Showing 99001 words to 102000 words out of 132567 words
Chapter 34 - BARRISTER IBRAHIM KHALIL Complete Document by Nafisa Isma'il Lawal.txt
kallo, ta rigada ta yarda a ranta tabbas yaron Khalil ne wannan, sai dai bata so tayi maganar ne yanzu sai idan hankalin kowa ya kwanta duk da kuwa zuciyar ta a matse take da son sanin gaskiya
Tabbas ba'a shedan ɗan yau, bata taɓa tunanin Khalil zai iya aikata mummunan aiki irin wannan ba, a jiya tayi kuka sosai akan wannan al'amarin, har abun ma yafi tada mata hankali a bisa ciwon Khalil ɗin, yanzu tana ji tana gani an haifa mata jika shege
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Tafaɗa a ranta tana ɗauke idanun ta kan yaron zuciyar ta cike da ƙunci
Numfashi taja kafin tamiƙa ma Ummi yaron tana faɗin
"Bari muje, dama zan koma gida ne sai anjima in dawo".
Amsar yaron Ummi tayi sannan tace "to Hajiya sai kin dawo".
Sallama suka yi daga nan suka fice ita da Nazeefa.
*****
Da yamma aka sallami Halwa kasancewar yanzu babu wata matsala dake damun ta, lokacin da zasu tafi Abba ya zo don haka shine yace su haɗo kayan su yakaisu
Halwa ta so taje duba jikin Khalil da Saleema amma babu hali, gashi har a lokacin ba'a basu damar sake ganin Saleeman ba
Lokacin da suka isa gida Halwa tawuce ɗakin ta kai tsaye, tana shiga ta'ajiye Yaron saman gado sannan tazauna tana riƙe kanta dake faman sara mata sakamakon kukan da tasha daga jiya zuwa yau
Husna ce tashigo ɗakin kasancewar ƙofan a buɗe yake, gaba ɗaya jikin ta da kayan ta ta ɓata shi da garin Flower, har ta a fuskarta zuwa gashin kanta dake ɗaure da Ribom duk Flower ne
Tunda tashigo Halwa take bin ta da kallo batare da ta motsa daga inda take ba
Ita kuma Direct wajen Halwan tanufo tana yarfe hannayen ta tana faɗin
"Mammaaa.."
Tana washe baki da ƙananun haƙoran ta guda shida da tamallaka
Gaban Halwan ta'isa tana miƙa mata hannu alamun ta ɗauke ta
Ita kuma ta zuba mata idanu wanda a baɗini tunani take yi don hankalin ta baya wajen Husnan
Ganin dai ba ɗaukan ta zata yi ba sai tajuya tafice tana sake kiran
"Mammaaa.."
Fitowar ta yayi dai-dai da fitowar Larai daga ɗaki tana kallon ta tazaro idanu tare da nufo ta tana cewa
"Ke.. ke.. ke haka kikai ma jikin ki wannan ɓarnan? Kai Husna ba kya ji yanzu ji be yanda kika ɓata jikin ki, da alamu dai kin zubar min da flowern nan?"
Ɓangale baki Husna tayi tana ƙyalƙyale mata da dariya
Ɗaukan ta Larai tayi tace "mu je in sauya miki kayan tunda kin ɓata".
Ɗan ƙaramin hannun nata taɗaura saman fuskar Larai ta damalmala mata da flowern da yaɓata mata hannu
Ita kuma Larai sai tacafko hannun tasaka a baki tana dariya
Still Husna ƙyalƙyace wa tayi da dariya tana janye hannayen ta
"Ƙaniyar ki, yarinya sai rashin jin tsiya, ke ko muje in sauya miki kayan inga kuma kin sake ɓata wa".
Daga haka tashige cikin ɗakin ta da Husnan a hannu tana mangare mata ƙeya.
Halwa na zaune a inda take har yanzu tasoma jiyo hayaniyan Abba da Ummi, abinda bata taɓa ji ba tun zuwan ta gidan, hakan yasa sosai tayi mamaki tayi shiru tana kasa kunne don jin abinda ke faruwa
Izuwa yanzu muryan Abba ake jiyo wa sosai yana ɗaga murya, duk da kuwa ba ta fahimtan abinda yake cewa amma tasan faɗa yake ma Ummi
Bata motsa a wajen ba sai da taji hayaniyan ya lafa sannan tamiƙe tafito, lokacin tahangi Abba har ya buɗe ƙofa ya fice
Ɗakin Ummin tanufa don jin abinda ke faruwa, duk da kuwa wani sashi na zuciyarta na kawo mata musabbabin faɗan, be wuce sanin gaskiyan samuwar jaririn nan ba.
[12/13/2020, 3:37 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
_wannan shafin naku ne wattapad fans kusha sha'anin ku, Nagode da soyayyar ku gare ni❤️_
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Nineteen*
________🎓 Nocking tayi tare da sallama, bata shiga ba sai da Ummi taba ta izni bayan ta amsa sallaman nata
Tura ƙofan tayi tashige tana kallon Ummin dake zaune gefen gado, kallo ɗaya tayi mata tahango tarin damuwa a fuskarta, wanda kowa yakalle ta ya san tayi kuka
"Lafiya Halwa?" Ummi tayi maganar tana sakar mata murmushi
Kanta tasauke ƙasa tana wasa da yatsun hannunta tace "dama naji kamar hayaniya ne shine nazo duba ko lafiya".
Still Murmushi Ummi tasaki tace "lafiya lau Halwa babu damuwa, yanzu ina yaron yake ne?"
"Yana ɗaki yana barci".
"To kema Yakamata kije ki kwanta ki huta sabida kin san abinda likita yafaɗa kenan".
Murmushi Halwa tayi kafin tagyaɗa mata kai tajuya tafice, ɗakin takoma tayi kamar yanda Ummin tace don dama barci sosai take ji, ga jikin ta duk babu daɗi.
*****
Fitan Abba babu inda yazarce sai asibiti, kasancewar sun yi waya da Dad ya tambaye sa inda yake zai zo su tattauna wani matsala
Dad ɗin sai da yace masa shi yabari yazo yasame shi har gida, but Abban yaƙi hakan
Lokacin da ya'isa waya yaɗauka yakira Dad yafito suka shiga mota suka zauna, sun daɗe sosai suna tattaunawa kafin Dad yafito ranshi duk a ɓace, duk da kuwa cewa sai da suka tsayar da mafita akan zancen kafin yafito, amma ɓacin ran da yake ji akan maganar ya gaza gushewa
Cikin Hospital ɗin yakoma
Shi kuma Abba yaja motar sa yatafi.
Yana shiga ɗakin Mom da Sameer dake zaune suna taɓa hira suka kallo sa, ganin yanda fuskar sa yake a matuƙar ɗaure sai abun yabasu mamaki
"Lafiya dai Alhaji meke faruwa?" Mom tatambaye sa har alokacin tana kallon sa
Numfashi yaja kafin yasauke idanun sa kan Khalil, kamar yana jin sa cikin ɓacin rai yace "zaka tashi dan ƙaniyar ka zaka gaya min abinda yasaka ka aikata ma ƴar mutane hakan".
Ƙirjin Mom ne yabuga da ƙarfi, cikin ruɗu tace "Alhaji kana nufin shine yay ma Halwa ciki?"
Girgiza kan sa yayi cikin takaici yazauna yana faɗin "yo ai ban ga banbancin abunda suka yi mata ba da cikin, wai ƙwanyin haihuwar su shi da matar sa aka saka mata don ta haifa musu ɗa".
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Cewar Mom cike da tsananin al'ajabi
Sameer kam kasa magana yayi sai mayar da idanun sa kan Khalil ɗin da yayi yana kallon sa, be san cewa ɗan uwan nasa har yanzu be da wayau ba sai yau
"Menene hakan kenan?" Wai yanzu kana nufin ɗan su ne Halwa ta rainan musu?"
Dad yace "wlh raina yayi mugun ɓaci da Alh. Mustapha yafaɗa min, amma dole zan ɗau mataki bari yafarka zai gane be da wayau".
Daga haka yamiƙe yafice yabar su nan shiru suna mamakin wannan abinda Khalil ya aikata, abun ma yay musu girma da yawa don haka basu sake yin magana ba har sanda Atine me aikin Mom tazo, sai Sameer yatashi yay ma Mom sallama yatafi akan sai gobe zai dawo sabida yau yana da dutyn dare.
******
Washe gari da yamma Khalil yafarka
Mom CE lokacin ita kaɗai a wajen sa, doctor takira yaduba sa sai da yatabbatar babu matsala sannan yatafi
Tea tahaɗa masa me kauri kamar yanda doctor ɗin yabuƙaci aba shi wani abun yaci, sai da tagama haɗa wa kafin tamiƙo masa Cup ɗin tace
"Ga shi ka daure kasha ko zaka ji daɗin jikin ka".
Numfashi yaja kafin yasoma yunƙurin dai-dai ta zaman sa, yana yi yana cije baki
Hakan yasa Mom ɗin ajiye Cup ɗin hannun ta, tamiƙe tataimaka masa yazauna tare da jingina da pilow
A hankali cikin sanyin murya na maras lafiya yace "zan wanke baki".
Vowel ta ɗauko sannan taɗauko ruwan gora ta buɗe ta kafa masa a baki
Yakurɓa yakuskure bakin sa yazuba cikin Vowel ɗin
Sannan ta'ajiye tamiƙo masa Cup ɗin ya'amsa yafara sha
Yana sha yana rufe idanun sa har ya ɗan sha rabi tukun yamiƙa mata Cup ɗin, a karo na biyu tun tashin sa yasake magana
"Mom Ina Saleema?"
Ita kawai tafaɗo masa a rai saboda yasan dole zata shiga wani hali da abinda yafaru dashi
Amsar da taba shi shiyasaka shi ɗaura idanun sa akan ta, be iya yin magana ba illa kallon ta kawai da yake yi
Har maganar haihuwar Halwa sai da tayi masa duk da kuwa bata nuna masa tasan ainihin zancen ba
Ɗan waro idanu yayi still yana kallon ta zuciyar sa na bugawa da tsananin ƙarfi
Ganin kallon da yake mata ba ƙaƙƙauta wa tace "lafiya ko akwai wani abu ne?"
Lumshe idanun sa yayi yana kwantar da kansa, be sake yin magana ba duk da kuwa Mom ɗin tana ta yin masa hira
Har sanda su Hakima da Nazeefa da suka zo a tare be sa ya buɗe idanun sa ba, iyakan gaisuwar su ya'amsa yasake juya bayan sa tare da ci gaba da tunanin sa
Hakima na ta tsokanar sa but be ma san tana yi ba.
Har dare suna nan zaune, sai da Sameer yazo sannan suka tarkata har da Mom drever yakai su gida, Sameer ne zai kwana dashi a yanda suka tsara tunda ya tashi
Tun fitan su Sameer ɗin yake tsaye bakin ƙofa yana yin waya, sai da yagama kafin yazo yazauna yana kallon Khalil da idanun sa suke rufe kamar yanda yake tun ɗazu
"Khalil wai su wanene kake zargi akan wannan abun da akai maka?"
Sai a lokacin yabuɗe idanun sa yana kallon Sameer ɗin, sai kuma ya yamutsa face ɗin sa sabida zugin da yake ji a ciwon sa, kamar bazai yi magana ba har Sameer ya buɗe baki da ninyan sake yin masa magana sai kuma yace
"Bana zargin kowa".
Jinjina kai Sameer yayi yace "su ma har yanzu ƴan sanda sun kasa samun wani ƙwaƙƙwaran shaida wanda zai sa agane me hannu ciki, wannan aikin naka yana da maƙiya da yawa matuƙa hakan yasa baza mu iya gane wanda yake da hannu ba, sai dai Allah yaƙara tsare wa, but insha Allahu ko ma wanene sai asirin sa ya tonu".
Khalil dai yana jin sa be tanka ba, har sanda yasauya maganar da faɗin
"Ni ban taɓa tunanin baka da hankali ba sai yanzu Khalil, wani wauta ne zai saka kayi wannan gangancin, kana tunanin wannan shine maslaha da zaku cutar da ƴar mutane? Haramun ne hakan a musulunci but har da kai aka haɗa baki wajen aikata wa, ka bani mamaki wlh".
A yanzu Khalil ya maida idanun sa kan Sameer ɗin yana kallon sa, sai dai be iya yin magana ba
"Yanzu kowa yasan cewa Halwa ta haifa mana ɗa?" Yatambayi kansa batare da yasan afili yayi maganar ba
Hannu Sameer yasaka yadungure masa kai yace "baza ka san kowa ya sani ba sai ka haɗu da Dad, wlh zaka sha mamakin sa domin yayi fushi sosai, meyasaka zaka biye ma yarinya don kawai bata haihuwa ku cutar da Halwa.."
"Ni fa ba Ni ne na bada shawaran hakan ba, itama ɗin ai har da yardan ta tunda ba mu mukai mata tilas ba". Khalil yakatse sa da faɗin hakan yana turo baki
"To tunda har da yardan ta kai kuma babban banza ko sai ka amince?"
Marairaice fuska Khalil yayi kamar zai yi kuka yace "Bro wlh tausayin Saleema yasaka na amince da wannan shawaran da Ummi takawo, kuma wlh ban tashi dana sani ba sai daga baya, Ni kaina na so azubar da cikin sai dai kuma hakan ba me yiwuwa bane tunda Matata ta ƙwallafa ran ta akai".
Sameer yace "kana nufin kenan da Ummi cikin zancen?"
"Eh". Yaba shi amsa yana sake langaɓe kai
Taɓe baki Sameer yayi yace "zaka sani ne babu ruwana Ni dai".
Ɓata fuska Khalil yayi be sake yin magana ba, sai kuma yasaki ajiyan zuciya jin Sameer ɗin shima be ce komi ba yakalle sa yace "Brother taimaka min zan yi sallah".
Tashi Sameer ɗin yayi yazare masa ƙarin ruwan da aka saka masa sannan yataimaka masa yamiƙe tsaye
"Kayi a hankali kar ka zuba ma wajen ruwa". Sameer yafaɗa yana koma wa yazauna
Be ce komi ba yataka a hankali yashige toilet ɗin, be wani jima ba yafito
A lokacin Sameer ɗin yamiƙe yashimfiɗa masa sallaya yasoma gabatar da sallan da ake bin sa bayan ya tambaye sa kwanakin da yayi a kwance
Sai da yagama sannan yakoma kan gadon yakwanta bayan Sameer ya mayar masa da ruwan, rufe idanun sa yayi yana sauke tagwayen ajiyan zuciya, be sake motsawa ba har sanda barci yaɗauke sa cikin ƙanƙanin lokaci.
**** ***** ***** *****
*BAYAN KWANA BIYU*
Alhmadulillah jikin Khalil yana ta samun sauƙi, har a lokacin ana ta binciken waɗanda sukay mishi hakan but ba'a samo su ba
Gwamna da kansa yasaka ayi bincike sosai don gano su, duk da kuwa har yanzu an kasa samo shaida ko guda ɗaya, Asibitin babu CCTV 📷 cameras Wanda zai sa ayi saurin gano su, amma duk da haka an zuba jami'an tsaro a Hospital ɗin don tsaron Khalil ɗin, suna da tabbaci waɗanda sukai yunkurin wannan aikin suna da ninyan kashe sa ne zasu iya dawowa at any time.
Fannin Saleema dai babu abinda yaci gaba tana nan a yanda take, su Ummi sai dai su zo ganin ta tunda har yanzu ba'a barin kowa yashiga inda take kwance, ta Glasses kamar yanda suka saba suke ganin ta sannan su koma gida, idan nace muku hankalin iyayen ta yana kwance nayi ƙarya, sosai suke cikin damuwa da halin da ɗiyar su take ciki, ita ba matacciya ba ita kuma ba rayayyiya ba.
Kamar yanda Dad yabuƙaci ganin su a yau saboda tattauna matsalan su Khalil ɗin gaba ɗaya, yau ne suka taru a gidan Dad ɗin, har da Halwa aka zo da ita sai aka bar yaron wajen Larai
Bayan sun hallara gaba ɗaya, Ummi Abba Halwa Dad da Mom sannan sai Sameer aka buɗe taro da addu'a
Dad ne yasoma magana da faɗin "Asma'u abinda kuka aikata hakan be mana daɗi ba, ko kaɗan bamu ji daɗin hakan ba domin wannan ba koyarwa ne ta addinin musulunci ba, shiyasa muka zauna don samun mafita kamar yanda muka yanke hukunci Ni da Alh. Mustapha, wannan yarinya dai an cuce ta matuƙa saboda da agaban iyayen ta take hakan zai jawo mana matsala, sai dai fatan Allah ya kiyaye gaba tunda wannan yarigada ya faru".
Sai ya ɗan ja numfashi kafin yaci gaba
"Sai dai ku gafarce Ni sabida hukuncin dana yanke daga baya, na cewar Ibrahim ɗin zai auri ita Halwan sai su zauna gaba ɗaya domin hakan shine yafi dace wa".
Gyaɗa kai kawai Abba yake yi kafin yace "wannan shine daidai domin nima da tunanin hakan a raina, ai ko ba'a haɗa su aure ba babu yanda za'a yi Khalil yazauna da Saleema ita kaɗai dole zai ƙara aure, tunda ba zai zauna haka nan babu yara ba".
Ummi kanta bata ji haushin wannan abun ba, sabida tasan dole ne Khalil yasake aure nan gaba, to abun farin cikin su ne tunda Halwa ce zata zama kishiyar ƴar su, ta tabbata baza ta taɓa cuta mata ba
Itama Mom ta nuna goyon bayan ta tare da farin cikin ta sosai duk da har a yanzu bata san ainihin wacece Halwa ba, but shi Dad ya sani tunda sai da Abba yafaɗa masa komi da wannan maganar tafito
Halwa kuwa tunda aka soma maganar kanta na ƙasa, ta shiga matsananciyar faɗuwar gaba jin cewa za'a haɗa ta aure da Khalil, sai dai bata iya nuna musu wani hali take ciki ba duk da kuwa cewa taji sanyi aranta ganin Iyayen Saleema basu nuna rashin amincewar su ba, har aka gama tattaunawan bata ɗago kai ba kuma su ma basu tambaye ta jin ra'ayin ta ba, shiyasa itama bata furta komi ba
Da zasu tafi Ummi ce tayi mata maganar tatashi, don haka tamiƙe suka fito sukai gida.
.
_To pa Kuna ganin hakan babu matsala?_
[12/13/2020, 6:17 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Twenty*
________🎓 An tsai da ranan auren nan da kwana huɗu masu zuwa ranan juma'a kenan
Kuma duk wannan abun da ake yi babu sanin Khalil, Dad ne yace kar a faɗa masa a bari sai ranan ɗaurin aure
Don haka Sameer da Brr. Tahir ne suke ta shirye-shiryen bikin, wanda yadace su gayyata sun gayyace shi duk da ba wai taron biki za'a yi sosai ba, kuma duk wani gyara na gidan sa su ne kan gaba akai
Abba ya haɗa mata duk wani kayan ɗaki da Yakamata ayi mata, shiyasa da aka kai kayan gidan sai su Sameer suka kwashe kayan Khalil ɗin dake ɗakin sa suka zuba nata, sai suka bar masa abubuwan da zai iya buƙata, amma gadon sa dasu sip ɗin sa duk an sauya dana Halwa
Ummi bata yi ƙyashin gyara Halwa ba duk da kuwa lokaci yazo a ƙure kuma gashi tana cikin jego, but duk wani abinda yakamata tayi mata
Halwa dai bata iya mata musu duk abinda tasaka ta tana yi, ko kaɗan bata damuwa da kanta wai ko tana son sa ko bata son sa, ita kawai Saleema ce a ranta, me zai faru idan har tasan cewa ta aurar mata miji? Hakan na ɗaga mata hankali matuƙa har tashiga ɗaki tayi ta kuka, tana jin cewa bata kyauta ba kuma sannan ita