Header Ads
Showing 6001 words to 9000 words out of 104570 words

Chapter 3 - SARAKI (The Accused Prince).txt

Ads the beginning of article before Image

ummi   

03 Jun 2024

1420

Ads at the middle of Article

gidan nan, in ta ƙaryata kuma kar ta fasa in har ta haifu cikin uwar ta wato ke".


Tana gama faɗa abin da ke ranta ta hayewar ta sama cikin tafiyar gudu gudu sauri sauri, key ta sa ta buɗe ƙofar ta shiga parlon tare da maida ƙofa ta rufe.


Haɗaɗden falo ne da yaji kayan ado na zamani masu matuƙar tsada da kyau wanda samun irin su se gidan wane da wane, tun a nan ta fara cire kayan jikin ta tana watsar wa, kafin ta shiga bedroom saura pant da bra kawa a jikin ta, toilet ta wuce ta shige cikin jacuzzi tana kunna tap ɗin ruwan sanyi.


Ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ruwan ya fara sauka a jikin ta, haka ta kasance cikin cold water for at least 30 minutes kafin taji ga dawo daidai ta buɗe rariya ya fita, fita tayi daga jacuzzin kana tai diluting hot water with cold one daidai yadda take so ta shiga ta fara wankan ta.


Towel ta ɗaura ɗan guntu da beko gama sauka ƙasan kwankwason ta ba ta fita daga toilet ɗin, wardrobe ɗin ta ta buɗe dan duba kayan da zata saka, cike damƙan wardrobe ɗin take da kaya kamar za'a buɗe shago, sutturu ne gasu nan kamar zasuyi magana kama da ga kan atamfa, lace, shadda, abayas se ƙananan kaya wanda sune sukai dominating.


Tsaki taja dan ta rasa wane ma kayan zata saka, kan gado ta faɗa ta ja bargo rabin jikin ta ta rufe ido, bacci take ji kamar me, sauƙin ta ma yau bata da lectures shiyasa zata yi abin ta ta more.


Kamar wadda akayi wa magana ta tashi da sauri zuwa jikin wasu drowers dake jikin bango, ɗaya dag ciki ta jawo slowly, hannu ta ɗora kan photo album ɗin dake ciki kafin ta jawo shi a hankali cike da takatsantsan dan bata buƙatar abinda ze taɓa mata shi balle har ya yage.


Zama tayi bakin gadon ta buɗe shi a hankali tana yi tana shafawa, photo ne ya bayyana a shafin Farko na album ɗin, hoton wasu kyawawan couple da kallo ɗaya za'a yi musu a tabbatar da tsananin ƙauna da soyayyar dake tsakanin su, ƙurawa hoton ido tayi tana kallo cikin wani irin maɗaukakin shauƙi da ya kasa ɓoyuwa kan fuskar ta, hannu ta ɗora daidai saitin fuskar macen ta shafa haɗi da lumshe kyawawan idanun ta, tsawon mintuna kafin ta buɗe idanun ta janye hannun ta ta maida fuskar namijin yayinda idanun ta suka cika da hawaye, shafa fuskar take cikin kewa da son kusan ci sedai hakan ba me samuwa bane.


Next page ta buɗe wanda ke ɗauke da hoton same couple sedai wannan karon hannun su riƙe yake da jaririya nannaɗe cikin showel me tsananin kyau da ɗaukar hankali dan an masa ado ne irin na yara a jiki, ko daga idanu kasan ze yi tsananin taushi, fuskokin ma'auratan ɗauke da kyakkyawan murmushi da ya ƙara musu kyau duk da duk cikin su ba baya wajen kyan.


Hawayen da ya zubo daga idon ta yasa ta maza ta rufe album ɗin tareda janye shi dan bata so ya ɗiga akai balle ya ɓata shi, maida shi tayi wajen ajiyar sa kana ta dawo kan gadon ta kwanta, ɗaga pillown ta tayi ta janyo wani photo guda ɗaya wanda shima dai photon wannan couple ɗin ne ta rungume a ƙirjin ta kana ta kashe wutar ɗakin haɗi da lumshe idanun ta..........................✍️


©️ Ouummey 📚✍️




☑️ote,Comment andShare fisabilillah.


































Ouummey 04 (7/30/2022 6:00 PM )





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________














Page 4️⃣












__________________📖 ƙarfe huɗu da rabi sannan ta tashi daga baccin, miƙa tayi ta ɗan zauna for some minutes har ta ji tayi daidai sannan ta miƙe ta shiga toilet. Wanka tayi sannan ta ɗauro alwala ta fito, zama tayi kan madubi ta lailaye jikin ta da mayukan shafawan ta masu matuƙar tsada da suke tashin ƙamshi kamar wani turare, busar da gashinta tayi tayi oiling ɗin sa ta parking ɗin shi in a crazy style.


Kwalliya ta zauna ta tsara a fuskar ta kamar me shirin zuwa zaɓen sarauniyar kyau na duniya, though nude make up ne amma ba ƙaramin haɗuwa tayi ba, gajeran wando ta saka wanda ya tsaya iya cinyar ta se ƴar shimi me siraran hannuwa biyu a each kafaɗa, band kalar wandon ta saka a kanta tareda sake yiwa jikin ta ɓarin turarurruka masu ƙamshi sosai.


Jikin wardrobe ɗin ta koma ta buɗe wani side ta Ciro dogon hijab Wanda take sallah da shi ta zura kana ta koma inda praymat ɗin ta yake ta tada sallah.
Shaf shaf tayi sallar ta idar da Azahar, without any azkar ta Kuma miƙewa ta tada sallan la'asar shima nan da nan ta idar, gaba ɗaya raka'a takwas ɗin a mintunan da basu fi huɗu ba tayi ta idar.


Cire hijab ɗin tayi ta saka wani flat shoe me matuƙar taushi ta buɗe ɗakin ta fita, ta ƙofar bayan dake jikin stairs ɗin nata ta fice zuwa garden, Zama tayi cikin ɗaya daga cikin kujerun da suka ƙawata kyakkyawan gurin da yake da matuƙar kyau da ɗaukar hankali duba da yadda korayen flowers da ciyayi suka lulluɓe shi, gefe ɗaya kuma swimming pool ne me ɗan girma ruwan cikin sa tsaftatacce dan ana iya hango ƙasan pool ɗin.
Gefen hagu kuma bishiyu ne da sukai girma na ban sha'awa, bishiyar guava, bishiyar ayaba, bishiyar mango and some other kinds of fruits.
Airpeace ta saka a kunnen ta ta lumshe idanunta tayi tana sauraren waƙar ta cike da jin daɗi da nishaɗi, a duk lokacin da take buƙatar kaɗaici nan ne wajen zaman ta, ta ji waƙar ta in ta Kai Mata ta taka rawar ta.
Se kusan ƙarfe bakwai ta bar wajen dan har an ɗan jima da idar da sallar magrib, wannan karon ta cikin main parlor ta ratso ta wuce su Mommy zaune suna hira ita da ƴaƴan ta, wani banzan kallo Maigado tabi ta dashi haka ma Mommy banda Awwaf da ya bita da kallon ƙurilla kamar ya cinye ta ɗaya.


Bata dubi ko ɗaya daga cikin su ba ta haye stairs ɗin ta tana yi tana moving jikinta towards each sound na waƙar.
Sauke ajiyar zuciya Awwaf yayi ya dubi mahaifiyarsa, haɗa ido suka yi tana jefa masa kallon gargaɗi, shafa kansa yayi ya ɗan zame zuwa kishingiɗa, hannun Mommyn ya riƙo yana marairaice murya


"Mommy I can't take my eyes off this beautiful creature, pls ki bar ni na aure ta mana".


Wani irin fisge hannun ta Mommy tayi tana watsa masa wulaƙantaccen kallo sedai kafin ma ta buɗe baki tuni Maigado ta riga ta
"Over my dead body, yanzu kai yaya da bakin ka kake faɗar zaka auri wannan karuwar? Are You in your right sense or yau ɗin ma kaje kasha kayi tatul ne, duk wulaƙanci da rashin mutuncin da take mana baka gani ba kake batun aurar ta? what came over you ne? Ko da yake ba abin mamaki bane zaka iya fiye da haka ma zakayi tunda ba uban mu ɗaya ba ai dole se ka nuna mana wannan bambancin".


Zaburowa yayi ze dake ta Mommy ta riƙe shi tana hararar shi kamar idanun ta zasu faɗo
"You stupid boy, har ni zaka kalli fuskata kace zaka auri maƙiyar da bani da sama da ita? Eye, ko da yake gaba ɗaya zantukan Maigado akan daidai suke , zaka iya fiye da haka tunda ka zama son of that worthless bitch, lemme tell you something, wallahi ko da wasa na kuma Jin that bitter sentence from your mouth se na saɓa maka ta yadda baka taɓa tunanin zan iya ba, stupid being kawai".


Komawa yayi ya zauna yana me dafe kansa kafin kuma ya buɗe su yana kallon ta
"Naji na bar maganar auren ta, but sincerely speaking I can't take my eyes off her, dan haka I'll follow ko ma wace irin hanya ce in same ta dan I have passion in her".


Washe baki Mommy da Maigado sukayi, Mommy ta dafa shoulder ɗin sa
"That's my son, se yanzu naji daɗi, nima ban ce ka ƙyale ta ba, ka bi kowace hanya ka biya buƙatar ka akan ta zan tsaya maka, in fact ma Sena fi kowa farin ciki da murna saboda rayuwar ta ta lalace".


Murmushi ya sake jin yadda Mommy ke goyon bayansa tareda ƙara masa ƙarin gwiwa, sosai yaji yana zumuɗin samun damar aiwatar da ƙudurin sa dan yasan ko ta wace hanya Mommy bazata taɓa bari a gano shine ba, haka suka cigaba da tsare tsaren su na abubuwan da zasu yi wa Kisnah su huce takaici da baƙin cikin da take ƙunsa musu.


Baiwar Allah ita tana can ɗakin ta kwance a gado bayan ta idar da sallar magrib, chatting suke yi da su Hameedah suna bata haƙuri kan abinda ya faru ɗazu ta bada umarnin a sake su Abeed ita kuwa ta kafe tace bata san zance ba, dole a wulaƙanta mata su dan bazata yarda su tafi Scot free ba.


Kashe datan tayi ganin tara yayi, a ƙa'ida tara take bacci in har bata da party ko club ɗin zuwa, wanda tuni ta ware ranakun juma'a, asabar da Lahadi as clubbing days ɗin ta.
Miƙewa tayi cikin shigar kayan baccin da tai wadda ƴar guntuwar riga ce da ta tsaya can saman cinyoyinta, ƙaramin hannu gare rigar masu kama da na brazier, flat bedroom slippers ɗin ta masu taushi ta zura ta fita daga falon gaba ɗaya zuwa ɗakin kawun ta mijin Mommy a Haka batareda ta nemi abin suturce jikin ta ba.


Gaba gaɗi ta murɗa ƙofar ɗakin fa shiga parlon nasa without any permission or sallama, Mommy kaɗai ta tarar zaune kan one of the cushions na ɗakij tana danne danne a waya, zagaye falon tayi da idanun ta amma bata ganshi ba which means Yana bedroom, hanyar bedroom ɗin ta nufa ta buɗe ta shige bata kula kiran da Mommyn take mata ba kan ta jira ya fito.


Sanye da jallabiya yana tsane ruwan kansa ta same shi, zama tayi gefen gadon sa shikuma yana gaban mirror sedai tun shigowar ta ya ajiye towel ɗin ya dawo gefen ta shima ya zauna.
Wani irin kallo yake ƙare mata ta gefen ido yayinda ita sam bata san yanayi ba dan abinda ya kawo ta ta shiga faɗa batareda ta gaishe shi ba dan tuni ta yaye gaisar da mutanen gidan.


"Nace matar can ta faɗa maka ina buƙatar 2 million urgently Amma sedai har yanzu ban ji alert ba, me hakan yake nufi?
Washe baki Kawu yayi duk kuwa da cewa zancen ta ba ƙaramin ɗaci yayi masa ba a zuciya


"Kuɗin Company ne yayi ƙasa ƴar Kawu shiyasa kika ga ban turo ba akan ta faɗa min, dama ina jiran gobe tayi ne se in turo Miki ko 1 million ne tunda ba 2 million a ƙasa".


Wani banzan kallo take bin Kawu dashi tun lokacin da ya fara magana har ya gama kafin cikin tsiwa da rainin hankali ta fara nata faɗan


"Bangane kuɗin Company yayi ƙasa ba, wai Kawu me kake da kuɗin nan ne da duk sanda zan yi maganar kuɗi seka kawo min wani banzan uzuri, wait, wane Company ɗin ne kuɗin sa yayi ƙasa, specify Ina jinka tunda dai kasan ai companies ɗin da yawa".


Haɗiye wani yawu Kawu yayi yana ɗan inda inda
"Ehm dama, dama , ehm dama Company ɗin flour ne amma ba ma wani ƙasa yayi sosai ba kawai dai na faɗa ne dan naga karɓar kuɗin da kike yayi yawa".


Wata muguwar harara ta watsa masa kana ta miƙe tana riƙe ƙugu
"Excuse me dattijo, the last I checked dai kuɗin bana wani ƙaton banza bane nawa ne ko? Ko kuwa kun haɗa ƙarfi da Abbu lokacin neman su da tara su ne ban sani ba?, bana son wani banzan excuse, dukiya dai ta wace , wakilci na baka to meye zaka ringa wani son nuna min gadara da iko, okay nagane duk laifi nane amma xan gyara, a tattara min bayanan shiga da ficen kuɗin kowane Company da nake dasu, ɗaiɗai har biyar , dole in canja wakilai dan nagaji da wannan baƙin halin naka, and mind you, kafin in ahiga ɗaki kayi min transferring ɗin 2 million ɗin da nace".


Ficewa tayi tana banging Masa ƙofar, dafe kai Kawu yayi cikin tsantsar takaici da ɓacin rai ganin yadda ƴar cikinsa take kallon idanun sa tana faɗa masa maganganu, har shi take kira da ƙaton banza batareda tayi la'akari da alaƙa da matsayin da yake dashi a wajen mahaifin ta ba, ƙwafa yayi yana miƙewa tsaye dan ƙarasa shirin bacci daidai shigowar Mommy, wata banzan kallo Kawu yayi wa Mommy Yana nuna mata ƙofa da hannun sa alamar ta fice masa daga ɗaki, turus Mommy tayi kafin ta buɗe baki zatai magana sedai rikitacciyar tsawar da Kawu ya daka mata yasa ta juya ta fice da sauri a ranta tana tsinewa Kisnah dan duk ta ji abinda take faɗa kafin ta fice.


Dogon tsaki Kawu yaja yana hararar ƙofar kamar Mommyn na gurin har lokacin.


Ita kuwa Kisnah tana shiga ɗakin ta wayar ta ta fara jawowa ta kunna, pop up ɗin message dake yawo kan screen ɗin ta ta danna, kyakkyawan murmushi ta saki akan fuskar ta da ya kuma ƙara mata kyau ganin 2 million ɗin da tace har ya shigo, ƙwafa tayi tana jijjiga kai dan fa dole ta canja Kawu a kan dukiyar ta tunda har yan da guts ɗin cewa karɓar kuɗin ta yayi yawa kamar wani gadon sa.


Ajiye wayar tayi ta koma tayi locking ɗakin sannan ta dawo ta kwanta, a maimakon addu'ar bacci se airpeace ɗin ta tajawo ta maƙala a kunnen ta bayan ta saita wani indian remix me awa huɗu, hoton ta ta jawo daga ƙarƙashin pillow ta rungume a ƙirjin ta ta rufe idanun ta, within seconds bacci yayi gaba da ita.


*************


Tsaye yayi gaban madaidaicin mirror ɗin da ya siyo dan gyaran fuskar sa, dubu da ɗari biyar ya siye shi dan yana da ɗan girma, towel ne ɗaure a ƙugunsa yayinda yake taje sumar kansa cikin nutsuwa bakin sa na motsi alamar yana karanta wani abu ne.
Oiling gashin yayi bayan ya tsaneshi tas da towel, tunanin yadda ze siyi hand dryer yake yi sedai kuɗin hannun sa gaba ɗaya dubu ɗaya da ɗari biyu suka rage, ajiye comb ɗin hannun sa yayi bayan ya taje shi to his satisfaction ya fara shafa mai a jikin sa, ɗaya daga cikin set ɗin ƙananan kayan da ya siyo ya ciro ya saka bayan ya saka undies, sosai kayan suka karɓe shi kamar dan shi aka yi su, perfumes ɗin sa ya ɗauka ya feffesa a jikin sa kana ya ajiye, gyara ɗakin yayi dan tun kafin yai wanka ya wanke toilet ɗin, seda ya gyara komai sannan ya share, plate, spoon and bowl ɗin da yaci abinci jiya da dare.


Tsane hannun sa yayi bayan ya gama ya ajiye su mazaunin da yai musu a ɗakin ya fita tareda rufe ɗakin.
Wajen me communication ɗin gaba da su kaɗan yaje ya karɓi waya ya kira Idriss kan gashi fa ya gama shiryawa har ya fito, amsa masa Idriss yayi da gashi nan ƙarasowa, kashe wayar yayi ya bawa me communication ɗin tareda kuɗin kiran da yayi Naira hamsin.
Nan wajen ya tsaya jiran Idriss ɗin har ya ƙara so, musabaha sukayi tareda tambayar lafiyar juna kana ya hau machine ɗin Idriss ɗin suka shiga cikin kasuwa inda za'a nema masa aikin da ze dinga yi maimakon zaman banza tunda yace arziƙi yazo nema.................✍️


©️ Ouummey 📚✍️


☑️ote, comment and share fisabilillah.
























Ouummey 05 (7/31/2022 4:13 PM)





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________
















Page 5️⃣












__________________📖 Sosai suka zagaya cikin kasuwar suka shisshiga shaguna da yawa inda Idris yake zantawa dasu har Azahar tayi, tsayawa Idris yayi wajen wata me abinci ya siya yayinda Saraki yace a ƙoshe yake.
Sallah suka yi bayan Idris ya gama, juyowa yayi ya dubi Saraki bayan sun idar da Sallah


"Me kake gani game da ayyukan da muka tuntuɓa? Munje shaguna da dama dakai, shagon kayan masarufi, kayan sawa, kanti nan sai da takalma da kuma aikin shara a Company, wanne kake ganin ka fi so yanzu muje in kaika dan da zafi zafi ake dukan ƙarfe, kar mu zauna a cike gurbin da wasu".


Shiru Saraki yayi yana tunani yayinda zuciyar sa ta fi kwantawa da kasuwar takalma, buɗe bakin sa yayi cikin yanayin maganar sa a hankali kamar baya so


"I prefer shagon takalman".


Though Idris be fahimci abinda yace da turanci ba saboda be yi karatu ba amma ya jin takalmi a ƙarshe ya gane ya zaɓi shagon takalmin.


"To tashi muje in kaika su san da kai". Miƙewa suka yi suka fita daga masallacin tareda hawa machine ɗin suka shiga cikin sabon gari ƴan takalma, wani ƙaton shago suka tsaya, shiga suka yi yayinda Idris ya ƙarasa wajen ainahin me shagon suka tattauna na tsawon lokaci kafin suka yi musabaha ya dawo wajen Saraki, jan shi yayi suka fito waje


"Da a nan shagon nake, me shagon tsohon megida na ne, nasan shi mutumin kirki ne

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads