Showing 33001 words to 36000 words out of 132567 words
Chapter 12 - BARRISTER IBRAHIM KHALIL Complete Document by Nafisa Isma'il Lawal.txt
ina so muhaɗu ne kawai, coz akwai tambayan da zan maka".
Be ce mata komi ba sai dai ƙure ta da idanu da yayi, yana jiran abinda zatace
"An bani labarin kuna Shari'a da wani Alhaji Mubarak mai kuɗi, and nan da five days zaku koma Court, shine zan iya zuwa muyi hira akai, ina nufin ina son nasan komai". Taƙarike maganar tana ɗan kwantar da murya tare da ƙifƙifta idanu
Shiru yayi still har yanzu idanun sa akan ta, sai tasake cewa
"Please kaji?"
"Ok". Yafaɗa ataƙaice yana ɗage kafaɗa
"Tom gidan ka zamu je yanzu ko?" tayi maganar cike da zumuɗi
"No kibari zuwa gobe sai kizo".
Daga haka yayi gaba, ita kuma tatsaya nan tana kallon shi har yashige, sai tasaki murmushi tanufi wajen gidan su tatsaya, dama abinda yafito da ita kenan shan iska, a cewar ta gidan yayi mata zafi, tana nan tsaye tana kallon tsare-tsaren gidajen mutane tana tunane-tunanen ta, wayan ta yasoma ringing, cirowa tayi cikin aljuhu takalli fuskar wayan, sunan HONEY ne yafito ɓaro-ɓaro hakan yasaka tasaki murmushi tana amsa call ɗin, tajuya tashige gida.
........ ........... ..........
Washe gari wajen ƙarfe 03:30pm. Kausar tashigo gidan Khalil, yau tana sanye cikin wata doguwar riga ce mare nauyi red colour, sai ɗankwalin shi da tayafa akan ta kawai, tansaya Hill shoes a ƙafafun ta, tana riƙe da wayan ta iPad fara, nocking tasoma yi amma shiru, hakan yasaka taci gaba da yi babu ƙauƙautawa, tafi minti goma a wajen tana nocking, sosai tagaji but kuma taƙi tafiya
A ciki kuwa tun da yadawo aiki yakwanta barci, sama-sama yake jiyo nocking ɗin daga ɗakin sa, ahankali yabuɗe idanun sa yana sake jiyo nocking ɗin, tsaki yaja yatashi zaune yana miƙa, sai da yafi 3min a zaune kafin yamiƙe yafito daga shi sai baƙar singlate ajikin sa, da gajeren wando yellow, ƙofan yabuɗe suka haɗa ido da ita, dasauri tasad da kai ƙasa tana jin matsananciyar kunya, cikin sanyin murya tace
"Sorry ban san kana barci bane, bari in koma zan dawo".
"Kishigo". Abinda yafaɗa kenan yajuya yashige ɗakin sa
Sai da taji ƙaran rufe ƙofa tukun taɗago kan ta, leƙawa tasoma yi kafin tashiga, saɗaf-sadaf haka take tafiya kamar wata munafuka, har ta'isa kan kujera tazauna tana kallon parlour'n, sosai tsarin gidan yayi mata kyau, har yaso yafi nasu duk da su ma nasu yana da kyau, but wannan komi kakalla kasan ba ƙaramin abu me tsada bane, sosai aka kashe kuɗi cikin parlour'n duk da ba wani kaya ne a ciki ba, tana nan tana kalle-kallen ta kamar wacce bata taɓa ganin irin sa ba, yafito sanye da riga me ruwan zuma da zane-zanen fari ajiki, sai wando Three qweater fari, ƙariso wa yayi yazauna a kujeran dake facing ɗin ta yana kallon ta, ɗago kai tayi itama tana kallon shi tace
"Ina yini?"
"Lafiya". Ya'amsa ataƙaice yana jingina bayan sa da kujera yalumshe idanu
Ita kuma sai tatsaya tana kallon shi cike da burgewa, komi nasa me kyau ne, yana da matuƙar kyau da kwarjini, babu macen da zata gan shi batayi fatan samun shi ba, buɗe idanun sa yayi yasauke a kan ta, sai tawayan ce takau da kai
Yace "me zaki sha?"
Sai tamaida idanun ta kan sa, kamar bashi yayi maganan ba
"I'm ok". Tace dashi tana mayar da idanun ta kan wayan ta da taɗaura saman jikinta, tasoma latsawa kana tace
"Ko zamu iya farawa?"
"Ok".
Daga nan yasoma bata bayani akan komi, har zuwa sanda suka gama yamiƙe yanufi hanyan kichen, wata iriyan yunwa yake ji, komi be saka a cikin sa ba tun tea ɗin safe, kuma da yadawo barci sosai yarufe masa idanu sakamakon jiya be yi ishashshe ba
Yana tsaye cikin kichen ɗin yana ƙoƙarin ɗaura tukunya, yaji muryan ta a bayan sa
"Me zaka dafa?"
Juyowa yayi yana kallon ta, don be tsammaci zuwan ta ba, murmushi tayi masa tatako ta'iso wajen sa tana faɗin
"Kaje sai in yi maka girkin".
Tayi maganar tana ɗaura hannun ta saman tukunyan tana gyara mishi zama
Babu musu kuwa yajuya yatafi, be san meyasaka yarinyan take son shige masa ba, but ko kaɗan ba ta bashi haushi sai burge shi da take yi, yana nan zaune a Parlour yana kallo har tagama tazubo mishi, a gaban shi ta ajiye saman Centre table tace
"Bismillah ko". Tayi maganar tana kallon sa da murmushi a face ɗin ta
Shima kallon ta yayi sai yakalli abincin, taliya ne me manygaɗa da yaji cUrry da yankakken ƙwai a sama, murmushi yasaki yace
"Thank you, kema ki zubo naki kici".
Yarfe hannun ta tayi tace
"No ni na ƙoshi, ina sauri akwai inda zan je".
Gyaɗa mata kai kawai yayi, sai tajuya tatafi shi kuma yabi ta da kallo, sai da takai bakin ƙofa tajuyo tana kallon sa taɗaga masa hannu sannan tafice.
[9/23/2020, 7:28 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 25*
*FEW DAYS*
"My dear kiyi sauri Kar kiyi late kuma?"
Halwa dake cikin ɗaki cikin sanyin murya tace "to Yaya ga ninan".
Fitowa tayi riƙe da Bairo a hannun ta tana kallon yayan nata, shima kallon ta yake yi cike da tausayin ta, gaba ɗaya duk ta rame sabida zazzaɓin da yasako ta agaba kwana biyu, tayi haske kallo ɗaya zakayi mata kagane sosai take cikin ciwo, itama Mama dake zaune kallon ta tayi tace
"Ni kuwa idan ba yazama dole bane Halwa a fasa zuwa makarantan nan mana, kinga yanda kika yi kuwa? Ba fa sauƙi kika ji ba?"
Kallon Maman tayi kawai tana marairaice fuska kamar zatayi kuka
Nura yace "Mama wannan jarabawan fa tana da muhimmanci tunda na fita ne, haka nan zata lallaɓa tayi har su kammala, kinga jiya ma taje tayi tadawo lafiya, zaki ga sauran ma kamar yanzu ne har an gama".
"Um um Nura, yau kaduba kagani sosai take jin jiki ko abinci ta kasa ci, ga wahalan da zataje tasha, me zai hana abari wani shekarar sai tarubuta".
Nura yace "kai Mama har shekara sai tayi ta zama agida? Kema kinsan halinta ba yarda zatayi ba".
Halwa tace "Mama ki dena maganar nan ma, kuma Ni haka nan zan je in zana jarabawa ta, sai dai in ciwon ya kwantar dani ne amma banga abinda zai hana ni zuwa ba".
Murmushi Nura yace "to kin ji dai".
Kaɗa kai Mama kawai tayi tace "ai shikenan Ni dama tausayin ki nake ji, yanzu ku hanzarta kutafi kar lokaci yaƙure".
Fita suka yi, A mashine ɗin Abokin Nuran yakai ta har cikin makaranta, yasauke ta a bakin ajin su.
Bayan kamar mintuna 20 aka zo raba musu pepper, lokacin ne kuma sosai jikin Halwa yayi tsanani, jikin ta sai kakkarwa yake yi zazzafan zazzaɓi yarufe ta, kasancewar mutum ɗaya-ɗaya ake zama a sit shiyasaka babu wanda ya lura da ita, tana can kusa da baya ajikin bango ta takure waje ɗaya, sai takifa kan ta a table tana hawaye, ita kan ta takasa jure yanayin da take ji, sai da Wani Malami yazo miƙa mata Pepper yakira sunan ta
"Halwa lafiyan ki lau kuwa? Za'a yi jarabawa kina kwance".
Ahankali taɗago kan ta tana ƙanƙame jikinta, face ɗin ta duk hawaye, kuma sai rawan ɗari take yi
"Subhanallah.. baki da lafiya ne?" Malam ɗin yafaɗa yana kallon ta
Gyaɗa masa kai tayi don takasa magana ma
"To yanzu ya za'a yi kenan? Zaki iya yin jarabawan?"
Shiru tayi bata iya cewa komai ba, su kuma ƴan ajin yawancin su hankalin su na wajen, har da Zainab aciki, duk tausayin Ƙawartan ya kamata, ɗaya daga cikin Malaman dake tsaron su yace
"Ku me kuke kallo ne baza kuyi abinda ke gaban ku ba?"
Sai kowa yamayar da kan sa ƙasa suka soma duba peppern, Malam Isma'il dake can bakin ƙofan yace
"Ai kabar su Malam Kamal, time na cika amsa zamuyi mu wuce".
Malam Jamilu dake tsaye har yanzu kan Halwa still yace da ita
"Halwa ko dai bazaki iya bane? In ciwon yayi tsanani kije ki amso magani kisha kinji?".
Cike da ƙarfin hali tace "zan iya Malam".
"Ok to gashi".
Aje mata yayi a gaban ta, yaja gefe nan yana kallon ta tare da kula da waɗanda suke wajen, ita kam ahankali tajanyo pepern ta'aza Bairo akai, tayi shiru ta kasa rubuta komi, sai da tayi kusan mintuna 5 kafin tasoma rubuta sunan ta daƙyar, bayan ta gama tasoma amsa Questions ɗin, Number One taɗauka tafara dashi, ahankali tatsayar da hannun ta daga rubutun da take yi tana runtse idanu, wannan karon jikinta sosai yake rawa har da hannun ta, Malam Jamilu dake tsaye yana kallon ta yace
"Gaskiya bazaki iya wannan jarabawan ba, tashi kije kisha magani, inyaso sai asamo wani yarubuta miki".
"Halwa". Malam Isma'il da yaƙaraso wajen yakira sunan ta
Zuwa lokacin kuka take yi kan ta a ƙasa ta kasa amsawa
Yace "wai meke damunki ne? Ciwon me kike yi sai a amso miki maganin?"
Still shiru babu amsa sai kukan ta dake daɗa ƙaruwa
Malam Jamilu yace "Zainab taso kije da ita tasha magani".
Dasauri Zainab tataso tataho wajen tariƙo Halwa dake langaɓe wa, ta rufe fuskarta still tana kuka, suna fita tasoma sheƙa amai kamar zata amayo hanjin cikin ta, sabida babu komi a aman kasancewar bataci abinci ba, nan da nan hankalin Malaman yatashi suka fito waje suna mata sannu
Malam Kamal yace "gaskiya wannan ciwon be kamata abarta anan ba, yakamata amaida ita gida".
Malam Isma'il yace "Eh haka za'a yi kuwa, tunda nasan gidan su bari inje in kai ta".
Daga haka yajuya dasauri yanufi inda suke parcking yaburgo mashine ɗin sa yataho wajen, da taimakon Zainab aka ɗaura Halwa akan mashine ɗin, zuwa lokacin duk ta galabaita bata ma iya tsayuwa
Malam Jamilu yace "Zainab kihau bayan ta kuje tare, sai ku dawo tare da Malam Isma'il".
"To Malam". Cewar Zainab kenan, kana tahau bayan mashine ɗin
Sai da sukaga tafiyar su kafin Malaman suka koma ciki.
Koda suka isa gida bayan sun sauka, Zainab tariƙo ta suka shiga cikin gidan, Mama na ɗaki tana kwance tajiyo sallaman Zainab, amsa mata tayi tana tashi zaune, ahankali suke tafiya har suka isa bakin ƙofar Maman, Zainab taɗaga musu labule suka shige
"Subhanallah.. lafiya Zainab me yafaru da ita?" Mama tafaɗa tana tashi tsaye cike da ruɗewa
"Mama wlh jikin ta ne yayi tsanani, shine Malaman sukace adawo da ita gida".
Mama tariƙo ta tana zaunar da ita saman gadon ta, kana tace
"Dama tunda naga jikin nata da tsanani na san bazata iya taɓuwa komi ba, sai dai taurin kanta ya saka taƙi haƙura, gashi an dawo dake ai".
Zainab tace "Mama bari inje, Allah yaƙara lafiya".
"Ameen ameen Zainab, mungode kinji?"
Zainab na fita, Mama tazauna gefen gadon tana kallon Halwa da har yanzu take rawan sanyi tana kuka tace
"Yanzu kuma da ina da ina yake miki ciwo inje nasiyo miki magani? Kamar ma amai kika yi ko? Don gashi duk kin ɓata Hijabin ki".
Tana sauke maganar ta Halwan tasoma kwarara wani aman daga kwance, dasauri Mama tariƙe ta ganin zata faɗo daga kan gadon, sai da tagama aman kafin tasake ta tana faɗin
"Oh Ni Hauwa, gaskiya ban ga tazama ba dole muje asibiti, tashi tashi muje kiwanke jikin ki mutafi asibiti, Allah dai yabaki lafiya ƴar nan, wannan ciwo haka".
Da taimakon Maman suka fito waje, taje taɗibo ruwa a botiki ta'ajiye a gaban ta, ita da kan ta Maman taɗauraye mata jikin takaita har ɗaki, kana tazaɓo mata wasu riga da wando na Pakistan, rigan Light and Dack Orange 🍊 colour ne, sai wandon kuma dack orange ne da ɗankwalin
"Gashinan ki saka, bari inzo". Mama tafaɗa tana ficewa
Ahankali Halwan tatashi tasaka kayan, sannan tasanya ƙaramin Hijab Baƙi tafito, itama Mama lokacin ta sanyo Hijabin ta suka fice.
Lokacin da suka isa asibiti minti goma suka ɗauka kafin sukaga likita, bayan sun shiga office ɗin sun zauna ne Doctor ɗin yasoma mata tambayoyi tana amsa mishi, har sanda yagama sannan yakira Wata Nurse yace "taje da ita tayi mata gwaje-gwaje". Bayan kamar mintuna 20 sai gashi sun dawo tare da Nurse ɗin, sakamakon Nurse tabashi sannan tafice, bayan ya amsa ya gani yayi rubuce-rubuce sannan yaɗago yana kallon su
"Am Mama.. a binciken da mukayi mata, sakamakon ya ba mu tana ɗauke da ciki har na wata ɗaya da sati, kuma sannan.."
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Ci..Cikiii?".
Mama tafaɗa da ƙarfi tana kallon Likitan da shima yadakata yana zuba mata nashi idanun
"Haba dai Likita kasake dubawa kagani sam ban yarda ba, ciki fa kace? Ciki Halwa take dashi? Ina sam ƙarya ne wlh".
Halwa kuwa tun sanda kalman cikin yadaki kunnen ta, atare zuciyarta da ƙwaƙwalwan ta suka amsa, tsananin tsoro da firgici yabayyana a fuskarta har sai da komi dake motsi a jikin ta yadena aiki na tsawon wasu sakonni kafin tadawo dai-dai, sai kuma tazamo saman kujeran da take kai tazube ƙasa jikinta na wani irin kyarma tana shatatar da hawaye.
.
_To ya kukaji FAN'S?_
_Ya za'a kaya?._
_Me zai faru?._
_Hmm yanzu aka fara muje zuwa._
_Taku Jikar LAWALI CE✍️ kubiyo ni don jin Me zai faru next.. karku manta ku suburbuɗo Comments da yawa da yawa don samun post me yawa._💃💃💃💃💃💃💃
[9/23/2020, 7:28 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 26*
Tunda suka fito daga asibitin suka shiga cikin keke napep Halwa take faman kuka, duk ta takure waje ɗaya ta rufe fuskarta da Hijab, Mama kuwa itama tunda tazauna taɗauke kai gefe, maganganun Doctor kawai suke dawo mata cikin kunnen ta, zuciyar ta sai wani irin tafarfasa take yi ƙiris take jira, suna kai wa tasauka tabashi kuɗin shi tashige gida dasauri, Halwa kuwa ahankali tasauko tanufi gidan nasu, sai dai takasa shiga ciki sai tatsaya a zaure tana ta kuka, tana nan tsaye a wajen sai ga Baba da Nura sun shigo atare, suna ganin ta sukasan babu lafiya, domin Mama takira su a waya tace su dawo yanzu, kuma bata faɗa musu abinda ke faruwa ba, Baba ne yasoma cewa
"Halwa me kike yi anan? Me yafaru ne?"
Bata ɗago kai ba sai ma ƙara volume ɗin kukan ta da tayi, nan da nan jikinta yasoma rawa kamar an sakata a shocking, Nura zuwa yayi yariƙo ta yana faɗin
"Lafiya Halwa? Menene haka wa yabige ki?"
Still shima shiru tayi masa
Baba yace "Nura taho da ita mushiga gidan sai muji ba'asi wajen Maman taku".
Riƙo ta kuwa Nura yayi, babu musu tabi shi suka shiga ciki, ɗakin Mama suka nufa gaba ɗayan su, Mama na zaune tana faman hawaye suka shigo, abinda yaƙara ɗaure musu kai kenan suka hau tambayan ta "lafiya?" Hankalin su duk atashe, but Mama taƙi tayi magana sai Hawayen ta take yi, zama Baba yayi gefen ta yayinda Nura ma yasamu waje yazauna yajanyo hannun Halwa itama tazauna kusa dashi
Baba yace "wai Hauwa lafiya muka ganku a wannan yanayin? Meke faruwa ne kiyi mana bayani?"
Ɗago kan ta tayi cikin baƙin ciki tace
"Wani bayani kakeso kaji Baban Nura? Ace wai yau Halwa ce tayo mana ciki agida, cikin shege fa Halwa tayi a gidan nan". Sai tasake fashewa da kuka
Atare Baba da Nura suka maimaita cikin Shegen, Nura har da ja da baya yana matsawa kusa da ita, cikin kaɗuwa Baba yakalli Halwa da har yanzu takasa buɗe idanun ta yace
"Dagaske ne cikin Shege kikayo min agida?"
Shiru Halwa tayi
"To ya za'a yi tafaɗa maka? yanzu muka dawo daga asibiti likita yatabbatar mana tana ɗauke da cikin Shege acikin ta, to wlh tallahi ba dai nan gidan ba, bazai taɓa saɓuwa ki haifa mana ɗan Shege agidan nan ba, duk gatan da mukayi miki Halwa kikasa saka mana da abun kirki sai abun tsiya? ashe duk zaman da muke yi dake amanar mu kike ci mu duk bamu sani ba? To baza mu ga wannan abun kunyan ba dole ki koma can dangin mahaifin ki tunda bakisan halacci ba, na rabo ki da can ne don naga kina shan wahala amma kin nuna mana ke ba mutumiyar arziƙi bace".
Baba ya'amshe zancen cikin sauri yace
"Ni Malam Ayuba za'a zubar min da mutunci agida? da ƙima ta da daraja ta yau za'a haifa min shegen ciki?"
Halwa kuwa in banda kuka babu abunda take yi, sosai zuciyarta takaɗu da kalaman Maman nata, "wanna wace irin baƙar rana ce tazo mata?" Meyasa duniya take son juya mata baya?"
Baba yaci gaba da faɗin
"Kin bani mamaki Halwa kinci amanar yardan da mukayi miki, kina son ki zubar mana da mutunci duk yanda ake ganin mu a gari sai gashi ace za'a haifi ɗan Shege a gidana, to ba dai nan gidan ba dole kibar min gida, iya zaman da kikayi agidan ma ya isa haka, kitashi kiwuce kije kihaɗo kayan ki tun kafin wasu suji, in kin shirya kizo ki amshi kuɗin mota".
Ɗago kanta Halwa tayi da idanuwanta suka kaɗa sukayi jazur sukayi luhu-luhu, cikin tsananin kuka tace
Don girman Allah Mama kuyarda dani wlh Fyaɗe akayi min, Yaya Nura ma ya sani wlh ban taɓa sanin wani namiji ba.."
Dasauri Nura yace "keeee Halwa sharrin kuma kaina zai koma? Aina nasan anyi miki Fyaɗe? Ke dai kawai kina zuwa makaranta kina yawon banzan ki kin kwaso ciki zakice na sani, kinci amana ta Halwa, kinci amanar soyayya da yardan da nayi miki, Allah ya isa tsakani na dake".
A firgice takalle shi sai dai takasa furta komi sabida zallan mamaki da kuma rawan da bakin ta yake yi, shi kuma Baba cikin ɓacin rai yace
"Halwa wato so