Header Ads
Showing 111001 words to 114000 words out of 132567 words

Chapter 38 - BARRISTER IBRAHIM KHALIL Complete Document by Nafisa Isma'il Lawal.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jul 2024

1162

Ads at the middle of Article

su, inda anan ne yafaɗa musu halin da ake ciki




Su ma Dad da Mom sun tashi hankalin su matuƙa, anan ne ma Dad ɗin yake faɗa musu labarin Halwan da alaƙan su dasu Saleema




Lokacin da Dad ɗin yagama faɗa musu komi sai kawai hawaye suka ciko idanun Khalil, miƙe wa tsam yayi yafice daga parlour'n yadoshi part ɗin su inda ɗakin su yake na Da




Akan gado yakwanta yana lumshe kyawawan idanun sa, haushi da takaicin kansa kawai yake yi






Meyasaka ya ɗau laifi ya ɗaura wa baiwar Allah batare da yasan musabbabin rayuwan ta ba? Shin meyasaka yamanta cewa ƙaddara irin wannan zai iya samun ta batare da laifin ta ba?




Shin meyasa mutane suke ɗaura laifi ga macen da suka ganta tana rayuwan ƙasƙanci? Shin sun tambaye ta dalilin da yasa har tafito gida take wannan rayuwan? ko kuma sun manta cewa wasu sanadin fyade ne yajawo musu rabuwa da gida akan tsangwama da kyara da ake musu, menene laifin su don ƙaddara ta faɗa musu ake koran su? Shin mun manta da cewa idan suka tafi zasu ci gaba da wannan rayuwan ne ko kuwa su faɗa hannun ɓata gari wani abu yasame su ta sanadiyar mu ne.. Allah dai yatsare mana imanin mu yasa mufi ƙarfin zuciyar mu, ya Allah ka kare mana zuri'armu daga faɗa wa mummunan rayuwa..




Ajiyan zuciya kawai yake sauke wa, ya jima a haka kafin daga bisani yamiƙe yaɗauro alwala jin ana kiran sallah yafice.




Wasa-wasa har dare babu Halwa bare labarin ta




Izuwa lokacin har ƙarin ruwa sai da aka yi ma Saleema, sai da akayi mata alluran barci sannan suka samu sukuni domin yanda tashiga wani hali hakan ya ɗaga wa iyayen ta hankali, babu daman tayi tari sai jini ya fito, gashi Doctor yayi musu bayanin cewa idan har taci gaba da kasancewa ahaka to tabbas akwai matsala domin zuciyarta ta gama kumbura sosai




Abba yaso akai ta asibiti but likitan yace abar ta zuwa safiya idan jikin ya sake tsanani.




Bata farka ba sai washe gari, Ummi ita ta taimaka mata tayi wanka tashafa mata mai tare da saka mata kaya, sabida ko kaɗan bata da ƙarfin jiki bata iya yin komi da kanta, sosai suke ta lallaɓa ta suna faɗa mata kalamai masu daɗi yanda zata kwantar da hankalin ta




Abinci ma abaki Ummi taba ta sannan taba ta maganin ta tasha.








**** **** **** **** *****


Tunda Halwa tafito daga gidan sai tasaka kuka, tafiya take yi batare da tasan inda zata nufa ba, ahankali take jan Trolly ɗin duk da kuwa zuciyarta cike take da tsoro matuƙa ganin yanda garin yaƙara duhu gashi babu kowa sai haushin karnuka, but bata jin zata iya tsaya wa hakan yasaka taci gaba da tafiyan ta tare da danne tsoron ta cikin rai, tafiya ɗaya sai ta waiga ahaka har tafito titi inda anan ne take ɗan ganin motoci suna wulƙa wa




Hannun ta tasaka tasharɓe hawayen fuskarta kafin tanufi titin don ta tsallaka, babu zato tahangi mota tayo kanta duk da kuwa bata san da zuwan motan ba sai ganin ta tayi kusa da ita, ƙwalla ƙara tayi amma ina tuni motan ta bige ta




Dasauri matar dake cikin motan tafito ita da ƴaƴan ta biyu suka yo Kan Halwa




"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Matar take faɗa




Yayinda ƴan matan tuni sun saka kuka sabida halin ruɗe wa




"Ku taimaka min.. ku taimaka min na ɗauke ta". Matar tasake faɗa cike da rawan baki




Daƙyar suka ɗaga Halwa suka nufi motan da ita suka saka ta daga ita har Trolly ɗin ta, matar taja motan suka bar wurin




Direct asibiti suka nufa, dayake sananniya ce wajen Likitan sai yasaka Nurse suka amshi Halwa batare da bincike ba akayi Emargency Ward da ita




A reception suka zauna zaman jiran fitowar likitan




Mintuna kamar 20 yafito yanemi Matar tabiyo sa, bayan sun zauna a Office ɗin sa yasoma mata bayanin abinda ke faruwa




"Ba wani abu bane yasame ta sai buguwa da tayi akanta wanda hakan yaja mata dogon suma, amma da yardan Allah zuwa gobe zata iya farka wa".




Wannan bayanin na likita shi yakwantar wa matar da hankali, daga nan suka tattauna sannan tafito tasami ƴan matan ta suna jiran ta




Tambayan ta suka hau yi har yanzu suna zub da hawaye don ba ƙaramin tashi hankalin su yayi ba




Kallon su tayi cikin kwantar musu da hankali tace "ya isa haka babu abinda yasame ta illa buguwa da tayi akanta".




Atare suka sauke ajiyan zuciya suna faɗin "alhmadulillah".




Murmushi tayi kafin tace "to yanzu yakamata ku koma gida inyaso Ni sai in zauna da ita don baza mu tare anan ba, kuma ban ce ko waccen ku takira Daddynku tafaɗa masa ba don kar hankalin sa yatashi kuna jina?". Matar Taƙarike maganar da jan kunnen ta




Gyaɗa mata kai suka yi atare suna cewa "to Mami".




"But Mami ki bari Ni zan kwana da ita mana tunda ba wani abu me wahala bane". Cewar Safina tana kallon Mami ɗin cike da son amincewar ta




"Ok to bari mutafi gida Ni da Nafisa, but ki kula bana son rawan Kan nan naki kinji Ni? Idan da akwai matsala kiyi kiran Doctor".




Safina tace "to Mami insha Allahu".




Daga haka babu abinda suka sake faɗa illa wuce wa ɗakin da aka kwantar da Halwa da suka yi, basu fi mintuna goma ba Mami da Nafisa suka fito suka bar Safina a wajen ta.








_sai muce Allah yabaki lafiya Halwa._
[1/5, 12:58 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️




*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_




*بسم الله الرحمن الرحيم*






*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```


*JIKAR LAWALI CE*✍️


*Wattpad: UmmuDahirah*👈




*\F.W.A📚/*


```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._


*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._


_Fateema Zahra, Hauwa Ali, Wanka Yakubu Isa, Munir Y Abdullah, M. Bintu Thank You for the loving My Book._




*BOOK TWO*




.


_______________________________


*CHAPTER Twenty Five*


________🎓Washe gari da sassafe Mami tadawo Asibitin da breakfast, Safina na gaishe ta ta'amsa tace mata




"Yauwa to tashi kije yi maza Drever na jiranki ki koma gida ki shirya kar kuyi late, ki tabbatar kinyi breakfast kafin ki tafi ko kuma ki ɗiba ki tafi dashi kina jina?"




Murmushi Safina tayi lokacin da tamiƙe tana ɗaukan gyalen ta




"Mami sai kace wata yarinya haka kawai sai inje da Breakfast school?"




Hararan ta Mami tayi tace "Ni dai na faɗa miki kuma na bada sallahu idan ma baki je dashi ba Nafisa zata faɗa min, ai na faɗa miki daga yanzu na dena baku kuɗi, wuce ki tafi kar in saɓa miki uwar shiririta".




Turo baki gaba tayi tafice batare da tasake cewa komi ba




Ita kuma Mami zama tayi idanun ta akan Halwa wacce ko motsi ba ta yi tun jiya tana nan ayanda take, an naɗe mata kai da bandage sabida ba ƙaramin rauni taji ba






Ajiyan zuciya kawai Mami take sauke wa cike da tsananin tausayin Halwa, kawai aranta tunanin yanda aka yi matashiyar yarinya kamar wannan tafito gidan iyayen ta da tsakar dare take yi.






Tana nan zaune wajen ƙarfe 09:00am na safe sannan ne Halwa tafarka, don haka tamiƙe da hanzari takira Doctor coz tunda tafarka ɗin tabuɗe idanun ta bata sake motsawa ba, duk sannun da tajero mata taƙi ta amsa ta




Doctor da yazo yadudduba ta yatabbatar bata da wani matsala sannan yace aba ta abinci taci sai tasha magani






Sai da yafita kafin Mami tasoma haɗa mata abin kari, bayan ta gama takalle ta kamar yanda Halwan tazuba ma matar idanu tamkar me neman wani abu ajikin ta




Murmushi tayi mata tace "tashi kisha kinji?"




Halwa batace komi ba tayunƙura tagyara zaman ta, duk da babu abinda ke damun ta amma sosai kanta ke mata ciwo daƙyar take iya motsa shi, amsar Cup ɗin tayi tariƙe da hannu biyu ta kasa sha




Sai da matar takula da ita kafin tace "af na manta baki wanke baki ba ko zaki fi jindaɗin sha".




Amsar Cup ɗin tayi tamiƙo mata ruwa, sai da tawanke bakin kafin tamiƙa mata Tea Cup ɗin, sannan alokacin tasake ciko mata Plate da Arish da soyayyan ƙwai ta'ajiye mata akan gadon, sai tatashi tafice don tabar ta tasake




Tana fita Halwa talumshe idanunta, aranta kewar gida kawai take yi tare da tunanin makomar ta a yanzu, bata dena tunanin ba take ta tsoma bakin ta tana shan tea ɗin zuciyarta duk babu daɗi




Ta jima ahaka batare da tasan awani hali take ciki ba, har Mami tadawo tatarda ita ahaka ko rabin Cup ɗin bata yi ba, babu ma abinda tataɓa acikin Plate ɗin




Mami kallon ta tayi tana nazartan ta, kafin kuma tatamke fuska cikin serious face tace "har yanzu baki ci komi ba ashe? Bana son shashanci Yi maza ki cinye ki bani Plate ɗin da kofin".






Kallo ɗaya Halwa tayi mata ta tabbatar matar ba ta ɗaukan raini, nan da nan taji tsoron ta ya kamata ta batare da tayi mata musu ba tayi yanda tace mata tamiƙa mata Plate ɗin kamar yanda tabuƙata






"Good kinyi kyan kai". Mami tafaɗa bayan ta amsa ta ajiye sannan tafice






Da kallo Halwa tabi ta tana tunanin ita kuma wannan matar daga ina? Menene haɗin ta da ita? Ita dai tasan an bige ta to ko dai ita ce tabige ta ɗin?".






Tana cikin wannan tunanin ne suka dawo da doctor, magani yaba ta bayan ya tambaye ta "ko akwai abinda ke damun ta?"




Dayake Halwa jin ta take yi tamkar a ƙaya musamman yanda matar nan tanuna mata sai taji ta ƙosa su raba hanya, don haka tace masa babu abinda ke damun ta




Hakan yasa Doctor ɗin ce ma Mami zuwa anjima za'a sallame ta.








Ƙarfe 02:35pm. Safina da Nafisa suka kawo abincin rana, ganin Halwa ta farka ga jikin ta dasauƙi hakan ya faranta musu rai sosai musamman ma Safina, kasancewar ita akwai ta da son mutane ga fara'a ba kamar Nafisa ba, hakan yasa lokaci ɗaya tashige ma Halwa tana ta janta da Surutu




Itama Halwa sosai tasaki jikin ta zuwan su ba kamar ɗazu ba duk da kuwa ba magana take yi ba iyakan ta murmushi da bin Safinan da kallo me zuba mata surutu.






Da yamma aka sallame su suka taho gida, babban gida ne dasu me kyau sosai, kai da gani kasan ba ƙaramin kuɗi ne da me gidan ba




Suna isa Safina taruƙo mata hannu suka yi ciki, ɗakin su takai ta tahaɗa mata ruwan wanka tashiga




Itama Nafisa sai gata ta shigo da Trolly ɗin Halwa ta'ajiye mata tafice




Safina na zaune bakin gado tana jiran Halwa har tafito, murmushi tayi mata tace




"Aunty ga kayan naki nan sai ki shirya ina zuwa". Taƙarike maganar tana miƙe wa cike da zumuɗi




Gyaɗa mata kai Halwa tayi tare da mata murmushi, har tafice tana kallon ta kafin tazauna gefen gadon tana zuba tagumi, ta ɗau lokaci ahaka har Nafisa tashigo ɗakin batare da ta sani ba, sai da tataɓa ta kafin taɗago kai dasauri tana kallon Nafisan, ko kaɗan ba wai ta gane ko wacece acikin su ba duk da kuwa taji sunayen su tun a Hospital, but tsananin kaman da suke da juna baka banbance wacece Nafisa wacece Safina, iyakan dai a fuska idan kakalli Nafisa zaka iya shaida ta sabida bata da fara'a ko kaɗan, miskila ce na ƙarshe saɓanin Safina ko yaushe haƙoran ta awaje suke




Murmushi Nafisa tasakar mata ganin yanda tatsare ta da idanu tana son tantance Nafisa CE ko Safinan






"Ki taso Mami na kiran ki". Tafaɗa ahankali tana juyawa tayi hanyan ƙofa




Ɗan numfashi Halwa taja batare da ta ɗauke kanta daga kallon Nafisa ba har tafice, yanda tanuna mata ɗin tuni ta gane ba Safina bace






Miƙe wa tayi tabuɗe kayan ta taciro riga da skert na atamfa kalan Baby pink sai ratsin Milk da aka yi amfani dashi wajen zanen Flower jefi-jefi, bayan ta gama saka wa taɗau siririn gyale baƙi tayafa akanta sabida bata saka ɗan kwalin kayan ba sannan tanufi ƙofa tafice






Suna zaune gaba ɗayan su a falo, Halwa da tafito ƙasa tasamu tazauna cikin sanyin muryanta tayi wa Mami sannu




Amsawa tayi idanun ta akanta kafin takalli su Nafisa tace "ku tashi ku bamu wuri".




Babu musu suka tashi, sai ma suka yi ƙofar fita suka fice gaba ɗaya




Juyo da idanun ta kan Halwa tayi tace "yauwa so nake yanzu ki faɗa min abunda yasa kika baro gida, ayanda nafahimta da nazarin da nayi miki hasashe na ya bani kin baro gida ne sabida wani dalili naki hakane?"




Halwa da kanta ke ƙasa ta kasa ɗago kai bare ta'amsa mata, sosai matar take bata mamaki da kuma yanda halin ta yake, kai da gani kasan ba ƙaramin jarumar mace akayi a wajen ba, dakakkiyar mata me tsananin kwarjini da baiwa..




"Kinyi shiru ina magana? bana son ina maimaita ma mutum magana biyu kinji Ni?"




Dasauri Halwa tagyaɗa mata kai cikin tsananin shakkar matar da yakamata tun ganin ta da tayi




"Ki buɗe baki kiyi min magana ba gyaɗa kai nace kiyi ba".




Cikin rawan baki Halwa tabuɗe baki tasoma sanar mata da abinda take buƙatar ji a wajenta, iyakan abinda tasanar mata tafito gida ne sabida anyi mata aure da mijin ƴar uwanta, ganin tanuna kamar bata ji daɗi ba shine ita kuma tabi wannan hanyan don guje ma auren".




Jinjina kai Mami tayi idanun ta kafe kan Halwa ɗin, cikin kausashshiyar murya tace "wato kin zaɓi guduwa ne don kawai ƴar uwanki bata ji daɗin wannan haɗin ba? Kin nemi ki baro iyayen ki sabida ki faranta mata ko?"




Cikin zub da hawaye Halwa tasake duƙar da kanta, cike da raunin murya tace "nayi hakan ne kawai saboda farin cikin ta, Ni bazan so in shiga rayuwanta ita da mijin ta ba, sannan zan so takasance cikin farin ciki ko dan ciwon da take fama dashi".




Shiru ne yabiyo bayan maganar ta illa shashsheƙan kukan ta dake tashi




Wajen shuɗewar mintuna biyar kafin Mami tace "shin ke kina son Sa ko kuwa bakya son sa?"




Baki na rawa tace "Ina son sa".






Murmushi Mami tasaki tana kaɗa ƙafafuwan ta, sai da taja lokaci kafin tace "shikenan yanzu abinda Yakamata zuwa gobe zan maida ki gida saboda babu ta yanda za'a yi in barki kibi duniya akan wannan banzan dalilin naki, idan yaso in namayar dake sai in faɗa musu su raba auren tunda baki son zama dashi, kinga babu ke babu guduwa kenan, tashi ki wuce na sallame ki".






Jiki a sanyaye Halwa tamiƙe takoma ɗakin su Nafisa, tana shiga tazauna kan gadon tana ci gaba da tsiyayar da hawaye kamar an kunna famfo




Ba wai maganar mayar da itan bane yaɗaga mata hankali, jin cewa zata faɗa a raba auren ta da Khalil, ita ji take yi a yanzu ta gummaci tatafi da auren sa tayi ta yawo da araba auren, hakan zai saka zuciyarta tayi sanyi daga zugin da take mata na tsananin ƙaunar sa da take yi, auren Khalil akanta shi zai sa duk inda taje takasance cikin farin ciki, ko babu komi zata mutu da auren wanda tafi ƙauna fiye da ranta a yanzu ɗin atare da ita.






Ita kuma Mami murmushi tayi lokacin da Halwan tashige ɗaki, sosai aranta ta tausaya mata domin tunda take bata taɓa ganin irin wannan sadaukarwan da Halwa tayi ba, kina son mutum amma sabida farin cikin ƴar uwanki ki zaɓi rugujewar rayuwan ki gaba ɗaya akanta, gaskiya samun me hali irin Halwa da wahala, tana da kyakykyawar zuciya matuƙa, tana iya sadaukar da komi nata akan masoyi




(Hmm nace Mami don ma bakisan sauran sadaukarwan da tayi mata bane)








Mami tana zaune da ƴaƴan ta biyu Nafisa da Safina masu shekaru 16 a duniya, twins ne su kuma daga kansu bata sake haihuwa ba, mijinta babban soja ne sosai yana aiki a Kaduna




Baza ku gasgata maganar nan da ake cewa matar Soja itama Soja bane sai kun haɗu da Mami, Kai in taƙaice muku tsaurin idanun Mami da dakakkiyar zuciyar ta ta ninka na mijinta da shine ma Sojan, bata da tsoro ko kaɗan gata macece me tsayawa akan komi da yashafe ta da tsananin jarumta, bata nuna gazawar ta a komi, tana da fara'a sosai sai dai ba ta yin sa sai a inda yadace, shiyasa Nafisa a halayya ita taɗauko, sai dai ita Mami ba wai miskilanci ne da ita ba dakakkiyar macece da bata ɗaukar raini koda yaushe, wannan dalilin ne zaka ga tamkar bata cika wasa ba




Yanzu haka ita ma'aikaciyar gwamnati ne me amsar zunzurutun albashi don babba ce sosai a wajen aikin su.




*WASHE GARI*




Wajen ƙarfe 10:00am. Mami tasaka Halwa tashirya






Dama tuni su Nafisa sun tafi school, Safina har da kukan ta jin cewa a yau ɗin Halwa zata tafi, domin sosai jinin ta yahaɗu da Halwa ɗin a kwana ɗayan nan da tayi agidan, ta ɗauke ta tamkar babban Yayarta wacce suka fito ciki ɗaya shiyasaka tasaki jiki sosai da ita, taso Mami tabar su yau dai rana ɗaya kar suje school atafi dasu kai Halwa gida, amma ina Mami taƙi yarda, daga ƙarshe ma sai da tayi kamar zata mangare Safinan kafin tatafi school da kuka






Ita kanta Halwa sosai taji ƙaunar Safinan aranta, sai bata ji daɗin yanda Mami tayi ɗin ba, sai dai bata da bakin magana iyakan nata idanu ne domin wargi ma wuri yaka samu






Bayan Halwa tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga na Baƙin yadi da zanen Flower da aka yi da dack orange Colour, fitet ne rigan sai tayi Rolling da gyale me ruwan madara irin me taushin nan sosai ya rufe mata har bandage ɗin kanta




Janyo jakan tayi tafito Parlour inda Mami ke zaune tana jiran ta, kallo ɗaya tayi mata ta ɗauke kai tana ci gaba da latsa wayan nata




Ita dai Halwa tana nan tsaye a waje ɗaya ko ƙwaƙƙwaran motsi bata iya yi




Kamar shuɗewar mintuna goma kafin Mami tatashi tayi wa Halwa nuni da hannu alamun su je






Gaba Halwa tayi dasauri tana jan Trolly ɗin ta, koda tafita sai da

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads