Header Ads
Showing 105001 words to 108000 words out of 132567 words

Chapter 36 - BARRISTER IBRAHIM KHALIL Complete Document by Nafisa Isma'il Lawal.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jul 2024

1167

Ads at the middle of Article

tana dariya




Sai kuma tace "Me muka samu ne?"




Tana murmushi tace "Ahmad".




"Allah Sarki ki ce sunan Saurayina ne? To Allah ya raya sa ta hanyan gaskiya".




Ita dai Halwa murmushi kaɗai tayi tana amsa wa aranta




Nafeesa tace "to gashi kuma abubuwa da dama sun wuce ki, an sha karatu wlh ga kuma tests da akai ta yin mana".




Cikin damuwa Halwa tace "eyya ban ji daɗi ba, yanzu ya zan yi kenan?"




"Kar ki damu zan raka ki wajen malaman sai kije ki nemi alfarma ko zasu yi miki tunda kinga an kusa fara Exams, kinga sai ki siya handouts ɗin da yawuce ki kije kiyi ta karanta wa".




"Ai kuwa Na gode". Halwa tafaɗa cike da jindaɗi




"Babu komi ai muna tare".




Daga nan sun ɗan taɓa hira akan karatun su wanda Nafeesan take ta ƙara mata bayani akai, sai da Malam yashigo sannan suka nutsu suka maida hankalin su ga karatun.




Kamar yanda Nafeesa tace mata zata raka ta wajen malaman, suna samun free suka tafi, taci Sa'a don wasu daga cikin malaman sun ce gobe tazo zasu yi mata, sai kuma waɗanda suka bata assignment, mutum ɗaya ne yayi mata text ɗin sa nan take, ai kuwa daƙyar ta amsa uku cikin biyar tunda babu wanda aka yi da ita, su ma ɗin wanɗanda ta'amsa turancin ta ne tagwamitsa yanda tafahimta sannan tamiƙa tafito.






Tunda tadawo gida babu abinda tatasa agaba sai karatun, sai wajen ƙarfe biyar tatashi tayi musu abincin dare sannan taƙara koma wa tadasa daga inda tatsaya tunda babu abinda zata yi.
[1/5, 9:31 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️




*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_




*بسم الله الرحمن الرحيم*






*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```


*JIKAR LAWALI CE*✍️


*Wattpad: UmmuDahirah*👈




*\F.W.A📚/*


```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._


*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._




*BOOK TWO*




.


_______________________________


*CHAPTER Twenty Two*


________🎓Zaman Khalil da Halwa zama ne tamkar ba mata da miji ba, babu abinda ke haɗa su sai gaisuwa, idan yatafi aiki itama sai tatafi school ɗin ta




Zata gyara gidan tayi musu girki kullum bata gajiya amma magana wannan baya haɗa su in ba ya zama dole ba




A ɗan zaman nan da suka yi a matsayin ta na matar sa tuni ta gane ta afka ƙaunar sa, bata da aiki yanzu sai tunanin sa da kuma zaman da suka yi abaya lokacin yana mata magana sosai, karatun da yasaka ta a gaba da kuma soyayyar Khalil wanda bata san sanda tafaɗa ba sun haɗe mata sun yi mata yawa, don haka gaba ɗaya yanzu ta rame ko kaɗan bata da sukunin zuciyarta, ga karatu ga tunanin da yazamar mata jaraba, da farko ta so duk yanda za'a yi ta yakice sa a ranta amma ina hakan ya gagara, wani lokacin har zuwa take yi tazauna kusa dashi tana masa magana ko wai zai riƙa kulata tasamu sukunin zuciya sabida yanda ƙaunar sa ke azalzalan ta, amma yanda tazauna haka zata tashi babu abinda ke haɗa su, hakan na ƙara saka ta shiga mawuyacin hali, har tashiga ɗaki tayi ta kuka tana tirr da zuciyar ta akan rashin adalcin da tayi mata, duk a maza ta rasa wanda zata so sai mijin ƴar uwanta da take ganin ƙimar ta sosai, wanda idan ba ƙaddara da ya haɗa su ba ba ta tunanin zata iya auren sa, a yanda tafahimta Khalil bazai taɓa son ta ba Saleema kaɗai yake so, ita kawai zata yi zaman haƙuri ne har sanda Saleeman zata samu lafiya tasan makomar ta, tunda tarigada ta saka a ranta idan Saleema bata son auren to guduwa zata yi, wannan shine kaɗai hanyan da taga zata iya guje wa auren nan.








*****
Ahmad na wajen Ummi har yanzu ita take kula dashi, idan tatafi aiki sai kuma Larai tahaɗa su ita da Husna taci gaba da kula dasu, idan kuma ta dawo sai tarage mata aiki wajen amsar Ahmad ɗin, tunda aiyukan sun yi ma Larai yawa, ga aikin gida ga kuma raino.




Har yanzu dai Saleema babu labarin ci gaba, kullum iyayen ta addu'a suke yin mata Allah yatashi kafaɗun ta, idan Ummi taje aiki wuni take yi a wajen ta tunda yanzu ana barin ta tana shiga




Itama Halwa wani lokacin tana zuwa duba ta, takan yi kuka duk sanda taje taga Saleema cikin wannan halin da ba ta sanin a duniyar da take ciki.




Rayuwa taci gaba da tafiya yanzu gashi har Saleema ta shafe wata biyu curr kafin tafarfaɗo, zo ku ga murna wajen ahalin ta duk da kuwa ba wai ta dawo hayyacin ta gaba ɗaya bane tana cikin ciwo sosai, amma dai ahaka kowa ke murna da samun lafiyan ta




An ci gaba da treating ɗin ta har zuwa ɗan wani satikai inda tasamu lafiya sosai alhmadulillah sai abinda ba'a rasa ba, ciwon zuciyarta yanzu shine matsalan ta, but duk da haka an ɗaura ta akan magani




Duk idan Khalil yatashi daga aiki can yake wuce wa, wani lokacin ma idan zai tafi da safe sai ya soma leƙa ta kafin yawuce aikin sa




Haka itama Halwa daga school can take wuce wa tayi zaman ta sai dare idan Khalil yazo sai su taho tare




Hakan na faranta ran Saleema sosai, musamman idan taga ƴan uwanta tare da ita, babu jima wa aka sallame ta gaba ɗaya suka dawo gida




Tunda suka dawo sai kuma Halwa takoma kula da ita, ita take yin mata komi bata barin ta taɗauki ko tsinke, idan har ba wani muhimmin abu suke a school ba bata zuwa, tunda a yanzu ba an cika yin musu lectures bane sabida kusantowar Exams ɗin su, idan kuma suna da Lecture irin guda ɗayan nan ƙin zuwa take yi




Shima Khalil yana bata kulawan sa sosai, yana faranta mata da iyawan sa, sosai yake ƙara jin son Halwa aransa musamman yanda yaga tana ɗawainiya da Saleema ko kaɗan bata gajiya, wani lokacin sai yazauna yay ta tambayan kansa meyasaka yake mata haka? Halwa tana da kyawawan hali da shiga rai ga duk wanda yazauna da ita dole sai ta burge sa, to shi meyasaka bazai yafe mata ba? A yanzu dai ba laifin take aikata wa ba tunda ta tuba, yakamata yabata dama yacire haushin ta a ransa ya amshe ta hannu bibbiyu a matsayin matar sa tunda abinda yafaru ya rigada ya wuce, ko Allah ana masa laifi ya yafe bare kuma shi bashi ne tay ma laifin ba, kawai yayi amfani da hakan ne yana cuta ma kansa bayan kuma yana ƙaunar ta sosai a ransa, shiyasa yanzu yasassauto yake shiga harkan ta




Hakan ba ƙaramin faranta ranta yayi ba, sosai a yanzu take matuƙar farin ciki saɓanin abaya da koda yaushe take cikin damuwa






Saleema duk bata fahimci komi akan auren Khalil da Halwa ba tunda ba wai faɗa mata akayi ba, kuma Khalil ba kwana ɗakin Halwan yake yi ba, babu abinda ke haɗa su wanda zata iya zargin su, saboda tunda tadawo Halwa takoma ɗakin ta na da tadena kwana a cikin ɗakin Khalil ɗin, kuma tayi hakane duk wai saboda Saleema kar ta zargi wani abun tunda ba'a so tasani sai idan ta samu lafiya




Shima Khalil ɗin ganin haka sai yadena kwana aciki yana bin Saleema ɗakin ta, tunda dai babu daɗi ace yana kwanar mata a ɗaki shi da wata matar




Hakan yasa Halwa ta ƙara ganin ƙimar Khalil a idanun ta, tabbas Khalil mutum ne na daban, tsananin kyawun halin sa tare da kirkin sa ya wuce yanda ake zato, ɗaya ne tamkar da dubu, dole ko kana so ko baka so ka ƙaunace sa, idan har kuwa zaka yi mu'amala dashi dole ne yashiga ranka.






Ahaka har su Halwa suka soma Exams ɗin su na First semester wanda daga shi ne sai Finally, sai kuma School of Low da zata shiga.








**** ***** *****


Yau aka yi ma su Halwa hutun school don haka da wuri tadawo yau ɗin tunda Pepper ɗaya suka yi




Saleema na kwance kan two sitter ta ɗage ƙafafunta ta ɗaura saman jikin kujeran tajiyo sallaman Halwan lokacin da taturo ƙofan tashigo, tashi tayi dasauri tana mata oyoyo, suka yi Hugging juna suna dariya cike da nishaɗi sai suka zube saman kujeran




"Ai gwara da Allah yadawo dake da wuri, dama yanzu nake tunanin kiran ki in sanar miki zan je gida don yau da kewar su Abba na tashi, na tambayi Barrister ya bar Ni". Saleema tayi maganar idanun ta kan Halwa tana dariya




Yamutsa fuskar ta Halwan tayi kamar yanda yazame mata jiki tace "kai sis yanzu sai ki tafi ki bar ni kenan?"






"A'a wlh nayi tunanin ba yanzu zaki dawo ba, Ni har nayi tunanin bari sai gobe ne kuma sai ga ki kin dawo, sai mu tafi tare yanzu".




Kaɗa kanta Halwa tayi kafin tace "anya zan je kuwa wlh agajiye nike, barci kawai nake so in Yi".




Saleema tace "to ki kwanta ki huta mana, ina tunanin ma idan naje zan taho dasu Husna ne".




"Aa Iyeee wlh baza ki kawo mana aiki ba, akan me zaki ɗauko su?"




Wani kallo me kama da harara Saleema tasakar mata




"Me kike nufi?"




Halwa dariya tayi tace "wlh babu komi, amma don Allah ki bar Husnan ki ɗauko Ahmad ne".




Miƙe wa Saleema tayi tay hanyan ɗakin ta tana faɗin "kar ki damu sister Ni ban ce ki tayani rainon su ba wlh Ni kaɗai zan iya tunda Ni ce uwar su dama ai".




Bata tsaya jin amsar Halwan ba tashige ɗaki abun ta




Itama Halwa tashi tayi tabi bayan ta don taga fushi tayi da ita










"Haba Sister daga wasa?"




Turo baki Saleema tayi tana hararan ta batare da tace mata komi ba tasoma cire kayan jikin ta




Ganin dai ba tanka ta zata yi ba, sai tace "to nima zan je bari in shirya, tare zamu je taho wa dasu".




Baki Saleeman tawashe tace "dagaske sis?"




Gyaɗa mata kai Halwa tayi tace "bari ma kigani".




Tayi hanyan ƙofa tana faɗin "nima bari in je in shirya".






****




Bayan sun gama shirin su drever yakai su gidan su Saleeman




Ummi tayi murnan ganin su barin ma da taga Saleeman ta sake samun sauƙi sosai har wani ƙiba tayi na kwanciyar hankali




"Ummi ina Abba ne don Allah". Saleeman tafaɗa tana kwaɓe fuska tana kallon Ummi ɗin




Ummi murmushi tayi cike da ƙaunar diyar ta tace "ai yau Abban ki yayi nisan zango, amma ina tunanin zai iya dawowa kafin ku tafi".




Gyaɗa kanta tayi tamiƙe tana faɗin "wai ina Husna ne ban ganta ba?".




"Tana wajen Larai wlh, shima Ahmad ɗin don yayi barci ne takawo shi amma da duk suna wajen ta".




Ɗakin Larai tanufa da ɗan gudun ta tana cewa "bari inje inga Ummina".




Tun bata kai ba take kiran sunan Husnan har tashige




Ummi dawo da kallon ta wajen Halwa tayi tana dariya wanda itama Halwan dariyan take yi tace




"Ummi wlh Saleema son yaran ta yayi yawa ko kunyan ki bata ji".




"To ina kuwa zata ji kunya na? Ai Saleema sai ikon Allah, ita da tazauna tana mana kukan cikin ta ya zube wani kunya zata ji anan".




Dariya sosai Halwa take yi itama Ummin na taya ta




Ummin tace "Allah yay muku albarka yarana, yaba ku waɗanda zasu ji ƙan ku".




Halwa na murmushi ta'amsa da "ameen Ummi".




Lokacin Saleema tafito daga ɗakin Larai tana faɗin "itama tayi barcin".




Dariya Halwa tayi tace "ai da kin taso ta tunda zumuɗin ganin su kike yi".




Hararan ta Saleema tayi tana zama gefen Ummi tace "bazan tashe sun ba".




Halwa dariya kawai take mata tana tsokanar ta, ita kuma tana rama wa cike da wasa da dariya




Ummi dai tana jin su bata saka musu baki ba, yau dai tayi ninyan faɗa ma ɗiyar nata auren dake tsakanin Halwa da Khalil, sabida a ganin ta be kamata ayi ta ɓoye mata ba kuma ana cutan Halwan, idan kuma hakan yaci gaba da tafiya tasan sun so kansu da yawa tunda sun gummaci su faranta ran ƴar su sannan su cuta ƴar mutane, yanda tagan su ahaka da tsananin shaƙuwar su bata jin Saleema zata wani damu, don haka ajiyan zuciya tasauke tana aza idanun ta kan Saleeman takira sunan ta




"Na'am Ummi". Saleema ta'amsa mata tana kallon ta




Ummi tace "nasan kinsan ƙaddara Saleema kuma kinsan duk wanda yacika musulmi dole ne ya yarda da duk wani ƙaddara da tasame sa me kyau ko mara kyau.."




Gaba ɗaya shiru suka yi har Halwa suna sauraron ta, yayinda itama kuma tasoma zayyano ma Saleema duk abinda ke faruwa har da juya mata mahaifa yau sai da tafaɗa mata, kuma tayi hakan ne wai don Saleema tasake ganin girman Halwa, tasan cewa bata cancanci ɗaukan wani mataki akanta ba tunda ta taimake ta ta fanni da dama, tayi mata abunda babu wanda ya'isa yay mata shine kyautar yara har biyu, Halwa ba wacce zatayi kishi da ita bane domin ita ɗin me son farin cikin ta ne




Sai da Ummi takai aya a zancen ta kafin Saleema tamiƙe tsam daga wurin tawuce ɗakin su




Hakan yasa suka bi bayan ta da kallo cike da fargaba aran su




Matse baki Halwa tayi hawaye na cika cikin idanuwanta




Kallon ta Ummi tayi suka haɗa idanu sai Halwan tasauya fuskarta da ƙirƙirar murmushi batare da tasan cewa hawayen cikin idanun ta sun sauka saman kuncin ta ba




"Menene na kuka kuma? Bana son shirme kinji ko?" Ummi tafaɗa tana ɗaure fuskarta




Dasauri Halwan tasaka hannu tana share hawayen jin danshin su sosai saman kuncin ta wanda har ɗiga akan hannun ta suka yi, tana so tayi magana amma kalma ɗaya takasa furta wa, tana so tamiƙe tabi bayan Saleema amma ta kasa tashi




Ummi ce tatashi tanufi ɗakin, inda tasami Saleema kwance saman gadon ta danne fuskarta saman pilow, zama tayi akan gadon tasoma yin mata nasiha me ratsa zuciya tare da kwantar mata da hankali, sannan tana nuna mata koda ba Halwa bace dole ne Khalil yaƙara mata kishiya.








Halwa na zaune a inda take ta haɗe hannayen ta waje ɗaya jikin ta nata tsuma, so kawai take yi tasami damar da zata yi kuka sai dai baza ta iya nuna raunin ta anan ba, bashi da amfani ko kaɗan




Tana nan zaune su Ummi suka fito, idanu kawai taɗaura ma Saleema tana son karantan yanayin da take ciki




Ita kuma Saleema sai taɗauke kanta gefe batare da ta bari sun haɗa idanu ba




Larai ce tafito daga kichen tanufi dainning tana jera musu abinci




Cike da farin ciki Ummi tace "to ku tashi muje kuci abinci tunda an gama".




Babu musu gaba ɗayan su suka bi umarnin ta, kan dainning suka zauna Ummi na ta jan su da Surutu duk dan wai su saki jikin su ganin yanda gaba ɗayan su suka yi shiru, babu wanda ke saka mata baki sai murmushi kaɗai da suke saki, sai kuma gajerun amsa da ke fitowa a bakunan su




Bayan sun gama suka dawo Parlour




Saleema bata zauna ba ta wayance tashige ɗakin Larai akan zata wurin Husna.






Har suka gama wunin su Saleema bata sake bari magana ta haɗa su da Halwa ba, yamma na yi Saleeman tace zasu tafi ganin Ummi ma zata wuce wajen aiki, haka suka yi sallama suka fito tare da Ahmad da Larai tahaɗo masa kayan sa tunda Ummi tace baza ta tafi da Husna ba, kuma dama yanzu Husnan ta soma zuwa school ɗin ta ba ma wuni take yi a gidan ba




A cikin mota ma tsit suka yi babu me magana, Halwa ta kasa yin mata magana ne sabida fargaba, ta rasa wani kalma ne zata iya amfani dashi wajen furta ma Saleeman, musamman yanda taga ita kanta bata son kula ta bare kallon ta, sai hakan yasake saka ta damuwa da tsoro cikin zuciyarta




Suna shiga gidan suka fito cikin motan atare, Saleema na rungume da Ahmad tana ƙoƙarin jan Trolly ɗin sa da drever yaciro mata a Boot




Sai Halwa tayi saurin miƙa hannun ta dake faman rawa tace "sister bari in taimaka miki".




Saleema bata ce komi ba tabar mata tajuya dasauri tawuce




Bin bayan ta da kallo Halwa tayi har sai da tashige cikin gidan, ahankali taja ƙafafun ta a matuƙar sanyaye tanufi ciki itama cike da rashin ƙwarin jiki, tana shiga da sallama idanun ta suka sauka kan su ita da Khalil ɗin dake zaune riƙe da Ahmad ajikin sa yana masa wasa, kallo ɗaya kayi masa zaka ga farin ciki tsantsa a fuskar sa wanda ganin tilon ɗan nasa ne yasaka sa wannan tsantsan murnan




Tunda tashigo shima yaɗago kansa yana kallon ta, wani irin kallo yake aika mata dashi me cike da zallan soyayya da nuna shauƙi ga duk wanda yagani




Hakan yaƙara saukar ma da Halwa kasala da mutuwar jiki, idanuwan ta tajanye daga kansa wanda suka kawo ruwa lokaci ɗaya tana ɗaura wa akan Saleema dake wasa da hannun Ahmad




Daƙyar tasoma jan ƙafafun ta bayan tacire idanun ta daga kallon ta tashigo cikin parlour'n, bata ce komi ba tayi hanyan ɗakin Saleeman tashige don ajiye mata Trollyn




Hakan yasa Khalil yabi ta da kallo cike da wani irin yanayi ganin yanda tasauya lokaci ɗaya duk da kuwa be ga hawayen idanun ta ba, amma ya tabbata akwai abinda ke damun ta




"Me yasami Maman Husna naganta ahaka?" Yayi maganar lokacin da yamaida idanun sa kan Saleema




Murmushi Saleeman tayi tace "babu komi wlh me kagani?"




Numfashi kawai yaja batare da yace komi ba yamaida idanun sa kan t.v




Lokacin Halwa tafito tanufi ɗakin ta tashige har da rufe ƙofan da keey, ahankali tazame ƙasa a jikin ƙofan tahaɗa kanta da gwiwa tasoma rere kuka, kuka take yi sosai wanda tatoshe bakin ta da gyalen ta ta yanda babu me jin ta, ita kanta bata san kukan na menene ba, sai dai tasan yana da alaƙa da yanda Saleema tanuna mata, wannan

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads