Header Ads
Showing 36001 words to 39000 words out of 104570 words

Chapter 13 - SARAKI (The Accused Prince).txt

Ads the beginning of article before Image

ummi   

03 Jun 2024

1438

Ads at the middle of Article

inda waccan ta tashin bisa dole, farko be yi niyyar zama ba sedai kalaman Mommy kan shi yasa yaji Yes se fa ya zauna duk da response ɗin da Kisnah ta mata ya burge shi sosai, dukkan su seda suka sake kallon shi lokacin da yakai zaune, ba Mommy ba har Kisnah da Maigado da se lokacin ta ɗago kanta daga pressing phone ɗin da take.


Zama ne irin na cikakku Kuma gawurtattun ƴaƴan da jinin sarauta ke circulating through their veins, tsantsar izzar dake tare dashi da kwarjinin da zaman ya ƙara masa yasa duk suka kau da kansu a kanshi kusan a tare, juyawa tayi ta haye saman ta yayinda su Mommy duk sukai wani irin shiru kafin ta miƙe ta shiga bedroom ɗin ta ƙawayen ta na rufa mata baya.


Barin dannar wayar Maigado tayi ta maida full attention ɗin ta kan Saraki da yake nan zaune idanun sa a lumshe, ko da be buɗe ido ba yana jin yawon idanu cikin jikin sa hakan yasa ya buɗe idanun towards direction ɗin da yake jin gaze ɗin, a bazata hakan ya zowa Maigado shiyasa har ya kamata dan bata tsammani ze buɗe ido lokacin ba, kallo ɗaya yayi mata ya janye idanun sa ya sake lumshe su itama kuma da sauri ta maida naga kan waya sedai ta kasa cigaba da abinda take.


Ƙarar takalmin Kisnah yasa Maigado kai kallon ta can, har tayi wanka ta canja rigar jikin ta zuwa wando three quarter da t-shirt mara nauyi ta saki gashin kanta da bata samu zuwa saloon yau dan gyarashi ba, ɗauke kanta tayi zuciyar ta na ɓaci ta maida kan wayar ta sedai ta kasa haƙura hakan yasa ta shiga satar kallon dukkan su biyu dan sosai taji baƙin cikin fitowar Kisnah da wannan shigar da haka kawai zuciyar ta ke faɗa mata zata iya burge Saraki da ita.


Zama kan one sitter gefen Saraki Kisnah tayi kafin ta saka hannu ta ɗauke files ɗin da ke kan cinyar sa da yasa ya buɗe idon sa kan ta, ajiye files ɗin tayi gefen ta kafin ta ɗauko bundle ɗin 1k ta ɗora masa inda ta ɗau files ɗin, kallan kuɗin yayi kafin ya maida kanta cikin sigar kallon tambaya


"Gashi nan ka siya kayan amfanin da babu a ɗakin ka ka kuma ƙara kaya, haka ake bawa kowani sabon ma'aikaci da ze Fara aiki a gidan nan, ba wai dan raini ko wani abu ba se dan kyautatawa".


Da farko so yayi yace baya so sedai yadda ta ƙare bayanin yasa ya fasa hakan wanda da alama ta fahimci yana son rejecting shiyasa ta ƙarasa a tausashe.


"Thanks". Ya faɗa yana miƙewa bayan ya ɗau kuɗin itama ta ce masa "thanks also for the drive".


Fita yayi yana mamakin ta a ranshi, jiya ma haka tace masa thanks yau ma gashi ta kuma, to akan me zata gode masa bayan aiki yake mata kuma biyanshi zata yi, a karo na biyu ya kuma ganin hali me kyau tattare da ita.


Khamees ya samu da batun ɗakin kamar yadda yace ya kuwa rakashi part ɗin ma'aikata har ƙofar da aka saka tag ɗin sunan sa Ahmad dake can nesa da part ɗin su Kisnahn.


Bin ɗakin yayi da kallo cikin yaba tsarin ɗakin, ƙatuwar katifa ce me matuƙar taushi sabuwa dal cikin ledar ta se three sitter sofa daga gaban katifar kalar ash ita ma me kyau da ita, madaidaiciyar wardrobe me murfi biyu itama kalar ashe da ratsin fari a kusurwar ɗakin se curtains Suma Ash color se ƙaramar plasma TV dake jikin bango tare da kayan DVD da DSTV a ƙasan ta kan kyakkyawan ƙaramin glass TV stand, sosai yaji daɗin ganin har da Ac akwai a ɗakin dan baya shiri da zafi ko kaɗan.


Ƙarasawa yayi ƙofar toilet da ya hanga acan gefe ya buɗe ya shiga, fari tass ɗin tiles ne a banɗakin tun daga ƙasa har jikin bangon sa gaba ɗaya sedai na ƙasan manya ne na jikin bango kuma madaidaita, ba wani tarkace bane cikin toilet ɗin illa hand shower, water closet, tap, sink, mirror, bucket se ƴar cupboard me ɗauke da towels masu kyau, sabon brush and new sponge, se cleaning apparatus a gefe.


Ƙaramar low cut broom ɗin ya ɗauka ya zuba car wash me ƙamshi da ya gani cike cikin jarkokin faro manya har uku a ƙasan ya shiga sake wanke toilet ɗin duk kuwa da cewa a wanke yake, seda ya tabbatar yayi masa yadda yake so kafin yasa ruwa ya ɗauraye sannan ya tuɓe ya yi wanka da ruwa dan be siyo soap ba kuma babu sabulu a toilet ɗin, ɗaure da ɗaya daga cikin sababbin towel ɗin ya fito ya zauna kan sofa, wani ƙaramin towel da ya ware yanzu dan goge jiki yasa ka ya tsane ruwan jikin sa kafin ya maida jeans da rigar da ya cire ya ɗau key ya fita zuwa motar da suka fita jiya da ya kwaso kayan sa a ciki.


Fito da kayan yayi da gaba ɗaya yayi wa leda biyu dan basu da wani yawa, kala goma ne gaba ɗaya se toothpaste ɗin sa da sabulai da mayukan sa ya kai ɗaki kafin ya dawo dan rufe motar idanun sa suka sauka kan shopping bags biyun da ta bari cikin mota ta kuma ce masa nasa ne, kamar ya bar su ya maida mata se kuma kalaman Mami suka dinga dawo masa kan sa kamar lokacin take faɗar su


"Ka Dena irin haka Saraki, sheɗan kawai ke maida alkhairi in an masa, ko mai ƙanƙantar abun da aka baka ko kuma girman shi ka karɓa ko dan wanda ya baka yaji daɗin baka raina shi ba balle abin hannun sa ko da bazaka yi amfani dashi ba kuma kayi godiya dan ya tabbatar kaji daɗi kuma ka yaba, ita kyauta tana zuwa ne da kyautatawa bawai raini ba kamar yadda kai kake gani, wanda ya baka kyauta bawai ya raina ka bane a'a yayi appreciating wani abu da kayi masa ne ko kuma dan ƙauna kawai dan akwai mutane da yawa a gari amma be bawa Kowa ba se kai , ka min alƙawarin zaki dinga karɓar kyauta indai bata zo ta sigar raini ko isgilanci ba".


Be manta kalaman da ya faɗa wa Mami ba a lokacin which is "I promise you Mami nah".


Ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗaukan bags ɗin ya nufi ɗakin dan be ga raini ko isgilanci tattare da Kisnah ba, wardrobe ɗin ya buɗe ya shiga jera kayan sa wanda be daɗe ba dan set goma ne, jeans da t-shirt ya cira ya saka kafin ya koma ya fara jera kayan da Kisnah ta siya masa, ko bai faɗa ba Allah ya sani kayan sun burge shi dan irin su ya saba sawa da ma wanda suka fisu, designer Kaya ne masu matuƙar tsada da kyau ta siya masa har kala sha biyar se wrist watch guda uku, silver, golden se black.


Godiya da addu'a yayi mata sosai a zuciyar sa tare da mata fatan shiriya daga dukkan abinda take aikatawa na ba daidai ba, kan katifar ya kwanta bayan ya shimfiɗa bed sheet ɗin da ya gani cikin wardrobe which is so clean se ƙamshi ma yake.


Kwanciya yayi cikin tunanin Mamin sa da ya saka shi gaba da yake ta faman dannewa sedai yanzu kam ya kasa, shaƙuwar sa da Mami daban ce da ba kowa ze gane ba, ƙaunar da yake mata bazata faɗu, itace ƙawar sa, yar sa, ƙanwar sa, haka kuma mahaifiyar sa shiyasa yanzu duk wanda ya sanshi a baya ya ganshi yanzu yasan ƙarfin hali ne kawai yake yi amma he's not well.


Haka ya cigaba da kwanciya har lokacin da akai knocking ƙofar shi ya tashi ya buɗe, ma'aikaci ne sanye da uniform ya ɗora rigar girki a kai se apron a kansa da zata shaida ɗaya daga cikin cooks ɗin gidan ne, miƙa wa Saraki plate ɗin hannun sa yayi yana sakin masa murmushi, karɓa yayi yana sakin masa murmushi shima kana ya koma ɗakin tare da rufe ƙofar.


Kan sofa ya zauna hannun sa riƙe da plate ɗin yana bin abincin da kallo kafin yasa hannu ya janye foil paper da aka rufe plate ɗin dashi, fried rice ce da ta yi kyau sosai a ido se rabin kaza a gefe da spoon shima nannaɗe cikin tissue, ɗaukar spoon ɗin yayi tare da ajiye plate ɗin gefe bayan ya maida foil ɗin ya rufe, toilet ya shiga ya sake wanke spoon ɗin thoroughly kafin ya koma ya zauna ya ɗau plate ɗin, bisimilla yayi ya fara cin abincin a nutse wanda yake nan ba yabo ba fallasa, wato dai ba wani daɗi gare shi sosai ba amma fa baza ace bashi da daɗi ba, ƙarar waya da yaji yasa yayi pausing hannun sa riƙe da spoon ɗin da ya ɗebo abincin, jin ƙarar sosai a ɗakin yasa ya ajiye spoon ɗin ya miƙe tsaye ya fara neman inda wayar take dan ba tasa bace take ƙarar dan ita tana gefen sa.


Can gefe ya hango landline kan wani ƙaramin fridge da be lura dashi ba tun da ya shigo, ƙarasawa yayi ya ɗau wayar tare da yin sallama, Muryar Kisnah yaji cikin maganar da ta sa ta kira shi batare da ta amsa masa sallamar ba.


"You get ready we're going out tonight, pls help me check if one dark blue car of mine is clean".


Ajiye wayar yayi bayan ya gama sauraren ta batare da ya amsa mata ba dan shima bata amsa masa sallamar da yayi ba ai, komawa yayi ga abincin sa ya ƙarasa cin iya yanda ze iya dan shi kam a dole yaci abincin dan shi fa be san wani abinci related to foreigners, yafi ganewa natural traditional dishes ɗin mu na Hausa shiyasa Mami da kanta take masa girkin sa.


Fridge ɗin ya buɗe ya ɗau bottle water da ya gani batare da ya kalli drinks ɗin wajen ba sannan ya fita duba motar da tace, its clean amma dai yace a sake goge ta kar tace ba'a yi mata daidai ba.


Ɗakin ya koma ya zauna a sofa looking at he's watch dan ganin ina lokacin sallah yayi, sedai to his utmost surprise se ma yanzu ƙarfe ɗaya yayi, alwala ya shiga toilet yayi kafin ya fita zuwa masjid ɗin da ya gani gaba da gidan, sallar Azahar yayi tare da azkhar ɗin bayan sallah kana ya dawo gidan, bacci yake son yayi sosai kafin la'asar dan kansa wani irin ciwo yake masa wanda yasan ba komai bane yaja illa damuwar da yake ciki da yawan tunanin da yake ga kuma ayyukan da jikin sa be saba da su ba duk da wata kusan biyu kenan da yake yin wasu kafin wasu su ƙaru jiya...................✍️.












©️ Ouummey 📚✍️.








☑️Ote, comment and share fisabilillah.


































Ouummey 16 (8/8/2022 6:49 PM )





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________
















Page 1️⃣6️⃣










________________________📖 Sallar Isha ya idar a masallaci amma be dawo ba se da ya gama duk tasbih ɗin da ya saba, fitowa yayi a hankali ya saka takalmin sa ya nufi komawa gidan yana me duba agogon hannun shi, its 8:45 pm.


Yana shiga compound wayar da aka kawo masa ɗazu me kyau da ita madaidaiciyar Android kamfanin Samsung matsayin wayar da ake bawa kowane ma'aikaci da sim da komai ta fara ringing, ɗan kallon screen ɗin yayi kafin yai sliding ya amsa


"Ya Saraki ka fito da motar gani nan fitowa"


"Okay" yace yana ending call ɗin tare da ƙarasawa ɗakin sa ya ɗauki key ɗin motar da kuma kuɗin da ta bashi ɗazu dan yana son yin siyayya.
Warming up motar yayi kafin ya matsa da ita kusa da flat ɗin nasu ya kashe yana jiran fitowar ta.


Cikin wata dark blue ɗin guntuwar gown iya ƙasan gwiwa kaɗan ta fito, rigar tasha adon silver stones masu matuƙar kyau se ɗaukar ido take tana walwali, gashin kanta parke cikin blue ribbon se ta sake shi ta baya kana ta ɗora p-cap akai, kyakkyawar farar ƙafarta kuwa sanye take cikin dogon blue Hill shoe da igiyoyin sa suka kai har kusan rabin ƙaurin ta, kyawawan hannun ta saye da agogo shima dari blue se ɗayan da ta sakawa siririyar sarƙar hannu ta kuma ƙawata yatsun ta da zobuna.


Tun da ta fito ƙamshin ta ya cika ko ina a harabar gidan har ya kai ga hancin Saraki da ya saukar da glass ɗin side ɗin sa, girgiza kai kawai yayi yana mata addu'ar shiriya dan tabbas saka irin waɗannan turaren dole ya haddasa fitina a ban ƙasa.


Tun a ɗazu da ta kira shi da Ya Saraki yaji wani irin abu ya tsarga masa, ba abun da yazo ransa a lokacin face ƙanwar sa ɗaya tilo da ita kaɗai ce mace dake kiran sa da sunan, hakan yasa yaji a ransa kamar ita ɗin ce ta kira shi sedai yasan ba itan bace, tun a lokacin yaji a ransa wata ƙanwar ce ya samu, ƙani, ƙanwa, yaya mace, wa namiji kai har ma iyaye ana iya samun su a duniya base wanda kake da blood relation ne kaɗai family ba, a hadisai da ayoyi da dama Allah da Manzon sa sun nuna mana so da ƙaunar juna, sun nuna mana duk wani musulmi ɗan uwan musulmi ne dan haka ya amshe ta as ƙanwa kamar Miemie da suka fito ciki ɗaya da baze iya barin any harm yaje gate ta ba, haka baze so yaga rayuwar ta ta lalace ba, he'll treat her as an elder brother that will protect his little sister ko ta wane hali sedai yasan for now ba komai zece dole ze yi magana kan se ta gyara ba dan abun ya riga ya shiga jikin ta da dole se an bi a hankali.


Cikin wannan tunanin yayi nisa da har be san ma ta ƙara so har ta shiga ba se da ta bubbuga bayan kujerar da yake kai tana kiran sunan sa


"Yaa Saraki mana, am late fa".


Buɗe ido yayi a kanta kafin ya bi shigar jikin ta da ido sannan ya janye ya maida fuskar ta da ba wata kwalliya banda lip balm se mascara da eyeliner, kauda Kai yayi ya maida gaban motar yasa hannu ya kunna sannan ya nufi gate suka fice, seda suka hau titi sosai kafin ya ɗan kalle ta a kaikaice


"Zaki makara? Makaranta zaki je?".


"Wane irin makaranta a wannan late hours ɗin, clear screen cinema za muje".


Jijjiga kai kawai yayi ganin bata ma fahimci baƙar magana ya faɗa mata ba, be kuma cewa komai ba har suka ƙarasa, be shiga parking lot ba ya tsaya a gefe kaɗan da gurin dan fita yake son yi


"Ya ka tsaya a nan, kaga fa zan daɗe kawai ka shigar da ita parking lot kar muyi blocking wasu".


Hakan da ta faɗa se ya tuna mata dasu Abeed da gaba ɗaya ta manta da batun su wanda ta san for sure suna nan a kulle dan in har bata sake su ba ba wanda ya isa yasa a sake su, dole yau insha Allah zata sa a sake su dan badan ta manta ba da tun kwana uku da ka masu zata sa ayi freeing din su.


"Zan je Mall in dawo, ko ba daɗewa zaku yi ba?". Ya faɗa mata


"Gaskiya zamu daɗe ina tunanin ma se to 1 Film ɗin ze ƙare, kasan fa Film biyu zan kalla, Film ɗin sharukhan me suna Ra one se kuma na Ajay devgan shikuma sunan sa Action Jackson".


Yadda take maganar cikin farin ciki ze shaida maka she drive pleasure talking about Hindu films talkless of watching it.


"You enter, Bari inje in dawo".


"Safe drive". Ta faɗa tana fita daga motar bayan ta buɗe safe ɗin ciki ta ɗau ledar crackers biyu, juya motar yayi ya fita daga cinema ɗin yana bin titi hopping to see a nearby Mall dan baya so yayi nisa, wani madaidaicin mall da ya gano yasa ya ƙarasa yai parking tare da shiga, ɓangaren takalma ya fara shiga ya zaɓi masu kyau guda biyar kafin ya koma ɓangaren turare nan ma ya zaɓi madaidaita dan wanda yake amfani dashi da is worth 350k duk ɗaya shiyasa yanzu sedai manage.


Kayan ƙamshin toilet ya siya ya haɗa kafin ya siya sabulan wanka da mayukan kai, a taƙaice dai 2k ce kawai tai ragowar cikin 100k ɗin da ya fito da ita.


Payment yayi aka masa bagging kayan security suka kai masa mota ya shiga ya koma cinema, Yana yin parking ya duba watch ɗin sa only to see 9:50, he's wandering how he'll be waiting cikin mota har to one kamar yadda tace.


Rufe glassan yayi gaba ɗaya kafin ya ƙure ƙarfin Ac ɗin motar ya saukar da kujerar sa baya ya kwanta sosai bayan yayi connecting wayar sa da Bluetooth ɗin motar ya saka karatun Alkur'ani mai girma in low tune, tun yana bin karatun har bacci ya sace shi .


A can cikin cinema kuwa kallo suke yi hankali kwance oganniya a tsakiyar da'ira tana taunar crackers ɗin ta har aka kusa gamawa aka zo waƙar kusan ƙarshe, sedai me tace bata san zance ba lokacin da waƙar ta ƙare ai se a dawo da ita baya ta kuma kalla, kusan gaba ɗaya mutanen wajen sukai mata caaa kamar zasu cinye ta da baki suna faɗin bata isa ba suna da abun yi, sosai in charge ɗin cinemar hankalin sa ya tashi dan yana samu da Kisnah ba kaɗan ba ga kuma ƴan kallo da suka customers ɗin sa ne, ko da aka kira shi rarraba ido ya hau yi tsakanin su

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads