Showing 21001 words to 24000 words out of 104570 words
Chapter 8 - SARAKI (The Accused Prince).txt
da suka ga Kisnah to fa yau sun warke, aikuwa alkhairi sosai tayi musu suna ta washe baki, cikin ƙankanin lokaci aka canjawa Surayya asibiti zuwa wata tsadaddiyar private hospital aka canja mata, take a ka kai su wani tanƙamemen ɗaki kamar a gidan su, likitoci suka rufu kan ta aka fara bata kulawar data dace, banbancin asibitin kuɗi dana gwamnati kenan, *KULAWA*!
Ƙarar wayar ta yasa ta cire tagumin da tayi tana duban
screen ɗin, ganin sunan Meenah yasa tayi picking tare da sawa a speaker.......................✍️
©️ Ouummey 📚✍️.
*☑️Ote, comment and share fidabilillah*.
Ouummey 10 (8/3/2022 3:52 PM )
💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠
Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey
*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*
______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________________
Page 1️⃣0️⃣
_____________________📖 "Hasbunallah wani'imal wakeel". Ya faɗa yana dafe kansa, shiru shagon yayi cikin jimamin tsaka me wuyar da ta same su lokaci ɗaya daga sama, dukkan su tagumi ne suka yi da hannu bibbiyu barin ma Alh Musa me shagon.
A hankali Alh Musa ya ɗan motsa kafin ya fara magana cikin muryar dake bayyana ainahin damuwar da yake ciki
"Wannan abu da ya faru damu rubutacciyar ƙaddara ce da bawa baze iya guje mata ba, na daɗe da sanin muna da magauta da mahassada cikin kasuwar nan kuma abokan sana'ar mu ne sedai ban ɗauka abin ze iya kaiwa har haka ba".
Numfashi yaja ya sauke a ɗame kafin ya cigaba cikin ƙarfin hali
"Ina me baku haƙuri domin nima ba haka naso ba sedai ba yadda muka iya da hukuncin Allah, ina me baƙin cikin sanar daku na sallame ku gaba ɗaya a yau, Allah ya baku wasu hanyoyin samu ya yiwa rayuwar ku albarka ya saka muku da alkhairi bisa zaman amanar da kuka yi dani da junan ku, duk wanda na ɓatawa a zaman mu ya yafe min dan ɗan adam ajizi ne, nikam baku taɓa min komai ba koma kun min na yafe muku duniya da lahira".
Shiru duk sukayi wasu na sharar hawaye, ko a shekaran jiya basu taɓa kawo tunanin haka na iya faruwa dasu ba, sedai in akace kana da magauta da mahassada to fa se kariyar Allah kawai.
Abin da ya faru kuwa shine ragowar maƙota da wasu daga cikin abokan kasuwancin Alh Musa ne suka fara fito masa da hassadar su ƙarara dan sun daɗe suna ɓoye ta sedai zuwan Saraki yasa suka kasa riƙe kansu ganin yadda al'amura da kasuwancin Alh Musan suka ƙara bunƙasa, yasan suna masa hassada sedai be ɗauka zasu iya cutar dashi har haka ba, akwai kayan da yayi order Wanda in suka zo ana sa ran ba ƙaramin roba za'a samu ba shine suka yi masa shune custom suka kama kayan wanda bana ƙananan kuɗi bane, kusan dukkan jarin shi ya tattare dan babbar order ce se Gashi custom sun kama kayan a shekaran jiya da daddare, hankalin da ya tashi sedai bisa tunatar war me ɗakin sa yasa ya barwa Allah komai ya cigaba da addu'a dan ko yaran da be sanar dasu ba, a jiya ne kuma abokan kasuwancin nasa dake son ganin bayan shi suka tada ɓallin son ya biya su bashin da suke binsa na kayan da ya karɓa kamar yadda ƴan kasuwa ke yi in sun karɓi Kaya su biya rabi daga baya su cika, be ja da nisa ba ya haɗa ragowar kuɗin hannun da ya basu tare da sauran kayan da ba'a siyar ba, hakan yasa yau shagon ya tashi kusan ba komai a ciki se tsirarun takalman da basu wuce a irga ba, wannan shine dalilin sallamar su Saraki da yayi tun da ba kaya a shagon yana son kwashe ragowar kayan sa ya saki rumfar dan dama suna watan biyan kuɗin hayar sabuwar shekara da za'a shiga ne.
A sanyaye Saraki ya ɗago kansa dake sunkuya ya fara tausar megidan nasu da kawo masa hadisai da ayoyin da suka tabbatar da nasara ga duk wanda yayi haƙuri yayi tawakkali ya kuma Ubangiji yadda ya kama ta, wannan ne karo na farko ga duk wanda ke shagon da yaji Saraki yayi doguwar maganar da ta wuce sentence biyu zuwa uku, cike da kewa da tausayi Alh Musa sukai sallama bayan sun taya shi kwashe ragowar kayan sa zuwa gidan sa kowa ya nufi hanyar da ya fito.
Ya daɗe zaune a ɗaki yana tunanin da be san inda ze ɓulle masa ba ba'a kan komai ba se kan sana'ar da ze kama nan gaba se dai be san ta Ina ze Fara ba, ajiyar zuciya ya sauke bayan sunan Idris ya faɗo ransa, tabbas ya zama dole ya sanar dashi abinda ake ciki tunda shine yai masa hanyar zuwa shagon.
Without any hesitation yai dialing number Idris Wanda bugu daya ya ɗauka da sallama Muryar sa cike da farin cikin ganin yau Saraki ya kira shi duk da dama yakan kirashi sa'i da lokaci.
Gaisawa suka yi kafin a nutse Saraki yai masa bayanin halin da ake ciki zuwa zaman da yake ba abin yi, sosai Idris ya jinanta faruwar hakan ya kuma tabbatar masa da zeje yayi wa Alh Musan jaje kafin a ƙarshe ya ƙarƙare da insha Allah cikin satin nan za'a samowa Sarakin wani aikin.
Ajiye wayar Idris yayi a gefen sa kafin ya sanar da yayan sa da suke tattauna batun gyaran motar shi (drivern da ya tuƙo motar da saraki ya hau daga Giwa zuwa Manya) karayar arziƙin da ta sami tsohon maigidan sa Alh Musa, sosai yayan sa shima ya jimanta abin tare da Allah wadai da mahassada kafin ya dubi ƙanin nasa
"Maganar aikin abokin ka ina ganin akwai aiki a hannu in ze iya".
Da mamaki Idris ya dubi yayan sa
"Farawa da iyawa, amma naji daɗi gaskiya, yadda aiki yake wahala yanzu amma har ya samu, gaskiya Ahmad me Sa'a ne".
"Bawai Sa'a ba Idris, aikin nan ya daɗe a ƙasa sedai duk wanda aka samarwa da yaji wadda zewa aikin da yanayin tsarin aikin se yace baze yi ba, kasan yanzu jama'ar garin nan sun fi ganewa kasuwanci kan aikin albashi".
"Sosai ma kuwa, nikaina bana jin zan iya aikin albashi yaya, amma me yasa ake ƙin karɓa, I mean ya tsarin aikin yake".
Numfashi yayan Idris ya saki
"Tuƙin mota ne, wata Hajiya ce ke neman driver da ze ding tuƙata duk inda zata, matsalar aikin shine tana fitar dare kuma duk lokacin da zata fitan ze tashi ya Kaita, a taƙaice dai duk min dare, safiya, sanyi, rana ko damina in ta buƙaci zuwa waje shine ze kaita".
"Wannan ai ba matsala bane yaya, ai dama amfanin ɗaukar driver ɗin kenan, Ni banga aibun aikin ba".
"Aibun shine fitar dare, tana fa ita fita ɗayan dare, biyu, uku, huɗu ko ma dai karfe nawa na dare".
Shiru Idris yayi cikin jinjina lamarin aikin dan gaskiya fitar daren matsala ce, daga yanayin aikin ya gane ba hutu ko kaɗan, ka wuni kana tuƙi sannan ka kwana kanayi gaskiya da matsala.
"Da matsala kam dan matsala yaya, amma me ze Hana in Masa Magana, in ya fara yaga baze iya ba se a neman masa wani dan na fahimci ba ya san zama haka kawai".
"In har ya yadda ni me farin ciki da haka ne dan na sama wa abokina mafita, kasan Inusa aka ɗorawa nauyin samo driver kasancewar da yayi aiki a gidan kuma sun yadda da amanar da kafin daga baya ya ajiye ya buɗe shago a nan kasuwa, yanzu haka kullum se yayi min batun aikin dan baya son suga kamar yana sane yaƙi sama musu bayan duk halaccin da sukai masa".
"Ai bari ma kaga in kirashi yanzun nan in sanar dashi, gwara mu sani in ze iya ko kuwa ba se ansa rai ya kasa ba".
"Yauwa maza kirashi".
Cikin sauri kuwa Idris ya kira Saraki da a ringing ɗin farko ya ɗaga da sallama, a taƙaice Idris yayi masa bayanin aikin da kuma yadda tsarin aikin yake be ɓoye masa komai ba har batun fitar daren kafin ya saura dan jin me Sarakin ze ce, shiru yayi kamar baze ce komai ba kafin ya amsa da ze yi insha Allah, cikin tsananin farin ciki sukai sallama da Idris ya ajiye wayar.
Lumshe ido Saraki yayi cikin daɗa jujjuya yanayin aikin a ransa, katse tunanin yayi yana miƙewa ya wuce toilet ɗin sa dake wanke fes yana ƙyalli, alwala yayi ya fito ya ɗora baƙar jallabiya a kan boxers da singlet ɗin jikin sa ya tada kabbara kan sallayar shi.
Raka biyu yayi wadda a cikin su ya sauke Suratul baƙara kafin cikin sujjada ya nemi zaɓin Allah kan aikin da aka kawo masa, tasbih ya ɗora ko da ya idar sannan ya buɗe Alkur'anin sa ya ɗora karatun sa da yake sauka duk sati, seda yakai adadin surorin da yake yi kullum kafin yayi addu'a ya ajiye ya kwanta.
Da safe ko da ya tashi wasai ya jishi tare da sake jin kwanciyar hankali kan aikin nasa, a safiyar Idris take ya tafi dashi wajen abokin yayan sa Inusa wanda anan za'a sanar dashi adadin albashin sa tare da raka shi gidan da zeyi aikin.
*********
Muryar Meenah ke fita daga speaker wayar inda ta shaidawa Kisnah sunje Ado Muhammad Manya hospital ɗin amma basu gan su ba, ɗan dafe kan ta dake mata ciwo kaɗan kaɗan tayi sannan ta bata amsa
"Am sorry, na karɓi sallama ne na kawo ta nan get well, ku ƙaraso nan".
Ok kawai Meenah tace ta kashe wayar, itama kifa kai tayi kan tata wayar cikin tunanin da ya kasa barin kanta na waye yai drugging ɗin ta jiyan, Surayya ce dama zata iya shiga zargi dan itace bata wajen lokacin data dawo sedai yadda tayi ƙoƙarin kuɓutar da ita dole ze shaidawa me zargin ba ita bace, to waye??? Wannan shine amsar da ta gagara samu gashi bazata iya barin asibitin ta tafi station ba a halin da Surry ke ciki.
Cikin wannan tunanin su Meenah suka shigo ita da Leekha da Meedah, cikin nasu tashin hankalin suma suka ƙarasa gaban gadon da Surry ke kwance suna jajantawa, Leekha da Meenah har da hawayen su, Meedah da tafi su karfin zuciya ce kawai bata koka ba sedai itama nata idon yayi jajir, haka suke basa san ko yaya cuta ta sami ɗaya daga cikin su duk da sukan sami saɓani ko jin haushin juna wani lokutan.
Kan sofar da Kisnah take suka zazzauna suna tanbayar garin yaya hakan ta faru da Surayya, cikin damuwa Kisnah ta sanar da su duk abinda ya faru, ko kafin ta gama faɗa musu tuni Meenah ta miƙe rai ɓace ta nufi fita daga ɗakin, da sauri Meedah ta bi bayan ta yayinda daga Leekha har Kisnah ba wanda ya dakatar dasu dan bama tsayawar za suyi ba, baki Leekha ta ringa ba Kisnah ganin yadda duk ta damu, se lokacin tunanin sanar da iyayen Surayya yazo musu, Surayya marainiya ce da take hannun yayanta namiji wanda su biyu kaɗai iyayen su suka haifa, yayanta ba mazauni bane haka kuma matar sa bata da mutunci Sam ba ta kuma shiga harkar Surayya hakan yasa ko zata kwanan nawa ba zata neme ta ba se in ita taga dama ta koma, sauƙin abin duk iskancin su basa kwanan waje, duk nisan dare se sun koma gida sedai in sun gaji da zaman gidan sun kama hotel dan hutawa shine fa se sanda suka gama hutun suka koma gida.
Cikin sanyin da jikin ta yake take scrolling through contact ɗin ta har ta samu sunan Auntyn Surayya da tayi saving da *matar yaya* kasancewar suna girmama Junan su da ɗaukar iyayen junan su matsayin nasu, ta sami number ɗin ne lokacin da Surry ta kwana tare da ita aka kuma yi rashin Sa'a yayan Surayyan ya dawo ranar shine fa cikin tashin hankalin tsoron faɗan da yayan ce mata Aunty ta kira number Kisnah dan ta yi ta kiran ta Surayya a kashe.
Kusan five miscall tayi mata kafin a kan na bakwai ɗin ta ɗauka cike da izza da yanayi na an takura mata take tambayar waye, batare da kula wulaƙancin Auntyn ba dan sarari tasan Kisnahn ce kawai salon wulaƙanci ne ta soma nata bayanin halin da Surayyan take ciki.
Sosai hankalin Auntyn ya tashi dan wasan every blame ze koma kan ta ne in yayan Surayya yaji abinda ya faru, hakan yasa tuni ta manta da batun wulaƙanci ta roƙi Kisnah kar ta sanar da yaya gata nan zuwa, kashe wayar kawai Kisnah tayi ta ajiye ta maida idanun ta ta lumshe kamar dai yadda take a ɗazu.
Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sefa Auntyn ta ƙaraso, ba wanda ya kula ta a cikin su ta ƙarasa gaban gadon da Surayyan ke kwance, zare idanu tayi ganin har da ɗinki, cikin tashin hankali take tambayar su garin yaya hakan ya faru da ita, Leekha ce ta bata labarin komai kamar yadda Kisnah ta sanar dasu dan ko buɗe idanun ta ita Kisnah bata yi ba bare ta bawa Auntyn amsa, zage zage ta fara a ɗakin tana blaming Kisnah kan ita ke koyawa Surayya lalacewa Gashi nan ta sanadin ta daraja mata mutuwa, banza tayi wa Auntyn kamar bata jin ta har se da taji ta fara taɓo iyayen ta kafin ta buɗe idanun ta da suka canja kala daga attractive golden brown oily and sexy eyes zuwa brownish color so scary ga me kallon su, tsit Aunty tayi da bakin ta ganin mugun kallon da Kisnahn take binta dashi, duk iskancin ta tana shakkar yarinyar dan tasan ta fita iya shege da sanin malamar rashin mutunci shiyasa tana iya taka su Meedah amma bata taɓa kwatanta yi wa Kisnah ba se yau, yatsar ta manuniya ta ɗaga tana nunawa Aunty hanyar fita wato ta fice ta basu waje, jim tayi kamar bazata fita ba kafin taka uban tsaki tayi waje fuuuuu kamar zata tashi sama.
Haka suka ƙarasa wuni wajen Surayya har su Hameedah suka dawo, anan suke shaidawa Kisnah wanda yayi musu wannan aika aikan
"Kin tuna wani gaye da i think two months ago yazo wai yana son ki??
Yamutsa fuska Kisnah tayi cikin son tuno Wanda suke magana akai amma ta kasa, ko banza masu cewa suna son nata ai ba iya ƙirga su zata yi ba dan haka ta girgiza wa Meenah kai
"Wanda fa kika mara a club da ya rungume ki kina rawa".
Cikin sauri ta gyaɗa kai dan shi kaɗai ya taɓa mata haka kaf shekaru uku da tayi tana zuwa hideaway club
"To shine ashe ya sa miki drug acikin kunun ayar da kika ake da zaki rawa, he take advantage of us da bama hayyacin mu ya saka ita kuma Surayya dama kina tashi itama ta bi saurayin ta".
Shiru Kisnah tayi cikin tuƙuƙin ɓacin ran abinda yaso aikata mata jiya, wato dan ta mareshi shine bari ya yaga mata mutunci ko, aikuwa zata yi maganin sa.
"Yanzu me kuka ce ayi masa a station?". Leekha ta tambaya
Meedah ta bata amsa da
"Mun ce kar a sake a bada bail ɗin shi ko uban waye yazo".
Jijjiga kai Kisnah tayi alamar hakan yayi kafin suka tarkata kowacce ta nufi gidan su dan ba'a kwana a asibitin dan suna da masu jinyar patients.
Ko da tayi parking ta daɗe Bata fito ba daga motar har se da taji kan ta dake ciwo ya ɗan tafi, tasan ba komai bane illa effect ɗin ƙwayar da yasa mata jiya wadda ita ke ta wahalar da ita dan ba ta taɓa sha ba, a hankali take takawa ba kamar yadda ta saba kullum ba sedai duk da haka cat walk ɗin nan dai take yi wanda haka asalin tafiyar ta yake.
Da sauri me bawa flowers ruws ya ƙarasa gaban ta ya ɗan durƙusa hakan yasa ta dakata da tafiyar da take yi ta duba shi
"Dama Inusa yace in sanar dake sun zo ɗazu ba kya nan, in ba damuwa zasu dawo gobe shi da sabon driver ɗin da aka samo".
Nodding kanta tayi kafin cikin rashin son magana saboda ciwon kanta tace
"Zan jira su by 9:30am".
Da hanzari ya amsa da ze faɗa musu insha Allah, bata ƙara jiran me zarce ba tayi gaba, a falo ta tadda kawu wanda wunin yau taga ya tsiro zaman falon su maimakon nasa da yake zama da, bata ko ce masa ƙala ba ta haura saman ta ta buɗe ta shige, bedroom ta wuce ta faɗa kan gado tana sakin nishin azaba kafin da ƙyar ta zare takalman ƙafar ta ta haye gaba ɗaya ta ja blanket saboda ɗan sanyi sanyin da taji yana shigar ta..........................✍️.
©️ Ouummey 📚✍️.
*☑️Ote, comment and share fidabilillah*
Ouummey 11 (8/4/2022 4:14 PM)
💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠
Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey
*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*
______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________________
Page 1️⃣1️⃣
_______________________📖 Bargo ta tashi ta ɗauko da ƙyar ta ƙara kan blanket ɗin ta shige ciki.
Ranar ko kayan jikin ta bata iya canjawa zuwa na bacci ba ta kwanta dana jikin ta.
Sosai tayi bacci saboda ɗumin da ke ratsa jikin ta wanda bata farka ba se to nine, wanka ta shiga tayi ta saka Black straight English gown me ɗan gajeren hannu da ta tsaya iya ƙaurin ta, yau bata kama gashin da ribbon ko sa masa band ba