Header Ads
Showing 72001 words to 75000 words out of 104570 words

Chapter 25 - SARAKI (The Accused Prince).txt

Ads the beginning of article before Image

ummi   

03 Jun 2024

1428

Ads at the middle of Article

da saƙon ta ta wuce sama da ɗan gudu gudu har ta haye, ƙofar ma seda ta san tana fushi dan yadda tayi banging ɗin tada akwai wani a kusa ba ƙaramin ciwo zata ji masa ba.


Kayan jikin ta ta fara ciccire wa tana watsar wa har se da ta cire komai na jikin ta kafin ta ƙarasa toilet, ruwan sanyi ta sakar wa jikin ta ta tsaya a ciki har se da ta ji ranta yayi mata sanyi kafin ta yi wanka ta fita, tsane jikin ta tayi da towel sannan ta zura guntuwar red gown iya gwiwa ta warware chignon ɗin da tayi wa kanta ta maida shi French plait ta saki jelar a bayan ta.


Ledar ta da ta shigo da ita ta fito parlo ta ɗauka tare da nufar mini kitchen ɗin ta, plate ta ɗauka ta wanke duk da fess yake ta goge da duster sannan ta juye abin cikin ledar a kai, lumshe ido tayi cikin zaƙuwar fara cin gasasshiyar kazar wadda ta sha kayan haɗi kamar me, take cikin ta ya fara kukan yunwar da ta yo guziri daga office dan yau bata yi launch ba aiki ya ɗauke mata hankali.


********


Juyawa yayi da ledar hannun sa ya wuce ɗakin sa bayan yayi locking motar, yaji daɗin yadda tayi wa Awwaf sosai dan hakan na nuna ta fara sanin ciwon kan ta kenan, a ganin sa da da kanta take rungume maza yanzu kuma tana fighting masu rungumar ta haka ma Nasara ce.


Poor Saraki be san ita Awwaf ɗin ne ta raina wa hankali ba ba wai dena rungumar maza tayi ba duk da an daɗe hakan bata faru ba tun da kullum tana hanyar office to a ina zata gan wanda ta sani balle har ta runguma?


Wanka yayi ya canja kaya kafin ya zauna kan ledar sa shima ya shiga aika ta ciki, sosai gashin ya yi masa daɗi abaki dan haka yake ta lumshe idanu, abin dariya har ya cinye ma be san ya cinye ba seda yaji ledar ƙwalam kafin yayi murmushi ya tafi toilet ya wanke hannun sa.


Kitabul kaba'ir ɗin da ya fanso recently ya ɗauko ya shiga dubawa, lokacin da aya baro gida yayi nisa sosai sedai kwana biyu da yayi be duba ba ya ɗan samu tangarɗa so ya koma baya ya shiga karanta wa cikin ransa.


Seda akayi kiran sallar magrib ya ajiye ya yi alwala ya fita zuwa Masallaci akayi sallah tare da shi har Isha sannan ya fito, da jallabiyyar jikin sa ya ɗau key ɗin motar da suka dawo da ita ya fita dan kai ta cinema Kamar yadda tace.


Cikin shigar jeans da half tigh shirt ta fito sedai ta saka brown overcoat a kai ta ɗora sou'wester a kanta ƙafar ta sanye da brown wedge shoe da ya mata masifar kyau.


Buɗe motar tayi ta shiga dan shi dama tuni ya shige ciki ita kawai yake jira, tana shiga ya tashi motar suka fita daga gidan bakin ta ɗauke da addu'a.


Suna ƙarasawa ya yi parking a lot ɗin wajen tare da kashe motar yana jiran ta fita.
Karkatowa tayi tana kallon shi cikin ɗan marairaice fuska


"Yaya pls mu shiga tare da kai kaima ka kalla, kaga fa kai kaɗai zaka zauna a nan ɗin har kusan 3 hours".


Da mamaki sosai ya kalle ta
"Kin taɓa gani na ina kallon Film bare ma irin wanda kuke kalla, I don't have that time to waste, ke dai kije ki kalla abin ki, kuma ai ba yau na fara zama ni kaɗai na jira ki ba ko?".


"Yaa ba fa romantic film bane it's a sport movie, Dan Allah kaji".


"Ki dena haɗa ni da Allah fa dan ba inda zani, am here zan yi night azkhar ɗina, you go and watch se ki bani labari later".


Duk magiyar da tayi masa ƙi yayi yakan yasa tayi fushi ta fice tana banging Masa ƙofar, murmushi yayi dan yasan haushi taji, shikam be taɓa shiga cinema ba wai kallo kuma baze fara yanzu ba, gwara a gida yana kallo sosai amma cinema ba da shi ba.


Kwantar da kujerar yayi ya kishingiɗa sosai a kanta ya shiga tasbih ɗin sa a hankali patiently waiting for her...........................✍️.














©️ Ouummey 📚✍️.
















☑️Ote, comment and share fisabilillah.




























Ouummey 30 (8/21/2022 10:31 PM )





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________
















Page 3️⃣0️⃣
























________________________📖 Ƙarfe sha ɗaya suka fito a tare su biyar ɗin suna tafe suna mata ƙorafin dena fitowar da tayi dan rabon ta da party da club tun kafin su je resort which is three weeks da dawowar su yanzu, har Gara cinema tun da gashi yau ta zo.


"Ni fa tun kafin tafiyar mu resort na fahimci wancan driver ɗin nata ya ɗauke mata hankali, ban san wane irin asiri yayi mata ba wai ta bashi aiki a Company kuma a office ɗin ta ta yadda kullum suna tare, ban sani ba ko kin soma irin halin Surayya ne shiyasa ne ko kuma meye oho".


Sosai maganganun Hameedah suka yi wa Kisnah zafi, wato a wasan dare take so tace mata ta fara bin maza shine ta wani dake, da alama dai zargin ta take da Saraki, da ƙyar ta samu tayi controlling kanta dan kar tayi something stupid wa Hameedar, cikin irin wannan ƙorafe ƙorafen na su suka ƙarasa wajen motar ta ta ɗan jingina tana kallon su


"Am sorry guys, Kuma kusan dole ce zata sa na bar zuwa partying da clubbing, am sorry to say na bar clubbing, har abada ne ko kuwa ban sani ba se abin da gaba ta haifar, for partying da zuwa cinema kuwa rashin lokaci ne yasa bana zuwa, abubuwa da yawa sun faru a Company da dole ana buƙatar attention ɗina, as you can see sabida yawan abubuwan dole se da na samo me taya ni dan ni kaɗai bazan iya ba, amma cinema kam insha Allah ko next movie da ni za'a kalle shi".


Jijjiga kai Surayya tayi cikin yarda da abinda ta faɗa kafin suka haɗa baki ita da Leekha wajen faɗin


"I believe you dear, Allah ya taimaka ya bada Nasara, worry not okay?".


Dariya duka suka saki ganin yadda suka haɗa baki kafin Meenah itama ta dafa kafaɗar Kisnah


"All the very best dear, Allah ya taimaka, we all are with you kinji".


Gyaɗa kai Kisnah tayi cikin farin cikin irin yadda suke nuna mata ƙauna, ɗan siririn smile Hameedah ta saki saying


"Wishing you lots of lucks". Murmushi itama tayi mata tare da nodding head alamar amsawa.


Jikin ƙofar side ɗin da take zama ta matsa ta shiga knocking a hankali, shiru be buɗe ba, ɗan ƙara ƙarfin knocking ɗin tayi nan ma shiru, matsowa Meenah tayi ta saka key ɗin motar ta ta shiga ƙwanƙwasa glass ɗin tsawon lokaci kafin yayi unlocking car ɗin ya fito hannun sa riƙe da gorar ruwa, zagayo wa wajen sa Kisnah take ƙoƙarin yi dan ganin ko lafiya yake suke ta Knocking ko kuma bacci yayi sedai tuni Hameedah ta riga ta isa wajen ta fara magana cikin sigar rashin mutunci tana watsa masa wani kallon banza


"Wannan wane irin wulaƙanci ne malam zaka kama ka wani rufe ƙofa ka bar ta a waje se faman bugu take kamar wani taka, ko kuwa dan kaga ta danƙa maka keys ɗin motar ne yasa kake feeling taka ce or what, ban da tsabar rashin iya samun guri irin na talaka har kai ka isa ka bar mu tsaye tsawon wani lokaci kamar wasu bayin ka ko masu yi maka maula, me kake dashi, waye kai, waye baban ka kuma waye ya tsaya maka, ko da yake ba laifin ka bane ita ce ta sake maka har kaga damar ta shiyasa ka rai nata, banda tsabar rashin ilimi da.............".


Razananniyar tsawar da Kisnah ta sake mata cikin kiran sunan ta ce ta dakatar da ita daga cin mutuncin da take wa Saraki da ya gama wanke fuskar sa da ruwan robar hannun sa sedai be kai ga mayar wa ba ya jingina jikin motar yana sauraren ɗibar albarkar da Hameedah ke masa sedai be ko ɗago kai ya kalle ta ba yana dai sauraren ta.


Da wani irin zazzafan taku Kisnah ya ƙara so inda Hameedar take tsaye tare da ɗaya hannun ta cikin son sauke mata kyakkyawan mari sedai a karo na farko Saraki ya riƙe hannun ta, da sauri ta waiwaya ta kalle shi tana son ƙwace hannun ta sedai be saki ba sema girgiza mata kai da yayi alamar kar ta mare ta tare sake mata hannun,


"Ƙyale ta, kar ki dake ta".


Ya faɗa xan ƙasa cikin murya irin ta wanda be daɗi da tashi daga bacci ba, juyawa tayi ga Hameedah da ta tsaya speechlessly watching at Kisnah kamar ta sami TV


"Da ka bar ni na koya mata hankali yaa, na daɗe ina tolerating iskanci da baƙaƙen maganganun ki gare ni amma ke baki gane ba, danne rai na nake kar nayi miki rashin mutunci amma You keep pushing me to the wall, to tau na kai ƙarshe da iya shegen ki ko kin ɗauka ban da hankali ne ban fahimci zagin da kika gama yi min ba yanzu, ko kin zata ban fahimci nufin ki we have an illegal dirty affair da ya Saraki bane a kalaman ki, na daure na share ne kawai saboda ƴar uwar ki gata nan.......". Ta faɗa pointing at Meenah dake nan tsaye kamar an dasa ta saboda tsabar tashin hankali


".......if not sabida ita wallahi da tuni nayi maganin ki, and ki sani Yaa da kike kira da driver ya fi mun ke sau adadin da za'a kuma bani zaɓi, je mau be mere driver a wajen ki amma ni a wajena shine mutum na farko da nake ganin matuƙar girma da darajar shi dan haka duk wadda a cikin ku take ganin ba zata iya girmama shi ba to na haramta ko magana tayi masa ehe, zulwajahaini kawai ƙaramar ƙwaruwa, ke iskancin ki na gangan ne yarinya, da ace kin isa kin cika kin kuma tumbatsa ba soka min magana da hassada a ɓoye zaki yi min ba fitowa zaki yi gaba da gaba ki tare ni ki faɗa min ni karuwa ce, ko an gaya miki dan kin yi hakan zan damu ne, ko kin manta ba yau na fara jin an dangan ta ni da sunan ba, kuma tun da ake faɗa kin taɓa ganin na damu, eh ni karuwa ce amma me aji dan ni maza da kan su suke bina bani nake bin su ba, na san abinda kike wa hassadar ke nan kuma dai se haƙuri na riga nayi miki nisan da ko hange na ba zaki iya ba balle ki kamo ni, mara mutunci kawai".


Zuwa yanzu hawaye kawai ke kwarara a fuskar Hameedah cikin baƙin cikin irin cin fuska da tozarcin da Kisnah tayi mata amma fa a ganin ta dan duk da dare ne seda aka samu masu tsayawa kallon abinda ke faru cikin waɗanda suka fito daga gidan kallon.


Ita kuwa Kisnah tana gama faɗar abinda ta ga dama wa Hameedah ta shige mota tare da maida murfin ta rufe, batare da ya dubi kowa ba shima Saraki ya shiga side ɗin da ya kamata ya rufe, cikin kankanin lokaci ya tashi motar suka fita daga cinema ɗin suna barin su Surayya da suka zama so speechless tsaye kuma daskare a wajen.


Tafiya yake a hankali kamar baya so time to time yana kallon gefen da take zaune tana fidda huci har lokacin kamar wadda zata ci babu.


"Relax, kwantar da hankalin ki pls, ni ban ma ga abin tashin hankali a maganar da ta faɗa ba, kema kin san gaskiya ta faɗa am just a mere driver to you Kuma be kamata na rufe mota na bar ki waje kina Knocking ba alhalin kina matsayin mamallakiyar motar, uhm to meye ta faɗa da zafi kuma".


A hanzarce ta juyo ta kafe shi da ido tana jefa masa kallo me kama da harara cikin jin haushin abin da yace


"To da kake driver ita ta ɗaukar min aikin, ko ita take biyan ka, ina ruwan ta in ma kwana nayi ina knocking da zata wani kama zagin ka, motar ta ce ko mun haɗa kuɗi da ita mun siya ne".


"To shikenan baku haɗa kuɗi kun siya ba, amma ni a ganina da baki kula ta ba, mace me class bata faɗa any how Kuma bata tsayawa ihu da kowane kalan mutane, wanda suka isa da wanda basu isa ba, and pls ki rage saurin marin da kike yi, da an miki abu se ki hau kai mari hakan ma is not good most especially ga maza, ba class ɗin ki bane".


Ajiyar zuciya ta saki fushin ta na ɗan raguwa saboda yadda yake magana cikin kwantaccen harshe da taushin murya


"Zan dena insha Allah, Amma for Hameedah dole nayi magana dan ta ƙure ni ne, na daɗe da sanin tana min hassada da baƙin ciki akan komai, ko kasan murna tayi lokacin da na kasa assignment ɗin CON005?, kuma na gani na gane amma na nuna ban san tana yi ba, yanzu haka da muka fito wasu banzan maganganu take faɗa tsakanin ni da kai wai shine dalilin da na baka aiki a office ɗina dan kullum mu kasance tare, shima na danne rai na to kuma meye ruwan ta da kai, shiyasa na ci mata dan gobe kar ta kuma min dan wallahi in ta kuma se ta gwammace rungumar transformer kan matakin da zan ɗauka kanta".


Ɗan murmushi ya saki ganin yadda take masifa kamar har yanzu Hameedar na gaban ta


"On her behalf, she's really sorry Miss, zata kiyaye gaba".


"Better for her". Ta faɗa tana kau da kanta gefe, a hankali a hankali yake ɗan mata hira though ba iyawa yayi ba amma ya ƙoƙarta dan ganin ya sauke mata fushin da take har se da yaga tayi ƴar dariya kafin ya ƙyale ta.


Yana yin parking tayi masa sallama tare da wuce wa cikin gida shima ya fice zuwa ɗakin sa.


Kashe gari da tashin hankalin fake currency ɗin nan suka tashi, sosai suke ta kan bincike amma ko trace ɗin mutumin da ya sayi kayan ba'a samu ba, hankali fa ya tashi manager ya shiga cakwakiya dan bank ɗin da yaje depositing riƙe shi suka yi suka handling ɗin shi wa hukuma kan zr damfare su da kuɗin ƙarya, ba ƙaramin kuɗi Kisnah ta zuba ba kafin aka sake shi.


Duk wanda yaga kawu kuwa ze yi zaton shine ainahin me dukiyar dan yadda yayi wujiga wujiga dashi ya fita kamannin sa wajen neman yadda za'a yi ayi tracing mutumin, kai kamar ma yafi ita Kisnahn damuwa dan se ita ta koma tana kwantar masa da hankali kafin asamu ya ɗan daidaita dan har suma biyu yayi.


Cikin wannan tashin hankalin aka kawo takardun hannun jari da wani Company ya zuba a K&S flour and food stuffs wanda dole ana buƙatar signing ɗin ta kafin ayi documenting a Kuma ba wa su waɗancan copy ɗin su.


Da wanna damar kawu yayi amfani wajen haɗawa da fake takardun ownership ɗin nan ya kai mata tayi signing sedai ba shi ya kai mata direct ba manager ɗin ta ya bawa ya kai, bata tsaya duba komai ba ta yi signing a duk inda akace tayi tare da bawa Saraki ajiya kan ya bawa manager in ya dawo karɓa ita kuma ta wuce station dan fa bank ɗin sun ƙi haƙura suna batun shigar da ƙara dole ana buƙatar ta dan ganin ko za'a iya cimma maslaha in suka zauna.


Gyara takardun yake yana girgiza kan sa ganin yadda gaba ɗaya ta ajiye takardun a hargitse kafin ya shiga jera su ɗaya bayan ɗaya yana ajiye kowacce inda ta dace ta hanyar karanta heading ɗin jiki har yakai kan ta ownership ɗin, cikin matuƙar mamaki ya ciro su har guda huɗu ya ajiye a gefe ya ƙarasa gyara waɗan can kafin ya shiga karanta su ɗaya bayan ɗaya, in akace mamaki to an rage matsayin yanayin da yake ciki, wani irin tsoron Allah ne ya ratsa shi a zaunen da yake ganin tsantsar rashin tsoron Allah, mugunta da kuma ƙarfa ƙarfar da wasu da suka daɗe da kwashe kayan su gaban manzon Allah suke yuƙurin aikatawa.


Takardar shedar mallakar kamfanoni ɗaiɗai har huɗu ne, K&S construction, K&S flour and food stuffs, K&S Furnitures, se K&S drinks, Kuma wai mugun se da ya duba manyan da suka fi girma, bunƙasa da kawo riba, dafe kansa yayi cikin tunanin waye me wannan aiki dan duk yadda aka yi wanda yasan ciki da bai na Companies ɗin ne da wannan aiki, kuma baya tantama shine boss ɗin Emeka, shine ƙashin bayan asarar da akayi yau haka kuma shine yake assasa duk wata asara dake ta afkuwa cikin kamfanonin a kwanakin nan.


Seda gaban sa ya faɗi da sunan kawu ya faɗo ran a, da sauri ya girgiza kan sa telling his mind it's impossible, yes impossible ace wai kawu ne behind all this evil act, no be ma yarda ba, taya ma ze zama kawu bayan shine ke kula da duka dukiyar tun kan ta girma kuma dukiyar tai ta haɓaka batare da wata matsala ba se yanzu, beside haka ma kalli fa tashin hankalin da kawun ya shiga a ɗazu, Bama shi bane, baze zama shi ba, ya sake jadda dawa a ran sa, to waye???


Yana cikin wannan tunanin har manager ya shigo be sani ba dan ya daɗe yana knocking Amma ba amsa so yayi tunanin ma ba kowa bari ya shigo ya ɗau takardun kawai ya wuce dan su kawu na jiran sa

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads