Header Ads
Showing 93001 words to 96000 words out of 104570 words

Chapter 32 - SARAKI (The Accused Prince).txt

Ads the beginning of article before Image

ummi   

03 Jun 2024

1446

Ads at the middle of Article

koren nan ne me yin furkaki in ana wanka, gashi ba yanzu arɗo ze Kuma shiga birni ba which means dole su cigaba da yin wanka da ruwa kawai.


Haka ya ɗibi ruwan a cikin gwangwani huɗu ya kai banɗakin nasu ya watsa kawai yana ɓata fuska ganin yadda jar ƙasan ke fallatsan masa a ƙafafun sa, Allah ya sani shima ya gaji dole ma su bar garin nan kwanan nan, da ya gama shukawa kawu seeds ɗin zasu tarkata suyi gaba dan ya gaji da irin wannan rayuwar, da ya bari ne akan ta ƙara samun life lessons sedai a yanzu kam baze iya daurewa ba dan se ya ga ma ita wadda yake yi domin ta kamar bata damu ba tunda yanzu ko me aka bata ci take yi haka baya tunanin yanzu akwai wata kusurwar da za'a shiga a ɓatar da ita a garin, ɗebo ruwa a rafi kuwa tuni ta zama ƙwararriya dan yanzu tare suke cika abubuwan ajiyar ruwan su da Bingel, kiwo kuwa fita take da shanun ita kaɗai kuma taje ta dawo.


Ƙawayen Bingel kuwa kusan duk nata ne itama duk da ta girme musu sosai dan su basu fi 13-14 years ba dukkan su ita kuwa tana cikin 20yrs ɗin ta ne.


Yana fama canja kaya ko furar da aka ajiye masa be kalla ba ya fita neman ta dan seda ya ce mata kar ta fita dan jiya saura kaɗan wani maciji ya sare ta Bingel ta ganshi ta kashe shi amma shine saboda tsabar rashin jin magana ta kuma saka ƙafa ta bar gidan salon ta ja masa tashin hankali, a yanzu da ya shirya barin garin in not more than a week baze so abinda ze sa su wuce kwanakin da ta ƙidaye ba amma in bata da lafiya ai dole a haƙura da tafiyar abinda baya jin ze iya kenan.


Duk wajejen da yake sa ran ganin ta ya dinga bi yana dubawa sedai ba ko alamar ta, tun yana tafiya da tunanin ze ganta har ya gaji ya tsaya, tunani yake tun da bata daji ina kuma take?


Sunan rafi da yayi ringing a kanshi yasa ya juya moving towards the direction da ze Kai shi can ɗin, ƙaton ruwa ne da har ba'a ganin ƙarshen sa dan a yadda arɗo ya bashi labari babban ruwa ne da ya ratsa ta cikin garuruwa ko ace ƙauyuka uku bayan nasu, ƴan mata ne birjik a wajen kowacce riƙe da tulun ɗibar ruwan ta yayinda gefe kuma samari da dai ƴan matan masu wanka na yi kowa dai na abinda ya sa kan sa.


Daga gefe kaɗan ya hango ta zaune a bakin rafin ta zura fiye da rabin ƙafafun ta cikin ruwan tana wasa dashi, kan buɗaɗɗen gashin ta ya sauke idanun sa takaici na kama shi dan ko jiya seda ya sake mata maganar fita ba ɗankwalin nan shine yau da ta ga ya fita da wuri ta fito a hakan, gurin nasu ya fara dosa dan su waje huɗu ne zaune a wajen suna hira yayinda gogar take ta dariya da alama labari ake bata......................✍️.












©️ Ouummey 📚✍️.














☑️Ote, Comment and share fisabilillah.






























Ouummey 38 (8/27/2022 12:38 PM )





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________


















Page 3️⃣8️⃣






























_________________________📖 Ɗaya daga cikin ƙawayen Bingel ce ta fara ganin shi aikuwa ta washe baki da sauri tana faɗin


"Kwarankwatsa ga kaɗo me shau nan yana zuwa, Bingel ka gani shi ne ko?".


A zabure Kisnah ta miƙe tsaye bayan ta zare ƙafafuwan ta daga cikin ruwan ta shiga zarar ido na rashin gaskiya dan tasan laifin ta, yace kar ta fita ta fita yace kar ta kuma fita ba ɗan kwali kuma bata saka ba, to amma me ya biyo ta ya mata dan duk fitar da take be taɓa biyo ta ba se yau.


Damƙar da yayi wa hannun ta ya saka ta ɗago ta ɗan kalle shi cikin alamun rashin gaskiya, haɗewar da ta gani kan fuskar sa yasa lokaci guda cikin ta ya bada ƙara, ƙululu, sosai ta tsorata dan zata iya cewa bata taɓa ganin ɓaci ran sa ba irin na yau shiyasa ta shiga neman abinda zata faɗa dan kare kanta in sun kai gida.


Be gama shan takaici ba se ganin yadda duk inda suka wuce se kaji ana mata magana daga maza har mata, wani me neman wajen zaman ma tasowa yayi daga inda yake zaune ta sha gaban su da sauri yana faman washe baki


"Kaɗo kana lahiya, yau baka jo ka karɓi lemon ka ba".


Ya faɗa yana miƙa mata wani ƙaramin buhu me kamar leda da yake cike da fruits, a yadda Bingel tace mata ɗan ƙanwar Nenne ne shiyasa ta sake masa fuska suke gaisawa yayinda shi kuma hakan yake sa shi cikin farin ciki yana yi wa mazan garin kurin kaɗo kyakkyawa yana kula shi kamar yadda suke kiran ta, Saraki kuma kaɗo me kyau, tun daga lokacin da ta nuna tana son fruits shikenan kullum se ta tsinko mata ya bata ita kuma duk in ta kai gida ta gyara ta sha ta ajiyewa Saraki in ya tambayi ina ta samo cewa take ita ta tsinko ko Bingel, to yau da wuri suka gama kiwo shiyasa basu haɗu ba shine fa ya bata yanzu da ya ganta.


Wani irin ƙululu cikin ta ya bayar amma se ta dake ta sa hannu ta karɓa tana mishi godiya shikuwa se aikin dariya yake yana faɗin gobe me yawa ze samo mata.


Figar hannun ta Saraki yayi suka yi gaba batare da ya bari sun ƙarasa shirmen su ba suka bar isuhulle tsaye yana ɗaga mata hannu tare da faɗin ta fito da wuri fa gobe.


Da sauri ta saka hannu ta dafe garin su na ƙasa wanda ba dan tayi haka ba tabbas da ƙasa zata faɗi saboda turo tan da yayi da ƙarfi.


Ko gama tsayuwa daidai bata yi ba ya ƙara so gaban ta yana huci kamar wanda ya haɗiyi garwashi idanun sa sun sauya launi saboda ɓacin rai, ƙanƙame jikin ta tayi jikin bangon ɗakin kamar zata koma Cikin sa saboda fargaba da tsoron Sarakin, kallon ta yake yana tuno yadda ta zagaye gari kanta buɗe ga shashancin da take yi da mazan garin, ɓacin ran da ya sake tuƙo shi yasa ya dunƙule hannun sa ya kaiwa garun da take tsaye jikin sa nauyi, runtse idanun ta Kisnah tayi jikin ta na ɗaukar rawa dan ta zata ita ze nausa sedai da suari ta buɗe idon jin ƙarar zubar ƙasa a bayan ta, zaro ido tayi waje ganin yadda gurin yayi rami yar ya fasa waje, da sauri ta juyo ta dubi hannun sa da duk ya kukkuje yana fitar da jini.


Ɗagowa tayi da niyyar yi masa magana sedai ya riga ta buɗe baki


"How dere you, eyeh nace how dere you in Baki umarni ki ƙi bi, ban ce kar ki fita ba shine tsabar raini ki ka saka ƙafa kika fice and to make it worse ba ma ɗan kwali dan ki nuna min ban isa ba bazan faɗa miki kiji ba, kina tafe kina shashanci da mazan gari ko?".


Kai ta shiga girgiza masa da suari alaman ba haka bane kafin da ƙyar tayi summoning courage ɗin yin magana


"Allah ba haka bane yaa, banga zanin da nake sawa a kaina ba shiyasa kuma..........".


"Will you shot your stupid mouth ko sena kwaɗa miki mari a gurin?".


Tsawar da ya daka mata ya katse abinda take son faɗa ta maza ta saka hannun ta ta ƙara taushe bakin ta, mugun kallo ya cigaba da yi mata kafin kuma ya saki ƙwafa ya matsa inda buhun kayan marmarin da ta shigo dashi ya faɗi ya ɗauka ya fice.


Ajiyar zuciya ta saki tare da zame wa ta zauna a gurin tana dafe ƙirjin ta da hannu, dama haka yake? Abinda ta shiga tambayar kanta kenan kafin kuma ta jijjiga kai, amma fa ya bata tsoro, tayi zaton dukan ta ze yi irin yadda taga jikin sa na rawa saboda ɓacin rai.


Bata san ze ɗau zafi har haka ba da bata fita ba ɗan kwali ba, ganin ba yau ta saba fita hakan ba kuma a gaban sa tun suna manya yasa bata ɗauki fitar ta ba scarf a komai ba bayan haka ma suma matan garin basa sa komai a kan su suke ficewa, to me ze sa yaji haushin ta ita, ta ƙarshe tananin ta tana tura baki.


A can waje kuwa Nenne Saraki ya bawa kayan marmarin yace nasu ne kar a taba dasu suna dashi a ɗaki ta kuwa karɓa tana godiya, can wajen zagaye bukkar su ya fita ya zauna dan in ya koma ɗakin su a yadda yake ji ze iya sa mata hannu and baya fatan hakan ya fara faruwa tsakanin su tun yanzu, a rayuwar sa ya ƙi jinin namiji me dukan mace dan a ganin sa rashin tunani ne da hauka so ba ze so ya zama one ba .


Haka ya zauna wajen yana kallon yadda kowa yake al'amuran sa batare da sa ido ko wani ya damu da wani ba har duhu ya kawo jiki amma ko tunawa da yunwar cikin sa be yi ba dan tuni ɓacin rai yasa ya manta da ita.


Seda yayi sallar magrib nan waje cikin wani ɗan fili da suka yi wa gini kamu bakwai da bulon su na ƙasa da sunan masallaci kafin ya shiga gidan, kan tabarmar kabar da ya tadda arɗo ya zauna suka shiga tattauna batun seeds ɗin da ze noma a filin da aka bashi, sunyi nisa a batun gonar kafin ya shigo da batun tafiyar su nan da kwana biyar, shiru arɗo yayi yana bin shi da kallo yayinda shi kuma ya sunkuyar da kan sa ƙasa har arɗon yayi magana


"Anyi muku wani abu na rashin kyautawa ne Ahmad da kake batun tafiya?".


Da sauri ya ɗago yana sakin murmushi wa arɗo ganin yadda duk tsohon ya damu


"Ko kaɗan arɗo, sedai kamar yadda na sanar da kai kuma ka gani haɗari ne ya kawo mu zama da ku, kuma alhamdulillah ku ɗin mutane ne na gari dan kun karɓe mu batare da sanin ko su waye mu ba haka batare da neman komai daga gare mu ba, kayi haƙuri arɗo sedai zamu tafi ne dan iyayen mu suna can cikin tashin hankalin rashin sanin ina muke da kuma wane yanayi muke amma ba wai dan kun gaza damu ba, a zamanin nan bana tunanin za'a samu mutane masu matuƙar karamci irin ku arɗo".


Murmushin jin daɗin yabon da aka yi musu arɗo ya saki yana gyaɗa kan sa at the same time cikin yarda da batun Ahmad ɗin,


"Hakane Ahmad, daɗin zama yasa na manta da ya kamata iyayen ku su san halin da kuke haka su san kuna raye, ban ji daɗin jin zaku tafi Ku bar mu ba amma hakan ya zama dole, kar ka damu Allah ya kaimu ranar".


Da Amin saraki ya amsa masa suka cigaba da hirar su har Nenne ta kawo musu abinci da ya kasance kwaɗon rama ne, tare suka saka hannu suka ci suka sha ruwa sannan suka ɗora firar, basu tashi a wajen ba seda arɗo yayi wa Saraki sallama kan yaje ya kwanta sannan ya tashi ya shiga bukkar su ba dan yaso ba.


Duk hirar da suka yi Kisnah na jin su dan takarar dake tsakanin bukkar su da ta su arɗo ba me nisa ba ce dan ana iya jin komai dake wakana a waje , ba ƙaramin farin ciki tayi ba jin batun zasu bar garin in five days time, Allah ya sani tana rayuwa ne kawai cikin nuna all is well alhalin ba haka bane daurewa kawai take amma she is not used to all in the environment, kiwo da zuwa rafi ne kawai abinda tasan tana yi da zuciya ɗaya yake kuma sata nishaɗi da farin ciki se kuma da green view of the palace shima is something lovable to her.


Jin ze shigo ɗakin yasa ta takure jikin ta waje ɗaya tare da kwanciya kan buhun da take zaune, baccin ƙarya ta nuna tayi har lokacin da na gasken ya ɗauke ta gaba ɗaya a yadda take, ko kallon inda take be yi ba ya wuce wajen kwanciyar sa ya gyara shimfiɗar sa duk da a gyare take ya zauna tare da karanto addu'ar baccin sa ya shafa yakai kwance abinsa.


Ya daɗe kafin bacci ya iya ɗaukar sa saboda kayan jikin sa, kullum haka yake fama dan shi be iya bacci da kaya a jikin sa ba most especially riga sedai a nan dolen sa ya kwanta da ita tunda an haɗa shi kwana guri ɗaya da wannan yarinyar, bayan haka kuma rigunan su masu nauyi ne saboda na saƙi ne.


Asubar fari yayi Sallah tare da sammakon tafiya gona, cikin kwanakin da suka biyo baya gaba ɗaya ya maida hankalin sa kan gonar dan so yake yayi ya gama dasa irin su tarkata su bar garin dan ya ishe shi, har kwana uku basa wani good times da ita dan fushi yake sosai, iya gaisuwa ke shiga tsakanin su kawai, in ta gaishe shi ya amsa mata da lafiya shikenan.


Ganin yadda ya ɗau fushi yasa ta kama kanta ta tsaya iya matsayin ta bata wani shisshige masa kamar da, in ya dawo yana ɗakin zata fita waje gurin su Nenne tayi zaman ta se dai in an kawo musu abinci sannan ta kai ɗakin su ci dan a kwano guda Nenne ke haɗa musu abinci, haka zasu zauna cin abincin shiru bame cewa komai, in sun gama ta ɗauka ta fita da ƙwarya to akushin ta cigaba da zamanta cikin su se lokacin da Nenne ta kore ta tukun take musu sallama ta shiga taya shirin bacci ta kwanta.


Ciki kwanaki huɗu kamar yadda yayi fata ya gama shuka seeds ɗin gaba ɗaya wanda ba abinda arɗo yayi a ciki se gyara masa in da ya kuskure har aka gama.


Ranar kam basu dawo da wuri ba duk da da wurin ya gama amma se arɗo ya ɗauke shi suka dinga zagaya gonakin da da kuma na maƙwaftan sa yana ganin yadda shukokin suka yi kyau sosai, nan suka ɓata lokaci har bayan isha kafin suka dawo, ko da suka shigo gidan ruwa kawai ya watsa tare da canja ya fita wajen arɗo dake zaune kan tabarmar sa dake gefen su Nenne, Bingel da Kisnah.


Tare suka cigaba da hirar gaba ɗaya cikin farin ciki da kuma kewar su Kisnah da zasu bar garin gobe, kayan marmarin da su arɗon suka shigo dashi Nenne ta gyara ta ajiye wa Saraki da arɗo tare a gaban su su ma su uku nasu a haɗe.


Basu tashi daga zaman ba se kusan karfe goman dare sannan akayi sallama kowa ya nufi ɗakin sa, gyara masa shimfiɗar sa tayi lokacin yaje banɗaki sannan ta koma ta gyara tata da tsurar buhu ne se zanin saƙin da yayi laushi saboda shan ruwa da take haɗawa ta kwanta a kai.


Ko kafin ya shigo tuni tayi baccin ta dan ita kam bata da nauyin yin Bacci, wuyar ta ta kwanta tuni zata yi baccin ta abin ta, haka damuwa bata hana ta bacci shiyasa yanayin rayuwar ta ya zo mata da sauƙi dan irin cases ɗin da suka wanzu a rayuwar ta ba kowa ce zata iya ɗauka ba, sedai ba fa wai bata damuwa bane a'a abin dai na zuwa mata da sauƙin ne dan rashin bacci ma babbar damuwa ce dake assasa cututtuka da dama.


Kashegari da wuri suka shirya dan akwai tafiya sosai kafin su shiga cikin gari, basu ɗau komai ba da yake sunan nasu dan ba abinda zasu yi dashi ko sun ɗauka ɗin, se a lokacin ne kuma arɗo ya kawo wa Saraki kayan sa da ya tsince shi da su a jikin sa, be yi zaton kayan zasu sake amfanuwa ba se gashi an kawo masa su a wanke, faɗar farin cikin da yayi a lokacin ɓata baki ne, kayan ya koma ɗakik su ya canja yana yiwa arɗo godiya yana fitowa kuwa se suka ga kamar bashi ba dan se ya canja musu sosai a cikin shigar, ita kanta Kisnah se taga yayi mata wani irin kyau dan har ta fara sabawa da ganin sa cikin shigar fulanin dajin.


Nata kayan Nenne ta bata suma an wanke har da ɗin ke guraren da suka yage sedai a idon ta ba zasu sawu a jikin ta ba dan haka kimonon kawai ta ɗauka ta ɗora kan saƙin jikin ta tare da scarf ɗin ta duk da shima ya sha ɗinki.


Cikin matuƙar kewa Kisnah tayi sallama dasu Bingel da Nenne kamar kar su rabu, shaƙuwar kenan, amalanken da arɗo ya tarar musu suka hau aka shiga loda musu tsarabar da su arɗo suka basu, ƙwaryar zuma me kyau guda biyu haka fresh sabon nono ƙwarya uku se curin fura dake cikin wata ƙwayar daban.


Haka me amalanken yaja suna ɗagawa juna hannu dasu Nenne dan shi arɗo se ya kaisu tasha, seda suka fara biyawa gidan baffa arɗo suka yi masa sallama shima ya basu tasa tsarabar ta kayan fruits har buhu biyu sannan suka tafi, duk inda suka bi haka ake ta ɗaga musu hannu dan kaɗan kaɗan ne basu san Kisnah ba kasancewar ƙauye kowa ya san kowa har suka yi nisa da mutane suka fara shiga dokar daji.


Kamar yadda arɗo ya faɗa tafiyar ba kaɗan bace dan se da rana ta ɗaga sosai sannan suka kai tasha, akori kura ne da yawa a wajen matsayin motocin tafiya, dole

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads