai bugawa yake yi tamkar zai faso ƙirjin yafito
Har mintuna 20 suka shuɗe be fito ba, sai kawai tasaki kuka jikin ta na wani irin rawa kamar mazari
Ahankali kukan nata yasoma isa kunnen sa, lumshe idanun sa yayi yana buɗe su a lokaci ɗaya, idanu yatsira ma kansa ta cikin mirror batare da ya sake motsa wa ba, sai da yaji kukan nata na fita da ƙarfi sannan yawanke fuskar sa yanufi ƙofa yabuɗe yafito
Dasauri kamar an tsikare ta ta'isa gaban sa, cikin kukan take cewa "don Allah mene yafaru ka ɗaga min hankali, ban taɓa ganin ka a haka ba me yasame ka?"
Idanu kawai yatsira mata cike da ƙaunar ta aransa, sosai taba shi tausayi yanda tanuna damuwar ta akan shi, hannun sa kawai yasaka yajanyo ta jikin sa yarungume ta sosai kamar zai maida ta ciki, gaba ɗaya ya zagayo da hannayen sa ta bayan ta yana faman shafa mata bayan, cikin sanyin murya a hankali yasoma rarrashin ta
"Shiiiiiiii.. Ya isa menene kuma na kuka? Ke abun kuka baya miki kaɗan ne ko kin manta halin da kike ciki ne..?"
Numfashi yaja kafin yaci gaba
"Babu abinda ke damuna kawai na tuna wani abu ne, amma duk kin bi kin ɗaga min hankalin ki".
Yaƙarike maganar yana ɗago ta daga jikin sa tare da sakar mata lallausan murmushi
Izuwa yanzu ta tsai da kukan nata sai dai kallon sa kawai da take yi tamkar t.v, sosai take hango matsanancin damuwa a fuskar sa da muryan sa wanda shi kansa ya kasa ɓoye hakan
Hancin ta yaja yana faɗin "ki dena saka damuwa haka kinji, bari in Yi wanka ina zuwa".
Sai yajuya batare da ya jira me zata ce ba yashige toilet ɗin
Tana nan tsaye bata jirga ba har sanda yafito
Shi kansa yayi mamakin ganin ta a wajen sabida daɗewan da yayi cikin Toilet ɗin
Matsowa kusa da ita yayi yana kallon ta
"Kina nan tsaye har na dawo?"
Kanta tasauke ƙasa batare da tace uffan ba
Hannun ta yariƙe yajanyo ta jikin sa yasake cewa "wai menene lafiyan ki ƙalau kuwa?"
Murmusawa tayi kafin tagyaɗa masa kai batare da ta furta komi ba, sai kuma tajanye jikin ta tana shirin juyawa tatafi yasake riƙe hannun ta yamaido ta jikin sa
"Ki faɗa min meke damun ki? ko dai.."
Sai yayi shiru be ƙarisa ba illa zuba mata idanu da yayi
Idanun ta tasanya a cikin nasa sai dai baza ta iya juran kallon cikin idanun ba, sai takawar da kai tana cewa "mu je in taimaka maka".
Matse baki yayi kafin yanufi gaban mirror yazauna, tasoma tsane masa jikin sa da towel ɗin da yaɗaura a kafaɗa
Shiru yayi kawai yana kallon ta ta cikin mirror, har tagama masa komi sannan tadube sa tace
"Wani kaya zan ɗauko maka?"
"Ko wanne". Yaba ta amsa a taƙaice
Juyawa tayi tanufi gaban sip ɗin sa tabuɗe tazaɓo masa riga da wando Three qweater, takawo masa har gaban sa sannan tajuya tafice.
Bayan ya gama shiryawa yafito yatarda ita zaune tana kallo
Tana ganin shi tamiƙe tanufo sa tana murmushi
"Kayi kyau".
"Thank you Matata". Yayi maganar yana maida mata martanin murmushin
Dainning suka nufa tayi saving ɗin sa, yasoma ci tana zaune gefen sa, tana so tayi masa hira sai dai yanda fuskar sa har yanzu babu walwala kamar yanda tasaba gani shiyasa tayi shiru abunta
Har yagama sannan suka koma Parlour
Tunda yazauna yaɗau wayan sa yana ta latse-latse wanda a zahiri ba wai komi yake yi ba, ya Bama kansa damar yin tunani ne batare da Saleema ta gane hakan ba, daga ƙarshe ma sai yatashi yashige ɗakin sa bayan ya sanar mata zai je yaduba wani aiki ne
Ita kuma sai tagyara takwanta saman Three sitter da suke zaune taci gaba da kallon ta
Har barci ya soma ɗiban ta Khalil yafito yatashe ta akan taje tayi sallah an kira, shi kuma yafice masallaci.
Lokacin da yafito masjid ɗin yahangi drever na ƙoƙarin shigar da mota cikin gidan, yana isowa yashiga gidan dai-dai itama Halwa ta fito cikin mota, ganin sa sai tatsaya jiran sa
Shi kuwa sai yaɗauke kai tamkar be ganta ba tare da ɗaure fuska tamau, ta gaban ta yazo yawuce be kalle ta ba, sai tayi saurin cewa
"Barka Yaya Khalil".
Tafiyan sa yaci gaba da yi batare da ya amsa ba, yanufi Garden ɗin gidan
Halwa jiki a sanyaye tabi bayan sa da kallo yayinda tanufi cikin gidan, bata bar kallon sa ba har sai da takusa cin ƙasa sabida tuntuɓen da tayi, sannan ne tadawo da nutsuwar ta jikin ta tabuɗe ƙofa tashige.
.
_plz kuyi comments da share sannan ku danna Vote._
[12/5/2020, 3:34 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Sixteen*
________🎓 Ɗakin Saleema tashiga nan taganta tana nannaɗe dadduma alamun ta idar da Sallah
"Oyoyo Maman Baby". Saleeman tafaɗa tana kallon ta fuskar ta cike da fara'a
Murmushi Halwa tayi taƙariso tazauna kan sofa tana faɗin "washh na gaji da yawa".
Ajiye dadduman tayi tazo tazauna kusa da ita
"Lallai kam ki ce zan yi tausa yau kar Baby yayi fushi damu".
Dariya Halwa tayi
"To ya jarabawan yayi sauƙi dai ko?"
Halwa tace " alhmadulillah komi normal ƴar uwa".
Saleema tace "masha Allah haka nake son ji, ya Baby be dai takura miki ba ko?".
Miƙe wa Halwa tayi tana bata amsa "to ga dai shi nan duk yabi ya ishe ni ya hana Ni saƙat yau".
Saleema marairaice fuska tayi tace "eyya sister Baki bashi abinci bane, i know kin bar shi da yunwa, muje yanzu ki bashi kar yasoma kuka".
"Ai kya bari nayi sallah ko?" Halwa tace tana dariya
Kafin tanufi hanyan ƙofa
Saleema ma miƙe wa tayi tabi bayan ta, suka fito tare Saleema tana faɗin
"Kiyi sauri sister Plz".
Halwa bata ce mata komi ba illa dariya da take mata tashige ɗakin ta, ajiye jakan ta tayi tacire Hijabin ta tashiga Toilet, alwala taɗauro tafito tashimfiɗa sallaya tamaida Hijabin ta tayi sallah, tana idar wa tazare Hijab ɗin tafita parlour
Lokacin Khalil ya shigo suna zaune shi da Saleema kan Two sitter, yayinda shi kuma yake latsa wayan sa
Ƙariso wa wajen tayi tana shirin zama Saleema tayi saurin cewa
"Sister je ki ɗibo abincin mana".
Yamutsa fuska Halwa tayi tazauna sannan tace "wlh bana jin yunwa fa, kuma ban ce miki kukan yunwa yake min ba".
Saleema kallon Khalil tayi tace "kana ji ko Ya Barrister, wlh sis sai ta haifa mana yaro ramamme ko kaɗan bata son bashi abinci".
Khalil be ɗaga kai ba bare yayi magana ba
Hakan yasa Saleema tasake kallon Halwa dake kallon Khalil tana jiran jin me zai ce, don dama sun saba irin hakan kuma yana saka musu baki, amma yau saɓanin tunanin su be tanka ba
"Sister don Allah kije ki ɗibo abinci, baki ji me Ummi tace miki bane?"
Miƙe wa Halwa tayi tana nufan dainning tace "to bari dai in ɗibo shikenan ko?"
Dariya Saleema tayi tana faɗin "shikenan wlh, sai kuma inga kin cinye".
Ɗago kai yayi yazuba mata idanu na tsawon soconni kafin yalumshe su yana jin wani baƙin ciki na ƙara shigan sa
Ji yake yi tamkar yaɗauke ta yakaita a cire cikin, kwata-kwata yanzu baya ƙaunar cikin kamar yanda yake jin son sa a baya, tunda a yanzu ɗin zai fito ne ta ƙazantar zina, "shikenan shi kuma yana ji yana gani za'a haifa masa yaro da dattin zina?"
Halwa na dawowa wajen yamiƙe yanufi ɗakin sa batare da yace komi ba
Saleema tabi bayan sa da kallo har yashige ɗakin sa, kafin tasauke ajiyan zuciya tana maida idanun ta kan Halwa wacce a yanzu ta lula duniyar tunani
Sosai taga damuwa akan fuskar sa wanda kuma yahaddasa mata rashin jindaɗi sam, sun rigada sun saba a ɗan kwanakin nan ko batay masa magana ba sai yayi mata, kuma kullum sai ya tambayi lafiyan Babyn sa, shiyasa da taganshi be tanka ta ba hakan be mata daɗi ba
"Sister yau kamar wani abun na damun Barrister ko baki lura da hakan ba?" Saleema takatse mata tunanin ta da faɗar hakan
Idanun ta tamurza tana kallon Saleeman tare da ƙirƙirar murmushi tace "Haka ne sister nima naga sauyi a tare dashi, but ki bashi lokaci zai koma normal tunda kinsan ba halin sa bane, kar ki ce zaki saka damuwa a ranki kinji?"
Murmusawa Saleema tayi tana gyaɗa kanta, sai kuma tace "yauwa Sister na gode har naji daɗi wlh, Allah ya yaye masa damuwar sa".
"Amin". Halwa ta'amsa mata tana saka abinci a bakin ta
Daga nan hira suka ci gaba da yi cike da nishaɗi.
****
Tun daga ranan kuma sai yazamana Khalil ya dena kula Halwa, ita kanta tuni ta fahimci hakan, idan har ya amsa gaisuwar ta daga hakan babu maganar dake sake shiga tsakanin su
Wannan dalilin ne yasaka itama ta dena shige masa kamar da, duk da abun na matuƙar damun ta aranta amma kuma ta danganta hakan da sabawar da sukayi ne a kwanakin baya, yanzu kuma ya zo ya dena mata magana.
Fannin Khalil shi kuma duk yayi hakan ne sabida son cire ta aran sa, amma kuma tamkar ƙara masa wutar ƙaunar ta ake yi, ya rasa ya zai yi duk da ko kaɗan baya ƙaunar wani alaƙa yashiga tsakanin su, koda yaushe babu abinda yake tuna wa a ransa illa kalaman ta, hakan na ɓata masa rai matuƙa
A yanzu kuwa tuni ya sake rungume matar sa wanda yasan ita kaɗai ce kawai zai iya zama da ita, tunda wacce zuciyar sa ke so bata kama ce sa ba, soyayya tsantsa yake nuna ma Saleema wanda a yanzu ita kanta tasan da banbanci dana Da, yanzu sosai yake ƙaunar ta ko kaɗan baya son abunda zai ɓata mata rai
Ita dai Halwa ta zama ƴar kallo ne domin ko a gaban ta haka zai zaƙe yanuna mata soyayya ko a jikin sa, don haka wani lokacin in dai akwai shi a wajen ta gummaci tashiga ɗaki tazauna ita kaɗai, da tazauna tana ganin abinda ke ɗaga mata hankali yana saka ta tunani tare da hana ta ishashshen barci
Har yanzu ba wai ta yarda da cewa zuciyar ta na begen sa bane, wanda bata san cewa tuntuni ta afka kogin ƙaunar sa ba, kuma ko kaɗan bata taɓa kawo hakan a ranta ba, tunda babu ta yanda za'a yi ta auri Mijin Saleema wacce ta taimaki rayuwan ta, tabbas idan hakan yafaru da ita ta gummaci ta mutu da ƙaunar sa amma baza ta taɓa ba ma zuciyarta damar wannan tunanin mara amfani ba.
Haka kwanaki suka shuɗe wanda har Halwa ta gama jarabawan ta an yi musu hutu
Kwanaki sun ci gaba da tafiya haka satikai yayinda aka tasar ma watanni, gashi yanzu har sun koma hutu sun shiga aji na uku
Ta ci gaba da rainon cikin ta yayinda yake ƙara girma, sosai cikin yake da girman mamaki wanda duk wanda yagani sai ya tausaya mata sabida tsaban girman sa, gashi ya saka ta ta kumbura ainun, kuma tun sanda yashiga wata na tara ta dena lafiya, yau ciwo gobe lafiya, tuni ta jingine karatun ta a gefe har sai sanda Allah yasauke ta lafiya
Shi kansa Khalil yanzu ba ƙaramin tausayi take bashi ba, duk da har a yanzu ba wai magana na shiga tsakanin su bane, idan ko kaji magana me tsawo ya haɗa su sai dai akan cikin ne
Tun farko shi ke kai ta awon cikin har yau kuma be fasa ba, wani lokacin su je da Saleema wani lokacin kuma su biyu suke zuwa.
Yau ma ɗin gaba ɗaya tare suka shirya zasu je asibitin, kasancewar yau ɗin Halwa tatashi jikin babu daɗi sosai, duk da a gobe ne Yakamata su koma Hospital a duba ta amma kuma Khalil ɗin yace su shirya su je yau
Saleema ke riƙe da ita har zuwa wajen motan, tabuɗe mata tashiga daƙyar sannan itama tashiga
Khalil na zaune cikin motan yana kallon su ta cikin mirror, sai da Saleema tarufe motan sannan yasaki ajiyan zuciya yana tada motan yanufi bakin Gate
Me gadi ya wangale masa Gate ɗin yafice da hanzari
Waya Saleema taɗauka takira Ummi
"Ummi ga munan zuwa asibitin".
"Subhanallah.. me yafaru ne ko haihuwar ne?"
Girgiza kanta Saleema tayi kamar tana kallon ta tace "a'a Ummi jikin ne dai babu daɗi shine zamu je".
Ummi tace "to gashi kuma yau ban samu zuwa ba naje duba jikin Sultan baya jindaɗi, amma idan kun ƙarisa sai ki nemi Sister A'isha ta duba ku".
"To Ummi ki gaishe da Aunty, Allah yabashi lafiya".
Daga haka sallama suka yi tasaka wayan a jaka, sannan takalli Halwa dake jingine da kanta jikin kujera ta rufe ido ruf
"Sannu Sister". Saleema tafaɗa kamar zatay kuka
Buɗe idanun ta tayi tasakar mata murmushi tana gyaɗa mata kai don baza ta iya magana ba sabida yanda take ji.
Koda suka