Showing 81001 words to 84000 words out of 104570 words
Chapter 28 - SARAKI (The Accused Prince).txt
namiji kwana takwas da suka wuce, a yanayin da na tsince su suna tsananin buƙatar taimako, a nawa idanun se na ga kamar ma'aurata hakan ne ma yasa na ɗauke su ba tare da wani tunani ba, yanzu haka ita macen ta sami lafiya har ta iya fita jiya shine suka haɗu da lamiɗo, shi kuma namijin yana jinyar karaya ne a hannu duk da cewa hadda gocewar ƙashi a ƙafa amma tuni wanann ya warke, tun ɗazu da aka sanar dani abinda ya faru da har lamiɗo ya nemi na zo fada nasan nayi kuskure, nayi kuskuren ɗaukar matasan matsayin mata da miji haka nayi kuskuren rashin sanar da kai labarin su, a yimin afuwa baffa arɗo, hakan ba zata sake faruwa ba nayi alƙawari".
Gyaɗa kai kawai baffa arɗo ya dinga yi har arɗo ya gama bayanin sa kafin ya amsa shi
"An maka afuwa arɗo sedai kasan ya zama dole a miƙa wannan budurwa ga lamiɗo yau ɗin nan ba se gobe ba dan kaucewa fushin rauhanai".
"Yanzu za ayi hakan baffa arɗo, ina komawa gida zan rakota gare ka se a miƙa ta ga lamiɗo, Allah ƙara tsawon rai ina godiya da sassaucin faɗa gare mu".
******
Cikin rashin daɗin rai arɗo yake taka ƙafar sa kan ƙasa a hanyar sa ta komawa gidan sa, be taɓa sanin yarinyar budurwa bace da baze ɗauko su ba badan komai ba se dan guje mata shiga turakar lamiɗo sedai aikin gama ya riga ya gama dan ba yadda za iya tsallakewa umarnin baffa arɗo da boka wassai, dolen dolen sa ya kai ta ga lamiɗo dan hakan ne zaman lafiyar su daga shi har su.
Ko da ya ƙarasa gida zaune ya samu su Bingel da Nenne cikin fargaba, yana shigowa suka bishi da kallo cikin son bayani sedai bece komai ba har Nenne ta kasa daurewa ta tambaye shi da baki, shiru yayi na wasu lokuta kafin ya buɗe baki ya fara musu bayanin abinda ke akwai cikin rashin daɗin rai, fargaban su ce ta ƙaru jin abinda ke faruwa dan Allah ya saka musu ƙaunar Kisnah cikin zuciyoyin su, ba zasu so abu makamancin haka ya faru da ita ba sedai ba yadda zasu yi.
Arɗo ya daɗe zaune wajen ƴar sa da matar sa nan ƙofar bukkokin su dake kusa da kusa da juna kafin ya yi ƙarfin halin miƙewa ya shiga ɗakin da Saraki yake dan ya sanar dashi abinda ke faruwa kuma dama Nenne ta sanar dashi Kisnah na tare da Saraki a ɗakin.
Da sallamar da ya koyo a birni da yake kai kaya ya shiga ɗakin fuskar sa ɗauke da damuwa ƙarara, da sauri Saraki ya buɗe idanun sa da ya rufe yana kallon shi tare da ƙoƙarin gyara zaman sa
"Sannu da shigowa arɗo, sannu da zuwa".
Be sami zarafin amsawa Saraki ba ya samu waje ya zauna daga gefen damar Sarakin yayinda Kisnah ke gefen dama, shiru suka yi a ɗakin ba wanda yace komai kafin arɗo ya daure ya tambayi jikin Saraki
"Ya jikin naka?.
"Da sauƙi arɗo, ina iya motsa hannun ma a hankali baba".
"Angodewa Allah, Ina maka fatan samun sauƙi cikin sauri".
Da Amin Saraki ya amsa suka sake yin shiru na tsawon lokaci
"Kayi haƙuri Ahmad, ban ɗauka za'a sami matsala ba da zaman ku a nan shiyasa ban sanar daku wani abu ba dangane da garin namu sedai gashi wata matsala ta Kunno Kai da tafi ƙarfin magance wa ta, ban san ya zan maku bayanin abinda ya faru ba dan shigowa ta ɗin nan daga gidan baffa arɗo nake wato me garin mu".
Zuba masa ido Saraki yayi cikin son matsalar da yake maganar tana son faruwa, fatan sa ɗaya Allah ya sa ba a fitar yarinyar can bane taje ta jawo musu wata maganar, shikam be san ya ze yi da ita ba, in suka bar nan ina zasu je, har yanzu ma basu san takaimaimai a wane garin suke ba su dai sun farka sun gamsu a wannan ƙauyen kuma be wani damu da ya tambayi ina bane tunda ba lafiyar barin garin gare shi ba.
"A shekarun baya munyi fama da wata annoba sanadin wata budurwa mayya da ta shigo mana, a cikin neman masu maganin da muke ne Allah ya kawo wassai garin nan da ya zama sanadin samun sauƙin al'amuran har muka dawo muka cigaba da rayuwa kamar da sedai ya kafa mana wasu sharuɗa da muke rayuwa a wannan ƙauyen akan su, sharaɗin shine ba karɓi baƙuncin budurwa mara aure ba in kuwa hakan ya faru to za mu miƙa ta ga Sarkin gobe lamiɗo auta ga Sarkin yanzu ya tare da ita a turakar sa na tsawon sati ɗaya.
Kayi haƙuri a lokacin da na tsince ku na yi zaton mata da miji ne shiyasa ban ji ko ɗar ba na ɗauko ku zuwa wannan garin, a fitar da yarinyar tayi jiya suka haɗu da lamiɗo kuma ya gane budurwa ce ba matar aure ba saboda wassai ya basu maganin da zasu dinga gane budurwa da matar aure shi da baffa arɗo dan gudun yaudara, yanzu haka baffa arɗo da lamiɗo suna jira ne na miƙa wannan yarinya ga turakar lamiɗo a yau, shine nazo na sanar da ku".
Kallon sa kawai saraki yake yana fassara dukkan bayanin sa tare da miƙa shi matatar bayanai wanda cikin lokaci kaɗan ya fahimci me arɗon yake nufi, in akace tashin hankali to kaɗan kenan, taya ze yarda haka ya faru? Ta ina ze iya zuba ido har hakan ta kasance? To meye ma amfanin guduwar su daga waɗancan makasan, meye banbancin wannan sharaɗin da bindiga hannun ƴan ta'addar kawu, in hakane ma gwara da ace tsayawa yayi aka kashe su gaba ɗaya, a ganin sa waccan mutuwar ma tafi sauƙi kan wannan batu dan mutuwar tsaye ne kawai.
A hankali ya juya ya dubi inda take kwance tana bacci peacefully, baccin da kana gani zaka san ta kwana biyu bata samu irin shi ba.
Dawo da duban sa yayi ga arɗo dake zaune ya duƙar da kai ƙasa, abubuwa da yawa ke zuwa ransa sedai ya rasa wanne ze yi, me ze yi da zai cece ta, ya sani baze yiwu yace zasu bar garin ba dan bashi da isasshiyar lafiyar tafiya dan har yanzu ba wai hana taka ƙafar sa bane an dai kunce ɗaurin ne, to idan ma zasu tafi ina zasu nufa su da basu san a ina suke ba haka kuɗi fa, su da basu da ko sisi dame zasu tafi, dole ya ajiye ma wannan batun dan ba mafita bace.
"Yanzu babu wata mafita ga hakan arɗo dan bana tunanin zan iya yadda da wannan sharaɗin na garin ku".
Girgiza kai arɗo yayi cikin son tabbatar wa
"Kayi haƙuri samari amma babu wata mafita se hakan".
Sake yin shiru suka yi ya rufe idanun sa cikin karanto duk addu'ar da ta zo bakin sa, fatan sa Allah ya bashi wata mafita da zata kange wannan matsalar dake neman kutso kai rayuwar su banda kuma wadda suke ciki.
Tunani yake yi sosai har yayi zurfin da be san lokacin da arɗo ya tashi Kisnah ba, ƙoƙarin fita da suke yi ita da arɗo ya sa ya farga haka kuma a lokacin ya yanke shawarar da yake ganin ita kaɗai zata kore wannan musiba dake neman danno kai gare su, da sauri ya dakatar da arɗo dake neman bin bayan Kisnah da ta riga ta fita
"Zan je fada arɗo, Ina son na biku dan Allah".
Tsayawa arɗo yayi cikin ɗan ƙure shi da kallo kafin ya girgiza kai
"Ta ina zaka iya bin mu Ahmad, har yanzu ba wai ƙafar ka ta gama lafiya bane".
"Kayi haƙuri amma dole na biku bana, akwai abinda nake san sanar da Sarkin ku".
Ganin ya dage yasa arɗo nemo me amalanke ya biya shi sannan suka kama Saraki suka taimaka masa ya shiga kafin shima da Kisnah suka shiga me amalanken ya ja, tsakanin su da gidan Sarkin akwai tafiya sosai sedai gare su ba wata tafiya bace, rashin lafiyar Saraki yasa ya biya amalanke da da ƙafar su zasu taka su je.
A ƙofar fada suka sauka nan ma arɗo da me amalanke ne suka taimaka wa Saraki zuwa cikin fadar Kisnah na bin su tana ƙare wa gurin kallo.
Ginin ƙasa ne gaba ɗaya ba kamar nasu dake da su asabari da yayi ba, ƙaton fili ne da aka ahimfiɗe shi da tabarmin kaba se daga can nisa bukkokin iyalin sa suke an zagaye wajen da asabari.
Zaunar da Saraki suka yi me amalanke yayi gaisuwa ya fita waje yana jiran su gama ya mayar dasu dan kuɗin zuwa da komawa arɗo ya biya, Hausar da sarki suka yi kafin arɗo ya shiga yiwa sarki bayani
"Gasu nan baffa arɗo, su ne matasan da na tsinta, ga macen da lamiɗo ya gani ga kuma namijin nan".
Kallon su ɗaya bayan ɗaya baffa arɗo yayi kafin ya aika aka shiga cikin gida kira masa lamiɗo, ba jimawa ɗan aiken ya dawo tare da lamiɗon da tun da ya shigo idanun sa na kan Kisnah yana Binta da wani mayen kallo saboda yadda jikin ta yake luƙwi luƙwi ba alamun rama ga laushin da ya san fatar ta zata yi uwa uba ga diri, duk gaisuwar da suka masa hankalin sa baya gare su ya amsa sa'annan ya kai zaune gefen baban sa.
"Kije gare shi yarinya, zaki kasance dashi a turaka na kwana bakwai".
Arɗo ne ya fassara musu abinda baffa arɗo ya faɗa dan su ba jin Yaren su ke ba sedai shi baffa arɗo yana jin Hausa mayarwa ne ba ya iya yi, wani kallon rainin hankali Kisnah tayi musu sedai kafin ta buɗe baki ta faɗi abinda tayi niyya Saraki ya riga ta
"Allah ya ƙara masa tsawon rai wannan yarinya da ake magana a kanta tana amsa sunan matata ne dan kafin mu sami hatsarin da yayi silar shigowar mu garin ku an riga na biya sadaki da komai na aure kawai ana jiran lokaci ne se wannan ƙaddarar ta afku".
Da wani irin sauri Kisnah ta juya gare shi tana kallon shi baki buɗe ido zare sedai tunda ya fara magana yawun bakin ta suka ƙafe hakan yasa ta kasa furta komi se bin shi da kallo shikan ƙin kallon ɓangaren da take yayi dan yana jin yawon idanun ta a cikin jikin sa, shima ba a san ran sa ze Fadi hakan ba sedai ba yadda za yi wannan ce kaɗai mafitar da yake hasashen zata hana faruwar abinda ke gab da aukuwa.
Gyara zama baffa arɗo yayi yayinda lamiɗo ya ɗago da sauri yana aikawa Saraki mugun kallo da ƙananun idanun sa
Magana baffa arɗo yayi cikin Yaren su yayinda arɗo ya ke fassara musu
"Baffa arɗo yace in dai haka ne to sedai su baka zaɓi biyu kuma dole ka zaɓi ɗaya a ciki ka yarda?".
Gyaɗa kai Saraki yayi duk da be san wane irin zaɓi bane amma ya tabbatar ze samu na ɗauka a ciki insha Allah
"Yace ko ka yarda a ɗaura muku aure yanzu a nan dan mu dole haka sharaɗin mu yake budurwa bata zama mana se ta kwanta da lamiɗo ko kuma in ba zaka aure ta yanzu ba to tabbas lamiɗo ze wuce da ita".
Arɗo ya ƙare fassara wa Sarakin yana bin shi da kallo dan jin wanne ya zaɓa.
"La'iha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimeen". Addu'ar da saraki ya shiga maimaita wa kenan cikin ransa dan tabbas yana cikin tsaka me wuya da dole ya nemi taimakon Ubangiji.
"Kayi shiru yaro, ka amsa mana da abinda ka zaɓa dan Musan abinda ya dace a yi.
Bashi da zaɓi da ya wuce buɗe bakin sa yayi magana, a lokacin, a lokacin ne kuma ƙaddara ta buɗe sabon shafi a rayuwar sa, shafin da be san da wani irin suna ze Kira shi ba abu ɗaya ya sani shine ƙaddara ke juya rayuwar sa a lokacin kuma bashi da wani zaɓi illa ya bata dama tayi duk yadda taso dashi da rayuwar tasa.
********
Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ya sauke yana me runtse idanun sa, bit by bit ya shiga tuno rayuwar sa tunda ga yarinta, zaman sa da mahaifiyar sa da irin so, ƙauna da shaƙuwar dake tsakanin su, ƙannen sa da halin kowanne a ciki, tafiyar sa karatu ƙasar waje, rayuwar sa a ƙasar da ba tasa ba, gama karatun sa da fara aikin sa zuwa dawowar sa, farin cikin da ya kasance a ciki na zama tsakanin iyayen sa da suke so da ƙaunar sa ga kuma ƙannen sa masu biyayya gare shi, Laylah da irin son da take nuna masa duk da ya nuna be gane ba, yarinyar da ban da yau be sake tuna ta an tun da ya baro masarauta dan je has no feelings for her ko kaɗan, shigowar Husna masarautar da kuma yadda ƙaddara ta fara nata sharafin da rayuwar sa, shigowar sa garin manya, haɗuwar sa da idriss, zaman sa kantin Alh Musa, shigowar Kisnah rayuwar sa ko shigar sa rayuwar ta ze ce, yarinyar da be san da me ze kwatanta haɗin da ƙaddara tayi musu ba, abu ɗaya za iya cewa shine ya ɗauke ta kamar Miemie ƙanwar sa ne, kulawa da kariyar da yake bata duk domin wancan matsayin ne se gashi lokaci ɗaya ƙaddara ta yi juyin masa da wancan matsayin ta bata wani matsayi da be shirya masa ba a yanzu, matsayin da yake ganin bata dace dashi ba haka kuma matsayin da be san da wane ido zasu dinga kallon juna dashi ba domin sa.
Wani irin nauyi yake ji a ransa da baya tantama nauyin bana komai bane se na gungumemen kayan da aka aza masa a kai, taya ze iya fara riƙe ta, da me ze kula da ita, be shirya ba , sam be shirya ba, ba tsarin sa kenan ba, ba lissafin sa ba kenan haka kuma a tanadin sa bane hakan.
Abinda saraki ya manta shine ita ƙaddara ba ruwan ta da tsarin sa, shirin sa, tanadin sa, lissafin sa ko burin sa...................!
"Alhamdulillah, aure tsakanin Ahmad da Sakeenah ya ƙullu, Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba ya tabbatar da kasancewar ku tare har abada". Kalaman limamin ke ta maimaita kansa a kunnen sa haka kuma idan har ba mantawa yayi ba a lokacin kalmar *Ameen* ta suɓuce daga bakin sa wanda ba ita yayi niyyar furtawa ba har zuciyar sa sedai be san me yasa harshen sa ya canja masa akala ba.
A hankali ya juyar da kansa yana ƙare wa sabuwar bukkar da aka canja musu kallo wadda aikin baffa arɗo bane, sannu a hankali yana yawatawa da idanun sa cikin bukkar har idanun sa ya faɗa kanta, ita ɗin dai da komai yake faruwa sanadin ta, ita ɗin dai da ta yi sanadin buɗe sabon babi wa rayuwar sa rayuwar sa, bacci take, bacci fa bayan shi gashi nan ya kasa ko da runtsa idanun sa a dalilin ta kuma a sanadin kare ta.
Haka Saraki ya ɓata daren da ya kasance daren auren su cikin tsananin tunani, tunanin mafita game da wannan bahaguwar ƙaddarar tasu, tunanin mafita kan wannan auren nasu da be san da tunanin da ze kira shi ba, be samu sauƙin nauyin da zuciyar sa tayi ba seda ya samo *mafita*, mafitar da yake ganin itace daidai kuma abinda ya dace.
Sake kallon wajen da take kwance yayi yana watsa mata zazzafar harara ganin yadda take bacci hankali kwance batare da ta damu dashi wane halin yake ciki ba a sanadin ta...........................✍️.
Wihuhu🤸🤸🤸🤸🤸 anzo wajen 💃💃 wallahi anzo💃💃💃.
Saraki ya zama na Kisnah Kisnah ta zama ta Saraki 💃💃💃💃.
🎶🎵Ai wannan bikin gidan mu neeee🎶🎵
🎵🎶Ɗaurin auren yayan mu neeee🎵🎶.
Ku zo mu taka team #sarakisna.
🎶💃biki yayi biki ashe da dangi muka kuriiii🎶 matan garin mu ba'a nuna musu komai💃💃💃
🎵🎵Daga munji ɗan kiɗan sa se rawa, sama mata💃💃.
©️ Ouummey 📚✍️.
☑️Ote, Comment and share fisabilillah.
Ouummey 34 (8/25/2022 9:56 PM)
💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠
Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey
*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*
______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________________
Page 3️⃣4️⃣
________________________📖 Hasken da ya ratso ta tsakankanin asabarin ɗakin ya haske masa fuska yasa ya fara motsa idanun sa a hankali har ya buɗe su gaba ɗaya, kallon ɗakin ya shiga yi kafin ya zabura cikin son miƙewa sedai tuni ya koma saboda zugin da ya ratsa hannun sa ya kai tsakiyar kansa.
Seda ya ɗan yi mintuna a kwance kafin ya yunƙura ya zauna a dabarance, hasken da ya shigo ta duk wata kafa ta jikin asabarin ya tabbatar masa da gari ya daɗe da waye wa har rana ta fito gashi ko sallah be yi ba, takaici ne ya kama shi dan baze iya tuna yaushe ya makara sallar asuba ba, haushin sa ya fi ta'alkaƙa ne kan rashin baccin sa da wuri ne ya ja masa makarar wadda duk sanadin tunanin mafitar wannan ƙaddararren auren da aka ɗaura masa jiya ne.
Duban gefen da yasan take kwance yayi ya ga bata nan, kenan ta tashi ita tayi sallah amma shine ko ta tashe shi, ƙwafa yayi yana me jin zafin hakan a ransa.
Daga zaunen da yake yayi gyaran murya cikin babban sauti dan haka yake yi se arɗo ya shigo ya taimaka masa zuwa matsuguni kafin ya dawo dashi yayi alwala.
Nenne da ke zaune tare da Kisnah tana taya ta mulmula furar da take curawa wadda sana'ar tace ta juyo gyaran muryar Saraki hakan yasa ta dubi Kisnah da ta maida hankalin ta kan furar gaba ɗaya
"Tashi yalo mijin ka na kila".
Tsayawa da abinda take Kisnah tayi ta shiga kallon ta dan bata fahimci me take cewa ba, sake maimaita wa Nenne tayi amma ita bata gane komai ba se miji kawai, seda ta nuna bukkar su tana sake