Showing 129001 words to 132000 words out of 132567 words
Chapter 44 - BARRISTER IBRAHIM KHALIL Complete Document by Nafisa Isma'il Lawal.txt
don faranta mata
Kasancewar yanzu yayi sabon gini, zasu tashi a anguwan da suke zaune, ya tsara musu babban gida wanda ya ninka wanda suke ciki a yanzu, ko wacce da nata Part ɗin, sai dai kuma haɗe yake da babban Parlourn na su gaba ɗaya
Saura kwana biyu su tare don haka ake ta faman shirye-shirye babu kama hannun yaro, tunda abun ya haɗe musu biyu ne, ga Waliman taya Halwa zama Barrister, ga kuma Waliman koma wa sabon gida.
Babu abinda zasu ɗauka na tsohon gidan su, komi sabo aka sanya agidan
Mom ita ta ɗaukar musu me gyaran jiki, don tana so su fito sosai, har gida ake bin su ana musu komi, an zana musu lalli me tsananin kyau, sai aka yarfa musu kitso wanda ya sake fito dasu ainun, idan ka gansu sai ka ɗauka sabbin amare ne, sabida duk abinda ake ma Amare ƴan gata an yi musu.
A ranan tarewan suka koma can sabon gidan nasu, tare da ƴan uwa na kusa
Zuwa ƙarfe 04:00 gidan ya cika maƙil da jama'a, su Mama da Baba ma duk sun hallara gidan, iyayen Haris ma sun zo, Zainab da ƙanwar Mijin ta har da mahaifiyar sa da Umman ta ma duk sun zo, su Zaituna ma sai da suka zo mata kara
Ana fara taron su Halwa suka fito, duk kansu sun sha kyau cikin Milk ɗin Material me tsananin tsada, doguwar riga aka yi musu fitet gown, sai akayi kwalliya da ston masu ƙyalli, an yi musu Light makeup da ya ƙawata fuskar su, takalmin su da gyalen da suka yi Rolling duka kalan baƙi ne, sun yi kyau Masha Allah, ba ma zaka iya tantance wacce tafi ba a cikin su
Ƙaramin cikin Halwa ya fito ɗass yayi mata kyau matuƙa, ga haske da tasake yi sosai sabida cikin
Haka Husna da Ahmad su ma an shirya su, tubarakallah Masha Allah kowa ya gansu sai sun burge sa
Mamy tunda ta hangi Husna ta ɗauke ta tana ta nan-nan da ita.
An gudanar da taro lafiya an gama lafiya, kowa ya tafi da tarin ɗumbin kyaututtukan da aka raba
Sai dai aka bar ma su aiki da gyara gidan
Su ma su Saleema ciki suka shige, suka ɗaura alwala saboda kiran sallan magriba da aka yi, sallah suka yi suka cire kayan jikin su suka sauya da wani atamfa me ruwan kuka da ratsin ja da baƙi, ɗinkin riga da skert ne iri ɗaya komi da komi, parlour suka fito suka zauna suna hiran Waliman cike da nishaɗi
Husna da Ahmad tuni barci ya ɗauke su, Dattijuwar matar da suka ɗauka me aikin su, ita tayi musu wanka ta shirya su a kayan barcin su ta kai su ɗakin su.
Sai da aka kira sallan isha'i kafin suka tashi suka je suka gabatar suka sake dawowa.
Shima Khalil ɗin be dawo cikin gidan ba sai da yayi sallan isha'i sannan ya shigo.
.
𝚙𝚕𝚣 𝚜𝚑𝚊𝚛𝚎 𝚊𝚗𝚍 𝚟𝚘𝚝𝚒𝚗𝚐
[1/21, 1:38 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
𝐁𝐀𝐑𝐑𝐈𝐒𝐓𝐄𝐑 𝐈𝐁𝐑𝐀𝐇𝐈𝐌 𝐊𝐇𝐀𝐋𝐈𝐋
♠️
𝑊𝑟𝑖𝑡𝑖𝑛𝑔:✍️ 𝐵𝑦
𝐍𝐚𝐟𝐢𝐬𝐚𝐭 𝐈𝐬𝐦𝐚'𝐢𝐥
(𝐹𝑒𝑒𝑛𝑎ℎ 𝐽𝑖𝑘𝑎𝑟 𝐿𝑎𝑤𝑎𝑙 𝐺𝑜𝑚𝑎)
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
𝐅𝐄𝐄𝐍𝐀𝐇 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑'𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎📖
®Ɗ𝚊𝚢𝚊 𝚝𝚊𝚖𝚔𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝙳𝚞𝚋𝚞💪✓
𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️
𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈
\𝗙.𝗪.𝗔📚/
𝙰𝙻𝙷𝙰𝙼𝙳𝚄𝙻𝙸𝙻𝙻𝙰𝙷! 𝙰𝙻𝙷𝙰𝙼𝙳𝚄𝙻𝙸𝙻𝙻𝙰𝙷!! 𝙰𝙻𝙷𝙰𝙼𝙳𝚄𝙻𝙸𝙻𝙻𝙰𝙷!!!
𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑛𝑎 𝑔𝑜𝑑𝑒 𝑚𝑎𝑘𝑎 𝑑𝑎 𝑘𝑎 𝑏𝑎𝑛𝑖 𝑑𝑎𝑚𝑎𝑟 𝑟𝑢𝑏𝑢𝑡𝑎 𝑤𝑎𝑛𝑛𝑎𝑛 𝑙𝑖𝑡𝑡𝑎𝑓𝑖𝑛 𝐵𝑟𝑟. 𝐼𝑏𝑟𝑎ℎ𝑖𝑚 𝐾ℎ𝑎𝑙𝑖𝑙, 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑘𝑎 𝑏𝑎𝑛𝑖 𝑖𝑘𝑜𝑛 𝑟𝑢𝑏𝑢𝑡𝑎 𝑎𝑏𝑖𝑛 𝑑𝑎 𝑧𝑎𝑖 𝑎𝑚𝑓𝑎𝑛𝑖 𝐴𝑙'𝑢𝑚𝑚𝑎𝑛 𝑚𝑢, 𝑘𝑢𝑠𝑘𝑢𝑟𝑒𝑛 𝑑𝑎 𝑧𝑎𝑛 𝑦𝑖 𝑎𝑐𝑖𝑘𝑖 𝑘𝑢𝑚𝑎 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑘𝑎 𝑦𝑎𝑓𝑒 𝑚𝑖𝑛 𝐴𝑚𝑖𝑛 🤲 𝑦𝑎 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ.
𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 ƴ𝑎𝑛 𝑢𝑤𝑎𝑛𝑎 𝑚𝑢𝑠𝑢𝑙𝑚𝑎𝑖 𝑏𝑎𝑘𝑖 ɗ𝑎𝑦𝑎.
𝗕𝗢𝗢𝗞 𝗧𝗪𝗢
.
_______________________________
𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 𝗧𝗵𝗶𝗿𝘁𝘆 𝗧𝗵𝗿𝗲𝗲
________🎓 Kallon su yayi duk kan su kafin ya lumshe idanun sa ya buɗe yana zuba murmushi, hannun sa ya saka acikin aljihun sa ya ciro Keeys kana ya kalle su, batare da yace uffan ba, yaja hannayen su ko wacce ya saka mata keey ɗin, be bari sun yi magana ba yace da su
"Keey ɗin mota ce, kyauta na a gare ku".
Duk kan su ɗago keey ɗin suka yi suna murmushi cike da farin ciki, kafin kuma su rungume sa cikin tsagwaron murna suka soma masa godiya, Halwa har da hawayen ta
Hannu yasaka kawai yana shafa kansu kana yace, "to ku tashi muje ku ga motan ko".
Babu musu suka tashi suka fice, ai kuwa motocin sun bala'in burge su, ga su masu tsada ne daga gani, na Saleema green CE, ita kuma na Halwa fara, sai da duk kan su suka shiga ciki suka dudduba sai santi suke yi, duk da Saleema ba yau ta saba yin mota ba, but kyautar mijin nata sosai ya faranta mata, kuma ji take yi kamar ma bata taɓa yin mota ba sai akan wannan
Shi Khalil ma dariya sukai ta bashi, ganin abun nasu yaƙi ci yaƙi cinye wa sai murnan santi suke masa, sai da ya ja hannun su suka yo ciki sannan suka haƙura.
Dayake ranan a ɗakin Halwa yake, ai kuwa ranan yaga gata, sosai ta zage ta faranta masa rai
Shi kansa yasan yau ya samu tukuici.
Washe gari ma haka masu zuwa taya su murna sukai ta shigowa, musamman waɗanda suke cikin anguwan, da yamma kuma suka je nuna wa su Ummi motan nasu, Saleema ita ta tuƙa nata, shi kuma Khalil ya tuƙo na Halwa, tana zaune a gefen sa, sun jima agidan har magriba kafin su wuce gidan su Khalil ɗin, can kuwa sai wajen sha ɗayan dare suka baro gidan.
Tun daga ranan kuma sai Khalil yake fita da Halwa koya mata motan, idan be samu time ba tare suke fita da Saleema tana koya mata, ahaka har aka shafe tsawon watanni biyu lokacin ta ƙware sosai, gashi ta soma aiki, duk da wajen aikin su ɗaya da Khalil, wani lokacin tare suke zuwa, bare ma yanzu da cikin ta yashiga watanni shida, so be barin ta tana tuƙi sosai, tare suke tafiya.
Itama Saleema ya buɗe mata Chamis, a shagunan dake bakin layin anguwan su anan ya kama mata hayan ɗaya, duk idan zata tafi tare da Ahmad take tafiya, duk da yanzu yayi wayo sosai babu inda ba ya yawata wa da ƙafan sa, har magana ya soma, amma ba ta barin sa agida, sosai take ƙaunar yaron koda yaushe yana liƙe da ita, shiyasa ma har ƙyuya yake dashi, don be cika yarda da kowa ba sai ita.
Yau ɗin kasancewar Asabar ne gaba ɗaya a cikin su babu wanda ya fita, suna zaune a Parlour duk kan su
Khalil da Halwa suna zaune a ƙasa sun yi baja-baja da takardu, shi ke aikin ita kuma tana taya sa, yayinda Saleema ke kwance saman dogon kujera, ta ɗaura Ahmad a jikin ta dake barci, idanun ta a lumshe suke, jefi-jefi suke ɗan taɓa hira, Husna na can gefen dainning table da kayan wasan ta, ta baza su sai yi take yi tana surutun ta.
Sosa kanta Halwa tayi da hannun da take riƙe da Bairo, sai kuma ta ɗan juya kai ta kalli Saleema tace mata "sis Wai yau naji ki so slowly ne, ko wani abun na damun ki?"
Ɗan buɗe idanun ta tayi kaɗan kafin ta saki murmushi tace, "a'a babu abinda ke damuna, yau dai kasala nake ji wlh".
Khalil dake faman aiki a Lapton yana jin su be saka musu baki ba, ahaka suka ci gaba da zaman, sai dai zuwa lokacin Saleema ta dena saka musu baki gaba ɗaya, numfashi kawai take sauke wa a hankali tana sake ƙanƙame Ahmad dake jikin ta, kwana biyu kenan da zuciyarta take mata zugi duk ta hana ta sukuni, sai dai bata ba da ƙofan da za'a gane wani abun na damun ta ba, don ba ta son ta tayar musu da hankali, sai ta mayar da hankalin ta kan shan maganin ta, sai dai yau gaba ɗaya jikin ta ya matsa mata tunda bata sha ba, har soma kumbura tayi wanda in ba kayi mata kallon ƙurilla ba; ba lallai kagane hakan ba
Ci je leɓen ta tayi ahankali, kafin ta buɗe idanuwan ta da zuwa yanzu sun sauya kala, sun koma kore-kore, miƙe wa take ƙoƙarin yi jikin ta na rawa tana son zame Ahmad dake kanta
Ɗago kai Halwa tayi ta kalle ta, sai kuma tayi saurin faɗin "sis meke damun ki ne wai? Lafiyan ki ƙalau kuwa?"
Sai alokacin shima Khalil yaɗago kai jin tambayan da Halwa take mata, da alamun ruɗu a muryan ta, shima dai saurin tambayar Saleeman yasoma yi ganin yanda duk ta sauya lokaci ɗaya, gashi jikin ta sai rawa yake yi tana faman cije baki, miƙe wa yayi ya koma kan kujeran yana tallabo ta yasake cewa "lafiya kuwa meke damun ki? Ko wani waje na miki ciwo ne?"
Murmushi tayi tana lumshe idanun ta kafin tace, "ban sha magani na bane yau, shine zan tashi in ɗauk.."
Be bari ta dasa Aya ba yakatse ta da faɗin "ya salam! Meyasa to? Wannan ganganci ne ai".
Sai yaja tsaki yana faɗin "nima bansan me ya hau kaina ba yau ɗin ban tambaye ki ba, tun safe ma baki sha ba ko?"
Gyaɗa masa kai tayi kawai
Kallon Halwa yayi ransa duk babu daɗi yace, "je ki ɗauko min maganin".
Dasauri tatashi tana zare hannun ta da tariƙe na Saleeman, ɗakin ta tawuce ta ɗauko magani ta kawo masa, sai ta koma ta ɗauko ruwa cikin Fridge tasake dawowa ta miƙa masa
Shi da kansa ya bata, sannan yace ta kwanta ta huta, idan anjima jikin babu daɗi sai su nufi asibiti
Halwan ɗaukan Ahmad tayi tamayar dashi ɗaki, don Saleeman ta samu sake wa akan kujeran.
Gaba ɗaya sauran wunin ranan sai suka yi a rashin walwala, musamman ma Halwa da duk motsin ta yana kan Saleeman, gwara-gwara Khalil ya fita gab da magriba, kuma be dawo gidan ba sai da akayi isha'i.
Ita kuma Halwa taliya ta girka musu me sauƙi bayan ta idar da sallan magriba, zuwa lokacin ne Saleema ta tashi, duk hankalin Halwa kacokan yana kan ta sai tambayar ta take yi ko akwai inda yake mata ciwo? Komi ita take mata
To dayake dama jikin dasauƙi, ita dai Saleema sai dai tabi ta da murmushi duk da har yanzu zuciyar ta be dena zugi da radaɗin da yake mata ba, har sanda Khalil ɗin yashigo gidan shima ya hau tambayan ta, sai dai yaji daɗin ganin ta wasai da lafiyan ta, don har hira suka koma suna yi, nan ne hankalin su ya ɗan kwanta.
Washe gari Sunday har yamma Saleema lafiyan ta ƙalau, domin a ranan ma tafi samun lafiya fiye da jiya, sai dai da dare jiki yaƙi daɗi dole suka dangana ga asibiti.
Duk wani makusantan su tun a daren tuni yaji labarin rashin lafiyan ta, su Ummi duk sun hallara asibitin hankalin su duk a tashe, musamman yanda suka ga likitocin sai kai komo suke yi a ɗakin da aka kwantar da Saleeman, kuma sun ƙi ce musu uffan bare su san meke wakana.
Zuwa goman dare, lokacin wajen awanni uku da shigar da saleema sannan likitan ta ya nemi ganin su, gaba ɗaya suka ɗunguma wajen su, doctor ɗin be musu wata ƙwaƙƙwaran bayani ba, illa kwantar musu da hankali da yayi, sannan ya faɗa musu baza su samu ganin ta ba har sai gobe.
Zuwa lokacin Halwa tasha kuka kamar zata ƙarar da hawayen ta, da zasu tafi gida cewa tayi babu inda zata je, daƙyar su Ummi suka lallaɓa ta suka koma gida har Khalil ɗin aka bar Ummi ita kaɗai, tunda su ma su Abba duk sun dawo, kowa ya tafi da fargaba a halin da Saleema take ciki.
Zuwa washe gari tuni duk sun hallara, har lokacin dai babu wani labari daga wajen doctors, sai daga baya tukun Doctorn ya nemi gana wa dasu, dalla-dalla yayi musu bayani
Zuciyarta ta rigada ta gama kumbura har ta kai matakin da dole sai dai ko ayi mata Theater da gaggawa a cire mata a sauya mata, ko kuma tarasa ranta domin ya daina aiki gaba ɗaya
Babu wanda be girgiza ba da jin wannan zance, amma ya suka iya da ikon Allah?
Tuni anyi cuku-cukun yanda za'a samu ayi mata aikin a cikin kwana biyu, Abroad za a fitar da ita
Sai dai kuma Allah shi yafi su ƙaunar ta, a kwana na uku ranan da ake saka ran tafiya da ita, a ranan Allah ya amshi abun sa, Saleema ta amsa kiran Allah batare da ta sake shaƙan numfashin duniya ba, tunda tun lokacin da aka kawo ta komi na jikin ta ya dena aiki sai da na'ura.
Musalta muku yanda Familyn nan suka shiga ɓata lokaci ne, domin dai alƙalami na bazai iya muku bayanin tashin hankali da ruɗun da suka kasance ba, tun a asibitin ma Halwa da Ummi suka zube ƙasa a sume, shi kansa Khalil sai da jiri ya ɗibe sa aka kwantar dashi, ga dai shi idanun sa biyu sai dai komi nasa ya dena motsi har sai da yayi kusan awanni biyu ahaka, (ma'ana yayi suman Ido buɗe ne) sosai mutuwar ta shige sa, tabbas kuka rahma ne ga bawan da yashiga ruɗin rayuwa, sai dai Khalil ya kasa samun hawayen da zai zubar don yaji daɗi da salama a zuciyar sa, wannan dalili ne yasaka zuciyar sa tayi masa nauyi fiye da tunanin mutum, be iya ma buɗe baki yayi magana kawai ya zama tamkar status ne
Itama Ummi an yi Sa'a ta farka tun a time ɗin, shi kam Abba dauriya kawai ya ara ya yafa wa kansa, but duk da haka sai da yayi ta sharan hawaye sabida ya kasa jurewa.
Halwa dai bata farka ba har aka kai Saleema gidan ta na gaskiya, mugun hawa jinin ta yayi, kasancewar tana da hawan jini tun lokacin cikin Ahmad da aka harbi Khalil, bata farka ba sai a washe gari, sai dai duk wanda yake ɗakin a lokacin dole ne ya zubar da hawaye sabida tausayin ta, sai da Nurse suka yi mata alluran barci kafin suka samu sukuni, Dattijuwa me aikin su ita aka bari a wajen ta, tunda duk sun tafi gida karɓan gaisuwa
Sai a daren ranan ne Khalil yasha kukan sa ma'ishi, tare da raya daren don nema wa Saleema gafara wajen Allah Sarki, a zaune ya kwana a ranan, kuma koda safe be samu yayi barci ba ya tafi asibiti ganin lafiyan Halwa, bata farka ba alokacin, sai ya nufi gidan su Saleema inda anan ne ake karɓan gaisuwa.
Sai da yamma ne aka faɗa musu ta farka, dole suka ɗunguma zuwa wajen ta
A kwana biyu kawai ta fita hayyacin ta, ga ciki da take fama dashi, gashi kuma ba'a son masu irin laluran ta da tashin hankali, amma ya aka iya, sai dai kwantar mata da hankali kawai da suke tayi tare da mata nasiha me ratsa zuciya, da kuma nuna mata yin tawakkali ga duk wani ƙaddara da yasame mu, Mom CE me ƙarfin halin mata wannan maganan, don ita Ummi ma tana gida ba da ita aka zo ba
Sai dai Halwa ta kasa barin kukan, domin ko tayi yunƙurin dena wa, da zaran ta tuna Saleema ce ta rasu sai kukan ta yadawo sabo, an yi rarrashin duniya taƙi yin shiru, dole suka zuba wa sarautar Allah ido, duk idan kukan nata ya dawo yi take yi kawai babu me tsayar da ita, sai idan ta gaji don kanta sai tayi shiru anjima ta sake dasa wa, gaba ɗaya duk ta ya mutse ta saka wa kanta ciwo na ƙarfi da yaji, domin dai sai da tayi wajen sati ɗaya a asibitin kafin a sallame ta, ga hawan jinin ta da yaƙi sauka, likitoci sun yi mata maganar hakan zai iya shafan lafiyan ta da abinda ke cikin ta amma taƙi sauraron su.
Tunda suka koma gida ma babu lafiya, haka rayuwan taci gaba da Gara mata yau ciwo gobe lafiya, Khalil haka yake fama da ita ko kaɗan ba ya gajiya da mata hidima, duk wani farin ciki dake gidan nan nasu yanzu babu, rasa Saleema cikin rayuwan su ba ƙaramin giɓi yay musu ba, idan kashiga gidan sai dai kaji shiru ko motsin kirki ba sa yi
Su Husna sai dai me aikin su ke kula dasu, ita take musu komi.
Daga baya ma Mom zuwa tayi ta tafi da Halwan gidan ta, tunda sosai take jin jiki, kullum cikin ciwo take
Shima Khalil can yake wuni idan ya je aiki ya dawo, aikin ma ba kullum yake zuwa ba, saboda shima har yanzu ya kasa dawo da kuzarin sa, ya kasa manta Saleema a ransa, baya iya taɓuka komi.
Ahaka rayuwan taci gaba da tafiya har sanda cikin Halwa ya shiga watan haihuwa, lokacin ma tuni tana asibiti saboda yanda takoma sai kun tausaya mata, gaba ɗaya ta kumbure tayi suntum kamar ba ita ba, cikin yayi girma sosai har ba ta iya ma tafiya
Lokacin da tasoma naƙuda an ma fid da ran zata iya rayuwa, domin kwanan ta biyu tana a halin ciwon naƙuda, gashi hawan jinin ta yayi mugun hawa
Likitoci sun yi iya yin su amma ta kasa haihuwa da kanta, tunda jinin ta ya kai matakin da baza ta iya haihuwan ba, kuma komi zai iya faruwa da ita
Ganin idan taci gaba da zama ahaka zata iya rasa ranta dole aka shirya yin mata CS, ahaka aka shigar da ita ɗakin Theater bata ma san a inda kanta yake ba.
Khalil yasha kuka sabida tausayin matar sa, daƙyar ma ya iya saka hannu da za'a yi mata CS ɗin, dole Sameer da Brr. Tahir sukai ta tausan sa suna ba sa baki, su ma duk