Header Ads
Showing 27001 words to 30000 words out of 104570 words

Chapter 10 - SARAKI (The Accused Prince).txt

Ads the beginning of article before Image

ummi   

03 Jun 2024

1421

Ads at the middle of Article

har ba ita tace ya dawo dani ba wannan uban naki da baƙin halin sa ze iya bari inyi wata ɗaya ko biyu a gida, ke har fiye ma wallahi".


"Ai sam Daddy be yi ba wallahi, Ni ban san me ya kaiki ma auren shi ba tun farko, shi abu ba kuɗi ba, ba ilimi ba, ba wani kuma kyau ba se shegen tsayi kamar me, yanzu dai jini yadda ya cuceni ya gada min tsayi kamar ba mace ba".


"Hmm Bari kawai, Ni kaina ban san me yaja ni ba a lokacin, kin san dai ƙaddara amma yadda nake da kyau na da diri a ƙuruciya ai be kamata na ƙare a wajen shi ba, yanzu dai ba wannan maganar ba, bari kiga in kira waccan sheɗaniyar dan in so samu ne in koma gidan nan yau dan wallahi na wahala matuƙa".


Mommy ta ƙare maganar tana dialing number Kisnah kana ta cigaba da faɗin


"Wai hatta caji fa a gidan nan bani da damar yi se ace in bada caja shiyasa yanzu haka 20% ne kawai dani".


"Ai wallahi Aunty Hasiya se ta san ba tada mutunci, banda arziƙin kina gidan ta ita har ta isa ta yi min ko da kallon banza ne balle zagi".


Da sauri Mommy ta nuna wa Megado tayi shiru ta hanyar sa hannun ta a bakin Megadon jin wayar na ringing.


**************


Cikin mall ɗin suka shiga inda Kisnah ta shiga lodar kaya kamar ba da kuɗi za'a biya ba, cart huɗu ta cika ma'aikata na bin ta dashi a baya dan shi kam Saraki tun da suka shigo ya nemi waje ɗaya ya tsaya.


Ɓangaren kayan maza ta koma ta shiga jida kamar ba zata dena ba har se da ringing ɗin wayar ta ya tsaida ta kafin ta ƙarasa kusa da Saraki ta miƙa masa ATM card ɗin ta tayi masa alamar ya bi ma'aikatan suje a biya ita kuma ta tsaya amsa kiran, har yayi gaba ya tuna bata faɗa masa pin ɗin ba dan haka ya koma


"Oh sannu fa, ashe kece, to ya hutu fatan kina jin daɗi tare da enjoying zaman".


Sentence ɗin da ya shiga kunnen shi kenan da ya iske tana faɗa cikin salo na rainin wayo, shiru tayi cikin sauraren Mommy kafin ta saki dariya


"Ke ɗin uwa ta? Wai Mommy nah! Mommy my foot kinji, Baki da wani matsayi wajena sama da na matar kawu na haka sunan ki a bakina da zuciya ta Halima ne ko ba haka gyatumi ya raɗa miki ba".


Daga can ɓangaren Mommy ta cika da takaici da ɓacin ran wulaƙancin Kisnah sedai bata da yadda zata yi, nema take dole ta danne komai a ranta, dan haka ta ɗan saki murmushin da be kai ciki ba


"Hakane sunana Halima, sedai duk mu ajiye wannan a gefe, dama na kira ne in baki haƙuri dan Allah kisa kawun ki ya dawo dani, na miki alƙawari Megado bazata kuma shiga sabgar ki ba".


Jinjina kai Kisnah tayi
"Amma nayi mamakin jin kinyi laushi cikin kwana uku, ashe dama ke ɗin kura ce da fatar damisa, damisar kwali me bawa yaro tsoro, anyways tun da kinyi apologizing ki shirya kayan ki ki dawo anjima sedai fa ko da wasa wani raini ya kuma shiga tsakanin ƴarki dani ko ke kanki to tabbas zan sa a yanka Miki red ticket, Kim San dai mijin naki a tafin hannu na yake, byee bye uwar me bed".


Katse wayar tayi ta maida kallon ta fuskar sa dan ta lura da tsayuwar sa tuntuni, sosai ta zuba idanun ta kan kyakkyawar fuskar sa wanda tun zuwan ta se yanzu ta iya karfin halin hakan, ƙarewa fuskar kallo tayi sosai ba tare da ta yadda idanun sa ya shiga nata ba kafin ta kawar tana me yaba kyan shi cikin ranta,


"The pin".


Ɗan juyowa tayi dan sam ta manta na bata faɗa masa pin ɗin ba


"1469".


Juyawa yayi ya koma wajen accountant ɗin ita kuma ta cigaba da tsayuwar jiran su tana kiran Leekha dan jin ya jikin Surry kafin ta ƙarasa.


************


"Barka da dare Mamin ya Saraki".
Cikin murmushin ta me kyau na dattijan ƙwarai ta amsa wa ɗan nata gaisuwar da yayi mata


"Barka kadai ƙanin Saraki". Dariya ce ta ƙwacewa Jamal na jin daɗin yadda yau mahaifiyar tasu ta sake har take iya barkwanci


"Fatan Abbin Maimartaba na cikin ƙoshin lafiya".


"Lafiya lau Mamin mu". Ya amsa mata cikin farin cikin jin ta kirashi da Abbin Maimartaba dan yaci sunan baban takawa ne.


"Nazo yi miki albishir ɗin amincewar takawa na tafiya ta dan haka insha Allah nan da kwanaki biyu nake sa ran tafiya".


"Naji daɗin hakan yaro na sedai ina jin damuwa kan tafiyar nan taka, nayi istikhara na tsawon kwana huɗu kuma alhamdulillah naji kwanciyar hankali sosai dan da alama Saraki na yana Lafiya dan haka ka bar batun nan dan ina son ganin giccin ka a tare da ni Jamal".


"Amma Mami na riga na faɗawa takawa zan yi tafiyar nan har ya amince min, ba kya tunanin ya kawo wani tunani na daban kan fasawar tawa?


"Sam ba zaka fasa tafiya ba Jamal, kaje ƙasar da kace masa zaka kayi course ɗin wata biyun under your field daga nan ka dawo kayi aure dan Allah, ina son ganin grandchildren ɗina kafin lokaci na yayi".


Da sauri ya ruƙo hannun ta jin tana kawo batun mutuwa da sam baya san ji bawai dan be san dole zata mutun ba se dan yana fatan tayi tsawon rayuwar da zata ga dawowar gudan jinin ta mafi sayuwa a ranta cikin gidan uban sa da aka koreshi, cikin gatan sa kuma tunƙahon sa har ya taka matsayin da maƙiya suka ƙulla masa sharri domin shi.


"Insha Allah zan yi kamar yadda kika ce Mamina, ki taya ni da addu'a Allah ya bani Sa'a kinji alfahari na".


Hannu ta ɗora kan shi tayi masa addu'a kamar yadda ta saba yayinda cikin ranta ke ɗauke da kewar ɗan ta da yafi kowa kusanci da ita itama tafi kowa kusanci dashi, addu'a tayi masa a ranta kamar yadda ta saba duk ta tuno shi duk dama be taɓa barin ranta ba sedai ta danne kawai.


Sallama Jamal yayi mata ya tafi processing duk abinda ke haɗa na tafiyar ita kuma ta cigaba da duba litattafan addu'o'in da ya shigo ya same ta tana yi.


Ko da dare ta shirya tsaf dan zuwa turakar takawa kasancewar ita ke da kwana ranar, cikin haɗaɗɗen falon sa da ya kasance bame shiga se shi da matansa da ƴaƴansa ta same shi hannun sa riƙe da jarida yana dubawa, da sallama ta shiga ta zauna kusa dashi kafin ta miƙa gaisuwa.


Hannu ya ɗaga mata kasancewar karatun yasha kansa itama bata kuma ce masa komai ba ta shiga zuzzuba masa kayan abincin da ta ƙaraso dashi dan a falon farko ma'aikata ke ajiyewa me girki kuma se ta ƙarasa dashi.


Seda ya gama karanta jaridar kafin ya ajiye ya juya gare ta, cikin sakin fuska da walwalar da yake tsintar kansa duk ya kasance tare da ita ya amsa mata gaisuwar da tayi masa ɗazu yana me tambayar ta ya ta wuni.


Abincin ta tura gabansa bayan ta amsa shi da lafiya lau, cikin kwanciyar hankali ya soma cin abincin sa yayinda gimbiya Haleematu ta kafe shi da ido dan ɗan ta Saraki take hangowa a tare dashi.


Yanayin nutsuwar shi, yadda yake riƙe spoon har zuwa yadda yake tauna abinci duk takawa ya gado hakan yasa yanzu take ganin kamar shine a gaban ta, a dabarance tasaka tafin hannun ta ta goge hawayen rashin ɗan ta da ya zubo mata dan bata so takawan ya lura da halin da take ciki sedai abinda bata sani ba tuni ya gane me take tunani tun sanda ta kafe shi da ido har hawayen da ta share.


Ya daɗe da sanin Haleematu macece me tsananin kawaici haka kuma yafi kowa sanin halin ta na haƙuri kuma yafi kowa shaida irin son da take yiwa gudan jinin nata.


Tissue ya zara ya goge bakin sa bayan ya gama cin abincin, tashi tayi zata janye kwanakin ya dakatar da ita ta hanyar nuna mata kusa dashi


"Zauna nan Haleematu".


Kamar yadda ya umarce ta haka ta zauna dab dashi suna fuskantar juna, a hankali cike da dattako ya ruƙo kyawawan yatsun hannunta ya shiga murzawa a hankali kafin cikin murya me taushi ya shiga mata magana


"Me yake damun Haleematu na da har yake sata hawaye da damuwa? Wace irin damuwa ce haka da har gimbiyar Giwa ta kasa daurewa har raunin ta yana bayyana a fili? Shin akwai matsalar da ta shafi gimbiya ta da zata gagara sanar da ni Sarkin ta?


Duk yadda taso daurewa kasawa tayi, tsawon watanni biyu na barin Saraki masarauta yau ne takawa ya nuna yasan tana da damuwa duk da ta daɗe da sanin ya fahimci hakan yana dai kawar da kai ne dan kar ya bata fuskar tunkarar sa da batun Sarakin ko yaya sedai abinda ya manta a cikin halayen ta shine tafi kowa sanin sa da iya karantar sa kamar yadda yafi kowa sanin ta da fahimtar ta, ya manta tunda har ya nuna baya son jin komai dangane da Sarakin ita ɗin bazata taɓa kawo masa batun ba saboda tsananin biyayyar ta.


Janyo ta yayi jikin sa yana bubbuga kafaɗar ta har tayi me isarta ta share hawayen ta kafin ya ɗago ta


"Faɗa min, menene damuwar gimbiya ta".


Murmushin da ya tsaya iya saman lips ɗin ta tayi kafin ta bashi amsa


"Ba wata babbar damuwa bace, kawai dai zuciya tace bata min daɗi haka ina ji na empty, shikenan"


Tsananin tausayin ta ne ya kama shi, dama ya sani ba zata kawo masa batun Saraki ba ko za'a shekara nawa ne kuwa, shi kansa yana kewar ɗan nasa sedai da ya tuno irin laifin da ya aikata se yaji baya ko san jin sunansa balle tunawa dashi, bare kuma ita da yana cikin wanda zasu bada labarin irin shaƙuwar dake tsakanin su, akan ce ƴa mace itace ta uwa mace sedai a ɓangaren Sarakin da gimbiya is different, komai nasa Mamin sa ce, itace abokiyar sa, malamar sa, Auntyn sa, yayar sa kuma mahaifiyar sa haka a gare ta Saraki ne ƙawarta, maman ta, yayar ta, kuma wanta, ya sani in yace kar ta damu ma be mata adalci ba dan haka be sake ɗaga maganar ba se nasiha da wa'azi da ya shiga yi mata har hankalin ta ya kwanta har tayi cikakken murmushin da ya fito tun daga zuciyar ta ba wai iya fatar baki ba. (Allah Sarki uwa, i love U so much my umma💞).


................................


Babbar macece sedai ba wai irin girma sosai ɗin nan ba a kishingiɗe kan tattausan gadon da yasha shimfiɗu na alfarma, a ƙalla bazata wuce shakara 48 ba , daga kishingiɗen da take ta ke girgiza ƙafafunta da suka sha zanen jan lalle irin na zamani fuskar ta ɗauke da ƙasaitaccen murmushi, daga gefen ta kuwa matashin saurayi ne zaune kan tuntun ƙafar sa ɗaya kan ɗaya yana dubanta


"Kar ka wani damu da wannan dan ni baya cikin lissafi na ko kaɗan, ko kana manta ka girme mashi ne kuma a halin yanzu kai ke amsa sunan YARIMA ME JIRAN GADO? kana tunanin zan yi sake da sarauta zata faɗa ɗakin Haleema ne bayan ina da ɗa babba? Ko kaɗan dan haka ka kwantar da hankalin ka ka cigaba da rayuwar ka ni mahaifiyar ka RUMANA na maka alƙawarin indai ina raye to sarautar Daular Noor taka ce".


Sosai farin ciki da murna suka wanzu kan fuskar sa


"Shiyasa nake matuƙar so da ƙaunar ki Ammi na, Allah ya bar min ke ya ƙara miki lafiya me inganci ki ganni zaune kan karaga matsayin sarkin daular Noor, Sarki UTHMAN MUHAMMAD HASHEEM". Ya ƙarasa faɗa sautin Muryar sa cike da tsananin buri da fata wanda itama gareta gimbiya RUMANA hakan ne a ranta.


***************


"Ke yanzu Laylah baza kiyi wa kanki karatun ta nutsu bane, shin baki san rayuwar mace nada limit bane, fidabilillah ace kin zauna jiran gawon shanu kin ƙi aure kin zauna jiran wanda baki san yaushe zai dawo gare ki ba, yanzu kin yiwa kanki adalci kenan? Ko kuwa kin manta har Yarima Saraki ya bar masarautar nan be taɓa son ki ba ne?".


Hawaye ne masu zafin gaske suka zubo daga idanun matashiyar dake duƙe ƙasan dattijuwar dake magana, kallo ɗaya zaka musu kasan uwa da ƴa ne saboda tsananin kamannin da suke yi, a hankali dattijuwar ta saka hannun ta ta ruƙo kafaɗar ƴar tata


"Bawai bana son ki da Saraki bane Laylah, hasalima se na fi kowa san tarayyar ku sedai dole in faɗa miki gaskiya, kin sani kaf masarautar nan ba da wanda na aminta sama da gimbiyar Giwa haka itama gare ta, dan Allah ki cire komai a ranki ki bawa maneman ki dama Laylah, wallahi zaman ki haka ba aure yana damu na".


Ruƙo hannun dattijuwar Laylah tayi cikin sakin murmushin da be kai zuci ba,
" Ki taya ni da addu'a Ummi na, insha Allah zan yi kamar yadda kika ce, nima ina so in manta dashi sedai har yau na kasa hakan, kullum gani nake kamar ze dawo gare ni amma insha Allah a wannan karon zan ƙoƙar ta".


Cikin tausayin autar tata Umma ta ce


"A yanzu kam ni Sameera bani da wadda nake wa addu'a kamar ke Laylah, dan haka kar ki damu kinji Allah na tare da ke".


Gyaɗa kai Laylah tayi kafin ta miƙa


"Bari in je in duba abincin can kar ya ƙone".


Ficewa tayi tana saƙa da warwara cikin ranta na yadda zata iya yakice Saraki cikin zuciyar ta....................✍️.






Hhhhhhh😂🤣🤣 su Mommy an yi laushi luɓuɓus😜😜.


Gimbiya RUMANA, ko ita kuma wacce haka🤔oho🤷


Toooooo faaaahhh😳 ke kuma Laylah daga ina, wata sabuwa inji ɗan caca, #team_saraki Ina tambaya 🤔


©️ Ouummey 📚✍️.






*☑️Ote, comment and share fidabilillah*
























Ouummey 13 (8/6/2022 9:46 PM )





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________


















Page 1️⃣3️⃣






_________________________📖ko da suka isa can suka tadda su Meenah and alhamdulillah jikin Surryn da sauƙi sosai dan ta ma farka har suna ta hira da Leekha, kamar yadda ta saba haka tayi wato just ta tura ƙofan ta shige without Salam yayinda Saraki dake bayanta riƙe da ledodin shopping be shiga ba se da yayi sallama ya jira izini tukunna dan ga dukkan alamu gareshi mata ne a ɗakin saboda tashin muryoyin su da ake ɗan ji daga waje.


Kujerar gefen gado Meedah ta turawa Kisnah ta zauna suka shiga gaisawa da tambayar ya me jiki kafin ta maida kanta wajen Surayya da tun da Kisnahn ta shigo take ta sakar mata murmushi.


"Ya jiki swee swee?


Ta tambayi Surry calling her with the name she used to,


"Alhamdulillah da sauƙi Kissy, Ina ta zuba ido amma shiru nace to akwai abinda ya tsaida ki, hope dai guy ɗin be miki komai ba ko?".


"Sure naso na fito da wuri sedai kuma i have to wait for my new driver da na bawa appointment ɗin ganawa dashi da safen, no kar ki tashi hankalin ki ba abin da yayi min, all thanks to you my swee swee".


"Masha Allah, that's what I wanna hear tun farkawana".


"And you'll heal faster insha Allah".


"We hope so my Kissy, so your new drive brought you here".


"Yesso, ai tare ma muke, here he is".


Ta faɗa tana juya wa dan nuna mata Saraki sedai wayam bata ganshi ba, miƙewa tayi ta nufi ƙofa tana faɗin


"A'ah, ina kuma ya tsaya, i thought tare muka zo kofar ɗakin".


Buɗe ƙofar tayi da niyyar fita duba shi se ta tadda shi tsaye hannayen sa riƙe da shopping bags ɗin har lokacin, zaro ido tayi cikin mamaki


"So all this while kana tsaye a bakin ƙafa still holding the bags ko ɗan ajiye wa ka huta ma baka yi ba kamar wani soja, tabɗi, okay let's enter".


Bece mata komai ba ya bi bayanta cikin ɗakin, be kalli kowacce ba cikin su dan ba wadda ta amsa sallamar da yayi ya ƙarasa gaban Kisnah ya ajiye bags ɗin ya juya ya fita, da ido duk suka raka shi banda Kisnah da hankalin ta ke kan waya tana duba messages a watsapp ɗin ta


"Lord of heaven, Ina kika samo cute and handsome guy ɗin nan Kisnah?".


Surayya ta tambaya a ɗan ruɗe dan ita fa Allah ya jarrabe ta ko ta ɗorawa kanta son maza zance, idon ta idon namiji me kyau se dai ƙarfin ikon Allah ya hana ta samun shi, hatsabibiyar kanta ce wajen sanin salo salo na kissa da kisisinar jan hankalin maza masu kyau shiyasa yanzu ma tana ganin Saraki taji ya fa yi mata.


"Shine sabon driver na".


"Driver!!!". Suka yi exclaiming in disbelief, gyaɗa musu Kai tayi in assurance ba tareda ta dube su ba.


"Amma gaskiya me kyau ne, Oh my Goddd!!


"Baki ƙarya ba Surayya yana da kyau kam sosai".


Leekha ta faɗa in support of Surayya's words.


Wani irin yatsuna fuska Hameedah tayi ganin yadda Surry da Leekha suka ruɗe da ganin wani banza wai shi driver
"Kyan banza kenan, kyan ɗan maciji da baya hana a kashe shi, duk wannan kyan nasa dai sunan sa driver, so disgusting, mtsww".


Ta ƙarashe tana tsartar da miyau in disguise, ɗan taɓe baki Meenah tayi tana ɗan jefawa Surry harara


"Kin San fa ita Surry anything related to men shine abun yabo a wajen ta, ni duk banga abin zuzutawa ba a guy ɗin dan ba yau muka fara ganin maza masu kyau ba ai".


Janyo bags ɗin Kisnah tayi batare da ta tankawa kowa daga cikin su ba ta tura gaban Surayya tana kallon ta


"Yau Aunty tazo ne?".


"Tazo amma bata daɗe ba ta tafi, dama zuwan nata bana Allah bane shiyasa tun da yaya yace mata ze Kai wata

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads