Header Ads
Showing 66001 words to 69000 words out of 132567 words

Chapter 23 - BARRISTER IBRAHIM KHALIL Complete Document by Nafisa Isma'il Lawal.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jul 2024

1149

Ads at the middle of Article

skert ne wanda yayi mata kyau sosai sai zuba ƙamshi take yi, ɗankwali kawai taɗaura tafito Parlour




Yana zaune saman kujera yana latsa wayan sa, ƙamshin turaren ta yasa shi ɗago kai yana kallon ta, sosai yake bin ta da idanu sabida tayi masa kyau ainun




Ita kuwa bata kula dashi ba sai faman gyara zaman ɗankwalin ta take yi da be gama zama da kyau ba, sai da ta'iso cikin parlour'n kafin taɗago kanta su haɗa idanu, yanda yake kallon ta ne yasa ta jin kamar tajuya takoma amma babu hali dole ta'iso tazauna can kujeran da ke gefen sa, hakan yasa babu yanda za'ayi yaganta dole sai idan ya juya kansa




Ɗan lumshe idanun sa yayi yabuɗe yaci gaba da latsa wayan sa, amma yanda turaren ta ke shiga masa ƙofofin hanci hakan yasa duk yarasa tunanin sa, sosai turaren yayi masa daɗi, sai lumshe idanu yake yi yana buɗewa, daga ƙarshe yaɗago kai yana kallonta yace




"Kin sha maganin ki?"




Ita da taɗan buga tagumi tana tunani nan taji saukar muryan sa a kunnen ta, tayi saurin ɗagowa tana kallon sa kafin tace "a'a sai anjima ne lokacin sha".




Be ce komi ba yakau da kansa yaci gaba da latsa wayan, dama chatting yake yi da Brr. Tahir, ganin dai turaren duk ya ishe sa da ƙamshi hakan yasa yatashi yanufi ƙofa yafice




Tabi bayan sa da kallo tana tunanin inda zai je




Yana fita Garden ɗin gidan yanufa yazauna kan fararen kujerun dake wajen, lumshe kyawawan idanun sa yayi yana sauraron bugun zuciyar sa, hannu yasaka yana dafe setting zuciyar sa tare da faɗa wa duniyar tunani




Har yau ya gaza gane meke damun sa, meyasa yake shiga damuwa akan abinda baya tunanin zai sake gani, kullum zuciyar sa ƙulafucin ranan da yakasa mantawa yake yi tare da fatan sake ganin makamancin ta




Numfashi yaja tare da fesarwa yana ci gaba da latsa wayan sa, be tashi a wajen ba sai da yaji kiran sallah, miƙe wa yayi yasaka wayan sa a aljihu yanufi wajen Me gadi, anan yayi alwala yafita masjid, sai da akayi isha'i kafin yadawo gida




Tana nan zaune a parlour'n, sallah kawai taje tayi tadawo tasake zama, sai dai yanzu kallo take yi, yana shigowa ta'amsa masa sallaman sa tare da yin masa "sannu da zuwa"




Amsa mata yayi yana kallon ta kafin yanufi ɗakin sa yaɗauko car keey yafito yafice


Mintuna goma da fitan sa yadawo riƙe da Ledoji, miƙa mata yayi yace "tasake abincin dake cikin Take-away ɗin a plate" ta'amsa tayi yanda yace sannan tadawo takawo masa, umartan ta yayi tazauna su ci, babu musu tazauna suka ci abincin suka gama sannan tatashi takwashe komi takai kichen, dawowa tayi tazauna taci gaba da kallon ta yayinda shi kuma yana ƙasa har yanzu yana danna waya, babu jimawa kuma yamiƙe yashiga ɗakin sa yaɗauko computer'n sa yadawo yazauna kan kujera yasoma aiki aciki




Har barci yakwashe Saleema a wajen yana nan yana aikin sa, sai wajen ƙarfe 11:00pm. Sannan yadakata yana kallon ta, hakan yasaka yamiƙe ba don ya gama aikin ba yatattara kayan sa yamayar ɗaki yadawo yatashe ta yace "su je su kwanta". Bayan shi tabi suka shige ɗakin sa yarufo ƙofa.




.




***** ****** ****** ****


Yau a makare suka tashi sai ƙarfe 11:30am. Sannan Khalil yasoma farkawa, wanka yayi yafito yana tsane jikinsa, alokacin ne Saleema tafarka itama sai dai taƙi tashi bare tanuna alamun ta farka, har yagama shiryawa yafita parlour yazauna, Kallo yakunna yasaka tashan CCT.V NEWS yana kallon labarai, jefi-jefi kuma yana latsa wayan sa




Ƙaramar wayan sa dake ajiye ne tayi ƙara yaɗauka yana karawa a kunne tare da yin sallama




Brr. Tahir amsa mishi sallaman yayi yana faɗin "Ango Ango kasha ƙamshi".




Murmushi Khalil yayi yana shafo kwantaccen gashin kansa yace "zaka fara ko?"




Dariya Brr. Tahir yaƙyalƙyale dashi yana cewa "iyeee Ango uhmm Ango Mijin Amarya.."




Katse shi Khalil yayi yana ɗaure fuska




"Wai kai meye haka ne kanka ɗaya kuwa?"




"Uhmm ai baza ka gane kaina ɗaya ba sai idan nazo ganin Amarya". Cewar Brr. Tahir Yana sake sakin dariya me sauti




Shiru Khalil yayi be sake ce masa komi ba sai yamayar da hankalin sa kan kallon sa




"Hello kana jina kuwa?"




Guntun tsaki Khalil yaja yana faɗin "ina jinka mana idan ka gama zan kashe wayana".




Brr. Tahir murmushi yayi yace "sorry Man akwai magana fa, kasan narigada naga gidan da mutumin nan yake zaune sai dai be bani dama har yanzu mun tattauna ba".




Khalil ɗan tattaro naman goshin sa yayi cike da takaici yace "yana son Raina mana wayau ne fa, but bari dai in taho sai mu tattauna don nima na samu ƙwaƙwƙwaran hujjan da dole sai ya saurare mu".




"Ok sai ka zo".




Daga haka sukayi sallama yaciro wayan daga kunnen sa yana miƙe wa tsaye yakoma ɗakin sa, abubuwan da zai buƙata yaɗauka sannan yanufi wajen gadon sa yana kallon Saleema da har yanzu tana nannaɗe acikin bargo taƙi tashi, yasan da cewa tun ɗazu ba barci take yi ba don haka yamatso gab da ita yaraɗa mata




"Ni na fita bazan daɗe ba zan dawo, ki kula da kanki uhmm?"




Tun sanda yasoma mata magana tabuɗe idanu tana kallon sa, sai tasaki murmushin da yakufce mata batare da ta shirya yin sa ba tayi saurin gyaɗa masa kai




Shima murmushin yayi bece komi ba yajuya yafice tabi bayan sa da kallo.
[11/7/2020, 4:01 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️




*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_




*بسم الله الرحمن الرحيم*






*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```


*JIKAR LAWALI CE*✍️


*Wattpad: UmmuƊahirah*👈




*\F.W.A📚/*


```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._


*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._


*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```




.


*CHAPTER 45*




Minti goma da fitan shi kafin tamiƙe tasauko daga gadon, Toilet ɗin sa tashiga tayi wanka tasaka towel ɗin sa tafito tanufi ɗakinta, akan stool tazauna gaban dressing mirror tasoma shafa Lotions a tattausar farar skin ɗinta, shafa Lotions ɗin take yi but hankalin ta baya wajen, sai faman zuba murmushi take yi cike da tsananin nishaɗi da kallo ɗaya kayi mata zaka fahimta, har tagama batasan a wani duniyar take ba, hakan yasa tashafe fiye da awa ɗaya tana abu ɗaya, daga ƙarshe tamiƙe tanufi wajen kayan ta tazaɓo wanda zata saka


Jan Material Less me stone ajikin sa, ɗinkin doguwar riga pitted, yayi mata kyau sosai ya kamata cif-cif cike da sha'awa, tayi wannan ɗaurin na ture gaka tsiya sai ƙamshin amarci take zabgawa




Fitowa tayi takoma ɗakinsa tagyara tasaka air freshener, har toilet sai da tawanke kafin tafito tazauna aparlour takunna t.v




Zaman ta babu daɗewa tajiyo Nocking, miƙewa tayi tanufi ƙofan don tasan ba Khalil bane, tana buɗe ƙofan idanuwan ta suka faɗa cikin na Halwa dake tsaye tana zabga mata murmushi, tana riƙe da Husna da hannu ɗaya rungume ajikinta, ɗayan hannun kuma tana riƙe da ɗan ƙaramin trolly


Cike da tsananin murna Saleema tatarbe ta tana rungume ta daga ita har Husnan dake barci




Daga ƙarshe shigowa sukayi suka yada zango a parlour'n bayan Saleema ta amshi Husna ta shimfiɗe ta akan kujera




"Sister kinga yanda kika sauya kuwa? Sai ƙyallin amarci kike yi sai dai fa kin rame". Cewar Halwa da tazuba mata idanu tana kallon ta da murmushi a face ɗin ta




Itama Saleema dake faman zabga murmushin tace "Hmm Ni dai bana son sharri, duka yaushe nayi auren da zakice ina ƙyallin amarci".




"Allah kuwa dagaske my Sister kin sauya sosai, gani nake kamar na shekara ban ganki ba saboda tsaban kyau da kikai min, gaskiya aure rahma ce".




Dariya Saleema tayi wannan karon tace "Allah ko ƴar uwa?"




Ɗage gira ɗaya Halwa tayi tace "dagaske My Sister".




"To kice kema kin kusa motsawa musha biki?"




Ɓata fuska Halwa tayi tana sauya zancen da faɗin "ƴar uwa nifa ba zama zanyi ba don tare da drever nake zai kai ni School, ƙarfe 02:30pm nake da Exams, Ina Mijin naki mu gaisa kafin in tafi?"




Saleema tace "ya fita yanzu".


Murmushi Halwa tayi tana kama haɓa tace "har ya gama cin amarcin ne ya soma fita?"




Hararan ta kaɗai Saleema tayi tana wani irin murmushi da bakinta yaƙi rufuwa




"To sister zan tafi kinga lokaci ya ja da yawa, akwai saƙon Ummi cikin jakan nan tabani in kawo miki, tace tana gaishe ki tare da Abba ma".




Saleema kamar zatayi kuka tace "Allah Sarki ina amsawa nayi kewar su sosai".




Dariya Halwa tayi tamiƙe tana faɗin "ko dai zakiyi kuka ne?"




Hararan ta tayi itama tatashi tana cewa "Sister ko ruwa baki sha ba fa? Bari in ɗauko miki".


Taƙarike maganar tana nufan wajen Fridge batare da tajira cewar Halwan ba, ɗauko ruwan tayi tadawo tana cewa




"Sai yaushe kuma sister?"




Wulla idanuwan ta tayi alamun tunani tace "uhmm sai dai idan nagama Exams ɗin nan sai in zo inyi miki wuni ko?"




Turo baki Saleema tayi kamar zatayi kuka tace "kai sister kenan har sai na jira kin gama Exams zaki sake zuwa?"




Murmusawa Halwa tayi tace "ke dai karki damu zuwa gidan ki ai sai kin gaji da ganina, yaushe ma akayi auren ne? Ki kwantar da hankalin ki".




Dariya Saleema tayi tace "to shikenan muje in raka ki".






Har wajen mota Saleema taraka ta, anan suka gaisa da Drever, Halwan tashiga mota yaja suka bar gidan




Sai ɗaga musu hannu take yi har Me gadi yarufe Gate ɗin kafin tasauke hannun ta tajuya cikin gidan cike da kewar ƴar uwan nata




Tana shiga parlour'n ta'iske Husna ta farka sai wutsil-wutsil take yi tana son sauko wa, dasauri taƙarisa wajen ta taɗauke ta tana dariya cike da ƙaunar ta tasoma yin mata rawa tana mata wasa




"Iyeee Mamana kin tashi? Yau kin dawo wajena ko? Oh i miss You so much".




Tamanna mata peck a baki, ita kuma sai faman ɓangale mata bakin take yi tana yarfe hannayen ta tare da tsalle jikin ta




Dariya Saleema tayi tana sake riƙe ta dakyau ganin yanda take ta zillewa wai adole tana wasa




"My dear ki dena karki suɓuce min kinsan girma ne dake".




Ita kuma kamar tana jinta taci gaba da zillewa tana tsallen murna sai ɓangale baki take yi, Allah ya zuba mata wayau gata kuma bata da ƙyuya ko kaɗan, duk wanda yaɗauke ta haka zatai ta ɓangale masa baki kamar tasan shi




Tana nan zaune tana ta jijjiga yarinyan tana mata wasa kamar ta sami sa'ar ta sai faman yin mata hira take yi da surutu




Khalil yaturo ƙofan yashigo da sallama a bakin sa




Ɗago kai tayi tana kallon sa kamar yanda shima ɗin yaƙure su da nashi idanun me tsananin kyawu da kaifi




Gaban Saleema ne yafaɗi, sai Lokacin tatuna bata sanar masa da maganar dawowar Husnan ba, daƙyar takawar da fargaban nata tana amsa mishi sallaman




Takowa yayi yashigo ciki still idanun sa na kansu, yarinyan kawai yake kallo cike da sha'awa, shi me son yara ne sosai suna matuƙar burge sa




Matsowa kusa da ita yayi yana faɗin "wannan yarinyan wacece?"




Yaƙarike maganar yana duƙowa gaban ta ya'amshi yarinyan yana sake ƙure ta da idanu, sosai yarinyan tayi masa kama da wacce yasani, lokaci ɗaya kuma yaji ta shiga ran sa har be san sanda yasakar mata kyakkyawar murmushin sa yana wasa da hannun ta ba, itama ɗin sai ɓangale masa baki take yi kamar yanda tasaba tana kallon sa




Mai da idanun sa kan Saleema da taduƙar da kanta ƙasa yayi




Har alokacin bata iya basa amsar tambayan da yayi mata ba




cikin murmushin sa yace "Ya sunan ta?"




Cike da sanyin murya tace "Husna".




Kallon yarinyan yasake yi sai kuma yamiƙe tsaye yana zama kan kujera ya'ajiye ta a cinyan sa yaci gaba da mata wasa




Ita dai Saleema na zaune tana jin su tare da satan kallon su, sosai taji daɗin yanda yanuna son yarinyan duk da kuwa be san ita wacece ba




"Ina Maman ta ne?" Yajeho mata tambayar yana kallon ta




Cike da fargaba Saleema tace "tana gida".




Ɗan waro idanun sa yayi cike da mamaki yace "kenan kawo miki ita akayi?"




"Eh zata zauna a wajena ne".




Kallon ta kawai yake yi cike da tsantsan mamaki, be kai ga magana ba yahangi ɗan kyakykyawar Trolly ɗin dake ajiye gefe




"Kayi haƙuri don Allah nasa an kawo min ita ban tambaye ka ba, wlh na manta ne". Tayi maganar cikin ladabi da sanyin murya




Still kallon ta yasake yi sai kuma yamaida idanun sa kan yarinyan




Shiru kamar bazai yi magana ba sai kuma yace "yanzu har kin warke da zaki iya raino?"




Murmusawa tayi bata iya cewa komi ba sai ɗauke ganin ta da tayi daga kansa




Ajiyan zuciya kawai yasauke be sake cewa komi ba kuma be bata yarinyan ba, aransa kuma tunani yake yi yanda ita Saleeman take son yara har da zata ɗauko yaran mutane da sunan riƙe wa, sai kuma tsananin mamakin uwar yarinyan da ta'iya rabuwa da ƙaramar yarinya kamar wannan, yana son yayi mata tambayan ya zatayi idan zata shayar da ita amma kunya ya hana sa tambayan ta, baya ga haka akwai tarin tambayoyi da yake son yin mata




Saleema ganin shirun dai yayi yawa sai tamiƙe taja Trolly ɗin tanufi ɗakin ta.




.




***** ***** ******* ****




*BAYAN SATI BIYU*


A cikin wannan kwanakin shaƙuwa ne sosai yashiga tsakanin Khalil da Saleema, sun yi kwanakin ne cikin nuna kulawan junan su tare da girmama juna




Duk wani kulawa Khalil yana nuna mata tare da tausayin ta me tsanani da yake yi cikin ransa, baza ka taɓa tunanin su ɗin ba masoya bane domin yanda suke gudanar da zamantakewar su ko masoyan asali albarka




A yanzu soyayyar Khalil sosai yaginu a zuciyar Saleema, tasan da cewa tayi dace ga miji na gari don Khalil ɗan halak ne kuma ya haifu




Shi kuma har alokacin ya kasa jin soyayyar ta cikin ransa, sai dai yasan yayi dace da mata na gari kuma yana ji aransa zai iya zama da ita har ƙarshen rayuwan sa batare da yayi dana sani ba


Zan iya cewa tare suke rainon Husna sabida yanda Khalil ke nuna kulawan sa agare ta, idan har yana gida ko baya aikin komi yarinyan ko yaushe tana hannun sa, sosai yarinyan tashiga cikin ransa.




Jikin Saleema alhmadulillah yanzu ta warke sumul babu abinda ke damunta, tattalin mijinta kawai tasaka agaba sai kuma rainon Husna.








*******


Yau ce ranan da Halwa tace zata zo don haka da sassafe Saleema tatashi cikin ɗoki tasoma aiyukan ta, babu laifi yanzu ta saba da duk wani hidiman gidan duk da ba wani aiki me yawa take yi ba




Shi kansa Khalil yasan da zuwan Maman Husna don tun jiya da sukai ta waya da Halwa yaga tana ɗoki yatambaye ta take faɗa masa Mamar Husna ce zatazo




Shirin Office yayi cikin Ash colour ɗin Suit da yayi masa kyau matuƙa yawuce wajen aiki bayan yayi musu solfie su ukun cike da nishaɗi.






Har tagama abinci da duk abinda yakamata kafin Halwa ta'iso.








_Alhamdulillah anan nakawo ƙarshen BOOK ONE sai ku tara a BOOK TWO don jin me zai faru._




.






_ya zaman Khalil da Saleema sai kaya, kuna ganin tausayin da yake mata zai iya juye wa yazama ƙauna?_




_Shin kuna ganin Halwa zata cika burin ta?_




_me zai faru idan ta mayar da Husna ga Mahaifin ta?_




_ya Maganar Haris da be san yana da ƴa ba?_




_kuna ganin Zainab zata amince da soyayyar Nura?_




_Ya maganar Nazeefa da takamu da soyayyan wanda be san ma tana yi ba?_


_kuna ganin idan har Mom tagane zata aura mata shi kamar yanda tayi alƙawarin gano meke damunta kuma tashare mata hawaye?_


_Shin kuna ganin Halwa zata koma ga Iyayen ta?_


_Shin ya za su karɓe ta?_




_duk a Two ne zaku samu amsar tambayan ku da dalilin da Nura yajuya wa Halwa baya?._






_sai ku biyo NI don ji amsoshin ku_


_Nafisat Jikar Lawal ce_✍️




Ba_byeee 👋👋👋👋👋👋👋👋😉🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️


[11/9/2020, 9:13 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️




*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_




*بسم الله الرحمن الرحيم*






*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```


*JIKAR LAWALI CE*✍️


*Wattpad: UmmuDahirah*👈 _WhatsApp Number 07065334256_




*\F.W.A📚/*


```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._


*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._


````Allah ya dawo dani mu tsunduma cikin labarin


Na gode masoyana.```






*BOOK TWO*




.


_______________________________


*CHAPTER One*


________🎓Suna zaune su Biyu akan dainning table suna cin abinci




Halwa kai abincin bakin ta tayi tana lumshe idanun ta cike da jindaɗi, sai kuma tabuɗe idanun taɗaura akan Saleema da itama tamayar da hankali wajen cin abincin ta, murmushi me sauti Halwa tasaki still tana kallon ta tace




"Sister gaskiya abincin nan kamar zai tsinke min kunnuwa, kina gani fa har rawa suke yi sabida tsaban daɗin abincin nan".




Dariya Saleema tasaki tana kallon Halwa da taƙara ɗibo wani abincin takai bakin ta tana faman lumshe idanu




"Bari dai in tashi in ɗauko pilow in tare ki dashi, idan ba haka ba babu me iya tare ki nan gaba in kikaci gaba da wannan santin".




"Allah Sister ba santi bane, kinji yanda abincin yake da matuƙar daɗi ne sai kace wacce tadaɗe da ƙwarewa, wlh ko Ni bazan iya rin wannan ba".




Murmushi Saleema tayi cike da jindaɗi sai dai bata iya cewa komi ba




"Ƙara min miyan". Halwa tace hakan tana miƙo mata plate ɗin shinkafan




Zuba mata miyan tayi tana faɗin "Kinsan jiya da Zazzaɓi Husna ta kwana, wlh duk na ruɗe sabida yanda naga tana yi, da ba don Yaya Barrister ba bansan yanda zan yi ba, shi yatashi yayi ta rarrashin ta har yana cewa in koma in kwanta". Taƙarishe maganar nata tana wani irin murmushi me ma'anoni da yawa wanda Ni kaina bangane mata ba




Shiru Halwa tayi bata ce komi ba illa kai abinci bakin ta da take yi




Ɗago kanta Saleema tayi takalli Halwan sai kuma tamayar da kanta kan abincin tana sake yin murmushi




Tasan da cewa baza ta taɓa tankawa ba, halin ko in kula shi Halwa ke nuna wa Husna,

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads