Header Ads
Showing 30001 words to 33000 words out of 104570 words

Chapter 11 - SARAKI (The Accused Prince).txt

Ads the beginning of article before Image

ummi   

03 Jun 2024

1424

Ads at the middle of Article

be dawo ba se ta tafiyar ta meaning ai dai kafin ya dawo na warke".


Jijjiga kai Kisnah tayi tana miƙewa ta fara tafiya


"Bari naje police station naga yadda zanyi da wancan ƙaramin ƙwaron, in na fito da wuri maybe na dawo akasin haka kuma se gobe insha Allah".


"Allah ya yarda, but what about test ɗin da zamu yi gobe ga kuma abinda ya faru kinga ba zan samu zuwa ba".


"Karki damu, I'll handle that".


"Goodluck then".


Yatsu biyu ta ɗaga musu ta ƙarasa ficewa daga ɗakin yayinda Meenah da Hameedah suka bi bayan ta dan mata rakiya zuwa wajen mota Leekha kuma ta zauna tareda Surry.


Zaune a cikin motar suka same shi yana sauraren karatun Alkur'ani da aka saka gidan radiyon Sa'a FM, buɗe mata ƙofar baya Hameedah tayi take kuwa ta girgiza mata kai ta saka hannu ta buɗe gidan gaba ta zauna tare da maida murfin ta rufe, sauke glass ɗin tayi tai waving ɗin su daidai lokacin ya tashi motar suka bar wajen.


"Durumi police station zamu je".


Ta faɗa tana lumshe ido saboda yadda karatun Alkur'anin cikin ƙira'ar Sheikh shureim ke ratsa jikin ta har tana jin kamar ta dawwama tana saurara, wani irin shauƙi da nishaɗi take jin yana shigar ta from nowhere da ya tilasta mata lumshe ido tare da kwanciya cikin kujerar, karon farko tana zaune cikin mota without her daily headphone a kunnen ta.


Cikin wannan yanayin suka ƙarasa gaban ƙaton ginin police station ɗin wanda bama ta san sun kawo ba seda ya ƙwanƙwasa glass ɗin kusa da shi kafin ta ɗago ta dube shi, ɗage mata gira yayi kafin ya nuna mata station ɗin da idon sa, saurin kau da kai tayi dan jin yadda jinin jikin ta ya tsinke da signal ɗin da ya mata.


Hannun ta na ɗan rawa ta buɗe ƙofar ta fice da sauri tare da mai da ƙofar ta rufe, ɗan jingina tayi jikin motar har ta samu ta daidaita nutsuwar ta kafin ta buɗe side ɗin da ta fito ta ɗau purse ɗin ta da ta manta, batare da ta dube shi ba tace ya fito su shiga.


Fitowar yayi kamar yadda tace yayi gaba tana bin shi a baya har cikin station ɗin, dogon baƙin kakkauran ɗan sandan dake kanta ya fito da sauri yana welcoming ɗin su dan polisawa kaɗan ne zasuce basu san fuskar Kisnah ba, ko ba domin tsiwar ta da yadda ake kawo report ko ita tasa a kama wani ba, ba wanda ke cikin garin Manya daze ce be san K&S drinks ba, K&S table water, K&S couture, K&S textiles, K&S Furnitures, K&S shopping Mall, K&S flour and food stuff Wanda duk itace mamallakiyar su a yanzu.


Da sauri police ɗin yayi leading ɗin ta to office ɗin D.P.O dan jin ƙorafin ta, kai tsaye ta shiga office ɗin without any knocking or neman izini, a fusace dpo ya miƙe dan ganin wane shegen ne ya shigo masa without excuse se kuma yai arangama da Kisnah, da sauri ya washe baki yana mata maraba


"Welcome Madam Kisnah, have a seat please". Ya faɗa yana tura mata ɗaya daga cikin kujerun dake gaban table ɗin sa, ɗan ɓata fuska tayi kafin kuma ta zauna tana ɗan sakin fuska, da sallama Saraki dake bayan ta ya shigo wanda dpo ne kaɗai ya amsa masa banda Madam ɗin da tayi kamar ma bata ji ba, shima kujera dpo ya nuna masa wadda ke kusa da Kisnah ya zauna.


Gyara zama Kisnah tayi tana ɗora hannayen ta kan table ɗin dpo
"Nazo ganin sheɗanin da ya nemi shiga hanya ta ne day before yesterday".


Da sauri dpo ya miƙe yana faɗin
"Bari a kawo shi Madam".


Ficewa yayi yana bawa wani kurtu umarnin kawo Sageer wajen sa, da sauri kurtun ya amsa yana wuce wa ciki inda aka rufe Sageer, ɗaɗɗaure cikin sarƙa hannu da ƙafa aka fito dashi kamar wani gawurtaccen ɗan fashi ko makashin jama'a dan da ƙyar ma yake iya tafiya, gaba ɗaya kamannin sa sun canja kai baka ce Sageer ɗin nan bane haɗaɗden gaye me ji da wanka.


Karɓar sarƙar dpo yayi ya iza ƙeyar sa cikin office ɗin sa wajen su Kisnah, jan kujerar ta baya tayi tana jefawa Sageer mugun kallo lokacin da dpo ya gurfanar dashi gaban ta.


Shiru tayi tana bin shi da kallo kafin ta daddage ta sheƙa masa kyakkyawan marin da se da ya hantsila saboda ƙarfin sa, ƙafar ta takai ta kuma shurin sa yayi baya ya bugu da bango, hakan be mata ba ta tashi ta bishi tana duka da ƙafa faɗi kawai take


"How dere you, I said how dere you".


Sosai baki da hancin Sageer suka fashe dan ya daku da takalmin Kisnah da ya kasance me tsini sosai, dukan sa kawai take dan duk ta tuno ƙazamin hannun sa ya taɓa jikin ta se taji kamar ana hura mata wuta a zuciyar ta, ga kuma raunin da yayi wa Surayya da take asibiti sanadin shi, dpo na zaune kan kujera ko pim bece mata kan dukan da take wa Sageer ɗin ba wanda a ƙa'ida hakan ya saɓawa doka, se ma aikin sa da ya cigaba da yi hankali kwance kai kace baya wajen.


"Stop it, I said stop it". Tsayawa tayi cak kamar wadda aka dannawa pause kafin a hankali ta juyo ta dubi Saraki dake tsaye bayan ta wanda shi ya daka mata tsawar, kafe shi tayi da ido kafin a hankali ta girgiza kanta


"Baka san me wannan annamimin yayi min ba that's why you're saying I should stop, had you know what he did cewa ma zaka yi in ƙara masa".


"Whatsoever, dukan yayi yawa, can't you see he's bleeding, don't you get a heart in your chest?".


Cikin ihun masifa ta shiga bashi amsa dan ranta ya kai maƙura wurin ɓacin cewa ta ƙyale Sageer da yayi, har yana wani faɗa mata whatsoever, kamar ita, lallai ma!


"I don't care, nace I don't bloody care if he'll loose all of his blood here, this stupid guy use his worthless dirty filthy hands to touch me with his dirty intention, he attempted to rape me after drugging me which without Surayya he would have succeed, can't you understand, nace can't you see Surayya is there laying on sick bed because of this stupid brat, he intends killing her if not Allah has saved her she would have been in her grave since yesterday, and you're here saying I should leave him, tell me how can I leave this devil".


Be kalle ta ba ya juya ga dpo da tuni shima ya miƙe tsaye yana rarraba ido tsakanin su a ransa yana ayyana
'this guy must be her brother or boyfriend' Dan if not one of the two baya tunani akwai someone that has the gut ya ma Kisnah tsawa like this giving her orders.


"Take him to hospital, he's unconscious".
Da sauri dpo ya ƙarasa gaban Sageer dake kwance ƙasa wanwar har lokacin hancin sa na fidda jini ya fara jansa kafin ya kira ƴan sanda ɗaya ya kama masa suka ɗauke shi, juyawa yayi ga Kisnah da ta kafe shi da idanu, kallo ɗaya yayi mata yasan ta kai maƙura gurin ɓacin rai, kujerar ta da ta ture garin dukan Sageer ya jawo mata


"Seat".


Banza tayi masa dan fa takai wuya, ɗan shiru yayi kafin ya ɗan rage kausasa Muryar da yai ya sake faɗa mata
"Saet Please".


Kamar bazata zauna ba se kuma ta zauna tare da kau da kanta daga gare shi tana huci, zama yayi a kujerar da ya tashi shima


"He attempted raping you saboda kin sa kayan da basu dace ba? Okay hakan is nothing, you live your life as you wish, Amma bakiyi tunanin ya mutu ba saboda dukan da kike masa bayan akwai harbi a ƙafar sa ga kuma dukan da police ɗin suka masa, ba kya tsoron ya mutu a hannun ki? Ko baki san duka zunuban sa zasu koma kanki bane, why not ki Kai shi court a yanke masa hukunci daidai laifin sa? Yes he's a devil for what he did but what if you decide to forgive him? Do you know the reward, ehm? The prophet said whoever forgive someone Allah will also forgive him, do you think you've no sin? No! We all sinned because we're bin Adams and we'll all like Allah to forgive us, didn't you want to be among?".


Ya ƙarashe cikin sigar tambaya, sosai taji jikin ta yayi sanyi with his speech, a hankali ta girgiza kanta alamun she want, ajiyar zuciya Saraki ya sauke a ɓoye ganin ta karɓi nasihar sa


"So forgive him please, leave him for the sake of Allah, in har halin sa ne hakan kuma be tuba ba se kiga Allah yayi punishing ɗin sa one way or the other, will you pls forgive him?".


"Na yafe masa". Ta faɗa so cool hoping Allah will forgive her also.


Sosai yaji daɗin yadda bata da taurin kai sosai, he pray Allah ya shirya ta dan ya fara yadda da abinda Inusa ya faɗa masa ɗazu, now he believed she's simple yadda be yi tsammani ba.


"Akwai abinda muke jira ne?".


"Yes, ka faɗawa dpo nace a sake shi".


Gyaɗa kai yayi ya fita daga office ɗin, bakin ƙofa suka yi kiciɓis da dpo so kawai se ya dawo ciki shima dpon ya shigo, cikin sauke ɗan numfashi saboda doguwar maganar da yayi ya kalli dpo


"You released him, ta yafe masa".


Da sauri dpo ya kalle ta daidai tana miƙewa tsaye, gyaɗa masa kai alamar hakane kafin ta fice daga office ɗin, fita shima Saraki yayi cos se ya buɗe zata shiga motar dan yayi locking motar.


Jingina jikin motar ya same ta dan haka tun kan ya ƙarasa yayi unlocking car ɗin using smart Lock na car ɗin, jin alamun yai unlocking yasa ta buɗe ta shiga ta zauna kalaman shi na sake yawo a kanta, shiga yayi shima ya zauna tare da rufe ƙofar ya tada motar suka hau kwalta, ƙwaƙƙwaran motsi bata yi ba har suka kusa isa gida traffic ya tsaida su, ɗan buɗe ido tayi ta kalli titin ganin yadda ababen hawa suka cika ko ina alamun an tashi kasuwa, daga can tsallaken titi ta hango wani tsoho tukuf duƙaƙƙe yana takawa a hankali hannun sa saƙale da buhu, ɗan sake buɗe ido tayi ganin kuɗaɗen sa da ya samo sadaka (not sure) na zubewa ta wata ƴar huda jikin buhun, kallon traffic ɗin gaban su tayi taga suna da sauran kusan 20 count downs kafin a sake su dan haka ta ɓalle murfin motar ta fita da sauri.


Ƙarar buɗe side ɗin ta ya sa ya juyo dan ganin ina zata, kan idon sa ta kukkurɗa tsakanin motocin har ta ƙarasa wajen tsohon da yake tafiya kamar yaron da yanzu yake koyon tafiyar,


"Sannu baba, kana ta zubar da kuɗin ka a ƙasa baka sani ba".


Ɗan tsayawa tsohon yayi kafin ya juyo ya kalle ta a hankali ya kuma kalli hannun ta da ta kwaso masa kuɗin Naira hamsin se ashirin biyu, da ƙyar ya buɗe bakin sa da haƙora da yawa sun zube


"Nagode jikata, kinga ban ma kula buhun ya ɓule ba, Allah yayi albarka kinji".


"Ameen kakana, kawo in maida maka kuɗin in Kuma gyara maka ya dena zubewa ko".


Ta faɗa tana karɓar buhun nasa ta jirkita shi zuwa side ɗin da be huje ba kafin ta ɗan nannaɗe bakin ta miƙa masa


"Gashi kakana, kaga an kusa sakin hannu ga kuma magrib ta kusa, ko zaka zo mu kaika gida tunda a mota nake kaga dare ya kusa".


Karɓa tsohon yayi yana sakin tattausan murmushi a fuskar sa da duk ta mokaɗe
"Nagode jikata, Allah ya saka da alkhairi ya yi miki albarka, Bama se kun kaini ba dan nazo gida, kin ga kwanar nan ita zan shiga".


"Allah Sarki, to Allah ya ƙarasa da kai gida lafiya kaka, bari inje kar a saki hannu".


"Allah ya shirya mana ku ya kawo miji nagari".


Da sauri ta amsa da Amin tana tafiya har ta ƙarasa wajen motar su, buɗe ƙofar tayi zata shiga se kuma ta juya inda ta bar tsohon, yana nan kuwa tsaye kallon ta, hannu tai masa waving kafin ta shige jin an bada hannu, ɗauke idon sa Saraki yayi daga kanta ya maida kan steering yaja motar, haka ta dinga leƙa window tana kallon tsohon da ya cigaba da tafiya a hankali fuskar ta ɗauke da murmushi har ya shige layin da ya nuna mata kafin ta koma ta zauna daidai tana sauke ajiyar zuciya.


Horn yayi a katafaren gate ɗin kafin gate ɗin ya buɗe ya shiga da motar har wajen parking, kashe motar yayi bayan ya gama daidaita parking ɗin hakan yasa Kisnah kwasar wayoyin ta da purse ɗin ta ta fita, zagowa tayi daidai shima ya fito yana kulle motar yaa miƙa mata key ta tsaya tana kallon shi batare da ta karɓa ba


"Ai kai zaka cigaba da riƙewa tunda kai ke driving ko".


"No zan je gida in kwaso kayana tukunna gobe na dawo". Ɗan shiru tayi kafin ta gyaɗa kai tunda yau bazata fita da dare ba


"Okay kaje da ita amma ka shigo da wuri dan ina da class by 9, wannan ragowar bags ɗin na bayan mota naka ne".


Batare da ta jira me zece ba tayi gaba kafin ta ɗan tsaya tace
"Thanks". Ta cigaba da tafiya har ta shige falon..........................✍️.














My Kisnah Allah yasa kina da rabon shiriya 🥺.






©️ Ouummey 📚✍️.






☑️Ote, comment and share fisabilillah.






































Ouummey 14 (8/7/2022 9:40 PM )





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________
















Page 1️⃣4️⃣








___________________________📖 Zaune a falon ta tadda Mommy da Maigado suna hira while watching TV, kallo ɗaya ta musu ta ɗauke kai ta cigaba da tafiya heading to the staircase, cikin danne takaici, baƙin ciki da tsanar da tayi mata Mommy tace


"Welcome back".


Hannu kawai ta ɗaga mata ta haye sama dan har yanzu jikin ta a mace yake ga kuma gajiyar dukan da tayi wa Sageer, dole tana buƙatar wanka yanzun nan ma kuwa.


Unlocking door ɗin tayi ta shige locking it back ta ciki kafin ta ƙarasa ta zube wayoyin ta kan sofa ita kuma ta wuce bedroom, undressing kanta tayi as usual without using towel ta ƙarasa bathroom ɗin tayi wanka sosai da cold water batare da damuwa ba kana ta fito yanzu kam ɗaure da towel se wani da tayi tying kanta ciki saboda jiƙewar da gashin ta yayi, goge kan tayi sosai kafin ta jefar da towel ɗin ta ɗau dogon brush ta shiga combing hair ɗin, dole gobe in ta fito test ta wuce saloon dan kan ya fara damun ta, in aka wanke se ayi mata ko kalba ne ko twisting sedai taje ta ga Wanda zata zaba.


Cikin wannan tunanin ta gama busar da kan da hand dryer ɗin ta sannan ta koma gaban wardrobe ta ciro sleeping dress ta saka dan bata jin zata kuma fita daga ɗakin nan se kuma gobe.


Kwanciya ta nufi yi dan ta gaji sosai so take ta huta ko kaɗan ne kafin ta tashi ta sake karatun test ɗin da zasu yi gobe se kuma ta tuna bata fa yi sallah ba yau, dafe goshin ta tayi dan wallahi ta gaji maƙura, haka dai dole ta tashi ta koma bathroom ta ɗauro alwala ta fito, hijab ɗin sallar ta tasaka ta hau duddungura sallar, nan da nan kuwa tayi ta gama tun daga Azahar la'asar har magrib ɗin da aka idar yanzu (wa yaga me shaf shaf😂🤣) kafin ta cire hijab ɗin ta bi lafiyar gado.


Bacci tayi har goma na dare kafin ta farka sedai bata tashi ba se da ta ɗan sarara har taji daidai dan ba'a son daga farkawa bacci mutum yace ce tashi, toilet ta shiga tayi brush tare da wanke fuskar ta sannan ta fito ta ɗau littatafan school ɗin ta tare da laptop other than that da tayi amfani dashi da safe, laptop ne me kyau da kana gani kasan ce yi tsada bayan sa ɗauke da tambarin K&S wanda purposely sabida karatu take amfani dashi ta koma falo kan sofar da ta ajiye wayoyin ta.


Ɗauke su tayi ta zuba kan center table ɗin ɗakin kafin ta zauna tana ajiye system ɗin kan ƙafar ta, cike da ƙwarewa da tsantsan iyawa take pressing keyboard ɗin wanda baka jin ƙaran komai a ɗakin se nasa.


Sosai ta maida hankali kan research ɗin da take yi har ta samu abinda take so kafin ta janye system ɗin ɗan gefe kaɗan da ya ita ta ɗau ƙaton littafin lauyoyi ta cigaba da going through.


A ƙalla tayi spending 5 hours tana karatu wanda bata lura lokaci yaja haka ba se da ta kalli agogo mistakenly, zare kyawawan oily cat eyes ɗin ta tayi kafin kuma ta dafe baki ganin har 3am, da sauri tai shutting down system ɗin ta ajiye tare da books ɗin ta wuce bedroom da gudu, kan bed tayi tsalle ta faɗa tana tura hannun ta ƙarƙashin pillow ta jawo photon ta ta rungume a chest tareda covering kanta with duvet, ƙarfi da yaji ta hana kanta tunanin komai dan haka cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi gaba da ita.


Ƙarar buɗe gate ne ya farar da ita daga baccin ta me daɗi (kun san ga every student daɗin baccin asuba daban ne😂), ɗan juyi tayi dan se taji kwata kwata baccin be ishe ta ba, she wants more and more, har ta rufe ido dan komawa kalman test tai ringing a mind ɗin ta hakan yasa ta zabura da sauri tana kai kallon ta kan designer wall clock ɗin ɗakin


"Oh my God".


Ta faɗa tana durowa daga gadon da sauri har tana

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads